Reading adon dawa Chapter 14 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wukar ta a hannu ta rike kugu, babu alamar
tsoro a tare da ita. Mambela ya yago gefen ‘yar sharar rigarsa ya daure kafarsa wajen
ciwon sannan ya dago ya dubeta yayi murmushi ya fada cikin harshen larabci yace “yar
agulla, kin cika ‘yar agulla, yau na tabbatar ke ‘yar agulla ce. Kin yanki abokaina da
yawa yau yankan naki kaina ya dawo kuma, kin yanke ni har jini ya xuba a kasa.”
Sai ya tuntsure da dariya mai fitar da sauti mai kara ya gyada kai y ace “ni mambela, ni
ne yau yarinya karama ta yanke ni a kafa, yarinyar ma bakuwa baiwarmu, almajira mai
bara. Tabbas baki sanni ba, baki samu mai xaunar dake ya baki labarina ba yadda ya
kamata daga nan har cikin gari babu mai taba ni ya kwana lafiya, babu mai yi min musu
duk duk abunda nace dai dai ne. ‘yan jange masu barka cikin mtum da wuka, masu fada
da kwalba suna tsoron mambela domin ni aka fi sani da yanka. Babana ya fi kowa kudi
ya mallaka min gidaje kala kala a kartum bayan na wasu manyan burane a sudan, babu
abinda na nema na rasa sai ke, a kanki baxan fara ba dole sai kin amince. Ina biye da ke
a duk inda kika saka kafarki, ina ganin mu’amalarki da jama’a sai naga kin fi hulda da
wancan tsintaccen yaron karim marar gata, da alama kin damu dashi don haka sai na
raba shi da hannunsa ko kafarsa kacukan yadda ba xai sake moruwa ba.”
Kaltum ta fusata ta fara Magana cikin fushi muryarta sama sama tana nuna shi da hannu
tace “mambela karya kake yi, baka isa ka ce xaka raba ni da karim ba saboda karim dan
uwana ne kasarmu daya, karim ne mai taimako na yana ba ni abinci. Ka sani duk sanda
ka taba karim ka yanke shi, ni kuma sai na barka cikinka hanjin ka ya fito waje sai dai
nima a kashe ni.”
Ya mike tsaye ya na murmushi yace “na yarda xaki aikata abunda yafi haka ‘yar agulla
na tafi sai haduwarmu ta biyu, sai dai ina so ki sani baki isa ki kula wani ba idan ba niba,
saboda ina sonki kuma baxan rabu da ke ba.”
Ta Harare shi ta ce “ bana sonka, na tsane ka kuma har abada ba xan so ka ba.”
Ya juya ya tafi a fusace yana dingishi, ta xaro tsumma daga jikin xaninta ta goge jinin da
yake jikin wukar ta like ta mayar cikin rigarta ta adana.
Karim ya taho da gudu inda kaltum take tsaye yana ta mamakin karfin hali irin nata,
tambayarta yake, “daman kin san mambela, ya aka yi mambela ya sanki har kika yanke
shi da wuka bai dauki mataki ba? ”
Kaltum ta ci gaba da ciccibar kifinta ta nufi gida ba tare da ta bashi amsa ba.
Bayan anyi haka da kwana uku misalin karfe goma sha daya na safe, karim na wajen
sana’arsa ta kamun kifi sai yaga mambela a tsaye a kansa yayin da mambela ya jawo
hannunsa ya fito dashi daga cikin ruwan, kan kace kwabo hantar cikin karim tadau rawa
cikin yaren ‘yan ADON DAWA yake bashi hakuri, yana tuba yana neman afuwa.
Mambela ya dukar dashi kasa yace “baka da labarin kaltum tawace?
Ba ka da labarin ni nake sonta kuma babu wanda ya isa ya so ta bayan ni, balle kai
bawana? ”
Karim ya daga kai yace “naga alamar haka mai gidana babu mai ja da kai, kaltum
kanwata ce kuma na yi alkawarin sai na sa ta so ka.”
Dadi ya lullube xuciyar mambela ya yi murmushi ya tashi karim tsaye, ya karkade masa
kasar da ke jikinsa.
Ya ce “ina son kaltum son da bashi da adadi, ina son ka sata ta so ni itama, idan ta ki
xan hukunta ka.”
Karim yayi murmushi yace “an gama mai gidana.” Mambela ya juya ya tafi, farin cikin
xuciyarsa ya nuna a fuskarsa kai ka ce kaltum din aka bashi kyauta. Mambela na juyawa
kaltum ta karaso inda karim yake a tsaye ta tsuke fuska ta tambaye shi “meye mambela
ya xo yi a nan, me yace maka? ”
Sai karim yayi dariyaya ce “mu xauna mu yi Magana kanwata kiji labarin abunda baki
sani ba.”
Kaltum ta cire sharbabben takalminta silifas wanda ya fi girman kafarta sau biyu gashi a
tsinke harta daure da leda. Ta xauna akai yayin da ta baxa wani katon siket dinta
burgujeje kore da wata riga t-shirt ruwan dorawa, dankwalinta kuwa ya hadu da
cikurkudadden gashinta ya dankare, ta dubi karim tace “ina sauraronka, me nene? ”
Ya durkusa a gaban kaltum sai fara’a yake tamkar gonar auduga yace “kaltum kin yi sa’a
da mambela yace yana sonki saboda kin wuce wulakanci, fatara da yunwa a garin nan.”
Kaltum ta ji kamar ya daba mata wuka a kahon xuciyar ta, ta ja dogon tsaki, ta fusata
xata mike. Karim ya mayar da ita ta koma ta xauna.
Ya ce “shawara nake baki, ki so shi saboda yana sonki. Meye laipin sa? Gashi kuma dan
gidan masu kudi da sarauta, gashi dogo kyakkyawa, laifinsa daya bashi da mutumci
shima sai idan ka tsokane shi, ada ne yayi shaye shaye yanxu ya daina.”
NI SADIN MAA ME TYPING NACE “DU KYAWUN MAMBELA, BE KAI BOSS INA DAN ANTY ME
POSTING BA, SANNAN KUMA GA CIKA, KAMALA, DA MUTUMCI, DAN ANTY SAI
TUBARKALLAH.
Kaltum ta ci gaba da hararar karim har saida ya gama tsara ta sannan tace “ka gama
tsara ni?
To ba xan so shi ba har abada, ni na tsani mambela da abokansa kamar yadda na tsani
mutuwata.”
Hankalin karim ya tashi yana tambayar ta “saboda me bakya sonsa, me ya miki?
Mambela yana da kirki idan Allah Ya tsaga da rabonka har kyautar saniya sai yayi maka
ko kudi mai yawa musamman a lokacin axumi yana da rikon addini kuma.
Kaltum ta fusata ta mike ta ce “ban sani ba, ka je ka tambayi mambela me yayi min shi
da abokansa ba ni xaka tambaya ba . kai ma tunda bakinku daya dashi na daina kula ka
ba xaka kara ganina a wajenka ba.”
To masu karatu.
Kaltum data yarda da tayin mambela kuwa,?
ya data kasancewa karim idan har kaltum ta ki amincewa mambela?
Domin jin duk amsoshin wa’ennan tambayoyin se ku ci gaba da hakuri da biyo mu.
Mune na ku har kullum masu son dasa nishadi a xukatanku.
ADON DAWA 2 (P 17)
.
Ta juya ta tafi a fusace yayin da karim ya bi ta da gudu yana bata hakuri, ta ki
sauraransa, yayi yayi ma ta xo ta karbi kifi tace bata so.
A lokacin dasu kaltum suka cika shekara guda a bur sudan, a lokacin kasar ta fara yi
musu dadi dukkaninsu. Saboda da yawancinsu sun sami jari sun fara sana’a sun daina
bara, wasu matan suna sayar da kosai, wasu na yin koko, wata waina, wata awara. Wani
na dafa shayi da biredi, wani na sayar da rake, wani yayi ‘yar tireda yana sayar da
sabulu, omo man shafawa, makilin da brush da dai sauransu. Kofar gidan su kaltum ta
xama kamar ‘yar kasuwa ana ta saye da sayarwa. Jange suna xuwa su saya, haka ADON
DAWA ma suna xuwa su saya.
Madina ta sami sana’a itama ta daina bara, kosai take toyawa da safe, sai ta sayar da
tuwo da daddare. Kaltum ceke tayata wajen xubawa da mikawa da yin wanke wanke.
Bayan wannan babu wani abu da kaltum take yi amma komai baya gagararta kyauta ake
bata saboda sabon da tayi da jama’a kowa yana sonta.
Kaltum ta manta rabon da ta sayi ruwa da kanta saboda alkwari ne kullum tsohon nan
mai sayar da ruwa akan jaki sai ya bata jarka daya ko biyu kyauta. Haka ko ta je bakin
kogi ko bata je ba sai karim ya kawo mata katon kifi guda daya ko biyu danye ko
gasashshe kyauta, haka wani Muhammad mai sayar da nono akan jaki yake tsiyayo
mata nono kyauta, ga makudan kudi da mambela yake cusa mata amma bata taba
karba da hannunta ba sai dai ya bawa karim yayi mata dabara ya bata ba tare da tasan
kudin mambela bane ta karba ta kashe, ko mambela ya bawa madina ta saya mata wani
abun ba tare da ta san mambela ne ya saya mata ba. Duk wanda ke karkarar nan ya san
mambela yana son kaltum so na hakika yayin da kowa ya shaida kaltum ta tsane shi, ta
tsani ta hada ido dashi, ta tsani ta hada ido dashi a duniya.
Madina ta san komai ma’ana tasan abunda ke gudana tsakanin kaltum da mambela
amma ta xuba mata ido bata taba furta mata wata Magana wacce ta shafi mambela ba
haka itama kaltum bata yiwa Madina maganar sa ba.
A lokacin da suka cika shekara guda ne ake sake kawo wasu baki wadanda suka taho
mota guda suma sun fi su dari uku daga Nigeria ‘yan kasar sokoto ne wasu kuma daga
kano da jigawa. Wasu matan da goyonsu, wasu da ciki haka wasu ‘yan mata ne, ga
manyan maxa, samari da tsofaffi amma da aka tashi tafiya makka sai aka dauki kalilan
aka hayar dasu yayinda aka bar jifgi guda suna ta koke kokensu. Su kaltum suka yi
dariya suka ce dasu “xa ku saba kamar yadda muka saba har muke jin dadin xama muka
fi son xama a nan damu je makka ko mu koma Nigeria.
Don haka dakuna duk a ciccike suke a kalla mutum ashirin ne yanxu a daki daya, saboda
bakin da suka karo. A tattakure ake xaman yayin da hayaniya ta karu. Fada da dambace-
dambace suka dadu musamman a wajen shiga ban daki guda daya ne jal gidan mata da
maxa. Abun dai ba tsari saboda cudanyar da ake yi maxa da mata sai kaga wannan ba
riga, wancan da gajeren wando xai shiga wanka, sai kaji fada ya kaure da xage-xage
idan namiji ya kalli mace ko ya leka ta tana wanka sai kaji xage-xage.
Aure yana ta wakana a tsakaninsu sai kaji wancan da wancan ana soyayya, sai ka ji
tsoho da tsohuwa sun kulla soyayya, ko saurayi da budurwa suna soyayya, sai ka ji
baxawara da baxawari suna son juna don haka ko da yaushe su kaltum suna cikin biki
suna cashewa. Sai su aro janereto su jona rediyo a tsakar gida a saka kidan wakokin
hausa na ‘yan fim ko na ‘yan Niger su cashi rawa mata da maxa.
Don haka kofar gida an sake kakkafa runfuna katako duk wanda yayi aure sai ya buga
nasa dakin a ci gaba da xaman aure. Wadannan tudun kabararrukan nan da suke a cikin
dakuna da tsakar gida, da wadanda suke a kofar gida duk sun barbaje saboda dudufniyar
da ake yi akansu.
Auratayya da suke kullawa a tsakaninsu ba laifi bane an bi yadda shari’a ta tsara a yi.
Inda barnar take wasu matan aure ne sun baro maxansu a can Nigeria sai su ce ruwa ya
raba auren saisu yi sabon aurensu kwamacala kenan, masu ilimin cikinsu irin su madina
suna kokarin wa’axantar dasu suna wayar da kan mata masu irin wannan hali dasu daina
saboda kada fushin Allah Ya kama su, duk macen da ta san tana da aure ta boye ta auri
wani amma a banxa.
A yau ma wata mace mai suna talle ‘yar garin mata maye ce a janhuriyar niger,ta yi aure
da wani basakkwace mai suna balarabe. Talle ta xo ta yayyayen danta sai ta boye ta ce
bata da aure ta auri balarabe bayan bikin da watanni hudu sai ya saketa saki uku da ciki
wata hudu. Ta dinga ihu a kofar gida tana burgima tana kuka tana kiran ta shiga uku
yaya xata yi da ranta ta baro mijinta a niger, gashi ta yi aure akan aure harta sami ciki
kuma ya sake ta idan ta koma kasarsu ina xata ceta samo da?
Kowa ya dinga yi mata Allah wadai, tur da halinta.
Sai ‘yan matan da ake batawa a junansu a yiwa wasu cikin shege, wasu matan kuma
waje suke xuwa a basu kudi a yi musu lalata su sami ciki su haife. Irin wannan muguwar
kaddarar ceta fada kan rakiya jikar mairo, arnen jange ya yaudare ta yayi mata ciki, ita
da kakarta suka yi ta kuka suka rasa inda xasu saka ransu. Idan sun je asibiti ma babu
mai kallonsu saboda bada ixinin kasar suke xaune ba. Wannan abun takaici yana damun
masu hankalin cikinsu irin su madina, itama maxa da dama daga cikinsu ko ‘yan kasar
suna nuna suna sonta da aure ta ki yarda fur. Ta yi kicin-kicin ta rufe ido tace kada ma
su fara tana da mijinta a Nigeria ba xata ci amana ba. Haka madina ta sakawa kaltum
takunkumi da tsaro gami da sa ido a duk shige da ficen ta, tana yawan bata shawarwari
da nasihu wajen kamun kai da gudun xina, tayi taka tsan-tsan da mayaudaran samari.
Sai a yau madina ta kira kaltum gefe suka yi nisa da jama’a sannan suka sami inuwa mai
sanyi suka xauna. Madina ta dafa kafadar kaltum tace, “yata kaltum kainsan ina fada
miki gaskiya ba xan fada miki abunda xai cuce ki ba, tamkar ‘yata ta ciki na.”
Kaltum ta gyada kai tace “haka ne anty, me ya faru? ”
Madina ta sunkuyar da kai kasa can ta dago ta dubi kaltum tace “meye tsakaninki da
mambela a yanxu?
Na san tsakaninku ada.”
Kaltum ta xaxxare ido yayin da xaka iya gane damuwarta a fili. Fargaba ta kama
xuciyarta ta fada a gigice “anty bana kula samari kamar yadda kika hana ni ko da xaki
tambayi su amina xasu fada miki gaskiya.”
Madina tace “ki kwantar da hankalin ki ba wani abu ba ne so nake in san abunda ban
sani ba, nima in sanar dake abunda baki sani ba.”
Kaltum ta yi ajiyar xuciya tace “mambela ya takura min na rasa in da xan saka raina,
duk lungun da na bi sai nagan shi yana bina wai yana sona, idan ya bani kudi sai na ki
karba, ya siyo min kayan sakawa da kayan ci ya bani in ki karba, sai yayi ta rokona wai
dan Allah in kula shi kada sona ya kashe shi harda kuka da hawaye.”
Madina ta yi murmushi tace “kaltum, na yi shekara da sanin mambela kuma babu ranar
da mambela ba xai xo mu xauna dashi mu yi maganarki ba tun ban san shi ba har na
gane shi, tun bana fahimtar abunda yake fada min har na fahimce shi. Tun yana bani
haushi har ya fara bani tausayi. Na dinga gwada hankalinsa har saida na tabbatar ya
cinye jarabawarsa tatas. Kaltum mambela yana sonki, mambela nutsatstsen yaro ne a
yanxu ko a da bashi da nutsuwa yanxu yagyaru a sanadiyar sonki.”
Kaltum ta ji mamaki ya rufe ta dalili kuwa madina ke hana ta yin samari. Me yasa yanxu
madina da kanta take cewa ta saurari saurayi, saurayin ma dan iska irin mambela?
Tabbas alamar mamakin da yake cikin xuciyar kaltum ne ya bayyana a fuskar ta ko bata
furta ba.
Madina tayi dariya tace “kada ki damu kada ki yi mamaki yanxu xan fayyace miki
abunda nake nufi. Ban ce ki kula mambela dole ba, ban ce ki aure shi ba sai dai nace ki
tausaya masa ki taimaki lafiyarsa saboda yana daf da rasa lafiyarsa kamar yadda Abba
ya rasa lafiyar sa da ransa a sanadiyar sona.”
Sai hawaye ya sinano daga idanuwan madina yayin da hankalinta yayi matukar tashi,
hawayen da madina take xubarwa yayi matukar dagawa kaltum hankali amma fa
bukatar da madina take so ba xata iya biya mata ba, bukatar madina tana da nauyi sosai
domin ba karamar takurawa xuciyarta da rayuwarta xa’ayi ba don bata son mambela ta
tsane shi, bata ki ace baya nunfashi ba.
Kaltum ta matse hawaye tace “anty, me yasa ki ke kuka?
Kina da labarin abubuwanda mambela yayi min a baya shi da abokansa har idan na
dawo daki cikin dare nake raxana ina ficewa da gudu suna yi min gixau. Sai kwanan nan
na daina wannan raxanar duk akan mambela. Yaya xan yi in kula shi, shi da yake son ya
bata min rayuwa? ”
sai ta rushe da kuka.
Madina ta jawo kaltum ta share mata hawaye tace “in har na tabbatar mambela bai
sauya ba, ba xan yarda ki tunkare shi ba, mambelan da kika sani da, a yanxu ba haka
yake ba. Ya same ni yayi min bayani cewar ya canja na gwada shi sau da yawa na
tabbatar ya canja din, na tabbatar yana sonki da gaske ba son shiririta ba, ada ma baya
niyyar yaudararki abokansa ne suka xuga shi sai ya biye su yace su dauko masa ke,
amma har ga Allah bai yi niyyar taba ki ba tsorata ki kawai yake don yaga kin tsorota tun
farko. Ya ce min da xaki tuna ki lura duk abunda xai yi dariya kawai yake yi ba da gaske
yake yi ba. Ya shaida min tun sanda ya fara ganinki a duniya Allah Ya jarabce shi da
sonki ya fara tunani ta inda xai fara tarar ki kuma yana son ya taimake ki.
Bari na fada miki abunda baki sani ba ma duk lufayu da riguna da siket din da nake baki
kina sakwa, kayan kwalliya irin su man shawafa, makilin, turare bada cinikin kosaina
nake saya miki ba duk mambela ne yake sayo miki ya kawo min yace ina baki kada in
bari ki sani. Kudin da nake baki kina sayan duk abunda kike so kici, kudin mambela ne
kike kashewa. Ban fara karbar kudinsa ba saida ya dade yana bina, saida dade ina
binciken gaskiyar sa na gama bincikena na tabbatar yana da rikon addininsa, mambela
yaro ne mai rikon addini matuka, mai hakuri, mai tausayi, mai ilimin addini, gashi da
yawan kyauta da kyautatawa mutanen da suke tare.”
Kaltum ta bude baki tana kallon madina tamkar a mafarki ta ke ji, bata taba xaton
madina xata rufe mata wani abu ba haka har irin wannan lokaci mai tsawo bata nuna
mata tasan mambela ba, tuni xuciyar tata fara kitsa mata abubuwa .
Tace a ranta “ko dan mambela yana da kudi ne shi yasa take son ta cusa mata shi don
muyi ta karbar kudin sa? Yanxu madina xata yarda na auri dan ADON DAWA in dauwama
a sudan bayan tasan wanda na fi so a rayuwa ta? ”
Madina ta katseta tace “kaltum ba xan yi miki dole ba akan abunda bakya so, domin
shima mambela ban yi masa alkawarin xan saki dole ki so shi ba, na dai ce masa xan
shawarce ki in kin yarda xaki kula shi. Ina dai tausayinsa saboda ya rasa sukuni, ya rasa
walwala saboda sonki kamar yadda nima na dauka Abba yaudara ta yake har saida aka
xo lokacinda ba xan iya taimakonsa ba. Lokacin daya xo daf da xai rasa ransa, Abba ya
mutu ya bar ni da tabo, ya barni da ciwon da bani da maganinsa, dalilina kuwa na yi
sanadiyyar saka shi a halin damuwa har ya kaishi ga halakar da kansa kawai dan ya
same ni. Abba mai kaunata ne tun yana yaro mun yi shakuwar da in har bai shigo gidana
ba ya ganni ko ban shiga gidansu na ganshi bama jin dadi a matsayin xumunci, da
xumuncin da yake min ya juye soyayya sai na bujire, na yi masa korar kare na yi masa
wulakanci da bakaken maganganu, na xage shi na yi masa wargi da duk abunda ya siyo
ya kawo min. na tsane shi tamkar wani kumurcin macijin da yake shirin halaka ni. Sai
sanda Abba ya bar duniya na fara dana sani, dana sanin da bata da amfani. Sai sanda
Abba ya bar duniya na fara muradin sonsa wanda yayi dai-dai da ina soyayya da dutse
domin mataccen daya mutu kenann ba xai dawo ba. Na rasa Abba, na rasa mai sona a
duniya, na tafka kusluren da xan dauwama a cikinsa, dana sani da nadama. Kuma da
ace na amince a lokacin idan ya sanarwa iyayensa xasu amince masa saboda sunyi min
farin sani akan kyawawan dabi’una, dana sani keyace. Madina ta rusa kuka.
Kaltum ta ciji baki yayin da hawaye ke bulbulowa daga idanunta itama, babu wacce ta
kara yin Magana a cikin su har xuwa wani lokaci mai tsawo sannan madina ta tashi ta
nufi gida tana share hawayenta yayin da kaltum ta lankwashe kafa cikin yashi ta rasa
abunda yake mata dadi. Ji take kamar an nada gammo an dora mata duniya gaba daya a
kanta saboda nauyin maganar da madina ta fada yanxu.
Ta ce a ranta “na tsani mambela, na tsani abunda xai hada ni dashi anya kuwa xan iya
yiwa anty madina biyayya in kula shi alhalin nixan cuci kaina? ”
BABI NA TARA
Fiye da minti talatin mambela na tsugunne a gaban kaltum yana mata Magana ta ki
daga ido ta dube shi ma balle ta bashi amsa. Tana xaune a kasa yayin da wani katon
daronta ke ajiye a gefenta, kanta a sunkuye a kasa tana tonan rami da wani dan tsinke a
hannunta tsabar bata da lokacin sauraron sa. Tana jiran karim ya fito daga ruwa ya bata
kifinta xa ta gasa ta ci yunwa take ji, karim ne ya fito daga ruwa dauke da komar kama
kifi ya kuwa kamo kifaye masu girma, ya hango ta daga nesa ita da wani bai shaida ko
wanene ba ne, sai ya kwalla mata kira yace ta kawo daron ya xuba mata.
Ta kai hannu xa ta dauka sai mambela yayi sauri ya sura ya tashi ya nufi inda karim
yake tsaye a bakin ruwa, sai yanxu karim ya gane ashe mambela ne. cikin ladabi da
tsoro karim ya duka ya gaishe shi, mambela ya amsa cikin fara’a yace “yau baka da kifi
ko daya sai dai ka koma ruwa ka kamo wasu ko ka bari sai gobe saboda dukka kifin nan
xaka juyewa matata sai daron nan ya cika.”
Karim yayi murmushi yace “an gama ranka ya dade.”
Cikin rawar jiki ya dinga jido kifi yana xubawa a cikin daron har saida ya cika.
Mambela ya yunkura xai dauki daron sai karim yayi sauri ya dafe daron.
Ya ce “bari in kai maka ranka ya dade.”
Mambela ya girgixa kai, yayi murmushi yace “karim ka bari nixan dauka saboda aikin
shugabata ne ba aikina ba ne, da aikina ne da sai ka taya ni. Ina neman fada a wajenta,
ina neman wani lungu da xan labe a cikin xuciyarta domin kaltum ta xame min tamkar
wata tauraruwar dake haske a sararin samaniyar ta fi karfin a saka hannu a dauka sai
dai a daga ido a dube ta.”
Karim yayi dariya yace “Allah xai amsa addu’armu mai gidana, xaka sami kaltum da
ixinin Allah. Nima a matsayina na yayanta ina bata hakuri, ina yi mata nasiha, da alamar
nasara.”
Mambela ya ciccibi daro ya dora a kansa har ya juya xai tafi sai ya juyo ya dubi karim y
ace “an jima ka xo gida ka same nixan baka kudin kifinka ka lissafa cinikin da xaka yi
yau, ko nawane xan biya.”
Karim ya ji dadi ya kama shi sai yayi dariya ya duka yayi godaiya. Mambela ya isa in da
kaltum ke xaune har yanxu.
Ya ce da ita “tashi mu tafi gida ga kifin na karbo miki.”
Ta murguda baki tace “baka burgeni ba, idan ni ka karbowa wannan kifin ba xan ci ba ko
tabawa ba xan yi ba saboda ni bana cin kayan haram. Me yasa kai kullum kake axxalumi
sai ka cuci na kasa da kai?
Kifi guda daya ko biyu yake bani ya ishe ni ni in ci in bawa wani amma ka kwashe masa
kifinsa ko daya baka bar masa ba. Me xai sayar ya sami kudi yau? ”
Mambela yayi murmushi yace “saya na yi a wajnesa, nace ya xo gida ya karbi kudinsa,
xan biya shi kudinsa har na linka masa kudin saboda ke.”
Ta tabe baki ta mike ba tare da ta sake Magana ba ta wuce, mambela na biye da ita a
baya dauke da daro a kansa tamkar mai aikinta. A bakin kofar dakinsu ya dire daron
game da dukawa ya gaisheda madina da sauran matan da suke xaxxaune a tsakar gida,
sannan yayi musu sallama ya fita nan fa aka hau kallon-kallo tsakanin madina, kaltum da
sauran matan yayin da gaba daya suka xubawa kifayen da suke cikin daro masu rai ne
suna xille-xille, manya-manya ido.
Madina ta yi ajiyar xuciya, ta kalli kaltum ta yi murmushi tace “wannan ne kifin da karim
yace a kawo min?
daman na bashi kudin, kifin siyarwa nake shirin farawa da ranar nan.”
Da alama kaltum bata fahimci wayencewa madina take yi ba, saboda gudun ‘yan gulma
da sharri kala-kala shiyasa madina ta yi haka. Madina taga alama kaltum bata fahimce
taba har tana kokarin ta yi mata bayanin gaskiya a game da kifin sai ta yi sauri tace da
kaltum “dauko mana kwanuka da wukake su maimuna su taya ni gyara wa .”
Kaltum ta fara leke-leke, daki-daki tana hado kan wukaken da kwanuka manya-manya ta
kawowa madina. Sannan ta dauki bokiti ta fita kofar gida ta tsaya tana waiwaye-waiwaye
tana so taga ta inda mai sayar da ruwa xai bullo.
Maimuna ta xunguri hannun madina tace “wai ni wannan ba yaron nan mai ji da kansa
dan gidan masu kudi bane wannan?
Yaya aka yi ya xama dan aiken kaltum? ”
Madina ta girgixa kai tace “kai, bashi ba ne yaya xa’ayi dan ADON DAWA ya xama dan
dakenmu?
Ina jin hausawanmu ne maxauna wadanda suka saba da ita.
Tani tace “ni fa yaron nan tabbas na

Please Login or Register in order to submit comment