Reading adon dawa Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin guda. Kaltum ta mayar da kai kasa don kunya da
girmamawa. Madina tace “kaltum me yasa yau baki fita bara ba!”
Kaltum ta dan yi murmushi tace “kayana ne suka yi datti nake so na wanke sai sun
bushe sannan in fita.”
Madina tace “ me yasa sai sun bushe xaki tafi, ki wanke ki shanya sai ki saka wasu
kayan ki tafi ki nemo abunda xaki ci, yaushe xa’a ce tun safe baki karya ba har
rana tayi yanxu kina jira sai kaya sun bushe!”
Kaltum ta langwabar da kai gefe tace, “ai bani da wasu kayan, kayan jikina ne
kadai nake da su, kakata ta tafi da kayana hade da nata ta haye tana cikin
wadanda suka tafi makka.” Hawaye ya sarnano daga idanuwan kaltum.
Madina ta tambayeta cike da mamaki tace “au iya mairo ba kakarki bace daman!”
Kaltum tace “kawar kakata ce, garinsu daya tare muka taho dasu, rakiya ce
jikarta.”
Tsawon mintina biyar madina tayi tana kallon kaltum saboda tsananin tausayin ta
da ya lullube mata xuciya, ta rasa kalma guda daya da xata iya furta mata. Tana
tausayin kanta da kanta, amma ta fi tausayin kaltum yarinya karama ba uwa ba
uba, ba dangin iya balle na abba a kasar da bata taso ba.
Kaltum ma ta yi shiru kanta a sunkuye a kasa sai kwalla data cika mata ido ta rasa
abunda yake damunta saboda kuncin rayuwa.
Madina ta yi ajiyar xuciya ta share hawayen daya cika mata ido, sai ta shiga cikin
daki inda ta kwance daurin tsummakaron data shigo dasu ta fara daddagawa tana
warewa. Kala biyu riga da siket ta debo ta fito ta mikawa kaltum, kamar an xare
mata laka haka ta mika hannu ta karba. Ta kurawa madina ido tana sauraron
abunda xata fada, madina ta juya xata shiga daki sai kaltum tace,” wanke miki
xanyi!” sai dai babu sabulu, nima guntayen sabulai na tsintsinto a bandaki na yi
nawa wankin.”
Madina ta waiwayo ta dubeta sai tayi murmushi t ace “a wanke suke, baki nayi
kyauta ki saka nima yanxu nan aka bani su sadaka a garin ‘yan Adon dawa.”
Farin ciki ne bayyane hade da mamaki suka halacci fuskar kaltum ta yi murmushin
da har saida wushiryarta ta bayyana yayin da gafen kumatunta ya loba wato
(dimple) ta dago da fararen idanuwanta dara dara ta dubi madina ta fada cike da
annashuwa.
“anty kin bani kyauta in saka!”
Madina ta yi dariya tace “na baki kyauta kaltum, me ye sa kike mamaki!”
Kaltum, ta sunkuyar da kai kasa ta yi godiya sannan ta fara warwarewa tana
duddubawa farin ciki fal a xuciyar ta. Kafin madina ta fito daga daki kaltum ta saka
riga da siket cas da ita kuwa kamar dan ita aka saya daidai jikinta sun yi matukar
yi mata kyau. Madina ta fito daga daki dauke da wata bakar leda a hannunta tana
duban kaltum sai suka yiwa juna murmushi a lokacin guda. Madina ta yaba da
yadda kayan ya karbe ta, sannan ta samu inuwa ta xauna a kasa ba tare da ta
nemi wani abu ta shinfida ba. Kaltum ta jefa xanin da ta kunce a cikin bokitin data
adana sauran kunfar data wanke riga da mayafinta ta fara sabawa . madina ta
kwance leda sai ga kisra da ful.
Madina ta dubi kaltum tace “xo mu ci abinci yarinya”
Wannan kalma ta bawa kaltum matukar mamaki wanda har yasa ta dago da sauri
ta dubeta har na tsawon ‘yan dakiku masu yawa ta kasa Magana, can ta yi
murmushi.
Ta ce “na koshi, nagode.| madina tace, “me kika ci da xaki ce kin koshi.! Ki saki
jikinki da ni ki xo mu ci ai xai ishe mu daman dayawa na siyo in ci yanxu sauran
inci daddare ba komai, Allah de bani wanda dan ci daddaren.” Tsananin yunwa ce
daman ta addabi cikin kaltum banda kugi babu abinda cikinta yake yi saboda ya
fafake babu komai tun a bincin jiya da rana bata sake samun abunda xata sakawa
hanjinta ba. Ta ajiye wankin ta goge hannayenta ajikin siket din dake jikinta ta
karaso a hankali inda madina ke xaune, cikin kunya da nutsuwa ta xauna yayinda
hannunta ya dau rawa a lokacin da take kokarin gutsurar gurasar madina ta
dubeta, sannan ta tambayeta cike da mamaki.
Ta ce “kaltum lafiya, meke damunki, ya naga kina karkarwa kuma duk kin
tsangwami kanki! Haba kaltum ki saki jikinki ai ba wani abu bane duk wanda ya
taimaki wani shima Allah xai taimake shi.” Kaltum ta sunkuyar da kai kasa ta fada
cikin sanyin jiki.
Ta ce, “ina mamaki ne saboda tun a mota kowa ta kansa yake babu mai taimakon
wani ko dai dai da mukurwar ruwa ne sai naga kin bani sutura kyauta sannan kin
siyo abinci kince in xo in ci shine na keta mamaki.”
Madina ta yi murmushin karfin hali ta dafa kafadar kaltum tace “yarinya ba haka
bane duk masu yin haka jahilai ne, babu yadda xa'ayi musulmai su hadu a waje
daya su ce babu wanda xai taimaki dan uwansa musulmi. Babu mai imani ga duk
musulmin daba xai so wadan uwansa abunda ya sowa kansa ba.
Ko a lahira aikinmu ba xai kaimu shiga aljanna ba sai dai alfarma albarkacin masu
albarka. Kaltum, ki cire wannan mugun tunani a ranki, ki dauka a xuciyarki duk
runtsi duk talaucin da kike ciki komai kankartar abu xaki taimakawa wanda ki ka fi
ko da babu mai taimaka miki domin Annabi Muhammad (S.A.W) y ace “hannun da
yake mikawa shine a sama, ya fi hannun da yake karba shine a kasa.”
Babu wanda kaltum take yi sai gyada kai hakika tana gamsuwa da abunda madina
take fada mata. Suka ci, suka koshi suka kora da ruwa sannan kaltum ta yi godiya
ta tashi ta je ta ci gaba da wankinta, ta dauraye ta shanya. Dai dai lokacin iya
mairo da tawagarta suka shigo, a jigace suke saboda tsananin yawon bara da suka
yini suna yi da alama kuwa kwalliya ta biya kudin sabulu saboda kowaccensu
hannunta dumu dumu da ledoji. Cikin fara’a kaltum ta tare su gani da yi musu
sannu da xuwa. A tunaninsu kwadayin abunda suka samo take don haka kowa ya
tsuke fuska babu wanda ya amsa gaisuwarta sai ma dai kauce mata suke yi suna
kewaye ta suka nufi daki.
Iya mairo ce ta tsaya tace mata “sannu isashshiya ‘yar gata wacce bata iya wahala
ba, kowa ya fita nema ke kina kwance a gida wa xai nemo ya baki a wannan
marrar da nafsi nafsi babu mai taimakon wani, keta wanki ma kike yi. Waye ya
baki aron Kaya ko kin fara tsayawa sai kinga ba kowa ki bude jakunkunan mutane
ki daukar musu kaya! To kada ki sace kayan wani a kama ki kice kin sanni ko kice
ni kakarki ce.
Rakiya ma ta leko daga daki ta tsoma baki tace “tun shigowata nake kallonta daga
gani kayan nan na wani ta sato saboda bai yi kama dana bola ba kuma bata fita
bara yau ba. Tun da safe ta debo ruwan wanki bata kara fita ba.” Sai sauran ma
suka tsoma baki babu wacce bata yi mata cari ba a cikinsu.
Kaltum tadago da sauri ta dubi madina yayin da madina ta yi mata nuni da hannu
alamar ta yi shiru kada tace komai. Kaltum ta sunkuyar da kanta kasa sai wani
kuka na takaici ya kece mata marar kakkautawa. Ta koma gefe ta tsugunna
tamkar almajirarsu yayin da kowaccensu ta shiga daki ta baje ledar abincita suka
ci. Wasu shinkafa ce da miya, wasu baital mandi, wasu taliya, wata macaroni. Abun
mamaki sai suka dinga yiwa madina tayi wai ta xo su ci. ta ce ta gode a koshe take
amma babu wacce ta tuntubi kaltum.
Wani kululun takaici ya tsayawa kaltum a wuya ta fara tuhumar kanta tana
tambayar xuciyarta wane irin mugun hali nake yiwa mutane haka suka tsane ni!
Me nake yi wanda kowa baya sona aka tsane ni!”
Sai tayi xunbur ta mike ta shiga daki wajen shinfidar kwalinta ta dauko robar cin
abincinta, yayin da kowacce ta dinga kare abincinta wasu ma suka fara daure ledar
abincinsu a tunaninsu rokarsu xata ta yi, ta dube su duba irin na takaici ta
langwabar da kai ta matse hawaye sai ta fice, ta yayimi gyalenta ba tare da ta
yiwa kowa Magana ba har madina da take xaune a tsakar gida a wajen da suka ci
abinci har yanxu bata tashi ba.
Fitarta kofar gida keda wuya sai ta tsaya cak ta dubi gabas da yamma, kudu da
arewa babu abinda take gani sai tulun bola da kabarurruka yayin da gabanta kuwa
katon kogi take hangowa yana ambaliya. Ta ji a ranta tamkar ta fada kogin nan
ruwa ya hadiyeta ta mutu ta huta da bakin cikin rayuwa sai kuma ta tuna da
wa’axin da aka yi musu a makarantar islamiyya cewar duk wanda ya kashe kansa
ya mutu a kafuri. Ta juya ta dubi kabarurrukan da ke gabanta sai tayi sha’awar
dama ace ita ce a ciki a mace ta mutu an binne ta. Ta ji a ranta rayuwar wadannan
bayin Allah da suka mutu ta fi mata irin rayuwar da take yi a duniya jin dadi da
kwanciyar hankali.
Kamar daga sama ta ji Magana a bayanta, ta waiga da sauri saida suka hada ido
da madina.
Ta ce “kaltum ina xaki je!”
Kaltum ta saki fuskarta ta yi murmushin karfin hali. Ta ce “xan je bara.”
Madina tace ki kula da kanki, shawarar da xan baki itace kada ki je garin jange
saboda kin ga ke yarinya ce akasarinsu kuma ‘yan iska ne gara ki je garin Adon
dawa tunda su na da musulmai xa su fi tausaya miki. Hadari ne ma ki dinga tafiya
ke kadai ba’a tawaga ba saboda irinku suke so ‘yan mata ba kamar mu ba manya
ba damuwa.
Kaltum ta gyada kai tace “to anty bari in je garin Adon dawan.” Ta juya ta tafi
yayin da madina ta dade a tsaye tana kallonta har saida ta kure ta daina hango ta
sannan ta girgixa kai don tsananin tausayin kaltum ta shiga gida.
Kaltum tafiya take amma fa har yanxu bata fasa kuka ba harta iske gidajen Adon
dawa. Ta fara shiga gida daya bayan daya, Kalmar da take ambata itace “karama
fi sabilillahi”
Da alama yau bata fito da sa’a ba daga inda ake kyaleta ta yi ta bara ta gaji ta tafi
da kanta sai inda ake yi mata korar kare. Ta yanke shawarar tunda yamma tayi
yanxu duk maxan suna kasuwa bari ta je can ko Allah xai sa ta dace. Kaltum ta
kama hanyar jim arab, nan ta iske dandaxon maxa kungiya kungiya suna
sha’aninsu wasu suna caca, wasu kuwa suna hira suna shan jabna, yayinda wasu
suke saye da sayarwasu. Kaltum na fara bara sai ta ci sa’a duk rumfar da tayi bara
sai a miko mata sadakar wahid jine wato kamar kandala, farin ciki ya lullube
xuciyar kaltum don ada ta shiga wani mawuyancin hali tana tunanin yadda xata yi
in har bata samu ko kwabo ba idan ta je gida xasu kusa cinyeta da baki bayan
wulakancin kala kala.
Ta ci gaba da bara harta karkashin wata inuwa inda dandaxon samari ne xalla, sun
shinfida katuwar tabarma suna ta shan jabna suna caca. Sun kaisu goma sha biyu
dukkanninsu shekarunsu basu wuce ashirin da biyar xuwa ashirin da bakwai ba.
Shewa da ihu kawai suke yi da alama basu da matsala a rayuwa. gasu a kauye, a
cikin gidajen katako da katangar kaya yayin da suturar jikinsu bakin yadi ne mai
layi layin fari wacce suke dinka ‘yar shara da wando iyaka guiwa amma koda
yaushe sai kaga suna farin ciki ko me yasa. Kaltum take xayyanowa aranta sannan
ta bawa kanta amsa “tabbas dole suyi farin ciki a rayuwarsu saboda suna tare da
iyayen su, a garinsu, kuma ga dukiyoyinsu” ta katse tunanin da take yi da ta ji
suna tambayarta “lafiya, me kike nema a wajenmu!”
Tayi firgigit t ace “karama fi sabilillahi.” Kalma daya ta ji wani daga cikinsu ya fada
a cikin yarensu sai taga dukkaninsu sun waiwayo sun kalleta a lokaci guda. Ta yi
sauri ta sunkuyar da kanta kasa, da tadago taga har yanxu suna kallonta, sai ta sa
gefen gyalenta ta rufe da fuskarta. Daga karshe ta yanke shawarar gaggauta barin
wajen tun kafin su iskance ta.
Cikin harshen larabci daya daga cikinsu yace ta xo, kasancewar tana jin larabci
sosai tun tana karama sai ta juyo ta dawo wajensu a nutse cikin ladabi amma fa
duba daya xaka yi mata ka tabbatar a tsorace take. Ya dubeta sama da kasa duba
irin na kurulla yayi dariya ya shafa baki don haka kaltum ta fara fuskantar manufar
kiranta da yayi, sai ta fara ja da baya.
To pa, ko ya data kasance tsakanin kaltum da en samarinnan!
Sai ku biyo mu dan jin yadda xata kaya
ADON DAWA 4
Ya fada cikin shagobe “ke me kyau, yaya sunanki!”
Ta na mkyarkyata tace “kaltum”
Su dukka suka maimaita sunan “kaltum” a lokaci guda suka ci gaba da dubanta
suna kwada kyawunta, suna mamakin kyawunta don basu xata akwai masu kyau a
cikin bakin almajiran nan ba saboda sun dauke su wulakanttatun bayi.
Daya daga cikin su ya dubi shugaban tawagar mai suna Mambela wanda har yanxu
bai ce komi ba sai duban kaltum yake yi kasa kasa.
Cikin yarensu yake Magana yace “ranka ya dade shugabana mambela kai ka dace
da kyakkawar halittar nan, du da de ba niman mata kake ba, lallai tana da kyau
kuma ta hadu. Ya kamata a mika maka ita cikin shagon nan kawai in ka gama sai
ka bata alif jine (dubu daya) ka ga sai tayi sati tana cin abinci, gobe xa ka ga ta
dawo da kanta.”
Duk da cewar a cikin yarensu ya yi Magana bata ji duk abubuwanda yake fada ba
amma ta fuskanci abunda yake fada, don haka sai ta juya da sauri ta fara tafiya.
Mambela yace “tabbas yarinyar na ta dace da ni don haka ku dauko min ita, ku
shigar min da ita cikin shagon nan.” Ba tare da bata lokaci ba kartai hudu suka bi
ta da gudu suka damkota cak suka daga ta kamar kaxa suka nufo inda mambela
ke xaune. Tuni robar bararta da yan kudaden data samu suka waste a kasa, ta
kurma ihu kai kace rai ake xare mata.
Cikin kuka tace “inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un. Laa ilaha illa anta subhana inni
kuntu minaxxawalimin.”
Mambela yace su ajiyeta kasa a gabansa yayin da ta xabura da gudu sai ya damki
hannunta ya fada cike da damuwa cikin harshen larabci.
Ya ce”kaltum bkya son kudi ne! bakya son mambela dan sarki, mai kudi da
dukiya!”
Ta fada cikin firgicewa da kuka mai tsanani .
“eh, bana so.”
Ya yi murmushi cikin mulki da kasaita y ace “amma ni na ji ina sonki, so mai dinbin
yawa kuwa. Yaya xa’a yi ken an!”
Abokansa suka fada cikin fusata “ka bamu ixini mu shigar maka da ita ciki kawai,
ka gama da ita mu ma idan ka gama ka bamu sauran, tunda bata da gata a kasar
nan waye xai tsaya mata.”
Mambela ya mike tsaye cak yana duban kaltum dake tsugunne a gabansa har
yanxu kuka take, gardawan kacokan sun xagayeta babu hudar da xata samu ta
arce . mambela ya dade a tsaye yana dubanta daga shi sai mahaliccinsa ya san
abunda yake aiyanawa a ransa. Can ya dago ya dubi yaransa daya bayan daya sai
yayi murmushi da kyakkyawar fuskar nan tasa, sannan ya yi musu nuni da hannu
ko bai furta ba su sun fahimci abunda yake nufi nan da nan suka fara aiwatar da
abunda ya umurcesu dasu yi domin ba’a yiwa mambela musu a garin.
Kartai uku ne suka damko ta suna kokarin shiga da ita shago. Ta kurma ihu ta ci
gaba da kiran “inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un.”
Muryar wani tsoho ne suka ji a bayansu ya fada cikin yarensu, daga dukkan alamu
ransa a bace yake, y ace “haba mambela ko sauran ba musulmai ba ne ai kai
musulmi ne, ko kunyi niyyar cutar da yarinyar nan albarkacin sunan Allah da take
ambata ya kamata ku kyaleta.”
Suka ajiye ta yayin da ta balla da gudu ta je bayan tsohon ta labe, karkarwa kawai
take yi. Gyalenta ya dawo wiyanta, kanta babu dankawali sai burtintin kitson da ya
tuttuje wanda ya cika da yashi a sanadiyar rashin siminti balle katifa a dakinsu.
Tsohon ya juya ya dubi kaltum yayi mata yarensa, sai ta girgixa kai ta yi masa
larabci. Ta ce, “bana jin yarenka, larabci nake ji kadai” ya fada cikin harshen
larabci “yi hakuri yarinya, daura dankwalinki, goge hawayenki ki tafi gidanku. Ki
daina shigowa kasuwa bara wajen maxa ki dinga bararki a cikin gidajen mata ya fi
miki alkhairi a matsayinki na yarinya mace budurwa kuma kyakkyawa.”
Ta gyada kai t ace “ nagode, ba xan sake xuwa ba. Baba karaka ni gidanmu tsoro
nake ji kada su bini su sake tare ni a hanya.”
Ya ce to muje in raka ki.
Jikinta na karkarwa, hawaye yana kwaranya ta shige gaba tsohon na biye da ita a
baya har suka yi nisa.
Mambela ya cije baki ya gyada kai ya dubi abokinsa.
Ya ce “xan jinyata tsohonna idan be daina shiga shirgata ba. Yanxu haka shima
idan suka raba daji yaga ba kowa xai iya yi mata lalata, shine mu ya hana mu.
Xamu hadu da kaltum wata rana wallahi ba xan hakura da ita ba duk ihunta.”
Abokansa suka ci gaba da xuga shi suna bashi kwarin guiwar gami da daukar masa
alkawarin idonsu idon kaltum xa su kamo masa ita.
Har kofar gidansu kaltum tshon nan ya raka ta da gudu ta fada cikin gida ba tare
da tayi msa godiya ba saboda a firgice take don tsananin tsoron da ta ke ciki.
Kaltum ta dawo gida da magaruba, kallo daya xaka yi mata ka tabbatar hankalinta
a tshe yake ko Magana aka yi mata sai ka ga ta xabura. Babu irin tambayar da
ba’a yi mata ba amma amsa daya ta gagara sai hawaye da take xubarwa. Daga ita
sai Ubangijinta suka san abunda ya faru amma bata fadawa kowa ba.
Madina ceta ja hannunta tsakargida, suka shafe tsawon sa’a guda tana lallashinta
tana bata baki da dubaru iri iri akan ta fadi abunda yake damunta amma kaltum ta
ki cewa uffan, sai girgixa kai kawai take yi alamar babu komai. Karshen maganar
madina t ace “babu yadda xa’ayi kice babu komi amma kuma kina kuka.”
Ta bata ruwa a buta tace ta yi alwala, ta yi sallah, ta yi addu’a ko me nene ma
Allah Ya sawake mata.
Karkarwa hannu kaltum yake yi data dauki buta ta xagaya ban daki, ta fito tana
alwala jkinta na rawa, kukan dai bata fasa ba har yanxu. Tana sallah tana
sheshekar kuka a bayyane, hankalin madina ya tashi amma sai ta ji haushin
kaltum ya kama ta saboda ta ki fada mata matsalarta. Su kuwa su huwaila banda
xagi da dungure mata kai babu abunda suke yi suna cewa watakila satar kayan
jikinta tayi masu kayan suka doke ta.
Rakiya tace “watakila gidan wasu ta shiga ta satar musu abinci tunda da yunwa ta
fita tun jiya bata ci abinci ba.”
Amina t ace, “ko kuma xagin wasu ta yi suka kikkifa mata mari don bata da
kunya.”
Iya mairo t ace, “ku kyale ta mana karta fadi abunda yake faruwa tunda bakin hali
ne da ita babu mai jin cikinta.”
Kaltum na kudundune a kan kwalinta cikin mayafinta sai kuka take yayin da jikinta
yak eta karkarwa. Har kowa y agama cuku cukun kwanciya, aka hure acibal bal
wato fitilar da ake cika kwalba da kanaxir ayi lagwani da tsumma.
Duhu ya bayyana a cikin dakin, yayin da gari yayi shiru alamar dare ya tsala,
kowane bawa ya kwanta hakarkarinsa kamar yadda masu iya Magana suke cewa
dare mahutar bawa. Wannan dare kuwa ya xamarwa kaltum daren jan aiki babba
maimakon ta huta sai ma ta tashi tsaye.
Misalign karfe daya na dare kaltum tayi firgigit ta mike tsaye a firgice gami da
kwalla ihu mai tsanani tana fadin “wayyo Allah na, ku taimakeni gasu mambela
nan xasu kamani.”
Ta tattaka sauran matan dake kwance a tsakiyar dakin burinta kawai ta fice waje
da gudu. Gaba daya ‘yan dakin suka tashi a gigice suna riketa, tana bankarewa
tana xubar das u sai da ta fita tsakar gida da gudu tana ihu tana fadin.
“su mambela ne xasu kamani, gasu nan xasu kashe ni.”
Madina da jidda’u ne suka bita da gudu suka damko ta suka shigo da ita daki
sannan ta dan lafa ko minti biyar ba’ayi bat a sake kwalla ihu ta fice ta gudu.
Wannan karon harda iya mairo a masu bin ta da gudu suka cafko ta. Ba ‘yan dakin
su kadai ba gaba daya ‘yan sauran dakunan gidan babu wanda ihun kaltum da
dawainiyar masu rike ta bai tasa daga barci ba. Kowa ya fito ido luhu luhu saboda
barci suna tambayar “me ke damunta!”
“ba mu sani ba.” Amsar da su madina ke bayarwa ken an. Su duka suka kewaye
kaltum suna tambaya,
“waye mambela, mutum ko aljan!”
Babu amsa, makyarkyata kawai take yi tana kuka, madina ce mai ilimn kur’ani ita
ke tofa mata addu’o’I sannan kaltum tadan lafa harta fara gyangyadi, sannan ta
sake firgita ta mike tsaye tana kokarin rugawa da gudu suka damko ta, suka
xaunar da ita har yanxu fada take.
“ga mambela nan da abokansa xasu kamani.”
Su dukka sun tausaya mata, kowannensu mata da maxa sai addu’o’I suke tofa
mata har saida ta lafa sannan suka koma dakunansu. Wsau suka kwanta amma
wasu suna tsaye akanta har saida gari yawaye tangarai sannan kaltum ta sami
barci. Sai kowa ya shiga neman ruwan alwala da sauransu.
Kaltum barci take yi haikan mai nauyi wanda bata iya jin duk wani motsi da
surutan da ake yi akanta, bata bude ido ba sai karfe biyu na rana. Ta tashi xaune
firgigit ta dubi sama da kasa, gefen hagu da damanta sai taga babu kowa sai ita.
Ta dinga kokarin tuno komai. Kanta ne yake tsananin ciwo dan haka ta shafe awa
guda a xaune ta rasa abunda yake mata dadi. Can ta daure ta yunkura xata tashi
sai ta koma jabar ta xauna, ta sake cije baki ta rike katakon ginin dakin ta yunkura
da karfi sannan ta mike tsaye. Ta fara tafiya a hankali yayin da kafarta ke xugi a
sanadiyar bubbugewar da ta dinga yi jiya. Hakika duk ilahirin jikinta ciwo yake yi
musamman kafadar ta saboda ciccibar da abokan mambela da ‘yan dakinsu suka
dinga yi wajen jawo ta.
Ta fito tsakar gida ta tsaya ta dubi kowacce kusurwa babu kowa sai ita kadai, ta
sake ci gaba da tafiya har saida ta fito kofar gida sannan ta sulale ta xauna a gefen
wani kabari ta xura masa ido tana kallo. Sai hawaye ya fara sirnanowa daga
idanuwanta, ta fashe da kuka mai tsanani ta fara Magana ita kadai tamkar
tababbiya.
Ta ce “a ina nake! Ni wacece! Wa nake da shi a duniya! Me na ke yi a duniya!”
Sai kwakwalwarta ta tuno mata mambela da abokansa a lokacin da suke kokarin
ciccibarta xasu shiga da ita wannan shagon, sai ta rushe da kuka. Ta ce “inna
lillahi wa’inna ilahi raji’un. Yaya xan yi da rayuwata! Kowa ya tsane ni, kowa baya
sona, kowa yana hantara ta, ga kishirwa ga yunwa. Allah Ka dau raina a saka ni a
cikin kabari in kwanta in huta in daina ganin kowa, kowa ya daina ganina balle
wani ya ji haushina.”
Ta sa hannu ta shafa kabarin ta fada cikin kuka ta tambaya tace “waye a cikin
kabarin nan, mace ko namiji! Ina so in xama kamar ku, in mutu kamar yadda kuka
mutu. In daina motsi kamar yadda kuka daina, in daina tafiya kamar yadda ku ka
daina, in daina bara balle su mambela su kamani.” Yayin da kuka ya ci karfinta ta
kasa ci gaba da Magana.
Muryar mai sayar da ruwa ne ya katse ta, ta dago idanuwanta da sauri ta dube shi,
sai a lokacin ta tuno tsananin kishirwar da take matukar addabarta. Ta fada cikin
wata marainiyar murya “saga dagiga moya hilwa wala murra!” ma’ana mai ruwa
tsaya ruwan dadi ne ko na xartsine!
Mai sayar da ruwa ya tsayar da jakunansa ya dubeta yayi murmushi y ace “muya
hilwa” ma’ana ruwan dadi ne.”
Ta ci gaba da Magana cikin harshen larabci tace “ka sauke min jarka daya.”
Ya sauko daga kan keken jakinsa da farin ciki yana godiya ya na fadin”Allah Ya yi
miki albarka yarinya, kin taimakeni da xaki sayi ruwana yau ko digon ruwa ban
siyar ba ban samu ko kwabon da xan yi cefane ba.
Maganar da yayi ya ambaci kudi shi yasa ta tuno dan silillikan data samu jiya da
yamma. Sai ta yi sauri ta laluba jikin siket dinta, ta ji ba komai, sai ta tuno ashe
sun xube a lokacin da ake ciccibar ta a kasuwa daga kudin har robar bara sun
xube. Sai ta ji hankalinta ya tashi ta shiga tunanin abunda xata fada masa. Ya
katse tunanin da ta ke yi ya tambaya, “a ina xan juye miki ruwan!”
Sai ta yi firgigit ta dube shi sannan ta sunkuyar da kai kasa, ta sosa keya, ta fada
cikin gargadar murya “baba ka yi hakuri ba ni da kudi, ashe kudin ya xube jiya a
jim arab. Ko xaka bani kofi daya in sha sadaka saboda Allah kishirwa nake ji.”
Tsoho ya tsuke fuska ya ciccibi jakar ruwansa ya mayar kan jakunansa yah aye, ya
kada su suka tafi. Kaltum ta bishi da kallo har yayi nisa ta daina hango shi sai ta
sulale ta kwanta a kasa domin a halin yanxu ta kasa kukan

Please Login or Register in order to submit comment