Reading adon dawa Chapter 28 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafka asarar da har abada bazan sami macen da zata yi kwatankwacin
rabinta ba ma balle ace irinta sak, na cuci Madina matana ne suka cuceni meya kaini
kara aure ma?
dan da ban auro Sa'ada ba daba ta dinga kulla mata tuggu ba nikuma na hau na zauna
nabiyeta na wulakanta,
Madina mace mai kaunata tsakani da Allah, madina kiyafe mini kuma yayan ta kuyafe
min danayi muku sanadiyyar rabaku da mahaifiyarku,
kutayani addu'a Allah Ya bayyana Madina Allah ma Ya fara amsar adduar da Ya bayyana
aka sami labarin kasar da take don a da ba amasan ko araye take koma ta mace. yadda
Allah ya bayyana inda take to in shaa Allahu Zai kawota gida ta zo dakanta idan tazo
kutayani rokarta ta yafe mini sannan tazo muzauna tare in sallami sauran matan gidan
tunda basu da amfani agareni, sannan inaso ku bujire ku nuna baku yarda ba bakwaso ta
auri wancan dan banzan yaron wato Abba don na fuskanci nemo ta yakeso yayi ya
aureta har nacinsa yasa iyayensa sunyarda zasu aura masa ita, ku aganinku ya dace ace
mahaifiyarku tana auran yaro karami?
ai zubar da mutuncine maku a wajenku abun gori ne idan kukaje gidan ma zai iya
korarku kasancewar yaga yanada kudi iyayen sa ma masu kudine gara ace mahaifiyarku
ta dawo hannun mahaifinku gaku ya yanmu muzauna tare ai yafi kwanciyar hankali ko
ba haka bane?
Babu wanda acikinsu ya bashi amsa saima murtuke fuska da suka sake yi sai Tasi'u
yafara tsorata da alama basa goyon bayan sa, har ya sallamesu suka bar falon babu
wanda ya furta masa kalma daya shi yayi kukansa ya lallashi kansa.
suna fita suka dunguma kofar gida don su sami lungu da zasu fake suyi shawara
kasancewar cikin gidan ko ina mutane ne, can wani kofar gida suka sami wani dakali
suka zauna Abdul hakim ya dubi yan uwansa yace Allah sarki mamanmu Allah Ya yi mata
jagora Ya taimake ta aduk inda take, mun saba mata mun zargeta alokacinda kowa ke
zarginta maimakon mukasance mu kadaine masu bin bayanta aduk duniya, na tabbata
dabadon abunda mukayi mata a asibiti ba da bata shiga duniya ta barmu ba, dako
saboda mu zata zauna a kasar koda kuwa za a dinga jefinta ne don tsana...
saiya fara kuka yayinda dukka suka rushe da kuka.
Abba Tukur ne ya bayyana agabansu basuga tahowarsa ba saida suka daga ido suka
ganshi a tsaye akan su, ya dubesu daya bayan daya sai yaji tausayin su, ya sunkuyar
dakai kasa sai hawaye ya surnano daga idanuwansa yayi karfin hali ya fara magana
amma kuka ya hanashi cigaba, ya dade a tsaye yana hawaye marar kakkautawa sai can
ya tsagaita yarasa wanda zai fara lallashi
acikinsu saboda tsananin halin kuka da yaran suke ciki, ya ce 'yayan Madina nasan
damuwarku wanda take dai-dai da damuwata nasan irin zafinda kuke ciki na rashin
mahaifiyarku wanda yayi dai-dai da yanda nakeji idan ma bai dara naku ba, kubar kuka
ku tayani da addu'a iyayena sumin lamunin tafiya,
zanje na karbo adireshi a wajen yarinyan nan
kaltum inje in taho muku da ita kusani ina so na auri madina saboda ina sonta saboda
Allah idan na auri Madina nagama samun farin ciki a rayuwata, nayi muku alkawari zan
rike muku mahaifiyarku tsakani da Allah daku 'yayanta gaba daya, kada ku biyewa
mahaifinku da yake fada cewar rashin kunya ce ni dan yaro inason in auri Madina, ku
tuna auren Nana Khadija da Manzon Allah S.A.W
Ya aureta tana bazawara kuma ta girmeshi bai haramta ba kuma bai hanata yi masa
biyayyh ba....
Abba bai rufe bakinsa ba yaji wata murya mai
firgitarwa daga bayan sa sai suka waiga da sauri a gigice,
Tasi'u ne ya fita a fusace daga cikin motarsa ya tunkaro Abba Tukur yana magana cikin
fushi yana nunasa da yatsa kai Abba kafita daga harkan gidana tunkafin ta kaimu ga
kotu, daman nasan kai kake tara yarannan kana yi musu hudubar banza to bari kaji na
fadamaka baka isa ka auri Madina ba indai ina raye ko kai ko ni.
Abba yayi murmushi yayinda ya zura dukka hannayensa acikin aljifan wandonsa ya
sunkuyar dakai kasa kamar mai tunani can ya dago yadubeshi yayi murmushin karfin
hali yace kada ka manta ka saki Madina saki uku, aurenta dakai ya haramta sai in har ta
auri wani ta fito sannan zaka iya mayar da ita, kaga ko bani zata aura ba sai ta auri wani
sannan takoma gidanka inhar zata koma kenan,
malam Tasi'u banzata akwai ranarda zaka dawo kana son Madina ba bayan musgunawa
dakayi mata ka wukantata ka koreta, banaji akwai wani nauyi ko kararta zanyi maka
akan aurena da Madina ba saboda bazan kira rabuwarku da kaddara ba kana sane ka
saketa iyayena sun lura inasonta sun kuma yarda in auri abunda nakeso don haka babu
mai hanani auren Madina...
a fusace Tasi'u zaikaiwa Abba mari sai yarike hanun nan da nan alh Isa da malam
muhammadu makwabtan su suka garzayo da gudu suka shiga tsakaninsu, akaja Tasi'u
zuwa motarsa Abba kuma aka kaishi gida.
hankalin 'yayan Madina yakara tashi ya sake tashi amma gaba dayansu sunfi amanna da
aurenta da Abba akan ta koma gidansu, gidan wahala da tashin hankali, fatarsu ma aga
Madina tukunna sannan afara zancen aure, yaran madina sunfison Abba sunsan shi
mahaifinsu dayake wannan fada ina yaga kudin jirgin da zai je ya daukota a sudan?
idan yadaukota ma ai bazai iya auranta ba saboda babu wani sauran igiyar aure a
tsakanin su, rabuwa uku ce Abba kuma in har an amince masa agidansu yanada kudinda
zai iya hawa jirgi ya taho da ita kuma sun yarda da sonda yake mata idan ya aureta zai
riketa amana ba ita kawaiba harsu kansu tun bayan da yashekara akwance a asibitin
london ya warke ya dawo yake basu duk wani abu da sukeso aboye naci kona makaranta
basu taba tambayansa wani abu sun rasa ba ko basu tambaye shi ba shi dakansa sai ya
kirawosu ya basu kudi mai yawa duk da ma yana tsoron basu kudi mai yawa kar
mahaifinsu yagane to inaga ya auri mahaifiyarsu kuma?
Abdul Malik yanzu jami'ar ABU zaria yake yana level 3 yayinda Abdul hakim yake level 1
a BUK, Shahida kuwa a sakandari take aji biyu duk wannan fadace fadace da ake yi har
ana ambaton kotu duk fa akan Madina ne to bata nan, ba amasan inda za a same taba,
gata batada niyyar dawowa kuma .
lalle Tasi'u dagaske yake kuma yadau abun dazafi saboda da daddare yashiga har cikin
gidansu Abba ya iske mahaifinsa da mahaifiyarsa a falo ya lankwashe kafa yakawo karar
Abba akan ya rabu da matar sa Madina,
abun yabasu mamaki domin su basu zata akwai ranarda Tasi'u zai sake waiwayan
Madina ba bayan juya mata baya dayayi yanunawa duniya yagaji da ita baya kaunarta,
irin tsawon lokacin da mummy hafsat take batawa wajen gargadinsa kada yasake ya
rabu da Madina amma baijiba sai gashi yau agabanta yana kuka yana maimaita
nasiharda tayi masa abaya yana nadama,
takaici yahana genaral tukur furta koda kalma daya tak har Tasi'u yagama yatashi ya
tafi,
mummy hafsat ce mai bashi hakuri amma ta shaidamasa basuda ikon hana Abba son
abunda yaji yanaso kasancewar Madina batada igiyar wani akan ta,
da alama baiji dadin abunda sukayi masa ba ba haka yaso jiba so yayi suce zasu tsinewa
dansu idan bai rabu da zancen Madina ba.
barister Abba Tukur ne da kaninsa engr Anas suka dira akofar gidansu kaltum da misalin
karpe biyar na yammacin laraba, suka ajiye motarsu a wurin get yayinda suka tura kai
cikin gidan, mai gadi ya taresu don jin wanda suke nema dasuka shaidawa malam saleh
kaltum suke nema saiya yi matukar mamaki gami da fargaba ya tambaya cike da firgici
lafiya kuwa kuke neman kaltum?
lafiya mana maigadi inji Anas yayinda yake murtuke fuska saboda rashin jin dadin
tambayanda yayi musu kasancewar yasan basu san shi ne mahaifinta ba, sai bai tamuba
ya shaida musu cewa batanan ta tafi makarantar islamiyyah sai karfe shida zata dawo,
sai suka koma wajen get suka shiga mota suka zauna zaman jiranta suka ci gaba da
shawarta abunda yake tafe dasu,
tajikin madubi Anas ya hango kaltum ita da kannenta suna kokarin tura get zasu shiga
gidansu ya fito ya kwala mata kira ta tsaya cak tana dubansa cike da mamaki ta rasa
inda ta taba ganin fuskarnan, ya karaso gareta yayi murmushi yace kada fa ace baki
gane ni ba kin manta gidan sojojin nan da kike zuwa a yankaba inda aka kusa zaneki da
belt kwanakin baya?
idan kin manta ai bazaki manta gidansu shahida ba yar Madina,
sannan kaltum ta tuna da fuskar ta kwace da dariya tace Anas ashe kaine?
malam saleh ya fito wuf ya dubi kaltum ya juya ya dubi Anas ya tambaya cike da bacin
rai waye wannan ?
Matsalan kaltum bata tautauna halinda take ciki da mahaifanta don haka basu taba
sanin labarin Madina ba balle ta shaida musu taje ta nemo danginta,
idan takama nan saita saki ta zargo can, zancen dai a cukurkude bai fahimceta ba don
haka yayi mata umurni ta shiga gida ba zata gansu ba,
Anas baiji haushiba saidai ma mamaki daya hanashi magana saboda baizaci mai gadi
yana da ikon hana yar maigidan abunda takeso ba, ya tsaya yana duban malam saleh
kawai har ya rufo get ya shige yabarshi tamkar gunki,
hankalin Abba ya tashi saboda yanaso ya shaidawa mai gadin cewar suba samarinta
bane kawai maganar Madina zasuyi, Anas yace su tafi kawai har yaushe zasu tsaya suna
rokar maigadi da wata tsummar rigar sa?
suje saisu dawo wata rana,
Abba yakasa sukuni kwana biyu da tafiyarsu yaji bazai iya jurewa ba har saiya dawo yaji
labarin madinarsa don haka bai gayyaci Anas ba saiya figi motar sa yayi gidansu kaltum
tunda yaga hanya, yazo da yamma tunda yasan jummaa ne babu issalamiyyah tsayuwar
sa abakin get din kenan yayi dai dai da lokacin da alhaji Adnan ya iso daga Abuja don
bazai ya shiga da motarsa ciki ba saboda Abba yatare kofa, kallon-kallon aka hau yi a
tsakaninsu alhaji Adnan, ya fuskanci tabbas Abba bai sanshi ba ne maigidan ba, kuma so
yake yashiga da motar ciki don haka sai ya fito ya dubi Abba yayi murmushi yace ranka
yadade kozaka matsa gaba inaso inshiga da mota ciki.
Abba yayi sauri ya shiga mota yace kayi hakuri na tareka don Allah idan ka shiga ciki
Kamin sallama da kanwarka kaltum,
mamaki ya dabaibaye zuciyan alh Adnan ..

ADON DAWA 38
.
TRUE LIFE STORY
.
mamaki ya dabaibaye zuciyan alh Adnan ya ratso har fuskarsa ya dubi Abba ya dubi
tsalaleyar motar da yake ciki,
bayan ya matsar da motarsa sai alhaji Adnan ya danna horn malam saleh ya bude masa
get ya kutsa ya shiga cikin gida, bayan yan sannu da dawowa sun iso suka kwashi
tsaraba zuwa cikin gida wato kaltum da kannenta kenan daga yanda alhaji Adnan ya
amsa mata da yadda ya kalleta ya watsar tasan ba haka ya saba yi mata ba, tabbas
akwai dalili daga yanda malam saleh yaga yau alh Adnan baya fara'a yasan ba lafiya,
don haka sai hankalin kowa ya tashi,
alh adnan yafito kofar gida batare dayayi bayani ba,
tabbas malam saleh ya zargi ko yan gulma ne suka fada masa cewar samari sunzo
neman kaltum shekaran jiya.
alh Adnan yakarasa har jikin motar abba a inda ya iske shi a tsaye yayi masa sallama ya
mika masa hannu suka gaisa,
alh Adnan ya dubi Abba yayi murmushin karfin hali yace kaltum kake nema ko?
daga ina yayi?
murmushi yace sunana barista Abba Tukur a unguwar yankaba nake .
alh Adnan ya kura masa ido yana dubansa can yayi ajiyar zuciya yace naji sunanka yaro
sai kuma inji dalilin nemanta da kake yi, daman ka santane kokuma tasan da zuwanka?
abba yayi dariya domin yaji tambayoyin sunyi masa kama da tambayoyin da lauyoyi
sukeyi wa mai laifi a kotu, ya ce kaltum tasanni amma batasan yau zanzoba nazo
shekaranjiya mai gadinku ya hanata zo wajen mu dalilin zuwana bawani abu bane illa dai
ina so tazama ido na ko ince itace fitilar da zata haskaka min hanya wajen neman allura
cikin duhu.
alh Adnan ya dago da sauri ya dubi Abba yayinda ya caka masa mashin harara ya fada
cike da gadara yaro ban fahimceka ba?
Abba ya girgizakai yakara yin wani siririn murmushi yace ranka dade karkadamu nazo
neman alfarmane a wajen ku kanwarka kaltum ne tazo min da labarin ta baro matata a
sudan tana can tana bara shine nake so tamin kwatance ko ta taimakamin ta rakani inda
Madina take mu dauko ta don mu mun rasa inda take har mun zata ma ta mutu...
alh Adnan yakatseshi tunkafin yarufe bakinsa
cikin sakin fuska da dariya yake magana don ya fahinci abba ba zance yazo ba yace yi
shiru yaro na fahince kana so kace min kaima matarka tana cikin yan gudun hijira ko
ince masu tarar aradu da ka masu tafiya makka da kafa ko?
to sai dai mu musan abunyi domin kaltum bazata sake leka wa sudan ba da sunan
takawaba ba balle rakiya, kai da kasan wahalarda nasha kafin akawo min ita ai da
bazakace zaka nemi izinin rakiyarta ba, kaltum karatun jarabawane a gabanta banaso a
dinga maganar sudan da ita saboda ina ganin alamun damuwa a tattare da ita idan aka
ambaci sunan sudan don haka banaso ka sake sakata ma acikin maganan duk abunda
kakeso ko kake nema ka nemeni nayi maka alkawari zan taimaka maka iya taimako
saboda nasan yadda kake ji.
ba karamin tashin hankali bane ace an gano matarka ko yarka ko kanwarka awata kasa
tana bara ba, sai sunyi bara sannan suci abinci mace musamman budurwa ai bala'in yayi
bala i sai fatan Allah ya kiyaye gaba, yanzu dai ka rubuta numban wayata ka kirani gobe
da safe muyi magana daga abuja nake yanzu nagaji,
sai godiya abba yakeyi ba iyaka yayinda farin ciki ya mamaye zuciyanshi yaji tamkar
ance masa ga Madina nan adaki za a fito masa da ita, ya dauko waya alh Adnan yana
karanto
masa yana rubutawa ya fada cike da ladabi wani suna zan saka?
alh adnan yayi murmushi yace ka rubuta kaltum Adnan.
Abba ya maimaita sunan kaltum Adnan...
alh Adnan yace karka damu ka rubuta haka sai kafi ganewa,
ya juya ya bar Abba a tsaye cike da mamaki yayinda yabishi da kallo har saida ya shige
cikin gida zuciyarshi cike da tambayoyi shin wannan mutumin yaya yake da kaltum?
Gashi dai sunso suyi kama amma yace shi ba yayanta bane kuma baici ace babanta
bane don shekarunsa baici ace ya haifeta ba ita ba matar aure bace bare kuma ace
mijinta ne to ko kawunta ne ?
Amma da gatanta to meyasa suka bari ta tafi sudan ?
Gara ace Madina ace rashin gatane kodayake a labarin ta ta ambaci wata tsohuwace ta
tafi da ita ta ambaci wani masoyinta abar kaunanta mambela don haka wannan ba
mijinta bane koma dai wanene wannan yana sonta kuma yana kula da ita sosai tabbas
yana tattalinta..
tunanin da abban Madina yake yi kenan a zuciyar sa har ya iso gida bai iya barci ba daga
ya rufe ido sai yaga kamar Madina sai yayi sauri ya jawo hotonta yaga Madina ta lalace
ta susuce ta fita hayyacinta idan yayi kuka saiyayi adduar Allah ya bayyana masa ita
amma jikinsa yakanyi sanyi idan ya tuna Madina zata iya zuwa taci gaba da bujirewa
aurensa.
bayan gari ya waye Abba waya yasa agaba yana kirga awannin yana jiran goma na safe
yayi sannan yakira kaltum bayaso yadoka masa sanmako.
alokacinda agogon alh Adnan ya buga karfe goma da wayar Abba tare suka isa
kunnuwansa alokacin da yake tautaunawa da mai gadinsa malam sale a katafaren
falonsa ya dubi agogo ya juya ya dubi wayarsa baisan lambar ba dan haka bai damu da
sai ya amsa ba yaci gaba da bayanansa amma wayan bata daina ruri ba da zarar ta
gama saita kara daukar kururuwa dole tasa ya saka hannu ya amsa ko dai wanene
tabbas bakone don duk wanda yasanshi yasan dokarsa ba ayi masa waya kafin karfe 12
rana, alh Adnan ya amsa
sallamar mai yi masa waya sai ya kasa kunne yana sauraronsa Abba ya fara da gabatar
da kansa dakuma inda yake da alama har yanzu alh Adnan bai gane ko wanene ba daga
yanda yake amsa masa Abba ya fahimci haka don haka sai ya bashi labarin yadda suka
hadu jiya cewar mijin Madina da take sudan tareda kaltum sai yanxu ya fahimce shi don
haka sai ya saki ransa suka gaisa cike da faraa,
cikin fargaba Abba ya tambaye shi yace alh kace yau inkira zaka bani shawara ka
taimake ni alh in samo madina kamar yanda Allah Ya taimakeka ka tsinto kaltum.
alh Adnan yayi murmushi yace samari ka kwantar da hankalin ka zan taimakeka abu
daya ne nace bazan iya yi maka ba shine daka roki alfarmar kaltum ta raka ka sudan
wajen Madina, bazan barta ba saidai zan hadaka da wanda na sani acan su taimakeka.
Abba ya yi godiya sannan ya gyara zama yana sauraronsa yayinda farin ciki ya
lullubeshi...
malam saleh yakara tura hula keya yaci gaba da durgushewa yana sauraron abunda bai
taba sani ba arayuwarshi wato maganan kaltum da Madina, koda wasa kaltum bata taba
basu labarin rayuwarta a sudan ba saigashi alh Adnan ya sani harma suna tattauna da
wani akan haka.
alh Adnan yabawa Abba labarin yadda akayi aka kawo kaltum gida yayi masa alkawari
zai tuntube alh saadu yaji yan da za ayi ya nemo musu Madina a bur sudan ayi ciniki ya
fadi yanda za a biya shi, ya umurci Abba yakirashi da yamma don yaji yanda suka
tattauna.
Abba yayi farin ciki matuka yanata godiya har suka kashe wayan malam saleh ya jinjina
kai
yayi murmushi yace wata yar gudun hijira ce ake nema ?
Alh Adnan ya kyalkyale da dariya yace yar gudun hijira ne kawar kaltum,
malam saleh yayi dariya ya sake lankwashe kafa yace daddy amintar nan taka da kaltum
sai Allah kaga harta fada maka labarin kawarta a sudan mukuwa agida bata taba bada
labarin tasan wata asudan ba ko da wasa bata taba zancen sudan da wani acikin mu ba,
ka santa da miskilanci dakai kadai take hira shine kwanaki muke tattaunawa da sofi
muke cewa ga kaltum ta kusa gama sakandari a cikin watan nan zasu gama, samari har
sun fara biyota ranan ma saida na fita na fatattaki wasu a kofar gida bana so taci gaba
da karatu a gida gara tayi jami'a agidan mijinta idan mijin ya yarda, saboda dandazo
gidan nan zai zama dan ma bata kulasu shine mukayi shawara da zaiyu kuma idan
kanada ra'ayi da sai na damka maka kaltum duniya da lahira hankali na zaifi kwanciya
babu wanda zata aura yafi kulawa da ita fiye da kai duk da dai madam saliha ta kufula
yanzu in taji zatace cin amana ne amma ai bai haramta ba, Alh sunan mun haifi kaltum
ne kawai amma kai ka rainata da wahalhalunta dukka da taimakon Allah da taimakonka
ne kaltum ta zama mutum,
badan haka ba ai da tuni ko a kwabo ba wanda zai dauke ta, saboda a kauye ko a sudan
ta dauwama tana bara tunda bamuda kudin da zamu dauko ta, banida abunda zan iya
saka maka taimako da rufin asiri da kayi min nida zuriata aduniya bazai misaltu ba, don
haka na dauki yarinyan nan sukutum na baka nasan duk da haka ban biyaka ba kuma
har abada bazan iya biyanka ba, ranka ya dade a duba maganata sosai agani idan da
yuwuwar yin hakan ayi idan kuma nayi kuskure a cikin maganata na bata maka rai ayi
hakuri kasan zuciya da sake-sake ni da sofi ne muka shawarta haka.
alh Adnan dai yayi shiru kansa akasa baya murmushi haka bai bata fuska ba da alama
dai yana sauraro kuma yana nazari.
malam saleh ya mike cike da tsoro yace alh na barka lafiya zan koma bakin get naji
motsi,
alh Adnan ya bashi amsa da to madallah sai anjima,
daga dukkan alamu dukkansu biyun sun shiga halin tunani da sake-sake kala-kala acikin
yinin wannan rana, don tun wannan lokacin alh Adnan bai tashi daga kan kujera dayake
zaune ba har karfe daya da rabi na rana, motsin shigowar danladi direba ne dajin
muryan kaltum ita ta katse masa tunaninda ya dulmuya aciki,
kaltum ta gaishe da mahaifinta sai ta juya ta dubi motar alh Adnan ta tambaye shi Abba
daddy bai fita ba yana nan ?
Malam saleh ya amsa cike da farin ciki, yau bai fitoba yana falonsa ta juya da sauri ta
nufi falon alh Adnan fuskarta cike da faraa bakinta cike da magana da alama wani labari
ta kunso masa,
malam saleh yayi tsaye ya hada hannu yana mamaki mai hade da fargaba yana tsoron
kada maganar da yayi wa alh Adnan dazu ta bata masa rai ya juya musu baya, taimako
da fara ar da yake musu ya daina, kada kuma ya dauka turo kaltum sukayi da tsigar
yaudara..
ta shiga falo shiga falon.
yanzu kada fa ya dauka kwadayin dukiyar sa suke yi shine suka kakaba masa 'ya?
zuciya da sake sake haka ya dinga sakawo malam saleh wadannan tambayoyi InnaLillahi
wa inna i ailaihi raji'un kalmar da malam saleh ya fada kenan a bayyane yayinda ya dora
hannu aka ya shiga dakin gadi ya kasa zama sai leke-leke yake ta jikin labule yana so ya
gada wanne irin yanayi kaltum zata fito, da farin ciki koda bacin rai idan ya Koro ta, ya
shiga zargin kansa da kansa me yasa ma ya furta wannan kalmar?
gashi zai raba zumunci musamman idan
saliha taji.
kaltum ta isa cikin falon da sauri gami da rada sallama yayinda suka yi kayi ido hudu sai
kowannensu yayi murmushi ta karasa gabansa ta durgusa ta gaisheshi ya amsa cike da
fara a gami da mamaki hade da zumudin jin abunda zata fada,
ta bude jakarta ta zaro wata doguwar takarda ta mika masa ta ce daddy yau math
mukayi na fada maka daman nafi iya maths in shaa Allahu ''A'' zanci don na amsa dukka.
Yayi ajiyar zuciya ya lumshe ido gami da wani
laulausan murmushi ya amsa mata cikin tattausan murya, yayi kyau kaltum Allah Ya yi
miki jagora nikuma nayi miki alkawari idan kinci jarrabawar ki sosai zankaiki duk inda
kikeso kiyi karatu a fadin duniyar nan inhar kina so, zan saya miki duk abunda kikeso.
dadi ya lullube zuciyar kaltum ta rufe ido da tafukan hannayenta tayi godiya ta mike cike
da murna, zata tafi kamar daga sama taji ya kira sunanta ta dawo da sauri ta tsuguna a
gaban sa tana sauraron abunda zai fada,
ya dube ta yace kaltum wacece Madina?
waye kuma Abba?
saitaji kirjinta ya buga don fargaba sai hankalinta ya tashi, tayi sauri ta sunkuyar da
kanta kasa yayinda aka fara daukar dauki ba dadi tsakanin harshenta da labban bakinta,
magana daya sak ta kasa fitowa daga bakinta ya sake maimaita mata tambayarsa
haryanzu ba ta sauya zani ba, amsa ta gagara sai kame-kame takeyi.
ya tsuke fuska yayi magana cikin kakkausar murya Yace zauna kaltum ki nitsu ki
fahimce tambaya na kibani amsar gaskiya, inaso ki bani labarin, saboda in sani kafin
inshiga maganar, bansan kida karya ba ada ban san ki da munafunci ba bakya boye min
komai koda kin boyewa malam saleh da sofi, kada kiyimin karya don bana tare da mai
karya bana shiri da mutum mai kame-kame nafi shiri da mai gaskiya.
saita durgushe ta zauna a sanyaye yayinda idanuwanta suka cika taf da hawaye ta
tabbatar alh Adnan yaci karo da su Abba a jikin get, fargabarta kada ya zargi ko
saurayinta ne,
muryanta na kakkarwa ta bashi labarin Madina kakaf sannan ta gangaro ta fada masa
dalilin da yasa ta nemo Abba,
daga yadda ta fahimci alh Adnan ya tausayawa Madina kamar yadda ta san shi da
makurar jin tausayi, saita fara sakin jikinta tana koro bayanai, yayi shiru tsawon yan
mintina yana tunani,
yayi ajiyar zuciya ya dubi kaltum yace lallai Madina tanada mutunci kuma ta taimake ki
ya kamata itama ataimaketa yanzu idan taji Abba bai mutu ba ai zata yarda ta dawo ko?
ma'ana idan na aika alh sa'adu ya daukota.
.ADON DAWA 39
.
TRUE LIFE STORY
.
Kaltum Tace bazata yarda ta dawo ba har sai dai idan anje da Abba, idan ta ganshi kila
ta yarda ta dawo saboda zuciyar ta tariga ta daskare ta sawa ranta har abada tabar
kasar nan bazata dawo ba.
alh Adnan ya gyada kai yace gaskiyane ke kika santa kika san ra ayinta, da
shawarwarinki za'a yi ampani, jeki ngd za a dawo da madinarki,
tayi murmushin jin dadi tayi godiya ta mike cike da farin ciki zata fice harta kai bakin
kofa zata fita taji yakara kiran sunanta sai taji hankalinta ya tashi mamaki ya rufeta ta
dawo cikin sanyin jiki ta durgusa agabansa tana sauraron sa,
yayi murmushi yace kin bani labarin rayuwarki a bur sudan kakaf keda Madina da irin
taimakonda Madina tayi miki amma koda wasa baki ambaci mambela ba?
daga inda yake yana juyo ajiyar zuciyar da tayi, saitayi sauri ta sunkuyar da kanta kasa
tayi shiru,
yaci gaba da cewa ni tuntuni nake jira ki maimaitamin abunda kika fadamin a waya kin
samu miji dan ADON DAWA zaki bishi garinsu bur sudan, mutuminda ya taimakeki tun
zuwanki bur sudan ya biki har Khartoum yana shirin mayar dake bur sudan ya aureki ai
bai kamata ba har ki gama bada labari baki ambace shi ba,
Sai yaga tana kuka share-share da hawaye batada shirin magana don haka ya kyaleta ya
hakura dajin amsarta ya umurce ta data tashi ta tafi gida,
ta mike jiki a sanyaye ta fice, a bakin baranda ta tsuguna ta sharbi kukanta ta goge
hawaye sannan ta gangara ta shiga gidansu,
haryanzu mahaifinta yana labe a jikin labulen
dakinsa yana kallonta

Please Login or Register in order to submit comment