Reading adon dawa Chapter 29 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankalinsa yayi matukar tashi daga yanda yaga tafito tana kuka,
abunda yake zargi ya tabbata cewar ya tafka kuskure daya furtawa alh Adnan zancen ya
auri yar sa kaltum gashi nan ya jawo mata tsana tunda daga lokacin yasawa ransa
zamansu ya kare a gidan nan sai ya shiga tunanin ta yanda zamansu yakare agidannan
sai ya fara tunani inda zasu fara babu gida babu gona babu sana a.
fitar kaltum keda wuya alh Adnan ya jawo wayar sa ya kira lambar alh sa'adu ta Nigeria
yajita a kashe saiya kira layinsa na sudan sai kuwa ya same shi bayan sun gaisa yake
shaida masa akwai wata mata da akeso anemo musu ita mai suna Madina a bur sudan
amma ana tunanin matar bazata yarda
tazo ba har sai an tafi da mijinta,
alh saadu ya zabura yace kai haba kamar bani?
aiko a daure zan daukota kamar bakasan dauki ba dadin da mukayi da wannan bararojin
ba mambela?
ai koshi kace in kawo maka duk da kasarsu ce sai na kawo shi da karfin tsiya balle yar ci
rani wacce ba kasarsu ba kuma mace ai karamin aikine wannan, alh ka bani wuka da
nama ka turo kudin jirgi kawai shine aikinka idan nakawota sai kabiyani yadda aka biyani
waccan karon, nikuma sauran aiki ya rage nawa nasan bur sudan nasan gidajenda
mutanenmu suke zama na tabbatar idan naje na tambayi sunanta za'a nuna min ba
boyayyiya bane tunda kowa yasan kowa a tsakaninsu.
alh Adnan yayi dariya yace karka damu da wannan zan fita anjima zanje banki zan turo
maka kudin komai ammafa kayi mata a hankali, ban saka dukan matar mutane ba koka
daureta da igiyaba, cikin lumana zaka tahoda ita idan taki kabata waya zanyi mata
magana in sha Allahu zata yarda ta biyoka, alh sa idu ya rusuna yayi godiya gamida
yarda dabin umurnin alh Adnan, suka yi sallama suka ajiye,
missed calls biyar ya gani da sunan Abba yanata kokarin nemansa a lokacin da yake
waya da alh Sa'adu ya amsa kafin Abba yayi magana ya bashi tabbacin cewar ya
kwantar da hankalinsa za'a kawo masa madinarsa har gida ba sai yasha wahalar zuwa
ba, Abba yaji labarin alh Adnan kamar tatsuniya bai fahimce shiba ma kwata-kwata sai
ya shiga jero wa alh Adnan tambayoyi cikeda magiya
yana neman alfarma ya taimake shi yadda Allah Ya taimakeshi,
alh Adnan ya fahimci Abba bai gane abunda yake nufiba baya da haka baisan waye alh
Adnan ba, shiyasa yake kokonton abunda ya fada masa, maganar karshe da alh Adnan
yayi itace Abba kabani sati daya za a kawo maka Madina insha Allah.
Abba yayi godiya suka ajiye waya batare da Abba ya yarda da abunda alh Adnan ke fada
ba kai har yanzu bai fahimci komai ba don haka sai hankalinsa yatashi, kamshin zuwan
madina da ya fara ji ada ya gushe, ya kwanta yaji kwanciyar ba dadi ya tashi zaune yaji
zaman ya gagareshi saiyayi zumbur ya mike yayi waje, a falo ya hadu da mahaifinsa ya
zauna agabansa ya fara koro masa bayanan da alh Adnan yayi masa,
sai mahaifinsa yace to ai shikenan mu jira zuwa sati dayan,
ba haka Abba yake son ji ba, yafiso mahaifinsa yace ya shirya yaje sudan din,
su kuwa mahaifansa da en uwansa bazasu taba barinsa yaje sudan yadda sukaji labarin
cewar Madina tace har abada ba zata dawo Nigeria ba to tabbas idan Abba yaje taki
biyoshi waje zai samu ya zauna da ita shima bazasu kara ganinsa ba.
Abba ya mike jikinsa a sanyaye ya shiga dakinsa ya dade a tsaye ba tare da yasan
abunda zaiyiba can ya dauki makullin motarsa ya fita da sauri ya kuwa ci sa'a babu kowa
a falon ya fizgi moto sai kofar gidan alh Adnan,
a wajen get ya ajiye motarsa ya fito ya nufi cikin gidan shigarsa keda wuya sukayi
kicibus da maigadi, malam saleh ya dubi Abba shima ya dubeshi sai hankalin malam sale
yayi matukar tashi saboda ya gane wannar fuskar, saurayin nanne dayazo wajen kaltum
ranan su biyu, malam sale ya tsuke fuska ya tambaye shi a fusace waka zo nema ?
Kamar yadda saleh ya gane Abba haka Abba ya gane mai gadinda yakoresu rannan ne
don haka shima afusace ya amsa masa wajen masu gidan nazo,
sale ya hasala yace kai yaro ba inda zaka wuce in har baka fada wajen wacce kazo ba.
Abba yace mai ya hadani da mace ai wajen mai gidan nazo alh Adnan yanzun nan muka
gama waya dashi kashiga kace masa barister Abba Tukur ne daga yankaba,
sai sale yayi sauri ya rabe ajikin get,
Abba ya wuce batareda wani ya sake magana acikinsu ba.
baisan kofarda zaibi yashiga wajen alh Adnan ba shikuma bayaso ya tambayi wannan
mara mutuncin mai gadin nan sai gashi Allah Ya
jeho masa kaltum ta fito daga cikin gida dauke da bokiti zata yi shanya a igiyar dake
daure a farfajiyar gidan kamar kullum daga ta dawo daga makaranta zata fara aikin
wanke kayan kazantan goggo fattu tana ganin Abba saitayi turus tana dubansa cike da
mamaki yayinda shi kuma farin ciki ya lullube zuciyarshi yayi dariya yace yauwa kaltum
ashe kinanan, yayanki kuwa yana ciki?
ya fadi hakane don yanaso yasan dangantakarta da alh Adnan,
saita dubeshi duba na rashin fahimta shima ya fahimci haka saiyace alh Adnan nake
nufi, sai tayi ajiyar zuciya ta nuna masa kofarda zai shiga jikinta a sanyaye maimakon
yatafi sai ya tsaya yana dubanta yana duban kayan shanyarda yake hannunta yana
duban kannenta da suka baibayeta yana duban mahaifiyarta datake daka agefe ga goyo
don ko ba a fada masa ba yana duban sofi yasan itata haifi kaltum da alama nan boys
quaters
shine gidansu amma kuma babban gidan ta nuna tace nan ne inda alh Adnan yake ciki,
tambayoyi fal acikin zuciyarsa babu damar tambaya saiya wuce zuwa bangaren da ta
nuna masa ya tura kofa yayi sallama sai suka
ci karo a tsakiyar falo har alh Adnan yayi wanka ya shirya da makullin moto a hannunsa
zai fice, yayi mamaki da ganin Abba don haka suka dunguma suka koma wajen kujeru
suka zazzauna,
alh Adnan dakansa ya dauko masa lemo da ruwa acikin firij sannan suka fara
tattaunawa.
malam sale tsaye a bakin get har yanzu yana zullumi, zuciyarsa tana ta tsaro masa
karya da gaskiya yace aransa wato dai alh Adnan yasan wannan saurayin kaltum ne don
haka ya aika akirawosa zai ba shi ita tunda shi bazai iya auranta ba amma tayaya
zandauki yata inbawa wannan fitsararren yaronda yake yi min magana cikin gatsali ba
mutuntawa?
saidai kuma bazan iya yiwa alh Adnan musu ba akan duk hukuncinda zai yanke akan yar
nan don shi yayi wahalarta, ni wani tsausayine ma yasa na furta masa wannan kalmar
taya auri kaltum?
malam sale ya nufi gida da sauri ya iske kaltum na shanyan har yanzu sofi na daka ya
dafe kirji ya fada cike da damuwa kaiku tsaya da aikin nan,
gaba daya suka sankare a tsaye suna sauraronsa cikeda fargaba yace wata katobara
nayi wacce ta dameni ga ta zata zame mana matsala, game da zancen yarinyan nan
kaltum da alh Adnan,
kaltum ta dafe kirji tace Abba lafiya?
mena yi?
ya juya ya dubi kaltum yace ina kika samo wancan yaronda ya shiga cikin gida?
kaltum agigice tace Abba ne ai wanda zai auri Madina.
wacece Madina zaki fara boye-boyen nan naki ko?
don ba a taba jin cikinki ba, basu bane kwanakin baya na koresuba?
saita fashe da kuka tana rantse-rantse,
sofi tajashi cikin daki don taji kan labarin saboda kar su alh Adnan din suji yanda yake
magana da karfi a fusace yayinda kaltum tazo ta labe a bayan wundo tana jiyo duk
abunda mahaifinta yake fada ya zayyanewa sofi duk yanda sukayi da alh Adnan da kuma
hukuncinda yake zargi alh Adnan zai zartar yana zargin Abba saurayin kaltum ne
wajenta yake zuwa kila alh Adnan ya kirawoshi yabashi ita donshi ya zame ya fita...
.
To jama'a wannan episode din yana nuna mana kuskure na mal saleh da matar sa Sofi
da aka daura su na rashin jituwa da er su da pahimtar juna,
Da akwai kyakkyawar mu'amala tsakanin su da er su da ba'a kawo nan ba, da tun wuri
sun sake da ita da ta basu labarin komai, kuma da sun san komai da ya shape ta
maimakon ta sanar da wani,
Wasu yaran tsabagen babu puska a wajen iyayen su abokai suke baiwa labarin kukan su
da daria, idan akayi rashin sa'a abokin bana gari bane sai ya basu shawara marar kyau,
Ana so iyaye lokacin da dan su yake taso wa xuwa shekara 7 su nuna masa soyayya,
daga 7 xuwa wani 7 su nuna masa abu mai kyau da marar kyau (ma'ana su tarbiyyar tar
dashi,) daga wani 7 din kuma su mai dashi abokin su, ta haka ne baxai na boye musu
komai ba, xasu san irin halayen sa da irin abokan sa kuma xai koyi irin halin su.
Amma wasu iyayen sunan sun aihu ne kawai, sai su barwa dunia ta raina musu 'yaya.
Sai kaga uba bai san halayen yayan sa ba, bai san abokan yayan sa ba, banda gaisuwa
babu abun da yake hada sa da su balle a samu lokacin hira ya pahimci damuwar su ba.
Ina mai Jan hankalin iyayen mu mata da maza ake shiga lamarin yaya, a jasu a jiki, ba
sai abu ya kwabe ba azo ana dana sani, wani kapin a ankara yaro ya lalace.
Allah Ya tsare mu baki daya.
ADON DAWA 40
.
TRUE LIFE STORY
.
kila alh Adnan ya kirawoshi yabashi ita donshi ya zame ya fita daga nauyin da akeso a
daura masa.
sofi tayi tagumi tayi shiru can tace malam kayi kuskure daka amayarda wannan magana
abunda muke tunani muke addu'a dama yakasance shine zaka je ka fada?
yanzu ga irinta nan,
malam sale yayi ajiyar zuciya yace tsausayi ne wallahi nima ina dana sanin, don kaltum
bazata fadi abunda ya fada mata bane dazu da ta shiga ta dade aciki saita fito tana kuka
kila zaginta yayi ma.
kaltum dake labe a bayan wundo saitaji kamar zata kurma ihu don haka ta damke
bakinta kuka ma mai tsanani ya kece mata, hankalinta ya tashi matuka yayinda ta
fuskanci gaba daya zancen mahaifinta zargi ne baisan gaskiyar al amari ba,
na daya baisan abunda ya sata kuka ba dazu ba, haka baisan tsakaninta da Abba ba,
baisan dalilin zuwan Abba wajen alh Adnan ba, wannan kalmar duk bai dameta ba tunda
zargi yake, babbar matsalarta yadda yaje ya furtawa alh Adnan wannan kalmar ta aure
alhali ga mijinta can a bur sudan wanda a koda yaushe yana ranta, tana muradin
ganinsa babu wani da namiji a duniya dayakai mambela a cikin zuciyanta bata da wani
uba ko uwa dayakai alh Adnan a ranta, don haka kowa da matsayinsa, ta koma dakinta
ta zauna ta kifa kai da gwuiwarta tana kuka,
Goggo fattu na kwance akan gado tamkar gunki amma sai yunkuri take tanaso ta
tambayi kaltum me aka yi mata take kuka amma maganar bata fita,
kaltum ta fahimci abun da goggo futtu keson ji cikin kuka ta fara magana batareda ta
dubeta ba tace Goggo abur sudan kika tafi kikabarni ba uwa babu uba babu mataimaki
sai Allah, iya mairo kawarki da jikarta rakiya dakika hadani dasu suka dinga
tsangwamata sai na hadu da wata mata a cikin mu mai suna Madina, itake taimakona
bayan ita sai na hadu da wani saurayi a garin ADON DAWA mai suna mambela shima
yana sona kuma ya taimake ni, munyi alkawarin aure dashi, shi nake so na aura amma
sai gashi Abba yaje yatari alh Adnan yace ya bashini ya aureni alhali ni a matsayin uba
na dauke shi, babu mai kula dani babu mai yimin wahala babu mai bani abunda nake
bukata a duniya sai alh Adnan, kiduba kiga irin tashin hankalinda matarsa mummy
salaha ta jefamu, ki tuna kiga irin rigimar da za a tafka idan ta samu labarin maganar da
mahaifina ya furta a yanzu tun kafin ma azo ga auren,
ta tsaneni bazata bari inzauna lafiya ba gashi inason mambela har yanzu shine na
shaidawa kawayena zan aura har an yi mana baiko.....
ki auri Adnan kalmarda goggo fattu ta furta kenan radau ta dira a kunnuwan kaltum,
kaltum ta zabura ta dago kai ta dubi goggo Fattu wacce ke kwance luf kamar ba ita tayi
magana ba, matar da a shekaru biyu maba a taba gane abunda tafada ba sai yau,
kaltum ta share hawaye tace goggo me kika ce?
shiru bata sake magana ba amma hawaye yana ta kwaranya daga idanuwanta,
kaltum ta rushe da kuka ta saka gefen zaninta tana gogewa goggo fattu hawayen da
yake kwaranya daga idanuwanta,
kafin lokacin makarantar islamiyyah yayi kaltum ta saka kayan makaranta ta dauki
Qur'an nta tanufi makaranta saboda kawai kada Abba da alh Adnan su fito su kirawo ta.
Abba yayi shiru yana nazarin akan bayananda alh Adnan yayi masa, saiyaji tunaninsa ya
hargitse ya kasa magana har lokaci mai tsawo?
Abba yayi ajiyar zuciya ya dubi alh Adnan yace alhaji meye abunyi yanzu kace kaltum ta
bada shawarar lallai a tafi dani sannan Madina zata yarda ta dawo, kace alh saadu yace
shizai iya kawo mana ita yaya ka gani ?
Alh adnan yace kabar alh Sa'adu mugani din idan zai iya idan yagagara sai kaje din ta
ganka kuma nace idan ya ganta yabata waya zanyi magana da ita nasan abunda
zanfada mata.
Abba yace to shikenan amma inhar ta yarda zata taho to kada maka fada mata ina nan
ka boye mata bayan ta dawo kun hadu ka roketa ta aureni saboda kai zata iya yarda da
maganarka ina fargaba ta bijire ta ki aure na.
alh Adnan yayi murmushi yace yarinta ke nan kana so aki fada mata baka mutuba kana
tunanin zata yarda tazo din in baka nan?
Abba yace ina kyautata zaton zata iya yarda da maganarka idan ta dawo zata iya
bijirewa taki aurena,
Alh Adnan yace ka bari ta dawo din nayi maka alkawari zanyi iya kokarina ka auri
Madina,
Abba yayi murmushi yace Allah Ya taimaka, alhaji nasan Madina tanada alkunya kayita
magiya zata yarda, yanzu nawa zaikama dukka harkawota kano da dan rakiyar kuma
nawa za a biya mai kawowar?
alh adnan yace karka damu nizan dau nauyin komai saboda Madina ta taimaki kaltum
tanada matukar mutunci, naji inaso na taimaka mata nima.
Abba ya langwabe kai yayinda kwallah ta cika
masa ido yace Wallahi alh ba wanda zai zauna da Madina koyaji labarinta baiji ta kwanta
masa a rai ba, macece mai matukar kirki da sanin ya kamata, madina ta banbanta da
sauran mata don haka duk wanda na tinkara nakeja da baya domin basuda halin Madina,
alh ka taimakeni nasamu Madina a rayuwata, inason matar nan idan ban aureta ba
nahakura da aure kwata kwata...
kayi addu a Abba, Allah Ya zaba maka abunda yafi maka alkhairi a rayuwar ka, alh
Adnan ya fada yayinda ya mike tsaye yana daura agogo,
Abba ma ya mike tsaye yana godiya yace bari natafi naga kana shirin fita ina ta bata
maka lokaci ko?
ai idan na sami wajenda za ayi min zancen madina banaso intashi daga wajen na gode
alh Allah Ya kara zumunci Allah Ya taimake ka yadda ka taimakeni.
alh Adnan Ya amsa da amin. suka dunguma suka fito,
saleh ya tako da gudu ya zo ya duka ya gaishe da alh Adnan yana jira yaji hukuncinda
aka yanke masa na mummunan laifinda ya tafka dazu, saiyaga alh Adnan cike da fara a
ya dube shi yace saleh ga Abba ku gaisa, kaltum na cikine ka kirata su gaisa?
sai malam sale yaji fargabar da yakeji ada ta dadu ya dago ido ya dubi Abba shima ya
dubeshi sai Abba ya gaishe shi, malam saleh ya amsa a sanyaye gami da kirkiro
busasshen murmushi yace ai kaltum ta tafi islamiyyah dazu,
alh Adnan yace to ai shi kenan dama gaisawa zasuyi da bako yayinda, Abba yake kokarin
furta tambayanda ya addabeshi aransa haka ma malam sale yake furta tasa a wannan
lokaci sai su dukka suka tsaya suna kallon juna,
alh Adnan kamewa yayi atsaye yana sauraronsu malam saleh yace da Abba yaro fadi
maganarka tukunna sai nima inyi tawa.
Abba yace daman tambaya zan yi ince yaya kake da kaltum?
sai malam saleh ya dubi alh Adnan ma'ana yabashi amsa,
alh Adnan yayi dariya yace mahaifin kaltum ne,
Abba yasake duban malam sale da alaman mamaki ya gallabi zuciyarsa amma bai sake
cewa komaiba saidai kallo daya zakayimasa kasan ba iyakar tambayarsa kenan ba,
malam saleh kuma yace nikuwa tambayanda zanyi shine waye wannan?
don ko a danginku bantaba ganinsa ba saboda asan juna idan an hadu a wani waje a
dinga gaisawa kada ayi abun kunya,
Abba ma alh adnan ya kalla ma'ana yanzuma shizai bada amsa,
alh adnan yayi dariya yace wannan Abba kenan angon Madina ne wacce suka zauna da
kaltum a bur sudan.
malam sale yaja dogon numfashi sai a yanzu ya samu nitsuwa.
Abba yayi musu sallama ya fice yayinda alh Adnan ya shiga motarsa malam sale kuwa
yahau aikinsa na bude get harsaida alh Adnan ya fice sannan ya rufe get ya koma ya
zauna akan benci yayi zugum yana sake-sake da alama ya yarda da zancen kaltum
cewar Abba ba saurayinta bane.
labbaika rasulillah sautin dake fita daga wayar alh Adnan kenan wayarsa tayi ta ruri
misalin karfe takwas na safiyyar asabar yayinda yake tsakiyar barci akan luntsumemen
gadonsa da yake katafaren gidansa na hadaddiyar unguwar nan mai suna asokoro a
babban birnin tarayyah Abuja, da kyar ya daga hannunsa ya lalubo wayar a karkashin
filon da yake kwance ba tareda ya iya bude ido yakaranta sunan mai kiranba saboda
tsananin barcinda yakeji saiya danna yamaka a kunne daga kwance batare da ya iya
magana ba haka yakasa amsa sallamar da mutumin yake radawa sauraronsa kawai yake
yi hello alh kana jina?
gani abur sudan tareda Madina,
kalmarda tashiga kunnen alh Adnan kenan a take yanemi naunauyan barci nan yarasa
sai yaji idonsa ya wartsake garau ya tashi ya zauna daram akan gado yayinda matar sa
salaha ta fasa ficewa daga dakin ta dawo ta tsaya akansa tanaso taji waye mai wannan
wayar da har ta wartsakar dashi daga barcin da yake,
yace alh sa adu da gaske kake katabbatar itace Madinan Abba?
alh sa adu yace kwarai kuwa itace kadai Madina ma agidan tasan kaltum kaima tace
tasanka Allah cikin ikonSa ma ankawo service din waya garin, itama da waya ahannunta
don haka gatanan zakuyi magana don naga a tsorace take bata yarda dani ba, alh sa
adu ya mikawa Madina waya ta karba atsorace hannunta na kakkarwa gami da yimasa
sallama cikin ladabi da girmamawa, ya amsa cike dakulawa yakara da cewa Madina
kamar yanda kikeda labarina nima inada labarin ki kakaf banason tone-tone banason
maimaita magana banason jin ra layinki na da, magana zamuyi ta yanzu maganar da ya
wuce, kaltum tafadamana irin kokari da kikayi ko ince jihadi da kika yi kika ceto
rayuwarta a wajenda kowa takansa yakeyi, ta fadamana dalilinki na barin ya'yanki
kikayi gudun hijira da zummar har abada baza ki dawoba a yanzu dai atakaice ni alh
Adnan na aiko alh saadu abokinane shine wanda na aika ya dauko kaltum inaso ki
biyoshi ku dawo m
ta rushe da kuka mai firgitarwa ta girgiza kai tace alh naji dadin kulawarka agareni Allah
Ya saka da alkhairi ammakayi hakuri bazan iya biyo shi ba har abada bazan dawo Nigeria
ba.
alh Adnan yaji hankalinsa yatashi yatambaya agigice Madina meyasa?
amatsayinki na musulma kike fadin haka?
bakisan kaddara ba?
kobakya yafiya?
ta girgiza kai ta share hawaye da gefen gyalenta tace bahaka bane alh nafi jin dadin
rayuwa anan fiye da can, na yafewa duk wanda ya zalunceni irinsu Tasi'u da matansa
nayafewa duk wanda sukayimin Kazafi irin mummy hafsat general Tukur da kawata
sumayyah, na yafewa 'yayana dasuka ki min biyayyah amma na hakura da kara cigaba
da rayuwa dasu babu mai wankeni a duniya sai Allah, Abba ne yafi kowa sanin gaskiya
lamarin shi zai fitarda ni, shikuma baya raye to mezanzo nayi?
sai ta rushe da wani kuka mai daga hakalin mai sauraro,
alh Adnan yayi ajiyar zuciya yace kinaso kigayamin da Abba na raye zaki yarda ki dawo
saboda zai wankeki daga zarginda ake miki?
Madina ta gyada kai tace eh da Abba naraye zan dawo saboda nayarda da son da yake
min koda ace bazan aure shi ba,
ADON DAWA 41
.
TRUE LIFE STORY.
.
Ko da ace baxan aure shi ba inason Abba har raina.
kinaso kice min da Abba naraye yace har yanzu yanakan bakansa na auranki da yake
son yi zaki aure shi?
Madina tace tabbas da matacce na dawowa da zan auri Abba, nayi nadamar abunda nayi
masa gashi duk da gudun rigimarda nakeyi naki amincewa saida ta afku har fiye ma da
ace na yarda,
alh Adnan yace bakya tunanin 'yayanki musamman karamar mace?
ta sharce hawaye tace alh na rayu ba uwa ba uba babu yayye amma daga baya na hadu
da mutanen da suka fiye min iyayena da dangina alkhairi duniya da lahira don haka
rashina bazai zama shine karshen gatansu ba Allah shine gatan bawanSa Allah Ya
hadasu da abokan zama na gari, ina daganan ina jifansu da kyawawan addu'o'i bazasu
tagayyara ba insha Allahu, babbar damuwana daman kaltum ne na matsu ta koma gida
ta rayu da iyayenta tayi aure cikin mutunci Allah Ya amsa addu'a ta yanzu hankalina ya
kwanta zanji da kaina,
alh Adnan ya shiga yi mata magiya yana hadata da ta duba girman Allah da darajar
Manzon Allah (s.a.w)ta dubi matsayin musulmi awajen dan uwan ta musulmi yayi mata
alkawarin bazai fadawa su mummy hafsat ta dawo ba bakuma kano zataje ta zauna ba, a
Abuja zatazo ta zauna tare kaltum,
tun Madina tana bashi hakuri akan ya daina ma rokarta bazata dawo ba har tayi shiru ta
rasa abunda zata fada masa daga karshe ya fada mata wata magana da tayar mata da
hankali yace da ita Madina dalilin da yasa nace a nemoki shine Abba bai mutu ba, duk
tsawon shekarun nan yana kwance yana jinya a asibiti anan Abuja, bai daina Kiran
sunanki ba ki tausaya masa kizo ki ganshi ko Allah zaisa ya warke...
alh Adnan ya katse waya ya barta a zaune kikam rike da waya ahannu tamkar gunki,
Hajia salaha ta dubi maigidan nata ta tsuke fuska yayinda ta rike kugu ta girgiza ko ba a
fada masa ba yasan yau akwai rigima ta tambayeshi tamkar danta, dawa kake waya
wacece Madina?
daman kai ai komai inda Madina aciki kafi bashi muhimmanci, wato bayan kaltum dinda
aka aika aka dauko har kawarta xaka dauko?
kaine bawansu kai zaka dauko ta to bari kaji babu matarda zata dakomin gida don naji
kana lallashinta idan batason kano taxo Abuja.
Alh Sa'adu kuwa sai magiya yake mata da nasihohi iri iri yake jero mata akan ta taho su
tafi, haka mata da mazan gidan suke shawartarta ta shirya ta tafi tun kafin damar nan ta
subuce mata suna masu yi mata albishiri da sune suka sami wannan dama da karshen
matsalarsu tazo a dunia, daga karshn Madina ta shirya tayi sallama da yan gidansu aka
yi ta kukan rabuwa saboda an saba, sabo turken wawa, bata fito daga bur sudan ba
saida ta garzaya jim arab kasuwar yan ADON DAWA ta iske mambela a rumfarshi da
abokansa suna shan jubna yana ganin jajayen idanuwan Madina sai ya wurgar da kofin
jabna ya zabura ya mike tun bata karaso rumfar ba ya tareta yana tambayar ko lafiya?
agigice ta rushe da kuka cikin yaren ADON DAWA tace mambela nima anzo daukana zan
koma Nigeria gidansu kaltum.
ya dade yana dubanta bai iya magana ba cikin sanyin murya yace da ita ki daina kuka ki
share hawayenki abun murna ne ki gaishe min da kaltum kice har yanzu ina son ta,
sai hawaye ya kwaranyo daga idanuwansu su dukka ya juya ya koma cikin rumfa ya
zauna jikinsa ya mutu ya zurawa Madina ido har ta kure, yaki amsawa abokansa
tambayoyinda suke ta jera masa,
daga bur sudan Madina da alh sa adu jirgin kasa suka hau na zuwa Khartoum ya kai ta
gidan wasu mata yan Nigeria acan ta zauna har tsawon kwanaki hudu ana cuku-cukun
tafiya visa da ticket sannan suka sami tahowa bayan komai ya kamkama,
ranar talata da yamma Madina da alh sa'adu suka dira a birnin tarayyah Abuja, daga filin
jirgi suka bugawa alh Adnan waya yace su ba wa mai taxi waya yayi masa kwatancen
gidan, tunda dan gari ne nan da nan yagane anguwar gwarumpa gidan alh Mansir
babban amininsa na Abuja kenan,
kafin sukaraso har alh Adnan ya bayyana a gidan daman ya shaidawa mai gidan zai
kawo musu bakuwa su rike masa har zuwa wani dan lokaci saboda yasan halin matansa
bazata bari ta sauka agidansa ba,
hankalin alh Adnan ya tashi dayaga Madina daga ita har jikinta da buhun kayanta da
take rike dashi, ya fada aransa daman wannan itace madinar da Abba yake muradin so
kamar zai rasa ransa adalilin rashin ta?
to koba haka take ba ada yanzune tazama haka?
Madina ta durgushe agabansu ta gaishesu ba tare da ta matso tsakiyar kafet din da yake
tsakiyar falonba balle ma ta hau kan kujera ta zauna,
hajiya zainab matar alh Mansir ta taso da fara'arta ta karbi buhun kayan Madina tana
mai yimata sannu da zuwa da bata izinin ta iso cikin daki, Madina ta na biye da ita a
baya zuwa cikin daki, katafaren daki mai dauke da
tafkeken gado da madubi da durowar saka Kaya, bandakin acikin daki bayan ta saka
buhun kayanta a durowa sai ta nunawa Madina bandakin ta umurceta ta shiga ta yi
wanka za a kawo mata abinci yanzu, sai mamaki da farin ciki ya lullube zuciyar Madina
yaushe rabon duniya da ayyaraye wai yau ita ake cewa ta shiga kayataccen bandaki

Please Login or Register in order to submit comment