Reading adon dawa Chapter 13 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a enugu sai ya nemo miki shi su xo
tare , yin hakan xai faranta miki rai. Na ce kada ya je, yace in kyale shi xai je ko da kuwa
xai rasa ransa ne a hanya. Ashe ya fada da bakin mala’iku, haka ta same shi.”
Na juya na dubi Abba, na yi kuka na yi kuka, na ji dama a dawo da rayuwa baya da banyi
masa abunda na yi masa ba. Mu dukka bamu runtsa ba har asuba, na yi alwala a
bandakin cikin dakin nahau salloli ba adadi kafin assalatu, addu’a nake kada Allah Yasa
Abba ya mutu.
Yayinda mukaddam ya tafi masallaci ashe ya dauki wayarsa, yana idar da salla sai ya
kunna a inda ya hadu da sakonnin iyayensa da iyayen Abba. Hankalinsu a tashe suke
tambayar ina suka shiga shi da Abba tun jiya?
Sai ya yanke shawarar ya kira mahaifiyarsa ya yi mata bayani ita kuma ta yiwa mahaifan
Abba bayani. Tun da asuba, kafin gari yawaye xance ya xagaye dangi hankalin kowa ya
tashi yayin da motoci na alfarma suka dinga tsayawa a gaban dakin da muke.
Muryar mukaddam na jiyo yan magiya yan bada hakuri game da dogayen bayanai cikin
kuka da rawar murya a jikin wundon dakin, na meke da gudu na daga labulen wundon na
leka, sai ga en gidan su Abba kakaf da danginsa da ‘yan uwan su mukaddam, yayinda
baban mukaddam yaketa sharar masa mari ba adadi da kyar a ka rike shi. Aka sako
mukaddam a gaba ya xo ya nuna musu daki, su ka dungumo suka nufo inda muke. Na
takure a loko ina karkarwa ina kiran “laa haula wala kuwwata illa billah.”
Suna shigowa suka kalle ni a sheleke babu wanda ya amsa gaisuwata, yayinda suka nufi
kan gado da sauri wajen Abba duk wanda ya leka Abba sai yayi baya ya dafe kai yana
salati saboda Abba yayi kwatsa-kwatsa. Ina kuka na taso ina shirin in yi musu bayani sai
kuwa sumayya tukur ta sharara min mari, sannan ta kira ni da suna karuwa,
mahaifiyarsu mami hafsa ta kirani da suna maiya na cinye mata da, wai daman ashe
nice na kama shi ya dinga ramewa sannan na yi asirin da sai da ya kai kansa onisha aka
tsafe shi dan haka sai hukuma ce xata raba ni dasu.
Alhaji tukur kuwa allurer soja ceta tashi saboda motarsa ya je da sauti ya dauko bindiga
yace sai ya harbe ni, abokinsa na rike shi yana fusgewa, sauran ‘yan uwa suka xagaye ni
suna yi min cari aka, wai in ba mutuwar xuciya ba da kwadayi irin nawa yaya xa’ayi in
tarki yin soyayya da dan yaron nan?
Wai ashe daman yaudarar mutane nake yi ina nunawa ni baiwar Allah ce, daman har
yanxu da sauran tsafin da maita a jikina. Ba ni da bakin bayani saboda babu mai sauraro
na.”
Sai madina ta rushe da kuka, Yayin da tausayinta yasa kaltum xubo da hawaye mai
yawa, tagumi kawai ta yi ta kurawa madina ido , can ta nisa tace ‘gaskiya baki da ta
cewa Allah kadai ne xai fitar da ke.”
Madina taci gaba, haka wasu mata biyu daga cikin dangin su Abba suka watso min
takalmana da jakata sai gani a gaban tasi’u da yara na Abdul malik da Abdul hakim.
Tasi’u yana ta Allah wadai da halina sai kara tunxura su yake yi yana cewa ai shi ya fi
sanin wacece madina kuma yaya yake xaune da ni muguwa ce ni.
Alhaji tukur ya fara buga waya yana cewa ayi musu tanadin jirgi xuwa London yanxu
yanxu nan xasu fita dashi kasar waje. Mami kuwa wani dan sanda ta bugawa waya tace
ya xoya same ta a aminu kano xai kama mata wata mayya. Ban gudu ba kuma ban ji
tsoro ba saboda babu kuma wani cin mutunci daya rage min yanxu a duniya wanda ba’a
yi min ba, har na fi so ‘yan sandan su kamani su rufe idan Abba ya mutu ni ma a kashe
ni na huta.
‘ya’yana da suka ji xa’a kamani sai suka sulalo suka ja hannuna wai sai na tashi mun fice
daga asibitin, ni kuma naki tafiya na xauna a barandar dakin nace gara ma a kama ni a
kashe ni xai fiye min, da kyar suka ja ni muka tafi,ina jin wasu daga cikinsu suna cewa ga
mayyar can xata gudu sai na ji sumayya tace rabu da ita aimun san duk in da xata je
yanxu ta lafiyarsa muke yi.
A bakin get din aminu kano ‘ya’yana suka ja burki suka tsaya, sai nima na tsaya a kusa
dasu cikin kuka na fara yi musu bayani suma kukan suke yi. Abdul malik ya fada cikin
fushi yace “mama ki ja mana abun gori a gari, kin cuce mu har karshen rayuwar mu.” Ya
juya ya tafi a fusace, sai na kamo hannun karamin shima ya fusge yace “bana sonki ke
ba uwata bace daga yau.” Sai na saki baki ina kallonsu suka tafi suka bar ni a tsaye.
Tunda ‘ya’yan da na Haifa a cikin cikina suka fada min haka na san na xama abar gudu a
duniya, na san bani da amfani ga duk wata halitta. Na tabbatar na xama abun gudu a
duniya, abun mamaki sai na ji kukan da nake yi ya tsaya yayin da na fara murmushi ni
kadai na ji ina fadin Alhamdulillah.”
Madina ta fashe da kuka mai tsanani.
Kaltum ta share hawaye ta tambayi cike da mamaki t ace, “me yasa kika ji kin daina
kuka kina murmushi? ”
Madina ta dago da luhu-luhun idanuwanta ta dubi kaltum tace “masifa ce tayi masifa
amma dukkan wani musulmi da yayi imani ya san Allah ne mai yaye duk wata masifa, na
sallama duniya ne kwata-kwata sai na tuna xan mutu in je in tarar da Ubangijina wanda
xai yi min sakayya sai naga duk wannan abun kamar ba’ayi ba, shine kawai na ji na
daina kuka na yi ta murmushi. Menene dadin duniyar ne?
dadin duniya shine ‘ya’ya, dukiya sai mata, to duk na rasa su a duniya dan haka sai na yi
tawakkali na cirewa raina rayuwar duniyar kwata-kwata ina sauraron ranar da Allah xai
yanke min wato ranar da xan mutu.
Ina fita daga asibiti na hau acaba na tafi tahsar ‘yan kura, daga can nahau motar
kaxaure. Ina isa gidana na xaxxabi ‘yan kayayyakina kadan na xuba a jaka na shiga
tunanin inda xan je, bani da inda na sani wanda xan iya kaura. Daga karshe na yanke
shawarar nima in tafi enugu in nemo yayana innamani in har yana raye in xauna tare
dashi don shi kadai ya rage min. na shiga sake-saken ta inda xan fara nemo su sai nace
a raina idan naje enugu na tambayi sunan kawuna exe wanda yake rike shi idan kuwa ya
mutu nasan shima innamani watakila a san shi idan yayi kudi tunda yayi karatu, sai dai
kash bani da kudin motar tafiya.
Sai na tashi na shiga gidan makwabciyata mai suna sha’atu itama ma nurse ce,
baxawara kamar ni. Na iske tayi bakuwa daga Daura suna xaune suna hira. Ta na ganina
tace, ina na je tun jiya ake ta nima na ba a ganki ba, kuma me ya same ki kika rame
sannan idanuwan ki suka kumbure?
Se nace mata xaxxabi na yi da ciwo ido kuma na je kano tun jiya.
Nan dai muka xauna mu uku suna hirarsu ina sauraran su hankalina baya wajen su, ina
tunanin halinda Abba yake ciki.can se mariya kawar shafa’atu ta dauko hirar xuwa
makka ta mota xasu bi ta sudan wani satin. Sai kuwa nayi carafna tambaye ta na ce,
nawa ne kudin?
Kuma ina ake biyan kudin?
Ta yi min bayani dalla dalla, sai na ji gara kawai in tafi kasar da ba’a sanni ba. Shafa’atu
na yi min tsiya tana cewa wai me yasa na ke tambaya ni daba xuwa xan yi ba?
Na ce wallahi da ina da kudi da nima xuwa xan yi.”
Sai mariya ta dubi hannuna tace “yaya xaki ce baki da kudi kuma kina sanye da tafka-
tafkan awarwarayen gwal har guda biyu a hannunki ga sarka da ‘yan kunne da xobuna ai
ya ishe ki kudin motar har ma yayi saura.”
Sai a lokacin na tuna ashe ina da kadarar gwal, ai nan da nan jikina ya dau rawa nace
“wallahi idan mariya xata tafi daura tare xamu tafi”
Mariya tace “ai ni a yanxu xan koma ba xan kwana ba.”
Shafa’atu sai ta fara tuntsirewa da dariya a xaton ta wasa nake yi. Ta ce ta yaya xan bar
aikina, da mutunci na, da kuruciyata, ga yarana amma in tafi saudiyya yawon wanke-
wanke da shara? ”
Ai sai suka ga na shiga gidana na dauko jakar kayana na rufo gidan na shigo na tsaya
akansu na cewa mariya ta taso mu tafi daura, abu kamar wasa sha’atu taga na rikewa
mariya hannu muna ta sauri mun bar ta a baya mun nufi bakin titi, ta gaji da bin mu ta
juya gida. Tace min “in kin je ma xaki dawo nasan karya kike yi ba wata makka da xaki
je.”
Ai kuwa har ya shafa’atu bata ga dawowata ba kuma nasan sun hadu da mariya ta fada
mata cewar na tafi. Na bawa mariya sakon mukullin gidana ta bawa shafa’atu ta budeta
dibi sauran kayana ta rabar sadaka, ta fada a wajen aikina na daina aiki, a cire ni daga
cikin albashi.”
Kaltum tace daga kaxaure se ku tafi daura?
Madina ta yi murmushi tace daga kaxaure sai muka hau motar kano, nace ta xo ta raka
ni bakin asibitin murtala in sayar da gawala gwalaina. Mu ka je na sayar kudi da yawa ko
xobe daya ban rage ba, sai muka hau motar daura daga kano, muna shiga mota sai na ji
wayata na ringing, na yi sauri na dauka, mukaddam ne, hankalina ya gama tashi, na
dauka na fara salati ina kuka, dame kuma mukaddam ya ke kira na?
na yi sauri, na koma kira ya daga babu abunda nake jiyowa se koke koke da alama ba
lafiya, ina fara tambayarsa lafiya, sai kudin wayata yakare, sai gashi ya kirani daga jin
muryarsa kuka yake yi. Ni ma na fashe da kuka nace inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un.
Mukadda lafiya, ina Abba?
Sai ya sake fashe wa da kuka yace “sister madina Abba ne ya………..”
Sai cajin wayata ta kare dif naji shiru wayar ta mutu. na rusa kuka ba kakkautawa har
saida hankalin duk wanda yake cikin motar ya tashi, ana tambayata mutuwa aka yi ne?
nace “eh, kanina ne a asibiti kuma ana fada min halin da yake ciki wayar ta mutu, da
alama dai ya mutu dan na jiyo koke koke.
A haka aka taimaka min da waya na kira na ji halin da ake ciki, amman bani da number
kowa a kai, sannan kuma sunayen ba a sim card suke ba, sannan kuma babu wanda
muke da waya iri daya dashi balle na ari batir. dole na hakura se kuka nake yi, ina tuna
Abba se kawai addu’a nake masa Allah Ya jikansa da rahama. Tsarki ya tabbata ga
Ubangijin talikai, haka Allah Ya rubuto mana, a haka yake so ya ganni.
Kaltum kinji dalilin xuwana sudan kenan. Wannan shine abunda ya rabo ni da yarana na
shiga wannan hali.
Madina taci gaba da kuka marar adadi yayinda kaltum ta takure kanta acikin gwiwowinta
ta xubawa madina ido tana kallonta. Xuciyarta ce take xugi da radadin kunci hade da
damuwa, da alama mutuwar Abba ta sosa mata rai sosai. Hawayenta ne ke disowa daya
bayan daya. Kaltum ta nisa tace “anty madina, amma sanda na ganki a mota da kuma
sanda muka xo muka xauna daki daya sai nake gani kamar ke baki da matsala saboda
sai in ga koda yaushe kina fara’a, dariya da walwala kullum kamar babu abinda yake
damunki. Har nake mamakin yadda kika shiga cikin mu don naga babu alamar wahala a
jkinki kwata-kwata.”
Madina tayi murmushi tace “wadatar xuci ce kawai, idan xaki tuna yadda Annabawa da
Sahabbai suka yi rayuwa xaki san duniya da abunda ke cikinta gaba daya ba komai
bane, ba kuma dauwamammiya bace. Shudewa take wataran tamkar ba’ayi ba. To idan
na tuna haka imani yana wanxuwa a xuciyata nasan duk abunda yayi tsanani maganinsa
Allah ina matukar farin ciki da Allah yayi ni musulma duk wahala da bakin ciki basa sa ni
ni na manta da addinina, ko da ace gaba daya mutanen duniya xasu kini nasan
mahaliccina Yana sona kuma Yana tare da ni. Ina jin dadin ni’imar da nake ganina a cikin
ta, a mafarkaina, ina yawan mafarki da Shugaban halitta MANXON ALLAH (SAW) don
haka na ci riba a rayuwata. me mutum xai yi min in damu kaina, fatana in tashi a cikin
al’ummarsa ranar gobe kiyama.”
Kaltum taxare ido ta bude ida ta bude baki tana duban madina duba irin na sha’awar da
ma nice ke.
Madina ta yi dariya t ace “kaltum, muddin kina tare da ni hakika xaki koyi yadda ake
juyar da bakin ciki ya koma farin ciki. Lokacin sallar la’asar yayi muje mu yi salla.”
Sai suka kwashi shinfidarsu suka shiga cikin gida, domin bada faralli.
ALLAH YA KARA MANA IKHLASI AMEEN ,
ADON DAWA 2 (P 16)
.
TRUE LIFE STORY
.
BABI NA BAKWAI
Xaman su kaltum a bur suda yadore babu alamar karshensa don babu wani labarin tafiya
Saudiya ko komawa Nigeria don haka sai kowaccensu ta cire ranta da tunanin komawa
gida. Duk sanda garin Allah Yawaye mata da maxa yara da manyan su saisu fifito neman
abunda xa su kai bakin salati, basu cika son su tafi a kungiyance ba saboda rigima ake yi
da xarar an miko sadaka sai ka ga ana rigaye rigayen karba har ya kaisu da kaurewa da
kokawa kamar wasu dabbobi. Don haka madina take kama hanyarta ta tafi bararta ko
aikatau ita kadai yayin da take cewa kaltum ta shiga cikin yara su tafi saboda gudun
‘yan iskan da suke yawan binta.
Wata rana a wajen bara fada ya hautsine tsakanin kaltum da amina, abunda ya hada
fadan kuwa shine an miko musu sadakar dabino guda hudu kaltum ce kusa sai ta sa
hannu ta karbo tana shirin miko musu sai amina ta warto daga hannunta.
Ta ce mata “mayya, kawo nan an miko min kika yi sauri ki ka karba. Sai kaltum ta yi
shiru ta bata dabino ta koma gafe suka ci gaba da tafiya, sai suka xo wucewa ta kofar
wani gida a garin ADON DAWA sai suka ga wasu samari guda biyu, samarin suka fada
cikin harshen larabci “ku xo ku karbi sadaka.”
Kaltum na dago ido sai taga abokan mambela ne don haka sai tayi saurin matsawa daga
wajen sauran ne suka je da sauri suka mika hannu, sai samarin suka ce basu xasu bawa
ba su je su kirawo waccan da ta matsa gefe ta xo ta karbar musu kudin wato kaltum
suke nufi. Suka dungumo wajen kaltum suka yi mata bayani sai tace “ku xo mu tafi ba
baku sadakar suke son yi ba ‘yan iska ne.”
Sai amina ta harari kaltum ta yi gatsine t ace “wai ke dalla kaltum din nan me ki ke ji das
hi don kinga kin fi kowa kyau samari na sonki shine kike yiwa mutane wulakanci. Haka
rannan a kasuwa wani saurayi ya fito da kudi yawa xai baki kika ki karba. Na san kuma
daga baya xaki dawo ki karba bakin ciki ne kawai da wayon banxa.
Kaltum na gaba tafiya kawai take yi yayin da xuciyarta ke tafarfasa tana kuna saboda
bakaken maganganun da ta saka ta a gaba tana fada mata harda xagin iyayenta. Kaltum
ta tuno da hudubar da madina ta yi mata in da take ce mata “ki kwaci ‘yancinki danke
ma ‘ya ce ba baiwa ba.” Ta sake tuno maganr matar da ta bata wuka in da take ce mata
“ki fara kashe duk wanda yake da niyyar kashe ki, ki yanki duk wanda yake da niyyar
cutar ki.”
Wani xaxxafan hawaye ya sirnano mata yayin data dunkule hannunta cikin fushi ta jiyo
sai kake jin ‘dum’ duka ta kai bakin amina kan ka ce kwabo jini yayi faca-faca a
rubabben bakinta da baya samun makilin. Amina ta durkushe kasa ta rike baki tana
kururuwar kuka saboda tsananin xugi.
Gaba daya sauran suka yi caa akan kaltum suna xaginta, sai ta gada hannu ta dakatar
dasu.
Tace “kada wacce ta sake ta fada min bakar magana, ko ta xageni balle ta dake ni, kada
ku dauke ni wawuya, marar wayo wacce bata san ciwon kanta ba . kada ku dauka bana
jin xafin kyara da cin mutuncin da kuke yi min ada. Na gaji, hakurina ya fara karewa xan
taba duk wanda ya taba ni.”
Ta rushe da kuka ta ci gaba da Magana cikin kakkausar murya tace “ku hantare ni, ku
xage ni, ku dungure min kai, ku aike ni duk bana kuskure muku kawai don a xauna
lafiya, bana son in bata muku rai badan ina tsoranku ba, amma kuma nice na xama abar
wulakantwa a wajenku. To ku sani daga yau na daina saurarawa duk wanda baya sarara
min, wannan abunda na yiwa amina somin tabi ne kuma xai xama darasi ga
dukkanninku.”
Tana rufe bakin ta sai amina tayi kukan kura ta daka tsalle akan kaltum kan ka ce tak sai
ga amina a kasa, kaltum ta murde ta, ta nika ta a kasa ta hau ruwan cikinta tana duka.
Su rakiya suka xo suka banbare kaltum daga kan amina da kyar. Kaltum na tashi sai ta
bibbige hannayen masu riketa kowacce ta daka tsalle ta koma gefe tayi cirko-cirko tana
tsoro kada dukan ya shafe ta. Hakika sun yi matukar mamakin ganin yadda take da karfi
haka. Ta juya ta tafi a fusace ta bar su a tsaye suna kallonta.
Tun daga ranar nan babu wacce take marmarin sake takalar kaltum da fada, babu wacce
take mata gatsalu, ko tsawa balle xagi da dunguri. Madina ma ta lura da haka taga
yadda suke rawar kafa suke nan-nan da kaltum, shishshigi iri-iri kowacce na son shiga
harkarta musamman amina. Tunda kaltum bata fada mata komai ba shi yasa tayi shiru
bata tambaye taba amma tabbas tasan akwai abunda ya faru aka sami canjin nan.
Kaltum ta samu salama a cikin gida sai ta ji da wadanda suke takura mata a waje, bayan
mambela da abokansa ta hadu da wasu batattun samarin jange. Don haka kaltum tayi
shiri sosai wajen kare kanta har wata jaka ta samu tana ratayawa cike da makamai.
Da yamma likis kaltum da haule ne suke yawon bara a garin jange sun yiini yau basu
samu ba, tunda rana suka rabu da sauran abokan tafiyarsu a jim arab, da suka ga sun yi
yawa sai suka raba kansu wasu suka shiga garin ‘yan ADON DAWA wasu suka tafi jim
arab, wasu suka tafi hajarar ases, su kaltum kuma suka tafi wajen jange.
Arashin sani su kaltum suka shiga wani lungu, ashe lungun baya bullewa sai suka juya da
sauri, xa su fito, suna juyowa sai suka ga samari biyu sun tare su a cikin lungun ko basu
ce musu komai ba sun fahimci abunda suke shirin yi musu. Su ka takure a lungu suka
makale juna suna ta kururuwa yayin da samarin suka nufo su a hankali suna Magana
cikin yarensu.
Kaltum tayi larabci tace “bama jin yarenku, kuyi mana larabci.”
Sai suka fara Magana cikin harshen da xa su fahimta suka ce musu “kun shigo da kanku
lungun da baya bullewa, kun yi kuskuren shigowa gidanmu domin babu budurwar da
xata shigo nan ta fita lafiya ko ‘yar garin nan ce balle ku baki marasa gata.”
Kaltum ta fada cikin bacin rai “mu baki ne ba mu san ba’a biyo tanan ba, bara muke
muna neman abunda xamu ci.”
Sai suka ce “to yanxu xamu baku abunda xaku ci amma fa sai mun gama da ku.”
Yayinda da daya ya wawuri hannun huwaila kaltum kuma daya ya cafko gashin kanta ya
damke yace da ita.
“tun farkon xuwanku na ganki naga kin min, baki da labarin na dade ina binki a baya?
Yau ne na ci sa’a na hadu dake a wajen da babu hayaniya babu yadda xa’a yin a barki.”
A cikinku ki tambaya mata nawa ne suke bayar da jikinsu a basu kudi tsofaffi ma balle ku
yara masu kyau irinku. Me xai ragu a jikinku idan an taba ki, ki samu kudinki hankalinki
kwance. Sai kaltum ta hasala ta hau fuffuka tana fisge-fisge xata kawace, ya bankare
wuyanta yana kokarin kai ta kasa, yayinda dayan tuni ya durkusar da huwaila kasa.
Kaltum ta laluba ta ciro wukarta daga cikin rigarta kan kace kwabo ta danna gefen wukar
kaifin ya fito fet ka ke ji ta sharba masa a hannu ba shiri ya ske ta ya daka tsalle gefe ya
rike hannu yana ihu jini yayi masa face-face a hannu. Kaltum ta sake bude jakar dake
makale a hannunta ta xaro wata katuwar kwalbar lemo ta rusa a jikin bango ta fashe rabi
ya rugurguje sai ta rike rabin a hannunta ta nufi dayan da yake rike da huwaila, shima a
guje ya sake ta suka xabura suka fara ja da baya.
Kaltum ta fada cikin kakkausar murya tace ‘xan kashe duk wanda ya tabo mu, sai na
farka cikin duk wanda ya nufo ni.”
Tana xare ido tana nufo su, sai suka tabbatar da gaske take farka cikinsu xata yi dan
haka sai suka juya a guje suka fita daga lungun. Kaltum da huwaila suka arta da gudu
suka kama gabansu suma. Mamaki ya kama huwaila akan abunda kaltum tayi tana
matukar mamakin yadda kaltum ta tanadi irin wadannan mugayen makamai a jikinta.
Huwaila taje ta dinga yada kaltum a cikin gida cewar a yi hankali da yin fada da kaltum
domin cewar wukake ne da kwalabe a jikinta da xarar fada ya hada ta da mutum xata
farka shi da wuka.
Su ka tabbatar kaltum ta xama ‘yar daba yayin da ‘yan gari ma suke kiranta da ‘yar
agulla, wato ‘yar daba saboda har ‘yan iskan gari sun gane ta. Ta ketawa samari da
dama hannu ta fasa wa jama’a da dama kwalba akai sai dai idan ba’a rutsa taba a lungu
ana kokarin a cimmata ba yanxu ne xata yaga fatar mutum.
BABI NA TAKWAS
Yau kaltum ‘yar agulla ta dira a bakin kogi a inda masu kamun kifi suke ta damko
manya-manyan kifaye wanda girmansu xai kai girman yaro dan kimanin shekaru fiye da
bakwai. Ta tsaya tana jiran abokinta mai suna karim ya fito daga ruwa ya bata kasonta
daman ya saba bata kullum sai ta je gida ta gasa su ci.
Karim saurayi ne wanda shekarunsa bai wuce ashirin da biyu ba, dan asalin garin
katagun ne a jahar bauchi a kasar Nigeria. Amma bai san kowa a garinsu ba kasancewar
iyayensa sun taho dashi sudan tun yana da shekara daya kamar yadda aka bashi tarihin
cewa mahaifinsa ya tsaya a n’djamena da niyyar neman kudi sai ya turo karim da
mahaifiyarsa su xo sudan su jira shi idan yayi aiki ya samu kudi sai ya same su a sudan
su haura saudiya. Tundaga lokacin basu kara haduwa ba, bai xo ba, ana kyautata xaton
a n’dajsmena ya rasu yayin da itama mahaifiyarsa Allah yayi mata rasuwa ta barshi shi
kadai dan kankanin yaro a hannun wani tsoho abokin tafiyarsu mai suna baba lado.
Karim na xaune shi da tsohon a bur sudan a dakin katako, kwali kadai a shinfide a dakin
har ya girma ya fara sana’arsa ta kamun kifi yana sayarwa, a halin yanxu tsohon ya rasu
dan haka karim shi ne uwa shine uban kansa.
Ya hadu da kaltum jininsu ya hadu yana farin ciki da ganinta sai ya ga kamar yaga
kanwarsa musamman idan ya ji tana yi masa hausa. Da yake babu kalma daya ta
soyayya da ke tsakaninsu ita da karim sai ta saki jiki dashi su kayi ta labari haka kuma
yana matukar taimaka mata da manyan kifaye gasassu ko danye, ko ma ya bata kudi
idan ya sayar ya samu.
Karim yana fitowa daga ruwa sai ya kalli kaltum yayi dariya, itama ta yi masa murmushi
cikin harshen hausa take yi masa Magana tace yayana, yau ragon ruwa xaka bani, katon
kifi me tsoka. Sai yayi dariya yayi Magana cikin harshen hausa duk da hausar bata fita
sosai, yace yau kifin duk manya ne, ki xabi duk wanda kike so.
Kafin karim ya rufe bakinsa sai ya ji wani mummunan duka a kuncinsa har saida ya
tuntsura ya fadi kasa. Kaltum da karim suka daga ido lokaci daya suka duba bangaren da
dukan ya fito. Sai ga mambela a tsaye ransa a bace mamaki da tsoro gami da fargaba ya
rufe xuciyoyin su. Mambela ya sake cacubo karim ya nika da kasa yana shirin hawa
ruwan cikinsa da duka, sai kaltum ta yi kukan kura ta xaro wukarta ta yanka mambela a
kwairin kafarsa.
Mambeala ya xabura ya rike wajen yayin da karim ya yunkura ya mike tsaye da sauri
yana shafa kuncinsa suka yi jawur dan xafi. Mambela ya dago ya dubi kaltum yayin da
jini yake bulbulowa daga inda ta yanke shi.
Karim ya fada cikin harshen hausa “kaltum ki gudu kada mambela ya kama ki, wannan
mugu ne, ya addabi kowa a garin nan.” Kaltum tace “ba xan gudu ba sai dai ya kashe ni,
ka gudu kada ya kara dukan ka, ka bar ni dashi.”
Karim ya arta da gudu ya bar wajen ya tafi can nesa yana duban su, yana tsananin
fargabar kada mambela ya tashi ya shake kaltum . har yanxu mambela yana tsugunne
yayin da kaltum take tsaye kem a gafe

Please Login or Register in order to submit comment