ba mai janye ni, ni naki ne har abada"
Sunne kai tayi dan taji kunya, fita yayi ya deb'i ruwan wanka yayi wanka, rabon dayayi wanka sau uku a jere a haka ya manta, tin kafin yayi auren fari.
(Matsalar shi kenan daga uwargida aka faro ta, itace bata tafi dashi yanda ya kamata ba har mai bi mata ta ɗora daga inda ta tarar)
Yana komawa d'akin ya shirya ya ce mata zai leqa kasuwa akwai abinda zai yi, rakashi tayi har bakin qofa tana d'aga masa hannu ya wuce ita kuma ta koma ciki,a tsakar gida ta tadda mero,
"Ohhhni Mero yau naji iyayi iya reto kad'a gado ba miji, ai na zaci tare zasu tafi kasuwar fa Abu,irin wannan kitifi haka?"
Murmushi Jameelaah kawai tayi ta wuce d'akin ta,a ranta ta na ayyana,
'Lallai ruwa ya daki tsohon zakara, in ba dan haka ba har kun faɗan rashin kunya ni?'
Farantai ta d'iba ta d'ebi kayan gara ta zuba dai-dai, ta kuma d'iban wasu a farantai bibbiyu suma ta zuba dai-dai, ta ɗauka ta fita sallama ta yi masu, idon su akan kayan garan Mero me habaici ji kake ta yi difff bakin nan ya mace murus, durgusawa tayi kaɗan ta gaida Abu, ba yabo ba fallasa ta amsa mata,
"Babar Hajjo ga wannan naki ne, wannan na yara su raba ba yawa ayi hakuri da shi,"
Amsa tayi tace
"To an gode, Allah yayi albarka,"
"Ameen"
"Babar Zara'u ga naki gana su Zara'u a basu na sune ba yawa,"
"An gode,"
Miqewa tayi ta koma d'aki yaran su da basu zuwa makaranta suka yo caaa a basu kason su, nan suka karkasa aka aje na sauran yaran da basu nan suka boye masu, sai aka bawa wanda suke gida kuma nasu kason.
Saida ta gama gyara d'akin ta sannan ta yi shirin wanka, wanke band'akin tayi tass sannan ta shiga wankan ta fito, ta shirya cikin wata shadda da tazo da ita daga gida ,ta ware wasu daga cikin kayan ta da zasuyi wa 'yan matan gidan ta aje a gefe sai sun dawo zata siye su da kyutatawa, ta haka zata siye manyan su kuma su taimaka mata da qannen su.
(Wa ya tuna gidan su Umaimah yanda yarinyar nan Jameelah ta dinga zuba mulki? Hummm ka ji tsoron Allah bawa ka zauna lafiya wallahi)
Tsakar gida taje ta saka kujerar ta ta zauna sai qamshi take zubawa, ga kuma uban kyaun da ta yi iyayen suna aiki suna kallon ta,
"Akwai aikin da zan taya ku da shi ne Babar Hajjo? Zaman shirun ba daɗi,"
"Kar ki ce baqar magana nake miki wato ina mamakin abubuwan da kika yi yanzu Jameelaah, saboda ni dai kin san na san ki na san kuma wacece Ramai, kuma na san dik ba haka kike ba a da, ko zaman zawarci ne ya koya maki hankali?"
Jameelaah bata ji daɗin tambayar nan ba amma ta san ita ta jawa kan ta, tinda ita ta b'ata kan ta tin farko,dan haka cikin bata tabbacin ta shiryu tace,
"Lallai a da ban zama daga cikin yaran kirki ba, amma kowa na samun dama ta biyu a rayuwar shi, ruwan mutun ne ya gyara Allah ya dafa masa,in kuma ya samu dama ta biyu ya sake jefa kan shi ga halaka,sai Allah ya barshi da iyawar shi da yake ganin ya iya,"
Shiru suka yi gaba dayan su nan ta miqa mata gyaran wake tace ta taya ta, tana cikin gyarawa ya Malam Tsalha ya shigo tare da wasu yaran a bayan shi, sai shigo da kayan abinci ake yi, dik da rabi-rabin buhu ne amma ba a taɓa yin hakan ba a gidan,abincin sun haɗa da dangin su ; shinkafa, masara, gero, wake, kwalin taliya, kayan su maggi da barkono da mai, sai sabulan wanka dana wanki da omo.
"Wannan fa daga ina Tsalha?"
"Naku ne kowa in ranar girkin ta ya zo sai ta d'iba a girka dan Allah banda almubazzaranci,
Ke Abu da Mero ku samen a dakin Abu ke kuma ki je ki karya, dan da ganin ki har yanzu baki ci komai ba,"
Cike da matsanancin mamaki matan ke bin shi da kallo, ledar da ta rage a hannun shi ya miqawa yaran yace,
"Ku raba harda 'yan makaranta,Allah yayi muku albarka, ya hore kuma a sanya ku a makaranta"
A tsorace suka amsa ya kai hannu zai shafa kan yaron Mero,yaro ya yi saurin kauda kai ya zaci mazge shi za ai, murmushi yayi ya san watarana zasu saba ne amma sai a hankali.
Jameelaah kuwa ta ji daɗi sosai da ya ɗauki gyaran da tayi masa da wuri, sai yanzu take ganin batai gaggawar neman gyara masa iyali ba kuwa, daga zuwa sai gyare-gyare kamar kafinta?
Dan ganin ya yi sanyi sai suka wani tsaitsaya a tsaye ba ladabi suna jiran suji me zaice, tinda suke bai taba tara su ba in ba sanadin rabon faɗa ba,
"Na kira ku ne saboda ina son na baku haƙuri akan irin zaman da muka yi a baya, ban taba kula ina saɓa maku ba, kuma ina saɓawa Allah ba sai yanzu da yarinyarnan ta nusar dani, bana kyauta maku na sani, ku min hakuri inshaa Allahu daga yau komai ya qare ya kuma wuce, zaman jahilci da muka yi a baya ba za a maimaita shi ba, ina fatan zaku bani had'in kai?"
Jikin su ne dik ya mace samun waje sukai suka zauna, suna jin kunyar abubuwan da sukai ta aikatawa.
"Ka yafe mana muma Baban Hajjo lallai zuwan yarinyar nan alkhairi ne a wajen mu baki ɗaya Allah ya yafe mana"
"Ameen sai ku gyara sosai, in ba haka ba ta kwace maku ni, dan dai kunga yanda take ɗaukan wanka da burushi ga kuma uwa uba qamshi,"
"Tabdijam ai mu mutu ka raba ne mu da kai takalmin kaza ba,ba wadda zata kwace mana kai"
Nan sukai ta raha da hirar da suka dad'e basu yi ba.
*********************
Bayan dogon bincike Sapnah ta gano ina ne gidan su Jameelaah, dan haka shiryawa tayi ta d'ebi 'yan kayan Humairah, ta qudurta ko Umar zai yi faɗa sai ta kai ta wajen mahaifiyar ta sun ga juna, itama taji daɗi a ran ta, ta san dik inda take tana kewar d'iyarta rashin ta a gare ta ya na damun ta...............
*Na rantse ba ruwana dik abinda Ummaru ya maki no my water insayiz tammm*
[09/09, 10:39 am] Aunty Hameeda: 💅🏼 *MAZAUNA GIDA* 💅🏼
*WRITTEN BY HAERMEEBRAERH*
Page 49:
Hankalin ta a tashe yake sosai dan bata san me zai je ya zo ba,amma ta riga ta qurdurta ma ran ta yau sai ta kai Humairah wajen Jamewelaah sai dai a yi wadda za a yi haba, koma meye ya faru da su a baya Jameelaah is her biological mother bai kamata ya datse alaqar dake tsakanin ta da 'yarta ba, a qalla ko da hutu ne ana kai ta musamman yanzu da yarinyar tai wayo take jin maganganu wajen yaran maqota da 'yan uwa tinda sunyi zama da mahaifiyar ta.
Tinawa tayi da tambayar da yarinyar ta yi mata a daren jiya bayan ta dawo daga maqotan su kai musu abinci, dan indai suka yi girki sukan kai masu musamman wanda ta san qamshin shi ya karade unguwa sai ta zuba komai kashin shi Humairah ta miqa wa moqota dan fidda haqqin maqotaka.
'Ammi wai dama ashe inada wata Maman Inji su Laure,?'
'Ohhh ni duniya, yanzu daga shigar ki miqa masu abincin nan har sun faɗa mki wannan maganar?
Tabbas kina da wata mamar itace ta haife ki kuma, amma ta koma gidan su itama, watarana zan kai ki ku ga juna inshaa Allahu,'
'Da izinin wa za a je ganin nata?"
Kama hannun shi tayi dan kar yayi b'arin baki a gaban yarinyar wanda har abada Humirah zata na ganin baqin shi, domin kuwa Uwa Uwace koda kuwa mahaukaciya ce.
'Me yasa zaki hana ni yin magana? Ai gwanda ta san wace irin uwa gare ta'
'Lallai kuwa daka zubar da qima da mutuncin ka gaban d'iyar ka har abada wai ni meke damun ka ne? Kai da mahaifiyar ta ku ka samu sab'ani fa ba da ita ba, ita bata san sanda kuka yi cikin ta kuka haife ta ba, da kun san zaku rabu har ya zamar mata tabo da baku haife ta ba, wannan shine sak abinda d'iyar ka zata iya faɗa maka in kanuna tsanar mahaifiyar ta a gaban ta, kar kace bazata iya ba,itama 'yar zamani ce, sannan kuma kai ɗin kai ne sanadin kawo ta duniyar da matar da ka tsana a yanzu, so ba ruwan ta da matsalar ku, wannan shawarata kenan in kaji ka ɗauka ta yi maka amfani a gaba,'
Umar shiru yayi, kamar ba zai ce komai ba,daga baya kuma ya ce,
'Ba za ta je wajen ta ba a yanzu har sai ta mallaki hankalin kan ta,taje da qafar ta a lokacin'
'Yarinyar da ta kai shekara goma ita ce bata mallaki hankalin kan ta ba?yara nawa kamar ta suke zuwa dik inda suka ga dama,ka diba ka gani yanda mutane ke faɗa mata labarai kala-kala na qarya da gaskiya akan mahaifiyar ta baka tunanin lokaci ya yi da za ka manta da baya ka fuskanci gaba? Shekarun fa da yawa ba jiya abun nan ya faru ba ba kuma shekaran jiya ba,amma a gaskiya Abbahn Humairah ka bani mamaki, ka ban mamaki, ashe kai baka yafiya?'
Rintse idon ta tayi a sanda ta tina yanda ta fita tana kuka daga d'akin amma ko bin ta bai yi ba dan ya lallashe ta ko ya bata hakuri,yau kuwa labarin da Humairah ta kai mata ance akan mahaifiyar ta shine dalilin da ya sa zata kaita dan ta tabbatar mata da kwanciyar hankali a ran ta, kuma ta gane me take faɗa mata akan mutane, in dai zaka bi ta maganar su ba zaka yi huld'a da kowa ba, saboda za a kushe mutum ne according to yanda aka tsane shi.
A qofar gidan su Jameelaah tayi parking ɗin kyakkyawar motar ta da Umar ya mallaka mata a ranar zagayowar shekarar haihuwar ta, dan kuwa yanzu likafa ta ci gaba ko gidan su ma da suke ciki Umar ya siye filin gefen shi ya qara faɗin shi ya sai mata mota ya kuma sayi wadda za a dinga kai Humairah makaranta da ita, arziqi sai shukran,Sapnah har yanzu bata samu rabo ba, sai b'ari da tayi sau biyu.
Buɗe qofar motar suka yi tare da ɗaukan kayan sawa na Humairah da suka deb'o,suka nufi gidan da ya sha fenti sakamakon bikin 'yan matan gidan da akai wata ɗaya daya wuce.
Jameelaah na kwashe abinci tana rabawa yaran na miqawa kowa nashi, Abu da Mero na zaune a tabarma babba suna jiran ta gama su ci nasu, kowaccen su ta sha gayun ta dai-dai iyawa da kuma wadatar ta, gaba ɗaya sun zama 'yan gayu sun sauya rayuwar da suke yi a baya mara kyau mai qazanta.
Sallamar su Humairah ne ya sa Jameelaah d'agawa da sauri dan kuwa har abada bazata manta da wannan muryar ba miqewa tayi tsaye sannan ta ambaci sunan ta cikin mamaki,
"Sapnah?"
"Na'am, Jameelaah,"
Maida kallon ta tayi gefen Sapnah ta ga 'yar matashiyar yarinyar da take kyautata zaton Humairahn ta ce,dan kuwa ko a ina ne zata iya gane fuskar gudan jinin ta dik da jimawar da suka yi basu haɗu ba, a ganin Jameelah girma kawai tayi amma kamannin ta na nan tun na yarinta, idanun ta ne suka tara kwalla mai mugun zafi, Sapnah ce ta tura Humairah gaban Jameelah da niyyar taje wajen Jameelaahn, amma sai ta koma bayan Sapnah sannan ta kama hanyar fita tace,
"Ammi muje kawai na gan ta na fasa yin hutun anan,dama dan saboda gaba kar mu haɗu a hanya na kasa gane wacece ta haife ni ko kuma har ɗayan mu ya mutu bai ga ɗaya ba shi yasa na matsu a kawo ni na gan ta"
Da sauri Jameelaah ta tsallake kwanukan dake a gaban ta ta bi Humairah da gudu ta baya ta jata jikin ta ta rungumeta tana kuka sosai, Humairah ma kukan take yi amma taqi yarda ta juya su haɗa ido da mahaifiyar tata da ta nuna halin ko in kula da rayuwar ta,ba dan Allah ya haɗa ta da matar uba mai kirki kamar Sapnah ba da shikenan haka zata watsar da rayuwar ta kamar ba ita ta haife ta ba? Kome ya faru tsakanin ta da mahaifin ta be kamata ta ɗauke qafa a cikin rayuwar ta ba, tana jin son Mahaifiyar ta amma tana jin haushin barin ta da tayi ko sau ɗaya bata taba neman ta ba bata waiwayi rayuwar ta ta ji shin tana lafiya? Ana kyautata mata ko kuma tana zaman qunci a hannun matar uba? Cikin kuka da sarqewar murya Jameeelah ke magana,
"Ki yi hakuri ki juyo ki kalli mahaifiyar ki Humairah, na san ban kyauta ba, shekaru masu yawa sun gushe amma na kasa fuskantar ki balle mahaifin ki, ina da babban tabo a zuciya ta, da jiki na, ina jin kunyar fuskantar mahaifin ki na ce ya bani ke ko da sau ɗaya ne mu kasance a tare, sannan naji labarin yanda Sapnah ke kula dake kamar ita ta haife ki, na san baki da maraicin Uwa, beside ko ina nan bana jin ina da cikakkiyar tarbiyyr da zan baki kamar wannan da Sapnah ke baki, na sani na yi ilimin addini mai tarin yawa amma ban tsaya na yi amfani da shi ba ta hanyar da ya dace, dan Allah Humairah ki yafe wa wannan gafalalliya kuma mai tarin zunubin mahaifiyar taki,"
Da sauri Humairah ta qanqame ta tana kuka,Sapnah kuwa sai lallashin su take yi dan itama sun sanya ta kukan.
"Humairah is time to go home indai har ba zaki zauna anan ɗin ba, coz ur dad is on his way back home yanzu bana son ya san mun fita bai sani ba,sanda kika shirya zama anan ɗin watarana sai mu dawo,"
Da sauri Jameelaah ta kalle Sapnah after all this years bai yafe mata ba dama? Lallai tana da aiki a gaban ta, ko shi yasa har yanzu bata samu rabon aure ba? Allah ya jarabce ta da tsananin son haihuwa, amma bai ba ta ba, dama a kullum tana zargin kan ta akan abubuwan da ta aikata a baya.
Share hawayen ta yi sannan ta shiga d'akin ta ta deb'o wa Humairah dik wani abu data ke da shi wanda ta san yarinya kamar ta zata buqata ta miqa masu, zuciyar ta ta dake sosai.
"Ga wannan maza ku koma gida, Sapnah kar ki qara fita bada izinin mijin ki ba rayuwata babban darasi ne ga kowacce mace, inshaa Allahu da kaina zan zo na bashi haƙuri, har sai ya yafe min zan daina zuwa, kin san dai illar fita ba da izinin miji ba, ko ni na ishe ki ishara, mu mata MAZAUNA GIDA ne ba masu yawo ba izinin miji bane"
Humairah na kuka haka ma Sapnah a haka ta sa yarinyar a mota suka wuce, Jameelaah na soro sai da ta ga wucewar su ta juya a guje zuwa d'akin ta tana kuka, d'akin ta ta shige ta faɗa gado tana ta zubar da hawayen tausayawa kan su.
Abu da Mero sun tausaya mata sosai, yaran ma kowa sai ya koma wani sukuku saboda ganin Jameelaah a cikin damuwa, Jameelaah ta taimaki darayuwar su, miji ya zama abin so agare su yanzu, mijin su na da lokacin su dana yaran su, ga shi yanzu har shagon kekuna gare shi arziqi ya bunqasa sai godiyar Allah, abinci ya wadatu, tsafta ta wadatu a gidan, ga uwa uba tarbiyya, dan ta tsaya tsayin daka dan ganin yaran sun kaucewa rayuwa irin wadda tayi a baya, soyayyar da yaran suke yi mata wata ran har kishi iyayen su suke yi.
Sun sani zai yi wahala kuma ta sake fita cin abincin, dan haka suka dakko mazubin Tsalha suka zuba mata nata, sannan Abu ta shiga d'akin nata ta ajiye mata sannan ta zauna a gefen gadon Jameelahn ta dafa bayan ta cike da tausayawa ta ce,
"Auntyn yara dan Allah ki daina kuka haka, komai yayi farko zai yi qarshe,duniya dama ta gaji haka, komai kayi a rayuwa kamar jifa ne, in yayi sama dik nisan dad'ewar da yayi a saman zai fad'o qasa, ko ya fad'o maka dai-dai yanda ka jefa, ko ya fad'o maka a tarwatse, ki godewa Allah a kan ni'imomin daya yi maki, dik da irin mugunyar rayuwar da ki kai a baya amma bai bari kin wulaqanta ba, muma ga shi kin taimaka mana da tarbiyyar yaran mu, tinda ke kika san maganin irin halin da matasan yanzu suke fuskan ta,wanda ba dan zuwan ki ba da yaran mu sun lalace, Allah ya taimake mu yanzu ga shi yara bakwai muka kai d'akin miji lafiya, ga mahaifin su yanzu yanda ya sauya dik ke za a godewa akan hakan, ko dan haka bai kamata ki sanya kan ki cikin qunci da damuwa ba, dan Allah ki warware ki fito, mu sha iskar duniya mu warwasa abun mu yanda muka saba,in ma bazaki ci abincin ba yanzu zuwa anjima kunci ke da Baban Hajjo kuna ci kuna soyayya abun ku,"
Cike da jin kunya ta rufe idon ta sannan ta yi murmushi ta share hawayen ta tace,
"Ni ba zan ci da shi ba da ku zan ci,"
"Gulmamma nan nan ba tare kuke ci ana kaiwa juna a baki ba, ana kalaman qauna, ai ina sane da yanda kike susuta mana ɗan tsohon mijin mu, amma karki damu, muma dik mun koya yanzu duk abinda muka ga kina yi mai kyau yana yabawa muma yi muke koda bai yaba mana kamar yanda yake maki ba a qalla yana nuna mana jin daɗin sa,"
Dariya sosai Jameelaah take tintsirawa cike kuma da jin nauyin Abu, ashe komai suke yi akan idon su ake yin shi.
Abu taji dadin yanda Jameelaah ta saki ranta,dan haka tare suka ci abincin su, suna ci gaba da tsokanar ta, tana ta faɗin dan Allah su bari, yara na ji fa.
Koda Tsalha ya dawo sai da yayi wanka ya ci abinci, sannan suna hutawar su ta faɗa masa komai da ya faru da rana, ya ji tausayin ta sosai sannan daga baya ya lallashe ta yayi mata alqawarin har da shi za a je a bawa Umar hakuri, kuskure ba wanda ya wuce ya aikata shi ai, Allah na san bayin shi masu neman tuba da masu yafiya idan an nemi tuban su.
Im fada maku gaskiya dana ga tsalhan ku ban gane hyi ba fa, Tsalha har wani ja ja ja ja yake yi, gemun nan ya tsaya carrr, kumatun ya bayyana, daga lob'awar da yayi, jikin shi kamar ba nashi ba, ya koma mijin yarinya, shima ya zama saurayi abun shi yana ta dangwalar romon dimokuraɗiyyar soyayya abinshi.
*********************
Bayan Ummee wato Umaimah ta haifi Ibraheem Khaleel ❤️sai Shukrah wadda take shayarwa a yanzu,Aunty Hauwaa kuma bayan Muhammad ta sake haifiar Saifullah.
Sadeeq da amaryar shi wadda yake ji da ita a yanzu kamar k'wai, suna da d'iya mai suna Fateemaah wato (Mamalo) dan shi da Mamalo ma ya ke kiran ta, Matar shi ta san ko me zatai da wahala ya so ta kamar Mamalo, dan haka take kyautata ma Fateen nasu, yana jin daɗin hakan kuwa sosai.
************************
"Washhh Allah na gaji Mama akwai dan abin kaiwa bakin salati kuwa? Yunwa nake ji kamar naci babu, na so na leqa shago na karb'i dambun nama kanna tafi amma da yake ina sauri sai na manta,"
"Da dikkan alama yau ma ba ai nasara ba kenan ko Bukar?"
"Kamar kullum kuwa Mama, har yanzu ban samu aikin ba, na rasa meke damun qasata Nijeria, wai a ce ka gama karatu, da k'yar da sid'in goshi, sannan aikin ma da k'yar da sid'in goshi za ka samu ba wani tanadi da gwamnati ta yi wa matasa dan ganin sun samu aikin yi da zarar sun kammala karatun su da kyakkyawan sakamako,yanzu ki duba fa Mama mu da muka kashe lokacin mu, jikin mu, da dik wani arziqin mu bama samun aikin, sai waɗan da zasu jera sati basu je lecture bama, ko jarabawar gama sakandiren ma siyan ta suka yi, sune suna zauna a AC za a kai masu takardar aiki har gida, aikin ma haka za suna zuwan shi sanda suka ga dama, in ba su ga dama ba suyi wa mutum aiki ba dai-dai ba, kayi magana su zage ka, kaiii subhanallahi, talaka na cikin izayar rayuwa Mama, gwanda ma ni ai ban cika shekara ina neman aikin ba, ga wasu abokai na da suka rigani fara makaranta suka rigani gamawa su fa mama akwai masu shekara biyu uku a cikin su ba aiki, in ka nemi sana'a a dinga yi maka kallon jahili bayan da kwalin ka mai kyau na degree, in ka zauna ba aiki k'wandala ta gagare ka, in kai sata a garqame ka, ya ilahi ina talaka zai sa ranshi ne ?"
"Oohhh an tab'o me baki yau, yau da gwamnati taji wannan sharhi da sun baka aiki Bukar kowa ya huta,"
Dariya yayi, sannan ya ja kwanon data kai masa abinci ya fara ci yana ci gaba da surutai,
"Ni kin san ma me nake tunani Mama? Aikin nan aje neman shi zan yi, na kama sana'ar nan tamu na bunqasa ta, ko ina ana kai dambun nan ana siyarwa ta haka ne masu sari da siyan ɗaya za su qaru, in da rabon na samu aiki shikenan, in babu ban dai zauna da jahilci ba ko? To godiya ta tabbata ga Allah"
"Baki abun magana kenan Bukariri Allah to ya sanya albarka, mahaifin ka da Malam Tsalha kaga suma Allah ya bud'a yanzu shagunan keke gare su,mahakurci mawadaci aka ce, sana'a maganin rashin aikin office"
Kamar yanda ya tsara haka ya gabatar, Bukar na sa hannu a sana'ar dambun nama Allah yasake sanyawa abun nasu albarka da nasibi, yanzu da wahala kaje unguwa a kano baka ji ana da shago ko wajen da ake bada sarin dambun naman su ba, in an samu riba sai su kasa ta uku, Jameelaah na da kashi ɗaya su kuma kashi biyu, da ita suke baiwa Kashi biyun ta ce su yafi cancanta da su riqe kashi biyu ba ita ba.
**********************
Umar ne zaune a farfajiyar gidan shi riqe da jarida kasancewar yau weekend ne ba aiki, Sapnah na zaune a gefen shi tana b'are masu lemo shi da Humairah itama tana sha.
"Wajen nan qwari sun yi yawa Ammi duk sai cizona suke yi,"
Cike da shagwab'a take yin maganar, kallon ta Sapnah tayi sannan tace,
"Ki shiga ciki mana kin damen da surutu tin ɗazu, kin saka ɗan qaramin wando da yar riga to tsoron ki suke ji da bazasu cije ki ba? Yanzu ga jarabawar JSSCE din ku ta gabato, ya kamata ki maida hankali wajen yin karatu ba wasa ba, in kin ga ina zaune ba abinda nake yi kema ki bi waje ki zauna,ni ɗin nan na sha gaya maki da kwali na na digiri digirgir yarinya,aiki ne dai naqi yi, saboda ina son zama na kula da iyali na,"
Humairah tashi tayi ta rungume Sapnah, tare da manna mata kiss a kuncin ta sannan ta shige ciki tana faɗin,
"Na wuce ciki ni dai tinda dai kin kore ni, karatu kuwa zan baki mamaki Ammi zaki yi alfahari dani watarana,"
"Haka nake so ai dama na sha mamakin sannan ko a yanzu ina alfahari dake Allah ya yi maki albarka,"
"Ameeen Ammin Humairah,kema Allah ya yi maki albarka"
Umar ne ke ta murmushi baya gajiya da jin hirar Sapnah da Humairah, a can qasan ran shi kuma yana jin haushin Jameelaah da taurin kai ya hana ta zuwa ta nemi qafarar shi ta roqe shi ya bata Humairah dan itama ta saba da ita haka, shi kuwa yayi alqawarin in ba ita ta zo ta nemi a bata Humairah ba ba zai taɓa kaita wajen ta ba da kan shi.
"Tinanin me kake yi haka Zauj?"
Ya buɗe baki zai yi magana kenan, aka buɗe qaramar qofar gate ɗin gidan nasu aka ziro qafa, qurawa qafar ido Umar da Sapnah suka yi dan ganin wanene zai shigo, ko a ina Umar yaga wannan qafar tabbas zai gane qafar da ya sha yi wa tausa da hannayen shi ce, qafar da ya sha shafa mata mai da hannayen shi ce qafar da...................
*Casssssss anayi ina jin nice, ana bari
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 30