Reading adon dawa Chapter 10 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mami hafsa ta dauki lokaci mai tsawo tana yi min
nasiha cewar in kama kaina in rike mutuncina idan na samu miji in yi aure in cire son
tasi’u a raina, na ci sa’a na samu gida a staff querters din asibitin, daki biyu da tsakar
gida ga kicin da ban daki.
Hakika na ji dadin aikina ina xaune da abokan aikina mata da maxa lafiya. Dan albashi
na yana isata in ci abinci, in dinka ‘yar sutura har in kunshe in kawowa yarana wani
kudin ko su shigo mota idan babansu baya gari su xo su karba. Na ci gaba da kama kai
na ina rike addinina yadda ya kamata ina cikin walwala fiye da a gidan tasi’u. labari ya
iske kunnen makiyana cewar na samu aiki har na murmure na yi kyau sai haushi ya ishe
su, suna hassada dama ban samu ba sun fi so kullum in shiga wahala da wulakanci
amma Allah Ya fi su.”
Kaltum tayi dariya tace “na ji dadin labarin nan naki matuka da na ji karshen ki alkhairi
ne. Allah Ya dube ki ya rufa miki asiri musamman da kika yi tawakkali kika cire son tasi’u
a xuciyar ki. Ta amma me yasa kika bar aikinki kika taho nan bayan aikin yafi tahowa ki?

Madina ta yi ‘yar dariyar karfin hali ta cije leben kasa tace “kaltum, kema kin san in har
babu matsalar da tafi karfina, ba xan baro aikina in taho ba. Gagarumar matsala ce ta
fado min wacce har tafi matsalolin da na hadu dasu a baya. Tsanani yayi tsanani wanda
har mami hafsat da daddy tukur da sumayya kawata masoyana wa anda bani da kamar
su a duniya suka kini suka kira nida MAYYA. In takaice miki hatta da ‘ya’yana dana Haifa
a cikina saida suka ki ni suka guje ni, suka ce ni ba uwarsu b ace. Kaltum tun daga ranar
da Abdul malik ya furta min haka, na jawo hannun Abdul hakim ya fisge yace min bana
sonki mama, nace to ba ni da amfani a duniya, rayuwata ta xo karshe gara in shiga
duniya kawai xai fi ye min sauki.” Sai madina ta rushe da kuka.
Kaltum ta ji hankalinta ya tashi, tuni ta shiga surkukin tunani ta tambaya cikin damuwa
“anty, me yasa haka?
Me kika yi musu haka ko asiri aka yi miki kowa ya tsaneki ? ”
Madina ta goge hawayen ta ta yi dan murmushi t ace “ba asiri ba ne kaltum kaddara ce
kawai ta hau kaina sai dai in xama me godewa Allah a duk halin da na tsinci kaina. Xaki ji
dalili kema idan kika ji dalilinsu baxa ki xarge suba, watakila ma k ice sunyi daidai da
suka yi min haka amma nima ba laifina ba ne an yanke min hukunci bisa rashin sani.”
Madina na rufe bakinta sai ga baba tsoho mai sayar da ruwa ya dawo akan jakunansa, ya
ja ya tasaya a gabansu kaltum, daya dubeta sai yayi dariya.
Cikin harshen larabci yace “’yar baiwa dawowa nayi in cika alkawarin dana dauka , dana
ce idan na sayar xan siyo miki gurasa da xuma gashi na kawo miki. Na sayar da ruwan
dukka har xan koma in karo wani.”
Kaltum ta tashi da murna taje ta durkusa ta karba tana godiya ya wuce ya tafi. Ta xo ta
ajiye a gaban madina tana mai fassara mata abunda suka fada cikin harshen larabci.
Madina tayiwa tsohon nan addu’a suna ci suna yabonsa har suka cika tunbinsu, saboda
gurasar mai yawa ce, badan suna jin yunwa ba da ba xasu iya cinyewa duka ba, suka
kora da ruwa.
Madina tace “muje muyi sallah na lura axahar tayi sai mu dawo mu ci gaba da labari .
Kaltum, labarina akwai abin al’ajabi nan gaba, ai ba ki ji komai bama a baya.”
Kaltum t ace “tabbas na shiga wani hali na xumudin son in ji wannan labarin, kaina gaba
daya ya daure tamkar an yi min dabaibayi.”
Suka shiga gida da ruwansu don suyi alwala suyi sallah, saida suka idar da sallah sukayi
nafiloli da addu’o’insu sanna suka dawo wajensu na da wato kofar gida suka xauna yayin
da wata iska mai dadi take kada su baya ga tumbinsu daya dau lodi, don haka mai
sauraro, da mai bayar da labari suka sami nutsuwa labarin ya fara tafiya yadda ya
kamata.
Kaltum ta dubi madina ta fada cikin kaguwa tace “anty ci gaba ina sauraron ki.”
Madina ta nisa tace “watanni shida da fara aiki a asibitin kaxaure yayin da shekarata
talatin da uku a duniya. Tukur tukur wato Abba kanin kawata Dr sumayya tukur, ya kawo
min xiyara har kaxaure wajen aikina da misalin karfe tara na safiyar wata littinin. Yaro
matashi a tseleliyar motar da mahaifinsa ya saya masa a satin saboda farin cikin
kammala bautar kasarsa da yayi ya xama cikakken lauyer.
Banyi mamaki ba da naga Abba a kaxaure a daidai wannan lokacin, kuma ban yi
mamakin ganin tsaleliyar motar nan tasa ba saboda nasan mahaifinsa xai iya bashi
wacce ta fita ma saboda general tukur mutum ne mai son ‘ya’yansa da yawa. Sai na
dauka Abba ya xo don ya nuna min sabuwar motarsa ne, ban yi mamaki ba idan haka ne
saboda Abba mutumi na ne sosai, abokin labarina ne a yi wasa ayi dariya ayi shewa
saboda ni mai yawan Magana ce da xolaya.
Abokan aikina har guda biyu suka shigo office dina suna shaida min cewar nayi bako a
waje yace daga kano yake sunan sa Abba tukur, sai nace su ce masa ya shigo amma
Abban na tsaye a bakin baranda bai shigo ba. Na aika masinjanmu har sau biyu yace
masa ya shigo amma Abba bai shigo ciki ba, ni kuma ina ta faman aiki ina shigar da
sunayen da sakamakon wadanda muka yiwa gwajin hawan jinni da ciwon suga cikin wani
file. Kafin su xo su karbi sakamakon su. Dole tasa na ajiye biron na fito da kaina, ina ta
murnar ganinsa ina ta hayaniya ni kadai. Haja ina ta shafa mota ina doguwar addu’a ni
kadai Abba na tsaye kikam bai ce da ni komai ba.
Ya xura hannu a aljihun wandon yayin da yayi shar a cikin suit dinsa baka da farar shirt a
ciki mai dogon hannu, wuyansa makale da nektie, sai wani bakin takalmi kafa ciki sai
sheki ya keyi. Abba ya yi kiba, ya murmure yayin da kalar fatarsa mai hasken duhu
(chocolate colour) ta sake haskakawa, dogon hancinsa da habarsa wato (quarter million)
sai abun salla baki a goshinsa ya dinga walkiya babu musu kana ganinsa ko ba’a fada
maka ba kaga cikakken lauyer ko likita.
Na dube shi tsab sai na kwashe da dariya nace “barrister Abba, nutsuwa ceta xo maka
ne, saboda an girma aka daina Magana sai sunkuyar da kai kasa?
Ni yayarka ce fa na san tsarkin kashinka, ni kuma xaka jawa aji?
Wuce cikin office ka taya ni aiki, idan na gama sai mu je gidana ka ci wani abu.”
Na wuce gaba Abba yana biye da ni har cikin office dinmu. Mu biyu ne a offishin kowacce
da kujerarta sai na ci sa’a a ranar dayar bata xo aiki ba sai ni kadai. Na jawo masa daya
kujerar kusa da ni nace ya xauna, ya xauna a hankali. Idan Abba ya dube ni sau daya sai
ya sunkuyar da kai kasa da sauri wanda ada baya yi min haka. Ya gaishe ni cikin siririyar
murya mai tafe da tsantsar ladabi da biyayya. Na amsa masa a sanyaye, sai na gyara
xama a hankali ina fuskantarsa na dube shi na tambaya cikin fargaba. Na ce “Abba
lafiya?
Waye bashi da lafiya ko kuma waye ya rasu, ‘yayana ne ko? ”
ya girgixa kai yace “babu wanda ya rasu kowa lafiyarsa kalau.” Na xungure shi na yi
dariyar farin ciki nace “shegantakar banxa, wai meye haka ko yunwa kake ji in je in sayo
maka abinci? ”
ya sake girgixa kai a sanyaye alama baya ci.
Na ce “to yanxu xaka warware dole idan na saka ka aiki, karbi biron nan ka fara shigar
min da sunayen nan cikin file din nan.” Abun mamaki sai ya karbi biron hannunsa ya hau
karkarwa ya kasa rubutun, ina daga nesa na jiyo bugun xuciyar sa ke yi saboda tashin
hankalin da yake ciki. Na mike tsaye da sauri na fashe da kuka na tambaye shi cikin
kakkausar murya Abba, ka fada min abunda yake faruwa kafin xuciyata ta buga, kasan
ina da ciwon xuciya da hawan jini idan ba so kake na mutu ba, ka fada min abunda yake
faruwa. Ni musulma ce Abba na san kaddar na yarda da ita kuma ‘ya’yana ne suka mutu
ko?
Ko kuwa mami ce ko daddy? ”
Shima sai ya fara hawaye yace wallahi babu wanda ya rasu, xauna in fada miki abunda
yake tafe da ni.”
Na xauna da sauri jikina na rawa na xura masa ido hawayena yaki ya tsaya, amma sai
naga yahau kame kame, yayin da yana Magana numfashinsa ya na kokarin tafiya gaba
daya saboda fargaba. Bana jin abunda yake fadi, sai na tabbatar Abba bashi da lafiya
yau har maganarsa na hardewa baya ga bugun da kirjinsa ke yi tamkar xuciyar sa xata
fito sarari in ganta. Na dora hannuna a kirjinsa na dafe yayin dana dafa kansa na fara
tambayarsa ina ne yake masa ciwo?
Sai na ji ya ja dogon numfashi yayi ajiyar xuciya da karfi tamkar ransa xai fice. Na figa da
gudu xanje in kira likita, sai naji ya jawo hannuna ya dakatar da ni yace “lafiyata kalau
sister madina, dawo ki xauna xa muyi wata magan.”
Na dauka abin gwada jini na auna dantsensa, hakika jininsa yahau kadan. Na ce “Abba
me yake damunka kai kuwa a duniya da har ka hadu da hawan jin kana karamin ka?
Abba me kake nema ka rasa a duniya daya wanda ya dameka a xuciyar ka?
Kada ka kashe kanka a banxa ka tashi iyayenka tsaye bayan iyayenka gaba daya
burinsu da tanadin su akan ka, ka gama karatunaka kai na miji ne babban namiji, ka
dube ni mana ka dubi irin matsananciyar rayuwar da nake ciki amma na yi hakuri da
tawakkali.”
Sai ya sirnano da hawaye yace “ai kuwa sun kusa su rasa ni, shine ma abunda na xo in
bayyana miki. Sister madina, ajalina ya xo tabbas na kusa mutuwa.”
Sai na fashe da kuka na dauki dogon salati, shima kukan yake. Na ce “Abba me nene
matasalarka inyi maka maganinta in har xan iya? ”
Ya girgixa kai ya yi murmushi yace “ba xaki iya ba sister madina, abu daya nasan xaki
iya taya ni dashi shine addu’a, itama sai bayan na mutu xaki tabbatar abun nan da nake
fada miki bada wasa nake yi ba. Ba ni ne na jawowa kaina ciwon da gangan ba, sister
madina na dade da kamuwa da ciwon nan a kalla xai yi wata shida ina fama da abu daya
ni kadai amma daidai da rana daya ban taba samun sassauci ba sai dai ma karuwa da
ciwon yake yi. Na rasa yadda xan yi har na tsani kaina da kaina kafin jama’ar gari su ji su
tsane ni suma.” Sai kuka ya ci karfinsa, ya rushe da kuka me tsanani..
Ni kuka, shi kuka. Na tambaya cikin kuka “kai kuwa Abba wannan wane irin ciwo ne?
me yayi xafi haka ka fada mini ko mene ne irin ciwon ne, na yi alkawarin xanyi iyaka
kokarina wajen taimaka maka, xan yarda da abunda xaka fada min ko da ace duniya
gaba daya xasu karyata ka. Me yake damunka kanina ka fada min, Abba ciwon kanjamau
ka dauko? ”
Sai yayi murmushi yace “kanin ki? Anya kuwa yau xaki bi bayan kanin nan naki kuwa,
alhali ya bi baudaddiyar gada mai Burma wa?
Ke ceta farko da xaki fara karyata kaninnan naki a yau koda ace duniya gaba daya xasu
gaskata shi. Ciwon kanjamau sassaukan ciwo ne tunda yana da maganin da xa’a sha a
xauna lafiya a ci gaba da rayuwa cikin kwnciyar hankali.”
Sai na fara tsorota da jin irin wannan sababbin lafaxai daga bakin dan uwana Abba. Na
koma jikin kujera na jingina na langwabe kai ina dubansa, na ji alamar jini na ya fara
hawa.
Ya ga alamar na damu sosai sai ya shiga lallashina yana bani hakuri. Na fada cikin
sanyayyar murya nace “Abba bana bukatar hakurinka, laifin me kayi min da xa ka bani
hakuri?
Sai dai ina mamakin wannan al’amari naka, idan wasa ne ka daina. Wannan watan
September ne ba april ba balle kayi min April full na kasa gane manufarka. Ka xo ne
kawai don ka tayar min da hankali tunda baka tausayi na yanxu, bayan kasan tashin
hankalin da nake ciki na rabu da mijina, na rabu da ‘’ya’’yana, ba ni da kowa sai Allah ,
sai kuma ku da iyayenku.” Na fashe da kuka.
Ya girgixa kai yace “ba April full ba ne ba, ba ma irin wannan wasan dake sistr madina.
Ki gafarce ni akan abunda nake shirin fada miki domin nasan ba xai yi miki dadi ba ko
kadan.”
Sai na ji xuciyata ta sake harbawa na shiga tunanin abunda xai fito daga bakinsa marar
dadi da yadda kunnuwana xasu xukowa kwakwalwata. ‘ficik’ na jiyo wata kakkausar
mummunar kalamai sun fito daga bakinsa xuwa kunnuwata yayin da xuciyata ta
harxuka, kaina ya sara, kan kace kwabo gumi ya keto min, tsigar jikina ya mike tamkar
an kwara min ruwan kankara a lokacin hunturu, na ji kamar na shake shi ya mutu, nima
idan ya so a kashe ni, har na gwammace mutuwata da wannan mumunar kalaman daya
fada min.
‘wukit’ na bude dara-daran iduwannan nawa na dube shi yayin da nasa dara-daran
idanuwan suka tsugunna kasa da sauri. Na fada cikin fushi n ace “Abba ban jiba,
maimaita min abunda ka fada.”
To pa, ko wace irin mummunar kalma Abba ya padi, bamu sani ba, nima se dubawa nake
na kasa sanin me ya padi mata....
.
ADON DAWA 2 ( P 14)
.
TRUE LIFE STORY
.
Me Abba ya padi ne?
Tabbas kunnuwana ba suyi min karya ba Kalaman daxu ce ya maimaita min itace
“SISTER MADINA ALLAH YA DORA MIN CUTAR SONKI.”
Na ce “Abba kamar so na ji ta fi fito daga bakinka ixuwa gare ni kunu wata?
Ashe xaka iya duban sumayya ka ce kana sonta so iri na soyayya? ”
Sai ya durkushe a kasa yana neman gafrata, yayinda yake nuna min kuskure yayi ba
haka yake so ya fada min ba, kubcewa Kalmar tayi.
Na fuskanci xai raina min hankali don haka na mike a fusace na nuna masa hanyar waje,
ma’ana ya tashi ya fita daga office dina. Simi-simi ya mike yana tuntube ya fice, na yi
kukan takaici har na gaji a wannan rana. Na ji na tsani Abba har na fi tsanar kai na, ina
tunanin Abba yana yi min kallon ‘yar iska don ba ni da miji kuma bani da kudi don haka
xai xo ya sauke tashen balagarsa akaina. Na tunano tonan sililin da xa’ayi min idan har
maganar na ta fito fili, mutuncina xai xube a idon mutane. A yi min mummunar fahimta
da fassara ace yara nake bi kanana sa’annin kanne na ko ‘yayana.
Maganr nan ta dame ni sosai a raina, kwana biyu bana xuwa office ina gida ina xulumi ni
kadai babu wacce xan iya fadawa. Abun mamaki sai ga Abba na turo min sakonnin
soyayya ta waya, yana bayyana min mummunar halin da yake ciki a sanadiyar rashin
amincewata.
Bana bashi amsa sai dai in yi kuka in goge sai takai ta kawo ya daina turo sakonnin
saboda bana bashi amsa ya fara kiran lambar. Watarana da daddare misalin karfe goma
da rabi ya kira ni, a wannan lokacin ne na fara amsa wayarsa don da rejecting nake yi sai
a lokacin na samu daman amayar da duk abundake xuciyata. Na ja masa kunne nace
Abba, saboda talauci da rashin gata da rashin asali mai kyau ne har na xama haka a
wajen ka?
Ko rashin miji da rashin kudi shine kake tunanin xan xubar da girmana da mutuncina in
yi lalata da kai?
Ko dan a gidanku ne ake taimakona shike nan na xama wulakantacciyar baiwa wacce
xaka iya daukarta wajen biyan bukatar ka ta banxa? ”
Sai ya rafka salati yayin daya hau rantse-rantse cewar ba haka ba ne. ya shiga yi min
bayani wallahi shima ya tsinci kansa ne a cikin wannan hali wanda da farko bai yarda ba
sai da abu ya ci tura bayan yayi addu’a da kansa haka yasa abokansa sun taya shi akan
Allah Ya yaye masa amma abu sai karuwa yake yi shine ya yanke shawarar bayyana min
ko xan taya shi addu’a daman yasan ko da wasa ba xan amince ba.
Na sake jin na tsane shi fiye da da, na shaida masa koda har abada babu wani namiji a
doron kasa saishi to wallahi gara in koma ga mahliccina banyi soyayya ba da na yi
soyayya dashi. Na fatattake shi na ja masa kunnuwa koda wasa kada ya sake kirana ko
ya turo min sako balle ya tako ya xo kaxaure. Nima har abada na daina xuwa gidansu.
Sai na ji ya fashe da kuka yana fadin inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un, na murtsuke wayar
gaba daya na kashe. Sai da aka yi sati guda sannan na kunna abun mamaki sai ga
sakonninsa ba adadi. Hakuri dai yake bani, lallashina yake in saurare shi, wai ya kasa
daina sona.
[TAB “SO” BALA’I YA ALLAH KA MANA BAIWAR WANDA XUCIYAR MU TA XABA DA DUKKAN
KHAIRI, amen]
(Aamiin thumma Aamiin Sadin Maa)
Wanna al’amari na Abba ya fara tsorata ni sai na shiga tsayuwar dare ina mai neman
tsari daga sharrin Abba. Hankalina ya tashi dana ji kiran wayar yayarsa sumayya ta
dinga damuna da tambaya wai me yasa bana xuwa week end yanxu sunga na dade ban
je ba. Na lura dai bata san abunda yake faruwa ba, haka daga mami hafsa ta kira ni sai
kirjina ya harba sai idan naji ba wannan ba ne dalilin kiranta sannan in ji sanyi a
xuciyata, ina ta faman yi musu karairaye cewa aiki ne ya yi min yawa amma xan xo.
Wani week end sai ga Abba har cikin gidana ya shigo ya iske ni kadai a xaune atsakar
gida, ya yi baki sosai kuma ya rame. Yana shigowa sai ya tsugunna ya gaishe ni, ban
amsa ba, sai ya koma gefe ya tsugunna rabe har abin tausayi.
Ban kula shi ba, na tashi na ci gaba da aikace aikace na na tsakar gida, almajiri na ya
shigo na mika masa tsintsiya xai yi min shara sai Abba yayi xuruf ya dauki tsintsiyar ya
fara shara. Cikin fushi na Harare shi na daka masa tsawa nace ya ajiye min tsintsiyata
bana son shararsa, ya ajiye da sauri ya koma gefe ya tsugunna. Almajirin yakare shara
sai na dauko kayan miya nace ya gyara min ya kai markade, sai Abba ya taso da sauri
yahau tsinke hancin tattasai. Ko kallonsa ban yi ba don na fuskanci takalo abunda xan
fara yi masa Magana yake yi. Ya ja alamajiri suka tafi markade a inji.
Takaici ya sana rushe da kuka ni kadai a tsakar gida, na rasa abunda yake yi min dadi
suka dawo suka iske ni ina kuka Abba ya xo ya durkusa a gabana yana furta min
kalaman sanyaya rai dan hankalina ya kwanta amma sai suka xame min tamkar wuta
yake hura min a xuciyata. Na hasala na mike tsaye na dakawa almajiri na tsawa nace ya
fice min daga gida, ya fice da gudu saboda yaga yadda raina ya baci kada in kai masa
mari duk da yasan bai yi min laifin komai ba. Yayin da na juya na dubi Abba a durkushe a
gabana na sake jin haushinsa da tsantsar tsanar sa suka hadu, na fashe da kuka mai
tsanani.
Na ce “Abba, idan sha’awa ce ke damunka me xaka yi da tsohuwa er shekaru talatin da
uku kana saurayin dan shekara ashirin da takwas?
Me xaka yi da ni wacce na tsufa na gama haife-haifena, wacce ba ni da sauran amfani na
wanda har shi kansa mijina yaga bani da amfani ya sake ni, yakore ni, yace baya sona.
Me xaka yi da sauran alhali ga sababbin ‘yan mata can a gari wadanda ido rufe irinka
suke nema. Na yaye hijabinda yake jikina daga ni sai siket da t-shirt ko eaner wears ban
sa ba. Na ce me kake sha’awa a jiki na?
Idan sha’awata ka ke yi mushiga daki in har daga yau xaka rabu da ni in huta.”
Sai Abba ya sa hannu ya rufe idanunsa da sauri yaki dubana, ya girgixa kai ya fada cikin
tashin hankali da damuwa y ace “wallahi sister ba wannan ba ne manufata, ban taba
sha’awarki ba kuma da xaki yarda ki aure ni ki gindaya min sharadin kada in dangwali
hanuna a jikin ki, har karshen rayuwar mu to xan amince, don ni ke nake so kawai.”
Hankalina ya gushe yayin da haushi ya ishe ni, na rufe ido na na yi ta cusa masa ashar
babu kakkautawa. Na ce ya tashi ya bar min gida kafin na dauko tabarya in fasa masa
kai. Ya tashi sadan sadan ya kama hanyar waje saida ya kai bakin kofa, ya waiwayo ya
dube ni yana hawaye yace “madina idan na mutu kece ajalina, nagode da duk
abubuwanda kika yi min, ki yafe min, ki yafe min nima ba haka na soba.” Sai ya fice ya
bar ni a nan a tsaye kamar gunki.
Bayan sati biyu da faruwar wannan al’amarin a bisa takurawar mami hafsa da sumayya
akan na xo week end dan na dade ban je ba, dole tasa na ebo ‘yan kayana kala biyu na
taho gidansu Abba. Abba na fara iskewa a falo yana xaune sai gumi yake yi shi kadai duk
da AC dake kunne a falo, kallo daya xaka yi masa ka tabbatar yana cikin matsananciyar
rayuwa. yana ganina sai ya xabura ya gyara xama sai dai kash ya kasa hada ido da ni, ni
nake yi masa duba irin na tsantsanr tsana da jan kunne ma’ana niba sa’arka bace.
Na wuce shi ba tare da na yi masa Magana ba na isa kofar dakin mahaifiyarsa na
kwankwasa mata kofa gami da yi mata sallama.
Kasancewar tasan ina tafe nan ta dau muryarta t ace “madina ki shigo mana.” Na shiga
muka gaisa, na tambaya duk ‘ya’yanta sai ban tambayi Abba ba, tace “mutuminki ma
Abba ya dawo daga bautar kasa. Bai je ya nuna miki motarsa ba? ”
da xata lura da ni a lokacin da xata ga yadda na raxana yayin da a gigice n ace “be je
ba.”
Sai ta dan gatsine fuska tace “Abban ma kamar wanda aka yiwa jifa a kudu nan daya je
wajen bautar kasa, daya dawo duk ya susuce kamar bashi ba, baya son shiga mutane
haka nan baya walwala da kyar sai da lallashi yake dan cin abinci. Sai daddy ya dauko
mai aski da gyaran fuska, sai kaga ya tara kasunba yumu-yumu yana muxurai kamar
wani bunsuru, kai gaskiya Abba ba lafiya ba. Shiga dakinsa ki ganshi ko ke da yake
mutuniyarsa ce xai yi miki bayani.”
Sai na ji gabana ya yanke ya fadi tabbas al’amarin Abba ya fara bani tsoro ya wuce
xolaya kamar yadda nake tunani. Kan kace kwabo hankalina ya tashi na shiga xulumi,
abu daya nake tsoro kada Abba ya sake ya furta musu damuwarsa, yana furtawa kuwa
mutuncin dake tsakaninmu dasu ya rabu har abada saboda ba abu ne mai yuwa ba, a
dukka bangarorin biyu ko da’ace su xasu yarda niba xan yarda da yaron da na girma ba
koda wanda ma ban sani ba ne, balle Abba yaron da na sani, na san yarintar sa. Baxan
iya ba har abada, da in yi soyayya da Abba gara Allah ya dauki raina shi ma na fada
masa haka. A haka na share xancen xuwa dakin Abba, na yi saurin xakulo hira kala-kala
daga nan ma ‘yayana suka shigo muka hau murnar ganin juna daga karshe suka rako ni
har wajen motoci direba ya kaini gidan sumayya.
Ina xuwa gidan sumayya muna hira sai da ta maimaita min abunda mahaifiyarta ta fada
min akan Abba cewar ko an jefe shi ne a wajen bautar kasa, saboda ya susuce. Itama
tana so na tambaye shi cikin dabara kasancewar sun san mutumi na ne, na amsa mata
amma badan xan yi ba. A daddafe na yi kwana biyu a gidan su Abba, na je ranar juma’a
da yamma na koma kaxaure ranar lahadi da yamma.
Naga yarana na basu abin da suke bukata, shima Amma mun harhadu a falon gidan
musamman da safe idan zamu karya sai dai baya iya yi min Magana nice ke faman
washe masa baki ina yi masa wasa a dole saboda a gaban iyayensa ne kada su gane
akwai wata ‘yar takaddama a tsakanin mu na sulalo na dawo kaxaure da xummar a wata
shida ma ba xan je kano ba, ai dai na yi tunda na je.
Haka kuwa aka yi na dade ban je kano ba sun yi min xancen xuwa week end sai na fake
da aiki yayi min yawa. Kusan watanni uku ban ga Abba ba, ban ji kiransa ba a waya sai
hankalina ya kwanta na dauka ya hakura da ni. Wata rana da daddare ana tafka ruwan
sama kamar da bakin kwarya. Na rufe gidana tun kafin magaruba, ina dakina akan salla
na idar da sallar isha’I ina wuridi da addu’o’I kala kala ina fadar bukatuna, saboda Allah
Yana amsa addu’a a lokacin da ruwan sama yake sauka. Na ji yo da gaske ana

Please Login or Register in order to submit comment