ina jin daɗi sosai idan ina karanta comments ɗin ku, Allah ya sa saqona na isa inda ya dace fiye da abinda na ji kuma nake gani a comments din ku, Allah ya shiryar damu dika ya tabbatar damu akan daidai,Allah ya yafe mana kurakuren mu, Ameen*
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 23:
"My love me kike faɗa ne haka? Bari in tambaye ki, shin waye namijin da ki ke son kasancewa da shi har qarshen rayuwar ki?"
"Kaine😏"
"To me yasa dan kina ɗauke da cikin da nine sanadin samuwar shi kike son zubar dashi? Kin taɓa jin na yi wa halittar ki kushe? "
"A'a"
"To yanzu zan maki wani alqawari, ni Umar na yi maki alqawari ba zan taɓa rabuwa da ke ba saboda lalacewar halittar ki ko kuma rashin ilimin boko mai zurfi ko wata nakasa ko tawaya da zata same ki anan gaba ke har abada ma,ni Umar ina tare da ke ne saboda Allah da son da nake yi maki, dik randa kika ga na rabu da ke to kin saɓawa Allah ne, ko kin yi abinda yake mummuma ainun, wanda na san ba zaki taɓa yin hakan ba,"
Nan da nan idon ta ya yi qifi-qifi ta hau sosa hanci, sai taji bata son a ja maganar ma saboda kar kuma a fara 'yar tone-tone.
Lallab'a ta Umar yayi tayi, tana masa shagwab'ar iya shege har daga qarshe ta nuna masa magana ta wuce ba zata sake tado ta ba.
**********************
Kwanci tashi asarar mai rai, yanzu cikin Jameelaa ya kai wata huɗu,a cikin watannin nan huɗu sau ɗaya ta yarda ta haɗu da Mum, Umaimah ba yanda bata yi da Jameelah ba akan su yi jigilar bikin ta tare amma taqi, ko sanda su Aunty Hauwaa suka kai lefe qememe taqi zuwa, wai bata da lafiya labarin cikin ta ya baza 'yan uwa da abokan arziqi, tanadi kuwa tini ta fara yi dan yin suna na gararin da ba a taɓa irin shi ba a lungun su,Mum kuwa na ta murna zata samu jika dik tinanin ta ya bata cewa Jameelaa kunyar ta take ji ta ganta da ciki shi yake hanata zuwa inda suke, in tayi wannan tinanin sai tayi murmushi ta ji daɗin yin dace da surukar kirki irin Jameelah da ta yi.
Mamalo kuwa na ganin fi'ili kala-kala dan kuwa kusan koda yaushe Jameelah na hanyar zuwa gidan ta,qaryar kuwa da ta d'ingimo za a yi da sunan nan ba qarama bace, qawayen ta na social media dik sun san tana ɗauke da ciki ta kuma sanar da su irin shirin sunan da zata yi, dan haka dik wanda suke a garin Kano sun yi mata alqawarin zuwa sunan, qawayen ta na makaranta yaran masu kuɗi da 'yan qaryar makaranta dik sai d'igimin zuwan jariri ko Jaririya suke yi.
Bikin Umaimah da Haroon ya taso gadan-gadan, dan kuwa Jibi ne d'aurin aure, Jameelaah uwar bidi'a tinda taji ance ba za ai partyn komai ba ranta yake a b'ace, dan haka ta gama shirya qaryar da zata yi ba zata je bikin ba sai ran kai amarya, ranar kuwa zata kasance kusa da Umaimah dan a bata kud'in siyan bakin amarya.
Motar Umar ce ta tsaya a qofar gidan nasu, tana jin qarar kuwa ta d'iba da gudu zuwa d'aki ta kwanta tare da qaqalo kuka ta hau rerawa, tana ta murqususu kamar me jin naquda, sallama ya dinga yi bai ga kowa ba a parlour ba, kwanon da taci soyayyar kaza da lemun da ta tsiyayo a cup na nan ajiye a saman center table, d'ankwalin ta na yashe a qasa, murmushi yayi dan ya san maybe tana d'aki tana bacci, tinda cikin nan ya shiga wata biyar ta daina laulayi sosai sai bacci da yawan cin abinci.
Yana dosar qofar d'akin nashi ya jiyo kukan ta da sauri ya qarasa ciki, ganin ta kwance tana murqususu ne ya sanya shi shiga damuwa duqawa ya yi a gaban ta ya na shafa ta ya ce,
"Subhanallah My love me ke damun ki?"
"Wayyooo Yah Umar zan mutu ciki na ! innalillahi wa inna'ilaihirraji'una ka kiramin Mamana da Babana ka ce su yafe ni ni tawa ta zo qarshe,"
"Plsss my love ki daina irin wannan maganar tell me, me kk ji a jikin naki yanzu haka?"
Nan ta rasa me zata ce masa saboda sam bata yi wannan tunanin ba ma ta fara wannan iya shegen ta jima bata amsa shi ba sai cann cikin kuka ta hau kiran,
"Wayyoo cikina sai motsawa yake yi da qarfi, Yah Umar ɗan nan so yake ya fasa min ciki na ya fito,"
"Dan Allah ki daina fad'ar haka, baby ne ke juyawa, ba tin rannan na fada maki ba haka zata faru sanda ya fara girma a cikin ki ko kin manta ne?"
"To ni zafi yake yi min, dan Allah na ce a cire ka qi, inna mutu wajen haihuwa fa?"
Kawai sai kukan gaske yazo mata, dan tana tsoron haihuwar da gaske har cikin ran ta,
"Yah Umar please do something"
Umar gaba ɗaya ma ya kasa cewa komai tsabar yanda ta kid'ima shi, a duniya baya qaunar abinda zai ji ance ya rabu da ita ko menene shi,dan haka ya qanqame ta yana shafa bayan ta, yana ajiyar zuciya,ganin haka yasa ta ji daɗi sosai a ran ta hankalin ta ya kwanta ta san ta gama da shi ya gama matowa akan ta ba abinda ba zata aikata masa ba ya shanye,daga baya ya sa ta kwanta a bayan ta ya hau duba cikin nata da kan shi,ya na gamawa ya tabbatar mata da ba ta da wata matsala ita da babyn suna nan cikin qoshin lafiya motsi ya fara yi shiyasa take jin abinda take ji.
Umar ko tsinke bai barta ta taɓa ba sai abinda ya zama dole, sai nan nan yake yi da ita, ga shi a matse take da buqatar shi, amma dan kar ya ce qalaou take haka ta hakura, sai dai taqi sam ya rab'e ta, dan in ya taba ta tana iya aje ciwon nan a gefe ta mamaye shi.
***********************
Tin da safe ta ke shirin zuwa gidan Mum, dan kuwa ta ci aniyar sai an bata kud'in siyan bakin amarya, ta qara a na sunan da ta d'ingimowa kan ta kamar amaryar ce ta sa ta yin sunan kece raini.
"Wai shirin me kike yi ne haka ke da baki gama warkewa ba? inace jiya da yamma nan ki kai ta birgima a qasa kina kuka, sai da na samu ki kai bacci kika samu sauqi"
"Zan je kai amarya ne mana, da ba zan iya ba ai ba zan ce zani ba ko? Ko baka ga alamar na samu sauqi bane?"
Umar shiru yayi saboda ya kula da wani rashin kunya-kunya take yin maganar, ya na tsoron tanka ta cibi ya zama qari.
Waya yayi ma Mum ya ce mata ga Jameelaah nan zuwa a kula da ita dan bata da ishasshiyar lafiya kwana biyu, ta bashi tabbacin zata kula da ita sosai, dan itama bata son ta wahal da ita din.
Sai da ta gama shirin ta tsaf ta fito,ba qaramin kyau tayi ba kuwa kun dai san mutuniyar taku wajen kyau, sai qamshi take zabgawa kanta daya sha gyara sai walqiya yake yi.
Umar na biye da ita da ɗan qaramin mazubin da take zuba ruwan sanyi da jakar ta, ita kuma tana tsaye tana yafa mayafin ta, yafin mayafin da ta yi irin na 'yan mata ta yi, a zuciyar shi baya son hakan amma yasan in yayi magana yanzu cibi zai zama qari dan haka sai ya kulle bakin sa ya yi gum ya kyale ta .
(Irin wannan soyayyar sai ta kai mijin da matar ma dika wuta)
Suna tsaka da kulle gidan suka ji maganar Ramai a bayan su.
"Ikon Allah Jameelaa ina zaku haka? Ko bikin zaki je da wannan zungurin cikin naki?"
"Ramai me ya kawo ki gidana da sassafe haka?"
"Habaa Jameelaa ya zaki na yima mahaifiyar ki tambayar me ya kawo ta gidan ki da sassafe?"
In ji Umar da ya ji maganar tata ta yi masa girma a kunnen shi.
Yaqe tayi ta sosa hancin ta, sai dai ɓacin rai ne kwance a zuciyar ta game da Ramai da ke son rusa mata shirin ta,washe baki ta yi sannan ta ce,
"Ba nufina ke nan ba, ina nufin naji daɗin ganin ta sai dai na yi mamakin ganin tane dan kuwa kamar ta san tana raina,"
"Allah sarki d'iyar albarka, zuwa na yi dama danna sanar dake mahaifin ki ba lafiya gashi can kwance, ruwan batirin babur ya taɓa masa qafa wajen yayi mummunan rauni, kin san kuma yanayin gidan namu a matse d'aki daya, ga band'aki na gidan gandu jiya da yamma ya shiga band'akin dan kama ruwa ya faɗi, shine ciwon ya sake kwab'ewa, nayi ta kiran wayar ki kuma bana samu, shine nace bari na zo na sanar dake abinda ke faruwa a can gida"
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un,"
Umar da Jameelah suka haɗa baki wajen faɗa, sannan Jameelaa ta fara magana cikin damuwa, dan kuwa uban ta na da matsayi mai girma a wajen ta, yanda take son shi bata son Ramai ma haka, soyayya mai tsafta take yi masa, matsala ɗaya zuwa biyu ne ya sa take jin haushin sa wato bai wuce tsananta mata da yake yi ba wajen bata tarbiyya, da kuma rashin wadata su da dukiya da bai yi ba kamar an faɗa mata shi ke azurtawa,wannan dalilan sune suka jawo take jin haushin shi.
"Muje Yah Umar ka kaini na ga babana, na shiga uku ni Jameelah ya Allah ka hore mana iyaye na su samu muhallin k'warai,"
Umar cikin tausayawa ya ɗauke ta ita da Ramai sai gidan su Jameelaah ,Ramai na ta zayyana masu yanda abun ya faru a hanya.
Koda suka isa gidan Baban Jameelaa na qofar gida a zaune a tabarma, ciwon dik ya kwakkwab'o abin tausayi, da alama yana jin jiki, Bukar na gaban shi ya dawo daga makaranta dan kula da shi, dan tinda Jameelaa ta sashi a makaranta, dan ta kare yawa kar a zagi qanin ta da ita kan ta shi kuma ya ji daɗin makarantar sai ya riqe ta da hannu bibbiyu,Bukar ne ya ce,
"Sannu Baba Allah ya baka lafiya Ramai na nan zuwa da Jameelaah taje ta fada mata,"
Murmushin takaici Baban su Jameelah ya yi sannan ya ce,
"In ba rashin hankali ba irin na Ramai ina wannan halin zata tafi fad'awa Jameelah da kan ta ba zata aika ka ba,ta kuwa san yanda zafin abunnan yake? Ji nake kamar ana yankan nama na, zuwa asibiti ba shine yafi mahimmanci ba? Amma saboda bani da kud'in zuwa shi yasa ba zata kai ni ba bayan ta na da kuɗi ta kuma san na san ta na da kud'in,Kaii Allah ka shirya min iyali na,"
Motar su Umar ce ta parker, Jameelaah ta bude ta fita da sauri, ganin qafar Baban nata ya sa ta saki kuka mai qarfi ta je wajen shi da gudu ta tsugguna tare da fad'in,
"Sannu Babana Allah ya baka lafiya, Bukar Yah Umar ku kama shi mu wuce asibiti yanzun nan dan Allah,"
Bayan Umar ya gaishe shi ya yi masa sannu ne shi da Bukar sai suka saka shi a mota, sai sannu umar yake yi masa shi kuma Baban Jameelah yana amsawa, cike da jin nauyin surukin nashi,dan a ganin shi bai dace ya shiga motar Umar ba, babban takaici da mamakin sa bai wuce na yanda Ramai ke qunshe da kuɗi a qugun ta ba amma ta kasa kai shi asibiti har sai ta kirawo taimako,ina soyayyar da take yi masa a matsayin ta na matar shi? Ina tausayi irin na miji da mata da kuma na musulunci?
A hanyar su ta zuwa asibitin kowa ya yi shiru ba ka jin komai sai tashin kukan Jameelaah, Baban ta ne ya kula da Umar kukan Jameelaah na damun shi, Murmushi yayi dan kuwa ya san yanda Umar ke tsananin son Jameelaah baya son ganin damuwar ta, dan haka sai ya ce mata,
" 'Yar baba ke da bakya kuka ai be kamata ki yi kuka mijin ki na gani ba sai ya tsokane ki bayan na warke, ko ki na so ya dinga tsokanar ki da me kukan banza ne? Rabon ki ma da kuka fa ni har na manta, me zai saki kuka kamar wanda na rasa qafa gaba ɗaya? Dan Allah kwantar da hankalin ki, ki yi min addu'a kawai kin ji?"
D'aga kai tayi, Umar kuwa cikin sauri ya ce,
"Dan Allah ki daina kukan nan haka, zaki iya samun ciwon kai, kina jin dai Baba yace he is fine,so please stop crying kin ji?"
Sai jan majina take yi Bukar kuwa na ta qoqarin taya baba riqe qafar kar ya fama ta.
Ramai kuwa sam bata so aka barta a gida ba, taso aje da ita ta ci gaba da cusa qoqon barar ta na a sai masu gida ko a kama masu wani su ci gaba da hayar, dan kuwa ta matsu su rabu da wannan gidan da ya zame masu kamar na gado.
Tin da aka shiga da Baban wani daki likita da nurses suka hau duba shi, Jameelaa ta lafe a jikin Umar sai matse hawaye take yi, ganin jini da azabar da Baban ta ke sha ya sa ta jin ba daɗi a ran ta sosai, Mum ce tayo wa Umar waya dan tana son ta ji ya taji su shiru basu je ba kamar yanda suka ce,Jameelah ce ta karb'i wayar ta d'aga ta sanya kuka, Umar ne ya amshe wayar shi ya kanga a kunnen shi ya yi sallama, cikin damuwa mum ke tambayar shi ko lafiya ta ji Jameelah na kuka?
"Mahaifin ta ne ya samu hatsari a qafar shi da ruwan batirin babur, shine muka kawo shi asibiti, dan ya fama ciwon wajen ya samu rauni sama da na da, gamu a asibitin ku ma yanzu haka,"
"Subhanallahi, Allah ya sawaqa inshaa Allahu zamu zo duba shi in aka kai amarya, dan ka san yanz ba a kaiwa da dare zuwa 4 zasu iso su d'au amarya daga nan zamu zo da Daddyn ku inshaa Allahu a gaida mai jikin"
Jameelaah dake manne da Umar tana jin maganar kai Amarya ta kid'ime ta raba hankalin ta gida biyu, ga mahaifin ta a asibiti sannan ga kai amarya, wanne zata ɗauka yanzu?
************************
Mamalo ce jingine da Sadeeq sanda ya gama buɗe masu qofa suka shiga gidan nasu sai sannu yake jera mata, a qasan ledar d'akin su ta zube, shima binta yayi ya kwanta a kusa da ita ya dora ta a jikin shi, hannun shi a cikin zanin ta saman marar ta, sai shafawa yake yana murmushi,
"Sannu maman biyu, Allah ya qara lafiya, ya sauke ki lafiya kin ji Fateena?"
Cike da shagwab'a ta ke murje murje a jikin shi, shi kuwa daɗin hakan yake ji, cikin sassauqar murya irin ta marasa lafiya Mamalo ta ce,
"Ni dai gaskiya ka bar tsokana ta bana so ba wani ciki da nake da shi ni, likitocin nan shegiyar qarya gare su, Jameelaaah nan haka rannan tace min wai ina abu kamar me ciki, ko kuma dai itama har ta zama likitan da gaske kamar yanda tace min, dama haka ake yi daga fara boko sai mutum ya zama likita?"
Dariya Sadeeq yayi sosai, sannan ya juya da ita suna fuskantar junan su ya ce,
"Likita bincikawa yayi ya tabbatar da samuwar cikin naki Jameelaa kuwa kinga tana da ciki itama, in taga wadda sukai anko kuwa kin ga ai dole ta gane ba wai dan ita ɗin ta zama likita bane, zama likita ba abu bane mai sauqi ba dan ina nufin ba zata iya zama likitan ba ko da anan gaba ne kin fahimta?"
Kad'a kai tayi,sannan ta saka kan ta a qirjin shi ta ce,
"Ni kunya ma nake ji, yanzu su Lantai sai kawai su ji ina da ciki?"
"Ke ce ai baki sani ba, wancan maganin da ta aiko kina sha tace na shawara ne, ai maganin masu ciki ne yana qara lfy,"
"Wayyoo Allah na na shiga uku na, da gaske kake yi Masoyi? Kenan likitan yayi gaskiya daya ce cikina wata uku yanzu? Tinda dai tin kwanaki da nai rashin lafiyar nan da tazo ta ganni take kawon maganin nan ina sha,"
Sadeeq dariya ya dinga yi saboda shi a duniya yarintar Mamalon nashi na tafiya da shi, haka ya dinga kwasar ta yana shan dariyar wautar ta.
**********************
Gidan dake manne da na su Ishaaq ya sha gyara iri daya ne sak dana Ishaaq, nan Haroon zai zauna da Umaimah, Ishaaq bai taɓa nuna ma Haroon cikin gidan ba, dan kuwa Haroon bai ma san mallakin su bane, tin da suka dawo Unguwar yau shekara sama da goma bai taɓa ganin wani ya shiga gidan ba, shi kuwa Ishaaq bai taɓa gangancin barin Haroon ya gan shi ya shiga gidan ba,dan baya son mallaka ma matashi mara aure gida ba tare da iyali ba, tinda aka fara auren su Haroon ke son a nuna masa inda zai zauna da iyalin shi amma yana jin nauyin ya tambayi yayan nashi, daya tambayi Hauwaa sai tace itama bata sani ba tana dariya kawai, sai tace masa ya jira yayan shi zai nun masa in lokaci yayi.
Sai gyara gidan ake yi ana sabunta abubuwa Haroon ya zaci maqocin nasu yana son dawowa ne shi yasa ake gyare-gyare,dake ana hidimar bikin shi ma sai bai wani damu da sanin abinda masu gidan ke ciki ba, hankalin shi na kan bikin shi,ya tabbata dai tunda yayan nashi ya ce ya na da gidan da zai zauna da matar shi kar ya damu to fa akwai ɗin yayan sa bai taba bashi kunya ba, ya tsaya masa a kan abubuwa da dama na rayuwar shi.
Abokan shi na makaranta da Islamiyya sun hallara anyi walima, suma su umaimah ana can ana walima kafin a gama mata suje d'akko masa amaryar shi.
Wayar shi ce ta fara ruri, dubawa yayi yaga sunan yayan shi.
"Yayan ango kayi wuyar gani,"
"Gaskiya kam, ai dole tinda qanina yace shima auren nan yake so, ka shigo gidan nan na maqotan mu ina ciki,"
Buɗe baki Haroon yayi ya na tunanin lallai yayan shi akwai cusa kai ba kwarjini, daga fara gyara gida har ya yi abota da masu gida har ya shige?
"Hello kana jina kuwa,"
"Ehhh... ehh ina jin ka, me kake yi a gidan mutane?"
"In ka shigo zaka gani,"
Murmushi Ishaq yayi kawai dan kuwa ya san zai sha mamakin ganin gidan, ta ciki komai iri ɗaya ne dana shi ta fannin tsarin gini, kuma shi ya zuba kayan d'aki da komai, dan islam bai ce dole dangin amarya ne za suyi kayan d'aki ba,dan haka duk yanda iyayen Umaimah suka so su yi kayan d'aki sai Yah Ishaq ya hana, ya nemi alfarma wajen Dad akan a barshi ya yi komai saboda qanin nashi shi kaɗai yake da shi Allah ya hore masa dukiya dan haka hakan da zai yi ya san zai faranta ran ɗan uwan nashi, da kyar dai ya samu Dad ya amince ya yi komai.
Gate d'in Haroon ya ja ya bude ya shiga da kyar dan shi wannan irin gate mai jan wahalar buɗe wa yake bashi, gate ɗin gidan Yah Ishaq mai qofa biyu ne, baki ya bude dan mamaki a lokacin da ya yi arba da asalin cikin gidan,ganin gidan ya yi sak irin na Yah Ishaq a hankali yake shiga gidan, karatun qur'ani ke tashi a ciki,Ishaaq na bakin qofar shiga cikin gidan yana ma Haroon dariya, cikin buɗe hannayen shi dika da farin ciki ya ce wa Haroon,
"Supriseeee"
Keys ɗin gidan ya kad'a ma Haroon da ya isa baki sake ya na kallon ikon Allah,cikin dariya Ishaq ya ce masa,
"Riqe nan ango ga gidan Amarya nan, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka,"
"Dama kai ne ka kunna karatu jiya da dare nake zaton ko masu gidan ne suka dawo?"
Dariya Ishaaq yayi ya damqa masa keys ya fice ya bar shi cikin ta'ajibi, ba inda haroon bai leqa ba a gidan tsabar daɗi da murna bai san hawaye na bin kuncin shi ba sai da yaji gishirin su a bakin shi, zama yayi a kujera riqe da remote yana kallon makka tare da sauraran qur'anin dake fita daga bakin Shaik alfasee, kuka sosai ya saki, Yayan shi ya zama uwa ya zama uba a gare shi, ba shi da wanda ya fishi a rayuwar shi, Allah bai ɗauke iyayen su ba sai da ya masa arziqin ɗan uwa mai riqo da zumunci fiye da abin duniya.
"Ya Allah ka farantawa ɗan uwana, ka qara masa arziqi mara yankewa, ya Allah ka bashi zuri'a mumina saliha,"
"Ameen 'yar budurwa me kuka, shin ko kaine amaryar ne banda labari? Sai ka tashi dan kuwa ga shi can an tafi d'akko amarya, na leqo na ga ko akwai abinda za a sake gyarawa kawai na gan ka zaune ka na kuka,"
In ji cewar Hauwaa da ta shiga a daidai wannan lokacin da Haroon ke kuka da addu'a, kallon ta ya yi ya na share hawayen shi ya ce,
"Yanzu dama har da ke aka yi min rufa-rufa dama wannan gidan namu ne? kullum nake cewa maqotan nan namu ba zasu shiga gidan ba sai aljanu sun gama samun muhalli, rana tsaka a d'aga su azo ana fama da matsalolin jinnu ashe namu ne,"
"Naka ne dai, kai ne mallakin gidan ai,tin kafin muyi aure ya siye filin dika biyun, sai da ya tabbata ya gama gin muka baro na haya muka dawo wancan aka kulle wannan yanzu da lokacin shiga yayi ba gashi za a shiga ba? Komai lokaci ne dashi ai dama a rayuwar nan, yanzu ka tashi na san ba wani jimawa za ai ba amarya zata iso, qannena biyu Safna da Safiyya ma sun zo za aje dasu d'akko ta,"
"Masha Allah na tafi nima na shirya dan tarbar amarya ta,"
"Ina zaka je? Kayan ka na can d'akin ai, ko baka kula zubin ginin mu ɗaya bane, Yayan ka ya tattaro maka komai ɗazu ai,"
"A gaishe da yaya wato ya ma sallame ni, ni ban taɓa ganin ango irina ba ana ta hidimta min ba tare da na sani ba,"
Hauwaa duba ko ina tai taga tsaf yake ba abinda zata gyara, dan haka ta fita tana ta godewa Allah, in zuciyar bawa babu tunanin sabawa Allah a cikin ta sai bawa ya ji ta wasai,sai ka ji ka baka da abin boyewa daga duniya har lahira, sai kaji ka kamar wani leda dan rashin nauyi.
**********************
A can asibiti kuwa tinda Jameelaa taga an fiddo Baban ta qafa ta sha gyaran likita bokan turai, Baban ta ma bacci yake yi ta saka borin sai an kai ta gidan Mum an kai amarya da ita, dan kuwa ba zata bari a karbi kudin siyen baki ba ita ba.
Dik yanda Umar ya so nuna mata ba komai ba sai taje ba qi tayi, daga qarshe yace ma Bukar ya zauna zai kaita ya je gida ya d'akko Ramai, sai su dawo tare, shi ya kula da Baban yanzu kan su dawo..........
*Wacce addu'a zaku ma Jamee, akan kudin siyan bakin nan data sawa ido kamar bakin ta za a siya...kar ku manta fa bata je bikin ba amma zata je dan kud'in siyan baki?*
😂😂😂😂😂😂😂😂
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 25:
Ko da ta koma gidan ta direct parlour ta shiga ta zauna a kan kujerar da ke kallon duk mai shiga da fita, tagumi ta zabga ta na ta tunanin yanda zata tara kuɗi Itama ayi suna mai qayatarwa idan ta haihu, har Sadeeq ya shiga gidan bata sani ba, a gaban ta ya tsugunna tare da qare mata kallo cikin yanayin damuwa ya ga fuskar ta,to meye ke damun Fateen nashi ne ko dai watace ta b'ata mata rai? Cikin yanayi na kulawa ya ce,
"My Teemaa meke damun kine har na shigo baki kula da dawowa ta ba?"
A dan tsorace ta kalle shi sannan ta yi ajiyar zuciya, tura baki tayi gaba ta maida kan ta dayan bangaren bata kula shi ba,cikin damuwa kuwa Sadeeq ya ce,
"Subhanallahi me aka yi maki ne fateena? Ni dai in dai ni na b'ata maki rai ki yafe ni sannan ki sanar dani laifi na saboda na kiyaye gaba, ko
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 30