Reading adon dawa Chapter 31 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gadi,
kaltum ta wuce kai tsaye cikin gidan alh Adnan a babban falo ta tsaya tana rada sallah
ma can yaji ya amsa bayan yan mintina ya fito daga daki a alama a kwance yake yana
hutawa, dubanta yakeyi cike da
mamaki domin ya ganta da gyale harda jaka
arataye ya tambaya lafiya ina zakije da tsakar rana?
ta durkusa agabanshi ta sunkuyar dakai kasa tana magana cikin ladabi daddy Madina
zan raka wajen 'yayanta da Abba tace ko minti daya bazata kara ba don hankalinta yayi
gaba.
alh Adnan yayi daria yace daman tana son Abba da yaranta ta tsallake su tabarsu dakyar
ta yarda ta dawo?
ke ma daman kina son Adnan kika ki biyo sa'adu a dadin rai kikace dan ADON DAWA zaki
bi?
sai kaltum tayi sauri dukar dakai kasa har ya gama bayanansa bata kara hada ido dashi
ba daga karshe yace kije ki duba danladi yakaiku a motarki ya jira ki ku dawo tare kafin
la'asar, kaltum ta amsa da to mungode ta mike ta fice tabar alh Adnan da tunani iri iri,
kaltum da Madina a cikin mota gidan baya babu wacce take magana a cikinsu
kowaccensu na tunani yadda za a yi arangama da juna har sun kama hanyar yankaba
Madina tace kada muje gidan general tukur gara ku kaini gidan sumayyah tukur a koroa
road saitace danladi koroa road zamuje ba yankaba dan haka saiya juya kan mota ya
doshi can.
Madina tana nunamishi hanya har bakin get din gidan dr sumayyah anci sa a kuwa bata
manta gidanba duk a akwai yan canje canje a unguwar ba ta manta lambar gidan ba da
alama dai tana ciki saboda motoci har guda ukune a tsaye a farfagiyar gidan har kaltum
ta fito daga mota madina na zaune cikin mota bata da niyyar fito wa, lafiya kika ki
fitowa?
kaltum ta tambayi Madina.
madina ta girgiza kai tace saida nazo kofar gidannaji bazan iya shiga ba saina tuna
marin da sumayyah tayimin da bakaken maganganun da ta fada min gara mu tafi basai
mun shiga ba,
Kaltum sai kawai ta tura get ta shiga cikin farfajiyar gidan da sauri bata kula da kwalla
kira da Madina take mata ba haka bata saurari dogayen horn dinda danladi ke matsa
mata ba burinta kawai ta ganta a cikin gida, dai dai falon shiga taci karo da sumayyah da
kaninta Abba suna fitowa da alama tafiya zaiyi don yana rike da makullin motarsa a
hannunsa sukayi kicibus suka tsaya suna kallon juna aka rasa wanda zaiyi magana
wakike nema yammata?
sumayyah ta tambayi kaltum, Abba ya
dubi sumayyah yace baki ganeta bane?
kaltum ce wacce ta kawo mana labarin inda Madina take,
sumayyah ta rike baki tace na tuna kaltum lafiya?
kaltum tayi murmushi tace lfy klau,
sumayyah tace ya ake ciki da zancen nemo Madina?
babanki yayi masa alkawari zai kawo masa Madina Abba ya damu yanzu haka zance ya
zo muka yi ina tabashi hakuri kalli idanuwansa kiga yadda sukayi ja kwana yake bai yi
bacci ba ku taimakemu...
Abba cikin gigita yace kaltum kada fa kice anje nemanta ba asameta ba?
kaltum ta girgiza kai tace kafin ince muku wani abu kuzo bakin get kuga wani abu ta
juya da sauri ta fara tafiya yayinda cike da fargaba suke biye da ita a baya babu wanda a
cikinsu yakawo abunda take shirin nuna musu ko a mafarki koda wasa basu taba zaton
zasuga abunda ta nuna musu ba, kwatsam saiga Madina a zaune acikin moto tamkar a
maparki bakin kowannensu ya kasa rufuwa,
sumayyah tukur ta kwalla kara ta fada cikin daga murya lah Madina kece?
AlhamduLillah Allah nagode maKa, suka rugo da sauri suka rungume juna yayinda
hawayen farin cike yake zubowa daga idanuwanta su dukka hudu sai aka hau kallon
kallo tsakanin
Abba da Madina saboda kallonta Abba har karkace kai yakeyi batareda ya iya mata
magana ba,
(Sadin maa nace, "Allah Sarki So, Boss se yaya? ")
ta fashe da kuka tace Abba Abba kaine wannan ashe zansake ganinka a rayuwata?
saiya share hawaye yace Madina mai yasa kika tafi kika barmu?
meyasa baki zauna ba kikaje kika jefa rayuwarki cikin wahala?
sumayyah taja hannun Madina ciki da sauri
yayinda Abba da kaltum ke biye dasu a baya har babban falo suka zazzauna sumayyah
ta jawo wayarta ta bugawa mummy hafsat tana dauka sumayyah ta fashe da kuka tace
mummy ki taya mu murna ga Madina a gida na.
mummy hafsat ta dau dogon salati ta karasa da hamdala sannan tace abawa Madina kan
wayan cikin farin ciki da fara a madina take gaishe da mummy hafsat sai data ji
muryarta sannan ta yarda Madina ce,
ke kuwa madina me yayi zafi haka dazaki tafi kibarmu haba?
madina idan baki zauna danmuba ai saiki zauna don Abba mai sonki da kananan
'yayanki.
Sai hawaye ya surnano daga idanuwan madina tayi shiru kanta a sunkuye akasa batasan
amsar da zata bata ba.
Abba ne ya taso da sauri ya mika mata hankici fari mai kamshi ya fada cikin lallausar
murya madina goge hawayenki ki daina kuka
(WAI INA BOSS NE?)
Ta dago ido ta dubeshi saita yimasa lallausan murmushi ta gyada kai alamar naji sannan
ta karba a nutse take sharce hawayen,
ya koma kujerar da yake zaune a saitinta ya kura mata ido ko kiftawa bayayi fuskarsa
cikeda annuri kamar wanda aka yiwa albishir da gidan aljannah,
kaltum kuwa Abba kadai take kallo
tana mamakin irin wannan so dayakeyi wa madina duk da lalacewarda tayi,
SADIN MAA NA CE, AI SO BB WASA, YADDA NA KAMU DA SON JAMA'AR GIDANNAN
tayi baki ta rame ba kamar yadda take da kyau kamar da ba saita dinga ayyanawa a
ranta dama itama a nemo mata mambelanta
(yess bosss)
kamar yadda aka nemowa Abba madinarsa,
madina ta mikawa sumayyah waya tace mummy tace yanzu zatazo nan gidan aida ta
bari naje na gaishesu ita da daddy,
dr sumayyah tace ai daddy baya kasar kinsan mummy bazata iya hakuri ba ta zo ta
ganki ba yanzu saboda ta damu da rashinki kullum tazo cin abinci sai tace Allah sarki
Madina ce mai dafa min abinci kala kala musamman idan ta tuna sakwararki wani lokaci
sai dai kaga tana hawaye.
Madina ta girgiza kai tace rayuwa kenan yaya za ayi da kaddara idan Allah Ya kaddarawa
bawanSa bai isa ya tsalleke ba cikin ikon Sa da yardarSa Ya dawo dani gida na ganku
lafiya Shine abun godia.
daddadar muryarta da lafazanta masu ma'ana sai suka ratsa jijiyoyin jikinsa ya lumshe
ido don dadi ya bude ido ya dubeta yaji kamar ya hadiyeta ya fada aransa inason
madina Allah Ka yarje min in aureta Ka bani ikon riketa amana, (SADIN MAA NA CE,
AMEEN ABBA)
sumayyah Tukur ta harareshi tace tashi ka tafi wancan falo ka zauna kabamu waje mu
tattauna da aminiyata kazo ka tsura mana ido,
Abba yayi dariya yace sister sumayyah keya kamata kitashi ki bamu waje mu tattauna,
sumayyah tace indai Madina ce sai ka gaji da ganinta karewa ma gidanka za a kaita kuje
can ku karata, sai Abba yaji gabansa ya fadi kar Madina ta fada abunda zai daga masa
hankali sai yaga ko kusa bata bijireba saima murmushi datayi kawai tace Allah ne mai
yadda Ya so da bayinSa Allah Ya zaba mana mafi alkhairi.
sai hira sumayyah takewaya Madina tana fada mata irin mummunan hali da suka shiga a
sana diyyar rashinta sannan sunyi nadama
da sukaji gaskiyar al amari cewar ba laifinta bane, ta kara da cewa hudubar shaidan ne
ta shigesu suka manta da kaddara har suka zargeta kuma harda zugar makiya wadanda
daman basa so su gansu tare, suka zuga su kuma suka tunzura suka yi mata abunda
sukayi mata, hawaye ne kawai ke zubowa daga idanuwan Madina shi kuwa Abba babu
abunda yafi daga masa hankali shi ne idan yaga tana kuka yace da 'yayarsa 6star
sumayyah don Allah ki bar zancen nan kina sata kukafa... shigowar mummy hafsat da '
yayan madina shi ya katse hirar da suke yi murna da hayaniya ta gauraye falon, Madina
ta tashi da sauri ta rumgumi mummy hafsat sannan ta rungumi 'ya yanta su dukka ukun
suka kankame ta suna kuka don farin ciki da kyar sumayyah ta bambare su daga jikin
uwarsu suka zauna,
mummy hafsat ta shiga lallashinsu domin har yanzu basu tsagaita da kukanba saiga
Tasi'u ya shigo wur janjan yana fadin ina matata Madinar take?
fuskar Abba zaka kalla kaga yadda ya bata rai yana hararar Tasi'u yayinda kishi ya tashi,
(ta yadda nima tawa kishin ya tashi sabida jama'ar gidannan me albarka) Sady.
kayi mata sannu da zuwa ka tafi mana saboda nan gidan surakai ne ba gidanmu bane
bai kamata ma aringa irin wadannan maganganuba,
Madina ta dago ta dubi Tasi'u sai taji ranta ya baci yana tsaye akanta yana ta surutai
barkatai kamar tababbe itadai tunda ta gaisheshi bata kara bashi amsa ba,
yace Madina ke kuwa meyasa zaki zauna a can?
kuskurene mukayi kuma kowa ya gane Madina ki rike amana ki tuna nine mutum na
farko da kika fara sani a arewa, nine mijinki uban 'yayanki na girmeki nafiki hankali nafiki
sanin dunia haka kuwa ya kamata miji ya kasance tsakanin sa da matar sa,
Abba yasan habaici Tasi'u yake masa don haka saiya fusata yayi magana cikin fushi yace
ina ganin bai kamata a fara yiwa madina irin wadannan zantuttukaba barkatai don yanzu
ta zo ko hutawa batayi ba ita ya dace ta zabi wanda zata zauna dashi basai anzabar
mata ba, saboda tafi kowa sanin abunda yafi dacewa da ita a rayuwarta, tasan halin
wahala da takaicin data dandana a baya, zata yi hasashe wacce irin rayuwa za tayi nan
gaba.
Tasi'u ya fusata ya juya ya dubi mummy hafsat yace mummy kinajin yaron nan ko idan
manya suna magana saiya dinga tsoma baki alhali niban ambaci sunansa ba.
mummy hafsat tace tashi ka koma wancan falon karka sake magana, Abba ya mike ya
fice daga gidan ma gaba daya,
Tasi'u dai ya lankwashe kafa yana ta magiya Madina ta dawo gidansa,
takaici yafi damun 'yayansu ma basu madinarba ma,
Abdul Malik ya fusata yace haba baba ka bari ta huta mana kafin ka sako wata magana a
ina aka taba yin saki uku kuma a koma a zauna?
Tasi'u yace ai nasan tayi aure a sudan ko batayi ba ma zata iyadawowa ta tausayamin
ina son ta da ba tanan a gidana sai duk ya mutu,
Madina ta girgiza kai tace Allah Ya saukake ni banyi aure acan ba,
sumayyah tace kinga babu zancen kome tunda saki ukune kuma batayi wani aurenba,
kema bayan kanin naki zakibi?
sumayyah haka zakimim?
Tasi'u ya pada ransa a bace,
mummy hafsat tace Tasi'u don Allah kabar
maganan a nan saikun hadu daga kai sai ita,
Madina duk hukuncinda ta yanke shikenan ai wannan ba maganar da za ayita bane
agaban yara ba, sannan matar nan yanzu tazo ko wartsake gajiya batayi ba.
Tasi'u ya gyada kai yace hakane gaskiyane ai
shiyasa ake neman shawarar manya toni zan tafi Abdul Malik kuzo mutafi,
Abdul Malik ya girgiza kai yace ba yanzu zamu tafi ba, tare da mummy hafsat mu kazo
daman,
Tasi'u yayi kasake don shima bayason tafiyan bai gaji da kallon abar kaunar sa madina
ba duk da hautsinewar datayi batada
kyauwun nan nata irin na da amma duk da haka tafi sauran matansa tsari da kyan gani,
yayi ajiyar zuciya yace to banyarda wani acikinku ya kwana ba ina gida ina jiranku kafin
magruba mekukeci na baka na zuba kuda uwarku zata dawo gidanku kacokan ma ku
kwana a dakin ta,
kowa ya zuba masa ido yana dubansa kamar wanda yake kallon tababbe a talabijan
babu wanda ya iya magana har ya fice a farfajiyar gidan suka sake jiyo muryarsa
yanayiwa Abba hayaniya duk dai akan Madina Allah cikin ikonSa sai Abba yaki kulashi ko
kallo ma bai isheshiba yayi surutunsa ya gaji ya tafi.
Madina ta juya ta dubi 'yayanta tace me yake damun mahaifinku ne?
ya gamu da matsalar kwakwalwa ne bayan
tafiya ta?
Abdul Malik yayi dariya yace lafiyarsa Kalau mama,
madina ta dubi sumayya tace anya alamaran
Tasi'u akwai hankali a ciki kuwa?
sumayyah ta kwashe da dariya tace zafin so ne da tsananin kishi yake damunsa.
mummy hafsat ta tabe baki tace nadama ce hakkin zalunci suke tambayarsa ni wallahi
har alamarin nan ya fara bani tsoro tun kafin ki dawo yake neman tashin hankalin balle
yanzu da kika dawo bamu san wahalar da zai ballo mana ba.
Madina tayi tagumi tace Allah ma zai yayyafa wa abun ruwan sanyi Allah Ya sa ya gane
gaskiya daga nan suka bar hirar Tasi'u,
Abba ya shigo aka dinga hira wasa da dariya yayinda sumayyah da masu aikinta suke
can akicin suna ta hidimar dafa abinci iri iri suna fitowa da shi, ana jerawa a gabansu
madina..
Jama'a gaskiya kishi na nima ya motsa PA, har yana neman sanya min hawan ruwa,
kowa kullum se Dan Anty kawai ake ta ambato domin an pi son sa an pipita sa a kaina
bayan nima ina yin ku kuma kun sani..
ADON DAWA 44
.
TRUE LIFE STORY
.
sumayyah ta kwashe da dariya tace zafin so ne da tsananin kishi yake damunsa.
mummy hafsat ta tabe baki tace nadama ce hakkin zalunci suke tambayarsa ni wallahi
har alamarin nan ya fara bani tsoro tun kafin ki dawo yake neman tashin hankalin balle
yanzu da kika dawo bamu san wahalar da zai ballo mana ba.
Madina tayi tagumi tace Allah ma zai yayyafa wa abun ruwan sanyi Allah Ya sa ya gane
gaskiya daga nan suka bar hirar Tasi'u,
Abba ya shigo aka dinga hira wasa da dariya yayinda sumayyah da masu aikinta suke
can akicin suna ta hidimar dafa abinci iri iri suna fitowa dashi ana jerawa a gabansu
Madina
kaltum ta sami hira da ciye ciye saita manta da direba a waje ta kuma manta da
gargadinda alh adnan yayi mata kada ta dade ta dawo da wuri,
bayan sunyi sallar magruba ne kaltum ta zaro
wayarta acikin jakarta saita ga 10 missed calls din danladi 5 missed din alh Adnan nan
da nan sai hankalinta ya tashi sukaga tahau rawar jiki har ta kasa yafa gyalenta dai dai,
kaltum lafiya saurin mekikeyi haka?
madina ta tambayeta.
na manta a gida ance kar in dade wayata a jaka bansan suna ta kirana ba shine nakeso
naje gida da wuri, a tsaitsaye tayi masu sallama ta suri takalminta ta tafi bata ma tsaya
ta saurari rakiyar madina keyi mata da rokon da takemata ta dawo gobe ba burinta
kawai ta ganta a cikin mota ta ganta acikin gida gaban alh adnan sannan tayi shirin
amsa dogayen tambayoyinsa,
danladi ya dubeta da alama ransa ya baci ya fisge mota batareda wani daga cikinsu yayi
magana ba saida suka yi nisa kaltum tace danladi kayi hakuri na barka kanta jira bansan
lokaci ya ja ba anata hira wayata a jaka ban ji kiranku ba.
dan ladi yace ai bani ne abun ji ba daddy ne kinga irin fadan da yake yimin a waya wai
me yasa za mu dade haka nace kina cikin gidan yace in aika a kira ki narasa dan aike
kuma nayi kiran wayar ki ba amsa niyanzu nasan duk fadan akaina zai kare,
sai kaltum ta dafe kirji tayi shiru tana karanto duk addu ar data gifto bakinta suna isa
bakin get taji wata jijiya ta harba acikin kirjinta tamkar zuciyarta ce ta tsinke don fargaba
daga yadda saleh ya bude get a fusace tasan yau ba lafiya saita fara kuka, suna tsayawa
da mota saita fito a hankali tana mai tafiya a hankali tamkar wacce kwai ya fashewa
mata a ciki,
alh adnan ta tsinkayo a tsaye akan baranda ko zama ya gagare shi da alama fuskar nan
ba annuri daga ita har danladi sai sunkuye sunkuye suke yi da kai kasa aka rasa wanda
zai fara wucewa gaba yaje yayi bayani.
tsawa ya daka musu saisu dukka suka hargitse fargabar ta karu yace bazaku karaso
bane ina tsaye ina jiranku sai wata sanda kuke yi kamar wasu hawainiya?
nan da nan suka karaso gabansa suka durkusa suna jiran hukuncin za a yanke musu,
hakika danladi yayi gaskiya fadan dukka akansa ya kare an gargadeshi da kada yasake
kaita anguwa da zasu kai magruba, kalma daya ya jefawa kaltum ita ya sallameta ta
fada da sauri yace daga yau kada ki sake cemin zakije wajen Madina tunda nan ba a
sudan kukeba dazaku kwana kuna hira,
ta shiga gida ta iske fadan sofi da saleh sunatayi mata fada ba kakkautawa sun nuna
mata cewar da ta bata wa alh adnan rai gara ta bata musu rai, ta shiga daki a sanyaye
ta iske an bawa goggo abinci da magani hartayi bacci sai dai tulin zannuwan kayantar da
aka cire wa goggon yana gefe yana jiranta ta dawo ta wanke, saboda rashin kuzari a
jikinta da tsoron fita tsakar gida don kada taci karo da mahaifinta ko alh adnan suyi mata
wani fadan saita shige lungu ta kishingide tayi lamo tana tunani taji duk kasar ya isheta
tamkar ta koma bur sudan wajen yan ADON DAWA ta zauna tareda mambela kamar
yadda Madina ta dawo wajen abbanta,
saida ta tabbatar dare ya tsala sha biyu harda rabi kowa yayi barci sannan ta fito ta hau
wanki ta gama tsaf ta shanya sannan ta dauro alwala tazo tayi sallar isha i ta dinga jero
nafilfili tana ta addu ar Allah Ya zaba mata abun da yafi alkhairi a rayuwarta,.
Madina ta kasance agidan aminiyarta sumayyah tukur dakinta da bandakinta a ciki aka
mallaka mata ita kadai cike da kayan more rayuwa babu abunda ta nema ta rasa ga 'ya
yanta kusan kullum sai sun zo sun ganta ita ma ta gansu tayi hira dasu taji dadi,
sumayyah tukur a matsayinta na wayayyayi cikekkiyar yar boko tana matukar kokari
wajen wayarwa da Madina kai domin duhun kai ne ya same ta a sudan bata san
abubuwan da ake yayi ba yanzu da yadda ake tsara kwalliya, tafi gane ta saka atamfa ta
kunshe kai da hijabi ko acikin dakine.

ADON DAWA 45
.
TRUE LIFE STORY
.
Madina ta kasance agidan aminiyarta sumayyah tukur dakinta da bandakinta a ciki aka
mallaka mata ita kadai cike da kayan more rayuwa babu abunda ta nema ta rasa ga 'ya
yanta kusan kullum sai sun zo sun ganta ita ma ta gansu tayi hira dasu taji dadi,
sumayyah tukur a matsayinta na wayayyayi cikekkiyar yar boko tana matukar kokari
wajen wayarwa da Madina kai domin duhun kai ne ya same ta a sudan bata san
abubuwan da ake yayi ba yanzu da yadda ake tsara kwalliya, tafi gane ta saka atamfa ta
kunshe kai da hijabi ko acikin dakine.
sumayyah kuwa tace bata isa ba dole saita zama yar gayu kamar yadda yammata suke
gayu saboda saurayi zata aura, tun Madina na cijewa tana kin saka matsattsun dinkunan
leshina da material har ta fara yadda tana sakawa,
sumayyah ta hana kitso saidai ta kai ta saloon a gyara gashin kafin watanni biyu sun cika
Madina ta waye tamkar ba itaba, haka Abba yafi kowa jin dadi da ganin wannan sauyi
yana kuma godiya wa yayarsa sumayyah da irin wannan taimako da tayi masa duk da
yawanci kudi yake bawa sumayyah tayi mata duk hidimamomin nan ko madinar ma bata
sani ba, kankace kwabo rayuwa ta dawo mata sabuwa tar ta fara mance himilin bakin
cikin da ta shaka a baya, babu ranar da Abba baya zuwa wa Madina sai dai har yanzu
Madina bata bari hiran soyayyah ya shiga tsakanin su ba duk hirarda za a yi a gaban
sumayyah akeyi sai dai a tsakanin waya wato text masseges yana turo mata dadad'an
kalamai masu shiga zuci sai tayi murmushi ta lumshe ido, amsar da take bashi bata
wuce na gode,
godiyarda take mishi ta ishe shi farin ciki ko bata biyashi daddad'an kalamai ba ya lura
Madina ta fara sakin jiki dashi, ta nuna a fili karara tana son shi,
koda yaushe Madina tana damun Abba ya kira alh Adnan a tambaye shi kaltum kuwa
lafiya bata zuwa gashi ba tada lambarta?
sai Abba yace sunyi waya dashi yace kaltum tananan lafiya.
hankalin Madina bai kwantaba harsai data sa sumayyah takaita gidansu kaltum ranar
alhamis da yammah ranar da suka tabbatar ba islamiyyah a karkashin wata katuwar
bishiya a kwance a tabarma suka hangota a farfajiyar gidan, kai tsaye suka tunkaro ta
tana daga kwance tana dubansu a zatonta bakin mummy salaha ne sukazo ne manta
don bata dade da komawa Abuja ba, kaltum tace aranta ko su waye wadannan masu
kudine da ilimi saboda kamshin turarenda ya daki hancinta tun basu karaso inda take ba,
sallama suka mata cikin wata lallausar murya saita amsa sannan tayi firgigit ta tashi
zaune ta dube su ta daka tsalle ta mike da sauri sannan ta rugumesu tana murna,
kaltum ta rike baki tana duban Madina tana mamakin irin wannan canjin data gani cikin
dan kankanin lokaci, tace aunty Madina haka kika wani canjawa?
Madina da sumayyah suka kwashe da dariya, sumayyah tace kema kya pada,
Madina tace ke kaltum kya yi zancen canzawa kinga inda kika zama wata katuwa fara
tas wa zaice kece yar yarinyar nan ta ADON DAWA.
kaltum tace aini na shekara uku da zuwa kefa bakifi watannin biyu ba, su dukka sukayi
dariya suka zazzauna suna hira sunajin dadin inuwar, zata kawo musu ruwan sha ma
suka ce yanzu suka sha swan water da juice a mota don haka kaltum ta koma ta zauna,
sumayyah ta dubi kaltum tace gaskiya kin canza saboda jiya madina ta nunamin
hotunanku a bur sudan tamkar an tono ku daga kabari wasu dakwal-dakwal daku yar
'kankanuwa dake amma yanzu dubi yadda kika girma kin zama cikekkeyar budurwa yar
gayu maganar ma kamar turawa,
suka sake kwashewa da dariya su dukka , Madina tace ai kuwa da kyawun p
hoton nan muke gani kaltum dashi take kwana a karkashin pilo a jima ta zaro ta duba ta
mayar,
sumayyah tace naga hotonta da wani zankadeden saurayinta mambela duk da a dawa
yake yanada kyau da ace a birni ne wayayye dan boko da matan kasarnan sun dinga
tuntube suna waiwayensa,
kaltum tayi murmushi yayinda idanuwanta suka cika da hawaye ta dubi Madina tace
aunty mun kasa samun damar da zamu zauna muyi labari tun ranar nake tambayar ki
ina mambela bakiban amsa ba .
Madina tace baki damu kiji labarinsa ba tuda baki sake dawowa ba tun ranar da nazo,
haba kaltum nice fa madinarki?
inzo kasarnan saboda ku amma ki shareni?
kaltum ta girgiza kai tace ba haka bane, nayiwa daddy laifine a ranar saboda nakai dare
shiyasa ya hanani fita ko ina kuma bani da numbarku shiyasa vankira va amma kullum
ina tunaninki, bani labarin mambela bayan tafiyana koya manta da nine?
madina tayi murmushi tace yaya za ayi mambela ya manta dake a rayuwar sa?
kema baki manta dashi ba balleshi dayafi son ki?
kaltum ta gyara zama tace kinsan ya biyoni har Khartoum zamu tafi bur sudan kenan
aka aiko aka tafi dani.
Madina tace kwarai ya gayamin amma na dauka karya yakeyi kokuma ince ya zautu ne
kawai yakeyimin shirme,
Madina ta dinga bawa kaltum labarin halinda mambela ya shiga na damuwa a sanadiyar
rashinta, da yadda ya daga musu hankali ya ce, duk sai sun bar kasarsu tunda kaltum ta
tafi, sai dai daga baya ya hakura, ya yadda da kaddara. Daga karshe ta bata sakon da ya
fada mata cewar ta fadawa kaltum har yanzu yana son ta ba zai dena ba har abada.
Kaltum ta rushe da kuka ta rungume madina, sai ita ma ta dinga hawaye. Sumayya ma
ta tausaya sai ta girgiza kai ta dafa kafadar kaltum.
Ta ce, "yarinyar Mai zai hana ki kwantar da hankalinki, ki cire zuciyar ki daga kansa, ki zo
ki gina sabuwar rayuwa da 'yan kasarku? Dube ki mai kyau ba mu da irinku da yawa a
kasar nan masu suffar larabawa, fulanin asali ki zabi saurayi ki darje, ke ko gwamna ya
ganki sai ya so ya aure ki. Ina ke ina dan ADON DAWA? "
Kaltum ta sharce hawaye ta ce, "zuwa na kasar nan na yi samari masu dimbin yawa,
kuma attajiran gaske, manya da samari, amma bana kula kowa, mambela nake so, sai
dai kash!!! Maganar nan da muke yi sati guda ke nan da a ka bayar da ni. "
Suka dafe kirji su dukka suka ce, "waye mijin? "
Kaltum ta yi murmushin karfin hali ta ce, "Alh. Adnan ne.".
Madina ta gyada kai ta ce, "yayi daidai, kin yi dace da miji na gari, mai tausayi wanda
yasan darajar mutum. Kin yi dace da mijin da yake matukar son ki ba don komai ba, sai
don Allah, kamar ni da Abba, tabbas mutum ne mai kirki, kun dace, Allah Ya barku tare ".
Madina ta dafa kafadar kaltum ta ce, "me yasa kike kuka alhali kin dade da sanin yana
son ki, ke ma kuma kina son sani? Mambela yana son ki, amma kin san auren ku, abu ne
mai wuya, saboda kun yi hannun riga wajen dabi'unku, yarenku da kasar ku, ba a san
asalinsa ba, ba a san inda ya fito ba, zai yi wuya a yarje masa ya aure ki".
Kaltum tace, "nasan da haka, amma ni ina son mambela, ina tsoron matar Alh. Adnan
mummy salaha, takura min zata yi ni da iyaye na".
Madina tace alh Adnan bazai bari ta cuce ki ba itama auranta yayi kamar yanda ya
auroki, babu abunda zata iya yi miki, yaya akayima ya furta zai aure ki?
kaltum tace bai fada ba, babane yace ya bashi ni, da farko bai amsa ba sai acikin
wannan satin yan uwan baba suka sameshi a zangon Daura suka sake mishi magana
sannan ya yarda , yanzu jira ake jarabawar jamb dinda nayi ya pito inga inda suka bani
domin nacika U.B.K Da gwagwalada Abuja, idan kano suka bani sai ya gina min gida a
kano ayi bikin idan kuma Abuja

Please Login or Register in order to submit comment