Reading adon dawa Chapter 35 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta basu jari da wajen zama saesu musulunta gobe ma idan taje wata zata jawo ta
taho da ita, da kadan kadan suketa musulumta har suma wadanda suka musuluntar
suke jawo wasu zuwa musulunci.
yayanta Abdullahi shima da shawarwarin Madina yake aeki tasashi ya musuluntar da
uwar gidansa uwar 'yayansa da 'yayansa kakaf sannan tasa ya kwaso su dukka suka
kauro Abuja suka shiga islamiyya suka sami ilimin addini.
haka ' yayanta Abdul Malik da Abdul hakim sun kammala karatun digiri dinsu Abba ya
samar musu da aeki, anan Abuja suke rayuwarsu yayindaduk wanda yasan shahida
abaya zaeyi wuya yaganeta yanzu, Abba ya dauketa yadawo da ita gidansa yace shi zae
riketa ko bayan ran Madina zae dau nauyinta harsae ya aurar da ita,
tashiga jami'ar A.B.U zaria tana karanta medicine.
Allah mai kyauta a duniya mae azurta wanda Ya so a lokacin da Yaso, tsarki ya tabbata
ga Ubangijin talikae.
misalin karfe tara na dare mambela ya dawo
daga wajen aeki daman yanada nasa makullin don haka sae ya bude kofar gidan ta baya
ya shigo kamar yanda ya saba ganin kaltum a falo tana zaman jiransa yau sae bai ganta
ba sae yayi tunanin ko tana daki ya leka dakinta yaga babu kowa daddy ne kawae ke
kwance a dan gadon sa yana barci saeya leka bandaki batanan sai yace aransa to tana
dakinta abun mamaki anan ma batanan ya leka kicin babu kaltum babu dalilin ta sai yaji
hankalinsa ya tashi nan da nan ya zaro wayarsa daga aljihunsa ya fara kiranta sai ga
wayarta akan kujerar falo ba ta tafi da wayar ba, kamar wanda akace masa ya leka
barandar waje sae kuwa ga kaltum tsaye ta rike karfen baranda tana kallon kasa, ya
sadada yaje ta bayanta ya rufe mata ido ta zabura ta waewayo a firgice kamshin turaren
jikinsa ne ya tabbatar mata da cewa rabin ranta ne mambela sae su dukka sukayi dariya
yayi mata rada a cikin kunnenta cikin wata tattausar murya cikin harshen hausa,
kaltum tunanin kike yi anan?
akwae abun da na rage miki a rayuwa wanda
yake damunki baki fada min ba?
ko akwae wani hali wanda ba kyaso in daina?
kada ki boye min komae my love.
Sai tayi murmushi ta lumshe ido ta dubeshi sannan ta nuna masa kasa tace duba kaga
Dubai da daddare haske tar kamar da rana sbd fitilu duba kaga kololuwar benen mu
hawa harna ashirin, duba kaga motoci suna yawo a kwalta tamkar tururuwarda suka biyo
layi haka muke hango su daga sama, ga teku mae fitar da iska lafiyayyiya yana kusa da
mu saena tuna da Bur Sudan a inda muke bara muke kwalfo ruwan gishiri muna wanka
da wanki muna barar kifi, yau gamu a Bur Dubai wancen duhun ya zama haske
takalmanmu da yake tsinkewa mu daure da leda saboda yashi yanzu anan sae dai
motoci su zagaya damu tsakaninmu da ruwa sai dai mushiga jirgin ruwa ta tuka mu
shakatawa, gasashen kifi a faranti turawa zasu kawo mana cikin ladabi su ajiye mana.
Shi ne nake mai godiya da Allah da Ya yi mana wadannan sauyi. Duk inda ka ji balarabe
ya ce bur, to tsallake ruwa ne, don haka nake godewa Allah da Ya rubuto min rayuwa ta
a kusa da ruwa inda na ke shakar sanyayyar iska wacce take fitowa kai tsaye daga cikin
ruwa duk a cikin ni'imomin Ubangiji ne. Maganin yunwa da talauci ruwa ne duk sanda
aka rasa ruwan sama an rasa amfanin gona, idan zuciya tayi zafi, masu iya magana
cewa suke yi, "a yayyafa mata ruwan sanyi."
Mambela ya tuntsure da dariya ya ce, "duk me ya kawo wadannan maganganun? "
Kaltum ta yi fari da ido tace, "idan Allah Ya yi wa mutum wata ni'ima ya kamata ya gode
ma Sa, gobe se Ya kara masa wacce ta fi ta da."
Mambela ya gyada kai, yace "gaskiya ne sai wace ni'imar Ubangiji Ya yi miki bayan
wannan? "
Kaltum tayi dariya ta langwabar da kai ta kashe murya ta ce "daga cikin ni'imomin da
Allah Ya min, Ya azurtani da miji na gari, mai son ya ga farin ciki na, sai nima Ya jarabe ni
da tsananin son sa har na ke ji a jiki na, ba zan iya rayuwa ba idan ba ya nan.
Idan baka manta ba, a shekarar da ta gabata, tafiya ta kama ka zuwa Abu-dahabi har ta
tsawon KWANA ASHIRIN DA HUDU, sai na ji na damu, tun ina daurewa har ya kasance
ruhina ya tafi Abu-Dhabi ranar da ka yini baka kira ni ba, nima na rasa ka a waya, sai na
fara tunanin me yasa mambela be damu da ni ba?
Sai na fara tunanin ko dai, GANGAR JIKIN SA NA AURA, na fashe da kuka na dauki gyale
na zan fice daga gidan don banga amfanin zamana ba inason maso wani har naje kasa
saina tuna YARENA ADDININA bazan iya fita bada izinin mijina ba idan wani abu ya
sameni a titi INA RUWAN WANI babu wanda yasanni bubu mai taemakona don haka na
dawo gd na zauna nayi tagumi ina tunani naga dai KAI KAFI CANCANTA ka ce to ni daga
cikin wannan hali dana shiga kuma kai kadai nakeso a rayuwa tamkar na taabu na shiga
daki na canja kaya na caba ado da wannan tsadaddan leshen daka siya min na saka
gyale da takalmi mae tsinin gaske, baya ga jan baki da hoda dana rambada na dubi
kaena a madubi naga nayi kyau matuka na juya zan fita falo a tunanina kana can in
nuna maka kwalliyar sai na tuna ashe bakanan sai nayi turus nayi kwalliya a dawa kenan
babu mai gani na, wannan shine ADON DAWA sai na sulale na fada akan gado na goge
kwalliyar na rusa kuka mai tafe da hawaye sai na naji wayata tana ruri a falo na ruga da
gudu na dauka sai na duba nace a raina mambelane ina amsawa sai na jika kace ke
bude min kofa na shigo gani a bakin kofa,
ina bude kofa sai na ganka, dan farin ciki bansan sanda nayi ihu nayi tsalle ba ina
maraba da dan ADON DAWA.
mambela yayi dariya yace lalle kin iya hausa bayanan naki sunyi min tsauri ashe har
yanzu da saurana ban koyi hausa ba dole sai na nemi sabon littafin nan wanda zai fito
kwanan nan acikin 2011 din nan duk KYAN TALKALMI a kafa ake takawa don in sake
koyan hausa.
sai dukka suka tuntsire da dariya suka kama hannu suka shiga cikin gida asuba ta gari
kaltumbela.
.
KARSHEN LITTAFIN ADON DAWA
ALHAMDULILLAHI,
.

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment