Reading adon dawa Chapter 8 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maye. Rigima
taki ci taki cinyewa, cikin dare dangin babana suka je suka kasha kanina xuka,
bayan kwana biyu aka tsinci gawar kanwata Enena a dawa suma dangin
mahaifiyata sun rama kenan. Aka tashi rigima kamar xa’ayi yaki a jinanasu,
tsakanin dangin wada da dangin xabiya daga karshe aka ce sai dai a raba auren
sannan a raba yaran wato ni da yayana kenan, mu masu lafiyar ana sanmu. Da
iyayena suka ji haka sai suka gaba xasu iya rabuwa da junansu ba saboda suna
mutuwar kaunar junansu, su suka san irin tsana da takaicin da suka sha a wajen
‘yan gari kowa yaki aurensu, saboda ita wadace shi kuma xabiya har saida Allah Ya
sa suka hada kansu suka xabi su rufawa juna asiri su xauna tare suka yi aurensu
babu mai yiwa kowa gori.
Cikin dare ya dauki ‘yar wadar matar sa, daman ya saba daukarta a kafadar sa duk
in da xasu je, ya shiga dawa suka gudu har yau ba’aji labarin suba. amma ana
kyautata xaton sun shiga wani kungurmin kauyukan arna sun tsafe su. Kinsan
kudu da arewa ba daya ba ne, yanxu a kudu sai kiga an kamo mutum an yi tsafi
dashi musamman aga irin wannan halittar ta wada da xabiya suna tafiya tare,
cewa xa su yi annoba ne ko su ce arxiki ne a kama su a yanka ko a binne su da rai.
Bawai na gaskata ba amma dodonsu y ace an kashe su a wani kauye don haka aka
yi bikin mutuwarsu aka raba gadon abunda suka bari, harda ‘ya’yan da suka bari a
rabon gadon wato ni da yayana. Shike nan gaba daya gidanmu ya waste daga ni
sai yayana muka rage, ba uwa, ba uba, babu kanne. Dangin uwata suka dauki
yayana, yayanta ya dauke ta ya dauke shi ya tafi dashi enugu garin da yake aiki,
dangin ubana suka dauke ni a nan cikin onisha nake. Kamar yadda kika sani da
xarar ance babu uwa, babu uba, a duniya to fa sai a hankali saboda gata yakare
sai wanda ya duba Allah xai dube ka.
A lokacin shekaruna takwas a duniya don haka na fara kiran kaina marainiya
domin na fara dandana maraici. Ba’a taba saka ni makarantaba sai talla da noma
koda yaushe, nice rainon ‘yayan ‘yan uwa, nice shara da wanke wanken a gidajen
‘yan uwa ba a gida daya ba. Baya ga duka, xagi da cin mutunci harda kala sata,
yau ace an ganni a gona na saci rogo gobe ace na balli ayaba a gonar wani ko
kuma ace na bude tukunya na saci naman miya. Kaltum ina bayan gari ina kuka ni
kadai gashi yayana innamani yayi min nisa baya onisha ya ci sa’a shi an saka shi a
makaranta. In takaice miki dai da wuya tayi wuya babu wanda bai san labarin
wahalar da nake sha ba a garin, ina tafe jama’a na nuna ni suna tausaya min.
kayan jikina a yayyage, tallar safe daban in koma in dauko abincin rana, idan na
sayar na koma na daukko na dare.
A kasuwa nake sayar da abinci anan ne na hadu da hausawa masu sayar da gyada,
man kulikuli, ridi, barkono da dai sauransu. Ta in da jini na ya fara haduwa da
hausawa shine suna da tausayi, suna da kirki, suna da kyauta, ga yawan fara’a.
muna xama tare muna sabawa sai na fara fahimtar ashe wadannan wadannan
mutane wato hausawa suna da wani addini da ake kira musulunci, suna bautawa
Ubangijinsu shine Allah madaukakin Sarki. Hakika idan musulmi y ace Allah xan yi
abu kaxa, tabbas suna tsoron Allah xa su yi din. Wannan al’amarin nasu yana
burge ni kuma yana matukar ba ni sha’awa, na ji ina son in yi huddar cinikayya
dasu. suna siyan kayana su bani kudina basa hanawa sabanin inyamurai ‘yan
uwana saisu cinye abincina su hana ni kudin, su ce in je in yi abunda xanyi, basa
tsoron Allah. A wanan dalilin ne yasa na fi so in sayarwa da hausawa abincina.
A haka muka saba da wani yaro saurayin mai suna Tasi’u, dan asalin wani kauye
ne da ake kira gurjiya, a hanyar wudil akwai wani kauye da ake kira kanyar babba,
daga nan ake daukar hanya sai ayi ta shiga kusurwa-kusurwa babu kwalta, sai
rigagen Fulani da kauyukan hausawa iri iri har a isa garin gurjiya.”
Kaltum t ace “yanxu daga surkukin kauyen na su tasi’u suke fitowa su tafi har
onisha neman kudi? ”
madina t ace “dabi’ar ‘yan garin ne duka shekara bayan amfanin gona yayi, anyi
roron gyada da wake saisu hada buhuhunan amfanin gonarsu maxansu da
matansu su hau mota su je garinmu onisha. Matan suna gida suna gyara gyada
suna yin man kuli da karago ko soyayyar gayada, maxan suna sayarwa a kasuwa.”
Kaltum t ace “har gidaje gare su a garinku kenan? ”
madina ta e “ba wasu gidajen kirki ba ne, tamfol ne suke bugawa a bayan gari, ko
suyi gidajen katako ko kuma su sami dakuna na kasa su kama haya. Suna xama
kamar watanni hudu ko uku sannan su hada kudinsu su sari manja, kwakwa, garin
kwaki, su juya garin su sai wata shekarar sannan su dawo.
Kaltum ta gyada kai tace “Allah mai hada mutum da mutum, idan ba ikon Allah ba
ta ina, ta yaya mutumin da yake hanyar wudil ya hadu da wacce take onisha. Yaya
kuka kare da mutumin da kika ce sunansa tasi’u dan garin gurjiya? ”
Madina tayi murmushi t ace “duk shekara muke haduwa da tasi’u, da yake bashi
da mata a wajena yake siyan abincin safe, rana da na dare ya siya ya bani kudina
cas har ma ya kara min, y ace na rike canjin komai yawan sa.
.
ADON DAWA 11
.
TRUE LIFE STORY
.
Don haka da xarar naga baki ‘yan garinsu sun fara xuwa sai nayi ta tambayarsu “ina
tasi’u?
ba xai xo ba ne?
yau she xe xo?
Me yasa bai xo bad a wuri? ”
haka kullum nake tambayar abokansa har sai ya xo hankalina yake kwantawa. Duk da
baya jin turanci sosai, amma duk da haka yafi sauran kokarin harhadawa in fahimce shi
ya fahimce ni don nima babu hausa a lokacin.
A lokacin da muka tabbatar wannan shakuwar tamu soyayya ce, sai a sannan na cika
shekara goma sha hudu. Na ji ina sonsa saboda yana tausayina ya fahimci ina shan
wahala a gidanmu, yana lallashina idan ina kuka haka yake cika min kudi idan cinikina
bai cika ba ina tsoro xa’a dake ni a gida. Haka yake kawo min atamfofi da soyayyiyar aya
da gyada duk sanda xai xo daga garinsu. Nima idan xai tafi sai in je gona in tsunko masa
kwakwa, abarba, ayaba da gwanda. Da kuka muke rabuwa duk sanda xai koma garinsu
sai inji duk bana jin dadin kasuwar idan baya nan.
Bana sha’awar samarin garinmu saboda ba abunda suka sani sai yiwa budurwa ciki, idan
taki amincewa sai suyi mata fyade (wa iyyaxu billa Allah Ya tsare mu da xuri’armu baki
daya.) da karfin tsiya ba’a kuma daukar matakin kirki idan haka ta faru dan haka nayi ta
taka tsan-tsan da duk namijin da yake kusanta ta. Da yawa samarin garinmu sun sha
kawo min hari, Allah Yak e kiyaye ni.
Wata rana na je na iske tasi’u a dakinsa bashi da lafiya yana cikin bargo yana
makyarkyata saboda tsananin xaxxabi mai xafi. Na xuba masa abinci nace ya tashi yaci,
yace ba xai ci ba idan yaci xai yi amai. Na kasa tafiya talla in bar shi cikin wannan hali
sai na xauna a gefen katifarsa ina shafa kafarsa. Sai naga ya xabura ya janye kafarsa. Ya
ce da ni baya so ina taba shi saboda haramun ne mace ta taba namiji idan ba mijin taba
ne, haka bai ma kamata in shigo dakinsa ba in xauna saboda gudun shaidan xai iya
shiga tsakaninmu, a takaice dai yana nufin in tashi in fita.
(ALLAH SARKI, JAMA’A SE A KIYAYE DOMIN KUWA WANNAN ITACE ADDININ MU KUMA
AL’ADARMU, DA YAWA MUTANE YANXU SUN XAMA DA SHI GANIN DAMA, DOMIN GUJEWA
SHARRIN SHAIDAN, JAMA’A SE A KIYAYE, A DAU DARASI, ALLAH YA SA MU DACE, KUMA
MU PI KARPIN XUCIYOYIN MU.
Aamiin )
Raina yabaci na dauki kayan talla na fice a tunanina yayi min wulakanci baya sona. Ina
shiga wani gida talla sai mutumin gidan ya rufe kofa da ni yana neman yi min fyade, da
kyar na kwaci kai na bayan da muka yiwa juna jini da majina. Ya fasfaska min mari, ni
kuma na rurrusa masa daron abincin tallar, na juye masa abincin aka duk abincin ya
xuxxube, da kyar na kwaci kaina na fito yaro-yaro kayana a yayyage. Sai a lokacin na
sake tabbatarwa da lallai tasi’u mai so na ne kuma baya niyyar cutar da ni, kuma
al’adarsu da addininsu yana da kyau yafi namu.
Kai tsaye dakin tasi’u na nufa ina rusa kuka, wannan karon sai na ki shiga cikin dakin sai
dai na kwankwasa masa kofa, ya fito da kyar yayin da hankalinsa ya tashi daya ganni a
cikin wannan halin. Yana tambayata cikin gigita dakyar na lafa da kukan na fada masa
abunda ya faru, na shaida masa cewar kwanukan abincin yana can a gidan mutumin
kuma abincina ya xube dukka ko cinikin sisi ban yi ba ina tsoran in je gida dan xa’a
kashe ni idan ban kai kudi ba. Haka tasi’u ya harhada duk ‘yan kudaden sa ya bani ya
saka ni a gaba na nuna masa gidan, muka iske gidan a rufe amma an watso min
kwanukan waje. Tasi’u ya harhada ya bani na tafi gida, duk da haka saida na ci duka
akan kayana da aka gani a yayyage.
Tun daga wannan lokacin na ji na kara son tasi’u kuma shi ya dace da rayuwata. Na
shiga tunanin ta yadda xamu fara domin na san ko a mafarki a gidanmu da wajen
bautarmu ba xa su bari na auri tasi’u ba ko xan mutu. Shima ya nuna min yana sona
amma fa ko xan mutu ba xa’a bar shi a gidansu ya su ya aure niba, a lokacin ma ya fada
min cewar har an bashi wacce xai aura shi ne baya so yake jan abun da tuni ma anyi
bikin.
Tasi’u ne ya koya min saka suturar da xata rufe min ilahirin jikina, na daina yawo da
shimi dadan siket iya gwiwa, shi ya nuna min kamun kai da kintsa jiki idan ina gaban
maxa saboda gudun sha’awa, muna son juna sosai har takai ta kawo sanda ya xo xai tafi
garinsu na rike shi ina ihu nace sai dai mu tafi tare ba xai tafi ya barni ba, dole ya fasa
tafiyarsa a ranar abokan tafiyar sa suka tafi suka barshi ya xauna yayi ta lallashi na
dakyar na yarda na koma gidanmu a bisa sharadin gobe xai jira ni mu tafi tare.
Cikin dare na sulalo na fito daure da kayana a dan buhu na xo na buga masa kofar
dakinsa nace ya fito mu gudu saboda gobe da safe xa’a a tashi a fadawa ‘yan uwana su
xo su kama ni. Da farko ya nuna ba xai tafi da niba, kukana da kalaman da nake fada
masa cewar ina so in musulunta in xauna da musulmai In baxe aure niba na yarda, na
shaida masa na gaji da wahalar aiki, talla, da duka kullum, in har ba xai tafi da niba to ya
sani kafin ya dawo wata shekara xan kashe kaina. Dole ya ji babu yadda xai yi sai ya tafi
da ni din. A daren muka shiga tasha muka kwana, da asuba muka shiga doguwar mota
xuwa kano. Babu wanda ya ganni har muka bar garinmu, daga kano muka hau motar
wudil kafin a isa wudil muka sauka kanya babba muka hau Babura suka shiga damu
garin gurjiya, garinsu kenan. Bamu isa gurjiya ba sai kimanin karfe goma sha daya na
dare a lokacin kowa yayi barci, sai ya kaini gidan wani abokinsa mai suna Dauda da
matarsa ramma itama mun saba da ita a garinmu, suma basu dade da dawowa ba daga
onisha. A nan na kwana shi kuma ya tafi gidansu har gari yawaye”
Kaltum ta yi ajiyar xuciya ta gyara xama t ace “yaki na gaba ahse, yaya kika kasance a
garin gurjiya da dangin tasi’u musamman ga wacce aka bashi ya aura ya bujire ya kawo
ki, ke ba bahaushiya ba, ba muslma ba?
Kuma can gidanku yaya xasu ji idan suka ji an ce kin gudu? ”
Madina ta digo da kwallar data cika mata ido ta yi murmushin karfin hali tace, “idan ki ka
ce yaki daya kenan. Yake-yake xa kice. An tafka yaki badan kadan ba tsakanin tasi’u da
‘yan uwansa harta kai ta kawo dole ya dauke ni muka gudu kano saboda sun ki su tsaya
su fahimce shi. Ba su ma saurari abunda yake fada musu ba, yana kokarin shaida musu
ba aurena xai yi ba. Ya kawo ni ne dan a musuluntar da ni in xauna a cikin musulmai dan
ni yanxu kafura ce. Sai gudu da tsallake Katanga ake yi a garin duk gidan daya shiga da
ni wai ga arniya, ko giftawa nayi ta gefen randa sai an fasa randar ko an kwalfe ruwan an
xubar. Kiyayya iri-iri har naji jikina yayi sanyi, dan ban dauka haka wasu musulmai suke
ba. A tunanina duk musulmai masu kirki ne da son jama’a, sai naga suna kora ta suna
guduna har nace masa ya mayar da ni garinmua na fasa xama da musulmai. Tasi’u yaki
yace in dauko kayana mu gudu cikin garin kano, haka kuwa aka yi ya kawo ni kano
unguwar yan kaba wajen limamin unguwar. A nan aka musuluntar da ni kuma a lokacin
tasi’u ya biya kudin sadakina aka daura mana aure a take
A lokacin ‘yan uwa musulmai suka dinga tallafa mana, masu bamu sababbin suture kala-
kala. Aka bamu kudi masu yawa sannan wani attajiri a unguwar mai suna general tukur
ya bamu aron wani dan karamin gida a jikin gidansa, gidan mai kyau kuwa daki biyu, sai
kicin da bandaki ga tsakar gida a sumulce da sumunti. Matan unguwar suka hada kudi
suka dinka min hijabai aka ce in dinga xuwa makarantar islamiyya a unguwar. Ni da
mijina muka sayi katifa, labulaye da kayan kicin muka xauna, xaman aure cikin farin ciki.
Turanci ya fara ratsa bakin tasi’u yayin da ni kuma hausa ta fara kama bakina don haka
muka dinga fahimtar juna.
Tasi’u yana jin dadin xama da ni saboda duk sanda matar bahaushe ta hadu da matar
kabila tabbas kabilar nan xata kwacewa matar bahaushe miji badan komai ba saidan mu
mun saba da aikin karfi ba aikin gida ba ma kawai. Kinga daga inda aka kira sallar asuba
nagama barci sai wani daren kuma. Ni ce shara, wanke-wanke, wankin bandaki, wankin
kayana, wankin kayansa, gugar kayansa dama sauransu. Ladabi da biyayya kuwa ba
iyaka domin ba ma mikawa miji abu a tsaye sai mun durkusa, idan ya ajiye min tsinke
yace, kar in tsallake bana tsallakawa, ban taba yi masa musu ba balle mu yi fada duk
abunda yace min ko bana so haka xan yi. Ina jin dadin xamana da tasi’u saboda bana
aikin wahala irin na da wanda nake yi a garinmu. Tsakanina da makwabtana sai gaisuwa
da hirar mutumci, haka na yi kawaye da dama a makarantar islamiyya. Kwakwalwata
kuwa tar ta bude duk wani karatu da xa’a koyamin sai ya shige, gani da nacin koyo.
Tasi’u ma bashi da ilimin addini sosai shima makarantar maxa ya shiga da daddare suke
yi a masallaci. A kasuwar bakin asibitin murtala tasi’u yake kasuwancinsa yana sayar da
danyen abinci kamar shinkafa, masara, gero, citta da ma sauransu. Sai a lokacin damina
yake xuwa garinsu ya noma gonar gadonsa domin babansa ya dade da rasuwa
mahaifiyarsa ce kawai sai ‘yan uwa jibgi guda mata da maxa. Tun mahaifiyarsa na kin
amsa gaisuwarsa har dai ta huce ta fara amsawa, ta huce amma koda wasa baya
marmarin kai ni garin, nima bana marmarin xuwa garinmu. Shima tasi’u bai sake
waiwayar onisha ba sai dai labari ya kai kunnen ‘yan uwana cewar ina tare da tasi’u a
kano. Da sun yi shawarar su xo su tafi da ni, sai bokansu yace a kyale ni xan dawo da
kaina, akwai tsibbun da xai yi xan dawo da kaina. Amma fa karya yake domin addu’ata
tafi tasu karfi.
Na dade ban samu haihuwa ba don haka na dinga kokarin neman ilimi ta dukka
bangarorin biyu Qur’ani da boko.”
Kaltum ta tambaya cike da mamaki tace “ta yaya kika shiga makarantar boko alhali kina
matar aure kuma ko primary baki yi ba?
To, mu hadu a #LITTAFI kashi na biyu,
ADON DAWA LITTAFI NA 2 (P 12)
.
TRUE LIFE STORY
.
Madina t ace “da kyau, na ji dadin tambayarki, wannan yana nuna min kina fahimtar
labarin da nake fada miki. Da farko dai ban taba xuwa makaranta ba kamr yadda na fada
a baya amma duk yaran gidanmu ‘yan boko ne don haka tun ina karama na koyi A B C D
har xuwa xed sannan na iya 123 har xuwa dubunnai, xan iya kirgawa kuma na iya
rubutawa. Sannan nasan yadda ake rubuta sunan abubuwa da yawa kamar su hen, cup,
ball da dai sauransu. Dalilin da yasa ba xan wahala a boko ba saboda na iya turanci duk
da turancin ba turanci ba ne sak (broken English) ne amma muna jin mai kyan din, duk
abun da ka fada min da turanci xan ji kuma xan mayar. Don haka satifiket din primary na
je aka yi min a dakata special primary school.
A makwabtan mu wato gidan attajirin nan daya bamu aron gida wato general tukur .
akwai wata budurwa ‘yarsa mai suna sumayya tukur. Sumayya sa’ata ce shekarunmu
goma sha takwas har ta gama secondary, ajinmu daya a islamiyya. General tukur
mahaifin sumayya babban soja ne, mai arxiki ne, gawurtaccen dan boko ne, gidansa
rayuwar turai ake yi tsantsa. Yana da ilimi matarsa hajiya hafsa cikakkiyar lauya ce har
ma tana koyarwa a jami’ar bayero ta kano, don haka su sumayya da kannenta ‘yan gata
ne basu san talauci ba balle wahalar rayuwa.
Sumayya tukur itace babba a gidan kuma itace kadai mace, duk kannenta maxa ne har
guda hudu. Mai bin ta sunansa tukur tukur ana kiransa da abba shekarunsa goma sha
uku a lokacin, kinga kenan sumayya ta girme masa da shekarunsa goma sha daya, sai
Hassan da hussain ‘yan auta shekarunsu bakwai bakwai. Tabbas mun shaku da ‘yan
gidan duk unguwar ana mamakin ni da mijina kadai muke wadaka a gidan, mu shiga
gidan mu fita a duk lokacin da muke so, haka suma yaran suke safa da marwa a gidana
koda yaushe. Duk da sojojin da suke gadinsu suna hana kowa shiga gidan amma ni basa
hana ni saboda hajiya hafsa tukur ta ce kada su hana ni shiga komai dare. Maigidana ma
duk sanda ya bukaci ganin general tukur kai tsaye yake shiga ayi masa iso, ya shiga ya
gan shi ya taimaka masa da duk abunda yake nema.
Allah ne gatanmu, general tukur da iyalansa sune gatanmu. Barrister hafsa itace uwar
dakina itace tamkar uwata a kano tunda bani da kowa a kano. Ita take ba ni shawara, ita
take fada min gaskiya idan na kuskure. Abubuwa da yawa idan ta sayawa ‘yarta
sumayya nima sai ta saya da ni musamman dinkunan sutura ko bata yi mana iri daya ba
tana kwatantawa nima tayi min. yawanci duk abunda suka dafa xata sa masu aikinta su
xuba su kawo min. nima kuma ina iya kokarina wajen xage karfina in tsaftace mata gida
ko tana nan ko bata nan xan hau sama bangarenta ko bangaren mijinta in tsaftace shi
tsaf,
(TAB!!! NI SADIN MAA ME TYPING NA CE “SAM, BANNA YARDA WATA TA GYARA MIN
DAKIN MIJI EHE. DAN ANTY ME POSTING, KO KUWA DA KA YARDA WATA TA GYARA DAKIN
KA BAYAN MATAR KA? )
( tab , ai ni Sadin Maa ko er aikin ma baxan yarda da ita ba, idan kawai naga aikin xai yi
wa mata ta yawa sai na karo wata ta biyu ta xo a taimaki juna )
Har bata so masu aikinta suyi mata gayarn daki idan ba niba, bata ganin dai-dai saboda
na fi su iyawa. Haka take aikawa in xo in yi mata wankin bandaki ko goge gogen kura, ko
dahuwar abinci kala-kala irin na garinmu musamman dakan sakwara.
Daga in da na fara sha’awar boko sai yadda naga ana rugurguxa turanci, ana
xaxxankada rubutu a gidan ni ban iya ba sosai. Kullum mummy hafsa t ace min “madina
dama ace kin yi boko da kyawunki ya kara futowa, haka da kin fi xama ‘yar gayu da
gogewa.” Sai na ji na fara tunanin ta ina xan fara karatun boko dan haka na sauke
girman kai na xauna xaman dirshen da biro da littafina, kawata sumayya take koya min
idan bata nan kaninta tukur (abba) yake koya min idan na iske mummy hafsa a gida
bata je aiki ba itama sai ta koya min, kan ka ce kwabo na fara gane me nene boko, ko
ina gida na abba yana shigowa ya koya min ni kuma ina nacewa ina tilawa har cikin
dare. Tasi’u mijina baya hana ni duk abunda nake so shima dai bai yi boko ba amma
bashi da niyyar koya kuma bai hana ni inje in koya ba. To kin ji yadda na koyi boko daga
wajen makwabtana don karfin hali ma harda biology da chemistry sumayya take koya
min da yake science tayi.
Ina da shekaru goma sha tara a duniya na haifi dana na fari, aka saka masa suna Abdul
malik, na yaye shi kenan na haifi kaninsa Abdul hakim. ‘ya’yana biyu kenan tamkar ‘yan
tagwaye kamarsu daya sak. Farare sol da ni suka yi kama basu dauko kamannin
mahaifinsu ba. Sumayya kuwa karatun likita take yi a B U K yayin da kaninta abba ya
kusa kammala secondary, shima dai ya dage yaketa koya min karatu, ni dole sai na koyi
boko nima. Yana matukar burge su, su duka har daddy su ya fada ya sake maimatawa
cewa shi kuwa in har xan dage in koyi karatu in nemo makaranta duk tsadar ta xai biya
min. sumayya da abba kaninta suka shiga tunanin ta in da xan fara karatu a makaranta.”
Da muka nemi shawarar mummy hafsa wacce makaranta ya kamata in shiga , gani
harda ‘ya’ya, sai t ace tunda ina da kokari har ma na fi wata wacce ta gama secondary
sanin karatu, to inje in yi register a wata private school wacce ake yin lesson a duk
lokacin da jarabawar WAEC ta karato wacce ake koyar da darussan da akayi a SS3, ana
amsa past question papers na WAEC.daddy ya biya min nayi register WAEC sannan nake
ta xuwa daukar darasi har na tsawon watanni uku kafin ranar jarabawar.
Na xana jarabawar WAEC na sami credit shida aka bani certificate da testimonial, kamar
yadda na fada miki daman na sami certificate da testimonial na primary school tutuni.
Kaltum tayi dariya t ace “’rabo ne wannan, ba kiyi boko ba amma kin xama ‘yar boko
dole.”
Madina t ace “sa kai ance ya fi bauta ciwo in ji masu iya Magana. Naci ne da son karatun
na saka a xuciyata sai kuma kwarin gwiwa da na samu daga masu koya min, musamman
abba yana mutukar karfafa min gwiwa.
Haka xa kiji yana cewa sister madina xa ki iya karatu ki dage.
To ko jikina yayi sanyi na daina koyo sai yasa in dauko littafi in ci gaba. Da yake abba
yana matukar jin turanci ya taimaka min wajen gane abunda yake koya min, haka irin
tsadaddiyar makarantar da suke yi mai kayu ita ta kara musu sanin abubuwa da yawa
suma suka koya min, ga lesson teachers dinsu ko wane subject suna da malaminsa.
A bamgaren addini kuwa idan ban koya musu ba, su ba xasu koya min ba, islamiyyarmu
daya dasu haka malamin da yake koya musu a gida nima ina shiga ya koya min , bikin
saukar mu tare aka yi mana da muka sauke Qur’ani mu uku, ni sumayya da abba babu
abunda suka bambata ni.
Abu kamar wasa sakamakon jarabawar WAEC dina ta fito, ina da credit shida da pass
uku haka ya taimaka min na shiga school of hygine inda na karanci aikin jinya. To kinji
yadda na xama ma’aikaciyar asitbiti kenan shi yasa na iya dinke miki ciwo, na iya allura
da bada magunguna.
Kaltum tace “na ji duk wannan sai dai na damu in ji dalilin da yasa ki ka rabu da mijinki
da ‘ya’yanki ki ka taho nan alhalin kina cikin rayuwar jin dadi da kwanciyar hankali.
Mijinki mai sonki, ‘ya’yanki a

Please Login or Register in order to submit comment