Reading adon dawa Chapter 11 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

buga min
kofa sai jikina ya dau rawa, kwallawa nake yi ina tambaya “waye? ” shiru ba amsa, sake
bugun kofar ake yi da karfi na wawuri lema na fito tsakar gida na tsaya, can dai na isa
bakin kofa na yi Magana “waye? Waye? ”
shiru sai bugun da ya karu. La’ilaha illa Anta subhanaKa inni kuntu minaxxwalimina” na
yi ta karantawa sannan na bude kofar jikina na rawa.
Dogon namiji sanye da shadda taxarce koriya da hula na gani a tsaye yaro-yaro yana
digar ruwa ya jike sharaf. Ban gane ko waye ba na tambaya cikin firgici “bawan Allah wa
kake nema ne, ko kayi batan kai ne? ”
sai yace “ke nake nema.” Na jima a tsaye ina dubansa saboda duhu ba wuta ban gane
ko waye ba ne amma ni xuciyata bata bani mutumin nan xai cuce niba saboda nayi
addu’a Allah xai kiyaye ni. Sai na ji ya bani tausayi saboda yana tsaye har yanxu a cikin
ruwa, yana dukansa. Na sa Allah daya a raina ko daya xo da niyyar cutar da ni Allah xai
kare ni sai na matsa ya shigo xauren. Ban de rufe kofar ba muka iso falo a inda na kunna
fitila sai ga Abba duban farko na gane shi sai na ji tamkar an hura min wuta a xuciyata
dan haushi.
Na fada a hasale “Abba, baka rabu da niba ko? Sai ya fada cike da tabbaci “ba xan iya
rabuwa da ke ba, har sai ranar da na rabu da raina.” Sai a lokacin na tabbatar na hadu
da alakakai, na hadu da masifar rayuwa.
Na ce “ni kuwa gara a raba ni da raina da in yi soyayya da kai.” Sai kuma ya rushe da
kuka harda dora hannu a kai, yana tambaya ta waishi a duniyar nan me yayi min haka
nake yi masa wannan wulakancn?
Wai me yasa na tsane shi alhalin yana so na?
sai naga ya dafe kirji da alama xuciyar sa ke yi masa ciwo, yaro yana kokarin kakkafe
min xai fadi ya mutu.
Nan da nan na fara lallashinsa ina cewa ya kwantar da hankalinsa na amince. Wannan
Kalmar na fitowa daga bakina sai naga Abba ya lafa, ya koma ya xauna ya mike kafa a
tsakiyar falon. Da yake babu kujeru a falon leda ce da labule kawai, ni ma na samu lungu
na xauna muka yi jugum kamar a gidan makoki. Idan ya dago ido ya dube ni sai yayi
murmushi ya sunkuyar da kai kasa da alama yau farin ciki ya same shi kasan cewar na
amsa masa . ni kuwa tuni takaici ya dame ni.
Fiye da awa guda muna xaune a cikin wannan yanayi, sai na dube shi na ce “ruwan
sama ya tsaya sai ka tafi gida ko? ” ya juyo ya dube ni yace “a ina xan hau motar kano?
” na fusata na harare shi na ce “da ta ina ka biyo ka xo? ”
sai ya dukar da kai kasa cikin ladabi yace “nagode xan tafi saida safe.” Ya mike ya fara
tafiya, ban amsa masa ba na saka shi a gaba muka fita har kofar gida. Na waiwaiga ban
ga motar daya xo da ita ba, ashe da gaske bada mota ya xo ba a motar haya ya xo. Ina
lekensa ya nufi hanyar get xai tafi tasha ga nisa, gashi garin tsit babu ‘yan Babura, ga
tsananin iska da sanyi, ga kayan jikinsa a jike sharkaf. Yana ta rawar dari ya tafi yayin da
ni kuma na ji ko a jikina bai dameni ba shiya dorawa kansa wahala, na jawo kofata na
rufe na shiga daki na kwanta. Ina ta sake sake a raina, idan na fara saka soyayyata da
Abba sai na yi maxa na warware baxan iya soyayya da kanina ba sai dai duk mu rasa
rayukan mu ni dashi gaba daya.
Wayata ceta hau kara na xabura na duba Abba ne, sai na yi sauri na katse dan ba xan
amsa ba , ya ci gaba da kira, ina ta rejecting. Sai ya turo rubutaccen sako yana shaida
min ya isa gida lafiya. Na tabe baki nace “ina ruwana, ni na aike ka.” Yaron nan bai iya
barci ba haka har cikin dare bai daina turo sakonni ba, har saida nayi masa reply, sannan
ya runtsa. Ka da ki dauka wata Kalmar soyayya na rubuta masa kalma daya na rubuta
itace. “ok” sannan ya kyale ni na runtsa.
Kaltum na rike haba ta afka cikin mamaki tace “cafdijam, haka soyayya take daman ko a
fim din indiya ban taba ganin irin wannan soyayya ba.”
Madina ta yi dariya tace “so ya wuce haka ma kaltum, ai ke yarinya ce karama baxa ki
sani ba sai dai nan gaba. Ke in takaice miki duk wannan halin da Abba ya shiga ban fada
miki komai ba ma saboda kwakwalwarki karama ce ba xaki fahimta ba, kadan nake
takaice miki, kuma duk wannan rigimar da aka yi ba’ayi komai ba. Bala’I na gaba sai kin
tausayawa Abba, ko makiyinsa xai tausaya masa idan ya ga halin da yake ciki.
Hakika daga baya na tabbatar bada gangan yake yi ba da gaske Allah Ya saukar masa
da jarabawar sona wacce ta xame masa matsala a dukkanin lamarinsa. Na fuskanci shi
kansa baya son nacin da yake yi min yana iya kokarinsa wajen danne son da ture shi
amma abu ya ci tura, ko baya so xuciyarsa xata tursasa shi sai yayi min waya idan ban
amsa ba sai ya taso ya xo ya ganni. Bayan na amsa gaisuwarsa bana kara kallonsa balle
na kara yi masa Magana, a gidana ko a office, da daddare ko da rana ya kara ci xamansa
ya karaci xamansa ya kara ci satar kallona in yi kamar bansan yana yiba, daga karshe
sai yayi min sallama ya tashi ya tafi idan ya dame ni da waya in amsa in ce masa
“menene? ” sai yace ya kira ya gaishe ni ne.in ce “nagode”. In kashe wayata, idan ya
fara turo sakon daya danganci soyayya sai na ja masa kunne cewar ya daina niba sa
arsa ba.
Sai gashi rannan a gidana shi da wani amininsa mai suna mukaddam. Na san mukaddam
sosai abokinsa ne tun suna sakadire suna shigowa gidana, tare ma suka yi jami ‘a shima
lauya ne.bayan sungaishe ni sai mukaddam ya kai-kai –ce xai tsara ni cewar abokinsa ya
shaida masa komai game da halin da muke ciki, wai in daure in kula shi ba hargetse na
daga musu hankali gaba dayansu, na xage su tsaf na kore su daga gidana. Na ce da
mukaddam ya fadawa abba kada ya sake nemana ko a waya balle a ido biyu, jikinsu na
rawa suka tafi.
Abba yayi ta kuka ya dinga turo sakonnin bada hakuri kala-kala a waya, na ce duk halin
da xai shiga ya shiga baxan cuci kaina ba na aikata abunda xai dame niba.
Wata rana da yamma ina cikin garin kaxaure ni da abokan aikina nurses muna bikin wata
abokiyar aikin mu. Sai wata kawata da muke xaune tare tace “wayar ki na ringing tun
daxu fa.”
Na yi sauri na bude jakata na dauko wayar sai naga 30 missed calls. Sai na ji gabana ya
yanke ya fadi na fara dubawa sai naga missed calls din Abba 19 ne 6 kuma na
mukaddam abokinsa, 5 kuma wata bakuwar lamba ce. Na fito gefe saboda kidan da ake
yi a wajen da kuma hayaniya, ina kokarin kiran lambar da ban sani ba amma ban damu
da in kira Abba ba balle mukaddam na san dai abu daya ne, shine su yi min magiyar
soyayya ni kuma ba xan yi ba, kuma bana yi. Na kira number na ji number busy ana
amfani da layin, ba’a jima ba sai naga lambar tana kara kirana na yi sauri na dauka sai
na ji muryar wani inyamuri yana Magana cikin harshen turanci.
Ya ce dani “madina ce? ” na amsa cike da mamaki “eh, madina ce.” Ya ce “to gamu a
kofar gidanki, kofarki a rufe.” Na tambaya cike da mamaki “waye kai? Lafiya? ” ya fada
cike da damuwa “madam, ki yi sauri ki xo, emergency ne muna tare da marar lafiya ne
yana neman taimakon gaggawa.” Na fada cikin mamaki marar lafiya a gidana kuma? Me
xan yi masa ni da ba likita ba, kuma ko ni likita ce gidana ya kamata akawo shi ba asibiti
ba?
Sai na ji mutumin ya hargitse yana Magana a fusace y ace “ina Magana ne akan mai
gidanki daya yi hadari a hanyarsa ta xuwa onisha, gashi nan rai a hannun Allah be san
ma a inda yake ba, jini ne ke xuba.”
Na ji gaba daya tunani naya hautsine na rasa me yake fada, kafin in ce wani abu ya kara
da cewa “muna nan a kofar gidanki ki xo idan baki xo ba nan da mintina goma sha biyar
xamu ajiye miki shi a kasa mu tafi da motar asibiti ce na roka aka kawo mu tun daga
onisha dan kawai na ceci ransa ya na gama fada ya kashe waya.”
Kaltum ta dafe kirji t ace inna lillahi wa inna ilaihi ra ji’una, waye wannan marar lafiyar ko
dan uwanki ne daga onaca? ”
Madina ta share hawaye t ace “xaki ji ko waye, ki ci gaba da saurarena. Mutumin na
kashe wayarsa sai ga lambar mukaddam ta shigo na yi sauri na amsa jikina na rawa. Sai
na ji y ace “sister madina wai me yake faruwa ne da Abba? Na ji ana ta kirana da lambar
sa idan na dauka sai na ji muryar wasu inyamurai daga karshe ma naji wayar a kasha.”
Na ce “nima ban sani ba, amma ka je gidan su ka duba shi ka gani.”
Sai mukaddam yace “ai Abba baya gida tun da asuba na kaishi tasha yahau doguwar
motar xuwa onisha.”
Sai na dora hannu a ka, n ace “inna lillahi wa inna ilaihi raji’una. Mukaddam me Abba xai
yi a onisha? ”
Sai y ace “babu yadda ban yi ba kada ya je y ace sai ya je wajen ‘yan uwanki su bashi
kwatancen inda xai samu yayanki innamani a enugu, yana ganin idan ya nemo miki
yayanki uwa daya uba daya wanda shine kadai dan uwanki wanda rashin sanin inda yake
yana damunki to yana ganin xaki dan tausaya masa ki aure shi ki tabbatar da gaske
yake sonki da aure. Abba yace kada na fada wa kowa a gidansu baya so ki ji.”
Ai ko rufe bakinsa bai yi bana katse wayar na rusa ihu na yi bakin titi da gudu, saura kiris
mota ta kade ni na tsayar da mai babur nahaye da sauri, kawayena da gudu suna kirana
tuni mai babur ya figa da ni, ce masa nake kara gudu malam yi sauri bamu tsaya a ko
ina ba sai kofar gidana, a inda na hango motar asibiti da marar lafiya a kwance abaya
tamkar gawa sai wadansu maxa guda uku. Na karasa gare su ina karkarwa suka bude
min bayan motar na leka dakyar na gane Abba daga kafarsa na shaida shi amma babu
mai gane fuskarsa saboda ta yi kaca kaca da raunuka. Kunnensa ma an manne shi dan
saura kiris ya fadi dan haka fuskar ta kunbure sumtum an nade da bandeji fari, bashi da
riga se dan gajeren wando saboda dorin karayar da aka yi masa a hannun hagu da kafar
dama kara bibbiyu sai kafadarsa wani katon rauni ne, an like shi da bandeji, sanna duka
ilahirin jikinsa babu inda babu rauni jini jage jage, a jikin shinfidarsa farare gasu nan a
gefansa a yayyage jawur da jinni tamkar an tsoma su a bokitin jinni a ka tsame su suna
ta diga.
Na tsala ihu na gigice ina tambayarsu me ya faru das hi? Ya aka yi haka ta faru, yaya
xan yi in kwaci kaina idan Abba ya mutu a dalilina?
Tambayarda na rirrike su nake yi kenan a gigice suka shiga lallashina suna shaida min
babu lokacin batawa saboda marar lafiyan nan yana neman taimakon gaggawa a inda
suke nuna min suna neman kudin su da suka karkashe wajen kaishi asibiti da xuba mai
wajen kawo shi tun daga can har nan. Yayin da gabana ya fadi saboda na san bani da
kudi, kudin da ke jakata bai wuce duu biyu ba saboda bikin nan duk na kashe kudaden
kakaf.
Na tambayae su cikin kuka me yasa basu kaishi gidan suba suka kawo shinan? Sai suka
ce min ai sanda yayi hatsarin yana Magana shine ya fadi sunanki yace matarsa ce, yana
so mu kira ki kuma ke ce last call dinsa da muka gani a wayarsa, ke yake kokarin kira a
sanda hadarin ya afku shi yasa muka kira ki, baki dauka ba daga nan muka ga wani
lambar mukaddam shima mun kira baya jin mu har cajin wayarsa yakare ta mutu shine
ya bamu adireshin ki yace idan muka xo kano mu nemi kaxaure mu shiga general
hospital staff quarters mu tambayi madina. Sai kuka ya ci karfin madina ta katse labarin.
Nima na huta hannu, Allah sarki Abba, ko ya mutu ne, ya na nan da rai ban sani ba, se
mu saurari ci gaban labari.
.
Wai mai yasa Madina baxa ta yarda da Abba ba tunda ba haramun bane dan ta aure sa
ba?
Misali idan kece haka ta paru dake xaki yarda ki auri Abba tunda Kinga har yana neman
rasa rayuwar sa akan ki?
Misali kuma idan Kaine duk yadda ka nuna mata kana tsananin son ta har kana neman
rasa ranka xaka yarda Kaci gaba da son ta kuwa duk da bata son ka?
ADON DAWA
TRUE LIFE STORY
LITTAFI NA BIYU (P 15)
NA JAMILA UMAR TANKO
GABATARWA SADIQ HALIMA (Sadin Maa)
DAGA Al-Hada Hada Hausa Book stories
.
Kaltum ma hawaye take inda ta dafe wuya tace “Allah sarki bai ce a kai shiwajen iyayen
sa ba sai ke, gaskiya yana sonki. Amma dai kin tausaya masa da kika gan shi a cikin
wannan hali? ”
Madina tayi murmushin karfin hali ta dafa kafadar kaltum t ace “na tausaya masa har na
fara nadamar wulakancin da na yi masa a baya. Dan na tabbatar ba son wasa yake min
ba. Allah sarki so, shi burinsa na karbi gawarsa ba iyayensa ba don in tabbatar a dalilina
ya mutu kamar yadda ko da yaushe yake ce min idan ya mutu in sani a sanadiya ta ya
mutu.
Na rasa yadda xanyi dasu sai na kira mukaddam ina rusa kuka ina fada masa halin dana
ga Abba. Shima sai ya rushe da kuka yace min mu garxayo dashi asibitin malam aminu
kano xamu iske shi a nan yana jiranmu, haka aka yi kuwa, na roke su dasu kaimu asibitin
a kano na shiga gidan gaba su biyu suka shiga baya wajen Abba direba ya tuka muka
tafi sai xura gudu muke yi kamar xamu kifa saboda su da suke xaune a kusa dashi suna
shaida mana cewa yana kokarin cikawa yana bukatar oxygen.
Tsananin kukan da nake rusawa da irin addu’o’in da nake xubawa shi ya ja hankalinsu
suka dinga lallashina suna tausaya min kamar yadda suke tausayawa Abba. Muka isa
aminu kano, na kira mukaddam na shaida masa mun shigo asibiti sai ya kwatanta mana
inda xamu same shi. Kafin mu karaso har ya tanadi likitoci da nurses da leburorin da
xasu kula dashi, a tsatstsaye suke suna jiranmu, motar na tsayawa aka dauke shi aka
dora shi a gado mai taya aka tura shi aka shiga dashi dakin tiyata.
Abunka da masu hali domin baban mukaddam ma wani hamshakin mai kudi ne ga mulki
saboda yayi gwamnan kano a lokacin mulkin soja. Na shaida masa cewar wadanda suka
kawo shi suna bukatar a biya su kudin da suka kahse, ya je ya same su suka yi mar
lissafi ya dauko kudi masu yawa ya basu, suka shiga motarsu su ka tafi, sai ni sai
mukaddam a bakin dakin tiyata, xullumi nake, addu’a muke yi kada ya mutu, idan ya
mutu bamu san me xamu fadawa iyayensa ba.
Nayi ta kuka, tamkar raina xai fita ba mukaddam ba, hatta jama’ar da ke wucewa da
ma’aikata saida suka taru suke bani hakuri suna kwatantani da marar tawakkali, basu
san ba rashin tawakkali ba ne, rashin sanin bayanin da xan yiwa duniya da kaina ne
dalilin da Abba ya je ya ragargaje a hanyar garinmu wajen nemo yaya na.
Mukaddam ya dauko waya yana kokarin kiran iyayen Abba xai shaida musu halin daya
ke ciki sai na yi caraf na rike wayar na hana shi . tambayata yake me yasa baxa’a fada
musu ba, halinda yake ciki ba?
Ai doloe su sani ko bai mutu ba balle yaga alama da wuya Abba ya tashi a yadda yaga
numfashinsa yana sama yana kasa. Ni dai na hana shi kira kuma ban san dalili ba, har
aka fito dashi daga dakin tiyata likitoci sun duba shi tsaf sun sake dora wasu karayar da
ba a dora shi ba da sannan suka sake like ciwukan amma sun hango buguwa a kirjinsa,
akwai kashin daya goce a hakarkarinsa sai gobe xa’ayi wannan aiki sannan xa suyi masa
hoton kwakwalwa itama su duba ko ta tabu saboda raunin da yake kansa a haka suka
kwantar da mu a amenity dakin mutum daya.
Mukaddam yabiya kudin daki mai tsada lafiyayya mai AC, fanka, firij da kujerun alfarma.
Mukaddam ya fita ya sissiyo mana abinci da abin sha , shi ma be iya ci ba balle ni, balle
kuma shi marar lafiyar wanda babu abunda yake yi sai suma an sakala masa roba a
hanci ana xuko numfashi, sai Karin ruwan da ake yi masa leda leda.
Ina xaune a gabansa a kan kujera yayin da nake rike da hannunsa na gaji da kuka sai
addu’a nake tofa masa Allah Ya tashi kafadarsa.
Yayinda mukaddam yake lungu yana ta sa addua’ar hankalinmu a tashe bamu Ankara ba
sha biyun dare agogon dakin ya buga ya yin da daidai wannan lokaci wayata da wayar
mukaddam tadau ruri. Ina duba tawa naga sunan sumayya tukur yayin da mukaddam na
duba tasa lambar mami hafsa tukur ce, maman Abba . sai gaba dayan mu muka mike
tsaye muka dafe kirji, muka xaxxare ido muka kalli juna. Na ce sumayya ce, yace, mami
ce, sai na yi saurin na karbi wayarsa dan kar ya danna . suka yi ta ringing har suka katse
yayin da na murtsika wayoyin na kashe gaba daya, duk na bi na rude, ban san me ya
kamata na yi ba.
Mukaddam na kokarin nuna min bai dace na kashe wayoyin ba saisu xaci ba lafiya ba ko
mun hada baki mun kashe shi musamman idan suka xo suka iske mu tare dashi a asibiti
cikin wannan halin, sai na cakumi kwalar rigarsa na matse shi a jikin bango Magana nake
yi cikin fushi da kururuwa ina kuka, nace kai ne duk munafukin da ka janyo mana,
saboda me xa ka kaishi tasha yahau mota ya tafi garinmu baka sanar min ba, baka
sanarwa iyayensa ba?
Dan haka baxa ka amsa wayarsu ba, in kuwa har Abba ya mutu ka sani gawa biyu xaka
kwashe domin ni ma sai na kashe kaina.
Kaltum ta tambaya “kuma ke lokacin da gaske kike xaki kashe kan ki? Duk wanda ya
kashe kansa dan wuta ne fa.”
Madina ta share hawaye ta yi dan murmushi tace “ba kashe kaina xan yi ba, bacin rai ne
kawai da tsantsar jin haushin mukaddam.”
Kaltum t ace “yaya kuka kare? ” madina t ace “kinsan kasa kwacewa yayi daga shaker
da na yi masa yana ta bani hakuri har saida Abba yayi Magana. Nan da nan muka
dungumo da gudu wajen gadon da yake kwance muna kiran sunansa idonsa a rufe
amma sunan madina ya ambata a hankali nan da nan na rike hannunsa na matso da
bakina saitin kunnensa na ambaci sunansa nace “Abba, ka ganni bude idanunka ka
ganni. “sai yayi ta kokarin bude idonsa amma ya kasa. Hawaye ne kawai yake tsiyayowa
daga idanunsa.
Ya fara Magana cikin sanyin murya wacce take fita a hankali y ace madina, ki yafe min
abubuwanda nayi miki sannan ki sani duk abunda ya same ni dominki bana nadamar son
da nake miki. Burina da fatana ki yadda da gaskiyar son da nake yi miki don kina xaton
yaudararki nake, ina so ki kasance akan gawata yayin da Allah Ya dauki raina tamkar
yadda mace ta gari take yiwa mijinta addu’a bayan ya mutu nima ki yi min saboda na
lissafa ki dan haka na ci burin na aureki Allah baisa kin fahimta ba.”
Na sulale na durkusa na dora hannuna duka biyu a ka ina rusa kuka gami da salati fadi
nake Abba na amince xan aureka, ka tashi kar ka mutu ka bar ni. Ya na cikin magana sai
jini ya ambulo daga baki da hancinsa, a guje na xura na kira likita. Ya na xuwa sai yace
xa su yi masa wata allura kafin gobe a shigar dashi tiyata idan iyayensa sun xo. Dan
mukaddam yace musu iyayensa ne xasu saka hannu, tun daga nan Abba bai sake
farfadowa ba barci kawai yake bai san inda kansa yake ba.
Jikina ya dauki karkarwa har saida na bawa mukaddam tausayi ya jawo ni ya xaunar da
ni akan kujera yayin daya durkusa a gabana yana xubar da hwaye yace, “sister madina,
naga kin rikice kin damu da yawa, na san abunda kike tsoro kada iyayensa su xo su ji a
dalilinki haka ta faru da shi kin manta da Allah ne Yake shedar bayinsa a nan duniya da
gobe kiyama?
Kin manta iyayen Abba musulmai ne, dole su yadda da kaddara mai kyau da marar
kyau?
In har bakya so su ji abunda ya faru na amince ba xan fada ba ki dauki jakarki ki fice
daga asibitin nan, kafin gobe su xo su ganki.”
Na girgixa kai na ce “idan na gudu shine xa su fi xargina su ce da sanina hakan ta faru
saboda dole sai ka fada musu a inda yayi hatsarin saboda ga motarsa nan daya fita da
ita a hannunka bada ita yayi hatsarin ba kuma dole likitoci sun dauki statement din yan
sanda da suka kawo shi cewar a hanyar onisha suka dauko shi. Don haka gudu ba nawa
ba ne duk daran dadewa gaskiya xata fito. Mukaddam, a ganin ka yaya iyayen Abba
xasu ji a ransu idan aka ce musu Abba ni yake so har ma dalilina xai rasa rana?
Me yasa ka bari Abba ya jefa kansa cikin wannan hali nima gashi nan ya jawo min? sai na
rusa kuka.
Mukaddam ya gyara xama ya bani labarin yadda abun ya faru daga farko har karshe.
LABARIN ABBA.
Mukaddam yace “tun muna yara idan kika lura Abba na sonki, ba son soyayya ba, yana
matuakr son ya xauna dake. Baya gajiya da sauraron labarinki haka baya gajiya da
kallonki, baya gajiya da yabon kirkin ki ko a bayan idonkine. Haka kawai kike burge shi
yadda ya ga kina da tsafta, kina kula da gidanki, yaranki da mai gidanki, yace baki da
kwadayi dan bakya roko sai abunda aka baki ki ke karba, baya ga rikon addininki bakya
wasa da sallah. Abba ya shaida min cewa ko ya girma xai yi aure sai ya duba mace me
tsafta da ladabi irinki sannan xai aura.
Bayan mun girma ya shaida min yana matukar damuwa da irin wahalhalu da wulakancin
da mijin ki da kishiyoyinki ke yi miki, hakan bai sa kin fice ba saboda biyayyar aure. Idan
muna xaune muna hira, sai ki ji ya tambaye ni yace, “mukaddam, anya kuwa a xamanin
nan xan samu mace kamr Madina? ”
sai n ace masa “rabo ne ai, kai dai kayi addu’a kawai. Abba yayi ‘yan mata da yawa
amma tun kafin aje ko ina sai dangantakar ta kwabe saboda bata da hali irin na madina.
Kinsan gidansu rayuwar turawa ake yi bai tashi ya ga mahaifiyar sa na yiwa mahaifinsa
hidima ba komai sai kuku da masu aiki ke yi, ke kuma ya ga komai ke ki ke yiwa mijin ki
hatta tsinke xaki mika sai kin taso da gudu kin durkusa har kasa sannan ki bashi haka
idan ya kiraki da gudu xa ki bar abinda kike yi ki je ki durkusa. Ba ki da lokacin kowa sai
kin salami mai gidanki ko kadan ba kya bata masa rai baki da kiwar aiki.
‘yan mata da dama sun so Abba sai sun fara sai ya daina yace baya son su, har Allah Ya
kawo lokacin rabuwarku ki ka bashi tarihin rayuwarki, ki kayi matukar bashi tausayi
musamman daya ji kince kin rasa inda xaki nufa baki da iyaye. Sai yace min yana
tausayinki yana matukar son yaga ya tallafawa rayuwarki kin koma cikin farin ciki kamar
kowace mace mai miji da iyaye.
Daga nan bai sake cewa komai ba sai da aka dade, sannan na lura yana cikin damuwa
na, na yi juyin duniyar nan ya ki fada min abunda yake faruwa sai ranar da muka je
kaxaure wajen ki kika kore mu nima ranar ya shaida min halinda yake ciki nayi ta bashi
hakuri kafin mu rabu yayi min alkawari xai hakura dake amma sai ya kirani a tsakar dare
yace ya kasa hakura dake gashi tunaninki ya hana shi barci. Muna ta addu’a amma abu
sai karuwa yake yi.
Ya ce min ya fi so ya auri matar daya ke tausayinta dan ya riketa amana. Burinsa ya raya
sunna kamar yadda Manxon Allah (SAW) ya auri Nana Khadija a baxawara, ta grime shi,
burinsa ya haifar miki da farin ciki, fatansa ya sami soyayyarki, ta iyayensa duk mai
sauki ne yasan yadda xai

Please Login or Register in order to submit comment