rantse, tinda kaga na taso na zo nan kasan na kai qarshe wajen tijara nima, kawai kome za a yi ayi ni dai na mallaki mijina ni ɗaya shine fatana, ko uwar shi ce a raba shi da ita, ya zama ni ɗaya ce a zuciyar shi,"
"Angamaaa indai zaki iya yin komai aka ce kiyi, kin aminceee????"
"Na amince"
"Kaii dan rakiya jeka daga waje za a yi mata aiki, Takan Tsamiya zata kira mazajen aljanu na Nijer su yi mata aiki, je ka wajeeee jeka wajeeee....za dai ki iya jure aikin aljanuuuu kooo?"
"Ni wai sau nawa zan ce maka zan iya ne, kaiii je ka waje ayi a min aikin nan na koma gida kar mijina ya koma yaga bana nan,"
Da sauri kuwa mai a daidaita ya shiga adaidaitan shi yana fita bokan qarya ya miqe yana rawa yana surkulle, dan abin wasa ya bama Humairah, sannan ya dau wani ruwa a cup ya bata, maganin bacci ne mai qarfi a ciki, nan da nan kuwa ba a jima ba ta bingire, Jameelaa ta tsora ta hau kuka tana tambayar me ya ba ma 'yar ta,
"Magani ne na kariya daga sihiri dan kuwa 'yar ki an mata mummunan asiri, ita da ya sake ta sai nan da kwana daya, karki damu, tub'e maza aljanu su fara aiki akan ki lokaci na tafiya, suna tsaye suna jiraaaaa, suna da aiki a wani wajen"
Wani ruwa ne a bokiti zundumeme, ya dinga yafita a cup yana fesa mata, sai qoqarin kare qirijin ta take yi, amma kun dai san Jameelaa da manyan halittar qirji ba za su karu da hannun ta ba, hakan da tai na dago su sama ne ya sa ya sake fad'awa cikin sha'awar ta, wata yar qara ya saka ya fara jijjiga yana surkulle,shi a dole aljanu sun shige shi zai yi mata aiki,
"Dauki ki shaaa... daukiii ... daukiiii shanyeee, mummunan sihiri aka maki maza shanyeeee"
Aiko cikin sauri ta shanye ta side cup din saboda zaqi zaqin da taji a ciki,
Nan ta fara ganin duhu a hankali ta kwanta bacci, ai kuwa Leqawa yayi ya kira abokin shi, su ka rufe qofa, nan sukai ta hawan Jameelaa wannan yayi ya bawa wannan tsabar ganin banza da arhar ta.
Bayan sun kammala ne suka ta shi suka gyara jikin su, suka maida ita gefe suka lulluba mata zani, tsaf suka gyara ta kamar ba abinda ya faru, suka manna mata Humairah a jikin ta, ɗan rakiya ya ce shi ya ware zai je yayi sana'ar shi, shi kuwa d'ayan ya tsaya a bakin shagon yana zuqar sigari, daga baya ya kulle ya shiga gida, ya samu an gama abincin rana yaci ya qoshi ya fice.
Bashi ya dawo ba sai bayan la'asar, yana isa shagon ya buɗe, Jameelaa na nan kwance ruwan gishiri da lemon tsami ya d'ura mata ai kuwa cikin minti uku ta fara tari tana kakarin amai, amai tai ta kelayawa na ruwa zallah da wani yalo-yalo a aman saboda ba abinci cikin ta ko karyawa batai ba ta fito yawan gantali.
Sai da tai amai ta gode Allah yana zaune yana ta surutai na surkulle,
"Da kyauuuu... aiki yayi kyauuu, aljanu sun yaba aikin da suka yi maki, kije gida ba ke ba zancen kishiya, balle takurawa ta uwar miji,"
Jikin ta taji yana wani irin wari mara daɗi kamar warin jikin maza, sannan can qasan ta kamar an sadu sa ita ganin kayan ta tsaf a jikin ta kuma an rufe ta kif ya sa ta amince wataqila aikin da aljanun suka yi mata ne yasa take jin haka dama ance maza ne.
Kuɗi ta zaro tace ga abin sadaka na aljanu, a yi musu yanka, nan da nan ya daka mata tsawa yace,
"Keeee ! aje cannnn kusa da aljanar kan Tsamiya, kar ki nufo ni da kuɗiiiii,bana soooo, bana soooo,"
Can kusa da wata kwarya ta ajiye ta goya Humairah ta fita, saida ta fita ta fara tinanin nan ina ne? Ina zata ce a kai ta? Ohhh yau yawon neman biyan buqata ya kaita dare dan kuwa har biyar na yamma ta gota, yanzu tasan a yanda cunkoson hanyar garin kano yake da yamma sai ta kai magrib kan taje gida.
Wani kid'imammen tsoro ne ya shige ta dan tunawa da me Umar zai ce idan yasan bata gidan su kuma bata je gidan iyayen shi ba? Cannn ta buga murmushi sannan tace,
"An mallaka min kai Umar na san yanzu sai yanda nace kayi zaka yi, Allah ka kaini gida yau na ga tasirin wannan magani,"
Tambayar wani yaro tayi tace masa meye sunan unguwar nan ya faɗa mata cikin tsoro ta dafe qirji, tabb ai sai isha'i kan taje gida yau, kallon inda ta fito tayi, ta ga wajen ba wuyar ganewa, da ta ji duku-duku kan Umar ya ɗan warware zata dawo.
Da kyar ta samu mai taxi ta hau aka kai ta unguwar su, cikin fargaba ta shiga gida, Umar baya nan ya bazama neman ta, kulu ta yi jigum dan yau ta sha faɗa wajen Umar da ko sunan ta baya iya kira, amma ya zarge ta da sakacin bar masa mata ta fita,
Tana shiga ta fara kuka ta zube a qasan tsakar gidan, sai kuka take harda majina da sauri Kulu ta latsa yar qwabirar wayar ta ta kira Umar, tace masa gata ta dawo.
Wani irin burki ya ja ya juya ya kama hanyar gidan su ,dan da ya nufi gidan su Jameelaa ne a karo na uku dan ya ji ko ta koma can daga duk inda ma ta je, tunda Ramai ta yi hatsarin nan ya gano akwai su da son satar fita ita da uwar ta, bai dai taɓa ba abun mahimmanci bane kuma bai zaci Jameelaah zata yi masa haka ba.
Da sauri ya fice ya rufe marfin motar ya shiga gidan da kukan Jameelaa ya fara cin karo, riqe da Humaira a hannu ta tana ganin shi ta sake zunduma ihu,a guje ya zube a gaban ta yana faɗin,
"My love me ya same ku haka? Kin gan ki kuwa? Kinga yanda kika koma a wuni ɗaya kuwa?"
"Umar ka yafe min yau na ga tashin hankali, dik dan akan karna takura maka, "
"Menene ya faru ne ki yi min bayani? ki gaggauta sanar dani, me yasami Humairah naga bata motsi,"
"Tin da ka fita ta fara kuka jikin ta zafi rau ta qi karbar nono, shine....shine...shineee nace ba zan takura maka ba ka fita aiki, bari na kai ta asibiti, shine adaidaita sahun da ya ɗauke mu ya ga taqi daina kuka, sai ya bamu ruwa a roba yace na bata ko qishi ta ke ji, ina bata kuwa ta amsa nima na sha, tin daga nan muka fara bacci,bamu tashi ba sai a wani daji,.....ya duba ya ga ban da kuɗi, ya mammare ni ya maido mu ya yasar ya guduuuu"
Kuka sosai take ta yi kamar ranta zai fice duk wanda ya ga yanda take kukan nan sai tsoron Allah ya kama shi ya tabbatar da abinda Allah ya faɗi na Innakaidakunna azeem,da sauri Umar ya ɗauke su ya wuce mota dan kaisu asibitu aga lafiyar su dika.
Kulu mamaki ya hana ta motsawa daga inda take dan kuwa tana ganin sanda Jameelaa tayi murmushin mugunta, tabi bayan umar tare da dan tsallen samun nasara, sannan ta ga sanda ta fita da safe lafiya lafiya ta bar gidan amma ta zabga qarya irin wannan anyaaaa????
A asibiti bayan an ɗauki jinin su da ita da Humairah an tabbatar ma da Umar sun sha maganin bacci ne, Umar kuka ya sanya ya qanqame Jameelaah saboda ya tabbata ta wahala ita da yarinyar su, itan ma kukan take amma mamaki fal ran ta, me zai sa a ga maganin bacci a jinin su? Bayan aikin karya sihiri aka yi masu????????
*Jameelaa ina zan sani? Tambayi bokan ki dame ya haɗa maganin*
[08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 35:
Karawa tayi a kunne tare da yin sallama cikin sauri tace,
"Bata kusa ka kira ta anjima.
Kit ta kashe wayar dan ko jiran ya amsa sallamar bata yi ba ma.
Sake kira yayi ta sake d'agawa tace,
"Nace bat..."
"Haba 'yanmata ai kin jira ma na amsa sallamar ki kafin ki katse ko amma ki ka yi saurin katsewa ke a dole gaki 'yar isar da saqo ko?.... wait a minute wai Sapnah ce?"
"Ohhh ni Sapnah gaskiya ka fini surutu,eh Sapnah ce,"
Dariya yayi sosai sannan yace,
"Tabbb na fiki surutu a ina? Muna dai da surutu ni da ke da ace gida ɗaya muke sai mun d'aga rufin gidan da surutun mu"
Wani iri ta ji a jikin ta dama ace maganar shi ta tabbata ba rufi ba ko katangar gidan ce ta zube ba komai in dai tana tare da shi.
"Ya ki kai shiru ne ko yau 'yan maganar basu kusa ne?"
"Ammm ba komai kasan akwai gajiyar suna da aka yi, kuma ka kyauta baka bamu aron matar ka tazo mana suna ba,"
"Ya salam...gaba ɗaya na manta anyi sunan, kuma baku tunamin ba shiyasa,"
"Ta ina zan tuna maka baka da no ta ban da taka?"
"Haka ne kuma fadon min No ki yanzu na maka su a wayata in case ko za a gayyace mu wani abun,"
"Ehhh zamu gayyace ku sunan Umaimah mana,"
"Dan Allah da ta fara naquda ki kira ni ai kar ki bari a ma kai ga haihuwa, in ta haihu banga naqudar auta ba ke zan kama,"
Sassauta murya tai cikin wani irin salon saye zuciya sannan tace,
"In ka kama ni mi zaka min to?"
Shiru yayi yana jin muryar ta na tsaga dikkan wani sashe na jikin shi tana shigewa tana kwanciya, kuma da dikkan alama wannan magana ta shige kenan har abada, a hankali shima ya furta,
"Inna kama ki zan....."
"Amshi wayar ki wannan yayan naki sarkin surutu yana ta kiran ki na taimaka na ɗauka, gashi ku ci gaba da hirar ku zan je gida,"
Amsa Umaimah tayi ta yi sallama suka fara gaisawa,
"Yah Umar lafiya na ji ka haka? Duk sai naji muryar ka dik a sake, ko dai wani abu ne ya faru? Wayyoo Yah Umar me ya faru sanar da ni,"
Sai da ta faɗi haka ya farfaɗo daga suman da Sapnah ta sa shi yi a zaune,
"Ke ke dakata kwantar da hankalin ki ba komai, ba abinda ya faru jikina ne kawai a mace, ina office na ce bari na kira na ji ya kike? Dan ina son na dinga jin ya kike har Allah ya nuna mana kin sauka lafiya, Allah ya raya mana abinda ke cikin ki dake kan ki sai anjima qanwata ina son ki,"
"Na gode Yah Umar da kulawar ka, baka gajiya wajen jin lafiya ta, ina son ka nima fiye da yanda kake so na, Allah ya bada sa'a ya sauqaqa gajiyar aiki,"
"Ameen bye"
"Bye"
Suna gama waya da Umar, wayar Haroon ta shiga wayarta,cikin murmushi ta furta,
"Masoya na kenan,"
Cike da fara'a ta daga wayar tayi masa sallama ya amsa,
"Gaskiya kai da Yah Umar kuna ji da ni sosai dole ne na yi maku kyauta na ga alama,dik wanda na kula yafi ji dani zan bashi kyauta mai tsoka, ba tare dana faɗa ma wani a cikin ku ba,"
"Haka kika ce? Inshaa Allah ni zan ci kyautar nan, amma sai dai a barni na zaɓi me za a bani,"
"Waaaayoooo, ni fa nace zan bada kyautar sannan kai zaka zaba?"
"Ehhh ni zan zab'a mana kuma dole abani dik abinda nake so, indai an yarda in ba a yarda ba to a bar wannan kyautar,"
"Na amince to,ina fatan ka isa kasuwa lafiya?"
"Lafiya qlou Mahboobatee, ya unborn dinmu? Ya jikin ki?"
"Lafiya qlou muke sai dai ni fa bayana na dan yi min ciwo,yanzu sapnah ta kawon ma naman kai naci, ina ta murna naci amma sai da nai amai bayan na gama, ni dai gaskiya na gaji da aman nan"
"Subhanallahi ! kar kice haka lada ne kike samu, kar ki manta a dik sanda bawa ya shiga cikin halin qunci Allah yana bashi lada, balle uwa dake ɗauke da ciki,ki qara hakuri kinji? Lokaci na nan zuwa da zaki daina aman,"
"Allah ya kaimu lokacin Mahboob, na gode da kulawar ka a gareni, Allah ya bada sa'a, Allah ya haɗa ku da halal komai qanqantarta, ya kare ku daga haram,komai yawan ta, Allah ya dawo min da kai lafiya, Allah ya sa in 'yan mata sun zo shago siyan kaya kar su gan ka suga Yah Ishaaq shi ɗaya,"
Dariya ya dinga yi kamar kullum in ta yi irin addu'ar nan, sannan ya dan haɗe fuska yace,
"Kashhh network ba kyau bana jin ki sosai me kika ce ne a qarshe? Saqo kike bawa Yah Ishaaq ko me? Ni ban ji ba sosai,"
Cikin wauta da rashin sani ta sake maimaitawa,
"Ba saqo na bashi ba addu'a nayi, nace Allah
ya sa in 'yan mata sun zo siyen kaya kar su gan ka, suga Yah Ishaaq"
"Tabbb di jamm, amma kuwa Umaimah sai na hada ki da Hauwaa, dama addu'ar son kai kike ma na? To kuwa.....
Dif Ishaaq yaji wayar ta katse ya kalla ya yi murmushi ya miqawa qanin na shi dake ta kwasar dariya,
"Ashe addu'ar mugunta akewa Hauwaa ko, kamar a kunnen ta kuwa"
"Dan Allah ka rufa mana asiri, wasa muke maku, habaa ai daga kan ta babu qari,"
"Za dai kuji sammaci daga kotun Hawaa'u Autar mata"
Haka sukai ta nishad'i abun su suna gudanar da kasuwancin su, har Ishaaq in ya tina da maganar da Umaimah ta yi sai ya yi murmushi saboda ya ji yanda ta tsorata da ta ji muryar shi.
Sai yamma da suka kusan dawowa Umaimah ta yi wa Haroon message,
*Ni kaiwa haka ko? Zaka dawo ka sameni, sai dai Yah Ishaaq din ya rako ka, amma yau ni da kai ne a gidannan i love u my Mahboob.*
Dariya yayi tayi Umaimah salon ta na bashi dad'i sosai shi yasa yake sake jin qaunar ta a koda yaushe, in ya fita zata kira shi ta ji ya isa lafiya? Ko shi ya kira yaji ya take in ita taita kira bai kira ba bata fushi bata qorafi uziri take ba shi akan maybe aiki ne ko karatu ne suka riqe shi.
In kuma sukai waya sai ta faɗa masa abinda zai ta tinawa mai daɗi, ko ta bashi dariya.
In ya kusan shiga gida zata masa message din addu'ar komawa lafiya mai daɗi, ko kuma in yayi laifi ta masa irin na ɗazu,wanda zai ji ya ma matsu ya koma ta hukunta shi ɗin.
Haka rayuwar Umaimah da Haroon take abar so abar kwatance ga kowa, bata raina abinda ya bata sannan bata sanya ido a abinda yake dashi, kuma bata taɓa roqon shi wani abu, sai abinda zai amfane su dika, buqatar ta ta danne ta har sai ya kula ya yi mata tunda bata rasa ci da sha da sutura ba balle wajen zama mai kyau, in bai mata ba bata damuwa dan ta san ba ita ta bashi ajiya ba, kyautatawa ne dama a tsakanin miji da mata,a ranta takan ce in tana son abu zata nema da kud'in ta ko ta yi kasuwanci itama ta ji daɗin cin kud'in ta, amma ba zata yarda da roqar miji ba har tin yanayi yaga dan kud'in shi take zaune da shi, duk abinda bai zama dole wajibun ba bata tambayar shi.
A kullum Haroon godewa Allah yake yi akan samun Umaimah da yayi a matsayin matar da ya aura, tindaga sanda ya fara son ta ta sauya masa tinani, gashi yanzu yana makaranta ya kusan kammalawa, ya samu ilimin sake haɓaka masu kasuwancin su, yanzu haka yafi Ishaaq ilimin kasuwanci na zamani.
Kasuwancin su ya bunqasa kwarai da gaske abun nasu ya zama sai godiya ga Allah, cikin kasuwa da cikin gari yanzu kusan dik an sassansu, da wahala ka haɗu da wanda bai san shagunan su ba.
Shi dai bai taɓa fita waje bane, yace ma Ishaaq sai ya kammala karatu ya amshi kwalin shi a hannu, zai tsindima cikin kasuwancin sosai.
***********************
Umar na fita ta goyi Humairah ko wanka basu yi ba ta fice itama, maqudan kuɗin dake hannun ta wanda ta tara a wannan satin ta qara matsewa a jakar ta, Humairah na ta tsala kuka, dan kuwa yunwa take ji sosai yanzu an fara bata abincin yara nono baya isar ta, balle ma yau ko na safe ba a bata ba.
Burin Jameelaah bai wuce tagan su gaban boka ba yau, dan ayi komai kwaf ɗaya a raba Umar da kowacce mace koda kuwa Mum ce bata damu ba, akan ya yi mata kishiya.
Sai da ta sai k'wai da bread da madara da milo sugar da butter sannan ta wuce a adaidata sahun da ta ke ciki, a gefen qofar gidan su ya aje ta tace ya tsaya zai kaisu unguwa, zata biya ko nawa ne wayar ta ta duba taga takwas ta gota kusan da rabi, ta tabbata baban ta baya nan sai ta faɗa gidan.
Tin daga soron gidan taga sauyi gidan ya yi fess qall ko ta ina, ga shi sai tashin qamshin turaren wuta dan tsinke yake yi.
'Sabon salo, kodai Umar ya sama masu mai aiki ne suma?'
Sallama ta rabka Ramai ta fito ta amsa, ba wata kwalliya tayi ba amma ba had'in gambiza yanzu sannan kayan ba mugun datti kamar da.
"Ramai lafiya kuwa Naga dik gidan ya sauya,me aiki umar ya sama maku?"
"Nice nan me aikin kaina shigo daga ciki,"
"Ni kam kinga ba shigowa zan yi ba, ga waɗannan na ɗan siyo maku na san zai dan maku ko sati ne haka a sa mana albarka, zuwa na yi ki raka ni wajen bokan nan, mai adaidaita sahu yana jirana, dan Allah ki yi sauri,"
"Jameelaah ni nan da ki ka ganni na tuba nabi Allah,Allah shine mai biyan buqatun bayin shi ba boka ko malam ba ko mai duba, Allah shine ya basu damar ganin komai da aiwatar da komai, dan ya masu talala, talalar ubangiji bata da daɗi in bawa ya faɗa cikin ta, ki kiyayi Allah Jameelaah, ni dai na kiyaye shi ina fatan ya kare ni daga komawa zunibin da na bari a baya, na maki alqawarin dik abinda ya dame ki zan maki addu'a ke sai nai azumin nafila ma dan buqatar ki ta biya sannan na kwana sallar dare, amma ba zan sake kai ki gidan boka ba balle muje tare ina maki nasiha da ki zubar da makaman yaqin ki na zuwa wajen bokaye macuta masu cin kud'in mata a banza kuma su kai su wuta a wofi,"
Baki sake Jameelaa ke kallon Ramai anyaaa kuwa Ramai ce?
"Kinga Ramai ana jirana na gode da nasihar ki, bai san na fito ba sai na nemi izinin shi zan dawo ki min nasihar sosai,"
Ramai ta ji dad'in yanda tashi ɗaya Jameelaa ta amshi shawarar ta, nan ta fita ta haye adaidaita sahu, Humairah har ta gaji tayi bacci, masifa ta dinga yi tana faɗin
"Tinda ke ba za a maki kishiya ba ai kince haka mana, taya za ai ma na zauna ban nemi taimako wajen bokaye ba, ke ni in bori aka ce na hau akan Umar sai na hau shi, keki ka ga zaki daina zuwa wajen boka ni banga hakan ba, daman ban fara ba ke keki ka koyamin sannan yanzu kice kin janye ina tsaka da neman biyan buqata? ba zata sab'u ba,"
"Ammm malama ba dan kar nai maki karambani ba dana kai ki wani wajen da na sani, ko yanzu sai da na bi can sannan na zo na ɗauke ki, kinga ba dan na je can ba ya min duba da ban sa'a ba har na haɗu dake ga shi har zaki biyani kuɗi mai yawa, da sai dai nai ta ɗaukan qananun masu tafiya ana ban hamsin sittin,"
"Bawan Allah ka taimakeni muje mu koma da wuri kan mijina ya koma gida,"
"An gama"
Hanya ya ɗauka d'od'ar sai gidan abokin shi da suke sana'ar kai mata gida da niyyar bokanci, tin a hanya ya danna ma abokin kira, dan haka akan kunnen shi akai maganar, shi kuwa kan su je ya maida gidan da shi kan shi na boka......
*Casssss ana yi ina jin nayis ana bari ina jin kuka*
[08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 37:
Ranar Umar kasa bacci yayi, saboda tausayawa Jameelaa da d'iyar shi, dan tin da ta farka take ta shan nono tsabar yunwa, an bata abincin ta na yara ta shanye tass, da sai da d'ura take sha.
'Da zan kama ɗan adaidaita sahun nan kan na kaishi wajen hukuma sai yaci tsinannen duka a wajena'
Washegari da safe Jameelaa ta tashi washar haka ma Humairah, sai wasan ta take yi, Umar sai da ya tabbata lafiyar su qalaou sannan ya fita, dan acewar shi har da sakacin shi, baya kula da lafiyar su yanda ya kamata shi ya jawo hakan ta faru, ya na can ya na kula da lafiyar wasu amma ya yi neglecting ta iyalin shi.
Kulu kuwa ta qudiri a niyar sanar da Mum dik abinda ke faruwa a gidan, amma tana shakkar kar Mum taqi yarda dan yadda suka yarda da Jameelaa abun har abun mamaki.
Amma ta ayyana ma ran ta ko ba zasu yarda da ita ba sai ta faɗa masu abubuwan da take gani kuma da wanda akai a gaban idon ta.
Jameelaa ce ta sha kwalliya tana zaune gefen ta Humairah ce kwance ta na wasa irin na yara, Kulu ce ta shiga da sallama ta durqusa kamar yanda take yi mata tace,
"Barka da hutawa uwar d'aki na,"
"Barka dai, ya aka yi?"
"Dama na gama aikina ne nace bari na zo na nemi izinin ki ina son naje na gaida su hajiya, na kwan biyu ban ji labarin mutan gida ba"
"Ki gaishe su,"
Magana take cikin isa da taqama ita a dole mai gida da mai aikin ta. Kulu ce ta tashi ta sanya hijabin ta dake hannun ta ta dan yi wa Humairah wasa sannan ta tafi.
Koda taje gidan Mum ta tarar bata nan, zama tayi suka sha hira da mai aikin Mum taci abinci tayi sallah ta dan kwanta, bata jima da fara bacci ba Mum ta dawo, mai aikin gidan ta sanar da ita, bari suka yi sai da taci abinci ta yi wanka, ta fito parlour sannan Kulu taje suka gaisa tace,
"Hajiya dama tin ɗazu nazo ai ni na ma manta yau ranar aiki ce, ina tafe da wata muhimmiyar magana ne Hajiya ina fatan ko baki yarda dani ba zaki yi bincike akai, saboda ki gano gaskiyar lamarin"
"Ikon Allah ! wannan wacce iriyar magana ce mai mahimmanci haka? Ina sauraron ki Kulu,"
"Yauwaa Hajiya.... dama magana ce akan Uwar d'akina Jameelaah da uban d'aki na Ummaru, a gaskiya Hajiya zaman nasu na kasa gane irin shi, yaron nan yana iya qoqarin shi na kyautata ma iyalin shi daga kan ci da sha sutura, lafiyar su, da komai na su da idona ya gani, amma matar shi bata da godewa Allah, kwanaki munje gidan mahaifiyar ta, ana zaune ana hira, sai kawai suka ban Humairah wai na je waje na yi mata wasa, ina fita na tsaya tsakar gida, ina jin suna tattaunawa akan Uwar zata kai ta gidan boka, sannan jiya abinda ya faru ya ban mamaki kuma ya sa ni zargi kala-kala, yarinyar nan tin da ta fita da safe sai dare ta dawo, ta dawo da wani irin salo na makirci, saboda kar Ummaru ya tambayi ina taje, qiri-qiri bata damu ko zan gani ba, bayan ya juya baya ta fara dariyar mugunta harda tsalle, ni ina zargin ma fa ko tana bin wasu maz......"
"Dan girman Allah dakata anan kulu, haba kulu da girman ki, da hankalin ki, kike aibata yarinya mai nutsuwa da hankali irin Jameelaah? Taya zaki zayyana waɗannan abubuwa a kan Jameelaa? Sannan har ki yi zargin tana bin wasu mazan bayan Umar mijin ta? Gaskiya ban ji daɗin wannan maganar ba,"
"Hajiya dama ai ba magana ce mai daɗi ba, magana ce ta kiyi bincike akan abinda na sanar da ke yanzu, ni dama ai bance ki amince da magana ta ba a tashi ɗaya ba tare da kin yi bincike ba, ki bincika ki gani, innai qarya a magana ta sai ki d'au mummunan matakin qazafi akaina na amince, soyayyar ku a raina ta daban ce, ba zan bari Ummar ya cutu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 30