ta ɗauka ta yi ma Ramai sallama Ramai sai jinjina kyau irin na d'iyar ta ta take yi kamar ba ita ta haife ta ba.
A mota ta gan shi zaune ya sha gayu da manyan kaya, ya yi kyau ainun matan layin su da 'yan biki kamar su janyo shi tsakiyar su tsabar yanda suke kallon shi duk ya qosa Jameelah ta fito su bar wajen, wanda suka san Mijin tane sai gulma suke yi suna fad'in, 'kyau da kyau an haɗu',wanda basu sani ba kuma sai suka hau tambayar waye shi, har ta zo qofa ta tina bata ma Mamalo magana ba ma tunda ta shiga gidan, da sauri ta koma ta ce mata Umar yazo zasu fita, in za a kai amarya zata zo.
Da wani irin taku ta fita kamar wata matar wani qusan a gwamnati sai wani hura hanci take yi,nan da nan kuwa ido ya koma kan ta har ta kusa isa wajen Umar ɗin da ya fita dan buɗe mata motar, ta na ganin haka ta sakar masa murmushi shima ya mayar mata, da ta shiga motar sai ya rufe ya zagaya ya shiga shima sallama ya yi ma samarin wajen sannan ya ja suka fice daga layin, wani ihun daɗi ta sake tana ta dariya,umar cikin murmushi ya kalle ta ya ce,
"Lafiya ki ke wannan ihun haka?"
"Yah Umar ka gama biyana yau, ka gama kashe gayun layin mu yau, kaga yanda kowa ke kallon mu,ka gama min komai Yah Umar,me kake so a duniyar nan na baka ko na yi maka dan kuwa ka fiddani kunya a lungun mu yau, kaiiii wani abu sai ma anjima a wajen kai amarya malam, har wasu kayan nazo da su dan sake kashe kala,"
Rage gudun motar shi yayi ya kalle ta ya ce mata,
"Kin tabbata komai nake so zaki yi min? Kuma kin yi alqawari?"
"Sosai ma na yi alqawari, in dai abun da ka ke so a waje na bai saɓawa addini ba zan yi maka shi, sab'on Allah ne kawai ba zan ba akan ka Yah Umar, amma indai ni Jameela ina da iko akan abu tambayi zan yi maka ko meye,"
"Kina ma da shi muje ki gani, zan faɗa maki me nake so,"
Wata hanya ya ɗauka da su wadda ta kula hanyar asibitin su ne da suka je rannan, me kuma za su sake yi a asibitin, tsoro ne ya kama ta kar dai allura za a sake yi mata yau ma a deb'i jinin ta?.....
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 17:
A k'ofar gidan nasu mai matuqar kyau da ɗaukan hankali ya ajiye motar shi,har ya buɗe mata qofar motar bata sani ba saboda yanda ta saki baki ta na kallon fasalin ginin gidan da ya tsaru ya gaji da kyau,sai da ya yi mata magana sannan ta fito tana ganin ya fara bude gidan ta fahimci inda Umar ya dosa da kawo ta wannan tsararren gidan dan ita ɗin dai kun san ba sabon hannu bace, amma saboda makirci irin na Jameelah sai ta daburce ta kalle shi a ɗan tsorace ta ce,
"Me muke yi anan kuma Yah Umar? wai ina ne ma nan ɗin?dan Allah ka maida ni gidan mu a kai amarya dani,"
Jikin ta har wani karkarwar munafunci yake yi,ganin haka sai Umar ya saki murmushin da bai kai zuci ba,a qasan ran shi yana tausaya mata ta bangarori da dama,labarin da ta bashi na fyad'en da aka yi mata ne ya bijiro masa ya qara dasa masa sabon tausayin ta a ran shi, sannan ga shi an aura masa ita har tsahon wasu shekarun bata san menene jin daɗin rayuwar auratayya ba, dole ne yau ya bata dikkan haqqin ta da yake a kan shi,dan kuwa Jameelah ta cancanci hakan a wajen shi.
Hannun ta ya kama ya shigar da ita gidan ya rufe gofar ba tare da ya yi tunanin sanya key ba, tsakar gidan ya yi bala'in ɗaukan hankalin ta har ta manta da me ke faruwa a wannan lokacin, madaidaicin gida ne ya sha adon fulawowi gefe da gefe da saman katangar gidan sun yi kore shar ga furanni nan sun fito jajaye da kalar pink,ga kuma wata babbar qofa ta shiga a salin cikin gidan wadda aka qawata ta da ado wajen gera ta, juyawa tayi ta kalli kitchen da toilet da ke tsakar gidan ta ga yanda aka yi su cikin tsari duk da cewa a rufe suke bata ga ciki ba ta yaba da fasalin su,a hankali ta taka ta murd'a handle ɗin ta leqa ta ga yanda cikin ya tsaru, murmushi ta saki a lokacin da Umar ya ke taya ta exploring gidan.
Nan da nan wani irin farin ciki ya lullube ta lallai wannan gidan dik da ba irin qaton nan bane ya yi mata matuqa gaya dan kuwa gida ne na ba raini daga wajen masu kuɗi har talakawan ma.
Koda suka shiga parlour baki ta saki ta na kallon ko ina da ko ina na wajen,komai an saka a parlourn banda kayan kallo, saboda ba a saka wuta ba a gidan, kujeru ne d'uma-d'uma masu numfashi irin royal chairs ɗin nan kalar blue dark da golden, carpet ɗin da aka malala musu kalar blue ne da adon flawowi baqi, ga manyan flower vase masu tsada da aka girke a parlourn sai frames masu kyau, qanqame hannun shi tayi shi kuma ya bita da kallo yana murmushi.
"Yah Umar dik wannan gidan na waye?"
"Gidan Jameelah da Umar da yaran da Jameelah za ta haifa wa Umar ne, ko baki san dama a ta nan area ɗin su Dad suka yi mana gini ba? Komai na gidannan mallakin mu ne da duk abinda za a karo anan gaba,dan kuwa kusan kullum Mum akwai abinda zata siya ta ajiye saboda mu,duk tanadin ta ita da Dad akanmu ne ni da Umaimah yanzu da an gama jan wuta a gidan da wasu gyare-gyare a kitchen da na ji tana magana akai zamu dawo ranar juma'a, kinga kafin nan sai mu riga su kawo kan mu, ko ya kika ce tawan?"
Ya qarasa maganar shi tare da kashe masa ido ɗaya ya na murza hannun ta a cikin nashi,cikin ran Jameelah kuwa ihu take ta na murna tare da ayyana,
'Wayyooo Allah na, Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana finally dai ɗan gidan Mummy zai karya alqawarin da ya yi wa Mummyn shi,waiii Allah na Jameelaa kin sha wahala, kin kuma yi qoqarin zama ba harka har na wannan tsahon lokacin mai tsaho na jinjina maki'
A zahiri kuwa sai ta fara matsawa baya ita a dole tsoro take ji, wasu marayun hawaye ta fara matsowa tana kad'a masa kai,cikin sigar lallashi Umar ya nufe ta ya na fad'in,
"Haba Love please kar ki yi min haka, ni fa mijin ki ne kar ki guje ni, in dai kina son ki halarci kai amarya ki bani had'in kai mu yi mu gama yanzu na maida ki da wuri, ga samun lada sannan ga shi ni da kaina zan kai ki kamar yanda kike so,"
Cikin ranta ta ce,
'U fool abinda nake jira kenan ka tsaya surutu,to wai surutun na meye kawai ka jani muje ciki, ko so kake na bika zoqal zoqal kamar wawuya'
Maqe kafad'a ta yi tana buga qafa irin na shagwab'ar nan wanda ta san dole ya sake jan ra'ayinsa gare ta, Jameelah ta san duk wani salon dake jefa maza cikin rud'ani, da ganin yanda ko ina na jikin ta ke motsawa Umar ya ja ta ciki, ni ko ganin idanun shi a tsaitsaye ba kunya ya sa na jira su a waje,tinda Jameelaah ma A-Z ce.
Na jima zaune ina jiran su, ga ba kayan kallo bare na kalla sai kawai na d'akko waya ta na fara Chatte wa da qawaye na na rai da rai, muna ta shewa a HAERMEEBRAEH NOVEL GROUP na ji bude qofar shiga gidan tare da fadin,
"Yauwa ku shigar da kayan cikin nan kitchen din, bari na duba shi na san wataqila ko daga Office ya shigo dan ya ɗan huta,ko gajen hakuri ne ya kawo shi gama kalle gidan yaje ya ba amaryar tashi labari,"
Ya zan yi ne? Shin zuwa zan na kira Umar nace a tashi haka daga....ko na bar Mum ta shiga ta yi gamo da kan ta?
Kafin na gama tunani na ashe Mum har ta shige sai ji nayi ta rafka salati an buga qofa da qarfin gaske, Mum dau ta shiga ta yi wa idanun ta mummunan gamo ta rufo musu qofar ta baro d'akin, cike da jin matsananciyar kunya ta dafe kan ta ta na salati,Umar ne sanye da gajeran wando ya na qoqarin sanya riga ya biyo sahun ta da sauri ya na kiran sunan ta, kafin ya iso Mum ta kora mutanen da suka zo tare da su waje.
Da sauri ya kama hannun ta ta tsaya cak ya kasa cewa komai saboda kunyar ta da ta mamaye shi,ita kan ta Mum kunyar ɗan nata ta gama baibaye ta, ina zata kai wannan kunyar da alhakin yaran da ta ɗauka na tsahon wannan lokacin? Gaskiya ta tafka babban kuskure na hana su kasancewa tare,yaran ma sun yi hakuri ainun kuma sun yi biyayya matuqa,dan haka ba zata ga laifin su ba sai ma dai ta ga laifin ta.
Cikin zubda hawaye Umar ya fara magana,
"Mum dan Allah ki yafe min ina tsananin buqayar iyalina kusa dani, kuma ban taba yi ba sai yau, ki yarda dani, ban taba yi ba sai yau, yau din ma bana nufin kwana a anan yanzu dama nake son mu koma na maida ta bikin qawar tata, bata da laifi sai da taqi ni na tursasa ta,"
"Umar Allah ya yi maku albarka, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba saliha kuma mumina, Allah ya baka masu yi maka biyayya fiye da yanda kamin a rayuwar ka, Umar baku min laifin komai ba, nice dai nake neman gafarar ku, saboda hana ku kasancewa a inuwa ɗaya da nayi, bayan kun halatta ga junan ku, ka yafe ni Umar, sannan ku yi zaman ku, zamu had'o maku sauran kayan ku da dik abinda ya dace, yau za a zo a ja wuta a gidan dama na riga na gama magana da masu haɗa wutar,dan haka a yau za a saka wutar da yardar Allah, Allah ya yi muku albarka,"
Dik maganar nan da take yi ta kasa haɗa idanu da ɗan nata kan ta na kallon waje take maganar nan, dan kunyar Umar da Jameelaah yanzu da take ji ko surukan ta bata jin kunyar su haka,da wanne ido zata sake kallon su? Ta shiga tagan su a tube? A manne da juna ɗan ta na qoqarin kaiwa ga buqatar shi? Wannan abu ba zai taba goguwa a zuciyar ta ba, da shi zata koma lahira tabbas, tayi dana sanin zuwan ta gidan a wannan lokacin, tayi dana sanin hana ɗan ta kasancewa da iyalin shi tun farko da bata yi wannan mummunan gamon ba, aure nawa aka yi shi ana karatu har aka haihu lafiya ? Aure nawa aka yi yarinya na da qarancin shekarun Jameelah kuma ta haihu lafiya? Tabbas bata yi lissafi ba, bata yi dogon nazari ba kafin yanke hukunci a baya, yanzu gashi ta jawowa kan ta ganin abinda ba zai gogu a kwanyar ta ba har abada.
Jameelaa da ta gama jin komai tayi tsallen murna ta faɗa gadon ta ta yi birgima ta sake yin birgima, da kuwa dik ranta a b'ace yake da zuwan Mum ɗin ta katse masu jin daɗin su, tin da take bata taɓa sanin haka rayuwar aure take da daɗi ba,ashe rayuwar zina bata da wani armashi shaid'an ne kawai ke qayata masu ita,rayuwar zina ana yin ta ne komai babu nutsuwa ba sakewa ga uwar fargabar kar a kama mutum, gwanda da aka basu damar kasancewa tare,tashi ta yi ta leqa su ta ga yanda suke ta tattaunawa Umar ya saki ran shi daga tashin hankalin da ya shiga da fari,ta nanan tsaye a bakin kofar ta ji sun fara sallama Mum za ta tafi,cikin sauri ta bar bakin qofar ta koma ciki ta zauna a bakin gado ta hau kukan munafurci.
Umar ya dad'e zaune a parlour kafin ya iya shiga d'akin, kunyar Jameelan yake ji sosai Mum din shi ta gan ta a yanayin da ko Mahaifiyar ta bai kamata ta gan ta a ciki ba kuma shi ne silar faruwar hakan, a hankali ya qarasa gaban ta ya durqusa a saman guiwowin sa tare da kama hannayen ta ya ce,
"My love dan Allah dan son Annabi ki yafewa Mum d'ina, kiyi hakuri ki yafe min nima, ni na janyo maki wannan abun kunyar, na san zaki dad'e kina jin kunyar Mum saboda yanda ta ganmu, amma ba zamu koma ba har sai sanda kika ji zaki iya zuwa gidan,"
Da sauri ta faɗa jikin shi tana kukan qarya tare da goga dikkan jikin ta a nashi, Umar kasa daurewa yayi suka koma ruwa.
Jameelaah ta hana Umar sakat a ranar kuma taqi ta nuna masa da gayya take nane masa,komai take yi cikin taka tsantsan takeyi da dabara yanda ba zai fahimci ita ke son abun ba.
Shi ko ya ɗauka naturally haka mata suke jikin su na qara sa namiji jin sha'awa ko da bai yi niyya ba.
A ranar dai Jameelaa bata je kai amarya ba a gidan su suka yi zaman su, masu gyaran wuta sun zo bayan la'asar lokacin su kuma suna sallah, dan sun makara yin azahar.
Bayan sun idar aka fara sanya masu abubuwan da suka dace, daukan ta yayi suka tafi siyan abinci, dan kuwa tace masa yunwa ta ke ji sosai.
Umar jin shi yake kamar a yau aka d'aura masa aure, koda suka je wajen siyan abincin farfesun kaji tace a siyo, sannan a siyo gasasshen nama irin mai ruwa-ruwan nan, daga nan suka sa yi freshyo da fruits masu yawa,shi kuwa harda tuwo ya siya dan ya saba cin tuwo da dare.
Gida suka koma a d'aki suka zauna har an gama da master bedroom , d'akin yayi kyau sosai hasken wutar kalar blue mai duhu da haske aka sanya masu,sai AC da fan dik an kunna dan su tabbatar suna yi, sanyin yayi yawa dan haka Umar ya kashe fan din ya rage sanyin ACn, suka zauna suka fara cin abincin, ya yi mamakin ganin yawan abincin da Jameelaa ta ci, dan kuwa ta tashi da kaza ɗaya tass ita ɗayan ta sannan ta qara da naman, ga fruits da ta sha sosai suma, gyatsa tayi ta jingina da gado, suna haɗa ido da Umar ta sauke nata idon dan tsabar kunya da ta kamata, turo baki tayi sannan tace,
"Yah umar dole fa naci abinci sosai kasan ka wahalar dani ba kaɗan ba, ba zaka gane irin yasar da naji anyi min a cikina ba,"
Dariya suka yi a tare masu sanya wuta sai bayan magrib suka kammala suka tafi, ya so ya sallame su suka tabbatar masa da Mum ta biya komai, duk da haka bai barsu haka ba sai da ya basu wani abu na ihsani suka yi masa godiya sosai suka tafi.
Umar wanka ya sake yi sannan yace bari ya ɗan leqa asibiti yanzu zai dawo, qanqame shi tayi wai ita tsoro take ji,ya kula da hakan dan kuwa da gaske tsoro take ji bata saba zama gida ita ɗaya ba, to mutumin da ya taso a gidan yawa? Gashi kuma gidan sabo ne,hawaye ya ga ta na zubarwa dan haka sai ya kama ta suka zauna ya ce mata,
"Jameelaa bari na faɗa maki gaskiyar inda zan je yanzu, dama zan dan leqa asibiti ne akwai wani yaro dani nake kula da shi ya karye a qafa, mummunar karaya yaron ya yi kuma yaron basu da hali, nakan kai masu abinci da dai abinda suke da buqata haka sannan daga nan zanje gida na d'akko maki uniform ɗin ki saboda gobe akwai makaranta ko kuwa har kin manta da makaranta?"
"Yah Umar ni dai muje tare ba zan iya zama ni kaɗai ba,"
"Zaki iya ganin Mum ba matsala?"
"Ai ba sai na shiga ba, ni dai ba zan zauna ni ɗaya ba,"
Haka Umar ya sa ta a gaba suka tafi yana ta tsokanar ta tare da kiran ta matsoraciya,sun tafi asibiti kenan Umaimah da mai aikin Mum suka je gidan dan kai kayan su musamman na sawa da na toilet suka tarar da gidan a kulle, mota suka koma ta dakko waya ta kira Umar ta sanar dashi zuwan su, sanar da ita ya yi su ɗan jira yanzu zai juyo ya dawo, sun ɗan fita ne,a tsorace Jameelah ta ce,
"Yah Umar wacece ta je gidan, na shiga uku na ni Jameelah Mum ce?"
"Ba ita bace Umaimah ce ta je kuma kaya suka kawo mana, sun hutar damu shan kunya"
Koda suka koma Jameelaa ta sha tsokana wajen su Umaimah, haɗuwa suka yi da me aikin Mum suna ta tsokanar ta wai amarya ta gudu d'akin miji ba 'yan rakiya,ita kuma ta yi ta shagwab'a, Umar kuma ya hau yi ma Umaimah faɗa akan ta kyale masa matar shi kar ta takura mata.
Cikin raha da nishad'i suka rabu, a ranar umar dai bai samu zuwa asibiti ba, sai wani abokin aikin shi ya bawa saqon yin komai.
Washegari da safe bayan sun yi sallah da asuba sun shirya dan fita malama Jameelaah da kyar ta kyale Umar dan kuwa dik ta wani maqalqale shi, Umar kuwa sai wani lallab'a ta yake yi yana matuqar qara jin son ta da wani shauqin kasancewa da ita na qara shigar shi, ji yayi kamar ma ta ajiye karatun ya isa haka, wani irin kishin ta yake ji fiye da da, anya ba daga secondary zata aje karatun nasaran nan ba kuwa? Tinda ta na da na muhammadiyya dai-dai gwargwado.
***********************
Zaune ya ke a d'akin shi tunanin duniya ya dame shi, yau Yah Ishaaq yayi tafiya zuwa Dubai dan shigo da wasu sabbin dogayen riguna da ake yayi.
Waya ya d'akko ya kira No shi da yake amfani da ita a can.
Sai da ta katse ba a d'aga ba, furzar da iskar bakin shi yayi sannan ya shafi gefen sajen shi, kira ne ya shigo, da sauri hannu na masa rawa ya dauka.
"Hello qanina har ka fara missing d'ina ne? Dan da alama lissafa awanni kake ta yi shi yasa ka daidaici lokacin da na sauka ka kira ni,"
Ɗan murmushi Haroon yayi mai sauti sannan yace,
"Ina fatan ka isa lafiya Yayana?"
"Lafiya qlaou muka sauka alhamdulillah, akwai damuwa ne naji yanayin ka wani iri?"
"Yah gaskiya ni dai yau na saddaqar ina son Umaimah, Yah Ina matuqar son ta, qirji na har wani zafi yake yi min da nauyi yau na rasa dalilin faruwar hakan Yah dan Allah ka yi ka dawo ka nema min auren ta kar na mutu, ban san haka so yake ba, a da na zaci shaquwa ce kawai a tsakanin mu, dan Allah Yah ka yi ka dawo, kar a bawa wani ita, zan iya mutuwa idan na rasa ta,"
Hawaye ke zuba a idon Haroon kamar wanda aka ce masa Umaimah tayi sabon saurayi za a d'aura masu aure a yau ɗin.
Ishaaq tsayawa ya yi tsak ya dena tafiyar da yake yi a lokacin da ake duba shi dan fita daga filin jirgin,tunda yake bai taɓa jin qanin shi a cikin wannan halin ba, kuma da alama kuka ma yake yi.
Ji yayi zai iya aje komai ya koma dan biyan buqatar qanin nashi, dan haka yace,
"Haroon kar ka damu, ka ban kwana uku zan dawo zan je kuma na nema maka auren Umaimah, kuma zan mallaka maka in da zaka zauna da ita kuyi rayuwar aure inshaa Allahu, ka daina kuka ka ji qanina, haba namijin duniya, ban taba zaton mace zata karya maka zuciya da izza irin haka ba,"
"Kaiii Yaya ba wata izza da mazantaka, kawai sai ka dawo din,Allah ya bada sa'a ya sa ka dawo lafiya,"
Dariya sosai Ishaaq yayi, yaro kenan da baka san mene ne soyayya ba, yanzu ka san ta ka gane ya ake ji a cikin ta.
Kiran Hauwaa Ishaq yayi yace ta kula da Haroon, yana buqatar kulawa a yanzu haka, ai kuwa tayi masa alqawarin kula da Haroon din cikin wani yanayin da shi bai fahimta ba .
Suna gama wayar ta ɗauki turarukan ta ta fesa a dik inda ya kamata, sannan ta cire komai na jikin ta ta saka qaton hijab, fita tayi dan zuwa wajen Haroon, tinda yayan shi ya bata Umarnin kula da shi, za kuwa ta kula da shi ainun..........................
*Casssssssss, hope u like this page? dan ni dai i no like am, ya ni b'arin hannu*
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 19:
Sallamar Ramai ce ta daki kunnuwan su Umar ne ya isa ya qarasa buɗe mata qofar ta shiga, kwance Jameelaa take ko motsawa bata yi ba daga inda take.
"Ke lafiya na gan ki kwance haka? Ince dai ba wata matsalar bace,"
Tana magana tana harar Umar kamar ta na zargin shi da ci mata zalin 'ya.
Da sauri kuwa ya buɗe baki dan kare kan shi, amma Jameelaa ta katse shi ta hanyar cewa,
"Wuce kaje ka qarasa abinda kake yi,"
"To"
Yace ya na dauk'ar da kai ƙasa,dan kuwa ya so ya kare kan shi wajen surukar ta shi,
"Ramai na faɗa maki kar ki dinga shiga lamarin mu, ina ruwan ki zaki na tuhumar shi kamar ya maki sata? Ni ba abinda ya yi min kaina ke ciwo, kuma Ramai yaushe yaushe muka dawo gidannan, amma kusan kullum sai kin zo,"
Juyawa ta yi tana murgud'a baki da fari da ido, ranta a mugun bace,
"Dan uban ki da ba na zuwan zaki samu maganin da zaki maida mijin naki haka? Ko uban ki ban taɓa nemawa maganin mallaka ba sai ke,saboda uban naki bai tara abinda zan mallake shin ba, ya ji da talaucin shi ma, kin samu ina kawo maki ne bari na koma da wanda na zo naga ɗan iskan da zai na kawo maki,"
Da sauri Jameelaa ta cafke hannun Ramai ta kwanta a jikin ta, tana dariya ta ce,
"Habaaa Ramai na, kin san idan bana jin daɗi dama haka nake masifa, dan Allah ki yi hakuri kawo na gani,"
"'Yar kwal uba kai, hanni zaki nunawa kin yi kud'in da ba zan zo gidan ki ba? Innai niyya ke kan ki sai na mallake ki naga ta tsiya,"
"Haba Ramaiinaaa bai kai na haka ba, muga wannan miqo min na fara amfani da shi, kin san shi da yawan ibada, sai abun ya damqe shi anjima kuma ki ji ya fara lalacewa,"
"Matsalar da malam (malamin dhibbu) yace kenan yana fama da ita akan wannan tattauran mijin naki, shi bai da aiki sai karya masa sihiri, ina kyautata zaton fa wannan biyayyar da yake maki ba wai naganin kaɗai ke aiki ba dan dai kawai yana son ki ne, amma ba dan sihirin mu ya kama shi da kyau ba,"
"Koh?"
"K'warai kuwa, yanzu dai kawon abinci na ci na ɗan sha jusi na tafi sannan ki ɗan haɗan kayan abinci, na gida ya kusan qarewa,"
"Ramaiii hooo,ba wani qarewa wannan uban abincin da kika kwasa shekaran jiya ne za a ce ya kusan qarewa? Ai na san zai kai ku sati ma aci a wadace,ke dai kawai ki ce sai kin sake diban wani,"
" 'Yannema mai kan kwando je ki deb'o kawai bar tone-tone"
"Yah Umarr ! Yah Umarr !"
"Na'am my love,"
"Dan Allah zuba mana abincin nan yunwaa nake ji,kaga ga Mamana ma tazo,"
"Na gama zubawa ma, dama naga kuna ta hira ne shi yasa ban yi magana ba,"
Da sauri ya tafi yaje ya kawo abincin a babban faranti da lemu da cups da dik wani abu da zasu buqata dai ya ajiye masu ya koma kitchen, a tsaye ya cinye nashi ya dau jaka dan komawa bakin aikin shi, kuɗi masu ɗan kauri ya miqawa Ramai, Jameelaa ta amshe ta raka shi, a hanyar dawowa ta rage wani ta soke, Ramai da tinda suka fita take leqen ta, ta kasa hango wajen saboda window irin na glass ɗin nan ne kuma rufe yake da labule jibga jibga ga kujera ta rufe ta dai-dai wajen ta kasa janyewa, ido ya sha
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 30