Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
din a lokacin da na tsaya a inda ba a ganina sai na cire Hijab din na cigaba da aikina hankalina a kwance. Wani abun burgewa ashe na wadanda suke reception din har da abincin ake kawo musu da ruwa tsabanin da da sai dai yunwa da kashe ni.    Mu uku muka je cin abincin tare da blessed da Walid, muna cikin cin abincin yake dauko mana labarin sabon kamfanin da za ake tunanin budewa a wata jihar sai dai suna tantamar garin da za a bude, mun dade muna tattaunawar har nake bayarda shawarar da ace za su yarda da sun bude a Kano domin can ne cijiyar Kasuwanci, ko kuma Jos duba da yanayin garin Walid kuma yace Abuja, a haka dai muka gama cin abincin muka tashi muka koma gurin aikinmu su biyun da basu ci ba suka koma ciki dan cin abincin.   Ina tsaye a gurin sai ga wasu fararen mutune sun shigo, da fari dai na dauka turawa ne, a take hankalina ya koma gurinsu tun kan su karaso nake ta kallonsu cike da burge domin kusan sai nace ban taba ganin turawa a zahiri ba sai yau, sai dai na lura sauran abokan aikina ba kamar ni suke ba, wata kila sun saba ganin turawa ba kamar ni ba da na zama bakwaya har murmushi nake musu kamin su karaso.   Ko miye abun burge a farar fatar ma oho sai kace ni din ba fara bace ko da yke nawa farin mai kyau ne, domin na su ba shi da kyau kallo farin yayi yawa har wani kashe ido yake.   Suna isowa sa abokin aikinki ya tarebe su da yaren turanci su kuma suka masa magana da faransanci hakan yasa na fahimci cewar faransawa ne ba turawa ba kamar yadda nake zato. Hakan yasa na yi kaudin yin musu harbun da tambayar abunda suke bukata a dan abunda na iya na yaren faransanci. A take suka mayarda min da amsa, aiko nan dade ya kusa kashe ni wai ni na magana da wanda ba yare ba kuma ba yan kasa ta ba. Da suka fada min wanda suke bukatar gani wato shugaban kamfanin sai na fadawa Walid shi kuma ya nuna min yadda zan yi na kira na sanar idan bukatar irin haka ta taso, kamin na danna number wanda yace min shi ake fara kira a sanarwa, sai ga Yunus din ya fito daga cikin kamfanin ya tare su da far'arsa har ya basu hannu suka gaisa, sai dai shima na lura be iya faransanci ba kamar dai sauran abokan aikina. Godiya suka min da yarensu na mayar musu da godiyar nima sannan suka bi Yunus zuwa ciki. After like 15 minutes ya fito yana tambayar wai na iya faransanci ne sosai. “Gaskiya ba sosai ba gaisuwa kawai na iya sai dan abunda ba a rasa ba, ban iya sosai ba” “Amman za ki iya kula da su kamin mai fassara mana ya iso?” “Yes” “Good zo muje” Sai da na dauki gyalena na yafa sannan na bi bayanshi, sai dai a yanayin yadda yake tafiya ne yasa nai saurin cin masa duk kuwa da kasancewar ina tafe ina dingishi ne sai muka jera a tare muna tafiya a tare, ba laifi yana da sakin fuska da son magana ba kamar mugun gogan ba, a nan yake tambayar inda na iya yaren faransanci, na fada masa tun a secondary school na yaren yaren sosai lokacin da muna can sai dai shiga FUG yasa na manta da wani abu, ga kuma abubuwa na rayuwa sai na watsar da abun. Sai a lokacin da zamu shiga cikin office din ya bukaci na cire mayafin nawa, hakan yasa ni jin babu dadi wanda har ya bayyana a fuskata. “No ba wani dadewa za ki yi ba, za ki yi tambaye abunda suke bukata ne kawai sai kuma fara gabatar musu da abunda zan nuna miki kamin mai aikinmu ya iso” “Ba fa komai na iya a faransanci ba, ba zan iya wani dogon bayani sosai ba” “I know saboda kar mu barsu shiru ne, tun mun zama kurame mu da su” Ban musa ba na cire Hijab din kamar yadda ya bukata, daman can dankwalin atamfa ne a kai, ga farar riga da bakin wando na kamfani sai ya bada wani kala na dabam, na yi zaton su kadai ne a dakin taron, sai na tarar har da Angry Bird din ya wani shakimce a saman kujera yana ganina ya wani hade rai. Ni kuma na tsaya bakin kofa har sai da Yunus din yai min iso. Na shiga ciki na tambaye su abunda suke bukata na sha suka bukaci ruwa kawai, shi ma kuma da aka kawo ba su sha ba, abunka da marar yarda, haka nan dai cikin rashin iyawa na rika dan nuna musu abubuwan da Yunus ya nuna min, wanda suke a katon wani abu mai kamar tv kuma shi ba tv ba, da removed din hannuna na rika nuna musu kalolin zinarin da suke a ciki, domin ya fada min abun nan ja na jikin remote din kawai zan taba su za su rika canjawa da kansu. Muna haka sai ga mai fassarar ya shigo, na yi zaton idan ya shigo umarni za a bani na fice sai gashi ya saka ni cigaba da danna remote din shi kuma yana musu bayani da halshen faransancin, ina jin wani abu wani abun kuma bana gane komai, wani abun zai fada ma Ahmad da Yunus abunda suka ce ne sannan ya cigaba da yi musu bayanin, har akai aka gama Ahmad be ce komai ba, sai aikin tsutsar minti yake, ni kuma ban ma sake kallon inda yake ba. Sai da suka gaisa da shi sannan suka fice tare da mai fassarar, hakan yasa na aje remote din ina jiran a bani umarnin ficewa, amman Yunus din sai karin bayani yake ma Ahmad din. Ni kuwa hankali gaba daya yana gida ga garin ya hada bakin hadari kamar yadda nake hange ta cikin gilashin da ke gafenmu. “Ranka ya dade zan iya tafiya” Na fada ina kallon Yunus din a tare suka kalleni daga Ahmad din har Yunus ne. “Sorry yau mun baki aiki da ba naki ba” “Babu komai” Har na aje remote din ina kokarin juyawa sai yace. “Ta ina za ki bi? Na sauke ki” Kamin na bashi amsa Ahmad din ya tari numfashinsa sound so serious fuskarsa babu alamun wasa. “Shi kuma wacan aikin wa zai yi?” Nikam daman ba shiga motar zan yi ba, hakan yasa kamin ma Yunus din ya bashi amsa na ce wa Yunus din. “Na gode ranka ya dade zan fi sakewa idan na hau napep” Daga haka na juyo na fito daga office din ina mamakin irin kiyayyar da Ahmad ke min akan abunda har a gurin Allah bana da laifi domin ban aikata ba, wato yaji haushin da Yunus din yace zai rage min hanya ko waya fada masa ma shiga zan yi oho. Da tunanin hadarin na fito hakan yasa ban wani tsaya canja tufafi ba yafa mayafina na dauki kayan na saka riga a handbag dina domin ita kadai zata iya shiga sauran kuma na rike a hannu na bi hanya domin tuni abokan aikina sun wuce har wasu sun karbi duty. Ina tafiya aka fara yayyafi ban yi zaton zai yi karfi ba, hakan yasa na kara harama da zimmar kamin ruwan yai karfi na samu abun hawa, da ganin hadarin ba irin wanda idan an fara ruwan nan ba ne a daina, wata kila za a dade a na ruwan. Ko da na fita gate babu masu Napep sai achaba su ma kuma kowa da goyonsa, sai gudu suke ni kuma na maida himma sai tafiya nake ina waige waige ko zan samu abun hawan, ban nisa sosai da kamfanin ba aka sako da wani ruwa mai mugun karfi, hakan yasa ni cira kafa har da dan guduna na nufi inda wata yar rufar kwano wacce ke kusa da inda Kabir yake. Babu kowa a gurin hakan yasa na shige rumfar da sauri na fake, domin tuni ruwan ya fara jikani. Sai dai wani abun mamaki duk ruwan nan da ake Kabir na zaune a inda ya saba zama ruwan na duka kansa, ban san lokacin da tausayinsa ya rufe ni, da sauri na aje kayana da jakar hannu a gurin na fita a ciki a rumfar na nufi inda yake cike da karfin hali domin a yanzu kafar ta fi min zafi fiye da dazun. Da fari magana na fara masa akan ya taso ya bar gurin sai na ga yana ta kallona kamar be gane ni ba, hakan yasa na kai hannnu zan riko shi, aiko kamar jira yake sai ya hayayyako min yayi cikina yana zare ido abun be taba, ina baya baya yana cikina har samu sa'ar riko mayafina ya fisge shi gani a gafen titi hakan yasa nai unkurin gudu sai yai nasarar kai mun duka mai shegen zafi, ya kuma rikoni yana kokarin makureni. “Ni ce ni ce Kabir.....” Shine kawai abunda nake iya fada cikin ihu da daga muryar, tare da kokarin kwatar kaina amman ina karfin mace da namiji ba daya ba tuni ya samu sa'ar fara makurata, ga ruwan sama ana yi balle a kawo min agaji, ko ma ba a ruwan ba kowa ke shiga lamarin mahaukaci ba ballantana ma gurin babu jama'a sosai. Kamar daga sama na ji ana kokarin taimaka, sai duka ake kaiwa Kabir ta ko'ina ban san ko waye ba har sai da na samu sa'ar kubucewa daga hannunsa, ruwan dake sauka da kuma makurar da na sha bata hanani gane cewar Ahmad bane, abunda ban tana zato ba, ban tana tunani ba balle har nai mafarki yau yake faruwa a zahiri. Nikam ban tsaya komai ba ganin fadan ya koma tsakaninsu yasa na dauki mayafina da sauri na nufi inda jakata take na dauka tare da kayana na fara tafiya kamar an koroni ko waige inda suke ban sake ba. Sai da nai tafiya mai nisa sannan na soma tafiya a hankali ina cigaba ta taron Napep, cikin sa'a motar Abdallah ta wuce ni sai kuma ta dawo baya daidai ta tsaya daga can cikin motar ya bude min front seat. Da sauri na shiga jikina har rawa yake. “Ina kika fito?” Ni dai ban iya bashi amsa ba domin har yanzu ban gama dawowa daidai ba. “Ina kika fito...?” “Aiki” “Aiki da wadannan kayan? Wando ne fa a jikinki da riga..” Na dan kalli jikin nawa, ruwan da ya jikani yasa tufafin sun dan kama jikina. “Karki sake saka su daga yau, idan ba barki ki saka tufafinki na hausawa ba, ki daina aikin” “Am.... ” “Ba shawara nake ba ki ba, umarni ne” Ya fada yana daga min hannu fuskar nan tasa a hade kamar dai ba shi ba. AHMAD POV. Hannunsa ya kai ya ciro chewing gum din daga bakinsa sannan ya mike tsaye ya nufi window ya jefar da cingan din yana cigaba da yatsinar fuska.   Ai tun farko be kamata ya ci cingan din ba ko da ba ita ta aje masa ba balle kuma a hannunta ya fito macen da babu ta biyunta a gurinsa gurin tsana. Yawun bakinsa ya tofar a window Yunus dai be ce masa komai ba bayan kallon da ya bishi da shi sannan ya fice.   Haka ya wuni yana tofar da yawu kamar wani mai sabon ciki, yaba ta jin haushin tauna cingan din da yai, daga bisani ya koma jin haushin Siyama wacce ta bukaci ayi masa abun, kamin jin haushin ya koma gurin Yunus wanda yake ganin shi ya biye mata.   After sallah azahar Yunus ya shigo office din yana sanar masa cewar bakinsu sun iso. “Amman Dahir ya zo” “No yana kan hanya dai” “To ya za'ayi communication da su” “Karka damu da wannan, yanzu dai kaje ka gaisa da su” After haka ya fice, Ahmad ya bata minti biyar a zaune sannan ya nufi freezer dake office din ya bude ya dauko sweet ya bude ya saka a bakinsa, dan yasan ba zai je can yana tofe tofen yawu ba sai kace mai sabon ciki, idan ma be sha sweet din ba tashin zuciyar da yake ji ba ba zai bar shi ba. Sai da ya dauki rigarsa ya saka sannan ya nufi dakin taro, yana shigowa suka mike tsaye tare da bashi hannu ya gaisa da su da halshen nasara ya fara yi musu barka da zuwa duk kuwa da yasan ba lallai ace suna jin wani abu bayan welcome da kuma gaisuwa ba. A gurin daya saba zama ya nufa ya zauna, yana kokarin ciro wayarsa daga aljihu aka turo kofar dakin Yunus ne ya shigo, Halimatu na bayanshi ta tsaya daga jikin kofar har sai dai Yunus din yai mata iso, wani irin bugawa zuciyarsa tai, duk sai yaji ransa ya bace sai dai ba damar ya nuna a gaban mutanen a dole ta sa ya shanye, sai dai yana mamakin abunda ya kawo ta dakin taron. Takawa ta fara yi tana juya yai arba da mazaunanta sai yai saurin runtse idonsa duka biyu, can kuma ya bude dayar yayinda dayar take a makkale ya rufeta, sai kuma yai saurin rufewa yana jan tsaki a ransa. Be bude ba har sai da yaji ta fara magana da su alamar ta juyo kenan sannan ya bude ido, kallo daya yai mata yaga yadda kayan suka karbe ta sai kuma ya dauke kai. Har akai meeting din aka gama be bari ta san yana kallonta ba, ba ma ita ba ko Yunus da ke kusa da shi ba zai iya gano ya kalleta ba ko a'a domin ta kasa kasa yake kallonsa irin na munafukai. After sun gama ta bukaci fita sa Yunus ya nemi rage mata hanya a take Ahmad yai karaf ya hana shi, yana ta mamakin shisshigi irin nasa, after ta fice ya tabe baki ya tashi tsaye ya face daga kamfanin, office dinsa ya nufa yana kara jin bachin rai na kama shi, zaunawa yai saman kujerarsa ya rufe laptop dinsa sannan ya fito daga office din ya nufi gurin motarsa da sauri, so yake ko da za a sako da ruwan yana gida ko banza yau ai ranar birthday sa ne. A hankali yake tukinsa, sai dai kamar yadda ya kusan zame masa ibada kallon gurin da mahaukacin nan yake zama a kullum saboda abincin da Halimatu take ba shi yasa shi kallo a yau, yana tunani a yau kam ba zata tsaya ba tun da ta fita tana sauri kuma gashi garin har ruwa ya fara sauka, to his surprise sai ya hangota a gurin tare da shi, at first ya dauka ko wani abu ne mai kama da wasa daga baya ya fahimci kokuwa ce suke wanda be san dalilinta ba. “Ashe dai itama bata da hankali, daman can ba tai kama da masu hankalin ba” Ya furta sannan dan karawa motarsa wuta, kamin ya sake kallonsu da kyau ya fahimci dai fada suke, sai kawai ya faka yana ta kallon yadda mahaukacin ya kai mata duka kamin ya hango mahaukacin ya makureta har tana neman taimako. Cigaba yai da kallonsu, har sai da ya fahimci da gaske mahaukacin kasheta zai yi sannan yai unkurin bude motar, a take wata zuciyar ta hana shi, then ya fara tunani ai shi human being ne not like her, ba zai iya kallo ayi kissan kai ba. Cikin sauri ya fita daga motar ya nufi i da suke ya fara dukan mahaukacin ta baya har Halimatu ta samu sa'ar kubuce a hannunsa ta ranta a na kare sai fadan ya dawo tsakaninsu da mahaukacin shi da mahaukacin aka rasa mai hankali kowane kai wa wani duka yake, a cikin rashin sa'a mahaukacin ya naushi idon Ahmad ai take ya ji kalar garin ta canja, be san lokacin da wani karfin ya zo masa ba ya saka kafafuwansa ya buge Kafafuwan mahaukacin ya fadi kasa, a take Ahmad ya ranta a ciki na kare yana dafe da ido daya ya nufi motarsa a rikice ya bude motarsa ya shiga saboda wani azababben zugi da idon ke masa, @360 ya fisgi motar da ido daya da yake gani da shi. 7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 4️⃣2️⃣ Da hannu daya yake tuka motar yayinda dayan hannunsa yake dafe da idonsa, wani zafin bala'i idon yake masa ga ruwan da ake kama da bakin kwarya, har baya iya gani da kyau saboda karfinsu. A dole ya faka motarsa gafen titi, slowly ya dauke hannunsa daga idon da ke masa wani mugun zugi, ji yai idaniyar ta cika da abu mai kauri shi ba hawaye ba kuma ba ya san jini ne har sai da ya duba hannunsa. Jini a ciki kuma shine yake cika masa idon har baya gani da idon daya.   Lumshe idanuwan yai duka biyu yana sauraren yadda zugin yake shigar masa har cikin kansa, a rufe da idon ya saka hannun aljihu ya dauko wayarsa sai a lokacin yai kokarin bude idon daya yana duba iPhone dinsa wacce ta gama daukewa dip, sakamakon ruwan da ta sha, ba wayar kadai ba tufafin jikinsa ma sun gama jika seat dinsa balle kuma wayarsa. Iskar bakinsa ya bushar yanzu be san yadda zai yi ya kira Doc Nura ba balle yaji idan ma yana gari ko yana asibitin ko gida, daman can a tsarinsa be yarda wani likitan ya duba shi ba sai family doc su, domin ya yarda da aikinsa hundred percent. “Ba ma ita ce mahaukaciyar ba ni ne mahaukacin, taya zan shigar mata fada? Fadan ma da mahaukaci dan'uwanta? Matar da ta kashe min yarinyar? What's is wrong with me?” Ya fada yana jin haushin abunda ya aika.. “Bata ma tsaya ta dubani ba fa sai kawai ta gudu, idan ma kashe ni zai yi ita dai ta tsira, mahaukaciyar banza i hate her” Ya sake fada cikin fusata yana cizon bakinsa. A gurin ya tsaya har sai da ruwan suka dauke gaba daya sannan ya karasa tukin zuwa gida kamin ya isa har wani jiri yake ji cikin kansa. “Ai I'm human being be kamata ina gani ayi kisan kai ba, shiyasa na taimake ta, amman yanzu na gano matar nan bakincikina take so take ta illatani bayan ta kashe min ya, be m kamata na barta tana aiki a kamfani na ba ai” Shi kadai yake ta magana da kansa har ya faka motarsa a harabar gidan, yana kokarin bude motar ya fita ya tambayi kansa. “Ko ma miya kai ni fada da mahaukaci? Da mahaukaci da mahaukaciya suna fada ni mai hankali miya kai ni ciki?” After ya fito daga motar ya bawa kansa amsa. “Kaddara.... ” Part dinsa ya wuce, yana shiga ya fara ziyartar bandakin ya wanke fuskarsa, ya saka tissue yana tare jinin a hankali sannan ya dawo dakinsa ya dauko dayar wayarsa da ke gida yana kokarin kiran Doc Nura. “Hasara nawa ga saka ni a yau? Ta saka na jika tufafina ga idona daya ga phone dina.....” Wani irin haushinta ne ya kara cika msa zuciya. Sai da ya tabbatar Doc Nura na aibitin sannan ya canj tufafin jikinsa ya dauko key din wata motar ya fice ba tare da ya leka part din Hajiya ba, domin baya son ya tashi hankalinta. A asibiti babu kalar dariyar da Doc Nura be msa ba. “To kai yanzu miya kaika raba fada da mahaukaci? Ai gashi an bak tukuici” “You make me hate her more” “Wai wacece wannan?” “Wata mahaukaciya ce mai ruwan masu hankali” Ya hada fuska babu annuri can kuma yai murmushi. “Ita ma fa taji wuya, ba da wasa ya moreta ba” Dadi yaji tun da ita ma ta ji wuya, but maganar Allah shi yafi kowa shan wuya tunda shi be shi yaja mahaukacin ba. Bayan Doc ya duba idon ya bashi maganin na sha da shafawa a idon ya kuma fada msa yadda zai kula da ido. After ya dawo gida ya kira shiga part dinsa ya kiran Yunus. “Yu akwai wani mahaukaci da ke kusa da kamfanin mu, daga hannun dama gurin wani shagon kwano, za ka iya gane shi?” Sai da Yunus yai tunani sosai sannan ya amsa masa da. “Yes na gane shi kullum nn yke zama” “Ka sa a dauke shi a kai shi gidan mahaukata” “Why?” “Why? Ya zan baka umarni ka tambayeni why?” Ya amsa a fusace, kamar Yunus din ba abokinsa ba ne, saboda yau yana cikin zafin kai. Bayan ya kashe wayar yaje gaban madubi yan duba idon, idonsa daya yayi kwancin jini a ciki gaba daya gefen idon ya kumbura, abunka da farin mutun har wani ja gurin yai.   “Ina zaman zamana ta ja min masifa.....” Ya karasa maganar ta tari sai jini ya biyo baya, daman haka yake yanzu da ransa ya bace sai ya fada tarin jinin sai ciwon kirji.   Toilet ya nufa aman jini yai ba kadan ba, shi kanshi sai da abun ya dan tsorata shi, har yana zargin wata kila saboda ya sha ruwan sama ne abun ya kara hade masa, wanka yai sannan ya dawo dakinsa ya sha maganinsa ha kwanta. Sai 4:21 ya farka, sallah ce abunda ya fara gabatarwa sannan ya duba idon nasa kamin ya nufi part din Hajiya. Tana ganinsa hankalinta yai mugun tashin musamman idon nasa wanda ta hango jan jini a ciki. “Miya same ka Gwarzo?” “Hadarin nan ne da ya taso ina kokarin shiga, mota sai kasa ya shigar min ido” “Wannan ba kasa ba ne, hannu ne ga kwancin shi nan a idonka, kaga ni ko shiyasa bana son kana zuwa kana dadewa a waje, na sha fada maka da kun gama aiki ka rika dawowa gida, na san halinka da zuciya wata kila kaje ka bugu wani ya rama” Hannu ya kama yana kokarin zaunawa da murmushi a fuskarsa. “Haba Hajiya ai na girmi wannan, Wallahi kaddara ce kawai amman In-Sha-Allah ba zai sake faruwa ba” “Bari na kira Doc Nura” “Naje gurinsa ya bani magani ya duba idon” Sam bata yarda ba har sai da ta kira shi da kanta tai magana da shi ya tabbtar mata da cewar ya dubashi sannan hankalinta ya kwanta. “And daga yau ba zaka je aiki ba sai nan da one week” Da sauri ya kalli Hajiyarsa yana sakin baki. “Amman Hajiya kin san idan ba da ni ba wani abun ba zai yiyu ba” “Doka ta ce wannan” Ta fada fuskarta babu alamun wasa. “Yaro ba san ciwon kansa ba, sai idan ana nuna maka abu kace kai ba yaro ba ne” Rasa yai abunda zai ce mata, ba zai iya karya dokarta ba, kuma ba zai so fashin zuwa aiki ba, zai iya amfani da bakin gilashi ya rufe idonsa. “Idan an yi magariba ka kwanta karka tashi sai an yi isha'i, zan dafa maka carrot da allayau da wake yanzu suma suna gyara ido” A dolen dolensa ya amsa mata da okay, ta tashi ta shiga kitchen da zimmar dora masa girkin, shi kuma ya bita da kallo yana ta tunanin randa Hajiya zata yarda da cewar ya girma san ciwon kanshi. HALIMATU POV. A hankali na kalleshi, fuskarsa a hade take sam babu alamar wasa a umarninsa. Na sani ba lallai ne su yarda su canja min aiki ba, balle kuma har su yarda na rika saka wasu tufafin na dabam, Ahmad ba zai min wannan lamanin ba, ko a da balle a yanzu da ba san yadda na baro shi da karfi ba, ba laifi ya nuna kulawarsa tun da har ya taimaka min ba dan shi ba wata kila da yanzu na zama gawa, domin ba kadan Kabir ya makure ni ba. Tunanin nake ta yi ni kadai ina shafa wuyana da har yanzu ciwon yake min. “Amman za su iya cewa ba za su yarda na daina saka kayan ba” “Sai ki daina aikin” “Idan na daina aikin da me zan kula da kaina? Kamin na samu wani aikin abu mai wahala, kuma ka san bana da mai taimakona a yanzu sai Allah” “To sai ki samu miji ki yi aure, ki rike Namra da Amal Aiman da Adnan kuma ki maidasu gurin Babansu.....” Kai tsaye ya fada min maganar nan ba tare da ya kalleni ba.

Chapter 33 of 55