Reading adon dawa Chapter 4 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka yi ta tsayawa a kanta suna tambayarta shin lafiyarta kalau ko jikin ne!
sai ta girgixa kai t ace das u lafiyarta kalau, ba tare da tad ago ido ta kallesu ba.
Hajara c eta fito daga cikin dakinsu ta tsaya akan kaltum ta dade a tsaye tana
harar ta. Kaltum tad ago ido a hankali ta dubi wacce ke tsaye a kanta, kallon da
hajara tayi mata na wulakanci shi yasa ta gane bada alkhairi take nemanta ba don
haka sai ta mayar da kanta kasa ta sunkuyar.
Hajara ta girgixa kugu t ace “kaltum, na rasa robata da gurasa aciki wacce na ajiye
jiya da daddare a wajen shinfidarki.”
Kaltum ta girgixa kai t ace “ba ni na dauka ba.” Hajara ta fusata t ace, “wane
shegen ne xai dauka idan ba ke ba! Ko kin dauka bamu da labarin sace sacen da ki
ke yi a gari!”
Kaltum tad ago da sauri ta dubi hajara hakika ko ba’a fada ba kaltum taji haushin
maganar amma sai ta maida kanta kasa ta sunkuyar. Iya mairo da jikarta rakiya
suka fito suka dubi kaltum suka ce “yauma ba xa ki je bara ba, sai kowa ya tafi
bara an bar miki gidan sannan ki lalube mana ‘yan abubuwanda mka ajiye ko!”
Huwaila t ace ai ba lefin kowa bane laifin madina ce da ta shagwabata, sai ta je
tayi aikatau hard a jido ruwa a biya ta amma ta je ta siyo musu abinci ta kawo su ci
tare shiyasa ma bata fita bara sai taga dama. Taci ta koshi dare yayi ta dinga ihun
karya tana hana mu barci.” Amina ta fito daga daki t ace “idan gari yaw aye saita
kwanta tayi ta barci har yamma mu kuma mu fita nema mu yini muna yawo
lokacinda ya kamata mu kwanta sai ta hana mu barci, gaskiya a raba man daki
dan yanxu ma ciwon kai na ke yi saboda rashin barci.”
Hawaye ya dinga xuba shaf shaf shaf daga idanuwan kaltum. Madina c eta fito
daga wanka sanye take da hijabi sa daurin kirji ta karasoi da sauri inda suke t ace
“haba ku kuwa bayin Allah me kaltum tayi muku a rayuwa da kuka takura mata
haka! Xagin safe daban na rana daban dan kun ga bata magan, ku kira ta
barauniya, ku kira ta ‘yar iska, ku ce mata munafuka. Da me xa ta ji, ciwon dake
addabarta! Baku ganin da xaxxabi take kwana kullum saboda raunin da ke jikinta!
Ku tuna fa ku musulmai na Allah Yan a son kaltum tunda Shine Ya halicce ta. Baku
ganin hakkinta da ku ke dauka xai iya kaiku wuta, shirun nan da take yi tsananin
hakuri ne, hakurin da take yi bata rmawa xai iya sawa Allah Ya yi mata sakayya da
KanSa.”
Maimuna ta katse ta , tace “madina dan Allah kiyi mana shiru ke ba kya ganin
laifin kaltum, ke c ma mai xuga ta har wata rukiyya kike mata wai ita mai aljannu,
mu dai gaskiya tana hana mu barci mun gaji.”
Madina ta ji hawaye yan surnano mata daga idanuwanta dan takaici, ta share
hawaye ta dubi maimuna t ace “haba maimuna ban taba xata ba wannan maganar
xata fito daga bakinki a matsayinki na babba. Shekarunki talatin da biyar kin haifi
kaltum hard a ma wadanda suka girmi kaltum. Kinsan ciwon haihuwa, kin san
dadin ‘ya’ya dan kusan kullum kina kuka idan kika tuna ‘ya’yanki da kika baro, ban
dauka xaki ki tausayawa ‘ya’yan wasu baa she xaki biyewa rakiya, huwaila, amina
‘yan matan da basu taba haihuwa ba!
Ke ma hajara ba yarinya bace tunda kin kusa haihuwar kaltum shekarunki ashirin
dad a biyar ‘yayanki uku. Ba kwa tunanin abunda ka yiwa ‘yar wani sai an yiwa
naku! Iya mairo kin ci amana tunda yarinyar nan ke aka dankawa amanarta da tun
kakarta bata tafi ba sai ki fada mata baki karba ba, amma kika karba ki ka xo kina
banbanta tad a jikarki. Ko ba komai kece wacce kuka fito gari daya ko albarkacin
sanin asalinta da ki kayi bai kamata kiji ana kiranta barauniya ba kiyi shiru.”
Kan kace kwabo hayaniya ya hargitse tsakanin madina das u dukansu. Harda masu
dammara xa’ayi dambe. ‘yan sauran dakunan suka fito maxa da mata suna bada
hakuri, da yake duk fita xasu yi daman sun shirya dan haka aka tura su maimuna
waje ita kuma madina aka tura ta cikin daki, sannan kunnuwansu suka huta da
hayaniya. Kaltum tana xaune har yanxu kantga a sunkuye yake a kasa.
Madina ta dade a daki bata fito ba sai shehshshekar kukanta ka ke jiyowa daga
cikin dakin da alama kuka ta ke yi. Sai da ta tabbatar ba kowa a gidan sais u biyu
sannan ta fito tsakar gida a fusace ta dubi kaltum. Ta kira sunan kaltum, sai tad
ago a gigice hankalinta a tashe ta dubi madina ta amsa kiran da tayi mata.
Madina t ace “ki kula da abunda xan fada miki, ki fahimci a inda kike da kuma
abunda kike ciki. Ki sani xaman nan da mukeyi xama ne na kowa yayi ta kansa.”
Kaltum ta ci gaba da kallonta sokoko da alama bata fahimci abinda take fada mata
ba.
Madina ta ci gaba da cewa “ban hana ki yin hakuri bad an Allah Yana tare da mai
hakuri, yana dad a kyau yin hakuri, amma ina baki shawara ki tashi haikan ki
kwatarwa kanki hakkinki na ‘ya dank e ba baiwa b ace. Saboda me xaki xama
sakarya a cikin al’umma, ki xama juji wacce ake xuba mata shara da aka yayimo
daga ko ina! Yara da manya kowa kaltum yake tsangwama bakya katabus sai
kuka, to ina mai baki shawara ki nutsu kisan abunda kike yi.”
Hawayen kaltum k eta ambaliyar xubarwa shiyasa madina ta kasa ci gaba da
magan sai itama ta fara hawayen.
Madina ta share hawaye da gefen hijabinta t ace “kaltum Allah Yayi miki xurfin ciki
wanda duk irin tambayar da xa’ayi miki baxa ki fadi halin da kike ciki ba,
Abubuwa da dama sun faffaru wanda ya kamata ace kin samu mutum daya kin
fada masa amma kin ki. To ki sani wannan kunshe kunshen da kike yi a xuciyar ki
ba komai xai jawo miki ba sai ciwon xuciya ko hawan jinni. Kina yarinya karama
xa’aji tuf kin fadi xuciyar kit a fashe.
Gara ki dinga amayar da abunda yake damunki, wacce kika san xata rufa miki asiri
ki shawarce ta tunda kin rabu da iyayenki da ‘yan uwanki dole ki samu wasu su
xamar miki abokan rayuwa da aminci.”
Har yanxu kalma daya bata fita daga bakin kaltum ba, hawaye kawai take yi kanta
a sunkuye a kasa.
Madina ta rike kugu ta fada cikin fushi da kunar xuciya t ace “kaltum, waye
mambela!”
Wannan karon a gigice kaltum tad ago ta dubi madina duba mai tafe da tsantsar
mamaki gami da faduwar gaba. Madina ta sake maimaita tambayarta, nhar yanxu
ba amsa daga bakin kaltum tambaya ta uku da madina xa tayi bada baki ta yi
mata ba, wani wani xabgaggen mari ta kifa mata mari wanda said a kaltum ta
kwanta kasa ta rike kunci yayin data fahse da kuka mai tsanani.
Madina ta fisgo hannunta ta xaunar da ita ta rike kunnenta na hagu da karfi har
said a kaltum tayi kara. Madina t ace “waye mambela! Ko kuma wacece mambela
idan mace ce! A ina take! Me yake faruwa a tsakaninku!”
Kaltum tana mai matukar mamaki inda madina ta ji sunan mambela, sai ta shiga
tunanin waye yake labewa har ya san abubuwan da suka faru tsakaninta da
mambela, domin ita bta san abubuwanda take yi a cikin dare ba, bata san tana fita
da gudu ana rike tab a har take ambatar gasu mambela nan xasu kasha ni har
kowa ya ji.
Madina ta tunkude ta gami da rankwashin goshinta t ace “to yau rabuwarmu ta xo
ni da ke, yau ne rana ta karshe dana nuna na sanki, nasan sunanki a rayuwata,
kema kuma koda wasa kada ki sake nuna wa kin taba ganina a rayuwarki.
Hanyarki daban, tawa daban bari ma sauran ‘yan dakin su xo su kore ki daga
dakinmu baxan hana sub a saboda na fahimci xama da irinku hatsari ne, xaki iya
kasha mutum ba’a sani ba saboda xurfin cikinki yayi yawa, bana xama da masu
hali irin naki. Ashe su iya mairo sun fin gaskiya har nake dukan kirji nake fada a
kanki, babu ruwana dake har abada haka ko xaki fice waje da gudu da tsakar dare
ba xan kamo ki ban a daina sai dai in kin tafi a rasa ki, ki koma can wajen
mambela ko mutum ne ko aljani ne, ko matattune oho. Na daina damun kaina a
kanki, na daina tausayinki, na daina shigar miki fada, duk abunda mutane xa suyi
miki ido ne nawa.”
Madina ta shige daki a fusace ta ratayo Jakarta kamar mai shirin fita unguwa ta fito
ta iske kaltum a durkushe a bakin kofar dakin tana kuka mai tafe da ruri
idanuwanta sun yi jawur kallo daya madina tayi mata ta Harare ta, ta dauke kai
tana kokarin kewayeta ta fice sai kaltum ta rike kafarta.
Ta ce “aunty madina, kiyi hakuri ki yafe min abinda nayi miki.”
Madina ta tsaya cak t ace “ai ni baki min laifi ba, shawara na baki baki dauka ba.
Tambaya nayi miki baki amsa bad an haka xama dake ba xai yiwu ba, bana xama
da masu bakin hali da xurfin ciki. Na kasa gane ko ke wa cece, ko ina kika dosa, ko
wane hali kike ciki! Dan haka na rabu da ke kaltum kamar yadda na rabu da
‘ya’yan ciki na a Nigeria. Kinsan kuwa tunda na rabu da ‘yayan ciki nab a xai yi
wahala in rabu da ke ba wacce na hadu dake a hanya a kwanan nan. Ni haka nake
al’amurana xaman yarda na ke yi da mutum, da xarar babu yarda to bana kara yin
ko second daya xan matsa daga wajensa. Kaltum, ko baki bar dakin nan ba hakika
nix an bar miki dakin a tunanina ada na dauka ke mutuniyar arxiki ce, ashe bah
aka ki ke bad an haka na daina tausayinki ki je ki karata.”
Madina na rufe bakinta sai ta fisge kafarta daga hannun kaltum ta juya a fusace
xata fice, cikin kuka mai tsanani kaltum ta sake wawuro xanin madina ta riketa
kam tana cewa ki taimakeni anty madina karki rabu dani ba ni da kowa sai ke a
kasar nan, na yi alkawari xan fada miki komai.”
Madina ta ji sanyi a ranta sai ta juyo, ta daga kaltum tsaye ta karkade mata
yashinda yayi mata bududu a jiki. Ta dawo da ita inuwa ta xauna yayin da itama ta
samu waje ta xauna. Madina ta san har ga Allah tana kaunar kaltum a ranta
tamkar jinin jikinta, tana tausayin rayuwarta dan haka ta kudiri niyyar taimaka
mata ba xata iya rabuwa da ita ba. Ta yi furucin rabuwa da ita dan ta tsorota ta,
tana tsananin son ta ji tarihin rayuwar kaltum da asalinta da abubuwan da suke
faruwa da ita suke damunta. Tana so taji ta ina kaltum ta samo kyakkyawar
halittar ta wacce kyawunta ya xama abun kwatantawa da sha’awa, sannan a ina ta
samo sunanda take kira idan ta firgita wato, mambela! A ina kaltum ta samo ilimin
addini dana xamani haka! Don ta iya larabci tamkar jakar makka. Haka ta iya
turanci tamkar karamar jakar London, shin ‘yar gidan masu hali ce ko ‘yar gidan
yak u bay ice! Tana da iyaye ko kuwa marainiya ce! Meye ya raba tad a kasarsu ta
taho sudan! Shin ita kuwa a matsayinta na yarinya karama meye damuwartada
hart a yadda xa ta yi hijira dan ta samu salama! Anya goggo fatu kuwa kakarta c
eta jinni, amma take axabtar da ita hart a iya tafiyar tat a bar ta bata damu ba duk
da yadda aka san soyayya da shakuwar dake tsakaninta da kakarta!
Amsoshin tambayoyinta suna nan tafe a bakin kaltum, kamar yadda ta ji kaltum ta
soma bata labarinta kamar haka, wanda ke kunshe da duk amsoshin tambayarta
kakaf.
BABI NA BIYAR.
Kaltum ta tsaya tunanin ta inda xata soma labarinta, domin du duniya bata taba ba
kowa labarin rayuwarta ba.
Madina ta katseta t ace, “ina sauraron ki fada min meye damuwarki!”
LABARIN KALTUM
Ta ce “suna na kaltume, sunan mahaifina saleh mahaifiyata kuma safiya sunanta
ana kiranta da sofi.
Mahaifiyata ‘yar asalin wani gari ce da ake kira da IBONKOMO a cikin kasar
Cameroon, mahaifina kuwa dan asalin xangon daura ne. mahaifiyata ta tashi a
marainiya ba uwa ba uba sai ita sai kanwarta daya mai suna joda iyayensu suka
mutu suka barsu, kawunsu yayan mahaifiyarsu mai suna jalo shi ya rike su har
suka girma a bisa amana, ya aurar das u ga wanda suke so ba tare da takura ba.
Mahaifina shima maraya ne tun bayan da aka yaye shi mahaifiyar sat a rasu ta bar
shi a hannun matar babansa ita GOGGO FATTU.
Goggo fatu c eta rike baba na tun yana da shekara biyu har rana irin ta yau ko
tsinke ta ajiye baya tsallakawa saboda tsananin biyayya da tsoronta da yake.
Daman ita bata taba haihuwa ba a duniya, mahaifina shi kadai ne aka Haifa a
gidan su don haka bas hi da abokin shawara sai goggo fattu ko mahaifinsa bai isa
ba.
Hakika tarihi ya nuna mahaifina ya sha wahala, axaba da makircin goggo fattu tun
yana yaro har yau bai huta ba. Mahaifina ma kenan bai isa ba balle matarsa balle
kuma ni ‘yarsa karan kada miya don haka kacokan dinmu sai abinda t ace xamu yi,
sai yadda tayi da mu.
Madina ta gyara xama ta dubi kaltum t ace “na ji asalinki. Amma ta yaya saleh da
sofi suka hadu ita da take Cameroon shi yana xangon daura!”
Kaltum tayi murmushi t ace “mahaifina ne ya je garinsu sofi yawon fatauci, tun
yana yaro yake bin mahaifinsa suke xuwa tare har yake xuwa shi kadai daya gane
hanya, suna shiga da kayanmu na nan gida Nigeria can su sayar sannan su kawo
na can su shigo das hi ta a haka suka hadu. Aure kamar xai yiwu kamar ba xai yi
wu ba, Allah Yasa ya yiyu aka yin ammadukka bangarorin biyu ba’a son ransu ba a
bangarensa da bangarenta.
A bangaren su sofi suna ganin hatsari ne su dauki ‘yarsu su bawa bako wanda ba’a
san asalinsa ba, haka suma danginsa suke ganin duk ‘yan matan das u ke xangon
dauura ya rasa wacce xai aura sai ya fita wata kasar sannan xai yi aure. Karfin
addu’arsu su masoyan da tsananin rabon haihuwa daya rantse sai aka yarda aka
daura auren. Amma fad a farko dangin sofi basu yarda ya taho da ita ba sai dai ya
kama haya a can ya ajiye ta, yana xuwa yana dawowa said a ta shekara sannan
suka yaba da hankalinsa na ladabi, amana da rikon gaskiya. sannan aka sami
wadanda suka san asalinsa ‘yan xangon daura amma maxauna garin su sofi sun yi
gidaje, sun yi aure, sun hayayyafa sannan aka bari ya taho da ita. ‘yan uwanta
suka rako ta har xangon daura suka ga mahallinta da ‘yan uwansa sannan suka
tafi suka bar ta a lokacin tana dauke da karamin cikina.”
Madina ta nisa t ace “to naji yadda iyayenki suka hadu har suka yi aure. Da
babanki ki ka yi kama ko da mamarki!”
Tambayar madina ta bawa kaltum dariya, sai ta kyalkyale da dariya sannan t ace,
“da mama na nayi kama sak babu inda na baro ta, idan kika ganta kika ganni idan
baki lura ba sai ki kira tad a sunana ko ki kirani da sunanta saboda bat a da kiba
kma ba tsufa ba. Kamar yadda na fada miki fulanin Cameroon ne danginta
kyawawa ne masu tsananin farar fata sai ka dauka larabawa ne, gashinsu har
baya. Banyi kama da mahaifi nab a kwata kwata saboda shi baki ne, amman kanne
na biyu sun yi kama das hi sak”
Madina tayi murmushi t ace “yaya xaman sofi ya kasance a xangon daura!”
Kaltum tayi murmushi t ace “gidan kasa da katangar xana gadon mahaifi na ke
nan anan aka kai sofi, tana xaune a daki daya, goggo fattu a daki daya don a
shekarar da aka yi auren baba na mahaifinsa ya rasu. Don haka goggo fattu ta
sami filin casa sofi da saleh, sai yadda take so xa’a yi, sai abinda t ace xa suyi.
Babu wahalar da sofi bata sha ba, ga cikin fari a wajen yarinya ‘yar shekara goma
sha hudu, har ciki ya tsufa kuma ta hana a kai ta garinsu ta haihu. Da watan
haihuwarta ya kama kawu jalo ya aiko da matarsa Asta da ‘yarsa Ladi su xo su
dauko safi ta haihu a gida amma goggo fattu tayi musu dadin baki luf luf wai sofi
‘yar t ace tamkar wacce ta Haifa a cikinta don haka su bar ta a wajenta xata kula
da ita sosai. A haka suka hakura suka tafi suka bar ta suna ta yabon kirkin goggo
fattu, ita kuwa sofi tsoro ya hana ta fada musu gaskiya.
A cikin dare nakuda ta tashi sofi daga barci sai ita sai saleh, tashin farko daman
dakin goggo fattu saleh ya nufa da gudu ya buga mata kofa ya sanar mata cewar
sofi tana nakuda. Ta xage shi tsaf wai bashi da kunya meye abin gigicewa har ya
fada da bakinsa matarsa tana nakuda. Ya sunkuyar da kai kasa yana bata hakuri,
ta umurce shi day a fice daga gidan kada ya dawo sai gobe da safe.
Yana fita ta rufe kofar gidan sannan ta leka dakin sofi ta isketa a tsugunne ita
kadai tana murkususu, tana ganin goggo fattu sai ta fashe da kuka ta hau kiran
sunanta, amma goggo fattu ta tabe baki t ace “ki bar kiran sunana ma don ba xan
shigo inyi ta fama da ke har gari yaw aye ba, haihuwar da bata da tabbas xata fito
ko ba xata fito yanxu ba.”
Ta juya ta koma dakin ta tayi kwanciyar tat a bar ta a wannan halin. Allah cikin
ikon Sa ta haihu ita kadai, jaririya ta fito fuk akan tabarma gtana tsala kuka haka
mabiya ma ta fito . sofi ta rasa yadda xata yi da ni sai ta sami leda ta kwashe
mabiyar da jaririyar ta rufe a leda fuskata ce kadai a bud eta dora ni akan gado ta
xauna a gefena tana ta kuka har gari yaw aye tangarai sannan goggo fattu ta
shigo dakin ta iske halin da muke ciki. Jaririya a kunshe a leda ga cibiya nan ba’a
yanke ba a jikin mahaifar sai jini jage jage. Duk idanuwana, hanci na da
kunnuwana duk busashshen jini ne.
Ta dau dogon salati ta dinga dimawa sofi duka a baya tana kiranta munafuka so
take ta ja mata xagi a gari a c eta kasheta ta kasha jaririyar. Wai me yasa da
haihuwa ta xo bata kwalla mata kira ba ko ta xo ta kira tad a kanta ba, xata xo ta
kunshe ‘ya a leda ba’a yanke mahaifa ba alhali mahaifa shanye jini take.
Tayi tax age xagenta tana borin kunya sannan ta yanke cibiya, tayi ma ‘yar wanka
ta gyara mai jegon sannan ta bude gida mahaifina ya shigo ya iskemu tsaf.
Haka danginsu su kayi tayi mata sannu da kokari yadda ta karbi haihuwar sofi
tamkar ‘yar cikinta don sun iske mai jego sumul da jaririyarta kalau.
Bayan an yi suna aka saka min Ummu Kaltum sunana da goggo fattu ta xabar
musu kenan wai sunan mahaifiyarta ne, basu isa su saka sunan mahaifansu bad a
suka rasu tuntini. Sai dangin sofi suka xo suka dage xasu tafi da ita da kyar goggo
fattu ta bari suka tafi da ita, mahaifina ya fi son haka daman. Bata dawo ba said a
nayi wata uku nayi kwari sannan muka dawo xangon daura tun daga lokacin na
fara shiga halin da nake har yanxu yak e bibiyata a rayuwata.”
Tab ashe haka wasu suke da busashshen imani!!!
Allah Ka sanya mu pi karpin xukatan mu, sannan Ka dada kare mu daga sharrin
miyagu.
Se a saurara nan gaba domin jin yadda ta

ADON DAWA 7
.
.
“kamar yaya halinda kike ciki har yanxu yake bibiyarki!”madina ta tambaya cikin
rudani kaltum ta xubo da hawayenn daya cika mata ido tace “goggo fattu ta hana
mahaifina ya dauke ni balle yayi min wasa ko ya rungume ni mu shaku. Ko kallona
yayi sai ta dauki dogon salati kai kace mutum ya kashe. Ta ce wannan ai rashin
kunya ne don haka kwata kwata baya kusanta ta. Haka mahaifiyata bayan nono da
xata bani babu sauran soyayyar uwa da ‘yarta, idan kuwa ta cika daukana da
tattalina sai xagi da Allah wadai take yi mata kala kala. Komai aka yi da ni, sai
goggo fattu tace rashin kunya ne.
Wata rana har kuka goggo fattu ta ke saka musu, ta ce dan bata da haihuwa,a
haka iyayena suka kyaleni, sai yanda goggo fattu ta yi da ni.kar ki dauka kulawar
take bani, sai ta ajiye ni a dakinta in ta kuka, sai taga dama sannan tace sofi ta
dauke nita bani nono. Har aka yaye ni na bar dakin mahaifana xuwa dakin goggo
fattu, ba komai kuma take min ba sai duka da rankwashi musamman idan nayi
fitsarin kwance, aka ce komai sanyin asuba xata kore ni waje tsirara bayan ta xane
ni.
A lokacin karayar arxikii ta far wa baba na bashi da cin yau bare na gobe sai ya
nemi shawara xai sayar da kiwonsa da mahaifinsa ya bar masa gado, akuyoyi da
yawa da gonaki xai yi jari, sai ta ki amincewa t ace bakin ciki yake yi don ta xuba
nata kiwon a cikin nasa shine yake so ya tona mata asiri a garin ace daman duk
tulin akuyoyin nan ba nata ba ne don tayi karya t ace duk nata ne. muka dade
cikin rashi da fatara da yunwa har Allah Yasa kawu Isiya kanin mahaifin babana ne
yayi masa hanya ya samu aikin gadi a kano,ya tafi kano amma ya bar iyalansa a
xangon daura.”
Madina ta gyara xama ta gyada kai ta ce “lallai yanxu xa’a fara labari. Daga nan
yaya aka yi? ”
Kaltun ta girgixa kai ta ci gaba da Magana cikin marainiya murya ta ce “duk
karshen wata yake xuwa ya kawo mana kudi albashinsa don mu ci abinci amma
yana tafiya xata juya akalar kudin tayi sha’anin gabanta dasu .kuli –kuli guda uku
shine bincin mu na rana, tuwon dawa da miyar kuka lami ko wace babu shine
abincin dare, dumamensa sine abincinmu na safe.Duk muka rame muka lalace ita
kuwa har tsire da kaxa take ci acikin shinkafa muna kallonta.
Da mahaifina yaga alamar mun rame sai ya dinga tambayar mahaifiyata ko lafiya
muke rame wa?
Ta boye masa don itama irin halinta kenan ba xa ta yi Magana ba ko abu xai kashe
ta, sai a makwabta aka fada masa duk abunda yake faruwa damu. Ya samu goggo
fattu yace yana so ya tafi kano da sofi itama ta samu aikin wanke-wanke da shara
duk wata xasu dinga hado mata albashinsu duka suna kawo mana ni da ita. Tuni ta
amince sofi tabi mijinta suka tafi kano suka barni cikin wahala Kaman ta kashe ni
tsunma ma ya fi ni nauyi, ga ciwuka kala-kala kullum.
Mahaifina bai fasa xuwa ba, duk wata xai shiga mota ya xo xango daura ya kawo
kudin albashinsa fiye da rabi. Ina ganinsa sai in hau murna ina kiran “ga baba, ga
baba.” Amma sai ya ture ni gefe in fadi kasa, ya dauke kansa baya kallon in da
nake saboda kada goggo fattu t ace yayi rashen kunya.
Ina shekara uku yunwa da ciwon kyanda suka sa ni a gaba na rame sai kashi da
fata, ido yayi min xuru –xuru kamar mai ciwon kanjamau sai ka kirga kashushuwan
dake kirjina. Sai in suma sau biyar a rana wanar ba xan rayu ba sai ta ji tsoro kar in
mutu a hannunta don haka sai ta nemi kawu isiya ya kawo mu har gidan da
mahaifina yake gadi, suka ci sa’a kuwa a boy’s kuarter gidan suke xaune da
mahaifiyata.
Ta hau fada hard a kumfar baki tana cewa sun gudo kano sun xo sun kwanta sun
bar ta da wahala tana fama da ‘yarsu ko barchi bata yi, don haka ga ‘yar sunan su
rike kayansu. Ta jankwabar dani da kayana ta juya ta tafiyarta, suna binta suna
rokonta ta xo ta huta ta ci abinci, tace ba xata dawo ba dole ta tilastawa kawu
isiya dole ya taso suka hau mota suka koma xangon daura.”
Madina ta girgixa kai t ace “daman haka halin goggo fattu yake! Ni fa na yi
mamakin ace kaka ce take tsangwamar jikarta haka yadda naga tana kyararki a
mota.”
Kaltum ta surnano da hawaye ta cika mata ido ta ci gaba da cewa “mai gidan da
muke gidansa sunanasa Alh Adnan Mahbub, shi da matarsa Salaha sai ‘dan su
daya Mashkur. Mashkur sa’ana ne shima a lokacin shekarunsa uku kamar yadda
shekaruna uku cur a duniya. Alh Adnan yana da arxiki mai yawa duk da matashi ne
a lokacin, aurensa ne na fari kuma haihuwarsa c eta fari bai wuce shekaru talatin
ba aduniya, matarsa kuwa baxata wuce shekaru ashirin da uku ba don da haka
kusan sun girmi iyayena ma. Suna xaune a kataferen gidan, kerarre mai girman
gaske yayin da mu kuma muke xaune a boys quarters in gidan.
Alh Adanan na ganin halinda nake ciki na rashin lafiya sai ya ji hankalinsa ya tashi
ya umurci direban saya dauke mu ya kai mu

Please Login or Register in order to submit comment