Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na rasa me kike ji a cikin tuwo sam baki gajiya da shi," "Hummm ba zaka gane ba na ma samo kuka da daddawa harda kub'ewa busasshiya, yau ba miyar taushe zan mana ba miyar yauqi zan yi," "Me ciki," "Ni dai bana so, ka daina kirana haka, wani in yaji sai a ce min 'yar....." "Yar me?" "Immm 'yarr...immm shikenan ina zuwa," "Zo nan ba inda zaki je sai kin faɗi me za a kira ki da shi," Matse ta yayi a jikin shi tare da daga mata kai tana kallon shi can ta sauke idon ta tana murmushi tace, "Ɗan sake ni na fada maka ka matse ni da yawa zafi na ke ji," Sassauta mata riqon yayi, ai kuwa ta balle ta ruga daki da gudu tana dariya, "Zan kama ki ne zaki qarasa me za a kira ki dashi," Juyawa yayi ya fara kwashe tuwon dan yayi ba shi da yawa, a leda ya daure ya kashe gas ya fita, bai ɗauke komai ba a wajen ya bar su, sai da ta kammala sauya kaya da wata guntuwar riga mai faɗi daga qasa, daga sama ta kama ta, armless ce rigar kalar baqi da flowrs jajaye, ta saka hula baqa a kan ta. Gyara kitchen ɗin tayi ta zubawa tukunyar ruwa, ta aje a cikin sink, ta ci gaba da haɗa miyar ta tana yi suna hira, shi kuma yana ta mata wasanni, sai kauce wa take amma yaqi barin ta tayi aikin ta da dad'in rai. Sallamar Sapnah ce ta dawo da shi nutsuwar shi ya shige d'aki ya yi zaman shi. "Oyoyoooo Sapnah saukar yaushe? Ba ko waya na tanadar maki abun daɗi?" "Kar ki damu ai gani a yi abun daɗin a gabana naci, me kike yi ne haka, nake ta jin qamshin girkin tsoffi?" "Tuwo nake yi ya karatu?" "Ahhh lallai zamu ci daɗi ashe...karatu sai godiya, mun kammala shi alhamdulillahi yanzu sauran mu jira Allah ya kawo mana miji muyi aure, dan kuwa Abban mu yace sai munyi aure zamu fara aiki," "Masha Allahu, Allah ya taimaka gaskiya na taya ki murna, nima Malam yace inshaa Allahu zan ci gaba da karatu, har sai na ce ya isheni, ina son karatu sosai Sapna," "Yauwa dakata wai dan Allah meye na cewa mijin ki malam? Ki waye mana, ko ɗan sunan zamanin nan ke baki sa masa ba sai wani malam, kamar a makarantar allo, ko bokon yanzu an daina cewa Malam," "Baki da dama Sapnah, Allah ya nuna min mijin ki, na san zai sha gata da tarairaya da kulawa,kuma ni ba Malam nake kiran shi ba ni da shi, a gaban mutane ne nake cewa Malam kawai" "Kwarai da gaske, dan kuwa inna auri mijin da ya iya soyayya shima sai mun fi Lailah majnun soyewa," Dariya suka yi a tare sannan suka tafa,haka sukai ta hira suna qarasa aiki, dan Umaimah ta qara samun wayewa ta zamani tunda ta kula Sapnah na da ita sai ta ce mata, "To yanzu dan Allah bayan Baby wanne suna kike ganin zan dinga kiran shi da shi?" "Ai shi miji ba dole sai suna ɗaya ake kiran shi da shi ba, ya danganta da yanayin da kuke ciki ne kawai,kawai dai ana son ki riqe suna ɗaya da in kin faɗa ko a gaban waye an san shi kike nufi,amma ke da shi ki dinga faɗa masa dik kala-kalan suna masu daɗi da ki ka sani, ki dinga la'akari da yanayin da kuke ciki ke da shi, in kina shagwab'a kina kiran shi da suna kamar Sweet one,zaunjee, mineeee, in kin zo qarshen kina ja cikin shagwab'ar, in ko miji ne ke maki shagwab'a, kina kiran shi da Baby, ko My baby, ko mine, su kuma irin su sweetheart, ko my dear, My love da honey, su misalin sunaye ne da zaki iya kiran shi da shi a ko ina Kuma a koda yaushe. Sannan akwai sunayen da in yana maki abu mai daɗi zaki dinga fad'in su, da yaren da kuke magana dan yafi shigar shi, ke ni fa na matsu nai aure na fara gabatar da dik wani ilimin gidan miji dana sani, nan da kika ganni practical ne kawai ban ba amma komai na sani akai na" "Ohhh ni Umaimah na shiga uku, 'yan matan yanzu sai su tsorata ka " "Dalla rufen baki ban girme ki ba? Amma kike a dakin miji har da result ɗin abinda kuke yi a d'aki, ke yanzu yarinyar primary ma ta san komai balle ni dana gama Jami'a" "Haka ne kuma, Allah dai ya tsare mana imanin mu," "Ameen... ina mijin naki, ko bai dawo daga makaranta ba?" "Yana d'aki ai ya dawo yau ko makarantar ma be je ba," Cike da jin kunya Sapnah ta ce, "Innalillahi Umaimah kin kashe ni, shine baki faɗan ba nake ta zuba kamar kanya? Ba zan sake shigowa wajen ki ba,tinda ni dai bakina baya iya shiru, sai anjima mun b'ata dake," "Dan Allah ki yi hakuri ki zo kici kayan daɗin nan," "Ke wasa nake maki a qoshe nake, ki ci abinki ki qoshi, dambun naman kawai zaki debar min na wice gida," "Ba dai gida zaki koma ba," "Ah ah ina nan sai aunty ta haihu, na ga yau ma tin da ta tashi sai yatsina take,anya ba ta fara naquda ba a tsaitsaye?" "Anyaa? ni dai ɗazu dana shiga normal na gan ta," "Aiko yanzu ta sauya kinga bani na tafi, dan ba zan so haɗuwa da mijin ki yau ba, kullum sai ya kama ni ina shegen surutuna da bana gajiya" Dariya suka yi tayi umaimah ta d'eba mata dambun naman ta tafi. Dakin ta ta shiga wanda a da shine d'akin Haroon, kwantawa tayi ta lumshe idon ta ganin Umaimah da hira da ita ya sanyaya mata zuciyar ta, dik da yayan ta taso gani ba ita ba, amma ta danji daɗin ranta. *********************** Sadeeq mahaifan shi sun aura masa wata bazawara dake maqotaka da gidan su yarinya ce shakaf sakin wawa, yarinyar akwai nutsuwa da hankali sosai, ga ta da kamun kai da tawakkali hakurin ta shi ke sa Sadeeq sake mata fuska, saboda har yanzu soyayyar Mamalo na nan a danqare a ran shi, sai ma kewar ta da yake ji a kullum na qaruwa, yarinyar bata damuwa, dan wataran ma mantawa yake da sunan ta ya kira ta da Fateema haka zata amsa ta masa abinda yake so, a hankali kunyar ta ta fara shigar shi, tin baya damuwa dan ya kira ta da sunan mamalo har ya fara jin nauyin ta, zaune suke cikin girmama juna har yau ba abinda ya shiga tsakanin su na auratayya, saboda ba shi da sha'awar kowacce mace in ba Mamalo ba. (Muje zuwa zama ka ware ne d'annan, indai mace ce ). ********************** Hauwa ke ta naquda dik ta jiga ta tsabar tausayi ya sa Sapnah kuka, dik fuskar ta yayi jawur, dik surutun ta kamar an dinke mata baki a ranar, addu'a kawai take Allah ya sauki yayar ta ta lafiya,midwife din da ke karb'ar haihuwar Hauwaa ce ta fito ta same su a bakin d'akin da aka shigar da ita, tace ma Ishaaq ya miqo kayan haihuwar da suka zo da shi ta kusa yanzu kam. Jiki na rawa ya tafi inda sukai parking ya d'akko kayan kafin ya dawo har ta haihu, yana isowa yaga Sapnah na dariya hawaye na bin fuskar ta cikin wani irin yanayi ya ce, "Sapnah lafiya?" "Yaya ta haihu lafiya kai ake jira ta sauka, sunqi sanar dani me aka samu sai dariya suke yi min" "Alhamdu lilLAAH Allah abin godiya, miqa masu kayan maza maza," Da sauri kuwa ta kai kayan sai da suka gama gyara su sannan suka miqo masu jaririn, yaro ne qaton gaske kamar ba ita ta haife shi ba. Ishaaq sai da ya zubda hawaye dan farin ciki ya manna yaron da qirjin shi, sanan ya masa addu'o'i, Hauwaa sai washe baki take bayan an maida ta wani d'akin dan hutawa. Nan da nan kuwa suka fara bugawa 'yan uwa da abokan arziqi waya ana sanar da su haihuwar, Sapnah sarkin surutu sai faɗa ma mutane take baby da ita yake kama. Umaimah ta sanar da Jameelaa haihuwar matar wan mijin nata, dan haka ta masu alqawarin zuwa in Umar ya dawo. Basu zo ba a ranar sai washegari da aka sallame su zuwa gida, tinda lafiya qlou suke daga ita har jaririn. Har cikin gida su Umar suka shiga Ishaaq ya ji daɗi sosai kuwa, ya na alfahari da yanda zumuncin su yake qara qarfi da su Umaimah tinda suna ziyartar juna. Sapnah ce ta kawo masu abin sha Jameelaa tana zaune ta na yatsina hayaniya tayi yawa wai a fad'ar ta, ta tashi ta yi ta koma ɓangaren Umaimah ita ɗaya kamar mayya, tana ta chatting da qawayen ta masu hannu da maiqo, nan kuwa Umar da Sapnah da umaimah har da mai jegon suka kafa dandalin hira, ba qaramin jin daɗin hirar Umar ya ke yi ba, Sapnah kuwa tafi kowa jin daɗin faruwar hakan, dan yanzu ta riga da ta gama gane cewar son Umar take sosai, kuma ta qudiri niyyar sai ta sanya masa soyayyar ta a tashi zuciyar da yardar Allah............. *Wa me son a yi wa Jam Jam kishiyaaaa??? A daga hannu na qirga ku.....banda mugunta dai ah toh* [08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻   MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 34: Sai da suka tashi tafiya sannan Jameelaah ta dawo sashen Aunty Hauwaa sai ya tsina take yi ita a dole ga 'yar gayu kyakkyawa ta wuce ajin su Sapnah da za a zauna ana wani hira da ita, Umar yana ganin ta ya tina ashe fa tare suka zo, wannan kuwa shine karo na farko da Umar ya zauna ba tare da tinanin Jameelaah ba tun bayan da suka haɗu da ita a rayuwar shi balle ma har ya manta da ita,cikin yatsina fuska tace, "Abban Humairah ina ganin ya kamata mu wuce gida mu bar mai jego ta huta ko? Surutun ku har gidan Umaimah ana ji" "Ke ba kin gudu ba ai da ke ya kamata ma ayi ta hira, ko dai baki son hira cikin mu ne?" Cikin wasa Sapnah tai mata wannan tambayar, kowa kuwa ya zuba mata ido ya na so yaji amsar da zata bayar, harda Umar a cikin masu jiran amsar ta ta. Kame-kame ta farayi can kuma ta basar ta ɗauki Humairah da key din motar Umar tace ma Umar ɗin, "Ka same ni a mota," Taji haushin yanda Sapnah ta qure ta da tambaya a gaban mutane,ina ruwan ta da qin zaman ta a wajen ko dan salon ta sa Umar ya ga bata son huld'a da qanwar sa?  Tayi tsaki yafi a qirga a dai-dai lokacin da take buɗe motar zata shiga ta zauna ta jira shi, ga wani qarin takaici Umar din ma bai fito ba a haka ta zira masa key ɗin ta gyara zama ta ci gaba da jiran shi,wani tsakin ta sake ja mai tsaho tare da kallon qofar gidan Umar ne da Sapnah suka fito suna ta sheqa dariya, Umar har wani duqawa yake yi, tinda take da shi bata taba ganin irin wannan dariyar ba a tattare da shi he is always calm and gentle, Sapnah ta gani tana tafiya tana turo hannaye gaba tana tafiya kamar wani robbot tana hura kumatu, Umar sake kwashewa da dariya yayi itama ta fara dariya, sannan suka tsaya, "To abokin surutu na sai da safe mun gode sosai da zumunci, Allah ya saka da alkhairi ya raya mana Humairah," Kallon ta Umar yayi cike da kulawa sannan ya saki wani qayatatten murmushin da ya nuna tsantsar jin daɗin addu'ar da ta yi masa da 'yar shi yace, "Ameen abokiyar surutu na,ni surutun ki yafi nawa har mamaki ma kike bani," "Anya kuwa na fika surutu? muje ga Maman Humairah can na jiran ka, kar taga mun dad'e sai wataran zamu tantance wanda yafi wani surutu a tsakanin mu," "OK we shall see then" "Yes Allah ya kaimu ranar tantancewa" D'aga masa hannu tayi shima ya d'aga mata sannan ya tafi, koda zai shiga mota ma sai da ya yi mata murmushi sannan ya buɗe ya shige ya zauna. Jameelaa ta ma rasa me zata yi saboda ganin wannan sabon salon lamarin da ke faruwa a gaban idanun ta, kawai sai ta sake baki da hanci da ido tana ganin ikon Allah, under her own very nose ana soyayya da mijin ta kambala'innan kayyasa, lallai yau za a ci uba kenan a unguwar nan kafin tayi yunqurin fita ta isko ma Sapnah a inda take wa mijin ta murmushi mai cike da tarin so da qauna tini Umar ya ja mota, da sauri ta cire hannun ta daga murfin qofar motar da taso budewa ta maida kallon shi gare ta. "Me na gani ɗazu kenan Umar? Me yake faruwa tsakanin ka da waccan me shegen surutun?" Cikin tsananin mamakin kiran sunan shi da ta yi gatsal ba Yah Umar ɗin ma babu kuma sunan soyayya balle kuma Abbahn Humairah ya biyo baya, ya rufe bakin sa ya shanye mamakin sa ya yi kamar ma bai gane me take nufi ba ya kalle ta sanan ya juya ya ci gaba da tuqin shi yace mata, "My love me kike nufi da maganar ki? Ban gane inda tambayar ki ta dosa ba," "Kana nufin kace min dik a cikin hira ne kake dariya da ita dariyar da baka taɓa min irin ta ba? Ko kuwa kana nufin dik a cikin hirar ne kake magana sosai wanda ko da ni baka taɓa sakewa kayi hakan ba? Ba zan ɗauki rainin hankali ba malam, tin wuri ka san me kake ciki na faɗa maka," Cikin ran shi yake maimaita kalaman ta kamar mai koyon magana, 'Me nake ciki? Ba zata d'au rainin hankali ba? Tin da muke me na taɓa yi mata na rainin hankali? I have to be a man just for today oo in ba haka ba wannan shirmen zai ta tabbata a gidana ,abun nata ya isa haka fa tana son ta tsallake dik wata katanga ta mutunci dana gina mata,' Dan haka cikin d'aure fuskar da bata taɓa ganin ya yi wa kowa irin shi ba balle ma ita ya ce, "Bana son maganar banza ni kike ce ma na san me nake ciki? Aje ni ki kai ko me? Ko kuwa sai na nemi izinin ki ne zan yi dariya ko nayi magana da wasu? Inace nan nan barka muka je amma ke basu ishe ki kallo ba kika tafi kika bar wajen,ni na zauna kuma sannan ya zama abin magana, idan da ki na so na har haka da yawa da baki tafi kin barni a inda zuciyar ki bata nutsu da su ba,kar ki sake min magana kamar kina magana da ɗan ki na faɗa maki ki kiyaye" Shiruuu Jameelaah ta yi kamar ruwa ya ci ta, dama Umar ya iya faɗa haka, 'Ya kamata na je wajen Ramai mu san abin yi, ba zai yu na rasa mijina ba, ɗan girman da yake ban ma yanzu naga yana qoqarin dai nawa gashi nan yanzu har wani faɗa yake min' Haka suka isa kowa ya yi fuska ba mai cewa kowa komai, Humairah ke ta ke 'yan waqe-waqen ta na yara. Yana tsaida motar ta fice ta shige ciki sai kumbura take yi, kwantar da kan shi yayi jikin kujerar ya lumshe idon shi, tunda suke ko zata b'ata masa rai bai taba biye mata ba sai dai ya danne, amma yanzu  ba zai iya ba ya isa haka, in bai taka mata burki ba haka zata mai da shi lusarin namiji. Jameelaa na can na fushi harda kuka, a zaton ta ya bita yayi ta lallashi yanda ya saba yi mata,(in kina ma miji kuka bayan kece baki da gaskiya a kullum,to akwai lokacin da zai juya baya ya daina biye maki,amma kukan shagwab'a da kuka akan kina son wani abu kamar yanda yara keyi, da kuka in kinyi laifi saboda a yafe maki, wannan yana sa miji ya qara son ki, ya kuma tausaya maki, sannan ya yafe maki laifin ki, mata a daina kukan banza akan rashin gaskiya) Haka suka kwana kowa na fushi da ɗan uwan sa, Umar na ta jin ba daɗi kamar ya bata hakuri sai kuma ya fasa, ya kamata ya koya mata respect, dole tana bashi girma a matsayin shi na uban yaran ta, nan gaba haka zata na wulaqanta shi gaban yaran su ko ta na faɗa masa magana a tsaitsaye. Cikin ran ta tana ayyana wulaqancin da zata masa in ya neme ta a daren nan, dan kuwa sai ya gwammace bai nema ba. Komai sai da kwanciyar hankali, dan haka Umar ko sha'awar ma bai ji ba, baccin shi ya fara cikin kwanciyar hankali, saukar numfashin shi taji alamar yayi bacci, cikin takaici kuwa ta buga masa qafa gyara kwanciyar shi yayi ya ci gaba da baccin shi, tsaki taja mai qarfi, sannan ta muskuta jikin ta ta rintse idonta ta so yin bacci sosai a wannan daren amma ta kasa, Umar kawai take hangowa da Sapnah suna ta dariya, a nata wautar ma har hango su take sun yi aure suna cin soyayya da yaran su, qara ta kwalla mai qarfi ta tashi zaune tana maida numfashi, Umar a firgice ya tashi yana tambayar ta menene, duka ta rufe shi da shi tana kiran shi da maci amana, "Ka cuceni ka ci amanata ba zan taba yafe maka ba, ashe dama abinda ke ran ka kenan? Qara aure zaka yi dama? Umar na baka dikkan soyayya ta amma shine kake qoqarin yi min kishiya Allah ya isa tsakani na da kai," Lallashin ta ya fara yi dan abun nata kuma ya fara bashi tausayi, ya kula tsabar kishi ne kawai ke damun ta ba wani abu ba. A haka ya samu tayi bacci bayan ta sha kuka ta qoshi.  Kwantar da ita yayi sosai shima ya kwanta a gefen ta, Humairah na gadon ta tana ta bacci abin ta, kallon fuskar Jameelaa yayi, yana ta mamakin halayen ta da suka sauya, first ya gano yanda ta tsani shiga mutane da kuma qyanqyamin talaka, sannan ya gano kwata-kwata bata son zuwa gaida mahaifan shi, dik ta inda ya ɓullo sai ta toshe dan kar taje, sannan kuma kullum tana  masa maganar qawayen ta masu kuɗi, gashi tana son ya na bata kuɗi, ko ya sai mata abun kuɗi mai tsada, dik a da bai taɓa kula da hakan ba sai baya bayan nan. 'Ko dai ban fahimce ta bane? Wataqila zuciya ta ke son yaudarata dan na zargi iyalina akan wani abu mummuna' Tinanin Sapnah ya fara yi nan da nan fuskar shi ta bayyana wani annurin haske da nishad'i, qanqame Jameelaa ya yi yana ta tina hirar su da Sapnah, in ya tina abun dariya sai ya sa dariya, a haka yana tinanin abokiyar surutun shi bacci ya dauke shi. *Bayan suna* Sapnah ce ke ta wasa da Muhammad sunan yaron Hauwaa kenan, yi take tayi kamar ance mata yana gane me take faɗa,shidai jariri sai bin ta da kallo yake yi,Aunty Hauwaa ce ta zauna a gefen ta tace, "Wai ke dan Allah baki gajiya da surutu ne? Jaririn ma sai kin yi masa magana" "Ehhh mana saboda ya samu ya iya magana da wuri, kinci  abincin kuwa?" "Eh na ci na sha magunguna na dika, thank you qanwata," "Ga shi bari na ɗan shiga wajen Umaimah," "Ok ki gaida ta ki yi mata ban gajiya," " Ok to" Kitchen ta biya ta d'auki farfesun naman kan da ta yi masu da safen ta wuce wa Umaimah da shi. Ta ɗan jima tana buga gate ɗin kafin Umaimah ta buɗe mata,shiga tayi tare da tambayar ta mai gidan na nan? "Baya nan da baki ga motar shi ba, me na samu ne naga kwano a hannun ki har naji yunwata ta motsa yawuna ya tsinke, dan kuwa na san ki gwanar girki ce," "To akwad'ai zaki bari na shiga ciki ko kuwa?" Dariya umaimah tayi ta amshe kwanon hannun Sapnah sannan suka shiga a tare, tin a hanya ta bud'a ta na ganin farfesun naman kan ta ji yawunta ya kawo, da sauri ta qarasa parlourn ta  ta buɗe tare da yin bismillah ta hau ci, "Ohhh wannan babyn naki akwai kwad'ayi," "Ba laifi dan kuwa ana tab'awa" Hira sukai tayi a hirar Sapnah ta dinga wayon jin abubuwan da Umar yafi so da wanda baya so sai hadda take yi ,Umaimah kuwa sai zuba take tana faɗin abubuwan da umar din baya so da irin shaquwar dake tsakanin shi da Mum din su, Sapnah sai taji tana qaunar Mutan gidan baki ɗaya, yanzu kuwa zata fara gabatar da dik wani abu da zai janyo mata soyayyar Umar dan kuwa ba zata bawa kowa dama ba a maneman ta har sai umar ya fara son ta ta tura shi wajen iyayen ta,idan yanda take so bai samu ba to ta san Allah bai nufa zai zama mijin ta ba dole ta hakura da shi. Umaimah ce ta gama cinye farfesun da aka kawo mata tass, ta shiga d'aki ta dan zuwa wanke hannu a toilet,ta na shiga wayar Umaimahn ta fara ringing, Sapnah ce ta d'aga nan ta ga me kiran, mayarwa tayi ta ajiye in Umaimah ta zo ta kira shi, kira yayi tayi Umaimah bata fito ba dan haka sai ta sake miqa hannu ta ɗauki wayar ta amsa sannan ta kara a kunnen ta............ [08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 36: A wani qofar gidan qasa mai shago a ta waje suka tsaya, a dai-dai jikin shagon ya tsayar da su, nan take ya fita ya riqe mata Humaira itama ta fita tana ta bin wajen da kallo, Abokin shi na ciki ya yi wata iriyar shiga kamar bokan gaske. Sai surkulle yake ta yi  Jameelaa na ganin shi jikin ta ya hau rawa dan kuwa bata tab'a zuwa gidan boka ba sai yau, yau ɗin ma gata ita ɗaya bata ko san sunan unguwar da suke ba, kukan zuci take tayi da dana sanin zuwan ta ita ɗaya wannan waje mai ban tsoro,amma da ta tino abinda ke gaban ta na son mallakar Umar ita d'ayan ta ba tare da ya haɗa ta da wata mace ba a rayuwar su sai ta samu kan ta da ware wa ta na jin wani farin ciki na shigar ta a hankali ta tabbata yau ta kawo kukan ta gidan mutuwa. "Ta kan tsamiya ta taimaki boka ga baquwa na kawo maka, tana cikin tashin hankali da damuwa akan halin mu na 'yan maza jincewa tana neman taimako ne ya sa na ce bari na kawo ta wajen me kankat dan haka gata nan a taimaka mata," "Firrrrr, tiiiirrrrr, sirrrrrrr, bucaaaaaa.... ke ta shi maza ki fita aikin ki ba mai yuwa bane firrrrrr," "Na shiga uku na lalace ni Jameelaah dan Allah ka taimaka min, ka tsaya na faɗa maka matsala ta na san zaka tausaya min kamin aikin nan, da dikkan alamu ana samun biyan buqata anan, tinda har kawo ma mutane ake yi" "Tiiirrrrr shin wai ba akan kishiya bane matsalar ki? Kuma kina son mallake miji? Ba zai yu baaaaa, tashi tashii kafin ta kan tsamiya ta fusata," Gurfanawa tayi a gaban shi ta fara kuka sosai har da majina, Humairah ce ta farka daga bacci ta fara kuka, Jameelaah ko ta kanta bata bi ba ta duqa gaban matashin nan tana kuka tana bada hakuri akan ya taimake ta,jin kukan Humairah ya yi yawai sai ta sa hannu ta janyo Humairah daga baya ta fara bata nono, nan take ta hau zayyana masa qarya da gaskiya akan matsalar da take ciki, bayani take amma hankalin su na kan nonon ta da take shayarwa da dashi, gani ya yi jan ran ya isa haka ya kamata su fara mata aiki kawai sai ya ce, "Siiirrrrrr, Hajiya aiki na mai sauqi ne ya kan d'au wata ɗaya ko biyu ana yi, ni ban cika karb'ar kuɗi ba ma, saboda aljanar kan tsamiya tafi son ayi mata yanka, fiiirrrrr bucaaaaaa... ga shi abinda muke son ki yi mana ke ba zaki iya ba kina da rauni, akwai imani da Allah kaɗan a ranki,in ance ki yi ba zaki iyaba," Da sauri ta janye nono a bakin Humaira ta aje ta a wajen, ta haɗa ta da yar jakar ta tayi wasa,sannan ta maida hankalin ta kan bokan nata tace, "So kake na rantse maka kan ka yarda zan iya komai akan Umar? In kana son na rantse zan

Chapter 21 of 30