Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sai ya fara romancing ɗin ta da zafi-zafi kamar zai zarce sai kawai ya ji wata iriyar fad'uwar gaba ta kama shi ya dakata duk da yanda Jameelar ke maqale masa watarana har kuka take yi amma haka zai qi ci gaba ya bar ta. Umar na son ya san waye ya yi mata fyad'e ta na qarama yana kuma tsoron me zai ji da zai tarwatsa tunanin shi, a qarshe ya yanke shawarar sai ya kaita asibiti an gwada ta in bata ɗauke da wani mugun ciwon to a sannan ne zai kusance ta, ba zai bari kowa ma ya sani ba sai sun koma gidan su sannan zai keb'anta da ita. Jameelaah kuwa ta yi duk yanda zata yi ya neme ta abun ya ci tura basirar ta har neman qarewa take yi, shi kan shi ya na buqatar kasancewa da ita amma tsoron mai zai tarar ke dakatar da shi, a yanzu dai ya yanke shawarar kafin lokacin komawar su ya cika zai ce su koma kawai dan ba zai iya qara sati ɗaya ba ba tare da ya san matsayin Jameelaah ba a likitance shin ta na da lafiya ko bata lafiya. Umar ne ya kai ta gidan bikin bayan ya bata kuɗi da zata yi liqi da su da wanda zata riqe ko da za a buqaci wani abun ta taimaka da shi a wajen bikin kamar yanda ta ke ta yi tunda aka fara shirin bikin,gaba ɗaya hankalin matasa da 'yan matan da ke qofar gidan duk ya tattare ya koma kan Jameelah da Umar tare da motar su dabuwa dal da aka ajiye ta a cikin ta, ko da ya ajiye ta sai da suka ɗan taɓa hirar su ta soyayya sannan ta ja ledar da ta boyo ta ajiye a gefen qafar ta ta busa masa sumba sannan ta fita suna murmushi tare da d'aga wa juna hannu ta shige cikin gidan su ta na taku kamar wata sarauniyar mata, ta na shiga ta tadda qawayen ta da su Mamalo ana zaune a tsakar gida, ihu wajen ya ɗauka Mamalo ta ce, "Heeeeeeeee shegiya qawata ! kina wutaaaa hajiya ta ina bin ki da fetur, dan Allah ku matsa ku bata waccan kujerar ta zauna qawata ba ta zama a tabarma bace, kuna ganin ta kun ga matar manya," Jameelaah kuwa nan da nan ta hau jin kan ta kamar zai fasa gini dan girma,har wani d'age gira guda ɗaya take yi, zama tayi ta harɗe qafa, sannan ta zaro gudummawar wata atampa mai mugun tsada dan neman suna a gaban qawayen su na layin ta bawa Mamalo, "Ga gudunmawa ta nan na kawo maki,ko yau ki ke so a d'inka maki ita a layin nan sai an d'inka ta saboda tsadar ta na ga dacewar na kawo maki ita a kai ki gidan miji da ita dangin sa sun san basu saka maki kamar ta ba a lefe dan haka kin ga ba raini zaki kankaro wa kan ki aji, ga wannan a kai ɗinki yanzun nan a kawo mana ita an jima a dinke," Shewa wajen ya ɗauka da shi ana yabawa da jinjina wa babbar qawar amarya, wasu kuma suka hau fad'in, "Ji baqauyiya kamar wadda tazo zanen suna, meye na kawo atampa ana bikin aure a matsayin gudummawa? Ko dan a nuna mana an kawo babbar atampa ne oho? Aikin banza kawai lalle a mazaunai,ai dama shi ɗan talaka bai iya samun arziqi ba sai ya nuna daga geto ya fito," Cikin turancin ta na 'yan qaramar sakandire Jameelah ta fara magana ta na yatsina hantsi ta ce. "What say? Say it loudly mana to hear u, ashe ma kuna jin tsoro na har yanzu, ni yanzu kun san i am not ur mate, dan kun samu ma mun gayyace ku bikin ne amma ba laifin ku bane, qazamai kawai" Tsit wajen ya yi, saboda da damar su gayu iya gayu an sha shi amma ba boko, ga kyau da iya ɗaukan wanka, amma wasu ko arabin ma babu,ba dan ba su zuwa ba ah ah sai dai kawai idan an je ba a maida hankali a yi karatun da ya kamata har a iya turancin. (Wasu daga yaran cikin gari haka suke,i repeat wasu ba dika ba, kar a ce na zagi 'yan cikin gari nima ita ce, da damar su sunan an je makaranta ne kawai an b'ata lokaci da kud'in makarantar amma ba a maida hankali a koyi abinda ya dace, haka zaka ga yarinya ta gama secodary school amma ba zata iya yin sentence ɗaya kwakkwara ba da kalmar turanci, na sani turanci ba shi ne ilimi ba amma yana daga cikin abinda idan mutum ya na fahimtar shi to an san ba asarar kud'in makaranta aka yi ba a kan shi,tunda karatun namu na Nigeria da turancin ake yin sa idan baka ji ta ya zaka fahimta? Dole sai an fassara maka zuwa yaren ka sannan ka gane me ake koyarwar, gashi da damar maza ba su cika son zuwa islamiyya ba da sun je na ɗan shekaru kafin su balaga shikenan suna balaga ake neman wasun su a rasa a islamiyya, dan haka mata musamman na cikin gari dan Allah mu dage da neman ilimi mu karya record ɗin da aka yi mana mara kyau mu bawa mutane mamaki da kunya akan tambarin da akai mana na rashin ilimin addini da zamani) Ta na gama zuba masu rashin kirkin da ta ga dama ta miqe ta shiga d'akin su suka gaisa da Ramai, ta bata kayan da ta deb'o mata da kuɗi, sannan ta bata na baban su ta kuma jaddada wa Ramai akan ta bawa Baban nasu dan ta san halin ta, in ma bata bashi ba zata kira shi ta faɗa masa ta bata kuɗi ta bashi, tsaki Ramai ta yi ta hau masifar dan za a bata abu shine sai an yi mata rashin mutunci,Jameelah bata bi ta kan ta ba ta yakice mayafi da jakar ta ta shige cikin 'yan biki aka ci gaba da shagali da ita. Biki ake ta sha ana tiqar rawa a ɗan tsukukun lungun su Jameelah duk da cewar ango ya hana amma sai da Jameelaa tai uwa tai makarb'iya tasa yaran layin suka samo redio da sipiku manya aka dasa, Bukar da abokan sa ne suke kula da kid'an har magariba ana nan ana abu ɗaya,inda Hajiya Jameelah ta dinga liqa kuɗi ta na taka rawa fili ya zama kamar dan ita aka buɗe shi. Wayar Jameelaah ce ta fara ruri tana dubawa taga Umar ne, da sauri ta fita daga filin rawar ta faɗa soron gidan su ta amsa wayar, umarni ya bata akan ta fito za suje wani waje daga nan sai su wuce gida, in yaso gobe ta dawo a ci gaba da bikin da ita zai ma raka ta har kai amarya. Ta ji dad'in hakan kuwa sosai dan kuwa zai qara d'aga ajin ta a wajen mutanen layin su, qawayen ta zasu ga mijin ta kyakkyawa na nuna wa sa'a ga kuma kuɗi ya na da su masu gidan rana,gida ta shiga a guje ta hau tattara kayan ta, cikin sauri ta ce wa Ramai, "Ramai zan tafi yazo yana jirana a waje," "Wai yanzu yarinyar nan ba zaki duba roqona ba da nake ta yi maki na tsahon shekara biyu, dibe ki ki ga yanda kika sauya kin yi jajawur dake kin yi bulbul gwanin sha'awa amma mu muna nan muna ci gaba da dirzar wahala, kin kasa koda sama mana gidan haya ne mu tashi anan mu koma can mu huta da wannan muguwar rayuwa?" Shigowar Baba kenan daga wajen aikin sa, duk da be so dawowa gidan ba a wannan lokacin duba da yanayi ne na biki mata za su cika wajen to amma yunwa yake ji ba shi da kud'in siyan abincin sayarwa a waje Ramai kuma bata yi hankalin aika masa koda abincin biki bane balle wanda ya bayar a dafa da gumin sa,cikin takaicin jin maganar Ramai ya ce, "Wai Ramai yaushe zaki yi hankali ne dan Allah? Haqqin ta ne nema mana gidan haya dama ko kuma haqqi na ne a matsayina na mijin ki kuma uban yaran ki?nace banda niyyar tashi anan yanzu saboda banda halin kama wani da ya fi wannan dole ne sai kin yi rayuwar jin daɗi a lokacin da Allah bai nufa ba?" Cikin d'aure fuska Ramai tace, "A gaskiya kana shiga haqqina da yawa malam to ni na gaji da irin wannan muguwar rayuwar hakuri na ya gaza, haba ! gida sai kace na gado, tin kan a haife ta muke nan kowa a nan ya sanni, ba zamu samu mu sauya rayuwa ba, ana ta mutuwa sai mu zauna bamu mori duniya ba, qiyamar ma baka da tabbas," "In har kina bauta ma Allah da gaskiya, kina kuma kwadayin rahamar shi Allah zai baki aljanna dan ya yi ma wanda ya yi kwadayin rahamar shi alqawarin samun rahamar," "Kai ka san wannan ni dai na gaji ehe, nace na gaji a dau mataki akan wannan muguwar rayuwar da muke ciki ko kuma na dauka da kaina,habaa sai kace akan mu talauci ya ƙare?" Juyawa ta yi dan ta yiwa Jameelaah magana taga wayam ba ita ba labarin ta,haka tai ta masifa tana gwada layin Jameelaah da 'yar qwabirar wayar ta amma ana yi mata turanci, soke wayar ta yi tana fadin zasu gamu ne goben. Hanyar asibiti ya ɗauka da su, dan kuwa a yau zai kaita a dau jinin ta a gwada ta in result ya fito ya ga lafiya take to a washegari zasu koma gidan su, dan kuwa komai na more rayuwa an zuba a gidan su kawai yake jira ......... *Allah ya kaimu goben muji meye sakamakon gwajin jinin da za a yi wa Jamcy baby, shin makaranta Umar ya kyauta kuwa da zai je ayi gwajin jini bayan Jameelaa bata da masaniyar me za ayi?* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 16: Ana gama d'iban jinin ta ya ce wa masu gwajin su yi mashi gwajin da suka yi magana za a yi akan wannan jinin yau zai je ya dawo,daga nan parking space suka wuce suka shiga motar su ya ajiye ta a gida, ta yi masa tambaya gwajin me za a yi mata yafi sau a qirga amma bai bata amsa ba, qarshe sai ce mata ya yi gwajin malaria ya kai ta a yi mata,mamaki take ta yi dan dai bata ce masa bata da lafiya ba ita rabon ta da ciwo ma musamman wanda zai kwantar da ita har ta manta, daya ga bata yarda da shi ba sai ya kama hannun ta yace. "My love tinanin me ki ke yi ne haka? Ko baki yarda da abinda na faɗa maki bane?" "Kawai ina mamaki ne Yah Umar akan gwajin da ka kawo ni a yi min naga ni dai lafiya ta qalaou," "Kin san yanda nake matuqar son ki ba zan so ki shiga cikin lissafin masu malaria na duniya ba a shekarar nan da za mu shiga, ko baki da masaniyar yanda malaria ke kisa ne kuma duk shekara ana tara data na iya adadin mutanen da ke ɗauke da cutar malaria na duniya? Qungiyar Wold health organization na fitar da wannan qididdiga duk shekara ki bincika zaki tabbatar da hakan,Baby dik abinda zai zama barazana ga rayuwar ki inshaa Allahu in ina da iko zan kawar da shi tun kafin ya riske ki, yanzu yayin mace-mace ake yi saboda wannan mummunan ciwo na malaria dan haka dole na kula dake," Jameelah ta ji daɗin kalaman shi sosai, saboda irin wannan kulawar da ya ke bata tana qara sanya mata hakuri da juriya akan qin kusantar ta da bai ba har na tsawon wannan lokacin,amma a qashin gaskiya ta fara gajiya akan rashin kulawar aure da yake bata,ita ai ba dutse bace in shi dutse ne, tana wanan tinanin ta ji buɗe qofar motar shi ya fita, nan ko bata san yana ta yi mata magana ba ma,itama fita ta yi suka shiga gidan a tare,cikin sauri ya juya ya gaishe da Mum da ke zaune a parlour ta na kallo,tambayar shi ta yi, "Saurin me ka ke yi haka Umar?" "Mum ina son naje na amso wani abu ne, yanzu nan zan dawo da yardar Allah akwai wani abu ne?" "No ba wata damuwa dama ina son na sanar da kai ne ko zaku bar komawar ku gidan ku sai ranar juma'a ɗin anan mai zuwa? Saboda akwai gyare-gyare da nake son na yi wa Jameelaah, domin so nake ku koma gidan ku kamar ranar aka yi auren ku, tabbas kun yi min biyayya dole ne nima na kyautata maku, fatana Allah ya yi muku albarka, ya baku masu yi maku biyayya fiye da yanda kuka yi min,ba kowanne ɗa bane zai yi abinda kuka yi, na sani ban kyauta ba dokar da na sanya maku ta yi tsauri, sai gashi kun bani mamaki har bayan kammala karatun ka Umar kuna riqe da kan ku kuna jiran umarni na da amincewa ta,ko da ace kun saɓawa doka ta ba ku yi laifi ba, amma riqe alqawarin da ka yi ya qaramin ganin qimar ka da son ka da kuma son na ga na qara kyautata maku dika a matsayina na uwa a gare ku," "Muuuummm, zaki sa na yi hawaye amma na farin ciki, na ji daɗin addu'ar ki sosai a gare mu Allah ya amsa, bari na yi sauri na dawo ana jirana" Kyab'e baki Jameelah ta yi ta wuce d'aki,cikin ranta ta na ayyana yanda zata muzgunawa Mum a duk sanda ta samu dama itama dan kuwa wannan ba qaramin zalunci aka aikata mata ba, mum kuwa ta zaci tsabar kunya ce ta hana ta tsayuwa a wajen ta gudu d'aki sai ta yi murmushi ta maida hankalin ta akan Umar ta ce masa, "To sai ka dawo," Da hanzari ya koma asibitin, sai da ya tsaya ya yi sallar Isha'i a masallacin da ke cikin asibitin sannan ya qarasa lab din, ana miqa masa result ɗin ya damqe shi tare da yin godiya mai yawa ya fita yana yi musu sai da safe. Zaune yake a mazaunin driver ya kasa buɗe takardar saboda fargaba,da kyar ya samu ya buɗe sakamakon da ya gani ya yi matuqar sanyaya zuciyar shi, wata hamdala ya dinga saukewa, sannan ya hau tasbihi ga Allah cikin farin ciki ya ke fad'in, "Na yafe ma dik wanda ya yi maki fyaden nan tinda bai goga maki ciwon da zaki haramta a gareni ba, na yafe masa duniya da lahira, na yafe masa duniya da lahira, na yafe masa," Nannad'e takardar yayi ya yagata ya zubar, shopping yaje ya yi wa Jameelah na kayan kwalama sosai da kayayyakin shafawa da turaruka masu kyau da tsada, sannan ya yi ma Mum da Umaimah siyayya suma, Dad ma ya sai mashi turarukan da yasan yana so. Gida ya wuce cikin farin ciki lokacin kowa yayi bacci banda Jameelaa, idon ta biyu ta na ta tinanin ina Umar ya shiga gashi har ta yi wanka ta shirya cikin kayan bacci jikin nan ta mulke shi da lotion mai gyara fata gashin ta ya sha gyara sai sheqi yake,sweet ce mai qamshi a bakin ta ta na ta tsotsa saboda tun tana gida ta tsani wani ya ji warin bakin ta balle kuma Umar da take mugun so. Da kaya niqi-niqi ya shiga gidan, d'akin Umaimah ya leqa ya ajiye mata ledar ta a gefen gadon ta, sannan ya aje na Mum a d'akin ta itama, dan kuwa bata d'akin ta na d'akin Dad,duk abinda yake yi akan idon Jameelaah yake aikatawa, tsaki taja mai qarfi sannan ta ce, "Dik bari mu koma sabon gidan mu za ku sha bakin mamaki ko ganin shi sai ya yi maku wahala, komai wai sai an yi raba dai-dai da ku, sai kace mijin su aikin banza," Ta na nan ta na surutu da baƙin ciki ya koma parlourn bata sani ba sai jin muryar shi tayi ya na fad'in, "My love ke da wa ki ke magana? To ayi hakuri indai ni ne gani na dawo, muje ciki ko?" Washe baki ta yi tare da amsar leda ɗaya dake hannun shi suka shiga d'akin su,suna shiga ya baje kayan a gaban ta tare da d'aga ta tsaye, ya manna ta da qirjin shi, cikin farin ciki ya ce, "Love na amso sakamakon  gwajin da aka yi maki kin samu nasara baki dauke da ciwon qa.....mammmamalaria," Cikin sauri ya sauya akalar maganar tashi kallo ta bishi da shi dan son gano me yake boyewa,idon shi tsilli-tsilli kamar na munafukin da aka turke ya na tsaka da gulma, sakin ta ya yi da sauri ya fara d'aga rigunan bacci  dogaye biyu daya siyo mata masu mugun kyau, chocolates da sweets gasu nan barbaje a qasa, nan da nan kuwa uwar kwad'ayin ta basar itama kamar yanda ya yi ta hau duba kayan da ya kawo mata, wata leda ya janye gefe idon ta na sauka akan ledar ta miqa hannu da sauri ta ɗauke ta na dariya, "Wannan turarukan na waye?" "Na Dad ne gobe zan bashi tinda sunyi bacci yanzu," Ranta bai so ba sam duba da yanda ta ga ya yi wa Mum da Umaimah ma siyayyar amma ta maze ta ce, "Ohhhh d'a da daɗi kaga ka sai ma Dad turare dan neman albarkar shi, Allah ka ban iko na kammala karatun nan na samu makarantar gaba da sakandire na gama ta nima na fara aiki na dinga sai ma iyayena abubuwan more rayuwa ko zan dinga samun lada kamar yanda ka ke samu a koda yaushe ,gaskiya Yah Umar in mutum na zaune da kai sai ya iya abubuwan alkhairi kala-kala," Ya ji daɗin yabon da ta yi masa, amma kuma sai ya ji bai kyauta ba da bai sai ma mahaifan ta komai ba, shi ya sai abubuwa ma nashi iyayen amma baya tunawa da nata sam,wayancewa yayi ya ce, "Ai wannan ma harda Baba na siyo, nafi son na bashi da kaina ne, saboda ya samin albarka," Kauda kai tayi ta murgud'a baki, taso ya kawo ledar da ya kaiwa Mum d'akin ta dan ta samu na daukar ma Ramai, amma ba komai zata fanshe ne a wani wajen watarana. Godiya ta yi ta masa har sai da ya rufe mata baki da nashi su Jameelaah an samu abin nema, ai kuwa ta qanqame shi ta hau shafa sassan jikin shi, Umar ya jiqu matuqa da salon Jameelaah, da kyar yake fidda numfashi tsabar yanda ta kannad'e shi kamar an ce mata guduwa zai yi. Ganin yanda ta kai qirjin ta saman fuskar shi ne ya sanya shi saurin janye ta a jikin shi, yana neman iska dan ya shaqa, hawa saman gado yayi ya kwanta ya yi shiru ya na qoqarin daidaita kanshi,Jameelah kuwa tana nan kwance a aqasan carpet tana maida nata numfashin cike da matsanancin takaici, wannan wace irin rayuwa ce suna zaune gida ɗaya daki ɗaya da mijin ta amma saboda wata dokar banza ba zasu iya jiyar da junan su daɗin zaman aure ba, wasu hawaye ne masu zafi suka gangaro mata. Umar idon shi lumshe suke yana sauke numfashi a hankali, gaskiya hakurin shi ya qare ba zai iya bari har juma'a ba kafin ya keb'e da matar shi inaaa ba zai iya ba hakurin shi ya qare, ya ma yi qoqari ai,a da fargaba da tsoron kamuwa da ciwon qanjamau na tsaida shi tare da dokar Mum ta ya bari ya kammala karatu,to a yanzu menene ke tsaida shi kuma? Babu komai, dan haka gaskiya gobe zai sama wa kan shi da matar shi mafita. Jameelaah a nan ta fara yin bacci Umar ya yi bakam kamar wanda yayi bacci, sai cikin dare ya tashi ya je d'akin Mum din shi ya duba keys ɗin gidan su ya zari biyu ya fice, d'akin su ya koma ya kwanta. Da safe Jameelaah ta gama dik wani shirye-shiryen tafiya gida yau za a kai amarya, daga yau an gama biki, Mum ta bata kuɗi mai ɗan yawa da atampa da sabulai na wanka da wanki da babban ledar omo ta ce ta kaima Ramai, daf zata fita ta hanyar kitchen Mum ta bita, dan bata son surukar ta ta taci gaba da satar abinci, dan haka tace "Jameelah bari na d'eba maki ɗan dankalin nan ki kaiwa Maman ki, ki ce ina gaida ta" Cikin kame-kamen ko dai an gano ta ne ta tsaya cak, sai zaro idon ta da yasha kwalliya take waje. Tana nan tsaye mum ta ɗebar mata dik wani abu data ga ya dace ta bata, Drivern dake kaisu makaranta shi ya kai ta, Umar yace tayi gaba taje gidan su, in ya gama abinda yake zai je ya ɗauke ta ya kai ta gidan amaryar. Koda sika isa gidan ta tarar da gidan cike yake ana ta hada-hadar biki, masu biki na nan na ta hidimar su gefe ɗaya masu sana'ar abinci na kullum na nan basu fasa ba, dan kuwa Ramai ma tayi nata yana can qofar gida ana ta saidawa, lungun shaqe yake da mutane kala-kala, can daga nesa ta hango yaran gidan nasu wasu na wasa wasu na zaune kawai suna kallon masu shige da fice, sai ta kira su ta sa suka d'ibar mata kaya suka nufi cikin gidan da shi, sai wani shan qamshi take yi ita a dole driver ne ya kawo ta, ga kaya nan niqi-niqi ta kawo gidan su, ai kuwa ta yaqi 'yan matan dake zaune a waje ana ta budiri da samari,nan da nan suka hau gaishe ta suna haɗa baki wajen fad'in, "Jameelaah kin iso kenan, sannu da zuwa.....Jameelaa sannu da zuwa.....jameelaa tare zamu tafi gidan amarya anjima...." Sai da suka gama surutan su ta d'aga masu hannu ta ce, "Sannun ku," Ta yi shigewar ta cikin gidan su ta bar su nan tsaye baki sake, ai kuwa samarin wajen me za suyi in ba dariya ba, nan aka dinga yi ma matan da Jameelaa ta wulaqanta dariya, tin suna iya kare kan su har suka kasa. Ramai na ganin an fara shiga da kaya ta hau gud'a tana yiwa Jameelah kirari har sai da ta shige d'aki tana wani nuna Kyankyamin zama a dakin,cikin yatsina fuska ta ce, "Ramai ina kud'in ledar d'akin dana baki ne dan Allah?" "Na cinye dan uban ki,ke bari ki ji fa ba yanda za ai na saka ledar d'aki anan wajen dik a lalace, in kina son in kin zo ki zauna a waje me kyau na sanar dake ki sa mijin ki ya kama mana haya amma kin qi, kamar ke ɗaya kike son hutun" Shiru tayi dan ba ta son su ja maganar ta yi nisa, Ramai ta kasa ganewa so take sai sun koma gidan su zata fara baza mulki son ran ta,tafi Ramai son ta gyara su su fito tsaf dan kuwa ta jima ta na yanka wa qawayen ta na makaranta qaryar iyayen ta masu azziqi ne, tinda gaba ɗaya yaran masu hannu da shuni take tare da su a makaranta a yanzu. Kayan da ta zo da su Ramai ke ta fitowa da su tana gani tana murna, kuɗi Jameelaah ta qirga dubu uku ta bata sannan ta sake qirga dubu uku tace na baban tane wannan, sannan ta aje ma Bukar dubu daya. Turaruka biyu ta bawa Ramai tace na Baban tane, Ramai dik amsa tayi tana ta godiya,a ranta kuwa ta na fad'in, 'Shashasha an faɗa maki kowa soko ne irin ki? taya ma zan bawa baban ku wannan turarukan masu tsada? ai saidawa zan yi na manne kud'in, tinda shi ko an bashi ba wani amfani yake da su ba, kullum ana fama da man babur da na keke yaushe yake da lokacin fesa turare irin wannan?' Waya ta tsinkayo Jameelah na yi da Umar, "Na'am Kana waje? Ka manta sai qarfe shida na yamma nace maka za a kai amarya?......k to gani nan zuwa," Jakar ta ta buɗe ta fesa turarukan ta masu qamshi, ta sake shafa hoda ta saka janbaki sannan ta jefa sweet mai qamshi a bakin ta ta yi saurin tattaunewa ta shanye, Jameelaah ta qara gogewa ta yi kyau sosai ta iya gayu na musamman saboda zama da yaran masu kuɗi,ta zama cikakkiyar budurwa 'yar sha takwas, jakar ta

Chapter 9 of 30