Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta ce, "Mu ba haka muka dauki rayuwar mu ba Jameelah, kuma na tabbata a jiya kin gane hakan da idanun ki,ko Mum sai da tace na gaida ki da safen nan kafin na taho saboda kin burge su, kin shiga ran Mum sosai" A cikin zuciyar ta ta buga ihu tare da murna ta ayyana, 'Alhamdu lilLAAH uwar mijina na sona' A zahiri kuwa sai ta ce, "Allah sarki Mum ba ruwan ta itama, ki gaidan ita sosai in kin koma, kinga karbi haddata kiji min," Mamaki ne ya kama Umaimah da Mamalo dake manne da su tana jin tattaunawar tasu,amma dole suka shanye mamakin su dan kuwa gimbiya Jameelah ko a jikin ta sai ta fara zubo karatun qur'anin da ya sake tsunduma duk wani mai sauraron ta a cikin duniyar mamaki,daga qarshe dole Umaimah ta shanye nata mamakin ta kasa kunne ta na sauraran haddar Jameelah wadda ke zubo karatun da murya mai dadin sauraro, sabon malamin su da ya shigo ya ji karatun da take zubawa nan take ya kira ta ya tambayi sunan ta saboda ta burge shi sosai. Bayan ta sanar da shi ne ya ce ta je ta zauna sannan ya gabatar masu da kanshi a matsayin Malam Haroon, sannan ya nad'a ta matsayin Monitan ajin,nan da nan 'yan aji kuwa akai ta ihu suna kiran ba sa so, wasu daga qawayen ta gudun kar ta ce harda su aka ce ba a son ta su kai ta cewa suna so. Ko bi ta kan su baiyi ba aka fara karatu, ganin haka yasa Jameela dagewa sosai dan kar ta ji kunya. Malam Haroon baqi ne kyakkyawa kuma Ustaz dan kuwa wandon shi ma a dage yake ga gemu mai kyau daya kwanta a fuskar shi, yana da gira cikakkiya kamar an zana ta, yana da tsananin tsafta, da kuma ilimin addini, yayi boko amma iyakar shi secondary, daga nan ya ci gaba da maida hankali akan kasuwanci da neman ilimin islama. Iyayen shi sun rasu daga shi sai yayan shi mai suna Ishaq,Haroon yana zaune ne a gidan yayan na shi wanda ke da mata guda ɗaya, Yah Ishaq yana da kuɗi sosai shi ɗin babban ɗan kasuwa ne, ana saida manyan laces, dogayen riguna, atampopi shaddodi da mayafai a shagunan shi, matar shi Hauwa'u mace ce irin 'yan duniyan nan masu yin abinda suka so a gidan miji ba tare da ya sani ba, Haroon ya san dik wani iskancin da take aikatawa na zuwa wajen bokaye dan mallake ɗan uwan na shi,Hauwa'u na matuqar son Haroon fiye da yanda take son mijin ta Ishaq, a cewar ta Haroon ne mai jini a jika yayan shi dik ya zama sauran basir, yanzu haka Haroon a cikin matsalar matar Yayan nashi Hauwa'u yake, dan kuwa ta ɗana masa tarko akan dole sai ya kusance ta, in ba haka ba zata masa sharrin da sai yayan shi ya kore shi daga gidan, dan haka zaɓi ya na wajen shi yanzu. Bayan kammala karatu sai ya sa yaran su yi masa addu'a akan Allah ya tseratar da shi daga sharrin dikkan mai sharri ya bashi nasarar tsallake dikkan tarkon maqiya, suna kammala addu'ar Haroon ya raba masu sweet, da zai fita ne ya kira Jameela. Cikin yanga irin ta ta wadda ta zame mata jiki ta durqusa a gaban shi, kallon ta yake daga tsayen gashin idon ta sun kwanta a fuskar ta, ga wani kwantaccen gashi a saman girar ta mai kyau,cikin muryar shi mai daɗin sauraro ya ce mata, "Jameela ko?" "Eh malam," "Ko zaki faɗan me yasa 'yan ajin ku basu son a nad'a ki monita?" Wata a jiyar zuciya ta sauke tare da dafe kan ta, alamar ciwo yake yi mata, ganin haka yasa shi cikin kulawa yace ta miqe tsaye, da sauri kuwa ta miqe, dan durquso ba dabi'ar ta bane. "Kan ki na ciwo ne," "Eh malam" "Subhanallah, maza to je ki amshi magani a office din malamai, sai ki koma aji, mayi maganar watarana," Ta bayan shi ta wuce dafe da goshi, kamar mai tsananin jin ciwon kai, A ranta kuwa sai masifa take yi... 'Kaji min mutum, kawai dan dai hauka akaina ya qare sai na hau faɗa masa ni ɗin ba marajin magana a kaf makarantar sama dani? ka ji a bakin wasu ni kuma na qarya ta su da aiki na,' Murmushin mugunta tayi, ta zagaye office din malamai ta koma ajin su, zaman ta tayi bata sake kula kowa ba dan kuwa a qufule take da kowa, 'yan zuwa surutu wajen zaman su sun taru,suna jiran su ji me zata ce game da wannan sabon salon da suka gani a wajen ta,banza tai da su ta d'au qur'ani ta fara hadda,dan kuwa Jameelah bata da aikin yi sai hadda yanzu, tana fatan ta kamo 'yan ajin,lokacin shashashanci ya qare. ********************** A cikin wata shida Jameela ta gama haddace dik inda aka barta abaya, a yanzu ta iya karatun ta sosai da sosai duk inda aka tab'o a qur'ani da hadith da duk wasu littafan da ake yi masu zata karanto wa mutum tsaf ba kuskure,data zauna a waje sai dai kaji karatu na zuba kamar ruwa, daɗin muryar ta ke qara ma mutane qaimin sauraron ta, gidan su Umaimah kuwa ta je shi yafi ba iyaka. Yau ma sun gama shiri akan zasu je gidan su umaimah yin karatu,driver na zuwa ta faɗa motar kamar tasu,suna ta hira a haka har suka isa gidan. Da sallama ta shiga, bakin ta ta washe data ga Mum. "Mum din mu ina wuni? ya aiki?" "Lafiya qlou Jameelan Mum, ya maman ki da Baba da Bukar" "Suna Lafiya qlou alhamdulillahi, Mum akwai wani aikin da zan taya ki ne? Ina Dad?" Umaimah dake murmushi ta wuce su zuwa d'akin ta dan sabon da Jameela tayi da mum ɗin ta na bata mamaki. "Daddyn ku ya fita, amma na san suna hanyar dawowa yanzu," 'Anzo wajen, na tabbata da Yah Umar aka fita yau,' Abinci ta taya ta suka qarasa dafawa, umaimah ma bayan tayi wanka ta sauya kaya suka qarasa shirya table tare, suna kammalawa kuwa su yah Umar na dawowa,a gajiye suka shiga gidan direct kujera ya samu ya zauna ya na qarewa yarinyar da ke yawan faɗo masa a rai a kome yake yi. Sake kallon Jameela ya yi wadda kullum yake kasa gane a uniform tafi yin kyau ko kuma a kayan gida ne tafi kyau, itama shi ta ke kallo tana masa murmushin da ta kula yana matuqar qayatar da shi. "Yaahh Umarr ina yini?" Sai da ya ji tsigar jikin shi ta miqe, tsabar yanda ta karya murya wajen kiran sunan nashi, "Lafiya Qanwa ta," Wucewa tayi ta koma d'akin su Umaimah, kamar yanda take yi in tazo ta taya Mum aiki sai ta shige ta d'auki karatun ta tayi tayi,hakan ke qara mata babban matsayi a wajen su dika mutanen gidan dan kuwa ko abinci bata ci sai ta kammala haddar ta, dik da mugun kwad'ayin da takan ji dan ganin ta ci abinci kan ta yi karatun, amma tinda akwai motive din yin hakan bata damuwa. A bakin qofar dakin ya tsaya yana bin ta da kallo, yanda ta cire hijab ta rufe kan ta da shi, ta gaba a bude hakan ya yi masa kyau, Umar kasa ɗauke kan shi yayi daga kallon qirjin ta yana mamakin cikar su, Umaimah ko bra bata sawa saboda ba su da wani girma, amma ita sun cika bra din ta sannan sun cika rigar ta har ana ganin su ta saman V neck din ta, Wani abu ke masa yawo a jinin jikin shi game da ita, dan haka komawa baya yayi yana sauke numfashi da sauri da sauri. Sai yamma Jameelah ta kammala isar da saqon zuciyar ta a gidan su Umaimah sannan tace zata tafi, kamar kullum Mum ta bata dubu biyu kudin mota suka yi sallama ta fito dan tafiya gida. A waje ta gan shi cikin motar shi yana zaune kamar mai jiran wani, yana ganin ta ya fita ya buɗe mata gefen mai zaman banza. Kallo ta bishi da shi mai matuqar daukan hankalin mai kallon ta, shagala yayi da kallon ta ta shagwabe fuska sannan ta ce, "Yahhhh Umarrr kallon fa?ko dama dan kayi ta kallona ya sa zaka taimaka ka maida ni?" Murmushi yayi ya sosa qeyar shi ya zauna a mazaunin driver sannan ya tada motar suka fice daga gidan, a hanya ya samu wani wajen bishiya mai iska ya tsaya, juyawa yayi yana fuskantar ta sannan yace, "Ina son na maki wata tambaya, tsakani da Allah nake son ki bani amsoshin su," "Inshaa Allahu zaka sameni mai gaskiya a dikkn abinda zan amsa maka," Umar gyaran murya yayi fuskar shi ba wasa a cikin ta, sannan yace............................ *Allah ya maimaita mana Sallah ta badi mai albarka, Hppy sallah to u all,amin hakuri aikin sallah kun san yanda yake akwai wahala, a ajen naman sallah na zan zo na amsa, sai muyi hakuri da wannan gobe ko dik sanda dai na samu dama mun ji me Yah umar zai tambayaq* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 6: Kitchen Umaimah  ta shiga sanye da zumbulelen hijab ɗin ta dogo,tafe take tana istigifari saboda tasan abinda zata yi bashi da kyau,sai dai wata zuciyar na ce mata, 'Ai ba komai abinda zaki yi ba laifi bane taimako ne, kuma ko su iyayen naki ai sun koyar da ke taimakawa marasa shi dan haka kar ki wani damu, je ki d'eba mata kawai' Da wannan shawarar ta yi amanna ta qarasa kitchen ɗin, tayi sa'a kuwa ba kowa a ciki, mai aikin su na d'akin ta tana cin abinci, nan ta buɗe kowanne abinci ta d'ibarwa Jameelah a leda mai kyau sannan ta ninka ledar sau uku ta yanda ko qamshi ba za a ji ba, ta saka a cikin Hijab din ta ta fice zuwa d'akin ta, a jakar Jameela ta saka wannan ledar ta rataya sannan ta bi bayan Jameelah parlour ,a tsaye ta ha Jameelah ba kowa a parlour sai kalle kalle take yi,raka ta wajen Mum ɗin su tayi dan yi mata sallama, Jameela a bakin qofa ta coge taqi shiga wai ita mai ladabi, kar ta fada masu daki ba tare da an yi mata izini ba,a  nan ma ta samu nasarar samun yarda da amincin Mum ɗin su Umaimah, cikin murmushi Mum ta ce, "Come in my dear, don't feel shy nan ai gidn ku ne kema" Zazzaro ido ta yi waje dan jin Mum ta yi mata turanci, yaren da ko a cikin mafarkin ta ganin shi take yi kamar mutum mai qafa yana mata yawo a kwanya, ba qaramin son ta ji tana yara turanci take ba, "Ammm ban san mee kike ce ba Mum,kiyi hakuri," Baki sake Mum take kallon ta,yarinya budurwa kamar Jameela amma ace bata san me ta fada ba da turanci,? kodai bata da qoqari a makarantar boko ne? Umaimah ce ta ce, "Mum Jameelah bata zuwa boko iyakar ta islamiyya, saboda wasu dalilai daya ke a cikin gidan, so ina ga kawai kuyi sallama zata koma gidan su yamma na yi," "Ya salam ! kiyi hakuri, indai da rabon ki zaki yi boko Jameelah, kin ji," Cikin wani ladabin mage mai kwanciyar ɗaukan rai Jameelah ke kad'a kai, tare da matse kwallar da babu ita a idanun ta, sai nan d nan Mum ta ji kamar ta zage ta ne, inda ta san bata iya turanci ba bata zuwa school da bazata yi mata turanci ba. Tashi ta yi daga kan abun sallah ta isa gaban Jameela ta kama hannun ta, Jameela ta qanqame jakar ta da kyau a hammata dan kar aji qamshin abinci a gane zata tafi da wani gida kamar abincin gidan biki, wato aci ayi guzuri. "My dear, kar ki damu kin ji? ki kwantar da hankalin ki na yi maki alqawarin indai ina raye zaki yi karatu mai yawa har sai kince kin qoshi zaki zama kamar umaimah, sai dai ina so ki yi min alqawarin kare mutuncin ki da kuma maida hankali akan karatun?" Cike da zumud'i da kuka mai hawaye Jameelah ke godiya,dan kuwa bata taɓa zatan wadannan kalaman daga bakin Maman Umaimah ba, durqusawa tayi tana kuka sosai dan jin daɗin kalaman nata. "Shshhhhiiii, ba kuka zaki yi ba Jameelah godewa Allah ya kamata ki yi kin ji? sannan ki bari zan samu lokaci mu ziyarci gidan ku na yi magana da iyayen naki ,babu bata hana karatu tunda ba kan ku farau ba, wani ma baki san da ya ya samu arziqin shi ba, dan haka ki godewa Allah with the little u have, ohhhh sorry, da kaɗan  ɗin da ki ke dashi komai qanqantar shi kuwa,watarana sai labari kin ji?" "Na gode Allah ya qara girma ya jiqan mahaifa, Allah ya saka maku da alkhairi mara yankewa," "Ameeen.....ga wannan ki sha alawa, dan da da akwai da na loda maki ita,dan na kula ke din ma kamar Umaimah ce wajen son zaqi," Dariya suka yi dikan su Jameela ta sunkuyar da kai ta na murmushi, ta ajiye kud'in da aka bata a gefen ta tana wani nuna ita an hana ta amsar kudi a waje, kar Maman ta ta dake ta. Da kyar aka samu ta riqe kud'in,cikin dabara ta qirga su a hijabi dubu biyar Mum ta bata cif-cif,ta na gama qirgawa ta danna abunta a jaka,cikin ranta ko sai gode masu take yi dan kuwa bata taɓa riqe kyautar kuɗi tsababa haka ba a lokaci ɗaya ba a wajen saida abinci ba, a ran ta ta ayyana, 'Kaga masu yi dan Allah, in za ayi za ayi kawai alaji in ba za ayi ba a bari kawai, haka nake so yanzu da wasu ne dana ce bana so zasu danna a aljihu ko jaka shikenan na rasa' "Ga Yah Umar din nan ma...Yah ga qawata zata koma," "Da wuri haka? Ki bari na aje ta gida to dama zan fita ne zan siyo wasu abubuwa, saboda karatu muje na aje ta ko?" "Ba dan zan yi hadda ba dana biku, na gode sosai Jameelaa sai mun haɗu gobe a makaranta," Dad ma dubu biyar ya bata kyauta, nan da nan Jameelah ta ji kan ta na neman buɗe wa, dan kuwa ji tai kamar ta haukace dan murna bata taba riqe kuɗi nata na kanta ba  a dunqule a hannun ta ba irin haka. Tin da suka shiga motar ta sunkuyar da kai tana ta muimui da baki kamar mai tasbihi ga Allah, Umar kuwa a ranshi yace, 'Yarinyar nan tana da hankali matuqa, da dikkan alama tasbihi take yi ko kuma karatun qur'ani' Cikin wata iriyar murya Umar ya ce wa Jameelah, "Kar na katse ki, amma ina son na tambaye ki," "Allah ya sa na sani," Murmushi ya yi kafin ya ce mata, "Kin ma sani Malama Jameelah, meye sunan unguwar ku? Sannan ki yi min kwatancen inda zan ajiye ki kinga ni ban sani ba, kuma baku faɗa min ba, in kuma so kike mu b'ata to shikenan ba zan damu ba dan na b'ata da ke a garin kano" Kama baki ta yi tana murmushi, ita a dole ta ji kunya,cikin murya mai cike da salo ta ce, "Na manta ai, na zaci Umaimah ta sanar da kai inda za muje" "Ta dai sanar dani sunan unguwar ku kuma na manta,sannan bata faɗan inda zan ajiye ki ba," "In mun shiga unguwar mu zan nuna maka waje, ba boyayyan wuri bane, saboda hada-hadar saida abinci da sha da ake yi a wajen musamman saboda masu kasuwanci da matafiya," Jinjina kai yayi, da yabawa yanda take magana cikin tsari da hikima kamar ta wuce shekarun ta. Shiru ba wanda ya sake magana har suka isa, lokaci zuwa lokaci ta kan ji alamar yana kallon ta, dan haka dik wani yanda zata yi ta matso kyau yi take yi ta yanda ba zai gane tasan yana kallon ta ba, ga bakin ta na rasa me take faɗa amma tabbas na san ba tasbihi bane sai dai wani salo irin na yaudarar ta shi ya jawo motsa shi da take yi. Lokacin da suka isa unguwar tasu ne ta hau yi masa nuni da hannun ta inda zai shiga, salon yanda take nuna masa waje ne yasa ya dinga bin yatsun ta da kallo, tare da yaba kyawun halittar su a zuciyar shi. 'Ikon Allah ! yarinya qarama amma masha Allah she is so beautiful' Motar ce ta tsaya a dai-dai inda ta nuna masa nan ne gidan su,wanda daga nan inda suke tsaye da motar ta nuna masa gidan nasu, ya tausaya mata matuqa ace kamar ta anan take rayuwa, sauke kai tayi qasa tana ziraro hawayen munafurci, ga masu shaye-shaye nan suna ta zuqar sigari, wasu ma wiwi ce suke sha, ga mata nan na fiddo da abinci suna ta wasanni da maza, abun dai sai wanda ya gani ba kyawun gani a wajen mai tarbiyya. "Me ya faru kike kuka? Dan Allah ki bar kukan nan, habaa don't cry mana is ok," A ɗan daburce ta kalle shi dan bata gane me yace ba,nan da nan Umar ya tuna yaji ɗazu suna magana akan bata yi boko ba, sai kawai ya yi shiru bai sake magana ba,miqa mata tissue yayi dan ta goge hawayen ta, tare da lallashin ta iyakar iyawar shi,da a kyar ya samu tayi shiru,dan haka cikin muryar lallashi ya ce mata, "So tell me, sorry, yanzu faɗa min me yasa ki kuka haka ke da na dawo dake gidan ku lafiya ba cizo ba yaqushi?" "Dan Allah kar ka hana Umaimah qawance dani saboda yanayin unguwar mu, bamu da zaɓin daya wuce zama anan, arziqin da iyaye na suke da shi kenan, kuma ni......" Ɗora hannun sa yayi kan leban shi yana nuna mata ta yi shiru, "Habaaa Jameelaah ! akan me zan raba ku qawacen ku da Umaimah dan na ga kalar unguwar da ki ka taso a cikin ta? Ki na tunanin ku kadai ne Allah ya ajiye a haka? Shin baki san rayuwar wasu ma  tafi taku babu ba? Babu abinda zai sa na raba ku ke da qawar ki, kina da qima da daraja a idon ahali na, ke din a cikin waɗannan mutanen kamar audigar da aka bata saman ta ne, sama datti ciki fari, kar ki damu kan ki akan qaddarar ki watarana sai labari," Jameelah kuwa cikin ranta ta ayyana, 'Ohhh Allah ya kawo labarin nan kusa, kawai ina cikin AC da carpet an dawo dani nan,yau na shiga uku ni Jameela talauci ba yi ba a rayuwa' A zahiri kuwa wani kukan ta sake saki, a zaton shi wani abun ta sake tinawa,cikin kuka ta furta, "Na gode, na gode sosai, Allah ya saka ma da alkhairi Yah Umarrr kai din mutumin kirki ne, wanda bai da girman kai da kuma kyamar talaka," Murmushi yayi, yaji daɗin yabon da ta yi masa, haka nan yake jin nishad'i kamar kar su rabu. Buɗe motar ta yi tare da juyawa suka haɗa ido, lumshe idon ta tayi cikin wani salon sace zuciyar shi, amma sai tayi saurin kauda ido ta fice wai ita a dole mai kunya. Kallon kuwa ya daki zuciyar shi matuqa, amma sai shima ya kauda kai, nan take ya sa a ran shi itama qanwar shi ce ai inda kara. Sai da ta ga fitar shi a lungin sannan ta fara tafiya gida, a guje ta shige gidan ta ja hannun Ramai zuwa daki. Suna shiga tayi tsalle ta fada jikin ta tana murna,  Ramai baki sake take kallon ta, daga baya itama ta hau murmushi tana tambayar Jameelah ko lafiya take murna haka? Cikin farin ciki Jameelah ta ce, "Ramai daga yau na daina talla ki samu mai zubawa mazan nan abinci, sannan zan maida hankali na dinga iya hadda ta sosai ke har ta baya sai na tisa ta zauna a kwanya ta tasss, Ramai hijabai za ki nemo min na daina saka mayafai, sannan kema daga yau kina saka hijab in zaki fita girki, Ramai dole ne mu gyara indai muna son kuɗi da jin daɗi su zauna mana zama na har abada, in yaso a bayan fage kome muke son yi muyi abun mu,taho mazo Ramaitaaa duba nan ki gani," Kud'in data samo ta d'akko mata da ledar abincin da aka qullo mata, ta ajiye a gaban Ramai ta na kallon reaction ɗin ta,gefe ɗaya kuma ga ledar 'yan tsarabe tsaraben da Mum ta hada mata. Sake baki Ramai ta yi tana jinjina yawan kudin, ai wannan kud'in yafi kud'in hayan su na wajen watanni ma, dan kuwa a wata dubu ɗaya suke biya kudin d'aki d'ayan da suke ciki, da dari biyar ne ma daga baya aka qara dubu ɗayan. (Na san halin wasu makarantan da yanke hukunci akan rashin sanin abu, amma kuyi bincike dan Allah kafin ku ce ba d'aki a cikin garin kano da ake bada haya akan nera dari biyar tabbas akwai su wasu ma wallahi sai dai a hakura a bar su su zauna dan ba su iya ci da kan su ma balle su bada na hayar,wasu kuma sabo da jimawa da aka yi ana tare idan suka samu mai gidan na da kirki sai ya bar su su ci gaba da zama a kyauta musamman idan basu da shi, dan haka in Allah ya maki/ka ni'ima ka/ki gode masa, Allah ya bama kowa yanda zai yi a rayuwar shi) "Ina kk samo kuɗi masu yawa haka Jameelah? Zo nan na duba ki ban yarje maki kwanciya da kowanne qato ba Jameelah, ban qi ba idan irin soyayyar wannan zamanin da ake yi zakuyi ba a baki 'yan kud'in da za a baki, amma kwanciya da namiji inaaa ba zan taba yarda ba Jameelah, ban shirya karb'ar jikan waje ba dan uban ki, kar ki ga ina sake maki ki je ki d'akkon magana," "Dan Allah ni sake ni meye haka zaki wani hau ciren zani, ko kin manta da inda nace maki zani ne? Gidan su Umaimah na je fa, iyayen ta ne suka ban kudin nan kyauta da wannan abubuwan dika, wajen wane qato zani na kwanta a wnanan unguwar kaff ya ban wannan maqudan kudin? Ni bana son haka gaskiya Ramai," Washe baki Ramai tayi tana bawa Jameela hakuri, tare da buɗe ledojin da tazo da su, ta bude qamshin abinci mai daɗin gaske ne ya ziyarci hancin ta,gefe kuma ga lemuka kala-kala har guda hudu, dik da ba wasu manyan kwali da gora bane amma taji matsanancin daɗin ganin su. Nama ta ɗauka ta kai baki tare da lumshe ido, tabbas mutanen nan wataqila da inji suke dafa nasu abincin, saboda daɗin ba irin nasu bane. Zama tayi sosai ta fara ci kamar mayya, kud'in kuwa ta raba biyu ta bawa Jameela rabi  Jameela na ta bata labarin gidan su Umaimah da abubuwan da tayi a gidan na munafurci dan kar su gane asalin halin ta, sannan ta sanar da Ramai alqawarin Mum din Umaimah na son saka ta a makarantar Boko, "Nan fa ɗaya Jameelah kin san halin baban ki sarai ba zai bari ba, kin san yana da wani ra'ayi, na rashin son kowa yana yi masa abu da iyalan shi, yafi son yana komai da kan shi, yanzu dole mu fitar da dabarar da zai yarda ya amince da maganar, yanzu ya ki ke  ganin zamuyi?" "Barni da shi kedai Ramai, ki rage masa abincin nan ki daina tsince naman dan Allah Ramai," Cikin faɗa ta yi maganar qarshen kamar ta na magana da qanwar ta,ita kuwa Ramai cikin wata dariya ta ajiye sauranta na side hannu ta ce, "Bari na koma kan abincin nawa, ki shirya in kika saida na yau sai a yau ɗin na nemi mai zuba min, dole na rage dahuwa kuwa, dan na san masu siya zasu ragu,indai ba zuwa zaki na yi gefe  kina zama ba har a gama, kin san dai wasu dan ganin ki suke zuwa dama," "Kar ki damu Ramai ai saboda sanin halin mutane da gulma na faɗa masu muna saida abincin, zan na zama a wajen tunda wasu ba dan su kauda yunwar cikin su suke zuwa ba dan su kauda yunwar idanun su suke zuwa, amma fa dole na koyi yin hadda Ramai, dan kuwa sun dauke ni mai ilimi sosai da tarbiyya," A ranar dik suka gama wani sabon abu da suke son gabatarwa. Jameelah ta shiga kasuwa da nata kudin tayo hijabai sabbi, sannan ta amshi kudi wajen Ramai ta sai ma baban su sabon jug da mazubin abinci, da sabon zanin gado, Bukar ma ta sai masa kayan gwanjo

Chapter 4 of 30