Reading adon dawa Chapter 5 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

asibiti ni da mahaifana. Ya ce ayi duk
abinda ya kamata ayi xai biya ko nawa ne. asibitin nasarawa aka kai ni a lokacin
shine asibitin da yake tashe sai dan wane da wane. Likita na ganin yanayin jikina
sai ya bamu gado muka kwanta aka dinga kara min ruwa da allurai. Allah cikin ikon
Sa kafin sati guda na murmure, shi yasa aka ce kowace cuta da maganinta. Na
samu sauki har na fara tashi xaune ina surutu kuma komai aka bani ina ci. Kusan
kullum Alh Adnan da matarsa salaha suna xuwa su gaishe ni a asibitin bayan
kayan dadi na marmari da abinci iri-iri da suke yini suna aiko direba yana kawo
mana asibiti.”
Madina tace “gaskiya wadannan iyayen gidan naku suna da kiriki.”
Kaltum tayi murmushi tace “suna da matukar kirki shi da matarsa dukka. Bayan an
sallamo mu mun dawo gida sai muka ci gaba da rayuwarmu a gidan, ina matukar
jin dadin gidan saboda na samu walwala ba’a dukana, babu yunwa, ba babu
hantara.
Makaranta mai tsadar gaske aka sani.
Madina tace “Allah kenan, haka yake ikonSa.”
Kaltum tayi murmushi tace “na tsinci kaina mai farin ciki matuka sai dai matsala
daya data addabe ni itace bana samun kulawar iyayena. Ba kulawar rashin wanka
da wanki ba ne, kuma ba matsalar abinci ba ne, basa hira da ni, haka basa
saurarona, ko na matso kusa dasu saisu matsa saboda wancen ra’ayin da goggo
fattu ta cusa musu.”
Madina tace “ban fahimci basa sauraronki ba, kamar yaya? ”
Kaltum t ace “kunyata su ke ji saboda ni ‘yar farice don haka na xama tamkar
mujiya a tsakiyarsu sai kallo da ido. Ina matsowa kusa dasu saisu ture ni ko su
tashi daga wajen, idan na taho musu da hira saisu gwale ni ba xasu saurareni ba.
Idan xan yini ina kuka babu wanda xai lallashe ni a cikin su. Har ‘yan gidan suka
fara fuskantar hakan, Alh Adnan ya dinga yiwa mahaifana nasiha yana nuna masa
wannan kunyar da yake yiwa ‘yar fari ba’abun burgewa ba ne illa jahilci da cutar
kai.
Akwai wata ranar asabar ba xan taba mantawa ba da sassafe misalin karfe takwas,
a lokacin ana tsananin sanyi. Ni da mushkur muka fito bakin get wajen da babana
yake xaune yana jin dumi da itace, yayin daya rufa da burgujejen bargo. Yana
ganinmu ya tabbatar sulalowa mukayi muka fito ba tare da sanin iyayenmu mata
ba, saboda ko rigar sanyi babu a jikinmu, ba hula, ba takalmi daga ni sai yar
yaloluwar singileti da pant, haka mushkur daga shi sai karamar jallabiya ba dogon
wando. Ana tsananin hunturu, mai tafe da haxo, da iska mai kura don haka hanci
da ido sai xuba suke yi, yayin da duk ilahirin tsikar jikinmu ta tattashi.
Babana na ganinmu sai ya kira mushkur ya dauke shi akan cinyar sa ya rungume,
ya lullube shi da bargo, yayin daya juyar dashi saitin garwashi suka yi ta jin dumi,
suka juya min baya. Ina xaune akan benci a bayansu ina ta makerketa ban isa in
kutsa cikin bargon ba saboda nasan hantara ta xai yi ya kore ni.
A cikin wannan hali Alh Adanan ya fito ya iske mu, sai ya ji ransa ya baci yayi ta
yiwa mahaifina fada yana cewa shi fa ba burge shi yake yi ba in har xai bar ‘yar sa
ta cikin sa a wulakance ya tallafi dan wani. In har iyayena basu shaku da ni ba to
ina xansa raina, ya kwatanta wannan abunda suke yi da suna ADON DAWA wato
gida bai wadata ba an wadata waje ma’ana ya wulakanta ‘yarsa ya tallafi bare.
Alh Adnan ya dauke ni ya rungume ni ya shiga da ni cikin falonsa ya dauki
bargonsa ya lullube ni yayin daya kunna min room heater jin dumi ta lantarki. Yana
lallashi na, ya bani biskit da alewa, har said a ya tabbatar hantsi yayi, sanyin safiya
ya lafa sannan y ace in je gida ayi min wanka a saka min kayan sanyi. Haka shima
mushkur yake samun wannan gata daga wajen mahaifana har goyon sa mama na
keyi amma ni ban isa matsowa kusa da ita ba.
Dan haka na kasance ako da yaushe ina hanyar bangaren daddyn mushkur. Ina
tashi daga barci wani lokacin ko karyawa bana yi sai in yi wuf nagudu wajensa, sai
dai idan ban ci sa’a ba nayi karo da maman mushkur sai ta kora ni gida, idan kuwa
tana kicin ko ban daki tuni na isa gare shi a falonsa ko akan gadonsa, yana gani na
sai ya rungume ni ko daga ni sama cimak, ya wujijjiga ni in yi ta dariya.
Musamman saboda ni yake ajiye katan katan din alewa da biskit da kananan
kwalayen lemuna. Ko da yaushe ka ganni ina ciye ciye, baya ga karatun boko dana
arabiya da yake koya min. ya na sona saboda ina son karatu, kuma ina son in
koya.
Ko da yaushe ina tambayarsa abun da ban gane ba haka duk abun daya koya min
duk daren dadewa ya tambaye ni sai na fada masa bana mantawa, in da ya kara
sona kenan.
Sabanin dansa wanda ya tsani karatu don haka ma basa shiri da uban. Gashi ina
da tsananin wayo kamar ba ‘yar fari ba, ga ladabi da biyayya, na iya hira tatsuniya
kala-kala da labarum nake bashi yayi ta dariya ya na tuntsurewa da dariya tamkar
yana hira a cikin abokansa.
Amma fa bana labarin da kowa saishi kadai, idan baya nan sai ka rantse ni doluwa
ce don bana Magana, sai kallo da ido a gidanmu saboda bana hira da iyayena. Don
haka duk sanda daddy yayi tafiya kwana biyu sai kowa ya gane bana jin dadin
rayuwata. Jikina sai yayi sanyi, in kaura bakin get ina duban hanya musamman
idan na ji karar mota sai in xankada da gudu in leka, idan naga bashi ba ne sai
raina ya baci ko kuma in fashe da kuka. Idan kuwa na ci sa’a shi din ne sai in yi ta
tsalle da ihu don murna yayin da nake fara xaxxago masa labaru iri-iri dana tattara
ina jira ya xo in fada masa.”
Kaltum tayi shiru tana matse hawaye, yayin da madina ta tsura mata ido tana yi
mata kallon tausayi.
Madina ta nisa tace “ikon Allah idan da ranka babu abunda baxa ka jiba. yaya kuka
kasance? ”
Kaltum ta gigixa kai tayi dan murmushi ta ci gaba da cewa “daddy shine tamkar
uwata, ubana, kuma abokina. Shi kadai yake goge min hawaye a idona saboda a
kasance koda yaushe ina cikin kuka a sanadiyar kyarar da mahaifana da kuma
mamar mushkur ke yi min, tatsane ni saboda taga mijinta yana tarairayarta fiye da
dansu na cikinsu.”
Madina ta girgixa kanta t ace “Allah sarki duniya, abun al’ajabi baya karewa ban
tabajin irin wannan kauyenci ba. Daga kanki ba’a kara haihuwa ba a gidan ku?
Mushkur ma ba’a hqifa masa kanne ba? ”
Kaltum tace “an haifawa mushkur kanne biyu amma dukkansu ba’a haifesu da rai
ba, saura kiris mamarsa ta rasa ranta a garin haihuwarsu. Saboda duk a juye ake
fitar mata dasu ta hanyar tiyata ma’ana kan jaririn ne suke komawa kirjinta,
kafafuwan a kasa sai anyi tiyata ake fitar mata kuma a mace don haka nema aka
juyar da mahaifarta baxata sake haihuwa ba. Ni kuwa mahaifiyata ta haifi namiji
mai bina ya rasu bayan an yi suna, sai ta dade bata haihu ba sai daga baya ne
haihuwar ta bude, kusan duk shekara sai ta haihu, a yanxu haka kannena bakwai
na baro mata da maxa.”
Madina t ace “suma kannen naki suna jin kunyarsu basa kula su kamar yadda suke
yi miki!” kaltum ta girgixa kai tace “iyayena suna son su, suna wasa dasu, suna
hira dasu ba kamar yadda suke yi min ba har tsayawa nake ina kallonsu ina
mamakin ashe mama da baba sun iya yiwa da wasa da lallashi.
Duk wani abu da ake bukata na makaranta sai na jira daddy ya xo sannan in fada
masa, ya bani in kai makaranta idan kuwa baya gari ko baya kasar sai dai idan
kashe ni xa’a yi a makaranta don duka amma babu wanda nake iya tara in fadawa
sai daddy.
Ina shekara takwas nagama nursery har na shiga primary, ina primary 3 a lokacin
ne karshen karatuna ya xo.”
“kamar yaya karshen karatunki ya xo? ”
madina ta tambaya cike da damuwa.
Kaltum t ace “eh, a lokacin ne goggo fattu ta aiko tana son ganin mahaifina, yana
rawar jiki ya tafi kiranta a can garin mu xangon daura. Ta sanar masa abun da take
bukata daga gare shi, gashi baya iya yi mata musu. Nan danan ya amsa mata ba
tare da yayi kokonto ba saboda tsoro.”
Madina ta gyara xama t ace “me take bukata a gare shi!”
Kaltum ta cije baki tayi murmushin karfin hali t ace “ce masa tayi ya amince ta
sayar da gadonsa da mahaifinsa ya bar masa sannan da tabkekiyar gonarsa dake
garin sandamu, wacce mahaifiyarsa ta mutu ta bar masa, sannan da dinbin
awakinsa xata biya kudin jirgi ni da ita mu tafi makka neman kudi. Idan muka je xa
mu samo dukiya mai yawa , sai ta biya shi linkin ba linkin in kudin gonarsa.”
Madina tace “ya yarda a cire ki daga makaranta ku tafi maka? ”
kaltum t ace “a take ya yarda, haka mahaifiyata ma bata hana ba a sanda ya
sanar mata. Ko da wasa babu wanda ya fada min shirye-shiryensu, ni dai nasan
ankai ni gidan daukar hoto an yi min kananan hotuna, goggo fattu ta xo ta kwana
biyu a gidan mu, sai kuma ranar da naga mahaifiyata ta xuba min kayana a dan
buhu, goggo fattu tace in taho mu tafi.”
Madina tace “daddy ya sani bai hana a tafi da ke ba? ”
Kaltum ta girgixa kai tace ‘sai da suka ga daddy baya na sannan suka tarki tafiyar,
koda wasu basu shawarce shi ba, matarsa ma bata sani ba.
Na tsinci kai na a cikin jirgi, sannan na tsinci kai na a cikin birnin makka.
Madina t ace ‘ki ce kin taba xuwa makka ba wannan ne xuwanki na farko ba? ”
Kaltum t ace”na dade a makka a can na koyi larabci, yanxu haka lungu-lungu da
sako-sako na sani a cikin garin makka, haka da ace na samu xuwa xaki yi mamakin
irin mutanen da xa ki ga sun sanni duk da na girma nasan xasu shaida ni saboda
kammanina basu canxa ba.”
Madina tace”yaya xamanku da goggo fattu ya kasance a maka?
Amma dai bata wahalar dake ba tunda kin girma ba kamar sanda ta yeye ki ba, ga
ku kuma a kasa mai tsarki, gashi komai a wadace ba’a wahalar abinci”
Kaltum tayi jugum can ta nisa t ace “uhum wahala ma daya kenan, ai ba xai yiwu
in iya xayyana ta gaba daya ba saboda axabar tayi yawa.
Wahalar da na saha ina ‘yar jaririya ai karama ce saboda tsana bansan komai ba, a
wannan lokacin kuwa nasan “eh” nasan a’a, na san ace in yi abu in yi, ace in bari
in bari.
Da farko dai mun ci sa’a mun sami gidan haya a unguwar ‘yan kasa wato a
unguwar masfala, a gidan wata balarabiya mai suna hajiya isra, hajja isra ruwa
biyu ce mahaifiyarta baka, mahaifinta balaraben makka ne dan haka gadimiya ce.
Hajja isra tana da ‘ya daya mai suna ahlan. Ahlan sa’ata ce, mahaifin ahlan ya rasu
ya bar musu gida sama da kasa. Suna xaune a sama, mu kuma muna haya a kasa
mu kadai ne.
Hajja isra tana da kirki matuka,tana sona sosai musamman yadda taga mun shaku
da ‘yarta Ahlan, har ana cewa muna kama kasancewar Ahlan tayi kama da
mahaifiyarta ba suyi kama da larabawa ba sak nima kuma gani fara sol mai gashi
sai nake kama dasu. Ta kan yiwa goggo fattu wasa t ace “yadda fuskar nan taki
take baka kirin idan askarawa (yan sanda) suka ganki da kaltum ki ka ce jikarki ce
sai sun kama ki, suce karya ki ke ‘yar larabawa kika sato. Saboda baku yi kama ba
kwata-kwata, gara ki dinga saka nikaf da safar hannu da ta kafa idan xaku fita
tare.
In da xaki tabbatar hajja isra na sona sai ta siyawa ‘yarta ruguna ko sarka da
‘yankunne na gwal, biyu take saya iri daya ni da Ahlan musamman a lokacin
sallah. Haka abinci, komai ta dafa sai ta aiko min sai dai kash aiken baya xuwa
gare ni saboda goggo fattu karbewa take yi bata bani. Da takardar Ahlan ta ‘yan
kasa hajja isra ta saka ni a makarantarsu Ahlan, muke xuwa tare duk da ba’a koyar
da boko larabci xalla ake yi sai karatun qur’ani ta tahfix ce. Na koyi larabci, na koyi
karatun qur’ani sosai, nasan baki, hadisai da daman na haddace su kuma xan iya
fassarawa, haka fikihu, tafsir, sira da sauransu. Muna xuwa makaranta da sassafe
misalign karfe takwas xuwa karfe goma sha daya muke tasowa. Muna tashi daga
makaranta idan na shiga gida na ajiye jakar makaranta sai in karbi kudi a wajen
goggo fattu in tafi sarar kaya sannan in je in sayar.”
Madina tace “ban fahimce ki ba. Ke kadai din ne xaki iya xuwa ki sari kaya da
kanki? ”
Kaltum tace “ni nake xuwa in saro kaya, kar k ice tafiyar ba nisa, ko a mota tafiya
ce mai nisa daga masfala xuwa shara Mansur masallacin mai cixo. Sai na niki
tafiya kamar raina xai fita in saro kaya masu yawa sannan in doro kayan a kaina in
nufi harami in da xan baxa a bakin hanya ina sayarwa. Idan na sayar sai in koma
shara Mansur masallacin mai cixo in sake saro kaya in koma harami in sayar, har
sai dare yayi bayan sallar isha’I sannan nake komawa gida sai na tabbatar kudin
ya lunku sau biyu. Ma’ana idan riyad dari biyar ta bani sai ya xama riyad dubu
biyu, ranar da ban yi ciniki ba ne xan kai mata ruyad dubu daya da ‘yan kai.”....
.
Gida fa ya fara shiru, mai yasa aka rage

ADON DAWA 8
.
Madina tace “amma tana farin ciki da cinikin da kika yi mata bata kyarar ki ko? ”
Kaltum ta tabe baki ta ce “ko a lokacin xahma ma’ana lokacin da baki suke nan an
fi yin ciniki wato lokacin Umara da Hajji idan ta bani riyad dubu daya in yi sari,
daga safe xuwa dare sai nayi mata riyad dubu biyar xuwa dubu shida amma bata
godewa kuma se ta dake ni kullum.”
Madina tace “to cnikin nawa take so kiyi mata? ”
Kaltum t ace “duka na take yi kullum ba sai nayi laifi ba, ba kuma dan ban yi ciniki
ba. Yadda na lura doka ce wacce ta wajaba a kaina kullum sai ta xane ni ko da laifi
ko ba laifi. Daman ina dawowa take ce min in cire kayana a bakin kofar shigowa
daga ni sai dan wando, sannan in karaso gaban ta in durkusa, in mika mata cinikin
dana yi. Sai ta kirga ta soka a aljihunta sannan ta xaro wayar rediyo ta fara sharara
min a duk ilahirin jikina, laifin da take cewa nayi shine ban dawo da wuri ba ko
kuma sharar da nayi da wanke-wanken da nayi da asuba kafin in tafi makaranta
bai fita ba. In yi ta kuka da ihu ina mata magiya tayi hakuri ba xan sake ba. Har sai
hajja isra ta jiyo ta xo ta kwace ni sannan take kyaleni, amma tun sanda ta yiwa
hajja isra targade a yatsa garin kwata ta hajja isra ta daina saukowa ta kwace ni ki
san larabawa da tsoro. Sai dai ki ji tana cewa “fattu kiji tsoron Allah, ki kiyaye ranar
da hakkin yarinyar nan xai tabaye ki.” Amma goggo fattu bata ji, gobe ma xatayi
min wanda yafi na yau.”
Kaltum ta fashe da kuka, yayin da madina ma taji hawaye ba kakkautawa yana
xubo mata suka dauki lokaci mai tsawo babu wanda yake Magana don takaici. Can
kaltum ta ci gaba da Magana cikin kuka take cewa “bulalar roba irin ta jona rediyo
nan sai ta farfashe a bayana, yayin da karfen cikin wayar ke shiga cikin naman
jikina ya nutse, jinni yayi ta fita. Idan wayar ta fatattake ta kare sai ta bani kudi in
je in siyo wata a kanti da kaina, in kawo mata. Idan itama ta kare sai ta sake
aikena in siyo wata.”
Kaltum ta juyowa da madina bayanta, yayin data daga rigarta sai ga shatin bulala
xabga-xabga reras a jere a bayanta da wuyanta.
Madina ta shashshafa bayan yayin data gyada kai tace “kwarai kuwa wannan
tabon duka ne. Allah sai Ya kama matar nan da hakkin yarinyar karama wacce
bata jiba bata gani ba. Ta rabo ki da iyayenki ta xo ta axabtar da ke.”
Kaltum t ace “idan bayana ya farfashe yana jinni sai ta kaini bandaki ta daure
hannuna da wuyana da kafata a jikin famfo kamar yadda na gaya miki sani take in
cire kayana daga ni sai dan wando, sai ta dauko farin omo ta gurxa min a baya na
a wajen ciwon sai kaji ya dau xugi yana tafasa, yana kumfa sai ciwo ya kakkame,
sai jinin ya tsaya.”
Madina tace “ta daure ki a bandaki fa kika ce, kamar wata dabba?
Ko dabbace xatayi mata haka? ”
Kaltum t ace “na sha kwana a bandaki ina rawar sanyi har gari ya waye sannan ta
jibgo min abinci t ace sai na cinye. Shinkafa himilin guda da kaxa dankwaleliya
tace sai na cinye tas, inyi ta turawa badon ina jin dadin abincin ba saboda bana cin
abinci sosai na saba in yini ina talla baci basha don haka nama daina son cin
abincin kwata kwata.
Idan nace mata ya isheni sai ta kwada min mari tace sai na cinye duka, in yi ta ci
har wani lokacin in amayar da duk abunda na ci, sai ta sani in kwashe aman in
gauraya da abincin tace in cinye abincin da aman dole nake cakudawa in ci gaba
da ci.”
Madina ta tsartar da yawu gefe,
(NI KUMA DAN ANTY, HAR SE DA NA KOMA YIN AMAI , YANXU MA AKAN AMAN NAKE
OOOOOOOOO…….)
Ta dau dogon salati. Ta ce “kaltum kin sha wuya, kai wannan abu da me yayi
kama?
Ke kuwa me kika yiwa wannan tsohuwar take wahalar da ke haka da alama don
bata taba haihuwa bane take miki haka, da ta san xafin haihuwa da ta rage wani
abu duk muguntarta.”
(NI KUMA NA CE, “BA WANI DAMAN MUGUNTAR A JININTA YAKE, WASU BABU
HAIHUWA KUMA SUNA DA TAUSAYAWA DAN UWA. ALLAH MA YA TSARE MU DA IRIN
WANNAN RASHIN IMANI. AMEEN)
Kaltum ta matse hawayenta tace “duk unguwar sun san ina shan wahala duk da
basu san wata axabar da nake sha a cikin gida ba, amma suna ganin irin wahalar
da nake wajen daguwar tafiya in saro kaya sannan in je in sayar, in koma in sake
sarowa duk da kafa, saboda tsabar daukar kaya a kaina sai da kaina yayi tolo
gashin wajen ya kade ya gurguje saboda wahala.
Akwai wani yaro saurayi a makwabtanmu mai suna Anwar. Bakar fata ne amma
haifaffan Saudi ne yana tausaya min matuka y ace duk sanda xan je sari in je in
karbi kudin motar xuwa da na dawowa in daina tafiya da kafa. Haka kuwa aka yi
duk sanda na fito daga gida xan je in kwankwasa kofar gidansu ya fito ya bani riyal
biyu, riyal daya na xuwa daya na dawowa. Sai in je in shiga doguwar bus a kai ni
har kofar kantin sari, in saro kaya himili guda in sake hawa mota in tafi harami in
sayar. Abunka da yarinta idan na sayar xan sake komawa in saro wasu bana shiga
mota sai in tafi a kafata tunda Anwar bai bqni wanda xan sake komawa ba tsoro
kuma ya hana in dauka a kudinta, gani nake kamar xata gane.
Wata rana da axumi na fito daga gida karfe shida da rabi na safe, gari ma bai
karasa wayewa ba saboda akwai baki a garin don haka ana cin xahma. Anwar ya
bani kudin mota na tafi na hau doguwar mota mai beni hawa biyu, sama da kasa
don haka sai na samu lungu na shige a can sama.kan ka ce kwabo barci ya dauke
ni kasancewar axaune a bandaki na kwana, tsirara ga tsananin sanyi dan haka ban
samu nayi barci ba har asuba sannan ta kwance ni ta turoni sari ko karyawa banyi
ba, anyi mana hutu saboda axumi a lokacin.
Ina wannan barci har aka wuce dani inda xan sauka ban sani ba. Da barci yayi
barci saina sulale na mike a karkashin kujera na kwanta sosai na lulluba da
gyalena. Ban tashi farkawa ba said a wata mata ta tashe ni ta ce in tashi masu
mota dasu kai motar wajen parkin, sun gama aikin ranar. Sannan nayi firgigit na
biyo bayanta muka sakko tare da ita. Ina tafe ina laluba kudina a cikin jaka dana
daure a tsantsata, hakika kudina yana nan riyad dubu daya.
Ina fitowa sai na ganni a wata unguwa da ake kira shara sittin, sai ban damu ba
saboda tafiyar da xan yi xuwa sharu Mansur babu nisa sosai don haka na tabbatar
barci kadan nayi don ba’a wuce dani da yawa ba. Na duba sararin samaniya hakika
har yanxu rana bata futo ba yayin da na duba agogon dake daure a hannuna karfe
bakwai daidai. Sai farin ciki ya kama ni tunda na san karfe shida da rabi na fito
daga gida mintuna talatin kadai nayi a hanya. Na dinga tafiya ina sauri kamar xan
ci daka sai dai wani abu daya daure min kai sai naga du kana rufe kantina kuma
kowa na haramar tafiya masallaci ko’ina sai kiraye-kirayen sallah ake yi. Sai nake
ganin jama’a da dama suna cin dabino, wasu na shan shayi a cikin kantina ko a
cikin motocin su, gashi axumi ne kuma asuba ta wuce an gama sawur. Na tambayi
xuciyata me yasa suke karya axumin su?
Tambayoyi kala-kala na dinga yiwa kaina har na isa kantin sari. Mutum daya na
iske yana alwala a bakin kantin. Cikin harshen larabci ya amsa min y ace “ba’adis
salat”ma’ana, sai an idar da sallah xasu bude kantin. Na dube shi duba na rashin
fahimta n ace “ba kuyi sallar asuba da wuri ba ne? ”
ya yi dariya yace sallar magariba xa mu yi ba dai asuba ba. Ko dan bakya axumi
shi yasa baki damu a sha ruwa da wuri ba ko?
Sai gabana ya yanke ya fadi, nan da nan na rikice. Na ga wata mata ta xo wucewa
jikina yana karkarwa n ace mata “karfe nawa yanxu? ” ta duba agogon dake daure
a hannunta t ace “karfe bakwai.” Na tambaye ta “bakwai na safe ko bakwai na
dare? ” itama sai tayi dariya sannan t ace “bakwai na dare ne. ba ki ga ana shan
ruwa ba? ”
Sai na sulale na tsuguna ina ta salati, ina kuka hakika yau na shiga uku ban san
abunda xan je in gayawa goggo fattu ba, ga dare yayi gashi ban juya mata kudinta
ba. Ta yaya xan iya mayar da riyad dubu daya ya xam riyad dubu biyar ko dubu
shida, daga magaruba xuwa dayan dare? Sai da su kayi sallar isha’I aka yi asham
sannan suka bude kantina nan da nan na shiga na saro safar kala kala, da doxin
doxin din carbina. Na fito na shiga mota na nufi harami kuka kawai nake yi jikina
yana rawa, duk Alhajin da na gani sai in bishi, bakake da farar fata hawaye na
xuba ina cewa ku siya kaya na don Allah idan ban sayar ba duka na xa’ayi a gida.
Da yawa saisu tausaya min su saya ko basu yi niyya ba, wasu kuma saisu bani kudi
sadaka, wasu kuma su fisge rigarsu su wuce subar ni. Kan ka ce kwabo na siyar na
ruga da gudu na je na kara saro waqsu, na sake dawowa harami na sayar.
Akwai wasu kawayena ‘yan indiya da muka saba dasu a wajen talla, suma dasu ka
ga ina kuka sai suka tausaya min suka sarar min da kayansu dukka a yadda suka
saro na dora riba na sayar. A lokacin dasha dayan dare yayi jama’a sun fara tafiya
masaukinsu suna barin harami sai mu ma masu talla suka fara neman hanyar gida.
Ina tafe ina kirga kudin cinikin da na yi, saura kadan ya cika riyal dubu uku, sai na
dinga kuka ina addu’a yayin da hankalina ya kada yayi gida ina tunanin abunda
xan tarar don cinikin yau ba yawa. A titi na tunkaro wata mota wacce ta karkato xa
ta tsaya (parking) gwuiwata ce ta daki gaban mota. Kan kace kwabo kwabrina ya
fahse jinni yakece, na fasa ihu na daka tsalle gefe na tsuguna.
Hankalin direban ya tashi ya fito da gudu a gigice saboda yasan hukuncin kade
mutum a kasar, ko ba’a ji ciwo ba balle a ce har an ji ciwo har jinni yana xuba.
Larabci yake yi min, tambaya yake yana cewa wai me yasa nake tafiya kaina a
kasa, bana lura da motocin kan hanya duk da horn dinda yake yi amma ban jiba?
gashi nan na ja ya buge ni xan janyo masa wahala. Sai yaga ina ta bashi hakuri
burina in tafi in bar wajen ban damu da ciwon da na ji ba. ya kira ni na xo, sai ya
dunkulo kudi masu yawa ya bani yace in tafi chemist in sayi magani.
Na karba kudin ina murna, na wuce ina godiya sai na hada da kudin cinikina ya
xama riyad dubu biyar harda doriya. Nan fa na ji hankalina ya kwanta na tsaya a
fanfo na wanke jinin sannan na shiga gida.

Please Login or Register in order to submit comment