Reading adon dawa Chapter 34 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba a yin soye
soye mijin kuma dan gayu ne ya saba da snacks da shawarma, kazar kfc, mr biggs,
mcbanas, pizza a dubai ba ya cin tuwo idan baki iya ba kije Madina ta koya miki tun wuri
nasan ita ta iya.
kaltum da iyayenta suka tunzure da dariya yayinda mambela yake tsaye yana kallon
bakinsu ba tare da yasan abunda suke fada ba cikin harshen hausa, yaji yanaso ya koyi
yaren hausa domin yanajin dadin sauraronsa tun ba yanzu ba.
daga yadda alh Adnan ya fuskanci mambela yana yawan kallon kaltum ya tabbatar yana
sonta matuka har kamar zai hadiyeta, zuciyar sa na ayyane ayyane sai alh Adnan yaji
kishi ya turnuke shi babu yadda zai yine kawai yaga kaltum ta kara kyau dariyarta ta
zame masa lu'u lu'u a idanunwansa sai ya dinga karanta a'uzubiLlah minal shaidanir
rajim kuma ya gaggauta barin wajen, da mambela ya rakashi mota sai alh adnan ya
damko kudi ya bashi yace ya sayi duk abunda yake sha'awa, da farko mambela yaki
karba yace yana da kudin Nigeria daya canza kuma yana da dalar.
alh Adnan yace saiya karba dole don haka mambela ya karba yayi godiya,
alh adnan yaja mota ya tafi yayinda hawaye mai radadi ya dinga fita daya bayan daya
har saida ya ji turnukukin da yake damunsa ya ragu saboda karatun kur'ani daya kure a
rediyon motarsa, addu'ace maganin masifa
haka hakuri maganin zaman duniya ya isa gida kuma ya iske matarsa na jiransa domin
sai yanzu yan gulma suka kawo mata labarin aurensa da kaltum ta ayyana a ranta
tafiyarda ya tarka da tsakar rana zancen auren yaje don haka tace ya zaba ko ita ko
kaltum don bazata zauna da kaltum a matsayin kishiyarta ba.
saiyaji ya kasa magana kallonta kawai ya zauna yanayi saboda babu ciwon da yafi aibu
irin jahilci ya yarda jahilcine ke damun salaha
kamata yayi ta tambayeshi gaskiyar magana tunda bayayi mata karya ai zai fada mata
gaskiya saita yarda da gulmarda yan gari suka fada mata ta zartar da hukunci yasan
hankalin mata tunanin su ragagge ne a matsayinsa na namiji sai bai kula ta ba tayi ta
fadanta harta gaji ta daina.
kaltum da mambela sun kasance koda yaushe suna zama tare a kan wasu fararen kujeru
a farfajiyar gidan sallah da cin abinci ne kadai yake tashinsu hira kawai suke yi cike da
farin ciki marar misaltuwa idan dare
yayi kowa ya shiga barci sai su dinga magana a waya har assalatu sannan su tashi suyi
wanka suci ado su fito su kafa kujera su zauna hira.
sofi da saleh suna ganin ikon Allah yarinya ta iya hira rairairai duk da larabci suke yi basa
fahimtar abunda suke fada amma suna ganin murmushi da kashe ido da muryar da
takeyiwa masoyinta ko ba a fada musu ba sun san sai yanzu kaltum ta sami wanda
takeso wanda take ganin ya dace da rayuwar ta.
dan ladi direba ya zagaya da kaltum da mambela gidajen yan uwa da kawayenta, sunsha
zuwa gidan madina da abba su gaisheta, madina ta taya su murna tayi musu nasihohi
masu yawa ta rubutawa mambela duk abubuwanda ake bukata a auren hausawa ta
kuwa zabga kudi fiye da yadda aka saba , sadaki ne kawai ta rubuta kadan don neman
albarkar auren, dalilinta guda biyu na farko dan tasan suna da kudin sannan tanaso ya
kashe kudi yaji ajikinsa zaifi rike aurensa da daraja duk da tasan ya gama shan wahala
kafin ya sami kaltum, inda kudin yafi yawa shine wajen kayan lefe akwatuna shida tace
ya ciko da tsadaddun Kaya baya ga lifgin gwala gwalai data ce ya zuba, abun mamaki sai
taga bai damu ba harma yana ce mata yanzu haka saiya koma dubai don ya kai kudin
gwala gwalan kamfani suyi masa disign mai kyau wanda za a rubuta sunan a jiki da
sunansa.
satin mambela uku a kano acikin kwanakin daya yi saida sukayi kwana uku a zangon
daura kwanaki uku a garinsu sofi saleh da danladi direba suka raka shi yaje ya gaishe da
dangi su suka ganshi tabbas sunyi farin ciki da zuwan mambela don dollar ya dinga raba
musu nan da nan suka ji kaunarsa a ransu sunyi amannah ya aure yarsu.
ranar dayazo tafiya madina da abba da kaltum ne suka kai shi filin jirgi sai ga kaltum da
mambela suna kukan rabuwa, madina tana musu tsiya,
mambela ya tafi yabar kaltum zuciyoyunsu va
dadi amma bayan ya isa dubai sai suka bude shafin yin waya ba dare ba rana bai damu
da daruruwan dirham din da yake kashewa ba wajen kiranta ba shi dai shidai burinsa yaji
muryarta haka da ya isa sudan tun a Khartoum ya saka layinsa ya fara Kiran ta har saida
ya isa bur sudan yanzu service har garin yan ADON DAWA don haka ba dare ba rana
waya sukeyi saidai idan sallah zasuyi ko cin abinci da sauran uzururruka suna gamawa
kuwa to sai su hau waya ko dayake mambela ne mai kudin kira ita nata sakon wasika ne
tafi iya turawo da turanci koda larabci ko da wanne yare ne ma dai yana bata
amsa, kalaman dai naso da kauna ne da tsantsar bege duk wanda yasan kaltum saiya
san labarin mambela haka shima sarki ya rasa kansa ba ya zuwa fada ko kadan yana
daki a nade yana waya ko yaushe.
iyayensa sun yarda da bayanansa sun amince zasu shirya zuwa Nigeria.
saboda farin cikin an bashi kaltum mambela ya sami yan gidan su kaltum na bur sudan
yayi musu albishiri da cewa duk wanda a cikinsu yake so ya koma kasarsu ya dauki
nauyin biyan kudin motarsu da guzurinsu har zuwa Nigeria duk ya sadaukar saboda
kaltum,
su iya mairo da jikarta su akawa wannan saboda sun matsu su koma Nigeria amma babu
kudin mota, kadan daga cikinsu ne sukeson zama a bur sudan da yawansu sun amince
zasu tafi ya umurce su suzama cikin shiri sai daf da bikinsa da kaltum a kano bayan biki
zai bawa kowa kudin mota ya tafi garinsa, suka hau murna da tsalle suna masu yi masa
addu ar fatan alkhairi sai suka hau hada tsummokarai suna wankewa.
kaltum ma bata zauna ba ta amince da shawaran alh Adnan tana zuwa gidan madina
akai akai tana koyar abinci kala kala, i dan madina ta koma abuja sai mummy hafsat ta
koya mata ko ta tafi gidan dr sumayyah ranarda bata zuwa aiki ta koya ba abinci kawai
suke koya mata ba suna koya mata duk yadda ake zama da miji da yadda ake masa
biyayyah yadda za arike zuciyar mai gida yaji babu wata a gabansa sai ita.
.
RANAR DAURIN AURE
rana bata karya saidai uwar ya taji kunya watanni shida mambela ya dauka sannan ya
dumgumo yazo da iyayensa tafe suke da kayan aurensa kakaf, abun nayine sarki da
matarsa sun hallara haka baban mambela da mamarsa aka zo sai maza biyu tsofaffi da
mata biyu tsofaffi suka taho a jirgi.
dandazon yan gudun hijira motoci biyu j5 ne suka iso kofar gidansu kaltum da kayan su
mata da maza da 'yayansu kanana su suka fara isowa kafin ma su mambela su iso , da
yake ya shaidawa kaltum tun a waya kuma ya turo kudin da za a sauke su don haka tayi
tanadin zuwansu an nemi gidaje biyu haya daya mata daya maza, aka dinga dafa abinci
ana cika daruka ana aika musu aka daura auren mambela da kaltum, aranar wannan
asabar din alh Adnan ne waliyin amarya manyan mutane daga wuri daban daban sun
halacci daurin auren nan, kawun mambela daga dubai da manyan abokansa sunzo yan
uwan sofi daga camoroun sunzo matansu da mazansu haka yan zangon daura da yan
daura suma ba a barsu a baya ba.
alh adnan bai manta da malam Abdulkadir ba na Khartoum, ya aika masa da kudin jirgi
shi da dan rakiyarsa mutum daya suka zo.
madina da yayanta gami da mijinta da surukanta da 'yayanta suma ba a barsu a bayaba
dasu aka yi komai a wajen shagalin bikin,
sai salaha taji kunya jikin ta yayi sanyi data gano ba mijinta za a aura ba,
.
ADON DAWA 49
.
TRUE LIFE STORY.
.
sai salaha taji kunya jikin ta yayi sanyi data gano ba mijinta za a aura ba,
tayi bajintar da babu wanda ya yi saboda dawainiyar data yi da yawa ta buga kalandu da
memo da robobi da barguna bayaga abinciccika da ta dauki ma'aikata aka yita dafawa,
itace mai yiwa amarya kwalliya da zabar mata kayan da ya dace ta saka, a bangarenta
amarya da kawayenta suke hidiman su duniya kenan budurwar wawa wanda ya biye ta
saita kaishi ta baro shi, alh Adnan ya tsaya kawai yana duban matarsa yana mamakinta
domin a iya sanin da yayi mata ta tsani kaltum tun tana karama ashe a lokacin ma kishi
ne sai yanzu ta saki ranta kenan, sai ta shiga kame kame tana bashi hakuri a bisa rashin
mutuncinda tayi ta shuka masa a baya a rashin sani.
gaba daya liyafar bikin nan ita ta tsaya ta tsara ta yadda ya kamata, bini-bini ta dafa
amarya a dauke su a hoto abu kadan saita kira sofi gefe ayi shawara kanka ce kwabo an
kulla kawance ita da Madina da sumayya tukur har da musayan lambobin waya,
danta mashkur ma yazo daurin auren daga London sun sha hotuna da amarya haka alh
Adnan da amarya da ango anyi hotuna ba adadi.
sati guda aka kashe ana shagalin biki daga nan sai jama a suka fara watsewa da yake
kowa yasan ba anan za'a ajiye amarya ba don haka babu jere, fataken da suka yo kaura
daga bur sudan suka kama hanyar garuruwansu bayan mambela ya damka musu kudin
motar da zasu karasa garuruwansu, yan Niger suka kama hanya, sakkwatawa suma suka
nufi Birnin Shehu, daurawa ma suka nufi Birnin Daurawa suna masu godiya da fatan
zaman lafiya tsakanin ma aura ta, yan camaroun ma suka daure kayansu suka nufi gida
kanwar sofi ce joda
kadai bata tafi ba saboda sunanta ya fito a yan rakiyar amarya dubai.
malam saleh kuwa shine yace zai raka yarsa da kansa babu wanda zai wakilceshi daga
danginsa sai kuma salaha daga bangaren kaltum kenan duk mambela ya dau nauyinsu,
yan ADON DAWA ma sun juya zuwa kasarsu sarki ne kawai zai raka jikansa Dubai,
sai kuma Madina da Abba da suka dau nauyin kudin jirginsu daman sunada niyyar zuwa
su huta.
maimakon kayan daki sai alh adnan ya kunshe zunzurutun kudi har miliyan daya ya
bawa kaltum yace taja jari, jirgin emirate suka hau a legos basu tsaya a ko ina ba sai filin
jirgn nan mai tsananin kyauwu da tsari wato
emara airport, kaltum da mambela sunga abunda basu taba gani ba sai suka ware ido
suna kallo tunda basu saba fita ba kamar su Abba da mummy salaha ba har gara kaltum
ma ta taba ganin wasu abubuwa a makkah amma dai shekarun da yawa babu wanda
yakai joda dashi kansa ransa ya dade sarkin ADON DAWA shima bai taba fita ba idan
yayi tafiya mai nisa to Khartoum ne sai santi yake yana basu dariya suna kyakyatawa.
acikin dubai gida mambela ya kamawa kaltum haya a wani anguwa da ake kira bur
Dubai, dogon gini mai hawa ashirin ne gidaje don haka a hawana ashirin gidan kaltum
yake babu wahalar hawa bene saboda akwai wuta ba a daukewa, na'urane zata kai ka
cikin lokaci kalilan wato lifta.
tsantsari gidan yayi kyau domin an kara kayata gidan da kaya masu kyau da tsada da
kalar da ya dace, dakuna biyune gidan da falo daya dining area da kicin sai bandaki uku
hardana baki a falo babu wani abu na jin dadin rayuwa na wannan zamani da mambela
bai saka mata ba wannan shi ake kira aljannar duniya, abun dariya harda katon photo
yayi enlargement shida kaltum a bur sudan ya kafa a falo duk da basu waye ba anma
sunyi kyau.
sati guda sukayi agidan amarya, mata adaki daya maza adaki daya duk da mummy
salaha bata cika kwana agidan ba a deira take kwana cikin kasuwa saboda sare sarenta
daman yar kasuwa ce, haka Madina da abba ma sau daya suka kwana suka kaura hotel
sukayita yawo wuraren shakawa kala kala suna ta sayayyar abunda ya basu sha'awa
nasu dana yayansu da iyayensu, tsaraba duk daban daban kowannensu ya kama gaban
sa, ba a tare suka tafi ba sarki ne ya fara tafiya kasarsu ya tafi yana santin kyawun dubai
da
Nigeria ya kudira a ransa yana komawa gida zai umurci talakawansa su fito birni suyi
rayuwar jindadi, su fito da wannan dumbin dukiyarda suka boye suci su gina gidaje na
zamani sai yanzu yasan ashe ba karamar tauyewa kansu rayuwa suka yi ba, sai ya tuna
idan duk garin suka watse suka koma birni wazai mulka?
don haka ya canja shawara gara ya ce duk su rushe gidanjen katako nan da kaya suyi na
siminti gwamnati tayi musu kwalta fitilu, makarantu a garin haka kuwa akayi yana isa ya
kira taron gaggawa da manyan gari aka fara shawarwari.
daga baya mummy salaha, joda, malam saleh suka dunguma suka kama hanyar kasar
su, sai kaltum ta fara kuka ta sun yoye sun barta nan danan ta hakura dasuka lallasheta
saboda tana ganin Madina da Abba.
kwanakin madina biyu a asibiti da yake a alnahdah mai suna ZULAIKHA HOSPITAL ana
duba lafiyarta hawan jini da ciwon zuciya
AlhamduLillahi lafiya ta samu sosai ba kamar da ba yanzu batada wata matsala arayuwa
ciwo ne dai inya shigeka sauki sai a hankali amma lafiyarta kalau anan ne aka hango
mata dan karamin ciki da take dauke dashi dan wata biyu,
sai farin ciki ya lullube Abba kan kace kwabo ya buga waya Nigeria yana yadawa, suma
satinsu biyu sannan suka yiwa amarya da ango sallama zasu tafi, a filin jirgi kaltum ta
rugume Madina sukata kukan rabuwa.
Abba da mambela sukayita basu hakuri, kaltum tanaji tana gani suka tafi suka barta
daga ita sai mambelanta ido yayi jajawur tana zaune agefen mambela shiyake tukawa a
hanyar su ta komawa gida daga airport ya dubeta yayi murmushi yace kaltum sai nake
ta mamaki da naga kina kuka dan bakinmu zasu tafi na dauka yau murna zamuyi kowa
ya watse ya barmu don mu samu mu sha hirarmu mu biyu, saina fara tsorata nace a
raina koba wannan kaltum din bace take sona nake matukar kaunarta ba.
sai suka kwashe da dariya su dukka tun daga lokacin ta ware suka dinga hira har suka
isa gida suna shiga gida mambela yahau harhada musu kayayyakinsu a cikin akwatuna
guda biyu sai mamaki yakama kaltum ta tambayeshi ina zamuje da kaya?
mambela yace aimu da dawo gidan nan sai
nanda sati biyu banaso kiyi shara banaso kiyi
wanke wanke balle girki hotel zamu kaura a dinga dafa mana ana bamu.
kaltum zata yi magana ya toshe mata baki yace kada kice komai kibiyo ni kawai suka
rufe gidansu suka dura akwatinansu a cikin mota suka tafi.
dankareren hotel suka kama yana daya daga cikin hotel dinda akeji dashi a dubai gari na
wayewa saisu yini, wuni suna yawo manyan mall irinsu EMERATE MALLS DUBAI, MALL
CANIPOUR CITY CENTER, da sauransu duk abunda takeso mambela sae ya saya mata,
dayammah kuma sae su tafi Beach har sha biyun dare suna shagalinsu su shiga suyi
wanka su pito su saya gasheshen kipi da lemo mae sanyi su sha ko su shiga kfc suci
kaza da icecream daga nan suka kada sukayi cikin Deira land mark hotel suka sauka nan
ne ma dae kaltum ta dinga haduwa da hausawa yan uwanta mata da maza tayi ta jin
dadi,
kaltum ta kashe kwarkwatan idanuwanta don babu abin da ba a sayarwa nan ce babbar
kasuwar dubai babu kabilarda babu kusan duk park din da take dubae mambela da
kaltum sun zagaya, acan suka yini suna shan iska daga karshe kuwa cikin jirgin ruwa
suka kwana jirgine mae girmar gaske wanda ya hada da dakunan kwanciya ,dakin cin
abinci (restaurant)ga dakin rayel-raye da kide kide nan ne kadae basu zagaya ba sbd su
dukka malamae ne, idan suka so sae su hau can saman jirgi kololuwa nan kuwa katuwar
farfajiya ce babu rufi sae kujeru na shakatawa anan ne zaga dinga hango ruwan da jirgin
yake ciki yana tafiya ahankali anan zaka hango ruwanda jirgin yake ciki yana tafiya
ahankali anan zaka hango jirage da kwale-kwale ga jama'ah suna loda kaya a manyan
jiragen ruwa mae daukar kaya wanda ake turawa kasashen ketare.
bayan sun cika sati biyu sun dawo gidansu su cigaba da zaman cikin kwanciar hankali so
da kaunar da juna sae abunda yayi gaba sun shaku tamkar wasu tagwaye su yini tare su
kwana tare su fita kasuwa tare suyi aekin gida tare,
mambela yana godewa Allah da Ya yi masa kyauta da mace da tafi sauran mata iya
biyayyar aure, itama tana godewa Allah da Ya bata miji na gari mae tattalin mace da
kula da ita tamkar kwae, kaltum bata mantawa da ginshikin rayuwarta wato alh Adnan,
bata kwana biyu ko uku bata kirashi a waya sun gaesa ba, yana jin dadin wannan abu
yana gode mata sae yayita tambayarta ko akwae wata matsala ta fada karta boye masa.
tana shaeda masa bata da matsala ko kadan a rayuwarta da mambela.
Allah Ya saukowa alh Adnan dangana zuciyarsa ta yi sanyi ya cire son kaltum a ransa, da
matarsa ta gyara halayyarta sae shi ma suka dawo da tsohuwar soyayyarsu. tafiyar
kaltum ba dadewa ba ya shawarci matarsa zae bar wa malam saleh da sofi gidan nan
kacokan su koma babban gidan su bar boy,s quarters sae ta amince ya mallaka musu
har da kayan ciki harda motarda danladi yake tukawa ya hada musu da kudinda zasu yi
jari su ma su kula da kansu su bar zaman bauta a karkashin wani, yayi wa kano sallama
ya koma Abuja kacokan sbd rashin kaltum bayajin dadin shigowa garin sae dae in wani
uzuri daban ne ya kawoshi, ya sake gina wani gdn a can wani anguwa acan suke sauka
yanzu.
ranar da sofi ta shaidawa kaltum wannan abun farin ciki sae kaltum ta fashe da kukan
farin ciki ta kira alh Adnan a waya tayi ta godia tana kuka yana lallashinta ya bayyana
mata duk abunda ka bayar a duniya shine rabonka a lahira,
kaltum na can acikin kayataccen gdnta tana sha aninta daga kallo sae waya da en
nigeria yayinda mambela na can yana shirya mata abunda zai amfani rayuwarta.
da farko makarantar koyan tukin mota ya biya mata ta shiga bayan taci jarabawar aka
bata dariving liences sae ya saya mata mota tana tukawa ahankali tasan ko ina a cikin
Dubai, sannan ya kawo mata littatafae na karatu manya manya har ya gama yi mata
registration a tsadaddiyar jami ar nan dake cikin garin Dubai wato MIDDLE SEX
UNIVERSITY reshe ce ta university a england kwasa kwasan computer ne don haka a
shekaru uku zata kammala digirinta a bangaren computer.
batare da vata lokaci va ta para tuka hadaddiyar motarta zuwa makaranta tana jin dadin
karatun saboda tana ganewa sosae tayi kawaye dayawa acikin en matan ajinsu saboda
akwae en nigeria dayawa a makarantar kuma hausawa sai turawa da larabawa.
wanda yasan kaltum a shekaru hudu ko biyarda suka shude zaesha mamaki idan ya
ganta yanzu kamar ba wannan almajiran nan
mae bara ba, kaya ayayyage takalmi atsinke a daure da leda ko tsumma yanzu kuwa
sae kayi da gaske zaka tantance wannan bakar patace ko balarabiya sai kaga kamar
inka mata hausa zata fita da gudu tsabar firgita idan ka kalleta sae ka sake kallonta
tsabar kyauwun fatarta duk da akasarin shigarta na
dugowar rigace da dankwalin abaya wani
lokaci ma hijabine har kasa sbd mambela yana kishinta idan yaga kallon da ake yimata
yayi yawa sae yace ta saka nikafi.
da sukayi hutun makaranta sae shirya zuwa nigeria ganin gd sukaci sa a kuwa aranarda
suka iso kano ranar Madina ta haepi santalelen danta mae kama da babarsa abba, ranar
suna aka radawa yaro sunan kakan sa da babansa wato Tukur, ake kiransa da Khalifa
Abba Tukur.
kaltum da mai gidanta sunyiwa Madina Kaya iri iri da kudi masu yawa haka tayiwa
iyayenta da kannen ta tsaraba kala kala da akwatuna baya ga kudi masu yawa data
rarraba musu, sofi da 'yayanta mata kuwa harda sarkokin gwal da en kunnen su ta hado
musu.
satinsu kaltum uku a kano suka tapi Abuja gdn alh Adnan, shida matarsa sun karbesu
hannu bibbiyu sunyi musu hidima sosae suma kuma sun kawo musu tsaraba mae yawa.
satin su daya suka tapi sudan a bur sudan ma satinsu uku agarin en ADON DAWA, garin
ya gyaru anyi matukar sumun cigaba sarki yayi matukar wayerwa da talakawansa da
kae suna cin kudinsu yanzu suna sayan kayan more rayuwa sun fara gina gidajen siminti
suna dinka suturu masu kyau ankae musu ruwan famfo da wutan lantarki gami da titina
da makarantu duk acikin shekara guda.
su kaltum sunyita rabon tsaraba babu adadi, kaltum takai ziyara gidansu na da taga
dakunansu har yanzu kuwa akwae saura daga ire ire mutanen tawagarsu wadanda zama
Ya Mike sukayi aure suka hayayyafa sun ganeta kuwa kamar yanda ta ganesu tayi musu
kyautar girma sunyi farin ciki,
kaltum bata manta da abokinta ba Karim mae kamun kifi yana nan a inda tabarshi ya
auri yar ADON DAWA har sun haefu yayi farin ciki da ganin kaltum musamman data yi
masa kyautar kudi da kaya mae yawa,
kaltum ta zagaya bakin kogi enda suke zama sannan ta zagaya garin Jange daga can
suka shiga Jim Arab kasuwar yan ADON DAWA kae tsaye ta tunkari rumfar tsohon nan da
ya kwace ta ahannun mambela da abokansa ta
tarar bayanan sae dansa ya shaeda mata Allah Ya yi masa rasuwa, saeta bawa dansa
kudi tace mahaefinka ya taemake ni bazan manta da shiba zan zamo mae yi masa
addu'ah duk sanda na tuna shi, Allah Ya yi masa rahma amin.
suna tafiya acikin tsaleliyar motarsu mambela ke tukawa a hanyarsu ta tafiya Khartoum
suma takae musu ziyara taga yan gidansu suna nan kamar yadda ta barsu taga malam
Abdulkadir da matansa ta kuma gwangwajesu da kyauta daga nan aka rakasu
gidan Fatsuma da Musa a can wata unguwa suke nesa, sunyi aure suna zaune lafiya
harda 'yayansu guda uku. fatsuma tasha tsalle da murna da taga kaltum da kyar ma ta
ganeta sbd canjin da ta samu sae alokacin take ta bawa kaltum labarin mambelane ya
musu komae na aure hatta gidan nan shi ya kama musu ya biya musu hayar shekaru
biyu sanan ya ba su jari.
kaltum ta sha mamaki don ko kadan bai taba fada mata ba ya dai ce mata fatima da
musa sun yi aure a Khartoum.
agidan fatima kaltum da mambela suka kwana dayake gidan dakuna 2 ne kuma basu da
talauci suna rayuwa cikin rufin asiri, washegari suka koma bur sudan bayan sun ambulo
musu makudan kudi.
duk inda kaltum taje saetayi kuka saboda tana tuna baya tana tausayawa wadanda har
yanzu suke cikin wannan rayuwa Allah bae yanke musuba tukunna.
hutunsu ya kare sae suka koma Dubai sukaci gaba da rayuwarsu,
lokaci daya mambela ya kira kaltum ya danka mata kudinta dala dubu goma da alh
Adnan ya bata tun lokaci aurensu ya kara mata da wasu yace ta kira iyayenta a waya
tayi shawara dasu ta zabi kasuwancin da zata dinga yi tsakanin Dubai da zuwa Nigeria.
kamar da wasa suka fara yi da Madina tana turo da kaya tana sayar mata a Abuja sae
malam saleh ma ya ke karbar kayan yana rabawa yan kasuwar sabon gari da kasuwar
kwari bayan sati biyu sae su hado masa kudi ya dauki ribar sa ya turo mata uwar kudinta
da ribarta kafin kace kwabo kasuwanci ya Mike suna samun alkhaeri, gaba dayansu
kannen kaltum sun warware sun goge sunyi kyauwun gani suna karatu a makaranta
masu kyau sunyi sallama da talauci a rayuwarsu.
Madina kuwa haehuwace ta mike kafin ta yaye khalifa ta sami wani cikin ta kara
haehuwar namiji sae suka saka masa sunan Adnan sbd alkhairan da alh Adnan yayi
musu.
yaji dadi matuka alh Adnan da wannan karar da suka masa alokacin kuma matar
mashkur ta haehu shima da namiji aka saka masa suna Adnan ake kiransa Amir, sae ga
waya daga Dubai aka shaeda wa alh Adnan kaltum
ta haihu na miji ansa masa takwara ana Kiran sa Daddy.
sae alh Adnan yaji hawayen farin ciki ya surnano daga idanuwansa.
mace mae kamar maza madina ta kutsa garinsu onitsha tana yakar arnar da har yanzu
basu san akwae ubangiji ba wanda ya halicce su, bada makami take yakarsu ba da
siyasa take samun galabarsu daya bayan daya take
zakulowa tana tahowa dasu Abuja ta zauna dasu ta cusa musu ra ayinta har sae sun
gamsu ta basu jari da wajen zama saesu musulunta gobe ma idan taje wata zata jawo ta
taho da ita, da kadan kadan suketa musulumta har suma wadanda suka musuluntar
suke jawo wasu zuwa musulunci.
yayanta Abdullahi shima da shawarwarin Madina yake aeki tasashi ya musuluntar da
uwar gidansa uwar 'yayansa da 'yayansa kakaf sannan tasa ya kwaso su dukka suka
kauro Abuja suka shiga islamiyya suka sami ilimin addini.
.
ADON DAWA 50
.
TRUE LIFE STORY.
.
da wannan karar da suka masa alokacin kuma matar mashkur ta haehu shima da namiji
aka saka masa suna adnan ake kiransa Amir sae ga waya daga Dubai aka shaeda wa alh
Adnan kaltum ta haehu na miji ansa masa takwara ana Kiran sa Daddy, sae alh Adnan
yaji hawayen farin ciki ya surnano daga idanuwansa.
mace mae kamar maza madina ta kutsa garinsu onitsha tana yakar arnar da har yanzu
basu san akwae ubangiji ba wanda ya halicce su, bada makami take yakarsu ba da
siyasa take samun galabarsu daya bayan daya take
zakulowa tana tahowa dasu Abuja ta zauna dasu ta cusa musu ra ayinta har sae sun
gamsu

Please Login or Register in order to submit comment