Reading adon dawa Chapter 27 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko ina tsaf-tsaf
kamar an tande da harshe, babu kura ko datti ko da yake ba abun mamaki bane
kasancewar hadiman gidan suna da yawa mata da maza kowa da bangarenda yake
kulawa dashi.
a babban falo kaltum ta zauna yayinda shahida ta kutsa kai can ciki tana rada sallama
domin basu sami kowa a falonba kalle-kalle kawai kaltum keyi yayinda idanuwanta suka
dira wani rusheshen hoto enlargement amanne a jikin bango da alama dai hoton yan
gidan ne kakaf uwa da uba da ya yansu,
nan da nan kwakwalwarta ta fara tuno mata lbr da madina ta bata don bata manta da
sunayensu ba tace aranta ga general tukur da mummy hafsat ga babbar yarsu Surayya
ga yan autansu tagwaye hassan da hussaini daga nan kuma takasa tantance Abba da
mabiyinsa Anas saboda girmansu daya kamarsu daya kayan jikin su ma iri daya a hoton,
kuma irin wannan fuskar ta wuce a kofar gida don haka ba tantama kanin Abba ne, taci
gaba da jimamin mutuwar Abba a ranta yayinda hawaye ya cika mata ido a yayinda ta
ayyanowa Abba da Madina rayuwar aure domin sundace da juna kowannensu
kyakkyawane, Abba Allah Ya jikanka ka yafewa Madina itama bata kinka,
kaltum ta fada azuciyarta yayinda taci gaba da duban fuskar Abba da kaninsa
kasancewar ta rasa waye Abba a cikin su, shahida ne ta katse mata tunanin da ta keyi
tace wai ki shigo inji mummy hafsat tana falonta, kaltum taji zuciyarta ta harba sai yanzu
tafara fargaba, ta fara tunanin abunda zai je ya zo, kada fa haryanzu suna kufule da
Madina kuma ace suna nemanta su kama ta fushin da sukeyi da Madina ya shafeta gashi
ta shigo lungu ko duka ne kafin ta samu ta fito angama dirkarta, ga uwa uba sojoji masu
jajayen ido a bakin get sai yanda Allah Ya yi da ita yau kenan, ta fara jero salati a
zuciyarta na neman agaji daga rabbis samawati Ya taimaketa ta isar da sakon da ta
kudira a ranta ba don ta sami wani abu ba kuma badon ta burge kowa ba sai don ta
taimaki Madina ta wanketa daga zarginda akemata domin tunda ta dawo ta kasa samun
sukuni da kwanciyar hankali har saita fitar da abunnan aranta zata huta koda fadarshi
shine hanyar ajalinta,
shahida na gaba kaltum na biye da ita a baya har suka isa katafaren falo na alfarma a
inda idanuwanta ya hasko mata wata lafiyayyiyar mata mai kamala, yanda mummy
hafsat ke duban kaltum haka itama kaltum ke dubanta, dukansu mamaki ne fal a
idanuwan su,
kaltum bata zauna a kujerunda suke farko-farko ba har saida ta karasa gaban mummy
hafsat ta zube kasa ta kwashi gaisuwa cikin fara'a ta amsa tayi mata izinin ta tashi daga
kasa ta hau kan kujera saboda sanyin tiles,
kultum ta gyara zama ta girgiza kai tace nan ma ya isa mummy hafsat,
kiran sunan ta datayi shine ya kara mata mamaki kasancewar ko amafarki bata taba
ganin mai kama da kaltum ba balle tace yar gidan wane ne ba, ta gyara zama ta dubi
kaltum tayi murmushi cike da zumudi ta tambayeta yar makaranta yaya sunanki ?
Daga ina ?
Kaltum tayi murmushi ta amsa sunana kaltum daga nassarawa G R A nake ina
makaranta a crensent collage ajina shida, haryanzu dai bata amsa mata tambayanta ba
saima hargitsa mata tunani datayi mummy hafsat ta yatsuna fuska kadan tayi shiru can
tace ke yar gidan waye kenan?
kaltum tace yar gidan malam sale a gidan alh Adnan muke....
a fusace kyakkyawan saurayin nan ya turo kofa ya shigo damin dama labe yake ajikin
kofa yanaso yaji abunda kaltum ke tafe dashi sai yaji ta shiga shirme kuma daman bai
yarda da ita ba, ya daka mata tsawa mai firgitarwa har saida kaltum ta zabura ta dafe
kirji,
yace mummy kirabu da yarinyannan bata da gaskiya tunba yau ba take zuwa gidan nan
tana leke-leke ba, munafuka ce, ki barni da ita kawai in sa su Ashiru masu gadi suyita
gana mata azaba harsai ta fadi wanda ya turo ta a mota da take zuwa wani direba yake
kawota shine take amfani da shahida tana tambayanta sirrin gidan nan, yau kuma ta
shigo da kanta gashi nan tana kame-kame yau sai kin gwammace baki shigo gidan nan
ba.
yayinda yake kwanto belt din jikinsa mummy hafsat ta jawo kaltum jikinta ta daga hannu
wa dan nata ta dakatar dashi gami dayi masa gargadi kada ya sake yakaraso gabanta
balle yataba yarinyan nan da sunan duka, a tsaye yake rike da belt din sai tsuma yakeyi
don bacin rai yayinda kaltum ta rushe da kuka hakama shahida kukan takeyi sai
kakkarwa jikinsu yakeyi mummy hafsat tana rike da hannun kaltum tana durkushe
agabanta, tasa hannu ta share mata hawaye tace daina kuka fadamin meke tafe dake?
waye ya aikoki?
me kike nema?
kaltum ta share hawaye tace babu wanda ya turoni nina nemo gidan dakaina nazo..
ya sake kufula ya cije lebe yaji tamkar ya damko wuyan ta ya shake, mummy hafsat
harararsa takeyi alamar karya kariso, ta dago da kan kaltum sama tace yarinya kimin
bayani yanda zan fahimceki ban san ki ba amma kekin sanni har kina kiran sunana dasai
agida ake fada min balle ince a wajen aikina kika sanni ke yar sakandarine ko jami'a
bakije ba balle ince ke dalibatace, meke faruwa ne kaltum ?
Kaltum tayi ajiyar zuciya ta matse hawaye game da gyara zama ta sunkuyar dakanta
kasa ta fada cike da fargaba mai yawa don bata san abunda furucinnan nata zai
haifarba, farin ciki ko bakin ciki,
awajen Madina naji sunanki ita tabani lbrinki da kwatancen gidanki.
su dukka ukun suka maimaita a lokaci guda MADINA!!!
Zuciyoyinsu cike da mamaki shahida ta mike zunbur ta dafe kirji a inda aka hau kallon
kallon a tsakaninsu su hudun ba tare da wani ya kara iya cewa komai ba,
kaltum ta dubi kowannensu daya baya daya ta ce eh Madina mamar Abdul Malik Abdul
hakim da shahida tsohuwar matar Tasi'u itace ta bani labarin rayuwarta kakaf harma ta
sako zancen nan gidan general tukur da mummy hafsat tayimin dalla-dalla akan rasuwar
Abba, Madina ba itace silar hatsarin Abba ba, ba mayya bace bata taba sanin yadda ake
maita ba, Madina musulma ce mumina mai rikon addini wacce bata dauki rayuwar
duniya da zafi ba, ta fada ta maimaita irin tsananin son da takeyiwa Abba musamman
bayan ya mutu hawayenda,
kaltum ke fitarwa saida na mummy hafsat ya linka nata yayinda na shahida ya linka
nasu dukka, saurayin ya jefar da belt kasa ya dafe kai yayi wuf ya fice itama shahida sai
ta zankada da gudu waje akabar kaltum da mummy hafsat sunata kallon kallo,
zuciyar kaltum ta cika da fargaba kasancewar bata fuskanci matsayin labarinta a
wajensu ba, bata san matakinda zasu dauka ba ita dai daman ta kudiri niyyar saita isar
da sakon nan dayan biyu ko ta mutu kotayi rai, Shahida ce ta shigo tare da samari guda
2 ko ba a fada ba yayun tane fuskarsu iri daya su dukka sak Madina da alama daya daga
barci aka tasoshi daya kuwa shirin filin ball yayi zaije kwallo hankalinsu a tashe tun kafin
su shigo cikin falon idanuwansu sun leko suna ta kokarin hasko kaltum zasuyi magana
mummy hafsat ta dakatar dasu ta nuna musu alamar suyi shiru sannan ta yi musu nuni
da kujeru alamar su zauna, haka kuwa akayi kowa ya zauna yayi carko-carko ga tagumi
iri-iri yayinda zuciyoyi suka hau bubbuge-bubbuge wajen tsaro labari daban-daban,
sautin ajiyar zuciyarsu ne kadai yake tashi a falon hakika sun kagu a fara bayani, wayar
mummy hafsat ne ta dau ruri yayinda ta mika hannu kan teburin dake gefenta ta dauka
ta duba sai ta ambaci kalmar AlhamduLillahi sannan ta danna, Sumayyah tukur ce ta
fada cikin farin ciki da tsantsar Kauna,
mummy kina gida?
Gani nafito zanzo na ganki tunjiya nake missing dinki har mafarkinki nayi nace meyayi
zafi in hakura da aikin mana yau nazo na yini guda naga uwa ta?
tayi murmushi ta lumshe ido donjin dadin kalaman yar tace kizo ina gida babyna ki
karaso da sauri kiga ikon Allah, da baki neme niba daman yanzu zan nemoki,
sumayyah tayi daria tace Allah mummy. Allah Ya sa alkhairi ne,
mummy hafsat tace alkhairi ne ma saikin karaso dai kiyi tuki a hankali ba gaggawa bane,
wata muryace tayi sallama sai dukkansu suka daga kai suna kallon mai shigowan sai ga
wani saurayi sanye da bakar riga da wando suit farar riga ce aciki wuyan sa daure neck
tied, kafarsa ba takalmi sai dai akwai bakar safa da alama daga bakin kofa ya cire
takalmin sai dai yana dan dingisawa da alamar bacin rai a fuskarsa domin dakyar yake
magana, abun mamaki sai sukayi kama sak da saurayin da ya fice yafice inji kaltum
tafada aranta ko shine yaje ya canzo kaya?
amma kamar wancan ya dan fi wannan kiba kuma wannan yafi wancan tsayi yama fishi
kyau sbd yafi wancan dogon hanci da haske, kuma fuskarsa a zagaye da kasumba, yazo
ya durgusa ya gaishe da mahaifiyarsa yace Anas yace inzo kina kirana?
ta gyada kai tace eh sami kujera kazauna yamike tsaye yana muzurai da alama bayason
zaman nan yayinda ya fara duban al'ummar da ke zaune a falon daya bayan daya sai
yanzu ya lura da wanda ke zazzaune,
matukar mamaki bayananne a fuskarsa duba yake musu na kurilla sai su dukka suka
zamo daga kan kujera suka gaisheshi ya amsa da kyar kasancewar harshensa ya masa
nauyi ya dubi kaltum ya sake dubanta sai ta sunkuyar da kanta kasa ya juya ya dubi
mahaifiyarsa ya fada cike da gargadar murya mummy lfy?
ta kawar dakai gefe tace lafiya ka nema waje ka zauna kawai.
yace fadamin abunda ke faruwa nabar mutane a mota?
wannan karon tsawa ta daka masa tace ka nemi waje ka zauna nace ko?
Ko sekon bai kara ba ya zauna....
.
To yau an samu post biyu, ya kamata kuma a samu kwana biyu kapin a yi, saboda na
san kowa ya sha karatu ya gaji, idan aka huta sai aci gaba,
Lol.

ADON DAWA 36
.
TRUE LIFE STORY
.
Ya xauna yacigaba da dubansu daya bayan daya,
daka shigo falon duban farko da zaka yiwa
kowannensu dauka zakayi a kotu suke suna jiran hukuncin kisa, a zabure suke haka a
kage suke su dukka tamkar su rusa ihu, cikin wannan hali sumayyah Tukur ta shigo ta
iskesu sai ta cika da mamaki bata ma gama amsa gaishe gaishen da yaran sukeyi mata
ba saita yada jakar hanun ta akasa ta runtuma wajen mahaifiyarta da sauri ta rike ta
tambaya take lafiya mutuwa akayi?
nemi waje ki zauna inji mummy hafsat.
kafin sumayyah ta kara cewa komai samari biyu ne suka shigo na dazu da abokinsa
yayinda kaltum ta dinga kallon masu kama dayan nan tana tantance inda suka
banbanta, suma suka sami waje suka zauna yayinda suka kurawa mummy ido kowa
yana so yaji abunda zata fada,
ta dubi kaltum wanda tuni cikinta ya duri ruwa ta fara nadamar zuwanta, ta zata suda
mummy hafsat zasu labarinsu ta tashi ta tafi sai gashi anyi gaiya an cika falo,
fito daga lungu yarinya ki dawo tsakiyar falo ki zauna yayinda ta daga kai tadubi idanu
ca akan ta saita sunkuyar dakai kasa,
daya daga cikin samarin nan wato mai riga suit ya dubi agogo ya girgiza kai yace afuwan
mummy kibani minti 2 zanyi magana inaneman izini zan tafi saboda inada uzuri labarin
wanan yarinya ba wani abu zai karamin ba tunda banida wani alaka da ita da labarinta...
ka rufamin baki ai kai dama ba a komai da kai ko kasanta ma ba sauraronta zakayiba
tunda bakason shiga mutane ko wani uzurine gareka saika tsaya ka saurara kobazai kare
ka da komai ba, inji mummy hafsat.
atakure yake jinsa kamar a daure shi yaci gaba da hararar kaltum yakagu ta gama
yatashi yatafi yace aransa banda abu irin na mata tayaya zaiyi su dauko yarinya yar
secondari da uniform da jakar ta a goye a bayanta ta tara kartai ace ta basu labari, me
ta sani a duniya mezata fahimtar da su ilimi ma aikatanda suka goge da ilimin digiri da
masters abu na biyu da ya ayyana a ransa shine ko kawota akayi sunganta ko daya daga
cikinsu ace ya aureta jira yakeyi yaga gudun ruwansu yaji karshen labarin sannan yaja
musu burki duk da yarinyan tanada kyau amma batayi masa ba bazata taba yimasa ba,
koda tafara labari saiya tsinci kansa ya fara nutsuwa yana sauraron ta takai takawo ya
gyara zama ya mika tunaninsa da hankalinsa kacokan a gare ta, kwakwalwarsa takasa
tantance masa karshen labarin kome take shirin baiyanawa?
yaji wata kalma wacce keyimasa gizau don haka sai ya katse ta zai yi mata tambaya
yayinda mahaifiyarsa ta katse tambayarsa ta mayar masa da amsar yayi shiru ya
saurara kawai kada wani a cikinsu ya sake magana har sai kaltum ta gama,
yaja numfashi ya rike kai yana jujjuyawa domin ya tabbatar shin gaske ne ko kuwa barci
yakeyi ga abubuwan tambayanan kowa yanaji amma babu daman yinta saboda hani
daga mummy hafsat.
kaltum ta fuskanci hankalin kowa nakanta da alama labarinta yanada tsarkakiya da
rikitarwa don haka sai ta dinga bin salo irin na marubuta masu batar da tunanin mai
karatu wajen kasa gano abun da zaifaru anan gaba har sai anzo karshen labari,
aketantance ta fara basu labari daga ranarda
suka hadu a daura da kayansu suka shiga motoci zuwa maiduguri suka tsaya suka yi
sallah suka ci guzurinsu sukaci gaba da tafiya har suka isa bur sudan da yadda suka
kwanta akan kabarurruka sukayi barci tabasu labarin ranarda aka zo aka tantance masu
tafiya wadanda takardunsu suka cika akabar wadanda suke da takardar bogi sannan ta
fara basu labarin yadda rayuwar su takasance su da aka barsu abur sudan sannan tafito
da sunan MADINA baro-baro saiyanzu suka fara fahimtar inda labarinta ya dosa sai yanzu
su kasan dalilin tarasu daka akayi a cikin labarin da Madina ta bata tundaga onisha har
ranar da ta rabu da Abba a asibiti har dalilin ta na barin kasar ta kuma basu labarin
rabuwarta da Madina da kuma ra ayinda ta barota na cewa bazata kara dawowa nigeria
ba har abadah ko gawarta bazasu gani ba...
kafin kaltum ta rufe bakinta tayi sharkaf da hawaye yayinda duk wanda yake falon
hawaye yake yi,
mummy hafsat ta share hawaye tace kaltum wayace da Madina Abba ya mutu a gabanta
ya mutu?
abokinsa mukaddam ne yayi mata waya duk da cajin wayarta yakare bataji karshen
maganar ba taji koke-koken mata kuma ya ambaci Abba ya ...Sai wayarta ta katse,
mummy hafsat ta nuna daya daga cikin samarin nan tace ga mukaddam din nan,
kaltum ta juya da sauri ta dubeshi ya gyara zama ya murza jajayen idanuwansa yace
hakika nayiwa Madina waya alokacin da ta tafi Abba ya farfado yake cewa akira masa
Madina zai fada mata wata magana kasancewar ranga-ranga yake rai ahannun Allah,
watakila wata wasiyyah zai bari wacce yaki fadawa kowa sai ita dana kirawo ina
tambayan ta ina take yanzu sai hayaniya tayi yawa naga kuma tana kidime tana
tambayana ko lafiya?
inaso nace Abba yatashi yace akiraki sai wayan ta dauke to banmasan ta zaci nace abba
ya mutu ba,
kaltum ta dubeshi ta gefen ido alamar rashin fahimta ta tambaya cike da fargaba
Mukaddam kana nufin Abba bai mutu ba?
Mukaddam ya nuna saurayin nan mai bakin Kaya suit yace ga Abba, yayinda aka hau
kallo kallon tsakanin kaltum da Abba,
ya dafe kai sai yajujjuyawa kalma daya yake fita daga bakinsa shine InnaLillahi wa inna
ilaihi raji'un yayinda hawaye suke tarwatse a idanuwansa,
shahida ta daura hannu akai tana kuka tana cewa wayyo mamana, Abdul Malik da
Abdulmajid ma ba asan wanda yafi wani karfin haliba kuka suke suna fadan a ina zamu
nemo mama?
Dr sumayyah tukur ta mike tsaye ta kifa kai ajikin bango tana kuka tana cewa Madina
kiyafe mana abunda muka miki kiyi hakuri kidawo muna sonki aminiyata...
general tukurne ya fado cikin falon yasake juyawa ya dubi ya yan Madina daya bayan
daya saiya girgiza kai yace Allah Ya kyauta Allah Ya sauwake ya suri bindigansa ya fice,
wani dogon numfashi kaltum taja don samun kwanciyar hankali da aka fitar da
bindigarnan, dr sumayyah tukur ta sharce hawaye ta dubi kaltum cikin siririyar murya
tace kaltum ya akayi kika rabu da Madina kika dawo gida?
kaltum ta langwabe kai tabasu labarin sanda hauwa tazo ta dauketa da yadda sukayi
sallamar karshe a fili jirgin kasa taci gaba da cewa watannina bakwai a Khartoum daga
nan iyayena suka turo aka taho dani sai dai mambela ya tabbatar min cewar Madina
tana bur sudan koda yake yanzu na shekara daya da rabi da dawowa duk da haka ina
kyautata zaton tana bur sudan ammafa mambela ya ce babu yadda baiyi da ita ba akan
ta rakoshi Nigeria wajena taki tace ita da Nigeria har abada,
Abdul hakim ya zabura ya mike yace nizanje bur sudan nemanta kibani kwatancen
wajen.
mummy hafsat ce tace dukkanku ku dakata kada wani ya yanke hukunci harsai abunda
muka shawarta da daddy, kada inji wani ya tarki hanyar sudan kwanan nan.
abba ya nisa ya dubi kaltum da idanuwansa
dasuka canja launinja saboda kuka yace yaya
Madina ta zama?
kaltum ta ciro jakarta daga bayanta saita ciro wasu hotuna guda uku ta mika mishi
yakarba da sauri ya duba yayinda hannuwansa yahau karkarwa yasa hannu ya toshe
bakin sa saboda kada ya rushe da ihu yaji dadin ganin
madina araye kuma Allah Ya amsa addu arsa da Ya bayyana inda take amma ya gigita
daganin yadda ta lalace ta fige kamar kaza tayi duhu tamkar mutanen da aka tono su
daga cikin kasa haka ya gansu yaro-yaro almajirai ne sak ba wai kama da almajirai
sukayiba donma hoton bikine a ranar duk sunyi kwalliya, da basuyi kwaliya ba ashe daba
a san yanda za a gansu ba, dagasu har gidansu abun tausayi, ya dubi hoto na farko
Madina ce da kaltum sun saka tsohon nan mai sayar da ruwa akan jakinsa atsakiyarsu
hoto na biyu kuwa Madina ce tsaye tsakar gidansu sanye da hijabinta tana dariya, hoto
na uku kuwa abakin tekune su dayawa ranar bikin Amina.
sumayyah tukur tasa hannu ta karba ta duba saita mikawa mamarta ta kallah itama ta
girgiza kai saita mikawa 'yayan Madina, tsananin kukanda sukeyi shi ya sake tayarwa
Abba da hankali, sai mukaddam ya lura ciwon kirjinsa da ciwon kansa sun fara tashi yayi
marmaza ya tashi yafita dashi yakaisa dakinsa don ya basa magani,
Anas kanin Abba sai yanzu yayi magana ya dubi kaltum yace kiyi hakuri kaltum bansan
labarin Madina kikeson bayarwa ba harnaso na dake ki.
ta girgiza kai tace bakomai nagode.
sumayyah Tukur tace kaltum koda Allah Ya sa kin riga mu ganin Madina ki gayamata
bada niyyah mukamata abunda mukayi ba rashin sanine amma daga baya Abba da
bakinsa yabamu labarin abunda ya faru a tsakaninsu kakaf, sai mukaji kunya mukayi
dana sani, muka nemi Madina sama ko kasa bamu sameta ba mukaji ina mamu ganta
munemi gafararta mu aura mata Abba Allah bai sa munganta ba sai muka nemi gafarar
Abba da na 'yayanta mukaci gaba da addu ar Allah Ya baiyana mana ita Allah Ya sa tana
hannu nagari idan kuma ta mutu Allah Ya jikan ta, saigashi Allah Ya amsa addu ar mu ya
bayyana mana inda take, zamu shawarta
yanda za ayi mu dauko Madina dole zata dawo wajenmu ko bazata auri Abba ba don
muna so Madina tazama tamkar jinin mu, Anas tashi kamayar da kaltum gida kaga inda
take saboda watarana ku tafi da shahida kada agidansu aganta dana miji,
kaltum tayi godiya suka dunguma suka fice sai ayanzu hankalin kaltum ya kwanta data
isar da sakon Madina sai dai kash ta kasa gano hanya guda daya cal da zata aikawa
madina sakon cewa Abba bai mutu ba, tayi tunanin duniyannan babu ta hanyarda zata
iya turawa Madina wasika ko a waya suyi magana,
kaltum tayi gum da bakinta bata taba bawa wani dan gidansu labarin madina ba babu
wanda yasan tana zuwa unguwarsu shahida.
haka ta taso tun tana karama rayuwarta ita kadai takeyi bata shawara ko doguwar hira
ita da iyayenta daman batada wasu kawayen kirki tuntuni su hadu a makarantane
surabu abakin get, gara yanzuma datake makaranta wayayyu tana da kawaye masu
nitsuwa su biyu Hamida da Aisha suma kawancennasu iyakaci a makarantane kawai
basu taba zuwa gidansu kaltum ba itama haka garama da alh Adnan ya sayo mata waya
daga America kwanannan suna yawan hira a waya suta zazzaga labari, da turawa juna
sakonni amma ko kadan kaltum bata tattauna abunda ya shafi rayuwarta ko gidansu,
ajinsu shida don haka suna tsakiyar karatu kamar yadda alh Adnan yake yawan
gargadinta kada tasake ta fadi jarabawar su ta karshe akallah ta sami credit bakwai a
waec da neco ta dage taci jamb kuma don ta wuce jami a kai tsaye,
a dai dai lokacinda take tsakiyar karatu haikam dai dai lokacinne jikin goggo fattu ya
tsananta har aka gaji da zamanta a asibiti aka dawo da ita gida.
.
ADON DAWA 37
.
TRUE LIFE STORY
.
kuma a dakin kaltum aka ajiyeta duk da akwai iya uwani awajenta wato kanwarta kenan
amma ta fara kosawa da zaman don haka kullum tana karairayi saita kirkiro tafiya
zangon daura, yau gaisuwar mutuwa gobe suna, bata cika zama ba kaltum ne mai
kulawa da ita tunda asuba take tashi ta fara fama da wanke-wanken zannuwan goggo
fattu na fitsari da bayan gida ko kaki da amai, ta goge mata jikinta sannan ta bata abinci
da magani,
daga kwance goggo fattu saitayita kurawa kaltum ido tana kallonta tana tuna bakar
muguntarda tayi mata a baya tana nadama a lokacinda take tunanin rayuwa tajuya mata
baya yayin da yanzu yan kankanuwar yarinyarda take azabtarwa itace mai karfi kuma
mai taimakonta sai gashi ta maye muguntar da tayi mata da alkhairi sai kaga hawaye
yana surnanowa da alama tana nadama sai kaltum tasa gefen zaninta ta share mata
hawaye ta kara da cewa goggo kidaina kuka komai ya wuce.
rayuwa kenan har sai kaltum tagama hidimar goggo fattu sannan ta fara shirya kannen
ta da ita kanta sannan su tafi makaranta, tana makaranta ma tana tunanin halinda
goggo Fattu take ciki shin batayi fitsari ko bayan gida a kwance ba kodai tanajin yunwa
ko kishi ruwa babu mai jiyo kiranta idan ba sofi bace ta leko dakin taganta ba, babu
wanda zaisan halinda take ciki ita kuwa tana kicin kullum hidimar girkin ta ma ya ishe ta,
kaltum tana da tausayi duk da duk sanda takalli goggo fattu saita tuna abunda tayi mata
a baya amma zuciyarta bata taba ayyanamata ta wulakantata ba ko tarama abunda tayi
mata abaya ba don tana da ikon da zata rama din ko duka zata iya mata babu wanda zai
sani don a kwance take bata iya ko daga hannunta bakinta a jirkice gefe don haka ko
magana take ba a ganewa idan ma ba duka ba zata iya hanata abinci kotaki cire mata
kayan data bata duk hanyoyine na musgunawa amma kaltum ko kusa bata tunaninyi
mata haka ba.
tana tuna nasihohi da hadisanda ake musu a
issalamiyyah akan mutum ya zama mai yafiya da kyatatawa.
duk rayuwa mai dadi da kaltum ta tsinci kanta baisa ta manta da Madina da Mambela ba
sai kuma tatuno ta fatsuma aminiyarta takan yi kuka saboda tasan wahalan rayuwar da
ta dandana abaya tanaso ta zauna dasu amma bata sha'awar ta koma wajensu inama za
akwaso minsu akawominsu kano muyi rayuwarmu anan?
tunaninta da addu'ar ta kenan a koda yaushe,
zuwan kaltum gidansu Abba ya kawo cece kuce iri-iri a cikin gidan domin Abba ya tubure
saiya tafi sudan ya nemo Madina iyayensa kuwa sunce bazasu barshi ba saboda basusan
halinda zaije ya fada ba akasarda baitaba zuwa ba,
Tasi'u kuwa ya kullaci Abba domin shima ahalin yanzu Madina yake nema ido rufe domin
yagane Madina ce mace tagari mai sonsa ita ta dace dashi inhar Ya tabbatar zai samu
Madina tabbas saiya sallami sauran matansa dukka domin Madina mace dayane tamkar
da dubu sai bayan tafiyar ta Ya tabbatar ya rasa mace, duk wadannan matansa har guda
uku sunansu mata ammadai ba mata bane basu san ma yadda ake daraja mijiba babu
tsafta babu komai don haka kowaccensu yayi mata saki bibbiyu ahalin yanzu igiyoyi
daya daya ya rage musu, kuskure kadan zasu tafka yakarasa tsittsinkawa, gidansa ya
zama sansanin yaki saboda kishi rige rigen haihuwa akeyi masa don haka 'ya'ya kanana
ne burjik agidansa, nauyi ya karu yayinda kasuwa tajabaya jari yaragu don haka Tasi'u
yarasa kwanciyan hankali a rayuwar sa, ya tsufa ya rame ya lalace ya kazance
kasancewar ya rasa matarda takeyi masa wanki da guga da girki mai kyau koda kudinsa
ko babu kudinsa zaici,
saigashi yanzu da kudinsa ma ba a dafa mai mai dadi sai yanzu ya dau son duniya ya
dorawa ya yan madina musamman shahida idan ya kalleta sai yaga tamkar yaga
Madina, saboda kamarsu daya sak, shiga goma fita goma saiyace ina shahida ina Abdul
hakim da Abdul Malik?
saiyagansu yakejin dadi, yana tarasu a falonsa yahau yimusu bayanai marasa tushe
tamkar tababbe sunayimasa kallon ya fara zautuwa tsabar nadamarda yakeyi yana
danasanin abunda yayiwa Madina, bai damu da kishin da matan sa sukeyiba akan yawan
ambaton Madina,
sunan madina dayakeyi fiye da sau goma arana burinsa kawai ya ambaci sunanta yaji
sanyi aransa saida ya tabbatar madina tayi masa nisa kuma ta haramta agareshi sannan
ya nutsuwa yashiga hankalinsa yayinda duk abubuwan alkhairi da tayi masa yake
dawowa kwakwalwarsa, Tasi'u ya matse hawaye ya dubi shahida ya juya yadubi yayanta
Abdul hakim da Abdul Malik ya girgiza kai yace kuyi kokari ku gaji halin mahaifiyarku
idan kuka yii irin halayenta zaku ci ribar zaman duniya da lahira, ku kwaikwayi Madina
domin mace ce mai hakuri da tawakkali, ni Tasi'u na yi kuskuren rabuwa da mace ta gari
irin Madina na

Please Login or Register in order to submit comment