Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hayaqin dafa wake da shinkafa ba wani gani take sosai ba, k'wafa ta yi ta ce, 'Zaki ci uban ki ne, ba dai ni ke kawo maganin ba, har aban abu ki wafce? Naga shegen da zai dinga maki wahala kina samu kina ci ke ɗaya,' Jameelaa ce ta shigo ranta b'ace dan ma kar Ramai tai maganar abinda ya faru ɗazu, aiko batai maganar ba abinci suka ci sukai nak, sannan Jameelaa ta shiga kitchen dan debarwa Ramai kayan abinci, sai da ta loda mata sosai sannan ta kira ta dan ta ɗauka, ita kam tace ba zata iya d'ibar kaya ba a gajiye ta ke. Ramai kuwa haka ta shiga dan tsabar kwad'ayi ta kwashe komai da aka d'iba domin ta, ta tsare mai napep ta shige sai gida. Jameelaa bacci ta kwanta tayi, sai da ta farka ta yi sallah gaba daya wato ta haɗe Azahar da la'asar dika sannan ta yi wanka ta shiga maqotan ta ta samu garwashin wuta ta turare gidan da mix din turaren wuta da maganin mallaka da aka kawo mata,ba a jima ba kuwa Umar ya dawo. Da ganin shi ka san a gajiye yake wanka ya shiga yayi sannan ya fito, kan shi yake ji yana juya masa, dan haka ya zauna ya dafe kan nashi, nauyi ya masa kamar an d6ora masa abu mai nauyi, tasbihi yake tayi ga Allah, yana istigifari, tare da hailala da hauqala, nan take ya ji ya fara jin sauqin jirin da yake gani. Zama tayi kusa da shi tana ta nazarin yanayin shi. "Yaushe ka dawo? Naga ma har kayi wanka," "Ban wani jima ba da dawowa ba na shigo na ji ki shiru,kawai sai na shiga na watsa ruwa na ɗan zauna na huta," Shagwab'a ta fara yi tare da d'alewa cinyar shi, ta zagaye hannayen ta a wuyan sa sannan ta manna qirjin ta dake rud'ar da shi a fuskar shi tare da kukan shagwaba, "My love menene shin me ki ke so?" "Ni gaskiya yau bana son ayi girkin dare a gidan nan,sha'awar naman rago nake irin gasasshen nan da ka ke siyo min da freshyo sai fruits," "To bari kuka dan dai wannan kawai? tashi ki sa kaya muje a siyo," Tsalle tayi ta qara faɗa masa gaba ɗaya a jikin shi kyakkyawar runguma ta samu a wajen shi, sai da suka dan taba soyayyar su sannan taje ta saka kaya suka fice, yawo ta sa yayi tayi da su tana shaqar iska, magrib ta wuce amma bata ji su koma gida ba daga nan su yi can, sai da ta sa Umar kashe kuɗi sosai,har yana tinanin anya za a samu kud'in su kai shi qarshen wata kafin wani albashin ma kuwa? Bayan magrib liss suka koma gida, bata b'ata lokaci ba wajen baje kayan a nan parlour, ta fara cin na ci,tana ware na iyayen ta, da nasu da alwala ya zo ya tsaya a gaban ta yana tambayar tayi alwala ne ta kalle shi tare da harara "Yanzu fa muka dawo, habaa ai ka bari ma na dan ci na qoshi tinda ka san yunwa nake ji," "Nayi sallah ta kenan tinda ba zaki zo muyi jam'i ki samu ladan bin liman nima na samu ba," "Yi taka sallar ni na haɗa da isha'i" Kad'a kai yayi ya je ya tada sallar shi, cikin sujjadar qarshe yake roqon Allah daya sa jameelaa kar ta sauya daga kyakkyawa zuwa mummuna,dan ya fara ganin wasu halayen da sam bai taba sanin tana da su ba. Da weekend ya so yaje ya gaida Mum amma sai yaji gaba ɗaya baya son shiga gidan nasu, ba wai iyayen nashi ne bai son gani ba ah ah gidan nasu ne kawai yake jin qiwar zuwa. Suna zaune suna shan soyayyar su, dan Jameelaa ba abinda ta fi so irin ya zauna yana wasa da ita, tare da yi mata irin soyayyar da ta saba da ita tin asali. Wayar shi ke ta ringing, amma bai gani ba saboda ta sa masa wayar a silent, tana ganin wayar na haske taqi yi masa magana, cikin dabara ta haye cinyoyin shi ta kwanta a jikin shi ta leqa wayar, sunan Mum ta gani a jiki,  hannu ta sa zata sake tura wayar qasan kujera suka hada ido da shi, sai ta wayance ta d'akko ta miqa masa. Karawa yayi a kunne bayan ya amsa, sallamar Mum ya amsa tare da gaida ita. "Ok Mum inshaa Allah zan zo anjima, ko yanzu zasu zo?........ok to ga ni nan zuwa" Kashe wayar yayi, da hanzari ya miqe yana murna, "Kin san me? Maneman auren Umaimahn ki ce zasu zo, shine Mum ke kirana ya kamata naje ayi komai dani," Dan yatsina fuska tayi, sannan tace, "Kuma zuwa za ka yi ɗin?" Dan haɗe fuska yayi ya kalle ta da alamar ban gane ba? Wayancewa tayi ta fara kame-kame sannan tace, "Nima gaskiya sai kaje da ni, dan kuwa ba za a yi maganar auren qawata kuma qanwata ba bana nan," D'aga ta ya  yi sannan ya saki fuska ya ce, "Muje maza mu shirya ana jiran mu," A tare sukai wanka suka shirya, cikin jallabiyya kalar blue wadda ta sha aiki ya saka wandon rigar, turaruka masu qamshi ya sanya, itama doguwar riga ce a jikin ta, dark blue, mai ratsin pink a jiki, ta yafa mayafin rigar tare da sanya takalmi mai tsini kalar pink da jakar shi suka fita zuwa gidan su Umar.   Koda suka isa an gama komai sun tadda kayan saka rana da Daddy da Mum tare da Umaimahn suna ta hirar bikin Umaimah, shigar su ce ta sa suka maida hankali kan su, Mum cike da jin nauyin su ta gyara zama. Dad ne ya fara yi masu barka da zuwa, Umaimah ta tafi da sauri ta rungume Jameelaah ta ce, "Gaskiya nayi kewar ki sosai,  da alama ke kam hankalin ki kwance yake, ji har wata qiba ki kai sati biyu kawai da tafiya," Wank irin haushin Umaimah ne ya kama Jameelah cikin ranta take fad'in, 'Ji dalla yanda ta wani cukuikuye ni kamar ta samu flour tana curawa,mtsssww' Yaqe ta yi mata suka samu waje suka zauna, suna gaida iyayen nasu. Bayan gaishe gaishe ne Daddy ya yi masu bayanin sanya ranar auren Umaimah da aka yi watanni biyar masu zuwa da Haroon,Jameelah ce ta ce, "Dama na san malamin nan na son ta, itama kuma tana son shi, amma dana tambayi yarinyar nan sai ta musa min," Rufe fuska Umaimah tayi ta tafi d'akin ta tana dariya, Jameelaa na nan a zaune taqi tashi, sab'anin da da take nuna jin kunyar Iyayen mijin bata son zama da su su dad'e a waje ɗaya,yanzu kuwa idon ta fess akan su, Allah Allah take ya tashi su wuce ta gaji da zama a gidan. Sun kula da sauyawar ta ta amma basu ɗauke ta ta wata mummunan hanya ba, a zaton su shaquwa ce ta ke tasiri a tsakanin ma'auratan. Message ta masa akan su wuce ta gaji kuma kanta na ciwo, sai ya mayar mata da ta ɗan jira kaɗan sai su tafi, aiko nan da nan ta b'ata rai, Umaimah na can d'akin ta tana jiran Jameelah ta je su ɗan yi hirar yaushe gamo amma ba ita ba alamar ta,shirun da taji yayi yawa ne ya sa ta leqa ta ce mata, "Qawata muje ciki mana ki sha labari, naji ance anyi bikin mamalo ko?" Wani kallo tai ma Umaimahn sheqeqe,sannan ta ce mata, "Lallai Umaimah baki da kunya, ni kike ce wa qawar ki? Ko kin manta ni matar Yah Umar ce yanzu? Dole yanzu suna na ya sauya a bakin ki, sannan ni kaina ma ciwo yake yi so nake mu tafi gida," Kowa a wajen har Umar kallon ta yake cike da mamaki, me ya same ta ne haka? Jameelaa mai kunya da hankali tare da sanin ya kamata ita ke magana kamar wata babbar mata mara tarbiyya, Umar ne zai yi magana, Mum ta kula da bacin ran shi, nan da nan ta tari numfashin shi ta ce, "Subhanallahi ! ciwon kai kuma Jameelah? Ya kamata kam ki sha magani ki kwanta ki huta, Umar tashi maza ka kaita gida, ka kula da matar ka sosai," Bai musa ba kuwa ya amsa mata da toh, kafin ya miqe Jameelaa ta tashi ta saɓa jaka a kafad'a ta kai qofa? Ba magana ba komai balle ta yi wa surukan nata sallama. Har suka isa gida ba wanda yayi magana, suna shiga ta fara cire kayan ta a parlour Umar yayi yayi dan ya ɗauke kai akan abinda take yi da gayya dan jan ra'ayinsa amma ya kasa jin idon shi yake yi kamar an manna a jikin ta, sai da ta gama cire komai tsaf na jikin ta sannan ta d'ebi kayan a hannu ta shige d'aki, kamar raqumi da akala haka ya bi bayan ta har ciki, bata ce masa ci kan ka ba ta sake fita dan shiga d'akin shi tayi wanka, dan nan ne kaɗai ke da band'aki a cikin d'akunan dika,manna ta yayi da jikin qofar bayan ya mayar ya rufe qofar, na so na ga me zai mata dan tana buqatar a zane ta ta dawo hayyacin ta haka na fita ina ta murna dan kuwa abinda tai ta cancanci a hukunta ta. Na kai awa ɗaya a waje ina jiran na ji kukan Jameelaah abun mamaki sai kawai na ga sun fito riqe da junan su suna ta sheqa dariya, ta na dukan shi cikin sigar wasa cizon yatsa na na yi na bar gidan gaba ɗaya ba zan iya kallon abin duka ba sanda ba. ********************** Haroon kuwa hankalin shi ya kwanta da aka bashi Umaimah, dan haka yanzu ya maida hankali kan karatun shi da kuma kasuwancin shi, sai chatting da waya da Umaimah da yake yi a koda yaushe dan sake kafa gwamnatin sa a wajen ta, kusan kullum suna tare da junan su a waya, hirar su rabi bata wuce akan qara mata junan su ilimin addini, rabi kuma ta soyayya. Yah Ishaaq ne ya dawo daga kasuwa tare da Haroon, suna cin abincin dare Ishaaq ke sanar da su za shi india dan saro wasu kayan. Hauwaa ce ta kalle shi cikin ɗauki tace, "Dan Allah kaje dani, ina son india sosai," "Kin dai san me kike tare da shi a yanzu ko? Kina ɗauke da ciki na wata ɗaya zan ɗauke ki tafiya wata qasa? Ba inda zaki je gaskiya," Haroon bai ce komai ba yana ta kallon su, tayi magiyar tayi roqon amma shiru ya qi yarda daga qarshe tana hawaye ta bar wajen. "Yah dan Allah ina son na maka wata magana a matsayina na qanin ka amma ina tsoro da tinanin ya zaka d'auki magana ta,dan Allah ka fahimci abinda zan sanar da kai, kar ka min mummunar fahimta, sannan ka gyara abinda zan maka magana akai, ba tare da ka bi diddigin ya akai na sani ba," "Haroon wannan bayani naka ya sa naji mutuwar jiki,me nake aikatawa mara kyau haka?" "Yah a gaskiyar magana ina son shawartar ka ne dama akan matar ka, mace na da matuqar rauni, mace tana da son a tattala ta, tana son ta zama dik inda take mijin ta na nan, yana bata soyayya da kulawa tare da girmamawa, Yah na san zaka ce me Hauwaa ta rasa? Komai tana ci ta sha ta sanya tayi ma wani ma, amma a gaskiyar magana ta rasa soyayyar ka, ba ina nufin baka son ta ba, a iya sani na bayan ni Hauwaa ce mafi soyuwa a gare ka, amma baka bata soyayyar da ke ɗauke cikin ran ka, in zan iya faɗan wannan kalmar ba tare da kaji haushi ba ina nufin u ar not romantic, gaba daya baka nuna mata kai ɗin dan soyayya ne, ba irin gifts ɗin nan na masoya tsakanin ka da ita, ba wata soyayya, kuma kwanaki na ji tana magana a waya akan baka biya mata buqata sosai, i am sorry to say amma kaga wannan babbar matsala ce da zata iya jefa ta neman wasu mazan musamman tinda baka nan, kuma baka tafiye-tafiye da ita,kuma Hauwaa mace ce da take very sensitive, abu kadan yana tasiri a ran ta me kyau ko mara kyau," Shiru Ishaq yayi cike da jin kunya yau wai qanin shi ke nuna masa me ya kamata yayi, "Me kake ganin ya dace nayi mata yanzu Haroon?" "Naji daɗi da ka fahimce ni, ina roqon Allah daya baka ikon sake siyan soyayyar ta da yarda ta a karo na biyu a rayuwar auren ku, shawara ta na farko shine ka je da ita wannan tafiyar, amma kai suprising ɗin ta, in yaso sanda zaka faɗa mata sai kace ka ce bazaka da ita bane yau dan kar ta rusa maka plan ne dama, ka dai lallashe ta in yaso in kun je su ta can ba ruwan su suna saida magungunan maza da na matan ma dika sai ka siya abun ka, sannan ka daure ka ɗan dinga ɗan wasanni da ita da zuwa wajen shaqatawa haka," "Lallai ba banza ba kake so a yi maka aure yaro ba abinda baka sani ba, na gode to na gode sosai, Allah ya yi maka albarka, gaskiya naji daɗin shawarwarin ka a gareni,ina godiya sosai qanina, ina godiyar yanda ka zauna ka bani shawara sosai wanda ba kowa ne zai iya ban shawarar yanda zan zauna da iyalina lafiya irin haka ba," "Yah ai kaima abin a gode maka ne ba dika mutane ke son a nuna masu gazawar su ba musamman ta ɓangaren rashin qarfi a wajen mu'amalar auratayya,sai ka ga namiji har na miji amma a d'aki babu fus, mata suyi ta haƙuri da shi, yana gani kamar shi ya gama yi masu komai dan ya mallaka masu dukiya," Haka dai sukai ta tattaunawa a kan matsalar ma'aurata Haroon na ci gaba da wayar ma da yayan shi kai a harkar aure a musulunci. ********************* A qofar gidan Mamalo umar ya aje Jameelaa, glass din idon ta ta cire tana kallon gidan cike da d'agun kai................... [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻  MAZAUNA GIDA   💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 18: Babu inda Hauwaa bata duba ba  a gidan amma bata ga Haroon ba,babu ma alamar yana cikin gidan,cike da takaici ta koma parlour ta zauna, wayar ta ta kunna ta nemo No Haroon ɗin ta hau kira, tayi ringing yafi a qirga amma bai d'aga ba. Har ta cire ran zai ɗauka ta ji sallamar shi,cikin muryar bacci, "Ina kaje?" "Ke meye naki na nema na a wannan lokacin?" "Ina son sanin inda kake ne, saboda yayan ka ya kirani ya ce na kula da kai," "Jariri ne ni? Ai ba jariri bane ni da za a ce ki kula da ni, ke in ba dan tsaurin ido ba da kuma kina auren yayana har kin kai wadda zata kula dani? Ke koda kin girmen ma, ni namiji ne da ace kina da halin kirki ni zan kula da ke amma ba ke za ki kula da ni ba, zan kashe wayata kar ki sake kirana dan ban ga abinda zan yi maki ba," Kuka ta saka mai ban tausayi sannan ta ce, "Dan Allah kar ka kashe tsaya kaji, dan Allah ni dai ko dan wasa ne ka dawo muyi, yayan ka kwata-kwata bai iya komai ba, bana samun abinda nake nema a wajen shi, da na san yana da qani kamar ka da ba zan taɓa auren shi ba kai zan aura,.....hello....hello...Haroon?" Shirun da ta ji ne ya tabbatar mata da cewa Haroon ya kashe wayar shi, kuka ta sa mai qarfi tana dukan kan ta da hannun ta, gaskiya ba zata iya zama gida ɗaya da Haroon ba, ko a sauya masa wajen zama, ko ita Ishaaq ya sake ta habaa, ga namiji tana gani amma bai iya tab'uka komai ba ya dinga abu sai kace ba namiji ba, Haroon yafi Ishaaq cikar mazantaka a ido ma. 'Zuciya ta baki yi min adalci ba, yaushe ma kika kamu da sha'awar qanin mijin ki haka? Ko miji na ban taba sha'awa kamar yanda nake ma Haroon ba,ina buqatar taimako indai ina son cimma buri na' Tinani ta yi tayi har bacci ya kwashe ta a wajen. Da safe wajen qarfe tara na safe Haroon ya shiga gidan, ta gyara ko ina kamar yanda ta saba, ta sha kwalliya da qananan kaya matsattsu, wandon iya cinyoyin ta sai qaramar vest mai bayyana baya da qirji, bra din data saka ita ce ta rufe mata qirjin sosai, tare da dago su,tin da ya kalle ta mistakenly bai sake kallon inda take ba, wani kallo ta kafe shi da shi kamar itace miji shine macen tace, "Ga abincin ka nan sanyin idaniya ta" "Really? Wai ke Hauwaa baki da hankali ne?" "Hauwaa? Ina ka baro aunty Hauwaan?" "Mata da dama suke samar wa kan su mutunci, sannan da daman mata suke saida wa kan su mutunci, ke baki da mutuncin da zan kira ki da girmamawa, matsa in ba haka ba dik abinda na maki ke kika jawo, dan kuwa zan maki dukan da Yah ba zai iya gane ki ba" Abincin da ya kai hannu zai ɗauka ta dauke, sam ita bata yi fushi da kalaman shi ba, ta ɗauka da niyyar ya bita daga nan suyi ta zagaye wajen dan ya k'wata, shaidan kuwa daga nan ba abinda ba zai iya kimsa masu ba baki ɗayan su, sai Haroon ya bata mamaki kamar koda yaushe. Tsaki ya ja mai qarfi ya shiga d'akin shi ya barta riqe da abincin ta a hannu, kayan shi ya d'iba masu ɗan yawa ya saka dik wani abu da zai buqata a jakar ya fita, a bakin qofar d'akin shi suka yi karo da Hauwaa, yi ta yi kamar zata faɗi, a zaton ta ya taro ta amma ko kula ta Haroon bai yi ba, aiko sai ji ya yi ta faɗa jikin shi, zuciya ta kai masa ko ina saboda haushi ji yake yi kamar ya zage damtse ya naɗa mata na jaki, amma ya hakura yawurga ta gefe ya fice daga gidan, Hauwaa kuka ta saka mai cin rai, a ranta ta na ayyana, 'Na zaci hakan da na yi zai taimaka min amma inaa, sai ma nesanta ni da yayi da shi, ina zashi oho? Gaskiya ba zan iya rayuwar quncinnan ba, dole ne Ishaaq yayi abu ɗaya acikin biyu, ko ya nemi maganin da zai zama cikakken namiji kuma ya iya soyayya da faranta min rai, ko kuma ya sakeni,gaskiya ba zan iya zama da shi a haka ba,' Sosai take kuka kamar wadda akai ma mutuwa, bata san iya lokacin da ta dauka ba a wajen,   da kyar ta tashi ta shiga d'aki ta kwanta tana jin wani zazzaɓi na shigar ta. Kwanan Ishaaq uku kamar yanda ya faɗa wa Haroon zai yi ya dawo ya dawo kuwa, Hauwaa shadda ce a jikin ta ta sha aiki daga sama har qasa kalar purple, an mata aiki da baqin zare da golden,ta kafe dauri mai ban sha'awa, abinci ta dafa kala-kala masu daɗi da kyau a idanun mai kallo, ta san dolen Haroon ya dawo gidan a yau. Shigo wa yayi cikin qananan kaya wandon nan a d'age kamar ko da yaushe ga gemun nan ya sha taja sai kyalli yake yi, baqin shi mai kyau na ta haskawa da annuri, sallama yayi ya zauna a cikin ɗaya daga kujerun parlourn, Ishaaq ya kalle shi cikin kulawa yace, "An ce min baka kwana a gida ko zan iya sanin dalili?" "Barka da safiya Yayah, ai ka bari a gaisa ko?: "Barka dai," "Ya kasuwa? Ina fatan ka gama komai lafiya? Yaushe kayan za su iso?" Nan da nan hirar kasuwa ta kan kama a tsakanin su, suna cin abinci suna hirar irin riba da kuma ci gaban da kasuwar tasu ke samu,Hauwaa takaici dik ya ishe ta ita taso a yi magana akan Haroon da inda yake tafiya ya kwan yanzu, amma sun tsaya suna wani zancen kasuwancin banza,da qarfi ta aje spoon din ta akan dinning din ta shige d'aki fuuuuu. Kallo suka bita da shi Ishaaq a tinanin shi ko dan ya share ta ne ya maida hankali akan qanin nashi. Haroon ne ya ke tinani a ran shi. 'Ta ya zan yi wa Yah magana akan rayuwar auren su? Bana son zargin wani abu ya shiga tsakanin su ya gano me matar shi ke aikatawa akaina,' Ishaaq ne ya tashi dan tafiya d'aki wajen Hauwaa, Haroon ya tsaida shi. "Yah ina son dama na yi maka wata magana mai matuqar mahimmanci..." "Haroon ko za ka iya barin maganar zuwa gobe? Iyali na na da buqata ta yanzu," Da sauri-sauri Ishaaq ya wuce ya bi bayan Hauwaa. "Kashhh da ka tsaya kaji ma me zan ce maka, ko kaje ba burge wannan mara godiyar Allahn za kai ba," Ci gaba yayi da shan juice ɗin da ya zuba a glass cup, daga baya ya fita zuwa gidan su Umaimah. Umaimah ce kwance tana danna wayar ta,dana leqa sai naga ashe karatun qur'ani take abun ta, labban ta da suke ta walqiya sai motsawa suke cikin nutsuwa, kira ne ya shiga wayar, ta qarasa ayar da take sannan ta dauka cike da murmushi, 'Ko me zai ce min oho? ' Sallama sukai ma juna tare da gaisuwa, sannan ya sanar da ita yana qofar gidan su, in ba damuwa yana son magana da ita, "Magana? Akan menene haka?" "Magana ce akan zuciya ta da taki," Nan da nan kuwa zuciyar ta ta ta fara tsallen murna, dan kuwa ji tayi kamar ta gan ta a gaban shi, amma ta dake, "Indai akan zuqatan mu ne ka makaro dan kuwa wani ya riga ka ya ɗauke tawa, ma'assalam" Kit ta kashe wayar tana ta dariya , cike da d'imaucewa da gigicewa Haroon ya sake kiran ta, qin ɗauka tayi tana ta yi masa dariya, 'Zaka gane kuren ka ne sai ka nemi Dad da kan ka,dan ko arziqin sanar da kai ka neme shi ba zan yi ba,yanda ka wahal da zuciya ta kaima sai taka ta jikkata,' Qin d'aga wayar shi da ta yi ya sake tabbatar masa da gaskiyar maganar ta, a wajen ya tsugunna sai ga hawaye na fita daga idanun shi. Dafa shi ya ji anyi ya miqe da sauri yana goge hawayen shi, kiran sallar da yaji ne ya tabbatar masa da lokacin daya ɗauka duqe a wajen ya na zubar hawaye domin kuwa sallar la'asar ake kira, "Barka da Yamma Alhaji," "Barka dai, Malam ya dai ka zauna anan cikin damuwa," Sosa kai yayi tare da maida hannun shi ɗaya bayan shi kai da ganin murmushin da yake yi kasan na dole ne, ji suka yi za a shiga sallah, da sauri suka nufi masallacin, "In an idar ka sameni a gida," "Inshaa Allahu," Bayan anyi sallah ya je gidan su Umaimah, yana zaune a kujera a harabar gidan Daddyn su ya dawo, katse azkar din da ya keyi ya yi, ya bi bayan shi zuwa ciki, Sai da Daddy ya shiga ya zauna bai ga Haroon ba ya kwala masa kira, ya tabbata bai shiga bane saboda yana ganin bai kamata ya faɗa gidan mutane ba kai tsaye ba tare da an yi masa izini ba. Da sallama ya shiga ya samu qasan kujera ya zauna,Daddy yayi yayi ya hau sama amma yaqi saboda girmamawa. "Malam Haroonaa me ya faru da kai ka tsaya a gate din gidannan kana hawaye? Ina fatan zaka sanar dani ko meye matsalar ka in ina da halin taimakawa na taimaka," Haroon ya dad'e yana kame-kame kafin ya bayyana ma Daddy abinda ya sanya shi kuka, murmushi irin na manya yayi, sannan yace, "Wannan wasan yara ne a tsakanin ku, amma ni dai ban san na yi ma Umaimah miji ba, kar ka damu kaje gida, zan yi magana da ita, in akwai wanda take so mun ji daga wajen ta, in babu zan baka umarnin ku fito inshaa Allahu," Zuciyar Haroon tana a tsakanin murna da kuma damuwa,what if tana da wanda take so ba shi ba? What if ba zai samu auren ta ba. Godiya yayi, sanan yace zai tafi gida, Daddy ya yi ta roqon shi akan ya tsaya ya ci abinci amma yaqi, zuciyar shi gaba ɗaya ba daɗi. Umaimah na maqale a jikin kitchen tana leqen shi, sai ta ji bata so yanda ta gan shi ba, sannan bata ji daɗi ba data ji Daddy yace ya gan shi yana kuka, ita bata zaci abun zai sanya shi baqin ciki har haka ba, kamar ta d'au waya ta faɗa masa dalilin ta na fad'in hakan amma taqi, iyaka in an tambaye

Chapter 11 of 30