Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daka mata akan dole ta koma ta kwanta, "Kina da hankali kuwa? Aljanu na maki aiki zaki miqe a zabure haka ba a maki izini ba? So kike yi ki haukace ko?" "Kaiii dakata dalla can, kuɗi na ya saken nayi shirme ban koma na kwashi komai ba na zo nan, ga uban kuɗi can a gida, matsa ka ga, in da da gaske aikin ka naci da ba a saken ba yau, da mijina bai daken ba cikin mutane, aure na ya ɓaci ne saboda kai, nayi dana sanin sanin ku a rayuwa ta, kwalama mai a daidaita sahu kira yayi, aikuwa ba a jima ba ya shiga, rufe qofar sukai, sukayi kan ta, daure mata baki suka fara yi, sannan suka ci gaba da yi mata dik abinda suka so, Jameelaa tin tana kuka ta cikin tsumman dankwalin ta har ta kasa, jikin ta ya mutu murus, ko hannun ta kasa d'agawa take, basu barta ta huta ba sai wajen 1 na dare. Suka wurga mata kayan ta suka fidda ta daga shagon, a adaidaita sahu suka sanya ta, har gida suka kai ta, dan bai manta inda ya kai ta ba ranannan, suna aje ta a qofar gidan suka gudu. Tsoron dare ne ya kama ta ya sa ta fara buga qofar tasu cikin sanyin jiki. Ramai a tsorace ta miqe ta tada Baban Jameelaah dake shaqar baccin gajiya,Bukar ma na d'akin shi ya farka yayi wuqi wuqi da idon amma ya kasa motsawa, tinda suka dawo basu taɓa jin an taɓa qofar gidan su ba bayan 10 na dare balle 1 da kusan rabi na dare. Malam Jameel ne ya kwantar ma da Ramai hankali sannan ya fita, yana ta magana Jameela murya bata fita sai faɗi take tana "Baba ni ce," amma inaa sam baya jin ta. Da addu'a ɗauke a bakin shi ya buɗe qofar numfashin shi kamar zai dauke dan fargaba, to muna cikin zamani na kashe-kashe, gani yayi bai ga kowa ba, ya fara jan A'uzubi kalimatillahi.... a zuciyar shi, wataqila aljanu ne suke musu bugu haka, da sauri ya ja baya zai rufe qofar Jameelaa tana daga kwance ta ja jikin ta ta shiga ta kama qafar Baban nata, ihu ya zunduma ya fara karanta qul'uuhiya. Cikin dasasshiyar murya tace, "Baba ni ce Jameelaa, nice Baba" D'agawa yayi daga faduwar da yayi ya kalle ta, nan da nan ya yi shiru, ya tashi zaune sosai ya sake kallon ta, sannan yace, "Jameelaa? Jameela me ya same ki haka? Kin gan ki kuwa kamar wadda tai artabu da manyan 'yan fashi da makami?" Kamata yayi suka shiga ciki, Ramai ta qule a qasan gado tin da taji ihun gwarzon mijin ta da bashi da tsoro, ta san ko meye yafi qarfin ta. Sai kwala mata kira yake amma haka taqi fitowa, Bukar ne yayi ta maza ya fita, ganin Jameelaa ya sanya ya kwala kiran sunan ta da qarfi, tare da zuwa inda take yana tambayar ta lafiya take ko dai fashi aka yi masu ina Yah Umar da Humairah? Ramai na qasan gado ta ce, "Jameelaa kuma, me zai kawo ta gidannan da tsohon daren nan?" Sai ta hau qoqarin fito wa daga qasan gadon. Da kyar Ramai ta fito, har ta rasa ya akai da fari ta shiga qasan gadon ma,abu kamar wadda aka d'agawa ta shige. "Malam Jameelaa naji kuna kira fa iwar haka, me ya faru" Ganin jameelaa a qasa ne ya sanya ta ruga wa wajen ta itama da gudu,Ramai ce ta kula ma kamar a sume take da sauri ta janyo butar tsakar gidan ta kuza mata ruwa, ai kuwa tana farkawa ta fashe da kuka mara sauti, dan kuwa muryar ta a dashe take. "Dora ruwa mai zafi Ramatu a yi mata wanka, dik jikin ta qasa ne ga shi na kula da wani yanayi a tattare da ita, in ta huta taci abinci, ta samu bacci gobe maji meye matsalar tunda mijin ta be kira ba kuma bai zo ba sannan ba tare suke ba" (Kun ga ko anan hakan ya nuna kyawun halin Umar da kuma yanda ya so Jameelaah ya nuna mata kulawa da tsananin qauna) Ba b'ata lokaci Ramai ta yi yanda mijin ta yace,a nan tsakar gidan ta wanke ta tass, ta tabbata kuma ta gani da idon ta alamar an sadu da Jameelan, lallai Umar mara mutunci ne, sai da ya gama saduwa da d'iyar tasu ya lallasa ta da dikkan alama shine ta gudo gida,ruwa mai kyau ta sa mata tayi wankan tsarki. Tinani Ramai ke ta yi akan,wataqila ma gudowa tayi saboda azabar ta yi yawa, Ramai na gyara ta tana kukan tausayin Jameelaa. Taci abinci sosai dan kuwa tana buqatar shi, koda aka gama mata wankan da kan ta ta iya tsaiwa yau har sallah ta rama tun daga farkon wadda bata yi ba a ranar,bayan ta idar ne ta samu waje ta kwanta, Ramai kuwa bata iya komawa bacci ba ita da Malam Jameel kwana sukai suna sallar dare, dan kaiwa Allah kukan su akan Allah ya bayyana gaskiyar mai gaskiya tsakanin yaran biyu. Washe gari da safe Jameelaa bayan anyi sallah an karya ta zayyana qarya da gaskiya tace Umar dan zai yi mata kishiya ya sake ta harda duka, amma ta b'oye dik wani laifi data aikata masa da mahaifiyar sa, Malam Jameel ne yace, "Kashhh anya Jameelaah abinda ya faru kenan? A halayyar ki dana sani yaron nan ba zai maki haka ba, sai dai ma ya girmama ki , ya karrama ki, sai dai in asiri aka masa aka juya kan shi akan ki," Cikin sauri ta cafe zancen da cewa, "Ehhh Baba asiri aka masa, boka na yace asiri aka yi masa aka rabani da shi," Fadin bokanta da tai ne ya sanya gabanta yin wata iriyar mummunar fad'uwa da tsittsinkewa, abu na farko tinawa da azabar da suka bata jiyan tayi, sannan ta furta boka a gaban baban ta da Ramai dake yawan mata nasiha a kwanakin nan akan ta gujewa sharrin bokaye maqaryata ne, "Jameelaah bokan ki fa ki ka ce? Har boka gare ki ma kenan, tabbas ruwa baya tsami banza, dole muje mu bawa iyayen yaron nan hakuri, sannan in ba shi yayi ra'ayin maida ki ba Jameelaa sai dai ki auri wani ko kiyi ta zama damu. Na maki izini Ramatu kije ki ba mahaifiyar yaron nan hakuri ki jiyo mana asalin me ya faru, ni kuma zan je naji daga wajen mijin nata me ya faru sannan na gana da mahaifin shi Bukar shirya mu tafi yanzu," "Inshaa Allahu zani malam anjima, ke kuma kin wa kan ki, kan ki kika zalinta, wai ace dik irin alkhairin da yaron nan yake mana ya sai mana gida, abin hawa, abinci, abin sha, da komai da muke buqata, amma kika qi hakuri akan rayuwar da kike ciki koda mata uku zai auro a rana ɗaya ,haka ki ka murje ido kika qi godewa Allah da dikkan baiwar da ya maki,  Ni kaina na uwar ki aje makaman jahilci na na koma ga Allah, Malam na koyan karatun addini kuma kullum sai na yi maki nasiha a qoqari na na kawar da tunanin ki akan mummunar turbar da na ɗora ki tun farko,kar ki manta fa Jameelah kin haddace qur'ani da wasu littattafan na islama, dik da ba dan Allah ki kayi hakan ba ya kamata ace sun maki amfani yanzu amma inaa, sai taurin kai da kauce hanya ma ki ka sake yi"   "Ramai na shiga uku na lalace Ramai, ina zan saka kaina, abinda na jawa kaina ba qarami bane Ramai, ki taimaka min Umar ya maida ni d'aki na kodan yarinya ta" Zan ga yanda za ai bari na shirya na je gidan nasu na ji me ya faru dan na san ba zaki taɓa fad'ar gaskiya gaba ɗaya ba ko za a yanka ki.......... *Maji ma gani in tusa zata hura wuta* [09/09, 10:36 am] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA   💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 39: Ramai ce zaune a parlourn su Umar Humairah na ta wasa a jikin ta, Mum sai mamaki take yi dan ganin yanda yarinyar ta sake da Ramai, can ta daina mamaki tabbas dole yarinya tafi shaquwa da Ramai tinda suna je mata akai-akai,  ita aka raina aka raba da jikar ta, dan haka bata san ta ba, shine dalilin yi mata qiwa. Umar ne ya fito cikin shirin tafiya Office, yana ganin Ramai ya isa ya durqusa gaban ta ya gaida ta, amsawa tai cike da jimami. "Umar na zo ne dan na baka hakuri, dan kuwa dik wani abu da Jameelaah take aikatawa koda bani nace tayi ba ina da kamasho a ciki, domin nice Ummul aba'isin lalacewar ta,anfi samun kaso mai tsoka na tarbiyya ne daga wajen uwa, ni ɗin na zama mai son kai, shi yasa Jameelaa bata da tarbiyya, lokacin dana gane gaskiya ina nuna mata hanya lokaci kuma ya qure min gaskiyar ba za ta wa Jameelaa amfani ba sai dai in Allah ne ya so ta da rahama, ta riga ta riqe dik wasu hanyoyi marasa kyau da na koya mata a baya" Hawaye Ramai ta share ta ajiye Humairah a gefe, ta durqusa a qasa, ganin haka Umar ya durqusa shima sosai yana roqon ta akan ta tashi, qin tashi tayi ya juya wajen Mum yana mata alamar ta yi mata magana,Mum ce tace, "Habaa Maman Jameelaah, hakan bai kamata ba, komai kike so wajen Umar kinfi qarfin shi, amma bai kamata ki durqusa masa ba, miqe dan Allah ki zauna," "Dole na durqusa Hajiya, mun maku ba dai-dai ba ne ai, tin daga ranar da akai aure muke rufar ku har yau, na sani Umar baka same ta a budurwa ba amma ka rufe magana kamar yanda tace min baka sanar da kowa ba,wannan ya zama sirrin ku, amma ina son ka sani ni na bata shawarar yanda zatai dan ka ɗauka an yi mata fyade ne, Umar ka yafe min, ni ke karba mata taimako na mallaka, daga nan ta fini zaqewa daga wajen malamai ta koma wajen bokaye, Umar tabbas mun cutar da kai, amma yanzu mun gane kuren mu, mun fayyace maka halayen mu munana a fili ka gani, muna bin ka da sharri kana bin mu da alkhairi, Umar ka yafe mana Mun tuba mun bi Allah , na maka alqawarin ba zamu sake aikata abinda mukai a baya ba,dik da na san bai kamata na tona mana asiri ba wajen neman gafara amma ya zama dole ka sani komai Jameelaa take yi ta sanadi na ne, amma inshaa Allahu ko zaka maida Jameelaa sai ta zama mutuniyar kirki, ba Jameelaar da ka sani a baya ba, ba zan takura maka ko na roqe ka ka maida ta ba, sai dai zan takura da roqo har sai ka yafe mana wannan babban laifi da muka yi maku," "Ballan tana ma aure  ni da ita ya qare, musamman dana ji waɗannan laifukan da kuka aikata akaina, na yafe maku duk abinda kuka yi min amma ba zan sake haɗa wajen zaman aure da d'iyar ku ba har abada, gida da babur da na sai ma mahaifin ta na yafe masa na baku kyauta, amma ba zan baku d'iyata ba zan riqe ta, ku kuma ku riqe ta ku d'iyar, na tafi office majinyata na jira na" Cikin tsananin damuwa ya fita, ashe qarya suka yi masa? Ya ci gaba da kwanciya da ragowar wani? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, wannan wace iriyar rayuwa muke ciki? Ko da ya shiga mota kuka mai quna ya saki saboda tsabar damuwa da tausayin kan shi, he is so innocent bai taɓa b'ata 'yar kowa ba, bai taɓa cewa ma yana son 'yar kowa ba sai akan Jameelah amma sai da aka samu wadda ta cutar da shi, baya nufin kowa da sharri, hasalima soyayyar ta ce fal ran shi, har yanzu da yake jin tsanar ta da halayen ta son ta bai fita a ran shi ba, zai daure zai jure amma ba zai koma mata ba, wannan alqawarin shi ne. Share hawayen shi yayi ya gyara fuskar shi sosai sannan ya kunna motar shi yayi asibiti. Fuskar Mum ma jawur saboda ɓacin ran abinda taji, amma haka ta danne saboda su ɗin mutane ne masu karamci, ta ce ma Ramai sun yafe masu, amma gaskiyar magana basu buqatar mace kamar Jameelaa a zuri'ar su. Ramai na kuka ta fita ta bar gida, ranta ba daɗi akwarai, Humairah ma kukan take dan ta saba da Ramai sosai, tinda kullum sai sun je. Tana zaune tana ta kukan baqin cikin rabuwa da d'iyar ta da mijin ta akan son zuciya ga kuma qasan ta dake ta mata rad'ad'i saboda tsabar azaba,dan ba kaɗan ba suka wahal da ita jiyan, Ramai ce tayi sallama ta shiga, idon ta yayi jawur alamar ta sha kuka, "Ramai lafiya... waye ba lafiya... Ko Humairah ce?me Umar yace zai maida ni ɗin?" "Ashe ma zai koma shan nonon mahaifiyar shi kenan Jameelaah? Ke da Umar kam in ba wani iko na Allah ba ko kuma rabo, na tabbata ba ke ba shi, domin kuwa ya jaddada min hakan da kan shi mahaifiyar shi ma haka, sannan yace ba zai ba da Humairah ba, shine babban abinda ke sanya ni kuka, ina tausaya ma yaron da aka raba da mahaifan shi uwa ko uba wajen rabuwar aure,wasu  yaran na tashi cikin qunci da tsanar kowa tare da lullub'ab'b'en munafurci da mugun hali a qasan zuciyar su, wanda suke aiwatar da shi ba tare da angane su ke yi ba, Jameelaa da yanda na fara koyar dake munanan abubuwa dana aje na fara koya maki mai kyau kin ɗauka da ba haka ba, yanzu wa gari ya waya? ki daina min kuka haushi ke qara kamani ni dan uban ki" Jameelaah har buga kan ta take a jikin bangon da ta jingina da shi tsabar shiga damuwa da tashin hankali, ina zata saka ran ta yanzu Umar ya barta har abada? "Na shiga uku na lalace na banu ni Jameelaa, yau na ga ta kaina, dan Allah ku taimakamin na koma gidan mijina, wayyooo Ramai na shiga uku na" "Dan Allah ni karki taran maqota a zaci mutuwa aka min, ki shiga d'aki ki rufen baki kar ki ja na lallasa ki laifin waye? In ina da laifi a lalacewar tarbiyyar ki ai na yi qoqarin sauya maki halayya dana gano gaskiya ko? amma haka ki ka kafe ki ka munafurce ni ki ka nuna min kin sauya ashe kina can kina qullawa kan ki gadar zare, ni ban girme ki ba amma na aje makaman jahilci na? sai ke kika maqale naki kamar jakar fata, to ga abinda kika jawa kan ki nan, ina bokan naki yau?" Haka Ramai ta yi ta aikin gida tana faɗa bakin ta ya qafe qafff ba yawu a ciki, ranta sai suya yake musamman in ta tuno Humairah, saboda ba da wasa take son yarinyar ba. Jameelaa kuwa daina ci da sha tayi saboda damuwa, abincin ma baya shiga ko ta ci sai ta dawo da shi. *********************** Yarinyar Umaimah ta ci sunan Mahaifiyar su Haroon Ameena sina kiran ta da Ummee, Haroon ji yake dik duniya ba wanda ya kai shi jin daɗin rayuwa, saboda samun iyali nagartacce, Sapnah na matuqar son yarinyar akwai kyau da qiba, futum-futum din kumatun ta mai lotsawa ke burge ta, Muhammad ɗin Hauwaa na son taɓa mata kumatu, Umaimah ta hana tace gani yake kamar balambalam ne hala, haka Sapnah zata haɗa su dika tai yi ta masu wasa, tana yi masu surutu kamar suna ganewa. Humairah yanzu ta fara sabawa da Mum amma ba wani sosai ba kamar yanda ta saba da Ramai, tinda tana zuwa aiki ba koda yaushe take a gida ba. Yau weekend dan haka suka shirya dan zuwa ganin baby Ummee, komai Mum ta haɗa a jaka na Humairah,  ta sanya mata kayan ta kalar nata, abin gwanin sha'awa, Umar ya qure wanka, dan yau yake son ya bayyanawa Sapnah sirrin zuciyar shi, shi ke jan motar suna tafe suna hira. Koda suka isa gidan Umaimah a rufe yake, tinda Ishaaq da Haroon suka fita ta koma wajen Hauwaa, Sapnah sanye take da riga da wando wanda suka yi matuqar amsar shape ɗin ta, sai cilla Muhammad sama take yi sama shi kuma yana dariya, "To zauna ayiwa Ummee itama," "Ah ah Sapnah ban isa ba, bata yi k'warin daza a wurga ta sama haka ba" "Ohhh yaran zamani babu ko kara? Ai itama uwar ta ce, ko an faɗa maki in ta wurga ta ba zata dawo bane?" "Mummm oyoyo," Da gudu ta faɗa jikin Mum Umar ne ya shiga gidan ɗauke da Humairah, Sapnah ta aje Ummee ta amshi jakar hannun Mum, ta durqusa ta gaida ta, sannan ta kama hanyar d'akin ta dan zuwa sanya hijabi, Umar kurrr yayi mata da ido, dik da bata kai Jameelaah shape ba ba ta rasa komai ba itama, ga kalar fatar ta mai kyau. Hararar shi ta yi sanda zata shige dakin tare da murgud'a masa baki, dan ta gama kama shi yana kallon ta,murmushi yayi ya sosa kai da ɗayan hannun nashi, sannan ya qarasa shiga ciki, bayan gaishe-gaishe ya tambayi masu gidan suka sanar da shi basu nan sun je kasuwa. "Ohhhh ashe fa ku 'yan kasuwa ne , ba kuyin weekend," "Muna yi mana ran lahadi amma," Dariya suka yi sannan Umaimah ta ɗauki Humairah, shi kuma ya ɗauki Ummee suna ta hira abun su Sapnah ta fita ta je kitchen ta had'o masu abun sha da na ci, zuwa tayi ta aje ma Mum nata a gefen ta, sannan ta aje ma Umar a nashi gefen, zata tafi yace, "Madam ba gaisuwa ne?" "Ina kwana?" "Bana cin miqe," Kallon gefen Mum tayi ta ga bata ma kallon su, murgud'a masa baki ta sake yi ta shige kitchen, murmushi yayi salon ta na burge shi. Yana sane ya ɗauki lemon ya zuba kaɗan a jikin shi akan idon Umaimah kuwa hakan ta faru, zata yi magana ya sa hannu a bakin shi alamar tai shiru, dariya tayi qasa-qasa, sannan ta kad'a kai alamar ta gano shi. "Kashhh abunnan ya zuba min a kaya, Sapnah ɗan zuban ruwa na wanke," "Ok taso to," Bata kawo komai a ranta ba haka Mum da Aunty Hauwaa ma basu gane komai ba, suna zuwa kitchen ta miqa masa ruwa a cup ɗin da suke amfani dashi wajen d'iban ruwa, qin amsa ya yi ya tsaya ya kafe ta da ido tana ja da baya yana bin ta, sai da bayan ta ya taɓa fridge sannan ta tsaya, kallon ta ya dinga yi, tin tana iya kallon shi har ta kasa, ta sauke idon ta qasa ,daga nan ta fara qoqarin guduwa, dubawa tayi space ɗin daya basu ba wani isasshe bane tana taku daya zasu hada jiki, wato ya mata haka ne dan kar tace zata gudu ko? "Please ni dai ka matsa na wuce kar su ga mun dad'e," "Sai su zaci me ke faruwa kenan," Wani qamshi taji ya fita daga iskar bakin shi nan take ta lumshe idon ta, zuciyar ta na gudu kamar zata fito waje, "Yah Umar dan Allah ka matsa," "Sai kin amsa min wata tambaya kuma da eh nake son ki amsa, in ba haka ba, daukan ki zan cak na maida ki parlour na ajiye ki a  gaban su Mum " Zaro ido waje ta yi ta kama bakin ta,Umar yace mata, "Kin amince?" D'aga kai tayi da sauri, dan ta matsu ya bar wajen, kusancin nasu yayi mata yawa. "Ina son ki, ina qaunar ki domin Allah, ina son ki zama uwa a wajen Humairah da qannen ta da zaki haifa min, ina fatan zaki aure ni?" Wasu hawaye ne masu zafin gaske suka fara sauka a kuncin ta na tsananin farin ciki, zuciyar ta kuwa na tsananin sauri saboda bugawa, sai wata zufa da ta fara tsattsafo mata ba zato ba tsammani, da gaske kunnuwan ta suke da suka jiyo wannan kalaman ko qarya ne? Da kyar ta buɗe baki, lips din ta na rawa tace........................ *Casssss sai anjima ko gobe maji me zata ce* [09/09, 10:36 am] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 40: "Matsa baya dan Allah, bana son wani ya gan mu a haka abinda matar ka ta zarge mu ya zama gaskiya a idon mutane," "Subhanallahi haba Sapnah ! inshaa Allah hakan ba zai taɓa faruwa a tsakanin mu ba har abada sai munyi aure" Baya ya ɗan ja, tare da rungume hannayen shi a qirjin shi ya langab'ar da kan shi gefe daya yana jiran yaji me zata ce masa, goge hawayen ta tayi idon ta a qasa, tana buɗe baki zata yi magana wasu hawayen suka zubo mata, "Dan Allah Sapnah kar ki min haka, ki tsaida zuciyar ki a wajen da ta dace, kar ki saka shakku akan abinda ke ran ki, na sani kina so na, nima ina son ki, kawai amsar ki na ke nema ko zaki aure ni?" "Yah Umar a gaskiyar magana ba zan iya auren ka ba, me kake tunani mutane zasu ce? Tinda kusan akaina kuka samu sab'ani da matar ka," "Akan ki aka fara rikicin amma ba dan ke na sake ta ba, saboda abinda tayi wa mahaifiyata ne naga ya kamata na rabu da ita, and yanzu haka da za ki ji abinda ta aikata lallai da ke kan ki kin tinkare ni da maganar aure dan ki sanya ni farin ciki, fuskata dake dauke da dariya bayan ta akwai wani baqin ciki daskararre mai wahalar fita wanda kece ruwan d'umi da soson da zata wanke min su, kiyi jahadi ki amince da aure na ki ceci rayuwa ta Sapnahh," "Please Sapnah domin Allah ki amince ki auri Abban Humairah, dan ki zame mata uwa ta gari, kar ta tashi da tarbiyyar da ba uwa a cikin ta, tarbiyya in ba uwa a ciki bata cika tarbiyya ba, dan akwai abubuwan da dole sai uwa ce ta san zu zata koyar da yaron ta su, ina nema wa yayana alfarma a wajen ki in ba haka ba zan kira Mum itama tazo ta roqe ki, and ku rage sauti an fara jiyo ku a parlour" In ji cewar Umaimah da ta shiga kitchen din, matse sauran hawayen da ke maqale a idon ta Sapnah tayi, sannan tace, "Allah ya zab'a mana abinda yafi alkhairi, zanyi shawara da Aunty Hauwaa dik abinda muka yanke zan sanar da kai," Fuskar tausayi ya sanya yaqi amsa ta, ganin haka ne ya sa tayi murmushi, he is so cute..... "Yah ka bari mana is just a matter of time, lokaci na yi komai wayon amarya sai an sha manta," Duka Sapnah ta kai ma Umaimah,tare da harara, Umaimah ta ce, "Dik ni kadai matar yaya? To na gode da kulawa," "Ni gaskiya a kira aunty Hauwan yanzu, so nake a gama komai yau, ko hankali na zai kwanta baki ji yanda nake  jin rad'ad'i a raina ba ne, da ba zaki iya ja min rai ba kema" Idanun shi sun sauya kala, alamar da gaske yana cikin wani hali. Umaimah ce ta leqa parlour da kan ta, ta kira aunty Hauwaa ta yafito ta da hannu, "Umaimah please ki bari mana zuwa gobe,yau da gobe ai dik ɗaya ne," "A wajen ki ba," "Ta samu ne? Me kuke yi ne shiru ba wanda ya koma, da an shigo kitchen sai a laqe ba a komawa?" "Shawara Sapnah ke nema akan ta amince zata auri Yah Umar ko kar ta amince? Ke meye ra'ayin ki akai?" Sapnah da kan ta ke qasa ce ta yi saurin kallon Aunty Hauwaa tana zaro ido, dan jin amsar da zata bayar zuciyar ta sai harbawa take da sauri, Allah ya sa tace ta aure shi, shine fatan da take tayi. Kula da yanayin ta ne ya sa Hauwaa tace, "A gaskiya ni dai Umar bai dace da Sapnah ba....... "Aunty me kike fada ne haka? Waye to ya dace da ni in ba shi ba?" "Ke ce kika dace da shi Sapnah, dan haka shawarata kuyi aure nan ba da jimawa ba," Wani daɗi da kunya ce ta kama ta, dan reaction din ta ya nuna tin da ta amince kenan amma tana neman izinin yayarta tane. Dariya suka fara yi mata ta rufe idon ta zata shige ya tare hanya, "Not so fast 'yan mata, baki faɗa min amsar ki ba, a yau ina son Dad yaji labari mai daɗi irin wannan daga waje na," Cike da shagwab'a ta buɗe fuskar ta ta turo baki gaba kaɗan tana wani langwab'e kai tace, "To wai

Chapter 24 of 30