Reading adon dawa Chapter 26 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da naira dari biyar ya mikawa direba sai kaltum ta
zurawa kudin ido tana kallo domin ganin kudin tayi bambarakwai ba irin na sudan ba.
Muhammad da makwabcinsu ne yafara ganinta tsohon saurayin tannan nata, da farko
baiganeta ba yayi mata kallo daya ya watsar sai tayi masa dariya har ya kawar da kai
gefe, saidai yasake waiwayowa ya dube ta domin fararen hakoran nan nata masu
haskawa har yanzu basu dafe ba suna kyalli duk sanda tayi daria, yace kamar kaltum?
ta amsa nice, sai da yahau salati yana mamakin yadda kaltum ta zama haka kamar ba
ita ba, ta rame tayi baki ta zama bakauyiya, tundaganan jikin kaltum yafara sanyi tasan
tazama wata halitta ba irin ta mutane ba tunda har Muhammad bai gane ta ba kuma ya
tsaya yana tausaya mata,
suka tura gate sukaji akulle daga ciki ko bude gida ba ayi ba, bugu daya sukayi saleh
mai gadi ya fito daga dan dakinsa na gadi ya bude musu da sauri da yake daman sun
san da zuwanta don haka yau babu wanda yayi barcin kirki a gidan yaransu da manya,
daga sunji motsi sai kowa ya bude ido,
alwalar asuba kuwa sun yi fiye da sau uku sai su ga ashe assalatu batayi ba saboda
matsuwarda sukayi gari ya waye suga kaltum.
kallon-kallo ne tsakanin kaltum da mahaifinta, hankalinsa yatashi yadda yaga yarsa ta
fige ta zama kaza ita kuma sai taga ya tsufa.
alhaji sa'adu ya fusata yace da malam saleh
matsa mu wuce kazuba mana ido inni ba kasan ni ba ai ita kasanta idan kuma batanan
aka kawoka to yar gidan ne, yar gidan alhaji Adnan ce, daga sudan muke yasan da
zuwanmu,
sai yaga kaltum da mai gadi sun hada ido sunyi dariya kaltum tace kai alhaji sa'adun nan
kaci ka fada, babana ne fa,
ta durkusa ta gaishe shi sai yau yataba ambaton sunanta yana rawar murya yace
AlhamduLillahi, kaltum naji dadin dawowarki da kika dawo kafin in mutu, Allah mai amsa
addu'ar bayinSa, ki yafe mana kaltum..
sai su dukka suka rushe da kuka malam sale yasa hannu ya tashi kaltum tsaye daga
sunkuyon da tayi suka dunguma cikin gida kai tsaye boys quaters ya nufa yana kwalla
kiran sunan sofi!!
cewa yake ku fito ga kaltum ta zo, sofi ta manno da gudu abunka da mara kiba tazo ta
rungume kaltum kuka take ta sharba ita ma taga uwar bari ko ina kunyar fulanin nan?
yayinda kaltum taga dandazon kannenta manya da yara da wasu guda biyu bata san su
ba matane amma ko ba fada mata ba tasan kannenta ne, su kadaine sukayi kama da ita
sak ta rumgumesu yayinda suke rera mata wakarda suka dade suna shiryawa ta
marhaba da zuwanta, dadi ya rufeta ta shiga cikinsu tana tafi itama tana amsawa babu
shakka hayaniyan nan ta isa kunnen makwabtansu ma balle wanda suke cikin gida,
daga ganin luntsumemiyar motar da ke tsaye a farfajiyan gidan kasan mai gidan yana
gari wato alhaji Adnan fari mai farar aniya matashin dattijo mai tumbin naira,

.ADON DAWA 33
.
TRUE LIFE STORY
.
.....ganin su duka sun kalle ta sai ta dukar da kai kasa ta gaggauta barin wajen. Ta shiga
gida ta iske sofi a gaban risho tana faman tuka tuwon shinkafa kamar kullum, kamar
yadda ta saba da yamma. Kallo daya ta yi wa kaltum ta tabbatar tana tafe da damuwa
don haka ta tsaya cak da tukin tuwon tana duban 'yar ta tana sauraron abunda zata
fada. Cikin sanyayyar murya kaltum take tambayar sofi.
"mama, daman Goggo fattu ta dawo daga makka har ma tana kwance a zangon daura
ba lafiya? "
Sofi ta nisa ta ce, "fiye da shekara guda Goggo fattu ta dawo sharkab babu lafiya, babu
hannu ba kafa, ai sai a lokacin muka san ba kwa tare da ita, don mu a tunaninmu kuna
tare. Sannan ta tabbatar mana da cewa ta baro ki a Sudan. "
Kaltum bata sake magana ba cikin sanyin jiki ta wuce zuwa dakinta ta shiga lungu ta
takure, ta rasa abunda yake yi mata dadi. Sai ta ji kuka ya rufto mata wanda yake tafe
da sakonnin zuciyarta kala-kala. Ta tuno azabar da Goggo fattu ta gana mata a baya, sai
ta tuno da ranar da ta shige jirgi ta kyaleta, ta tuno rayuwarta a Sudan ta wahala, sai ta
ji tausayin wadanda ta baro a can a cikin wahala, don haka kuka ya rikito mata ba
kakkautawa. Abayyane take fadin, "wayyo madina, wayyo mambela na, wayyo fatsima ".
Daddy da baba Saleh ne ke zaune a falo suna ta shawarwari kala-kala bayan an gama
shawarar yadda za a shirya tahowa da Goggo fattu sai aka shiga shawarar shigar kaltum
makarantar boko don ta karasa karatunta. Shekaru sun nausa tun da yanzu shekarunta
goma sha takwas kuma daga J.S.S 3 ta tsaya don haka shawarar da suke yi ta ina zata
datsa.
Alhaji Adnan ya zaro waya ya fara bubbugawa mutane daban-daban yana tambayar
tsare-tsaren makarantu daban daban don tantance makarantar da ta dace da kaltum. Ya
nemi shawarwarin abokansa masana makarantu ya hada da shawarwarin shugabannin
makarantu daban-daban, daga karshe ya yanke shawarar ya saka ta a wannan
makarantar da take tashe, wato "crescent". Ajin da za a saka ta ne aka ce sai an yi mata
jarrabawa za a tantance, aka tsayar da shawara jibi littinin a kawo kaltum makaranta
don zana jarabawa.
Alhaji Adnan ya umurci malam Saleh da ya kira kaltum ya shaida mata halin da ake ciki.
Fitarsa babu dadewa sai gashi ya shigo da 'yar sa. Kallo daya zaka yi mata zaka kula da
jajayen idanuwanta alamar ta yi kuka. Ta durkushe a kasa kusa da mahaifin ta wanda shi
ma a durkushen yake suka nutsu suna jiran abun da uban gidan su zai fadi.
Ya sake luntsumewa a cikin lallausar kujerar da yake zaune, yace.
"Kaltum, kukan me kike yi? Ashe har yanzu akwai abunda yake bata miki rai a duniya? A
tunanina kukanki ya kare tunda kika dawo gida ga mahaifan ki, ga mahaifiyarki ga ni
nima ina tare da ku. Me nene matsalarki, ko me kike nema kika rasa in yi miki? "
Sai mahaifin ta ya fara zubar da hawaye, yace
"Alhaji babu gata da kulawar da baka yi mana ba, ko mu muka haife ka ko kai ka haife
mu iyakacin abunda zaka yi mana kenan. Kukan da take yi kuwa ba wani abu ba ne,
maganar Goggo fattu ce da ta ji muna yi cewar, tana kwance babu lafiya, sai dai ta yi
komai akwance a kwashe. Ka san kaltum da tausayi shine ta je daki ta fara kuka".
Alhaji Adnan ya girgiza kai, ya ce "Allahu Akbar, haka mutum ya kamata ya kasance. Ya
zama mai yafiya da maye gurbin mugunta da alkhairi. Ba komai kaltum, ki daina kuka ki
yiwa fattu addu'ar Allah Ya bata lafiya, kuma ki yafe mata domin ta zalunce ki, idan ba ki
yafe mata ba Allah ba zai yafe mata ba. Don Allah ba ya yafe laifin wani, ko yafiyarki
zata sa ta sami rangwame daga ukubar da take ciki yanzu."
Kaltum ta fada cikin kuka.
"na yafe mata duk abunda ta yi min".
Malam Saleh ya dora da, "Alhamdulillah, Allah Ya miki albarka ke ma, Allah Ya baki
'ya'yanda za su miki biyayya ".
Kaltum ta amsa da, "Ameen ". Yayinda Alhaji Adnan ya shaida mata dalilin kiran da yake
yi mata shine, a kan karatu. Ya bayyana mata cewar ta je ta sami 'yar makwabtarsu
Nana ta fara koya mata karatun da ta manta kamar "Maths da English" saboda ranar
litinin zataje tazana jarabawa don asan ajinda za a sata.
farinci mai baiyani zaka dinga hangowa afuskar kaltum kankace kwabo hawayen kuka ya
kafe, idanuwanta sun washe sai
fararen hakwaranta ne ke haskawa afili don
dariyarda take kyalkyalawa, na gode dady inason makaranta daman,
kalmar da kaltum ke maimaitawa kenan ta kaura gidansu nana tana koya mata aikin yan
aji biyar domin aji biyar takeda niyar farawa
duk da a kureren lokacine, kwana biyu kawai
amma yin karatun ya tuttuno mata da abunda ta manta abaya dayawa saboda tunda
taje sudan ko biro bata taba rikewa ba balle tayi wani abu waishi rubutu, ta kanta kawai
takeyi.
ranar litinin duk da alh Adnan baya gari amma yabar musu komai harda Danladi direba
don haka sassafe kaltum ta shirya ta shige bayan mota direba ya kaita makaranta ta
hadu da yan mata kamarta a cikin makarantar tana yi musu kallon suna jin dadi daman
itace su suma sunayi mata kallon yar gata dama zasu sami gatanta yarinya karama da
mota da direba.
a offishin shugaban makarantar aka bata jarabawar ta zauna tayi tsaf ta gama ta mika,
kwanaki biyu kacal suka bata ta fara zuwa bayan sun duba jarabawanta zasusan ajin da
zasu sakata, awaya suka shaidawa alh adnan cewar kaltum tayi kokari ta amsa musu
jarabawan su wasu kuma ta fadi don haka a aji hudu ta cancanta a ajiye ta, ya amince
yace ba damuwa ya riga ya biya kudin komai don haka direba yaje yakarbo mata kudin
uniform da littatafai da yawa,
akace ta fara zuwa duk da haka tayi farin ciki kuma ta kudiri niyyar dagewa wajen gyara
kuskuren jarabobi data fadi,
Dan ladi dai a fakaice yazama direban kaltum aikinsa kawai yakai kaltum makaranta da
sassafe ya dawo gida ya ajiye mota idan karfe biyu na rana yayi ya dauki mota ya
daukota, umurni daga alh Adnan don haka kallo daya zakayi mata ka tabatar rayuwa
takeyi mai dadi da kwanciyar hankali yayinda damuwa ta kau sai kwakwalwa ta washe
karatu tayi ta shiga babu duka babu zagi babu bauta ga abinci a wadace,
kaltum babu sauran kuka goggo fattu kuwa
ankawota asibitin malam aminu kano ana kulawa da lafiyarta duk da akwai wata
tsohuwa a wajen ta kullum sofi sai ta kai abinci, kaltum kuwa duk ranar asabar da lahadi
a asibiti take yini tana taimakawa da dagata abata abinci, kwashe kashi da wankin
fitsarin da take yi a shimfida duk da goggo bata iya magana bakinta ya juye amma da
hankalinta tana fahimtar komai,
saitayi ta kallon kaltum tana hawaye da alama tana nadamar abubuwanda tayi mata
abaya.
BABI NA GOMA SHA HUDU
ranar wata talata da misalin karfe uku na yamma kaltum ta dira a kofar gidan alh Tasi'u
tsohon mijin Madina,
kaltum sanye take da riga da wando sai dan hijabi shine kayan makarantarsu sai bakin
kamvas da farar safa, katuwar jakar littatafanta ta baro a mota da direba a jikin wata
inuwa yana jiran ta, tafiya take tana sanda kamar wacce take tsoro kada akamata
kokuma ince mara gaskiya sai taji tafiya ta bayan ta a lokacin da tashiga zauren gidan
tayi firgigit ta waiga ta bayanta wata yar matashiyar yarinya tagani wacce shekarunta
bazai wuce shekara sha biyu ba amma kallo daya tayi mata taga kamar Madina, babu
tantama yarta ce kaltum taji zuciyarta ta harba don fargaba yadda take duban yarinyar
haka haka itama yarinyan take duban kaltum cike da mamaki, kaltum ta fara magana
cikin tuntuben harshe batare da tasan abun da zatace ba tace yarinya nanne gidan alh
Tasi'u ?
Ta gyada kai ahankali tana mai duban kaltum a tsorace nan ne.
yaya sunanki ?
Kaltum ta tambaya,
cike da murmushi sunana shahida ta amsa mata, sai kaltum ta daina kokonto ta gasgata
wannan itace yar autan Madina.
daga makaranta kike ?
Inji kaltum, shahida ta gyada kai tace eh, kaltum ta lura shahida a tsorace take da ita
domin idan ta matso kusa da ita saita ja da baya kokorin guduwama takeyi, kaltum tace
da ita toki gaida yayyanki Abdul hakim da Abdul Malik, sai shahida tasake dubanta cike
da mamaki ta amsa da cewa to zasuji yayinda ta wuf ta fada cikin gida da sauri,
kaltum ta gaggauta barin zauren don kada
taje ta kirawo yan gidan su fito a tutsiyeta da
tambaya ace meya kawota ?
Tana fito wa sai ta dubi katafaren gidan da yake jikin gidansu shahida tana ganin sojoji
biyu suna gadi ta gasgata nan gidan General Tukur, gidan su marigayi Abba taci sa a aka
wangale get din gidan yayinda wata dambasheshiyar mota kalar (blue black)ta fito daga
cikin gidan wani zankadeden saurayi ta gani a cikin motar sanye yake da jeans da tshirt
baka hade da wani bakin glass a idanuwan sa, kallonda kaltum take masa na kwakwap
shiya jowo hankalinsa ga dubanta shima har ya rage gilashin wundo ya rage tafiya suna
kallon juna, kallon mamaki har sunkuyowa tayi tana lekensa bayan ya wuce ta, yayinda
shi ma ya saita gilashin mudubin motarsa yana hangenta don yaga me take nema,
wacece ita, kuma can yaga ta je a hankali ta leka get din gidansu, sai yaga ta da ka
tsalle ta labe da alama ta hango wani da ga cikin gidansu yana tahowa, tabi jikin
katangar tana shafawa a hankali yayinda takara dawowa kofar gidansu shahida ta tsaya
ta dade sannan ta tafi, yana kallonta ta nufi wata camry ruwan silver ta bude kofar baya
ta shiga ta kame direba yaja suka tafi, mamaki ya kama saurayin nan sai yaji ya fasa
zuwa unguwan ma gara ya dawo gida domin ya tsorata da yarinyan nan yar makaranta
tunda yake ko a hanya bai taba ganin mai kama da ita ba, yayi kwana ya juyo kofar
gidansu masu gadi sukayi sauri suka
bude masa get sai ya canja shawarar shiga gida sai yaji gara yabi bayan yarinyan nan
yaga daga ina take kuma me tazo nema a gidansu,?
saidai kash da yabi inda sukabi sai yaga wayam ko gabas ko yamma baiga ta inda sukabi
ba ya dawo gida cike da mamaki shi kadai da zuciyansa ba tare da yasan yanda zai
baiyana wa wani ba,
kaltum ma ta dawo gida cike da tsansar damuwa da nadamar meyasa bata bi shahida ta
shiga har gidan Tasi'u ba, ta bayyanawa 'yayyan shahida inda mahaifiyarsu take kuma
meyasa bata tsayar da dan saurayin nan ba, da alama dan gidan ne kanin Abba ta sanar
musu labarin da Madina ta bata akan hakikanin gaskiyar abunda ya faru cewar Madina
ba mayyh bace, ba ita ta kashe shiba kamar yanda suke zarginta, ta kuma fada musu
inda Madina take dakuma wahalarda take ciki sai ta tuna sojoji ne, daga sanda basu
gamsu da bayanintaba zasu iya afka mata da duka,
yini guda kaltum tayi cikin damuwa ko abinci takasa ci da zarar kuka yazo mata saita
shige bandaki tayi ta wanke fuska ta fito bataso kowa yagane abunda yake damunta
saboda babu wanda yataba tambayarta labarin sudan a cikin iyayenta.
da yamma makarantar islamiyyah take zuwa ita da kannenta dayake acikin unguwar
makarantar take da kafarsu suke tafiya yayinda direba ya ajiye mota ya tafi gidansa
aikinsa na ranar yakare indai ba oga Adnan bane ya aikesa cikin gari wajen yan uwansa
ba sai dai ko madam salaha ce ta aikeshi gidan kawayenta ko en uwanta itama.
tafiya tayi tafiya kaltum tayi shekara da dawowa daga sudan haka har ta gama aji hudu
tashiga aji biyar, ta sake gogewa ta waye saboda wayayyun kawayenda tayi a ajinsu
kusan duk abunda suke dashi tana dashi saidai inbata fadawa daddy ba zai saya babu
musu, kama daga sutura zuwa jaka da
takalmin makaranta masu tsada kayan kwalliya irin su hoda jan baki da sauransu,
aranar wata asabarce yan aji shida masu fita suke bikin fita (send up)amma da kayan
gida kowacce taje dan haka kaltum tasa dandashen leshinta ruwan zuma mai fulawa
koriya, anyi mata dinkin matsattse na riga da siket yayinda tahau kan wani dogon
takalmi (high hill) saita kara tsayi sosai, gyalenta kore ne ya shiga da adon leshin
yayinda jaka da takalminta suka zama ruwan zuma, ta dandasa wani farin gilashi a
fuskarta, yalo-yalon gashin kanta yazubo zuwa keyarta, tayi fari jawur da ita saikazata
idan kayi mata hausa bazata amsa ba, sun sha party anyi bayanai sannan akayi ciye-ciye
da tande-tande bayan an cashe sai aka watse.
direba najiranta a mota don haka tana fitowa tafada mota bayan ta gaisheshi cikin ladabi
sai ta shaidamasa unguwan yankaba takeso suje , tana fadar haka yasan inda take nufi
domin sun doshi shekara suna zuwa kofar Tasi'u su tsaya tayita leke-lekenta su tafi wani
lokacin ne idan sunga yarinyan nan shahida ta kirata tabata alewa su juya su dawo,
abun ya dade yana cinsa arai idan yayi alamar zai tambayeta saiya fasa domin kusan
kullum idan sukaje gidan a hanyar su ta dawowa kuka ta keyi shi yasa ma baya samun
damar tambayar ta, a yau kuwa ya sami damar jero mata dogayen tambayo yi a jejjere
saidai kash guntayen amsoshi take bashi ya dubeta ta madubi yayi murmushi yace kina
nufin wannan gida damuke zuwa bakya shiga?
kaltum ta gyada kai tace eh nan ne.
yayi murmushi yace yau dai zaki shiga ciki ko?
wannan karon ma gyada kai tayi tace eh zan shiga, Danladi ya fahimci kaltum bata son
tambayoyin nan don haka sai yayi shiru.
a inda ya saba ajiyeta anan suka tsaya wato karkashin wata katuwar bishiya dake kallon
kofar gidan Tasi'u, kaltum ta bude kofar mota amma bata fita ba, idonta ne cak akan
kofar gidan Tasi'u tana fatan kuma tana addu'ar Allah Ya fito mata da Shahida,
Allah mai karbar addu'a sai ga Shahida ta fito burum daga gida sanye da hijabi kuma
rataye da wata jaka mai kama da buhun sikari da alama makarantar islamiyyah zata tafi,
idon shahida akan motar su kaltum a inda idanuwansu ya kyallaro junansu sai su kayi wa
juna murmushi a lokaci guda.
kaltum ta daga mata hannu alamar kira babu
kokonto a zuciyar shahida saita tunkaro inda kaltum take zaune wato a cikin mota tana
isowa saita zube akasa ta kwashi gaisuwa, kaltum tayi caraf ta dagota tsaye yayinda
take rike da hannunta tana mai ambaton sunanta, shahida kin ini lfy?
ina zakijene da rana fatso-fatso?
shahida tayi dariya, islamiyya zan tafi.
kaltum ta tambaya cike damamaki islamiyyah da rana bada safe ko yamma ba?
shahida tace ina zuwa da safe duk ranar asabar da lahadi a taso mu shabiyun rana mu
koma tahfiz karfe biyu zuwa hudu na yamma sannan bayan magrib muje na dare.
kaltum ta gyada kai tace lallai ashe yanzu kinkusa saukewa ki zama malama kamar
mamarki?
shahida ta dubi kaltum cike da mamaki domin a iya saninta matan babanta dukkansu
biyu jahilaine, to wacce mamar ta take nufi?
ta rike hannun shahida tace kinci abincin rana ko?
shahida ta girgiza kai tace a'a ba a gama ba
shine na taho karna makara idan na dawo zanci.
kaltum tace haba dai ya za'a yi ki iya karatu cikinki da yunwa?
shigo mota kici cake da meat pie da lemo a wajen party aka bani, shahida tashiga bayan
mota kusa da kaltum ta zauna,
kaltum ta jawo ledoji dake ajiye a gefenta ta mika mata guda biyu kowanne akwai
dankwalan cake da meat pie ga lemon kwali da daurin cin-cin,
shahida ta tsinci kanta cikin farin ciki ta karba ta fara turawa daga yadda take cusawa
kasan tana tsananin jin yunwa.
.
Allah sarki, dan halak baya manta alkhairi, ko sharri aka masa sai ya saka da alkhairi, ku
dubi yadda kaltum ta sakawa Gg Ftt da alkhairi akan tsiyar da ta mata, haka ma kala,
Kuma ku duba yadda ta sakawa Madina da alkhairi akan erta da irin alkhairin da ta mata.
Da patan xamu ke lura da duk wata gaba na wannan littapin mai kyau domin mu dauka,
kuskuren cikin sa kuma mu nemi tsari wajen Allah da kiyayewa. Kamar yadda yau
kaltum tayi shigar ta bai dace ba, kamata yayi ko wace irin sutura ta sa ta dauko hijabi
ta daura akai ba gyale ba, yadda xai suturta ta a ko ina kuma a ko wannan biki
ADON DAWA 34
.
TRUE LIFE STORY
.
shahida ta tsinci kanta cikin farin ciki ta karba ta fara turawa, daga yadda take cusawa
kasan tana tsananin jin yunwa. dakuma marmarin abunda takeci don bata saba ci ba,
tausayinta ya kama kaltum saitaji kwalla ta cika mata ido tana tuna sanda Madina take
ciyar da ita asanda takejin yunwa, Allahu akbar, haka duniya take duk abunda ka shuka
shi zaka girba idan ka shuka alkhairi shi zaka girba idan ka shuka tsiya ita zaka girba ta
bibiyeka 'yaya da jikokin ka,
Madina ta taimakawa miskiniyar yarinya alokacinda take da iko da halin taimako yanzu
ga yarinyar tazo ta taimaki yar miskiniyar yarta ba tare da ta taba zaton ko amafarki
kaltum zata hadu da ire-iren zuri' arta ba,
kaltum kallon shahida kawai takeyi tamkar Madina take gani a idanuwanta sbd kamarsu
da sak hatta farcen yatsun hannunsu iri daya ne, maganarsu, kallonsu, dariyarsu duk iri
daya, kaunarta ta sake harde zuciyar kaltum kamar yadda takejin Madina a ranta,
shahida ta lura kallon yayi yawa saita fara takura tanajin kunya,
kaltum tayi sauri ta kawar da idanuwanta kasa, can ta dago ta dubi shahida tace ina
Mamar kine?
shahida ta kora lemon kwali tace tana gida.
kaltum ta girgiza kai tace ba sa'ada ba ina nufin mamarki data haifeki Madina.
shahida ta dago da sauri ta dubi kaltum yayinda ta tsaya cak daga abunda takeyi tajima
bata iya cewa komai ba sai ta fara magana cikin sanyin murya tace mamana Madina ta
bata an rasata.
da kaltum ta fara hawaye sai shahida ma ta fara kuka,
kaltum ta dafa kafadarta tace shahida daina kuka mamarki bata mutu ba tana raye
kuma bata bataba tana nan.
shahida ta zubawa kaltum ido tana mata duba irin na karyatawa,
kaltum ta sharce hawaye tace kinaso kiganta?
shahida ta girgiza kai tace nasan bazan taba ganinta ba don bazata sake zuwa ba har
abada,
kaltum ta gyara zama tace meyasa kika ce haka Shahida?
shahida ta sunkuyar da kai kasa tace ance mamana mayya ce ita ta cinye yaya Abba.
kaltum tayi caraf ta toshe mata baki tace karki sake fadar wannan maganar, kada kisake
fadawa kawayenki wannan maganar
sai ayi miki gori, sharri ce akeyiwa mamarki, Madina macece mai kirki ga hakuri Allah zai
wanketa in sha Allahu daga sharrin da akayi mata, kada ki fitar da rai zaki sake ganin
mahaifiyarki don haka kiyita addu'a Allah Ya dawo miki da mamarki kema ki zauna da
uwa kamar sauran kawayenki.
hawayene kadai yake kwaranya daga idanuwan shahida sai gyada kai kawai takeyi,
kukane yakecewa kaltum harsaida danladi yayi magana don tausayinsu don tun dazu
yana zaune agabar mota yana sauraron su yaji hawaye ya cika masa ido yace kaltum
yayakike kuka keda kike lallashinta ai saiki tayar mata da hankali idan taga kina kuka.
get din gidan general tukur aka bude wannan karon ma zukeken saurayin nan ne ta
ranan idanuwansa kiri-kiri akan kaltum da shahida kamar yadda suma suke duban sa har
ya wuce su, saiya dannan rivas ya dawo baya yazo dai dai inda suke ya zuge gilashin
wundon kasa ya kwalawa shahida kira a fusace,
shahida tahau karkarwa ta fito da sauri ta nufi wajensa sai kaltum taji ta tsorita ganin
yadda yake harararta saita rufo kofar mota da sauri tacewa danladi direba ya fizgi mota
su kara gaba don haka yakara tabbatarwa basuda gaskiya kuma bada alkhairi suke tafe
ba saiya tsorata musamman daya tambayin shahida tace bata santa ba, batasan
sunanta ba kuma gashi kullum sai ta zo ta kirata tana bata alewa ko biskit kuma tana
tambayarta ina mamarta Madina?
ANAN MUKA KAWO KARSHEN LITTAFI NA 3
ADON DAWA
LITTAFI NA HUDU
TRUE LIFE STORY
NA JAMILA UMAR TANKO (JUT)
PART 35
TARE DA SADIN MAA.
DAGA Al-Hada Hada Hausa Book stories
.
misalin karfe biyar na yammacin litinin kaltum yar makaranta sanye take da uniform na
makaranta harda jakar littatafanta agoye a bayanta tana tafe a bayan babur na adai-
daita sahu Keke napep, bata tsaya ako inaba sai a kofar gidan su shahida ta zaro kudi ta
biya mai napep yatafi,
ta kalli kofar gidan tsaf tana tunanin yanda zataga shahida, garin waige-waigenta ta
hango wannan zukeken saurayin zaune akan motar sa yana dubanta daga kofar gidansu
wato dan gidan general tukur daga yanda yake kallonta kasan akwai magana, bayan
duban mamaki da ganinta akwai duban dama ke nake nema babu mai kubutar dake
daga wajena yau saikin fadi abunda kike zuwanan kike nema,
bata tsorata ba saima ta harareshi ta kawar da kai gefe ta cigaba da tsayuwa akofarsu
shahida, ya tsaya kawai yana duban ikon Allah yayinda kansa yayi masa gingiringim yayi
sauri ya cire bakin gilashin da ya ragemasa ganinta sosai yayi sauri yayi kamar ya
kwallawa sojojin dasuke yi musu gadi kira su kamo masa yarinyan nan sai ya fasa ya
zura mata ido don yaga gudun ruwanta amma tabbas ya kudiri niyyan a yau dai bazai
bari yarinyannan ta subuce masa ba sai ya damketa yaji wacece ko waye ya aikota kuma
me take nema a wajen shahida.
tsawon mintina ashirin tana tsaye shi kuma bai daina kallon ta ba sai ga shahida da
kannenta sun taso daga islamiyya suna isowa wajensa suka duka suka gaishe da
makwabcinsu cikin ladabi ya amsa gami da cewa shahida ga bakuwarki can tana ta
jiranki tun dazu,
shahida ta dubi kofar gidansu domin can ya nuna nan da nan shahida ta isa inda kaltum
ke tsaye suka rike juna cike da murna,
kaltum ta rike hannun shahida tayi mata magana cikin sirri sai shahida ta waiwayo ta
kalli gidan general tukur gami da nunawa da hannu abun mamaki sai gani yayi sun
dunguma gidansu yana kallon kaltum duba na mamaki yayinda take masa duba na gani
kashe ni bana tsoro,
suka wuceshi kai tsaye suka tura katafaren get din gidan suka cusa kai basu dauki dogon
lokaci ba wajen amsa tambayoyin sojoji masu gadi kasancewar sunga kaltum da yar
gidan wato shahida shahida ce ke gaba yayinda kaltum ke biye da ita tana tafe tana
duban gidan yayi mata kyau kuma ya tsaru tunda farfajiyar daga farfagiyar gidan har
zuwa babban falon gidan, abunka da gidan yan boko komai an jere shi inda a inda ya
cancanta kasancewar babu kananan yara dazasu bata waje dan haka

Please Login or Register in order to submit comment