Reading adon dawa Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng Adon dawa
ADON DAWA
.
BABI NA DAYA
.
Rana ta fadi daf da magaruba dogayen motoci kirar j5 har guda bakwai ne suka
shigo jahar Maiduguri daga kasar daura, dauke da fasinjoji dari uku da hamsin
manya da yara, mata da maxa. Tafiya yankin axaba, hakika matafiyan cikin
motocinnan a gajiye suke kallo daya xaka yi musu ka fahimci haka. A layin suke
firfitowa daga cikin motocin yayin da duk wanda ya fito sai ya yi mika ya yi hamma
saboda yinin da suka yi cur a hanya suna tafiya.
Kaltum ‘yar kimanin shekaru goma sha biyar tana daya daga cikin matafiyan cikin
motar nan. A galabaice take a sanadiyar amaye-amayen da ta dinga yi a mota,
baya ga matseta da aka yi a lungu kafafuwanta sun kumbura sumtum kamar mai
cikin watan haihuwa.
A tsaye take a gefe tana jiran kakrta ta fito daga bayan bishiyar da ta kewaya don
rage tumbinta daya cika da fitsari itama ta bata buta ta kewaya. Sai ta ji muryar
wasu samari guda biyu suna Magana a bayanta suna Magana dogo da gajere,
dogon saurayin ne ya tambayi gajeren. Ya ce “wadannan fa daga ina suke kuma
ina xa su je riki-riki da kaya kamar masu gudun hijira!”
Gajeren ya bashi amsa y ace “ ‘yan gudn hijira ne ma ba kamar ‘yan gudun hijira
ba. Daga nan ma gaba xasu kara har xuwa sudan xa su tafi a mota, daga sudan
kuma su haura ruwa su shiga saudiya. Haka kawai mutanenmu suke wahalar da
kansu saboda kwadayi, yanxu wadannan da ka gansu wahala ce xata kashe rabin
su a hanya.”
Kaltum ta waiwayo da sauri ta dube su hankalinta ya kara tashi yayin da suka yi
ido hudu da kyakkyawar fuskarta wacce ta basu matukar sha’awar dubanta ba
kakkautawa. Dogon ya sake tambayar abokin sa gajeren, y ace, “kai, kalli wata
kyakkyawar yarinya. Ba dai itama sudan din xa ta je ba!”
Gajeren ya amsa masa da cewa “sudan xata je mana, baka ganta a cikin suba!
A banxa xa a wargaxa mata rayuwarta duk kyakkyawar halittar nan tata a
wulakance xa ka gansu a sudan ko makka idan sun samu ma sun haye kenan.,
rashin tawakkali ne kawai irin namu na ‘yan Nigeria, ba xasu iya hakuri da
talaucinsu ba sai sun je kwadayi.”
Kaltum ta sukuyar da kanta kasa yayinda hawaye ya fara bulbulowa daga idanunta
tana tausayin kanta tana tausayin rayuwarta. Ganin hawayen da take yi ne
samarin biyu suka karaso wajenda take tsaye, suka yi mata sallama sannan suka
fara tambayarta sunanta, daga inda ta fito da kuma inda ta nufa!
Babu amsa se kuka take yi kawai da suka ga halamar bata da niyar Magana sai
suka fara bata shawara. Gajeren cikinsu y ace, “ ni dai a matsayi na na musulmi
dan uwanki shawarar da xan iya baki shine kada ki sake ki tarki wannan tafiyar
shiga makka ta sudan a matsayinki na yarinya budurwa gara ki xauna a kasarku
gaban ‘yan uwanki koda ace baki da iyaye saboda bala’in dake tattare da irin
wannan harkar.”
Muryar kakarta goggo fatu ta jiyo a bayanta ta kwalla kiran sunanta gami da jan
dogon salati harda ihu da dora hannu a ka.
Tace, “na shiga uku, kaltum me xan gani! Me nake jiyowa ana fada miki! Ina kika
samo wadannan ‘yan iskan da har suke so su baki shawara ki bujire ki fasa tafiya!”
Kan ka ce kwabo kaltum ta fara rawar jiki saboda tsoro da firgici gami da gigicewa
duk suka far mata a lokaci guda. Ta fara bayani cikin rawar murya “gwaggo ban
san suba wucewa suke suka xo yi suka ganni tsaye, ba xuga ni suke yi ba.”
Goggo fattu ta cije baki ta dunkule hannu ta duma mata dundu a baya gami da
wurga mata butar dake hannunta a kafarta. Kaltum ta yi tsalle ta ruga da gudu
gefe ta tsuguna tana kuka. Hankalin samarin ya tashi suka fara yiwa goggo bayani
cewar ba laifin kaltum ba ne, suma bada niyyar xuga ta suka xo yi ba wucewa
kawai suka xo yi suka ganta tsaye. Goggo ta koma kansu ta rufe su da fada tana
musu korar kare wai su tafi su bata waje kafin ta farfasa musu kai. Magana daya
suka fada mata wacce ta kashe mata jiki.
Suka ce “ke tsohuwa, ki ji tsoron Allah ki san xa ki mutu, Allah xai tambaye ki
dalilin da ya sa kike wahalar da yarinyar nan xa ki kai ta makka ki jefa ta a wata
matsananciyar rayuwa kin rabo tada iyayenta. Kuma idan ki ka yi wasa sai mun je
mun hada kida hukumar NAPTIC da take da alhakin kwatarwa yara hakkin su
daman suna neman irin ku masu wahalar da yara musamman ‘ya’ya mata. Kina
ganin yarinyar nan ko bata fada ba kowa ya san bata son tafiyar nan dole aka yi
mata saboda tsoro gashi a gabanmu mun ga irin dukan da ki ke yi mata da xagi.”
Tsohuwa ta gaggauta barin wajen da sauri gami da fixgar hannun kaltum suka
kutsa cikin jama’arsu ma’ana ‘yan tawagar su ta matafiya domin ta tsorota da
abinda samarin suka fada mata. Hakika sun yi gaskiya kaltum bata son tafiyar nan
tilas aka yi mata.
A wannan wajen su kaltum suka yi alwala suka yi sallolin da ake bin su Axahar,
La’asar, Magaruba da Isha’i. kowa ya bude jakarsa ya dauko guxirinsa yana ci,
wasu buredi da miya, wasu suka jika garin kwaki da sukari da gyada wasu kuwa
fura ce wacce aka murtuke da nono aka shanya ta bushe suka jika da ruwa suka
xuba sukari suke sha.
Misalin karfe takwas na dare suka sake duruwa a cikin motocinsu suka ci gaba da
tafiya. Kai tsaye garin gamborin gala suka nufa, basu isa ba saida tsakar dare anan
suka yada xango. Garin barebari ne amman akwai wasu yaren daban daban, a
bayan gari akwai wasu tsofaffin gidajen kasa anan ake sauke su daman an yi su
don sauke matafiya irin su, kuma daga nan garin motocin da suka kawo su suka
juya xa’a sake musu motocin da xasu ci gaba da tafiya dasu.
A gambori aka wagarar dasu dakunan mata daban na maxa daban, amma a daki
daya ana xuba mutane fiye da goma sha biyar, kar ku dauka daki ne mai gado da
leda da labule a’a babu ko daya, ciccirarun tabarmi ne na kaba kawannensu sai
yayi matashi da kullin kayansa ko jakar kayansa.
tafiya se da suka share sati biyu cur a gambori, jagorin tafiyar su, wato (agents)
suna ta yi musu karairayi kala kala su ce yau xa’a tafi gobe xa’a tafi, wasu da yawa
sun kusa cinye guxurinsu don haka suka fara sayen abinci da dan kudaden da suka
boyo. Saboda gashi ba’a yi rabin tafiya ba ko Nigeria ba’a bari ba guxurin ya kusa
karewa. Mutane biyu ne suka riga mu gidan gaskiya a cikin matafiyan tsoho daya
da yarinya matashiya daman tun a hanya basu da lafiya anan aka sallace su aka
binne, ‘yan uwansu suka sha kuka.
Matafiya sai mita suke yiwa agents babu ranar da yawa daga cikinsu basu yi kuka
ba saboda wahala. Daga inda suke xuwa cikin gari yana da nisa haka suke faman
tafiya kafin su je su siyo abunda xa su ci ko debo rowan da xasu yi wanka da
wanki. Kowa ta kansa yake, babu babba ba yaro, babu mace babu na miji, babu
mai taimako ko tausayin dan uwansa. Akwai mata masu ciki da yawa wasu
karamin ciki wasu kuwa tsohon ciki ne, wasu masu goyo amma dole kowacce ta
fita ta yi doguwar tafiya sannan ta nemo abinda xa ta ci, ta debo rowan da xata yi
wanka da wanki.
A ranar da suka cika sati biyu aka kawo musu katuwar motar nan da aka yi ta
musamman don daukar kaya wato tirela. A bayan motar aka dura su gaba dayansu
su da kayansu kamar wasu shanu. Bayan haka aka jibga masu buhuhunan gyada
da ridi wadanda xa’a sayar a sudan har buhu dari duk a bayan motar. A cunkushe
suke a tattakure kafada a marmatse babu wanda xai iya mike kafarsa, da yawan
su basu sami waje ba a bayan motar sai a saman mota aka loda su.
Kwalta ta kare don haka cikin kasa (sahara) ake tafiya, tafiya suke yi a mota amma
a wahale suke tamkar da kafarsu suke tafiya sun jigata don haka rayukansu
kowannensu a bace yake, babu abinda yake tashi a cikin motar sai kyara da
bakaken Magana a jima kadan ka ji fada ya tashi ana sursurfawa ashar gunduwa
gunduwa. Wannan tace waccan ta matseta sai wannan yace wancan ya shure shi
aikin kenan.
Bayan sun yini suna tafiya suka isa kusuri, a dawa aka sauke su a nan ma saida
suka yi kwanaki biyu. Sai dai kowannensu ya shimfida xaninsa ya yi filo da kullin
kayansa. Babu famfo ko rijiya a kusa don haka jarkokin ruwa agents suke kawo
musu jarkoki hudu a tartarfawa kowa a kwanonsa ya sha ya jika gari, alwala kuwa
sai taimama babu batun wanka.
Daga kusiri sai suka nifi chadi (N’DJAMENA), basu yi niyyar kwana a N’djamena ba
amma dole suka kwana a sanadiyyar ruwan da ya dates hanyarsu ta wucewa.
Rowan daga cikin dutse yake bulbulowa ya dates hanyar wucewa dole motoci suka
dakata har saida rowan ya tsaya, ruwa ya kafe hanya ta bude amma se da shirin
tafiya ya wargaje dole suka sauke kayansu daga cikin mota a sanadiyar wasun su
guxirin su ya kusa karewa sai sun nemi kudi sannan a ci gaba da tafiya. Nan fa
matansu da maxajensu suka baxama cikin gari neman kudi sune dako, wankau
faskare da dai sauransu. Satinsu uku a Ndjamena sannan suka kama hanya, a
boda kuma ake sake duba takardarsu wato anan ake duba passport da visa sannan
su wuce.
Daga N’djamena sai suka shiga Abbashe nan ma a bayan gari suka yada xango
cikin rubabbun gidan katako, tabbas basu yi niyyar wuce kwana daya ba a
Abbashe amma hakan bai yiwu ba a sanadiyar nakuda ta wata mace ke yi, yini
guda ana abu daya da kyar aka samu dan da yake cikinta ya fito, ya fito da rai
amma bayan awanni ya rasu.
A ka’idar garin duk wanda ya mutu sai an sanarwa da maigari ya rubuta takarda
an nunawa hukumar da abunda ya shafa sannan xa’a yarda a binne gawa. Don
haka hankali ya tashi ana tunanin yadda xa’ayi doguwar tafiya xuwa cikin gari,
sannan a yi ta dogon bayani kafin su yarda a binne yaron. Daga karshe aka yi
shawara a nannade gawar jaririn a kunshe a tsumma sai a sami mutum daya ya
xagaya dawa ya binne gawar jaririn. Haka kuwa aka yi aka binne cikin dare. A
daren kuma Allah Ya yiwa mai jegon rasuwa itama daman tunda ta haihu bata da
lafiya.
Nan fa hankalin kowa ya tashi ‘yan uwanta sai suka yi ta kuka suna kururuwa. Da
yawa daga cikinsu kaltum suma suka yi ta kuka duk da basu santa ba, haduwar
motace kawai sai dai don tausayin rai da tausayawa kansu da kansu. Dakin da
kaltum take shine dakin da aka yi mutuwar don haka a xaune suka kwana tangarai
ko gyangyadi basu iya yi ba. Kaltum na lungu jikinta sai tsuma yake, hawaye ke
kwaranya saboda tunda take bata taba ganin gawa ba,. Ta ji dama ace itace ta
rasu kamar yadda wannan baiwar Allah ta rasu. Tana tunanin yadda rayuwa xa ta
kasance mata nan gaba.
Da gari yawaye direban da jagorannin tafiyar (agents) suka hadu suka tafi wajen
maigari ,dan gari ne ya jagorance su cikin yarensu mai suna wadai dan rakiyar ya
yiwa sarki bayani cewar wadannan baki ne suka xo daga Nigeria xasu wuce sudan,
suka yada xango a wajen gari sai Allah Ya yiwa mace daya rasuwa suna so su
binne ta a nan. Sarki ya yi amanna ya basu takarda suka je suka nunawa masu
jiran makabarta, sannan aka yarda suka binne ta bayan suna sallace ta kamar
yadda ake yiwa kowane musulmi.
A ranar suka sake kama hanya suka ci gaba da tafiya, yini guda cur a mota har
dare ba tsayawa saida kyar direban ya yarda ya tsaya a wani gari da ake kira Adre
suka yi sallah suka ci guxurinsu garin kwaki ne dai, sannan suka ci gaba da tafiya.
A xaune suke tangarai, se gyangyadi kowa ke yi a xaune. Gargada ce a dukkan
hanyar a sanadiyar rashin kwalta, idan mota tadaka tsalle sai ka ga mutum ya yi
sama ya dawo ya xauna dabas, idan aka yi rashin sa’a wanda ke xaune sai ya
dawo sama dororo a jikin mutane matsi ya hana direwa a xauna daidai sai dai idan
motar ta sake daka tsalle adan ka yi sa’a sai ka sami wajen xama wani kuma ya
xama derere shi ba xaune ba kuma ba tsugunne ba, shi ba a kasa ba shi ba a
sama ba.
Sai cikin dare suka isa jinene bayan sun yi sallolinsu suka haba garin kwaki da
busashiyar gurasa sai suka ci gaba da tafiya, kwana daya da yini daya da yini daya
guda cur suka yi a hanya suka isa wani gari da ake kira mukwar. Bayan sun huta a
mukwar sai suka ci gaba da tafiya babu abun da yake kan hanyar nan sai namun
daji, xuma caba caba ga ‘yan fashi. Basu tsaya a ko ina ba sai da dajin majawara.
Dajin majawara daji ne wanda yake shiru, tsit ko kukan tsuntsu babu balle gidajen
bil’adama. Daga nan kowa dakatawa babu mahalukin da xai iya tsallakewa a
sanadiyar tsantsar hadarin da ke tattare da ci gaba da tafiya. Dole ne duk motar
da ta xo dajin majara sai ta ja ta tsaya a doka har sai motoci saba’in sun cika
sannan sojoji su xo su tsallakar dasu saboda mugaye, kasurguman ‘yan fashin da
suke fashi a hanyar. Don haka said a ‘yan tawagar su kaltum suka yi kwanaki uku
a nan suna jiran motoci saba’in su cika sannan a hayar dasu.
A ranar da suka cika motoci saba’in sannan aka shirya ci gaba da tafiya a lokacin
da xa su tafi da yamma wani dankareren maciji ya sari daya daga cikin ‘yan
twagar su kaltum, kan ka ce kwabo mutumin ya sassankare kumfa na xubowa
daga bakinsa. Jama’a suka bi macijin da jifa amma tuni ya sulale ya shige dawa
basu kashe shi ba, daga karshe mutumin ya mutu a wajen, a nan aka binne shi
suka shiga motocinsu suka fara tafiya. Amma a kowace mota said a sojoji bibbiyu
suka shiga suna harba bindiga sama har sai an wuce mugayen daxuka da barayin
suke. Tun da yamman da suke tafe ba tsaya ba har se da gari yawaye, sannan
sojojin suka sassauka daga motocin da suka rako suka shiga motocinsu suka juya.
Sannan su kuma matafiya suka ci gaba da tafiyarsu.
Tafiyar kwana biyu suka yi ba kakkautawa sannan suka shiga kartum tutu babban
birnin sudan. Sun kwana daya a kartum, a wajen garin akwai dakunan katako da
aka yi musamman don kwanan matafiya. Da suka waye a nan sannan suka ci gaba
da tafiyar, kwana guda cur suka yi a hanya sannan suka isa kartum bahari sai suka
nufi bur sudan nan ne inda ruwan daya hada sudan da makka ,ruwanne ya hade da
ruwan maliya. Daga bur sudan kuma tafiyar mota ta kare don haka masu mota
suka sauke su su da jifgin kayansu suka juya.
Daki ne na guntayen katakwaye joni joni, rufin dakin ma duk hudaddun katakwaye
ne baya da katakon nan babu ko kwayar dakunan sai wanda ya ci sa’a ne xai tarar
da kwalaye a shimfide a dakin. Ga duhu a sanadiyar rashin fitila gashi tsakar dare
suka iso don haka babu wata wata kwanciyar kowa yake so ya yi. Aka ware
dakunan mata da na maxa daban, amma a kowane daki mutane ashirin ne xuwa
ashirin da biyar duk da haka wasu a xube suke a tsakar gida wasu maxan kuma a
xube a kofar gida. Su dai fatansu su kwantar da hakarkarinsu su mike a sanadiyar
kagewar da bayansu ya yi saboda kwana da yinin da suke yi a xaune a mota a
tattakure.
Misalin karfe daya na dare suka isa bur suban a gajiye suke don haka idanuwansu
a rufe suke burin kowanensu ya sami inda xai yada hakarkarinsa. A guje suke
rububin hayewa kan wasu tudu da suka iske a cikin dakunnan katakon cikin rashin
sani basu san kabarurrukan suka kwanta yayin da wadanda basu sami hawa ba
suka bi layi suka doddora kansu a kan kabarurrukan.
Kaltum da kakarta sun yi sa’a sun sami daki, a cikin dakin ma kaltum ta yi sa’ar
samun hayewa kan tudun dake tsakiyar dakin. Dan tudun maidan tsawo ne da fadi
daidai kwanciyar mutum daya don haka da ta shimfida xaninta aka ta yi filo da dan
karamin bacco dake dauke da kayanta sai ta yada kai xata kwanta. Kakar tace ta
daka mata tsawa tace “kaltum, kina da hankali kuwa! Ina kasa cikin kasa turmus
ke ki sami mulmulallen tudu ki kwanta harda shimfida xani ki yi filo da jakar
kayanki ni babu ko daya, to ki sauko kasa cikin kasar ki kwanta nixan haye tudun.”
Kaltum na karkarwar jiki don tsoro ta sauko da sauri, goggo fatu ta haye tudu
harda juya baya ta yi kwanciyarta, kaltum ta mike a kasa cikin yashi ta kwanta,
burinta ta kwanta da hakarkarinta ma kawai ta huta gajiya. Nan ma manyan mata
suka dinga yi mata carin masifa wai sai ta matsa lungu ta babbake musu fili. Ba ta
tankawa kowa ba ta takure a lungu ta yi shiru.
Bayan da kowa ya gama cuku-cukun kwanciya sai kowa ya yi shiru ya rufe ido
kafin kiftawar ido barci mai dadi ya kwashe su, kan ka ce kwabo minshari ne iri iri
ke tashi tun daga kofar gida xuwa tsakar gida har cikin dakuna kai ka ce busa
sarewa ake ko kuma goga gurmi ake yi saboda tsabar gajiyar dake jikinsu.
Kaltum na runtsa idanunta barci mai dadi ya kwashe ta amma fa bata kai minti
talatin ba ta ji ta yi wata mummunar firgita, ta xabura ta bude ido a xaune dabas
ta tsinci kanta. Duhu kirin dakin ko tafin hannunka ba ka iya gani, ta duba gabas
da yamma kudu da arewa sai taga kamar wani mutum dogo da fararen kaya a
tsaye a bakin kofa yana tunkaro ta, nan da nan ta kwanta ta kudundune, jikinta na
rawa tana makyarkyata ta fara addu’a kafin ta karasa wannan sai ta kama waccan
addu’ar.
Irin wannan raxanar ceta afkawa goggo fattu wacce ta haye kan tudu. Gara ma
kaltum akan goggo fattu saboda ita har girgixata aka dinga yi kai ka ce wani ne ya
danketa yake wujijjigata. Ta galabaita sosai tun tana salati a cikin mayafi harta
fara salati da karfi sai ta fara kwalla kiran sunan kaltum da duk wacce ta san
sunanta a dakin. Can kaltum ta yi karfin hali tana cikin mayafinta tace “goggo,
menene!”
Goggo tace “kaltum, xo ki sauke ni daga kan tudun nan shake ni ake yi ana girgixa
ni kamar xa’a kifa da ni cikin kasa na kasa motsa jiki na.
To pa!!! ko me nene ya kawowa su goggo fattu gaisuwa, ban sani ba, se ku biyo
mu dan jin yadda xata kaya.
.
To da patan littapin ya muku?
ADON DAWA 3
BABI NA UKU
A lokacin dasu kaltum suka cika sati uku a bur sudan dole tasa suka fito neman
abunda xa su kai bakinsu, mata da maxa, yara da manya kowa ya ja xugarsu suka
shiga gari.
Tawagar ‘yan mata su biyar kaltum, rakiya, huwaila, jidda’u da amina suka
fankama garin ADON DAWA don yin bara. Suka kuwa ci sa’a suka samo kudi da
yawa wanda xai ishesu su ci abincin yinin yau. Kalmar da suke ambata itace
“karama fisabilillahi” sai kaga an miko musu kudi. Su kan basu wahid jine wato
kamar naira daya kenan, wasu se su basu hamsin jine ficika kenan idan kuwa suka
ci sa’a sai a rana daya saisu hada maitan jine daga nan saisu wuce cikin gari maka
makan wajen sayar da abinci (restaurant)su sayo abunda suke so, kamar su kisra
wato sinasir ko su sayi esha wato gurasa, wani lokaci saisu hada da ful. Ful wake
ne manya manya sai a dafa shi ba gishiri ana ci da gurasa. Idan suka samo kudin
bara da yawa saisu sayi baitil mandi shima dafaffiyar shinkafa ce fara sai a
kwarara madara akai, a yanka tumatiri da albasa, a yanka karas da kabeji, sannan
a dora gasashshiyar kaxa a barbada dan gishiri sannan a ci.
Daga dukkan alamu yunwar da ke addabar su ta fara sauki har sun sami karfin da
suke iya debo bokitai da manyan darukan ruwa akansu, su niki tafiya mai nisa
sannan su samo ruwan da xa suyi amfani dashi wajen wamka, wanki da wanke-
wanke. Ta cikin makabarta suke bi sannan su isa gabar kogin da suke debo ruwan.
Ruwan baya shawuwa saboda jajawur ne mai dandanon gishiri.
Jikin kaltum yakan yi sanyi har takan fashe da kuka idan taga yadda ake binne
mutane a makabarta. Saboda sahara ce don haka suke yin dogon rami mai xurfi
sosai, wanda mai hakawar sai ya shige ciki sosai yayi xurfi.sai an daina hango shi
sannan ya miko hannunsa a kamo shi waje dan ba xai iya fitowa ba. Sannan saisu
taru su saka gawa, sannan su jera bululluka a maimakon itace saboda yashi ne
itatuwa ba xa su tsaya ba. Allahu Akbar!
Allah Ya sa mu cika da imani, Y a jikan musulman da suka riga mu gidan gaskiya.
Ameen.
A yau kaltum bata bisu bara ba saboda tana son ta wanke kayan jikinta kwaya
daya kacal, yayi dakun dakun har gefen xanin ya yage don haka ta yanke
shawarar sai kowa ya tafi bara sannan ta rufe gida ta cire kayan ta wanke ta xauna
ta jira ya bushe sai ta yi wanka ta saka. Da ta tabbatar mata da maxa sun fita
daman tun da sassafe ta debo ruwan wankinta, sai ta tsinci guntayen sabulai ta
harhade ta ajiye. Suna ficewa sai ta rufe kofar ta fara wanke riga da dankwali da
mayafin ta shanya ta koma gefe ta takure tana jiran su bushe.
Ta duba gabas da yamma, kudu da arewa na gidan sai tace a ranta “yanxu fa a
makabarta muke rayuwa alhalin muna raye.”
Ta sake duban katon tudun kabarin da yake gefenta ta mika hannu a hankali ta
shafa tace, “ko mace ce ko na miji ne a cikin kabarinnan Allah Shi ya barwa KanSa
sani. Allah Ya jkansu da gafara.”
Ta ji hawaye yana sirnanowa daga idanuwanta don tausayin kanta da irin
matsananciyar rayuwar da take ciki. Ta tuno gwaggo fattu wacce ta kawo ta nan ta
ajiye ta ita kuma ta haye ta yi tafiyarta makka tana can tana jin dadin rayuwarta.
Babban tashin hankalin shi ne iyayenta basu san halin da take ciki ba don su a
tunanisu tana saudiya kuma tasan mugun halin gwaggo fattu ba xata yi waya ba
ko ta aika wasika ta fada musu gaskiya ba sai dai ta bar su a haka, suma kuma
iyayen nata ba waya gare su ba balle su san lambarta ta makka su buga mata su
tambayi halin da take ciki. Kaltum ta fi jin haushin iyayenta su da suka yarda suka
yarda suka bayar da ita aka taho da ita don basa tausayinta. Ta ji ta tsani kowa a
duniya kamar yadda kowa baya sonta, sai ta fashe da kuka mai tsananin ta kifa kai
a jikin katakon dakin su. Kuka take yi haikan amma tana fada cikin daga muryar ta
“inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”
Tsananin bugun da ake yiwa kofar gidan ne ya sata tsagaita da kukan da take yi,
ta kasa kunne tana sauraro sannan ta gaskata wani ne yake buga kofa. Sai ta mike
tsaye ta yi wuri wuri tana tunanin yadda xata yi. Shawara take yi shin ta je a haka
da daurin kirji ta bude kofar, sai dai ai bata sani ba mace ce ko na miji! Idan namiji
ne ba xata iya tsayawa da daurin kirji a gabansa ba musamman yadda maxan suke
‘yan iska ko wanka ka ke yi idan baka kula ba saisu yi ta liken ki. Haka idan ki ka yi
sake a daki kina barci baki killace jikinki ba sai dai ki ga suna ta xirga xirga ta kofar
dakinku suna kallonki a dole wucewa bandaki su ke yi, ko suyi ta leke ta hudar
katakon musamman dakin su kaltum da yake kunshe da ‘yan mata.
Ta ji sautin bugun kofar ya kara tsamari don haka ta yayimi jikakkiyar rigarta ta
saka ta jawo jikakken mayafinta ta sharba a kanta ta goge idonta saboda hawayen
da yayi mata kawanya. Ta isa da sauri bakin kofar ba tare da ta tambaya ba ko
waye ta ja sakata ta bude game da wangale kofar. Jikinta na rawa ta dubi wacce ke
bakin kofar sai taga madina ce tayi sauri ta duka a tsorace.
Ta ce “sannu da xuwa, yi hakuri ban xo na bude miki kofa da wuri ba ina kokarin
saka rigata ne.” madina tayi murmushi t ace”lah ai ba komai kaltum.”
Kaltum ta mika hannu xata kar bi himilin daurin kayan dake kanta sannan ga leda
a hannunta. Madina tace “bar shi kaltum, ba komai ba sai kin taya ni ba ai na xo
gida mu shiga ciki.”
Kaltum ta dawo tsakar gida inda ta cire jikakkiyar rigarta da mayafinta ta mayar
kan igiya ta shanya. Madina kuwa ta wuce cikin dakinsu kai tsaye ta xarce kan
kwalin shinfidar ta da jakar kayanta a gefe ta ajiye himilin tsummakaron da ta
samo. Ta fito tsakar gida inda kaltum ta daga ido da sauri ta dubeta sai suka yiwa
juna murmushi a

Please Login or Register in order to submit comment