Reading adon dawa Chapter 6 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Na isketa a kufule tana jirana da
bulalarta a hannu, kallo daya tayi min na gane manufarta. Sai na fara cire abayata
na xama tik daga ni sai wando. Ina karkarwa na xo na durkusa na mika mata ciniki,
ta karba ta kirga. Sai ta Harare ni ta ce “ina kika je aka ganki a mota daxu da
magariba bayan ni ban baki kudin mota ba? ”
Sai na ji xuciyata ta harba tabbas wani ko wata sun ganni har an fada mata. Sai na
shiga dogon tunani ina neman hanyar da xan kare kaina. Ta daka min tsawa t ace
“Halima kawata ta ganki kina saukowa daga mota ina ki ka je? ”
Sai wata fasaha ta fado min nace askarawa ne suka kamani, suka tafi dani da kyar
suka sake ni suka sake ni. Ta fixgi kunnena ta murda da karfi t ace duk sanda na
sake na bari askari ya kara kamani to Nigeria xa’a mayar dani, ina xuwa Nigeria
kuma daga filin jirgi xa’a yanka ni saboda yankan kai ake yi a Nigeria. Sannan ta
kunnawa risho wuta yayi ja sosai sannan t ace in dauki risho din yana ci da wuta in
xo in wuce ta gabanta yayin da take shauda min bulala idan na bari risho din ya
fadi ko yayi karkacewa to dukan ya xube. “sai kaltum ta fashe da kuka mai
tsanani.
Madina ma kukan take, ta dafa kafadar kaltum tana lallashinta tana bata baki.
Tsawon lokaci kaltum bata daina kuka ba, saida kyar ta ci gaba da Magana. Ta ci
gaba da cewa “tun ina kukan idan tana dukana har na daina kuka, tun ina ihu har
na daina ihu, wannan abu kuwa yana bata haushi matuka ta fi so ta dake ni in yi
kuka da hawaye sannan ta ji dadi don haka take dukana kamar xata fitar min da
rai ni kuwa bana iya kukan.
Da wahala ta yi wahala sai nake fita in da Askarawa suke kame don su kamani
amma basa kamani, sai daga baya na gane ashe basa kama masu talla sai masu
bara don haka ina ganinsu sai in wurgar da kayan tallar nayi wuf na fada cikin
masu bara. Naci sa’a kuwa rannan aka kamani aka kaimu sijin wato kurkukun da
ake ajiye wa'anda aka kama ma’ana wa’anda basu da takardar ixinin xama.”
Madina tace “yaya rayuwar kita kasance a sin?
Kuma yaya goggo fattu ta yi data ji an kama ki? ”
Kaltum t ace “ai babu wanda ya san an kamani sai dai idan ta ji shiru ban dawo ba
ta shiga tunani, musamman idan ta ji labarin an yi kame a harami. Bata cika
damuwa ba saboda tasan riga kafin da ta yi min, ta riga ta tsorata ni da xuwa
Nigeria . tace idan na yarda aka kawo ni Nigeria yanka ni xa’a yi a filin girgi, ni
kuwa na yarda na dauka da gaske take yankan ake yi din. Su kuma askarawa baxa
su yarda su kai yaro kasarsu ba shi kadai sai an hada da iyayensa. Don haka saisu
tambayemu muna da iyaye a nan Saudi ya? Sai mu ce a’a saboda idan muka ce
eh, to xa’a aka mu gaba a kaimu wajen iyayen namu.
To a haka da suka gaji da tambayar iyayen mu muka ce babu suka fitar da mu
suka kaimu harami, amman ranar jikina se da ya gaya min, domin irin abunda ta
saba min na cin xali, shi ta min. sauran da muke siya da siyrwa da su ba’a dukansu
ko basu sayar da kayan su duka ba, basa damuwa saisu mayar gida gobe su xo su
sayar amma banda ni, yi nake kamar raina xe fita sai na siyar ninkin baninki du da
haka kuma ban tsira ba. Kaltum ta rushe da kuka.
Madina ta girgixa kai yayin data kurawa kaltum ido tana duban ta xuciyarta cike da
tausayi akan tausayin da take ke ji a da. Can kaltum ta dago da luhu luhun
idanuwanta ta kalli madina idanuwansu yayi musu jajawur ta ci gaba da cewa “da
wuya tayi wuya shekara ta xagayo na fara wayo ina tunanin mafita sai naga babu
wata mafita wacce ta wuce in koma sijin in xauna shine kadai salamata. Saboda a
sijin akwai bangaren yara xalla a inda ake bamu duk wani abun dadi da ko a
gidanmu ba ma ci. Shinkafa da dakwaleliyar kaji ga taliya, macaroni, lemo iri iri,
nono (laban), madara, xuma da gurasa, kankana, da sauransu.
Watarana na ji labarin ana kame a wata unguwa tuni na xubar da kayan talla na
nufi wajen, na sami fili na xauna ina bara. Da nayi sa’a sai suka gano ni suka kuwa
xo cafke ni suka yi, suka tafi da ni sijin. Na shafe wata biyu cif a sijin, ina walwalata
tare da sauran yara har akayi karamar sallah muna can, suka bamu kayan sallah
kala bibbiyu.”
Madina tace “atamfa ko leshi? ”
Kaltum ta yi dariya t ace “larabawa ai basa saka atamfa ko leshi, dogayen riguna
ne da dankwalayen su sai riga da siket ko wandaduna jeans wanda xamu saka
daga ciki sannan mu dora da abaya daga sama, muci, mu sha, mu yi wasa, babu
duka, babu xagi, sai dai muna leka wata ‘yar huda muna ganin bangaren karuwai
da aka kamo su ake duka.”
Madina t ace “kullum sai ayi ta xane su? ”
Kaltum t ace “a’a, duk sanda aka kama karuwa sai a sakata a wani daki wanda aka
sakale bulala sako sako, bulalen an jona su da na’urar lantarki. Ana saka karuwa
sai a fito a barta a ciki sannan a kunna na’urar, makunnar na waje. Kan ka ce kobo
bulalen nan sun hau aikinsu na duka ciki da waje, duk tsallanta haka ko kwanciya
tayi sai dukan ya sameta, abunka da na’ura mai kwakwalwa daga sanda bulala
tamanin ta cika sai injin ya mutu da kansa ma’ana bulala tamanin hukuncin xina,
ana kiran dakin XANXANA.”
(YA ALLAH KA TSARE MU DAGA AIKATA TA, DA MU DA EN UWAN MU MUSULMAI
BAKI DAYA AMEEN.)
Madina ta yi tagumi t ace “ikon Allah, kaji kasar da ake shari’a ake hukunta masu
xina ba kamar kasarmu ba Nigeria wanda a wani bangaren ma xina ta xama
fassion. Yaya ake yi da karuwa, idan an gama dukan ta? Nasan mafi yawancin su
‘yan Nigeria ne ko? ”
Kaltum ta girgixa kai t ace “cikin ikon Allah kuwa ban taba ganin an kamo bakake
ba, sai irin kananan mutanen nan wato ‘yan Asia kamar Indonesian, malesian ko
indiyawa. Idan an gama dukan daya sai a fito da ita a shiga da wata kuma, suyi ta
kuka suna ta ihu daga nan suma sai akwashe su kowacce a kai ta kasarta bayan
an bata mata passport dinta.”
Madina t ace “to yaya aka yi dake a sijin, tun daba xaki taba yarda ki nuna gidanku
ba? ”
Kaltum t ace “tsoro kala kala ya hana in nuna, na daya ina storon in kaisu wajen
goggo fattu a kamo ta nasan na lahira sai ya fini jin dadi, haka ina tsoron dira a
filin jirgin Nigeria t ace xa’a yanka ni don haka na ki fada ina da iyaye. Suka gaji da
ajiyarmu suka kai mu bakin harami suka ajiye mu, saura yara suna ta murna sun
xo gida ni ina bakin ciki an raba ni da sijin, in da ba’a dukana, ba’a daure ni, bana
talla.
Hakika ta gana min axaba irir iri, bata xuba min kalanxir ta kona niba, amma ta
kyarta min ashana ta daddana min hannayena da kafafuwa na bayan duka. Ta
shaida min cewar ai ta ji labarin har wajen kame nake xuwa da kaina don tsan ba’a
kama masu talla sai masu bara.
Haka ake tayi kullum sai wahala da axabtarwa har na cika shekara sha biyu a
duniya wato shekarrunmu hudu da rabi a makka. Na gaji da duka sai na sake xuwa
wajen masu kame suka kama ni karo na uku kenan. Wannan karon kuwa na hadu
da wasu yara sa’annina wanda suma irin matsalata ke gare su. Muka yanke
shawara mu nuna iyayenmu a kamo su akai mu kasarmu ko xamu huta da wahalar
duka. Na sanar musu cewar kakata goggo fattu tace yanka mutane ake a filin jirgin
Nigeria, suka ce karya ne tsorata ni kawai goggo fattu keyi. Don haka ana
tambayarmu muna da iyaye mu uku muka ce “eh muna da iyaye.” Sauran da suka
ce basu da iyaye aka dawo dasu bakin harami aka xube su. Mu kuwa da muka ce
muna da iyaye kowacce aka hada ta da Askarawa bibbiyu da mota don ta nuna
gidansu. Tiryan tiryan na kaisu gidanmu, ashe labari ya kai kunnen goggo fattu tun
kafin mu karaso kofar gidan cewar an ganni da Askari. Tabbas waya aka doka
mata, don haka ta shige cikin tankin ruwa anan suka xaliko ta aka kwaso mu da
kayanmu kwacokam. Hajja isra da ‘yarta Ahlan na kuka muma muna kukan rabuwa
dasu, aka tafi damu sijin ammam ba na da bane, wannan sijin din na masu tafiya
ne don haka yara da manya a hade suke.
Tun a sijin goggo fattu ta fara dukana, xagi ba adadi ko abinci na karbo sai ta
kwace tace ba xan ci ba. Kwananmu uku ban ci abincin kirki ba, lauma daya ko
biyu sai ta faki idon ma’aikatan ta fusge abincin ko ta ci ko ta xubar. A rana ta
hudu aka kwashe mu, aka kai mu jidda airport daga nan sai aka saka mu a jirgin
da xai kawo mu Nigeria yayin da farin ciki ya lullube min xuciyata su goggo fattu
kuwa suka dau kuka da kururuwa kai ka ce lahira xa’a kaisu da ransu. Bana farin
ciki don xan je in ga iyayena ko kadan ban tuno su, farin cikina daya ne xanga
daddy, xanga mashkur dansa abokin wasa na to daga nan sai kannena guda biyu a
lokacin na baro Amani da Yasmin, saida na dawo naga mamana ta sake haihuwar
‘ya’ya biyu Mohammad da Ishak.”
Madina ta tambaya “ya kuka kasance da goggo fattu a Nigeria? ”
Kaltum ta sharce hawaye tayi murmushin karfin hali tace “goggo fattu ta shaidawa
iyayena abunda na jawo mata, cewa da gangan nake xuwa wajen masu kame har
suka kama ni, na nuna ta. Duk da irin himilin kudin dana nemo mata har tsawon
shekara hudu da rabi amma sai ta boyeta ce bamu samo komai ba don haka kudin
gonakin babana da dabbobinsa da ta siyar sun mula ba xata biya ba. Ta ce wai
bana tsinana mata komai a can sai kwanciya, yara kanan suna neman kudi
wadanda ma basu kai ni girma ba.
Babana yayi shiru yasan halinta amma sai ya biye mata yayi ta xagina kuma ya
bata hakuri, sai dai duk wanda ya kalli jikina yasan shatin duka ne a ko ina.
Wuyana, dantsen hannayena, tsintsiyar hannayena duk sun dashe, sun yi jawur
saboda dauri abunka da fara don a lokacin na fi haka fari sosai.
Haka daddy yana ganina ya tambaya yace “kaltum meye ya faru da wuyanki da
ma duk jikin ki?
amman wannan shacin duka ne. wa yaketa dukanki haka? ”
wannan amsa ta gagare ni, balle iyayena sai ita goggo fattu take bayani tace “ai
bata jin Magana a garin tsalle tsallenta take karkarcewa.” Ai idan mafadin Magana
wawa ne, majiyanta ba wawa ba ne. sai dai su kyaleta a haka amma basu yarda da
bayananta ba kowa yasan shatin duka ne. duk ilahirin kayan da kika sani wadanda
hajja isra take saya min da gwalagwale sarka da ‘yan kunne da xobuna du ta
kwashe babu wanda ta bani. Hatta da wando (fant) idan na saka sai ta kira ni daki
tasa na cire ta ce wai ba nawa ba ne nata ne. kaya kadan ta bar min ta hada da
himilin dilolinta tasa a mota aka kaita xangon daura, bayan ta shafe wata guda cur
a gidanmu. Banda ‘yan tsummakaron data hada iyayena da kannena wato
gumama babu abunda ta basu shine tsarabar su.”
Madina t ace “amma wannan matar makira ce bata tsoron Allah. Yanxu ina xata
kai hakkin dukiyar mahaifin ki data danne ta gado? Yaya rayuwarki ta kasance
kuma a kano tare da iyayen ki? ”
Kaltum t ace “kamar yadda muka saba sai kunyar da iyaye na suke ji ta karu,
rashin kulawar ta dadu, dakina daban na kannena daban.
Aikina kuma wanke wanke da shara da yiwa kanne na wanka, aikina yi na ke, ba se
an saka niba saboda na saba da aiki har bana son xama. Mama kuma ita ke dafa
abinci safe rana da dare.”
Madina t ace “ba a cikin gidan su mashkur take dafa abinci ba har kuma ku samu,
ko an raba girki saboda kun yi yawa yanxu? ”
Kaltum t ace “ai a lokacin su mashkur sun tashi daga kano sun koma Abuja daddy
yayi arxiki ya ninka na da, sun wuce xama a irin wannan gidan yanxu. Gidansu na
Abuja tamkar aljannar duniya, ga motoci kala kala.”
Madina t ace sai suka bar muku babban gidan kuka bar boys quarters? ”
(Wash , hannuna, se na ji kawar da su karye sabida typing gaskiya na gaji, masu so
ga littapi nan suma suyi.)
.
ADON DAWA 9
.
TRUE LIFE STORY
.
Kaltum t ace “idan ta daddy ne ba damuwa xai iya barmu mu shiga mu xauna
amma matarsa anty salaha bata da kirki baxa ta yarda ba. Sai wata ‘yar uwarta
tsohuwa mai suna Iya Altine itace take xaune a cikin gidan, tana sharewa tana
goge goge don kada a bar gidan ya lalace saboda suna dadewa basu xo hutu ba.
Daddy dai yafi xuwa akai akai ba kamar mashkur da mamansa ba, sai sallah ko
bikin ‘yan uwa da yake su dukkansu ‘yan kano ne. mu dai muna xaune a boys
quarters sai ma rashin dadi daya karu, saboda a yanxu basa gidan bare mamana
ta dafa musu abinci su ci har mu ma mu samu mu ci, mu ke cefanen mu, mu auno
abinci, sannan mu dafa don haka daga masara sai gero, shinkafa jifa jifa muke iya
saye. Ga uwa uba duk gonakin da ake nomawa mahaifina kakaf goggo fattu ta
sayar, bama samun ko kwayar masara daya daga gona sai dai mu auna daga
albashinsa, sai ‘yar kyautar da daddy yake yi masa akai akai idan yaxo. Tunda ta
abunda xa’a ci ake, babu wanda yayi tunanin a saka ni a makaranta. Da kanwar
mahaifiyata ta xo wato goggo joda daga garinsu Cameron sai na bi ta muka tafi
can na xauna. Hakika na ji dadin xama a kasar kuma na sake, ina walwala acikin
dangin mahaifiyata suna sona sosai. Duk da kauye ne, talakawa, Fulani ne amma
komai ya wadata. Ga abinci iri iri, ga ruwan fanfo, ga wutar lantarki.
Duk wasu labaru da tarihin rayuwata, da ta iyaye na, da yadda suka hadu aka yi
auran, da yadda xamana ya kasance a hannun goggo fattu ina yarinya duk goggo
joda ta fada min, badan ita ba da ba xan san komai ba saboda da mahaifana basa
hira da ni. Amma mahaifiyata tana hira da kanwarta tana fada mata komai. Naja
baki na gum na rufe ban fada musu irin axabar da goggo fattu ta gana min a
saudiya ba. Sai dai duk sanda na cire rigata xanyi wanka kowa ya kalli bayana sai
ya tambaya ni “wannan shatin meye.” Kuma har rana irin ta yau ina kwaikwalo
robar wayar da ta shige min jikin nama na.
Wata na uku cur a Cameron sai kwatsam naga babana da direban daddy a mota
sun xo daukana wai daddy ne ya turo su, su xo su tafi da ni kano an samarmin
makarantar sakandire, rabi boko rabi Arabic ce. Bada sona ba na baro Cameron na
dawo kano don bana jin dadin gidan mu musamman dasu daddy suka kaura Abuja
ga tsananin rashin abinci.
Na iske daddy a kano, ya kira ni, sannan ya kira babana, mama ta muka xauna a
gabansa a kasa kan kafet.
Ya fara bayani yace “nayi matukar bakin ciki dana dawo daga tafiya aka ce an cire
kaltum daga makaranta an tafi da ita saudiya neman kudi. Naji tamkar in fasa ihu
saboda takaicin yadda kuka tauyewa yarinyar nan hakki, ku ka tauye mata rayuwa
gashi dai yanxu ta dawo ba dammar a mayar da ita aji uku na primary saboda ta
girma, in da Allah Ya rufa asiri ta shiga makaranta a can, tasan qur’ani, tasan baki
xataa iya karanta larabci aduk inda ta gani haka duk abunda aka fada mata da
larabci xata ji shine naga ya dace asamar mata sakandire wacce ta hada Arabic da
boko sai kwakwalwarta ta tafi daidai saboda har yanxu ta iya karatu da rubutun
boko don haka ta je ta gurgura ta tsinci abunda xata tsinta.”
Daga karshe ya roke su Allah da Annabi su barni inyi karatu kada su sake cire ni su
ce xa’a kaini Makka ko xancen aure. Ni kuma yayi min fada da na mayar da
hankali nayi karatu musamman a bangaren boko shine wanda ban iya ba sosai.
Muka yi masa alkawarin xamu bi duk abunda ya fada mana.
Makarantu uku na shiga, makarantar boko da safe, ta Islamiyya da yamma sai
kuma ta dare karatun hadisi ake da tauhidi. Nayi bakin jini a waje ‘yan makaranta
saboda na fisu kokari, nice karama a ajin manya cikin xabga xabgan ‘yan mata,
suma na fi su kokarin domin kullum ni nake karatu da larabci malami yana fassara
musu. Duk in da aka bude daga cikin kowanne littafi sai kiga na iya saboda an
dade da koya min a Makka. Hakan ya jawo min farin jinni a wajen malamai
kacokan suna so na, wasu ma daga cikinsu so irin na soyayya suke nuna min.
yayin da hakan ya jawo min tsananin bakin jinni a wajen dalibai kacokam sun
tsane ni, ba ni da ta kamammiyar kawa guda daya saboda ana tsoran kada bakin
jinina ya shafe su.
Kullum idan aka tashi daga makarantun nan da nake xuwa guda uku, sai dalibai
sun tare ni sun ja min kunne akan kada in sake dagewa wajen yin karatu tiryen
tiryen bayan su basu iya ba, malamai su dinga yi musu kallon dakikai. Wasu kuwa
saisu tare ni su dake ni akan samarinsu da suke ji kishin-kishin yanxu ni suke so
alhali ni ban san hawa ba ban san sauka ba. Ba na saurayi, ban taba yi ba saboda
da wadannan dalilai duk sanda garin Allah yawaye sai na ji gabana yana faduwa
ina fargabar tafiya makaranta saboda a makarantar boko ma nice monita a ajinmu
saboda kokarina suma sai suyi ta xagina idan na rubuta sunan ‘yan surutu, a
islamiyyar yamma har abun yafi haka ta dare ma haka. Abu ya hadu ya yi min
yawa na rasa yadda xanyi da rayuwata gashi babu wanda xan iya tara in fadawa
har iyayena tunda ba hira muke yi dasu ba.
Wata rana daddy ya gani da idonsa an tashi daga makarantar islamiyya da yake
makarantar bata da nisa daga gidanmu da kafa nake xuwa. Shi kuma ya xo gari,
ya xo wucewa xai tafi gida sai ya hango manyan ‘yan mata su hudu sun tarar min
suna ta dukana suna yi min kwallo da jaka da dan kwali. Ya tsaya da mota yayin da
ya fito a gigice ya xo ya raba yana daga ido sai yaga ashe nice. Ya fatattake su,
yahau lallashina yayin daya dauko tissue ya bani na goge hawayena, ya karkade
min hijabi na da dan kwali na ya bani na sa ke haka jaka ta da kan sa ya dauko ya
saka min a mota yace in shiga gidan gaba in xauna. Bayan ya bani baki kuka ya
tsaya sai ya shiga yi min tambayoyi a kan abunda ya hada ni da manyan ‘yan
mata har guda hudu fada. Ya ce a iya sanin da ya min bani da jan fada amma yaya
akayi na tsokane su.?
Da farko na boye masa nace ba komai saida naga ransa ya fara baci, ya fara
Magana cikin tsawa da fushi sannan na xayyano masa duk abun da yake wakana a
duk makarantun da nake xuwa cewar haka ake tare ni kullum ana dukana da xagi
saboda na fi su kokari. Ya tausaya min matuka amma ransa yabaci saboda ban
fada masa tuntuni ba ya dau mataki. Yasan ba xan fadawa iyayena ba don bana
hira dasu meyasa shi ban fada masa ba da wuri ba tunda ya xo garin a ‘yan
kwanakn?
Nayi shiru ban bashi amsa ba.
Sannan yayi min wata tambaya cikin wata tattausar murya y ace “kaltum ada
bakya boye min damuwarki, ada bakya shakkar ki tare ni ki fada min abunda yake
damunki ko abunda ki ke so amma a yanxu bakya yi. Kina so in yi fushi dake? ”
Na girgixa kai yayin dana sunkuyar da kaina nace “a’a”. y ace “to daga yau ki tare
ni ki fada min duk wata damuwarki, xan yi miki maganinta in shaa Allahu. Gobe da
safe xan je makarantarku ta boko in sanarwa malamanku da shugabannin
makarantar duk abun da dalibansu ke yi, haka da yamma xan je islamiyya, ta dare
ma xan je xan fada cikin babbar murya duk dalibar da ta sake dukanki sai nayi
shari’a da iyayenta. A haka muka isa gida, bai bar niba saida y ace in rubuto masa
duk abunda nake da bukata na makaranta da na gida na ci da na sakawa a jiki,
sutura da man shafawa da sabulai. Haka kuwa aka yi na je gida na rubuto masa ba
tare da na nemi shawarar kowa ba, na shiga har falonsa washe gari da sassafe na
durkusa na gaishe shi sannan na bashi na wuce xuwa makarnta.
Kafin a fito breakfast sai ga daddy da shugaban makaranta (principal) a ajinmu.
Principal ya tashe ni tsaye yace un nuna masu dukana, daya bayan daya na dinga
xakulo su, sannan ya sa su wankin bandaki da sharar sati guda. Haka da yamma
daddy ya xo ajinmu shi da shugaban makaranta, irin na safe aka yi musu, suma na
nuna su . amakarantar dare ma haka aka yi, shike nan daga nan na sami salama
da kwanciyar hankali, ganin daddy da aka yi yayi shiga ta alfarma, ga lumtsetsiyar
mota shi ya kara min daraja a wajen malamai da dalibai suka dinga gulma suna
cewa ashe ni ‘yar gidan masu kudi ce har ake cewa babana mai gadi ne. duk
xancen ya dawo kunnena sai nayi dariya kawai. A gaskiya kuma na fi kama da
daddy fiye da mahaifina saboda daddy fari ne dogo mai hanci sam dansa mashkur
bai yi kamada shi ba, ya fi kama da anty salaha mamarsa, baka ce gajera amma
dai fuskarta mai kyau ce tana da dogon hanci siriri.”
Madina ta nisa tace “cafdijam ana irin wannan kara da xumunci ashe? Amma
daddy nan yana da kiriki, a xamanin nan waye xai tsaya ya damu da rayuwar ‘yar
mai gadinsa? Irinsu basu da yawa a xamanin nan.”
Kaltum t ace, “sai lokacinda wani dan unguwar mu mai suna Hussain ya takura
yana sona, ya hana ni sakat a unguwarmu. Gidansu ajikin katangar gidan mu yake.
Har gidansu ya fi gidan mu girma da kyau . Ya ce shi fa a duniya babu macen da ta
yi masa sai ni, ni kuma bana son sa dan ban isa xance ba dan haka duk sanda ya
xo sai in gudu gida in ki fitowa. Haka idan xanje makaranta sai ya dauko
lumtsetsiyar mota wacce babansa ne kadai yake hawa a gidan yace sai na shigo
ya kai ni makaranta ni kuma in ki shiga. Ya yi ta bina a mota har bakin get din
makarantar. Idan an tshi ma shi xan gani dam ma ma haka.
Da daddy ya xo gari na fada masa, ya dauki mataki kuwa ya jawa yaron kunne
kuma ya shaidawa mahaifinsa aka yi masa fada cewar ya kyale ni in yi karatu,
sannan na sami sa’ida ya rabu da ni. Duk wannan abunda ake yi iyaye na basu
sani ba, ko da sun sani ma basu nuna min ba, nima kuma daman ba fada musu
xan yi ba.
Ina aji hudu na sakandire wato S.S 1, domin an yi min tsallaken aji guda daga aji
daya aka kai ni aji uku saboda kokarina a dukka bangarori biyu boko da na addini.
Shekaruna goma sha biyar a duniya, tsautsayi ya rufto min har na tsinci kaina a
cikin wannan hali.” Sai ta rushe da kuka.
Madina ta daga kan kaltum ta goge mata hawaye ta tambaya cike da mamaki “ban
fahimce ki ba? ”
Kaltum ta goge hawaye da gefen siket inta, t ace, “wata rana da maraice muna
xaune ni da iyayena a tsakar gida. Ina wanke wanke a gefe, babana da kannena
suna xaune a kan tabarma suna cin gyada, mamana tana xaune a bakin murhu
tana tuka tuwo, yayin da iya Altine tsohuwar da nace miki a baya ‘yar uwar
mummy salaha ce wacce take xaune a gidan tana kular musu dashi.”
Madina t ace, “eh na gane ta, me ya faru? ”
Kaltum ta nisa t ace “itace ummul aba’isin da ta hada min tuggun daya kawo ni
nan.”
Madina ta gyara xama ta yi tagumi tace “ina sauraronki kaltum.”
Kaltum ta yi shiru yayin da hawaye ya fara diga da alamar maganar da take shirin
fitowa daga bakin xaxxafa ce, tana yi mata kuna a rai.
Ta ce “iya Altine ta dube ni ta yi murmushin munafurci t ace “oh kaltuma gidanku
shiru-shiru da ke tun daxu ana ta hira da kannenki ko uffan baki ce ba kamar
bakuwa. Wannan da rikon ki ake yi a gidan nan ba iyayen ki ba ne ai sai ace
wahalar dake ake yi, kowa yana cin gyadar nan

Please Login or Register in order to submit comment