Reading adon dawa Chapter 30 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi
wanka ta fito taci abinci?
da irin wadannan tunane tunane ta shiga wankan kafinta fito ta iske mai aiki ta jera mata
abinci kala-kala agaban gado, kamshi da tururi ne suka daki hancin ta,
haj zainab ta shigo da fara-arta ta dubi Madina tace ga wata atamfa nan tawace sabuwa
ce na dinka ko sakawa banyi ba jiya aka kawomin daga wajen dinki ki saka alh Adnan
yace kada abari kisake mayarda kayan
jikinki yace kikawo buhun kayan a zubar zai dinka miki wasu, kin san shi dan gayune ga
tsafta baya son tsohon abu, sannan kici abinci mutafi asibiti yanason a duba lafiyanki
gaba daya agani ko akwai rashin jini ko wata cutar a baki magani,
madina tayi kasake tana duban hajiya zainab kamar a mafarki take jinta, tayi murmushi
yayinda hawayen farin ciki ya cika mata ido tace to ta jawo sabuwar atamfa super
holland ta saka kayan kuma daidai jikinta kasancewar itama hajiya zainab din bamai kiba
bace saidai kash bazata iya yafa tsalelen gyalenda aka hado mata da atamfarba, hijab
kawai take iya sakawa tafita waje saita yiwa hajiya zainab bayani cewa inda hijabi ta
bata bata yafa gyale aka kuwa yi sa'a akwaita da hijabai kala kala saita dauko mata
ruwan daurawa wanda ya dace da atamfar kalar koriya ce da ruwan daurawa,
Madina ta zauna ta fara bubbude manyan fulasan abinci taga soye soyene na doya da
dankali da wainar kwai ga flask din shayi ga biredi da cake duk wanda takeso zataci,
tsohuwar yunwa dake jikinta ta taso sai citakeyi batasan inda abincin ke tafiya ba ma,
har taci rabin abincin batayi rabin koshiba rabonta da tasami abinci mai dadin wannan
harta manta.
alh Adnan alh Mansir dakuma alh sa'adu haryanzu suna zaune a falo suna tattaunawa
akan irin wannan matsananciyar rayuwa da mata da yara kanana suke jefa kansu ta
tafiya kasashen wasu da zummar neman kudi, daga karshe naira na dukan naira har
naira dubu dari biyu da hamsin aka bawa alh sa'adu bayan tikitinsa na komawa sudan
kamardai yanda ka bashi dayakawo kaltum sukayi sallama,
alh Sa'adu yana sake nanawa alh Adnan cewar yana nan dai idan aka sake samun irin
haka a tuntubeshi a shirye yake daya taimaka sannan ya tafi,
bayan ya sallami alh sa'adu sai Adnan ya caske kudi yabawa haj zainab ya umurce data
kai Madina asibiti a kwantar da ita a asibiti ko lafiyarta kalau akwantar da ita ta huta
sannan a dinga Saya mata duk wani abinci mai gina jiki domin daga ganin Madina ko ba
a fada maka ba kasan babu blance died a jikinta, yasa aka kira masa Madina ya dade
yana yimata nasiha akan ta kwantar da hankali a sami lafiyarta kafin ayi maganan
Abba...
Sai tayi caraf tace alh zanso nafara ganin Abba tukunna kafin inje asibiti tunda dai ahaka
lafiyata Kalau.
ya girgiza kai yace ta Abba mai saukine bani nace Zaki gashi ba?
zankawo mikishi ki ganshi.
ta sunkuyar dakai kasa sai hawaye sharaf sharaf sharaf sharaf tasan wayo yayi mata don
ta dawo amma babu Abba, ya mutu
alh Adnan ya lura kuka takeyi sai ya shiga lallashinta yana dada jaddada mata zataga
Abba ta kwantar da hankalin ta ita dai ta fito daga asibitin tukunna.
tayi ajiyar zuciya tace Allah Ya kaimu Allah Ya sa muga alkhairi, ina kaltum kuma?
alh Adnan yace kaltum tana nan lafiya itama zaki ganta tare da Abba,
saita kura masa ido tana masa duban rashin
yarda yayinda tashiga kokonton ko ta fada hannun yan damfarane?
saitace aranta Allah na tare da ita Shizai fitar da ita ko a wanne hali ta tsinci kanta,
alh Adnan yayi musu sallama ya tafi,
Haj zainab da mai gidanta suka umurci Madina ta biyo su za'a kaita asibiti tana zaune a
bayan moto tana duban gari yayinda hawaye bai daina zuba ba, wata zuciyar nace mata
meyasa ta yarda ta dawo gashi ita ta zo ita bada ganin kaltum ba balle Abba, wai shin
ina hankalinta da tunaninta yatafine da har akayi mata wayo aka dawo da ita Nigeria?
Sai ta tuna da komai yasami bawa mukaddarine ne daga rabbul samawati abunka da
mai ilimi saita share hawayenta taci gaba da kallon gari tana duban manyan gine gine da
titina kayatattu a birnin tarayyah Abuja daman bata taba zuwa Abuja ba a rayuwarta
tace aranta ashe muma munada kudi a kasarmu. tome sudan zata nuna mana dahar
muka je muka makale musu.?
ta gangaro tunanin 'yayan ta taji a ranta babu abunda tafison gani ahalin yanzu irin ta ga
' ya yanta tayi kamar tace musu sukaita tasha su sakata a motar kano ta fasa zuwa
asibitin
saita daure tayi shiru tana mai biyayyah da umurnin wanda ya taimaketa alh Adnan,
suka isa kelina hospital dake cikin unguwar gwarumpa, lafiyayyen asibiti mai kunshe da
kwararrun likitoci.
ADON DAWA 42
.
TRUE LIFE STORY
.
haj Zainab ne da Madina suka shiga ciki da yake suna da file a asibitin lambar file din ta
fada, aka tambaye ta likitan da zata gani sai kuwa ta jero likitoci daya bayan daya har
guda shida kowanne kuma kudin ganinsa daban, ta biya,
kamar yadda aka yiwa kaltum binciken nan da gwaje gwaje irin sa alh Adnan yace ayiwa
Madina ma, yana ta koro bayanai a waya har saida likitoci sukayi masa abunda yakeso
daga karshe sakamakon gwaje gwajen suka firfito, Madina batada wata matsala ajikinta
sai hawan jini da ciwon zuciya tanada rashin isheshen jini da ruwa a jikin ta, sai ya
umurcesu dasu kwantar da ita su bata kulawa ta musamman har sai komai ya daidaita
zasu sallameta, kada su damu da yawan kudinda zai kashe, daki mai tsada na kwanciar
mutum daya yace a bata, sannan asibiti su shirya mata time table din abincin da zai kara
mata jini da kuzari su dinga bata basai haj zainab ta dinga zirga zirgar kawo mata abinci
ba saida komai ya daidaita sannan akabawa Madina gado ta kwanta haj
zainab ta dawo gida alh Adnan bai daina waya ba yana fadar yanda za ayi da Madina ba,
yace gobe haj zainab taje kasuwa ta siyowa Madina kayan sawa sannan ya sake
umurtarta haj zainab taje da almakashi asibiti ta askewa Madina gashinta,
Haj zainab ta tuntsire da dariya tace haba dadyn Mashkur yaya za ayi ka sani in dauki
almakashi Inje in hau gwaguyewa mace kai haka kawai baruwana kanta ras yake da
kitsonta gata da gashi mai tsawo da tsananin baki,
alh Adnan yace ai na zaci irin gashin kaltum ne uwarta ta rasa ma yadda zata taje kan
sai askewa tayi sbd cukuikuiyewa, kura da amosanin fari tas,
haj zainab tace a'a wannan da kitsonta kuma mai tsafta ce dayake babbace basai anceta
gyara jikinta ba, kaltum kuwa ai yarinyace,
tunda alh Adnan ya fara waya da haj zainab Abba ne akan layi yanata nemansa a waya
yana gama waya da haj zainab sai wayar Abba ya shigo bayan sun gaisa alh Adnan
yabashi hakuri cewar yaga missed call dinsa
tun dazu yana ta amfani da wayar bai samu ya kira ba,
Abba yace babu komai yau sati daya yacika kamar yadda alh saadu ya dauka ko akwai
wani labari daga gare shi?
alh Adnan yace kwarai kuwa akwai alamar nasara ka kwantar da hankalin ka zan kawo
maka Madina har kano.
Abba yayi shiru na tsawon mintina daya yakasa magana yayinda zuciyarsa ta sakamasa
lalle alh Adnan ya daukeshi karamin yaro don bayaso kaltum tarakashi sudan shine ma
yake kokarin hanashi zuwa har ma yake masa wayo wai ya kwantar da hankalinsa zai
kawo masa Madina har gida?
tayaya zai kawo masa ita gida?
saiyaji haushin alh Adnan ya lullube zuciyarsa
yayinda alh Adnan yayi ta magana shi kadai batareda Abba yana sauraron ma abinda
yake cewa ba yana can yana tunani, can ya dawo da hankalinsa kan alh Adnan kalmar
dazu dai yake maimaitawa har yanzu basai kaje sudan ba har gida zan kawo maka
Madina da izinin Ubangiji,
Abba yaja dogon numfashi yayi murmushin takaici yace alh ina ganin zaifi kyau in shirya
in tafi sudan din nan sai ka hadani da alh saadu muje nemanta tare,
alh Adnan yace Abba kasanni ne ada ko nayi
maka kama da karamin mutum wanda zai yi maka karya?
Abba ya girgiza kai yace a a ranka ya dade,
alh Adnan yace to tunda nace maka ka kwantar da hankalinka zan kawo maka Madina
har gida da izinin ubangiji zan kawo ta.
abba ya sankare a zaune har sai da alh Adnan ya kashe waya bai cire wayar sa daga
kunnensa ba, kwakwalwarsa ta hautsine tamkar hayaki ake turnuka masa, ya shiga
kokonto ya kasa gane gaskiyar al amarin alh Adnan baiyi kama da wanda zaiyi masa
karyaba to yayi masa karya a wanne dalilin?
idan yayi masa karyar mezai samu?
kodai iyayensa suka hada baki dashi don a hanashi zuwa sudan?
irin wadannan tunane tunane ya yini ya kwana yanayi sharkif cikin tunani da damuwa ya
kasance sai da duk yan gidan suka lura da haka aka tambayeshi yaki fada sai shi sai
zuciyarsa ne suka san gaskiya.
saida Madina ta cika sati daya cur a asibiti kafin aka sallamota hartayi kuzari tayi
kyawun gani ba kamar yadda tazo ba, washe garin ranar da sassafe misalin karfe bakwai
alh Adnan da direbansa simon suka dira agidan alh Mansir batare da Madina tasan ita
suka zo dauka ba, tayi sallar asuba tunda assalatu tana zaune akan abun sallarta tana ta
tasbihi tana kwararo addu o i kala-kala akan Allah Ya sa alh Adnan da dagaske yake
Abba bai mutuba kuma Allah Ya sa jikinsa da sauki bai nakasaba yadda bazai sake
moruwa ba, ta kara da addu a Allah Ya sa 'yayanta suna raye suna cikin koshin lafiya da
nutsuwa,
haj zainab ta shigo dakin yayinda ta zauna a gefen gadon har saida Madina ta shafa
addu'a a fuskarta suka shafa a tare,
Madina ta waiwayo ta dubi haj zainab saitayi murmushi ta gaishe ta,
haj zainab ta amsa cikin fara'a tace alh Adnan da direbansa sunzo daukarki zaku tafi
kano ashe tun giya ya fadawa mai gidana shikuma ya manta bai fadamin ba, balle na
fada miki, ki shirya gasu can a falo ke suke jira amma ki shirya a nitse suma sai sunyi
karin kumallo zaku wuce.
sai Madina taji wani abu ya harba a cikin zuciyarta fargaba mai tsanani ta far mata saita
fara karanta InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarta, ta amsa da to sannan ta mike a
sanyaye ta shiga bandaki ta dade a tsugunne a bandaki tana kuka tana fargabar abunda
zata je ta iske a kano, taji kamar tace bazata je kanon ba gara a bata kudin mota ko jirgi
ta koma sudan ko ta bazama cikin Abuja a neme ta arasa,
kafin ta fito daga wanka an jera mata abinci kala kala a tsakiyar dakin bata yi wata wata
ba ta bude akwatinta trolly wacce aka shake mata da kaya har kala biyar gaba dayansu
a
dinke aka sayesu, dinkin yan senegal, ta zabo wata shadda kalar jan duhu maroon ta
saka a jikin ta yayinda ta zabi bakin hijabi ta saka da ta zauna cin abinci sai ta kasa ci
saboda fargaba ta tura loma biyu ta mike ta harhada sauran komatsanta ta cusa a cikin
akwatinta ta kinkimo ta fito falo jikinta a sanyaye, ta durgusa ta gaida alh Adnan da
abokinsa suka amsa mata cike da kulawa sannan suka dunguma zuwa wajen mota.
haj zainab na rike da akwatin Madina har cikin mota, Madina ta shiga gidan baya alh
Adnan na gaba da direba yana tukawa,
alh mansir da matarsa sunayiwa Madina fatan Allah Ya kiyaye hanya ita ma tana musu
godiya hadi da fatan Allah Ya saka musu da alkhairi bisa abun arzikinda suka mata,
suna daga mata hannu suma suna daga musu hannu har suka hau titi suka fara tafiya,
madina taja dogon numfashi tayi ajiyar zuciya yayinda tayi tagumi tana sauraron inda
Allah zaiyi da ita nan gaba, ta kurawa wundo ido tana kallon gari tabbas akwai attajiran
da sukejin dadin rayuwarsu a kasarnan ashe ba duk en Nigeria bane rayuwa tayi musu
zafi ba, akwai masu jin dadi saboda sunsha wuce tsala-tsalan motoci dauke da zankada-
zankadan en mata a kame a baya direba yana tuka su, kota gansu tareda mazajensu da
'yayan su, kallo daya zaka musu ka tabbatar suna cikin ni ima
basuda damuwa,
dasuka bar cikin gari sai suka fara keta daji babu abun kallo kuma saita bude yar
karamar jakarta da yake rataye a kafadanta ta zaro Qur'ani tahau karantawa yayinda
taketa jero addu o i a zuciyarta tana fatan Allah Ya nuna mata alkhairi a kano kada ta
hadu da abun ki shine ta iske Abba a raye ta samu 'yayanta
lafiya, tana matukar fargabar haduwa da general Tukur da iyalansa da kuma Tasi'u da
matansa, tana gudun kada Allah Ya sa a maimaita mata waccar kalmar datayi sanadiyar
rabata da kasarta wato maita sai hawaye ya balle mata yana gudana daga idanuwanta
yayinda alh Adnan ya tsura wata ido ta madubin dake gefensa da yake a saitin bayan sa
take zaune, ya zare farin gilashin da yake fuskarsa ya ajiye jaridar da yake karantawa ya
waiwayi baya ya dubeta yace haj Madina meye matsalarki ne a yanzu?
tayi sauri ta dago da jajayen idanuwanta ta dubeshi saita girgiza kai tace bakomai alh,
yace ki cire damuwa ki fauwalawa Allah komai nayi miki alkawari zan taimakeki zan
tsaya miki a duk al amuranki har sai kinji dai dai kamar yadda kowacce mace takejin
dadin rayuwarta a gidan ta, kuma a kasarta kada ki manta shi alkhairi baya fadawa a
kasa duk abunda ka shuka shizaka girba, kaltum ta fada min irin abun arziki da kulawar
da kika yi mata a waccan duniyar taku a inda ake takai-takai hatta kakarta wacce ta
rabota da iyayenta ta tsallake ta barta amma kika kula da ita saboda me yasa ni bazan
taimaka mikiba?
ta fashe da kuka tana matukar godiya dashi albarka,
ya juxa ya saka gilashinsa yaci gaba da karatun jaridarsa kamar daga sama yaji muryan
Madina ta furta masa wata kalma wacce tayi matukar bashi mamaki sai ya juyo a hankali
ya dubeta batareda ya iya sake tambayarta abunda ta fada ba ko kunnensa ne baijiye
masa daidai ba,
madina ta maimaita maganar tace alh mezai hana ka auri kaltum?
ina ganin zatafi samun nutsuwa a rayuwarta tunda kun shaku, kaltum na son ka kuma ta
shaku da kai don kusan kullum tana bani labarin ka,
ya juya ahankali yacigaba da karatun jaridarsa batare da yagane abunda yake
karantawa ba, kwakwalwarsa ta shiga rudani yakasa tantance dalilinda yasa mutane
sukeyi masa sha'awar auren yarinyar nan karama, wai shin ko akwai wata alama da yake
nunawa yanason kaltum afili bai sani ba?
har suka isa birnin kano ta dabo tumbin giwa babu wanda yasake magana acikinsu sai
wa'azinda yake tashi daga rediyon jikin motar, dama Simon (direba) ko hausa bayaji
balle yaji abunda ake fada ya bude wuta sai gudunsa kawai yakeyi yayinda sanyin a.c ya
dinga ratsa jijiyoyin jikinsu,
Madina ta zubawa garin kano ido tana ganin irin ci gabanda akasamu fiye da da bakamar
yanda ta bar garin ba ta rufe Qur'ani da ke a hannunta ta mayar cikin jaka ta ci gaba da
dararradin abunda zata gani ko kadan bataga sun nufi gidan general Tukur ba can wata
unguwa suka kutsa saitaji dan sanyi a ranta, a gaban wata get suka tsaya aka matsa
horn batareda bata lkc ba sai wani bakin mutum ya wangame get da alama dai mai gadi
ne saboda yanayinsa a kukkuje yake akwai alamar rashi a tare dashi suka kutsa da
motar cikin gida sai gasu a farfajiyar wani kayataccen gida mai kamada aljannar dunia,
alh Adnan ya juya ya dubi Madina yace BismiLlah fito munzo gida,
cikin sanyin jiki Madina ta sa hannu ta bude kofar mota ta sako kafarta daya waje kafin
ta
sauko da dayar sai ga kaltum ta manno da gudu ta yi tsalle ta danneta tana ihu don
murna,
suka rungume juna suna murna fuskokinsu cike da annashuwa yayinda mamakin ganin
Madina ya hana kaltum sakat, kalmar farko da kaltum ta fara furtawa Madina itace ina
mambela?
sai karaf a kunnen alh Adnan wanda ke tsaye a gefe yana dubansu.
Madina ta dago da sauri ta dubeshi sai a lokacin kaltum ta lura da cewar ashe yana tsaye
a wajen, kunya ta kamata sai taje da sauri ta durgusa ta gaisheshi ya amsa cike da
fara'a yakara dacewa nafara cika miki burinki na kawo miki Madina?
kaltum ta tsunkuyar takai kasa tana murmushi tace ngd.
kaltum dauke da akwatin Madina suka nufi cikin gidansu basu tsaya a ko ina basai a
gaban gadon goggo fattu ,
Madina ta dade a tsaye tana duban tsohuwarnan itama tsohuwar tana dubanta
kowaccensu ta kasa tuno inda tasan fuskar nan,
kaltum ta lura da hakan saita katse tunaninsu tace aunty Madina goggo fattune fa
batada lafiya shekara da shekaru, goggo Madina ce wannan wacce muka tafi sudan da
ita a mota daya, sai Madina ta dauki dogon salati ta karasa da sauri wajenta ta zauna a
gefen gadon ta rike hanun ta tana maiyi mata addu'ar Allah Ya bata lafiya, hawaye ya
fara surnanowa daga idanuwansu su dukka ukun goggo fattu ta bude baki dakyar tayi
magana
duk da maganar bata fita gaba daya amma ana gane wata daga ciki tace Madina kinga
kaltum ita ke kula dani tabani abinci a baki tayimin wanka, tayimin wankan tsarki,
madina ta girgiza kai tace Allah sarki rayuwa goggo ki nemi gafarar kaltum domin kin
zalunce ta a baya kice ta yafe miki, don Allah ba ya yafe wa wani laifi wani, sai goggo ta
gyada kai har sau uku sannan ta fashe da kuka, Madina ta jawo hannun kaltum ta hada
danata goggo fattu ta ce kaltum ki yafe mata duk abunda tayi miki a baya.
cikin hawaye mai tsanani kaltum ta gyada kai ta ce goggo nayafe miki duniya da lahira,
ana cikin wannan hali sofi da saleh suka shigo cikin dakin suna masu marhaba da zuwan
Madina bayan sun gaisa kaltum ta gabatar da Madina ga iyayenta sannan ta gabatar
dasu ga Madina sai a lokacin kaltum tabasu tarihin rayuwarta da Madina a bur sudan da
irin taimakon datayi mata da yadda akayi ta nemo ta, yayinda iyayen kaltum suketayi
mata godiya ita kuwa Madinar hankalinta ba ya jikinta ta nutsa kogin tunani da rudani
mai yawa a sanadiyyar sunan Abba da kaltum ta dinga ambato a cikin labarinta, bata iya
katse kaltum ba a lokacin sai da iyayenta suka fita kaltum ta yunkura zataje ta dauko
mata ruwa sai Madina ta rike hannunta ta dawo da ita ta zaunar da ita ta dubeta cike da
kidimewa tace kaltum naji kina ambaton Abba a zancenki wanne Abba kike nufi?
kodai anas kanin sa kinsan fa kamar su daya Abba ai ya mutu kin manta?
kaltum ta dafe kirji tace ahaf ashe na manta
ban fada miki ba na dauka kinsani Abba bai mutuba naganshi da idona yazo gidan nan
har sau biyu,
sai Madina takame azaune tana duban kaltum kamar gunki harta fice daga dakin ta kasa
magana tace aranta daman alh Adnan da gaske yake yi dayace Abba bai mutuba yana
raye?
amma ai yace min a kwance yake har yau bashida lafiya kuma kaltum tace yazo gidan
nan har sau biyu lafiyarsa lau kenan wai shine menene gaskiyar al amarin nan ko dai
don su kwantarmin da hankaline suke kiran Abba na raye?
kaltum ta shigo da babbar kofi dauke da lemo da kananan kofuna tazo ta ajiye agaban
Madina zata juya ta fice saitaji Madina ta damko hannunta, kultum ta firgita da ganin
jajayen idanuwan Madina mai zubar da hawaye mai yawa, cikin rawar murya take
magana tace kaltum ki fadamin gaskiya game da Abba na riga nazo Nigeria ba komawa
zanyi ba idan na iske ba Abba na yarda da kaddara haka alh Adnan ya fadamin Abba na
raye kema gashi kina fada min.
.
ADON DAWA 43
.
TRUE LIFE STORY
.
kaltum ki fadamin gaskiya game da Abba na riga nazo Nigeria ba komawa zanyi ba idan
na iske ba Abba, na yarda da kaddara haka alh Adnan ya fadamin Abba na raye kema
gashi kina fada min Kinga Abba, kinsan ina da matsalar ciwon zuciya ban cika son samun
faduwar gaba ba, idan shi babbane yayimin irin wannan wasa ke karama ce bana irin
wannan wasan dake.
hankalin kaltum ya tashi ta sulale ta zauna agaban Madina tace Wallahi Abba na raye
yana nan lafiyarsa kalau ai da dashi ma za aje daukoki daddy yace zai sa alh sa adu ya
kawo ki donni ma shiya nemoni,
Madina ta sulale tayi sujjada ga Ubangijin talikai don farin ciki da godiya ta daga kanta
sama da hannayenta biyu tana fadin AlhamduLillah Allah kaine abun godiya tsarki ya
tabbata ga Ubangijin da Ya halicce ni ya raya Abba Allah na gode maKa daKa amsa
addu'ata Ka wanke ni a idon duniya kafin inbar duniya, naji dadi daKa fitar da 'yayana
daga bakin dunia cewar uwarsu tabar musu abun gori,
kaltum ta toshe bakin Madina gamida zaunar da ita tace aunty Madina kiyi shiru mana
da karfi kike magana fa kada mutane su shigo su dauka wani abu ne.
madina ta rushe da kuka tace kaltum dole ne in godewa Ubangijina domin Ya amsa
addu'ata dana dade inayi, farin cikin da nake yi ba dan in auri Abba ba sai don Allah Ya
taimakeni Abba bai mutu asanadiyyata ba ya
warke ya tashi daram na tabbata zai yi musu bayanin duk abunda ya faru na gaskiya,
Allah Ya wankeni 'yayana zasu huta da gori shine kadai fatana daman,
kaltum tace kwarai Abba yayi musu bayani sun gamsu sunyi nadama sun bazama
nemanki don sunemi gafararki basu sameki ba dole tasa suka hakura,
Madina ta mike da sauri ta ce tashi ki rakani gidan su Abba,
kaltum tace ki bari gobe ko anjima kici abinci tukunna har a gama,
Madina ta girgiza kai tace bazan iya kara awa guda ba banje naga Abba da 'yayana ba,
kafin kaltum tace wani abu Madina ta suri akwatin kayanta ta fice tsakar gida don haka
kaltum ta dubi goggo Fattu wacce har yanzuke kwa
ADON DAWA 43
.
TRUE LIFE STORY
.
Jama'a patar za ku mana uzuri, wannan coplete ne.
.
kaltum ki fadamin gaskiya game da Abba na riga nazo Nigeria ba komawa zanyi ba idan
na iske ba Abba, na yarda da kaddara haka alh Adnan ya fadamin Abba na raye kema
gashi kina fada min Kinga Abba, kinsan ina da matsalar ciwon zuciya ban cika son samun
faduwar gaba ba, idan shi babbane yayimin irin wannan wasa ke karama ce bana irin
wannan wasan dake.
hankalin kaltum ya tashi ta sulale ta zauna agaban Madina tace Wallahi Abba na raye
yana nan lafiyarsa kalau ai da dashi ma za aje daukoki daddy yace zai sa alh sa adu ya
kawo ki donni ma shiya nemoni,
Madina ta sulale tayi sujjada ga Ubangijin talikai don farin ciki da godiya ta daga kanta
sama da hannayenta biyu tana fadin AlhamduLillah Allah kaine abun godiya tsarki ya
tabbata ga Ubangijin da Ya halicce ni ya raya Abba Allah na gode maKa daKa amsa
addu'ata Ka wanke ni a idon duniya kafin inbar duniya, naji dadi daKa fitar da 'yayana
daga bakin dunia cewar uwarsu tabar musu abun gori,
kaltum ta toshe bakin Madina gamida zaunar da ita tace aunty Madina kiyi shiru mana
da karfi kike magana fa kada mutane su shigo su dauka wani abu ne.
madina ta rushe da kuka tace kaltum dole ne in godewa Ubangijina domin Ya amsa
addu'ata dana dade inayi, farin cikin da nake yi ba dan in auri Abba ba sai don Allah Ya
taimakeni Abba bai mutu asanadiyyata ba ya
warke ya tashi daram na tabbata zai yi musu bayanin duk abunda ya faru na gaskiya,
Allah Ya wankeni 'yayana zasu huta da gori shine kadai fatana daman,
kaltum tace kwarai Abba yayi musu bayani sun gamsu sunyi nadama sun bazama
nemanki don sunemi gafararki basu sameki ba dole tasa suka hakura,
Madina ta mike da sauri ta ce tashi ki rakani gidan su Abba,
kaltum tace ki bari gobe ko anjima kici abinci tukunna har a gama,
Madina ta girgiza kai tace bazan iya kara awa guda ba banje naga Abba da 'yayana ba,
kafin kaltum tace wani abu Madina ta suri akwatin kayanta ta fice tsakar gida don haka
kaltum ta dubi goggo Fattu wacce har yanzuke kwance tana kallonsu taji tausayinta ya
kamata sai ta dawo ta tsiyayi lemo a kofi ta daga kanta ta bata sannan ta juya mata
kwanciyar kamar yadda ta saba yi mata kullum idan ta juyata dama in aka jima sai ajuya
ta hagu kota zaunarda ita ta jingineta ajikin filo don dai taji dadi a jikin ta, cikin sanyin
murya kaltum tayi mata magana tace goggo zan raka Madina sauri take yi nasan kina jin
yunwa ba yadda zanyi dana baki abincin kafin mutafi amma zan fadawa mama ta baki
saidai tace bakya ci dayawa idan bani na bakiba ki daure kici dayawa anjima zan dawo,
goggo fattu ta gyada kai tayi murmushi sannan itama kaltum taji dadi tayi dariya ta fice
kuka kawai Goggo Fattu keyi tana nadamar abunda tayiwa yarinyannan sai gashi duk
duniya babu mai kula da ita irin kaltum yanzu ko ancewa sofi tazo ta bata abinci saita ga
dama zatazo, hidimar mijinta dana 'yayanta ne kawai agabanta,
hankalin sofi a tashe take tambayan kaltum yaya bakuwarki tace tafiya zatayi ko abinci
bataci ba?
kaltum tace hankalinta yayi wajen' yayanta bazata iya zama taci abinci ba ki barta kawai
zan rakata idan daddy ya barni ga Goggo can a daki tana jin yunwa kibata abinci saina
dawo zanci,
sofi ta amsa da to saikun dawo, kaltum ta fita tana waige waige tana neman Madina can
a jikin get ta hangota tana amsa tambayoyi malam saleh mai

Please Login or Register in order to submit comment