Reading adon dawa Chapter 25 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin halin goggo fattu ta
dawo daga makka tace zata dauketa sukoma makkah iyayenta kuwa ko musu bazasuyi
mata ba yarda zasuyi,
sai ta dubi dayan bangaren kuma wato mambela mutum ne mai kyauta da kyautatawa
yana sonta yana bata duk abunda takeso basai ta roka ba sannan ta tuno rayuwarta da
madina a bur sudan rayuwar yanci dajin dadi wasa da dariya da tsalle-tsalle, abinci ya
wadata babu yunwa ko kishir ruwa tace aranta bazan koma Nigeria ba gara ingama
rayuwata a bur sudan...
alhaji Adnan ya katse tunaninta data tsunduma tanayi yace kaltum magana fa nake miki
bakice dani komai ba?
cikin kuka da sanyin murya tace na'am dady,
jin muryan kaltum ne yasa alhaji Adnan doguwar ajiyar zuciya game dayin hamdala a
cikin zuciyarsa domin sai yanzu dayaji muryanta ya tabbatar da cewa da kaltum dinsa
yake magana saboda yana kokonto ko ba ita bace, ya yi farat ya mike daga
luntsimemiyar kujerar daye juyi a babbar offishinsa dake Abuja babban birnin tarayyah
yafada cikin zumudi da farin ciki kaltum kece ?
To naji dadi yanzu abunda nakeso dake shine ki biyo alhaji sa'adu da alhaji jabiru ku taho
nigeria sauran bayanai in anzo za ayishi wahala da gallazawa da su Fattu suke nuna miki
a da ya wuce rayuwa ce mai kyau da kyanciyan hankali zaki samu a Nigeria, me zakiyi
da rayuwar wahala har bara akace kinayi ni, alhaji Adnan ina raye a duniya kaltum kiyi
bara?
InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un..
sai kaltum ta fashe da kuka ta girgiza kai tace daddy ka yafe mini banyi niyyar saba
maka ba, nasan kokarin da da kayi akaina amma bazan iya dawowa Nigeria ba, yanzu
zanbar Khartoum inkoma bur sudan inda nafi sabawa dasu zan auri mambela domin
shine mai taimakona..
acan alhaji Adnan ya dafe kirji yafada cikin gigita kaltum waye kuma mambela ?
Kaltum ta sharce hawaye tace mambela dan ADON DAWA.
ne alhaji Adnan ya sulale yayi zaman dirshan a kafet yayinda yasa hannu ya fisgo hulan
kansa don tayimasa nauyi a halin yanzu wayar ya ajjiye a gabansa yana duba batare
dayasan abunda zai yi ba, ji yake tamkar ya huda wayar ya ganshi a Khartoum kusada
kaltum ya damkota ya dawo da ita gida, zufa yaketa hadawa duk da babbar rigace a jikin
sa ai akwai sanyin split A.C a offishin,
tsabar tashin hankaline kawai kaltum ta mikawa mai kibar wato alhaji sa'adu wayansa ta
koma bayan mambela ta labe har yanzu mambela acikin rudani yake don bai tsinci
kalma daya ba a cikin duk wannan bayani da akeyi ba, ya juya ya dubi kaltum cikin
harshen larabci yake tambayanta wai meyake faruwa ne?
saita rushe da kuka yayinda kukanta yake sake daga masa hankali.
alhaji sa'adune ya duba wayarsa har yanzu sekonni na tafiya ma'ana alhaji Adnan yana
kan layi saiya kara wayar a kunnensa ya dinga magana sautin maganan ne ya ankarar
da alhaji Adnan cewar su kaltum nakan layi basu kashe ba, saiya rarumo wayar ya kara
ta akunnensa muryan alhaji sa'idu yaji yana magana, alhaji sa'adu yace yanzu ranka ya
dade haka za a kyale yarinyar nan tayi abunda ta ga dama ?
Mufa da muke zaune a sudan mu mukasan wahala da wulakanci da mutanen mu suke
gani,
alhaji Adnan yayi tambaya cikin fushi wai wani irin yare takeminne naji tace mambela
zata aura kuma wai daga ADON DAWA anya kuwa ba aljanine ya auri yarinyannan ba
domin a bil'adama babu mai suna mambela kuma aduniyan nan kakaf ban taba jin wata
kasa ADON DAWA ba saidai in a garin aljanu, don haka kuriketa kada tashiga daji bada
mutum take zama ba.
alhaji sa'adu yayi dariya ya subuce masa yace ranka ya dade mutum ne mambela, ADON
DAWA kuwa kabilarsu ce, a bur sudan suke.
alhaji Adnan yace kai ya akayi ka sani ?
kana ganin mambela da idonka ko itace take fadamaka ?
Alhaji sa'adu yace ina ganinsa alhaji.
"alhaji adnan yace ka tabbata shi mambela datake fada kana ganinsa?
Alhaji sa'adu yace tabbas mutum ne saidai idan kuka kuskura kuka bar yarku ta auri
wannan dan ADON DAWAn to mu'amalanku da ita har abadah, a cikin dawa suke rayuwa
gidan katako da 'kaya, abincin su dabino da madarar shanu ce kawai.
hankalin alhaji Adnan yakara tashi baisan sanda ya yaye babbar rigar sa ya wurgarba ya
mike saye yana magana cikin daga murya da dukan bango har ma' aikatansa suka dinga
rugowa a guje zuwa offishinsa don suga abunda yake faruwa sunsan ba lafiya ba, basu
tabajin yana irin wannan hayaniya ba da daga murya kasancewar mutum ne mai sanyin
magana cikin kamilalliyar murya, mutum mai hakuri da fara'a yau bacin ran kaltum yana
sashi ruri tamkar zakin da yaga nama,
alhaji Adnan yace alhaji sa'adu da kai da alhaji jabiru nabaku amana kuma kun karba
nace ku yanke da kanku yawan kudin da kukeso da kanku kunyi kokari kunnemomin
kaltum kamar yanda kukace inyi zamana basai nazo ba zukuyimin komai gaku ga kaltum
ga kuma aljanin saurayin ta mambela kuna tare ni ina Nigeria sannan zaku dinga
tambayana abunda zakuyi?
alhalin kunsan ra'ayina shine ku kawo mini kaltum gida ko tana dariya ko tana kuka duk
yanda zukuyi kuma duk yanda za ayi karkubar kaltum ta subuce muna bukatarta anan,
idan kwatarta zai muku wuya to ku kira yan sanda su kaiku kotu a fara shari ' ah nikuma
kan a gama zanshigo sudan din ayi dani kungama aikinku.
alhaji sa'adu ya tuna makudan kudinda alhaji Adnan yayimusu alkawari mai dumbin
yawa sai jikinsa ya hau makyarketa kaikace dan taure ne.
yace alhaji Adnan kwantar da hankalin ka daman ra ayinka nakesonji ko ka canja kuma
ina neman izini kar rigima ta kwabe kace baka sani ba ace mana mu masu satar mutane
ne hukumar sudan kuwa tanada zafafan hukunci akan masu aikata irin wannan kazaman
laifi, kabani nanda minti goma zan sake kiranka kaji halinda ake ciki sannan suka kashe
waya.
mambela ne ya fusata ya damko gashin kaltum ya wujijjiga yana magana cikin gigita
dazubo da hawaye mai yawa yace kifamin abunda yake faruwa anan kunzamar dani
mushe a tsaye bansan meyake faruwa ba kuma gashi sai anbaton sunana akeyi wai shin
laifi nayi dana baro garinmu nafito nemanki a Khartoum don in ceto rayuwarki da kuma
nuna miki kaunar da nakeyi?
kaltum ta rusa kuka harda kurma ihu kaikace rai ake fitar mata,
fatsuma ta karaso da gudu ta kwaci kaltum a hannun mambela abun mamaki saiyaga
fatsuma kukan takeyi sannan ta fara yi masa bayani abunda yake faruwa,
data kira sunan alhaji Adnan sai ya tuno da sunan wato kishiyarsa don haka sai yayi
shirin gagarumin rigima a zuciyarsa yasan yau za ayi dayan biyu koya kashe ko
akasheshi wajen kwatar kaltum,
sai yayi wani irin dariya mai ban mamaki ya juya yadubi kaltum wanda har yanzu tana
rungume ajikin fatsuma yace kaltum kije kishiga cikin motar can taxi ki zauna gani
zuwa..
jikin kaltum na karkarwa ta juya aguje ta nufi inda motar take yayinda alhaji sa'adu ya
cire babbar rigarsa ya hada da hular dake kansa ya wurgar akasa ya damkara da gudu
ya damko kaltum ta baya saiya fisgota tamkar kaza saboda rashin nauyi..
da mambela yaga haka sai ya fusata ai ko sekon daya ba karaba ya kaiwa alhaji sa'adu
wani dankareren naushi a hanci yayinda jini ya wanke masa fuska nan da nan ya saki
kaltum ya rike hanci ya durgushe.
da abokinsa alhaji jabiru yaga haka sai shima ya ya fisgo hannun kaltum ya tura keyarta
cikin gidan su,
mambela ya yunkura zai hana sai alhaji Sa'adu ya mike a fusace ya cafki mambela da
dambe...
.
Yayin da ni kuma Dan Aunty na tsaya kallon mafadata akan abar kaunata,
Wannan shi ake cewa '' kura da shan bugu... ''
A gama komai nazo na aure ta, shi kenan.
ADON DAWA 31
.
TRUE LIFE STORY
.
jama'a suka farga kan kace kwabo an shiga tsakaninsu,
mata da maza sun firfito, masu wuce a kafa, babura ,keke da masu motoci duk sun tsaya
kallo da neman ba'asi don a sulhuntasu,
zage zage ake tsakanin mambela da alhaji sa'adu yayinda dukkansu jikinsu na tsuma
sunaso a sake su su kaure, zuciyoyinsu sun hargitsa karfine yazo musu yayinda
hannayensu ya hau kaikayi, naushi kawai sukeso sukaiwa junan su,
larabcine ke tashi inda mambela yake dukan kirji yana cewa kaltum tasa ce babu mai
dauke masa ita,
shima alhaji sa'du yana ikirarin baban yarinya ne mahaifi yasa a dauko masa ita don
haka duk kotun da za aje sai dai aje amma bazai bar kaltum ta subuce masa ba, bayan
watanni shida da suka kwashe suna nemanta a Khartoum gida-gida,
malam Abdulkadir aka kira ya fito daga gidansa da sauri hankalin sa atashe ance yazo
ana wani fada a kofar gidansa,
dazu mata ne yanzu kuwa maza ne ke casuwa ransa abace sai karanto InnaLillahi wa
inna ilaihi raji'un yake, yana ta jan dogon carbinsa, yana karasowa ya dubi mambela ya
juya ya dubi alh.sa'adu yaga babu wanda ya sani a cikinsu, sai bacin ransa ya fadada
cikin harshen larabci yace kukuma su waye daga ina ku kazo kofar gidana kuna dambe?
Dazu yan sanda sun zo ana can ana shari'ar fadan dazu ba a gama ba yanzu ma an ce
antafi kira suzo su iske a kofar gidan ne kuma ?
Yanzu daman abun alkhairi zai zama sharri?
don nace duk mutanenmu wadanda ba su da gida suzo su zauna kyauta sai in zama
abun tozartawa a garin nan?
sunan gidana ya shiga tsinuwa a bakin jama'a ?
Alhaji sa'adu ya fara jawabi cikin harshen hausa ya yiwa malam dalla-dalla akan abunda
ake ciki
Kowa ya gamsu don haka kobin ta bakin mambela ba ayiba malam ya yanke hukunci
nan take kaltum baza tabi mambela ba, kasarsu za a mayar da ita domin shima babban
burinsa kenan, duka manyan matan nan da yammata da kananan yaran dake zube a
gidansa su wa kansu fada su koma kasarsu cikin gata da yancin kai.
kaltum tanajin haka saita kurma ihu ta fadi tana kuka, fatsuma na riketa itama kukan
take taya ta, sauran matan gidan kuwa hayaniya sukeyiwa kaltum suna dungure mata
kai suna cewa keba dadinki bane da har kika sami iyayenda suka damu dake su aiko a
daukeki ko ba kece mai kuka da ihuba a sanda kalah ta karbi kudin iyayenki ta arce ta
bar kiba?
Me ya yi miki zafi da zaki koma bur sudan da rayuwa kauyen da babu wuta babu ruwa
babu wayar sadarwa, kakaf garin babu gidan siminti sai na katako, amma ki koma
Nigeria kasarki a najeriyan ma a babbar birnin kano ai kin caba don haka ki tashi kibi
mutanen nan kawai.
cikin kuka kaltum tace saceni zasuyi malam bazan bisuba.
sai jikin malam yayi sanyi ya dubi Alh.sa'adu yace da kamshin gaskiya idan anbi ta
barawo sai abi ta mabi sawu, ku su waye ?
Kuma daga ina kuke ?
Alh sa adu yace nima mutumin kano ne amma bazan ce muku komai ba bari na hadaku
da mahaifinta awaya kuyi magana, ya latsa number alhaji Adnan nan da nan ya amsa
alhaji sa'adu ya ce alhaji rigima fa aketa tafkawa yanzu haka an fasamin hanci yana jini
saidai yarinyan tace bata san mu ba saceta zamuyi shine nakeso kayiwa wani dattijo
bayani wanda kusan kaltum a hannunsa take don ya gamsu, a gabansa abawa kaltum
waya kayi mata magana don idan ita bata san mu ba mu barayin mutane ne kai ai baza
ta kiraka barawo zaka saceta ba, alhaji sa'adu ya mikawa malam Abdulkadir waya suka
dade suna magana daga karshe malam Abdulkadir ya fahimci ashe kaltum jikar fattu ce,
fattu kuwa tare sukayi wasa a zangon Daura .
don haka ya yarda kaltum tabi wadannan mutane,
da yan sanda sukazo malam ya kora musu bayani cewar ba rigima bace don haka basai
an tafi police station ba,
mambela yanaji yana gani aka tafi da kaltum cikin gidan malam tana waiwayensa
yayinda shi kuma mambela a tsaye, musa da fatsuma da mai taxi suna lallashinsa
hawaye yana zuba daga idanunwansa zuciyarsa kamar zata fashe dan tsananin
tafarfasar da takeyi,
fatsuma ta sharce hawaye tace da mambela yayana mambela zantaimake ka ka sami
kaltum, kamar yadda baka san mu ba ba nida musa ka kudiri aniyar zaka taimake mu.
mambela ya koma ya zauna a cikin taxi gidan gaba yayinda ya jingina da kujera, ya daga
kansa sama ya cije lebe wannan shine ake kira ga samu ga rashi ya samo kaltum da kyar
amma ta subuce masa yana ji yana gani,
mambela ya yunkura zai tashi a fusace musa ya mayardashi,
yace da musa kabarni inshiga cikin gidan malamin nan muyi duk abunda za ayi kosu
kasheni ko in kashe su saboda alkawari nayi saina lahanta duk wanda zai rabani da
kaltum...
musa da direba su kayi kukan kura suka danneshi ya koma ya zauna,
sunfi minti talatin suna bashi baki sannan ya yarda zaitafi,
Su fatsuma suka shiga motar suma aka tafi dasu zuwa tashar jirgin kasa ta zuwa bur
sudan,
cikin hawaye mambela ya zaro kudi mai yawa ya bawa mai taxi, farin ciki ya rufe direba
ya dinga yi masa addu'ar Allah Ya bashi kaltum Ya kwato masa ita daga hannun
wadancan. mambela ya amsa da Ameen ya juya ya dubi musa da fatsuma yace ina yi
muku fatan alkhairi a shirin aure da kuke yi, kuma ina baku goyon baya dari bisa dari
nayi alkawari zan taimake ku ba ku kadai ba ma duk wasu masoya da suke son junansu
zan taimaka masu duk rintsi su auri junansu duk na sadaukar wa kaltum.....
sai hawaye ya kara kwaranya harya kasa ci gaba da magana.
saisuma suka fara kuka don tausayinsa, can ya juya ya dubi musa yace a halin da nake
ciki yanzu bazai bari muyi wata magana ba
saidai kawai duk sanda ka shiryo kazo wannan tashar kahau jirgi kazo Khartoum Tutti ka
gangaro bur sudan kusa da ruwa zakaga garin yan kasarku hausa, sai kace sununa maka
garin yan ADON DAWA gidan sarki kokace musu mambela kake nema, ko karamin yaro
ka tambaya mai shan nono indai ya iya magana to yasan sunan mambela, idan bana
gida to za a rakoka bakin kasuwarmu Jim Arab nanne kadai wajen zuwa na, kazo mu
zauna muyi magana game da auren ku, nayi alkawarin zancanja muku rayuwarku da
izinin Allah amma da sharadi guda daya, idan har kasan bada gaske kakeson fatsuma ba
yaudaranta kake kada kazo inda nake, kaga fatsuma amanace a wajanka inhar ka yarda
ka aureta kaine uwa Kaine uba a gare ta, don batada kowa a kasar nan, tunda wuri ka
fadamin gaskia sai inbiya mata kudin jirgi tabi kaltum su koma Nigeria.
nan take suka zaburo don tashin hankali saboda suna kaunar junansu baza su iya
rabuwa ba sai su duka suka durgusa a gaban mambela suna rantse-rantse cewar zasu
zauna amana,
sai mambela ya sake shiga damuwa yasake tausayawa kansa da kaltum, ku mike tsaye
kada ku damu zaku zauna tare, Allah Ya baku zaman lfy da zuri a ta gari, sukace kaima
Allah Ya baka kaltum ya kwatota ta dawo wajenka ka aureta da yardar Allah.
mambela ya girgiza kansa yace ada dana rabu da kaltum zuciyata ta kasa fitar da ran
zanganta kuma nazo naganta a halin yanzu banji ajikina zan sake haduwa da kaltum ba
har abada, nasan na rasa ta kenan ko bayan mutuwata kuka hadu da ita ku shaida mata
ina sonta bazan daina sonta ba kowa na aura kuma kome na zama a wannan dunia,
kuka da hawaye yabe-yabe mambela , musa da fatsuma keyi harsuka rabu.
ya yanko tikiti yaje yahau jirgi ya zauna yayinda suke tsaye agefe suna daga masa
hannu basu baro tashar jirgin kasa ba sai da jirgi ya tashi sannan suka juyo gida Jiki a
sanyaye.
al amarin malam Abdulkadir dasu alhaji sa'adu kuwa suna shiga gida a falon malam
Abdulkadir aka zauna aka sake mayar da magana da alhaji Adnan a waya aka tsayar da
shawarar kaltum bazata sake fitowa kofar gida ba, a dakin matar malam zata zauna har
tsawon kwana biyu har a gama cuku-cukun tafiya,
malam yace da kansa zai rakasu har filin jirgi yaga tashinsu.
kaltum ce zaune a falon Manal amaryan malam Abdulkadir kenan, budurwa ya aura yar
kasar sudan ce,
kaltum tayi kuka ta gaji don haka ta hada kafafuwanta ta kifa kanta ta kanannade don
takaici, abinci mai lfy ne a gabanta miya ce nashe-nashe da kaji masu maiko amma ko
kallo basu isheta ba balle ta dandana.
Manal tayi larabcin duniyan nan wajen lallashin kaltum don ta daina damuwa taci abincin
nan abu bai yiyuba, saita shiga yi mata nasiha akan to ta tashi tayi sallolin da ake binta
sannan tayi addu'ar abunda yafi alkhairi.
kaltum batada mafita ita kanta tasan addu'a ce kadai mafitarta don haka ta tashi tayi
sallah tana kuka tana fadawa mai duka, amma idan tayi addu'ar Allah Ya zaba mata
abinda yafi mata alkhairi sau daya sai ta roki Allah Ya mayar da ita wajen mambela sau
goma dan shi zuciyarta tafi so.
kaltum tana son mambela a halin yanzu tafi sota zauna dashi data koma cikin yan
uwanta data zauna da alhaji Adnan abun kaunar ta.
tsowon kwana uku kaltum na cikin gidan malam daga daki sai bandaki duk inda tayi ana
biye da ita ana zuba mata ido, a cikin gida ma kenan balle a kofar gida inda yake
dankare da malamai da almajirai ta ina zata fice ai bazai yiwu ba, kamar yadda ba a bari
ta fita ba haka aka hana kowa ya shiga ya ganta, duk irin nacin da fatsuma tayi don a
barta taga kaltum ba a barta ba.
ranarda kwanaki uku suka cika a lokacin komai na tafiya ya kammala alhaji sa'adu ya iso
gidan malam dauke da tikitin tafiyarsu a hannu, yazo ya nuna wa malam yace karfe
takwas na dare ne buking din su,
don haka karfe shida na yamma kaltum dasu malam suka dunguma suka fito yayinda
fatsuma da yan gidansu suka yo waje a guje, waje ya dauka da hayaniya cewa ake ku
fito na cikin gida kaltum zata tafi...
lah kaltum tafiya zakiyi?
da dai sauran surutai irin na mata.
malam ya umurci kaltum da ta shiga gidansu ta dauko buhun kayanta tazo su tafi, sai ta
girgiza kai ta sharce hawaye tace nabarwa fatsuma dukka tayi amfani dasu.
fatsuma ta kamkame kaltum tana kuka tana cewa yanzu kaltum tafiya zakiyi kibarni?
Sai da malam Abdulkadir ya hada da shauda mata carbin hannunsa sannan ta saki
kaltum, dan anyi mata maganar duniyar nan ta saketa taki, malam ya dubi fatsuma cikin
fushi yace wannan yarinya rawar kanki tayi yawa ke kike sake tunzura kaltum kike kara
sata kuka idan bakiyi wasa ba sai na koreki daga gidana yau din nan,
fatsuma najin maganar kora saita nitsu don idan aka koreta yanzu ina zata nufa?
musan nata da take takama dashi su shidane a shago daya suke haya.
a ina za a cashe idan bikinta ya tashi inba a
makeken tsakar gidan nan na malam ba?
saita koma gefe tayi tsuru da ido, da niyyarta dama ta tubure tace saita shiga motar
tabisu airport, kaltum ce ta shiga gaban taxi malam da alhaji sa'adu suka shiga gidan
baya,
yan gidan suna dagama kaltum hannu itama tana daga musu yayinda direban mota ya
fizgi mota,
kaltum kuwa jiniyar kukanta ta barke, malam da alhaji sa'adu kuwa sukace dawa Allah
Ya hadamu inbada kaltum ba sukatayi mata surutu har suka kai filin jirgi suna cewa
inbanda yarinya da rashin hankali ina za a hada zaman sudan da Nigeria?
ke a najeriyan ma yar gata ce yar gidan masu hali zakiyi iliminki asirinki a rufe ki zauna
kina wulakanta kanki a nan?
daga bara sai tsince-tsince a bola.
kaltum dai tayi mukus tana sauraron su kukanne bazata daina ba.
kaltum taga yanda mata suke cin ado a filin jirgin nan na Khartoum ai sai ta raina kanta
ta ganta tamkar daddawa a cikinsu duk da wannan pink lafayan nan da mambela ya siya
musu ita da fatsuma ce ta wanke ta saka takalmin ma sabo ne wanda mambela ya saya
mata ga matar malam ta bata sabon siket da farar t shirt daga ciki ta saka ta cire
yagaggu na da, ashe da bata carallee ba abar gudu da kyama zata zama a cikin jirgi, nan
sabon brush matar malam ta siya mata ta wanke bakinta tas turare kawai bata samu ta
shafaba saboda yanzu Abbas baya bata, matar malam kuma bata bata ba amma duk da
haka kayanta na kamshin koren sabulu na wanki ,
ina laifinta abunda kaltum ta dinga zaiyanowa a zuciyarta kenan don haka ta saki jikinta
a cikinsu bayan anyi musu screening sai aka yi bording suka shiga cikin jirgi suka zauna
duk da ta taba shiga jirgi tana karama amma sai taga kamar bata taba shiga ba.
Domin ganin jirgin tayi tamkar aljannar dunia do kyau saita tsinci kanta tana mai farin
ciki harda murmushi, Alh sa'adu ya juyo ya dubeta ya tabbatar murmushin takeyi ba
gizau ba yayi dariya yace ja'ira waya fada miki borno gabas take?
ana so a ceto ki kina ki har kika ja wannan aljanin saurayin naki yake kokarin ya cire min
hanci,
sai kaltum ta sha kunu ta tura baki don taji ya fara cewa abun kaunarta mambela
mutunci.
kujeru masu zaman mutum uku ne, alh sa'adu ne a jikin wundo kaltum a kusa dashi sai
wata matashiyar mata mai suna Hajir a karshe, tunda suka zauna Hajir ta dinga
surnanowa kaltum larabci tana jero mata tambayoyi.
kaltum bata bata amsa ba saboda a tunanin Hajir kaltum yar sudan ne hutu zai kaita
Nigeria,
Hajir ta shaidawa kaltum cewa ita yar Khartoum ce ta auri wani hamshakin dan kasuwa a
kano yanzu haka kakarta ce ta rasu tazo tayi gaisuwa zata koma.
kaltum tayi murmushi tace ni kuwa yar kano ce aure ya kawo ni bur sudan mijin ADON
DAWA ne mai suna mambela.
Hajir ta damke baki don mamaki tace keko meya miki zafi da zaki baro kano birnin garin
arziki ki taho sudan a sudan dinma a bur sudan?
alhaji sa'adu ya zabura yace karya fa takeyi bata da wani miji abur sudan.
sai aka hau kalon kalo tsakanin Hajir da kaltum da kuma alhaji sa'adu batare da wani
yasake magana ba a cikinsu.
mamaki mara misaltuwa zaka iya gani a cikin idanuwan Hajir, ta shiga tunanin meyasa
kaltum zata mata karya irin wannan alhali karyan ma bata dadi bace ?
ko kuwa wannan mutumin ne ya ke karya ?
To ko babanta ne yaje ya raba auren ya dauko ta zai mayar da ita garinsu ita kuma tana
son mijin ta?
kwarai haka ne ma don daga gani kaltum anga wanda ta kwaso da talauci. abun da Hajir
ta dinga sakawa kenan a cikin ranta kenan,
jirgi ya tashi ya bar Khartoum ya lula cikin gajimare da izinin Ubangiji yayinda fasinjoji
suka hau tofa addu ar nan ta matafiya wacce shugaban halitta ya koya mana, '' Allahu
Akbar, Allahu akbar , Subahanaanal laziii sakkhara lana hazaa wama kunnaa lahu
mukrinina wa innaa ilaa Rabbina lamunkalibuuna, Allahumma innaa nas'aluka fii
safarinaa hazaa birra wat tak'waa wa minal amali maa tardha ,Allahumma antas saahibu
fis safari wal khaliifati fil ahlil ,Allahumma innii a uzu bika min wa,asa'a'is safari ,wa ka
aabatil manzari wa suu il munkalabi fil maali wal ahali.''
yayinda kaltum ta runtse ido hawaye mai zafi ya dinga zubowa daga idanuwanta tana
fadin wayyo mambela a zuciyarta.
KANO NIGERIA
misalin karfe shida na safiyyan alhamis jirginsu kaltum ya sauka a malam Aminu
international airport dake birnin kano, kaltum ta shaki iskar kasarsu saita lumshe ido taji
sanyi a ranta atake taji ta fara farin ciki zataga kannenta da alhaji Adnan, ta tuno
mahaifiyarta sofi da mahaifinta saleh sai taji tanaso ta gansu ma, tafi kowa sauri wajen
shigewa gaba don saukowa daga jirgi da fitowa daga wajen bincike akayi aka gama suka
fito waje inda kaltum take duban kanawa sai hausa sukeyi yayinda suma suke dubanta a
matsayin bakuwa ba yar kasarsu ba,
musamman da suka ji ita Hajir sun juye harshe suna larabci, Hajir ta rubutawa kaltum
nonbar wayanta a takarda ta bata tunda kaltum ta shaida mata batada waya,
Suna tsaye mijin Hajir da ya yanta biyu sukazo daukar ta, tana murna suna murna ta
shiga mota suka tafi, sha'awarsu ta rufe kaltum ta ayyana a ranta dama ita da mambela
ne suka sami sukuni haka..
kinsan hanyar gidanku idan muka shiga taxi?
alhaji sa'adu ya tambaye ta,
tayi shiru kamar mai tunani, yace idan bazaki ganeba zansaka layina na MTN na
shaidawa alhaji Adnan munzo aiport ya aiko a dauke mu,
kaltum da zabura tace zangane gidan, domin bataso alhaji yazo tsoron haduwarsu take
yanzu, kunyan bijire masa datayi takeji domin
ita kanta tasan baikamata ya turo azo daukarta kiri-kiri tace bataso tazo wajensa ba
tafiso tabi mambela ba, alhaji sa'adu ya tsayar da taxi ya shiga gaba kaltum na baya tayi
tsuru da ido, fargaba ta hadu mata da farin ciki suka cakude da takaicin rabuwa da
mambela, tace da direba nasarawa G.R.A zaka kaimu babu bata lokaci direba ya manna
da gudu yayinda kaltum ta tsura ido a jikin glashin wundo tana duban kanawa matan su
da mazansu yara da manya sai hidindimunsu sukeyi, akasarinsu fara'a garesu kuma duk
sun fito neman na kansu ga kasuwa iri-iri, haka ma'aikatan gwamnati kala-kala.
babu inda yafi kasarku dadi da yanci kaltum tafada azuciyarta yayinda ta hango almajirai
akan bola suna tsintar gwangwanaye, taga ba'a hana su ba kuma zuwa zasuyi susayar
ba bu mai hana su saboda suma yan kasane, sunada yanci ba kamar yadda su aka saka
musu takum-kumi aka tsorata su da hukuma ba,
kaltum tana nuna musu hanyan tiryan-tiryan har bakin gidan ashe bata manta ba, a
tunaninta ba zata gane ba duk a akwai canje-canje a unguwar da gidan amma bata
manta ba, suka firfito daga mota, kaltum ji take tamkar a mafarki data ganta a tsaye a
kofar gidansu, alh sa'adu ya fito

Please Login or Register in order to submit comment