Reading adon dawa Chapter 33 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daman nafiso mu hadu a Kano nima zan shigo kano in anjima dan
haka bayan magruba kuzo ku sameni agidana zamuyi wata magana.
sai madina ta tambaya cike da fargaba alh badai wata matsala bace dai ko?
ka fara fadamin don hankalina ya kwanta.
alh adnan yayi dariya yace alkhairi ne Madina wannan karon dai maganata ce da kaltum.
madina tayi dariya tace AlhamduLillahi haka nakeso inji saboda har na fara damuwa ina
tambayar zuciyata ko lafiya har yanzu bakayi magana ba gashi harta sami admission ta
fara zuwa makarantar BUK.
yace ai maganar ta taso gadan-gadan yau dai komai zai bayyana.
Madina tace Allah Ya tabbatar sai munzo na gode, farin ciki ya rufe madina suka dade
suna tautaunawa da Abba har saida ta daidaici yamma tayi lokacin dora abinci dare yayi
sannan ta tashi ta shiga bangaren mummy hafsat ta durgusa ta gaishe ta ta tambaya
cike da ladabi mezan dafa miki yau mummy?
mummy hafsat tayi dariya tace 'yata Madina ki dafa manan duk abunda da kika ga
yadace da tsofaffi,
su dukka suka tunsure da daria, madina tace to shikenan abinci kala goma zanyi muku
keda daddy duk sai kun cinye.
karfe takwas nadare afalon alh Adnan tayiwa su Madina, ga alh Adnan ga kaltum azaune
akan kafet ga Abba da madinarsa akusa dashi akan kujera daya gefe kuma sofi ce da
abun kaunarta saleh su ma suna sauraron abunda alh Adnan zaice, kowa zuciyarsa cike
da fargabar abunda yasa alh Adnan ya tara su.
can alh Adnan ya daga kai ya dubi kowannen su yayi murmushi yace AlhamduLillah da
Allah Ya bamu ikon haduwa anan kafin muce wani abu Madina ki bude mana taro da
addu'a,
Madina tace suka karanta salati goma ga Annabi (s.a.w) sannan ta dinga koraro addu o i
kala kala daga karshe ta shafa.
alh Adnan yace nakasance ina kaunar yar yarinyarnan kaltum tun tana yar yarinya
karama naga ya dace ta sami mai tattalin ta da nuna mata kauna kamar kowanne yaro
domin ta rasa shakuwa da shagwabarda zata yiwa iyayenta naji inason kaltum tamkar
nina haifeta mun shaku tamkar kawata haka muke labari duk yanda zanyi na gyara
tarbiyarta nayi haka, nayi kokarin turata makaranta don ta samo ilimi kamar kowacce
'ya, duk inda kakai ga iko da dan wani bakayi kamar iyayenda suka haife sa ba, sun fini
iko
da ita saboda bana gari suka cireta daga makaranta suka turata makka wai neman kudi
taje ta wahala aka bautar da ita tamkar baiwa, nayi takaici nayi kuka don takaici na
hakura har saida Allah Ya yanke mata akadawo da ita tazo takoma makaranta sannan
wasu shekaru aka sake daukarta bada shawaraba akasake tafiya da ita sudan, shekaru
biyu da tafiyarta muna tunanin tana
makkah sai ga marigayiya goggo fattu an kamo ta sai a lokacin ma take fada ai basa
tare da kaltum ta barota a sudan, dana bincika sai aka ce ai bara sukeyi a sudan na aika
kudi a daukota aka daukota tabbas kamar yadda saleh da sofi suka fada cewar ni nafi
can-canta in auri yarsu saboda ni nafi kowo sanin darajarta zanfi riketa amana fiye da
kowane da na miji hakane gaskiyane saidai kash!
kaltum ta hadu da wanda takeso fiye dani wanda take ganin zatafi samun nutsuwa
dashi, wannan kuwa shine mambela.
sai kowa ya zazzare ido yana kallon alh Adnan daga nan suka hau kallon kallon a junansu
hawaye ya surnano daga idanuwan kaltum ta girgiza kai tace basai mambela zan aura
ba,
sofi ma ta fashe da kuka tace alh yarinyarnan batada zabi mu bata taba ce mana tana
da wani mambela ba niban ma taba jin sunan ba.
alh Adnan ya girgiza kai yayi murmushi yace sofi ke baza ki san mambela ba kuma na
yarda vaki sanshi ba din saboda bata hira daku yanada nasaba da babban kuskurenda
kuka tafka arayuwa na rashin janta a jiki, tun farko ta tashi tana dar-dar daku bata sakin
jiki daku tamkar dodonni wannan ba daidai bane amma nida take hira dani take fadamin
matsalolinta ta shaida min tana son Mambela, Madina tayi rayuwa dasu acan ta tabbatar
min akwai mambela daga dukkan alamu shima yana kaunarta sosai tsakani da Allah.
Madina tayi ajiyar zuciya tace zancen mambela ai ya wuce alh duk inda aka kai da yabon
kyawawan halayensa baikai kamar ka ba, duk yanda mambela ya kaiga sonta da kula
dakai bai kaiga yadda ka kula da rayuwar kaltum ba itama ta sani kowa anan ya sani ba
kaltum kadaiba koni danazo a baya bayan nan kayimin halacci da ko dangina ba aminba
nida mijina Abba babu irin addu ar da bama maka, saita fashe da kuka.
malam saleh yace alh mudai kai muka sani, kai muka bawa babu kyau mayarda hannun
kyauta baya, yanzu mudai ba mu san da wannan saurayin nata ba, ko baxa ka aureta ba
bazan bashi ba tunda ban san asalinsa ba, ba yarenmu daya ba kuma ba kasarmu daya
ba....
alh Adnan yayi caraf yace amma addininku daya ko?
mambela mutum ne mai nitsuwa wanda yasan ya kamata, mai amana da tsoron Allah na
yaba da halayyarsa kuma na yarda yana son kaltum zai riketa amana ko bayan ranmu.
sai kowa ya zubawa alh Adnan ido suna duban sa duba na rashin fahimta ko basu furta
ba tambayarda suke jerowa azuciyoyinsu bai wuce kai ina kasan mambela da har ka
shaida shi da irin wadannan kyawawan halaye?
alh adnan yayi murmushi ya dubesu daya baya daya yace zaku tambaya ina nasan
mambela da har na shaideshi?
to ba almara bace kuma bana duba amma zan iya rantse muku da Allah duk halayyan
nan dana zayyano muku mambela ya hadasu dukka.
kaltum tayi ajiyar zuci yayinda kwakwalwarta ta kasa tantance abunda alh Adnan yake
nupi ta tambayi zuciyarta shin ko Madina ce ta bashi tarihin mambela?
sai Madina tace alh abunda kake fada akwai daure kai don kaltum ta baka labarin abun
alkhairinda yayi mata shine ka gama tantancewa har ka shaideshi?
ko kuwa alh Sa'adu ne ya fada maka haka?
alh Adnan ya girgizai ya kwashe da dariya yace ga kaltum nan zaune ki tambayeta nida
ita mun taba zama munyi labarin mambela?
tun a waya da ta ambaci sunansa bata sake ambatonsa ba a gaba na ba, haka Sa'adu
babu wanda yaki jini irin mambela sbd har hanci ya fasa masa a garin kwato kaltum suka
yi dambe har yau zaginsa yakeyi yace sanda yaje dauko Madina ma sun hadu ko kallon
juna basu ba don haka zancen ko wani ne yabani labarin ma ki cire.
ni na san mambela kuma na zauna dashi har tsawon shekara uku ina ta gwada shi a
bangarori daban daban kuma yaci jarabawata kuma ya cancanci ya auri kaltum .
Sai sofi da malam saleh suka daura hannu akai suna ambaton InnaLillahi wa inna ilaihi
raji'un.
yayinda kaltum taji maganar alh Adnan tamkar almara ko kuma mafarki ta rasa dalilin
dayasa taji zuciyarta ta kamu da farin ciki Mai tsanani ta tsunkuyar da kanta kasa tana
jinjina hikimar ubangiji tana mai gaskata
addu ah bata faduwa kasa komin daren dadewa Allah Ya na amsa addu ar bayin Sa duk
abunda suka rokeShi, ta kagu taji karshen labarin.
madina ta tambaya cike da mamaki alhaji ina ka hadu da mambela?
kaje bur sudan ne?
alh Adnan yayi murmushi yace ko sudan air port din nan ban taba hawa ba balle in yada
zango a airport din Khartoum tunda nake a rayuwata amma saiga Allah Ya hada ni da
mambela tun bayan dawowar kaltum da wata
guda,
membela ya kirani a waya kasancewar bayajin turanci balle hausa sai malam Abdulkadir
yayimin magana da hausa.
kaltum tasan malam Abdulkadir din, malaminda ya basu masauki a Khartoum wajensa
mambela yaje ya karbi lambata saboda a ranarda nakira sa'adu ya bani malam shima
munyi magana daga baya malam din ya kira ni da lambarsa nima nakirashi to bai goge
lambar ba yana da ita, mambela yayi masa bayani shima kuma yayin min bayanin komai
game da soyayyarsa da kaltum ban dauki abunda muhimmanci ba a nan na bar zancen,
saida aka kwana biyu mambela ya sake kirana wannan karon kuma abokinsa ya bawa
waya mukayi magana donshi yanajin turanci, sake rokona sukayi wai in ba shi izini yazo
ya auri kaltum, amsar da na basu shine ai kaltum ba yar tsana bace, na kashe wayata na
sharesu mambela dai bai daina kira ba wani lokaci in fahimci larabcin da yakeyi nima in
gwamutsa
masa nawa ya fahimce abunda ya tsinta bayani dai dayane kaltum ta dawo gida bata
koma garin ADON DAWA ba, yar makarantane bazata auri wanda bashida ilimba, kunsan
saboda maganarnan dana fada masa ya bazama burni neman lesson teacher da zai koya
masa turanci, anyi watanni da dama banji mambela ba sai gashi ranar ya kirani yana
magana da turanci duk da bai kwareba amma zaka fahimce shi yace min ya shiga
makaranta saboda kaltum don na yarje mishi ya aureta, saina fara gaskata soyayyarnan
dayake ikirarin yana yiwa kaltum, don haka saina tambayeshi meyakeso yanzu?
Yace min so yake abashi izini yazo da iyayensa Nigeria su nemi auren kaltum.
sai nace masa a a kada yazo da iyayen sa yazo shi kadai tukunna, nayi masa hakane don
na kure shi naga ko bazai zo ba sai kwasam najishi a waya yana tambayana adireshina
na Abuja, bayan kwanaki biyu da yin wayarsu saiga mambela dan ADON DAWA a
ofishina an rakoshi.
Madina tayi kabbara gami da cewa Allah mai iko Allah mai hada soyayya, yanzu
mambela sai daya zo Nigeria saboda kaltum?
ashe bai hakura ba?
malam saleh ya gyara zama yana sauraron irin wannan abun al ajabi yayinda sofi ma ta
buga tagumi tana sauraro, Abba ma yakura wa alh Adnan idanu yana kallon hikima da
dabaru irin na mai ilimin da yake amfani da iliminsa,
kaltum ta dade da bude duk wata hudarda dake jikinta tana sauraron labarin, ta kasa
tantance karshen abun da zai faru taji ta sake son mambela ta sake girmama alh Adnan
tabbas ko baban ta daya tsuguna ya haifeta ba zaiyimata irin wannan kiwon da tattalin
ba irin yadda a alh Adnan ya damu da rayuwar ta ba.
saiyaci gaba da cewa sai gani ga membela mun hadu muna kallon kallo ko kadan
bantaba zaton haka membela yake ba, wayayyen mutum natsattse mai ilimin addini
shine babban abunda yasa na fara sauraronsa nan bayan nabashi abinci da ruwa ya huta
saina shiga yi masa tambayoyi game da tarihin rayuwarsa banajin ya boye mini komai,
ya bayyana min koshi wanene da turanci duk muke magana saidai idan turancin ya
kakare ya mako larabci duk ina fahimtarsa, yayi labarinsa ya gama sannan nace meyasa
ya tsallake duk yammatan sudan kyawawa ya makalewa kaltum?
saiyace ba ruwansa da kyau ko kudi shi dai yana son kaltum don Allah sai kuma
halayyarta ta gari da nutsuwa yasa yaji baya son kowa sai ita, zai kuma dauwama cikin
damuwa idan bai auri kaltum ba yayi kokarin rabuwa da ita
tunda ta tafi zuciyarsa ta kasa daurewa ya
shaidamin a shirye yake wajen yin duk abunda aka umurce shi don ya sami kaltum, na
zayyano masa dokoki masu yawa kuma masu tsauri da wahala sai ya amsa da cewa
zaiyi duk abunda na umurce shi, sharadi dayane baiji dadinsa ba danace bazaiga kaltum
ba har sai an shekara uku cur saiya gama cika duk rukunnan dana gindaya masa kuma
sai kaltum ta gama makaranta sannan zasu hadu.
ya rokeni da nabarshi ya ganta ko sau dayane, nace mai ai kaltum bata garin nan tana
kano garin kano kuwa da nisa daga Abuja, don sai an hau jirgi kafin aje.
Abba ya gyara zama yayi murmushi yace alh wanne irin sharuda ka gindaya masa haka?
alh adnan yayi dari ya yace ce masa nayi idan ya auri kaltum a ina zai ajiye ta?
saiyace a Khartoum zai ajeyeta bazai kaita kauyen su ba saboda suna da gidaje a burni,
sainace a'a bazan bar kaltum ta zauna a Khartoum ba saidai idanshi zai dawo Nigeria ya
zauna,
Sai yace min iyayen sa bazasu yarda ba amma in bashi dama yaje ya gina rayuwarsa a
dubai saboda yanzu abunda yan kasarsu suke yi kenan, kawunsa ma yana dubai ya ginu
yayi kudi yana kasuwanci ta jirgin ruwa yake tura kaya sudan dama yanada sha'awar yin
hakan, don haka yakeso ya sayar da gidanjensu guda biyu a Khartoum ya ja Jari,
iyayensa bazasu hana shi ba.
nace yaje dai ya shawarci iyayensa idan sun amince yazo zan hada shi da abokan ciniki
na na gari wadanda zasu saka shi a harkar kasuwancinsu a can dubai din, na shaida
masa nima ina kasuwanci a dubai harma na mallaki gida a dubai a jamaira so nake d'ana
Mashkur ya kammala karatunsa a London ya dawo dubai ya kula da harkokina na can,
sai mambela yayi murna ya kwana bakwai tare dani a Abuja, hotel na kama masa duk
yamma ina daukarsa in zagaya dashi gari har yake sha awar kasarmu yana cewa ashe
Nigeria kasace mai kyau haka mai dimbin arziki amma mutanen kasarnan suke zuwa
sudan suna bara ana korarsu suna kin tafiya tamkar karnuka?
nace masa mutuwar zuciyane kawai da rashin hakuri da kaddara, munada arziki
akasarmu rashin shugabanni na garine babbar matsalarmu a kasar.
membela ya koma kasarsu bayan watanni naga ya kira ni da lambar dubai ya shaidamin
ya dawo dubai harya fara kokarin gina sabuwar rayuwar sa, na sake shawartarsa daya
nemi ilimin boko don bashida ilimin boko, ya shiga wata makaranta mai kama da
diploma kuma yaki da jahilci ce amma zaka fita da satifiket dinda za a iya baka aiki, abur
Dubai makarantar take ana koyarda turanci da larabci, lissafi dakuma kompita tamkar
yanda ake koyawa yara yan aji daya kuma da karfe shida na yammah zuwa karfe takwas
na dare ake zuwa aji, don haka tundaga safe har yammah mambela yana kasuwancinsa,
karatun na wata shida ne kacal saidai in dai kanaso kaci gaba akwai makarantar da zaka
shekara kanayi ita ma satifiket da za a baka, ya kirani a waya ya shawarceni cewar ya
gama wannan makarantar yanaso yaci gaba da karatu nace yaje ya shiga ya shiga yaci
gaba da karatu na shawarceshi ya shiga makarantar koyar tuki dake quasis don y huta
da zirga zirgan hawan bus daga ajman garinda yake zaune zuwa bur dubai inda
makarantar take idan yaje ya tafi makarantar koyan boko, saida ya shekara cur a dubai
sannan naje dubai na yi masa shigar ba zata awajen container inda ake lodi na iskeshi ya
tube yana loda kaya har abin tausayi, muka gaisa naje har gidan da yake zaune shi da
yan kasarsu nayi masa kyautar bata taka kara ta karya ba na taho abuna.
mambela yake fadamin a hira cewar yasha yi min zargin ni mugu ne banida tausayi na
rabashi da iyayensa na kawoshi yana wahala kuma dakyar in zan yarda ya auri kaltum
yaudararsa kawai nake yi sai daga baya ya fara ganin alfanun abun, daman masu iya
magana na cewa bayan wuya sai dadi, dai dai
sanda ya gama makarantar koyan tukin moto ya sami driving liences abune mai matukar
wahalar samu a dubai daga nan sai ya sayi moto wacce ba abune mai tsada ba a kasar
sannan ya sami sakamakon babbar diploma,
da sakamako mai kyawun gaske yadda zai iya samun aiki a dubai sannan ya kware
wajen magana da turanci da iya rubutu da turanci, ya iya amfani da computer.
sannu ahankali saiga mambela ya goge a dubai yasan komai ya sami alkhairai masu
yawa harta kai ta kawo shima yana da yaranda suke yi masa aiki suke samun alkhairi a
wajensa.
ya shekara yana aiki a wata ma'aikata da take garin NASIR KAIMA daga baya ya daina da
yaga kasuwancin yafi ci, sunata tura kaya daga Dubai zuwa sudan nan danan ake
juyewa a hada masa kudinsa, koda yaushe mambela yana tuntuba ta awaya yana
shaidamin duk irin cigabanda ya samu nikuma sainayi masa addu ar fatan alkhairi. naje
dubai naga canjin da ya samu a rayuwarsa yayi min hidima tamkar yanda ake karrama
gwamna ko shugaban kasa haka shida abokansa da kawunsa sukayi min, bayan
abubuwan arziki da suka hadamin nida kaltum nace suyi hkr bazan iya daukar abunda
suka bani ba nagode na taho na bar musu kayansu duk da basuji dadi ba dole ce tasa
don babu inda zankai himilin kayan nan tunda ni kadai nake abuna kaltum bata sani ba,
a wani bangaren kuma nasa malam Abdulkadir na Khartoum yaje ya binciko min asalin
mambela, su waye iyayen sa, yaya rikon addininsu yake.
ya kira ni bayan ya gama binciko min asalin mambela dan asaline karewama su suke
rikeda sarautar garin su ba boyayyu bane kowa ya sansu kuma gidansu gidan malamai
ne masu riken addini ne.
da lokaci ya cika na gama tabbatarwa da abunda nake so in tabbatar gameda mambela
sai na umurce shi yazo Abuja yasameni muyi magana.
abangaren kaltum na binciketa kuma nasa kaninta ya taya ni bincike muka tabbatar har
yanzu tanason mambela idan ta kebe ita kadai tana koke koke tana yawan saka hoton
mambela a gaba tana kallonsa, Abdul ya shaida min ni ma kuma na lura da haka na dai
amsa muku ne kawai zan auri kaltum amma ni a zuciyata nasan wanda ya dace da ita,
aikina shine in tabbatar mun aura mata miji na gari wanda zai riketa amana ko babu
idanun mu.
.
ADON DAWA 48
.
TRUE LIFE STORY
.
na dai amsa muku ne kawai zan auri kaltum amma ni a zuciyata nasan wanda ya dace
da ita, aikina shine in tabbatar mun aura mata miji na gari wanda zai riketa amana ko
babu idanun mu.
AlhamduLillah na cika alkawari dana dauka, na cika amanarda na kudira a raina zancika
shine na aurar kaltum ga mutumin da ya dace wanda zai riketa amana ta dauwama a
cikin farin ciki, mambela ya dace da ita da kyakkyawan zato zai rike ta amana in shaa
Allah,
Allah sarki alh mungode Allah Ya biyaka, kanuna mana kauna, sofi ce ke fada yayinda
take zubarda hawayen farin ciki kaltum ma kukan takeyi ta rasa kalmar da zata yi
amfani da ita wajen godewa wannan bawan Allah.
madina ta dubi Abba tace kaji wata hikima ta ubangiji ko?
Allah sarki rayuwa ashe akwai mutane masu koyi da hali irin na sahabbai irinka alh ?
Alh Adnan yayi murmushi yace bancika son kuna godemin ba nayi ne don Allah ina
neman sakayyah awajenSa duniya da lahira, ku saurareni zan shiga daki na fito, saiya
miki ya tashi ya shiga dakin sa.
kaltum ta rugo tazo ta rungume Madina tasa kuka, Madina ta shafa kanta tana ta bata
baki sai kuwa sukaji motsin fitowar alh Adnan suka daga ido su dukka suka dube shi sai
suka ga su biyu shida mambela, idanuwan mambela akan sofi yanata kallonta domin
yaga sunyi kamada kaltum sosai kamar daga sama yaji kaltum ta kwalla kiran sunansa
yah mambela!!
ya waigo da sauri sai yaga abar kaunarsa kaltum saiyaji ya gigice gaba daya saboda ta
goge tayi kyau kamar ba kaltum dinda ya sani ada ba yaji tamkar ya sureta ya cafe saiya
daure ya koma gefenta ya zauna cike da farin ciki, cikin harshen larabci yace kaltum
daman ina da rabon in ganki a rayuwa ta?
AlhamduLillahi ko bazan aureki ba na godewa Allah da Ya nuna min ke a rayuwata kafin
in mutu, sai hawayen farin ciki ya surnano daga idanuwansu dukka biyun.
madina ta ambaci sunansa cikeda farin ciki sai ya juya da sauri ya dubeta sai yanzu ya
shaida Madina ce, itama ta canja ta goge kamar ba ita ba sai mamaki mai dimbin yawa
ya rufeshi ya fada cikin yarensa na ADON DAWA a ah yaya naganku kunzama tamkar
larabawa dama kunfi jin dadin a kasarku kukaje kasarmu kuke wahala?
dubi yanda kuka zama fa?
kaltum da Madina sai dariya sukeyi kawai donsu kadai sukeji abunda yake fada.
Madina cikin harshen turanci ta gabatar masa da Abba, mambela ya mika masa hannu
suka gaisa cikin harshen turanci yace Abba na dade inajin labarinka ashe baka rasu ba?
Madina ta gabatar masa da saleh da sofi cewar ga iyayen kaltum, da taga mambela na
kokarin mika masa hannu sai tayi masa larabci tace ya durgusa ya gaishesu al'adarmu
ba a hannu da surukai don haka mambela yaje gabansu ya durgusa ya gaishesu da
larabci suka amsa da hausa ya dawo ya zauna a kasan kafet kusa da abar kaunarsa
kaltum,
alh Adnan yayiwa mambela bayani cewar ya fada musu komai kuma in shaa Allahu babu
matsala komai zai dai daita yanzu abunda ya rage shine idan ya koma kasarsu ya taho
da iyayensa mata da maza da duk kayanda akeyi na al adarmu ta hausa wajen nemar
aure,
mambela ya tambayeshi me ake bukata a auren hausawa?
alh ya nuna kaltum yace ga amarya ka tambayeta ta yadda akeyin komai amma kafin
atashi daga wannan zaman inaso inbawa iyayen kaltum dama ko suna da abun fada ko
korafi ko suka gameda hukuncinda na yanke saboda kunada hakki akan yarku, wlh duk
abunda baiyi muku ba ku fada zan cenza ra ayina kuma bazan damu ba.
saleh ya girgiza kai yace ko da wasa baka taba zartar da hukunci akan kaltum wanda zai
zama ba dai dai ba ko wanda zata yi nadama daga baya ba, ka fimu ilmi kafimu tunani
kafi mu kula da rayuwar yar nan sunan mun haifeta ne kawai babu wata matsala wallahi
fatanmu Allah Ya bada zaman lafiya kaikuma Allah Ya saka maka da alkhairi,
sofi ma irin wannan addu ar ta dinga zazzago masa,
Abba da Madina ma sunyi masa addu'a da godiya a bisa kyakyawar niyyarsa.
kaltum ta durgusa a gabansa tayi masa godiya haka ma mambela sannan ya umurci
kowa ya tafi sai da safe kuma,
suka duguma su dukka suka fita daga falon,
alh Adnan kadai aka bari a zaune fuskarsa cike da fara a da alama yafi kowa farin ciki da
Allah Ya nuna masa ranar daya cikawa kaltum burinta.
Madina da Abba suka raka har motarsu suka shiga suka tafi sannan sofi da saleh ma
suka shiga gida,
mambela da kaltum ne a zaune akan kujera a farfajiyar gidan suna rera hirar yaushe
gamo hirar so da kauna suna masu godewa Allah daya sake hadasu badon sunaso ba sai
don dare yayi sukayi sallama kaltum ta shiga gida mambela ma ya shiga gida, alh adnan
dama ya nuna masa dakinda zai kwana anan ya ajiye akwatinsa tun sanda sukazo yadda
bacci ya gagari idanuwan mambela haka ya gagari kaltum juyi kawai sukeyi suna
tunanin juna yayinda farin ciki yayi musu katutu a zukatansu kamar wadanda suka hada
baki a alokaci guda suka ayyana aransu tunda bacci ya gagara gara su tashi suyi alwala
suyi sallah su godewa Allah dayayi musu wannan
babbar kyauta.
Madina ma da Abba suna can a gidansu sun raba dare suna hirar wannan abun al'ajabi
ashe sofi ma da saleh farin ciki ne ya hanasu
barci suma suna daga daki suna tattaunawa sai dai duk rabin hirar tasu addu a ce suke
jerowa alh Adnan suna yi masa fatan Allah Ya biya shi da gidan aljannah.
daya bangaren kuwa alh Adnan ne kwance kan gadonsa ya takure yayinda kuka ya kece
masa yana addu ar Allah Ya kara masa dangana da juriya rabuwa da kaltum domin yana
sonta har cikin ransa kuma yayi niyyar auranta saidai ya fuskanci zai tauye mata rayuwa
saboda akwai wanda takeso bashi ba don haka ya sadaukar da son da yake mata ya
bata wanda takeso donta sami nutsuwa arayuwarta shiya yarda da duk wani tsanani da
zai shiga na sanadiyar rabuwa da ita,
juyi kawai yakeyi yayinda zuciyarshi ke tafarfasa don tsananin tashin hankali da yake
addabarsa, yana kiran InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah Ka yayemin abunda nakeji
kada in dauwama dason kaltum a raina har gara in mutu da in dauwama cikin wannan
hali ,
ahankali yaji zuciyarsa na sanyi saiyayi wuf ya tashi ya shiga bandaki yayi alwala yazo
ya kwana yana sallah yana neman hakurin dangana da neman sauyi mafi alkhairi,
washe gari da safe sofi da kaltum suka dinga hidimar dafe dafen abinci kala kala don su
bawa bakonsu, sun san halin alh Adnan ba cin abincin safe yakeyi ba kofin shayi dayane
zaisha saikuma da rana ko sun kai sunsan bazai ci ba saidai mambela.
kannen kaltum ne suke jerawa kan daning table dinda ke falon alh Adnan yayinda alh
Adnan da mambela suke zazzaune a falon suna tattaunawa da alama alh Adnan shiryo
tafiya zaiyi harda yar jakar kayansa a gefensa, ya umurci mambela daya cigaba da zama
a gidan kamar na sati biyu ko uku Madina ta zayyano masa komai sai ya tafi ya shirya
suyi waya su fadi ranar da zasu zo sai a buga katin gayyata anan a rarraba suna zuwa
sai a daura aure ayi biki gaba daya.
farin ciki ya rufe mambela ya rumgume alh Adnan yayi godiya suka dungumo suka fito
zuwa bangaren su kaltum.
sofi da saleh suka fito da sauri suka durgusa suka gaishe shi, alh har zaka koma Abuja da
sassafe haka ko karyawa bakayi ba?
sofi ta tambaya cike da kulawa,
alh adnan yayi dariya yace ai yau akwai aiki saboda mambela nazo amma zan barshi
anan ya zauna har sawon sati biyu ku saba sosai kuma ya gana da amaryarsa sannan sai
ya tafi daga nan basai yaje Abuja ba idan ya shiryo sai yazo da iyayensa a daura aure ayi
biki akai ta dubai shi kenan, yasaka hannu a aljihu ya damko kudi ya ambulowa saleh a
hannunsa yace ka rike wannan saboda cefene ya karu adinga dafawa mambela abinci
mai kyau kuma kala kala ina kaltum din ne?
kaltum tayi wuf tafito daga daki sanye da hijabi tazo ta durgusa ta gaishe shi yayi dariya
yace kin iya abincin zamani kuwa kosai tuwo irin na sofi?
donshi shi tafi kwarewa kullum kaga sofi to muciya ce ahannunta tana tuki

Please Login or Register in order to submit comment