riqe, sai abun hannu kowanne hannu an sa masa awarwaro na zinare, da kudin sadakin ta da wanda Abban ta ya bayar Aunty Hauwaa ta siyo mata a d'azun, kukan murna taji na son ya zo mata, sai qoqarin maidawa take yi kar ta b'ata kwalliyar ta,
"Kika sake kika min kuka saii na make qeyar ki"
Dariya suka yi tayi dikan su sannan suka raka ta waje inda motocin kai amarya ke tsaye ana jiran ta, a wuce da ita gidan mijin ta abin son ta, dik yanda ta so ta riqe hawayen ta kasawa tayi, ganin qoqarin da take na kar tai kuka kadai sai da yasanya mutane kuka suma, Aunty Hauwaa har sai da Umaimh ta riqe ta saboda kuka take sosai na tausayawa qanwar ta, zata shiga sabuwar rayuwa,rayuwar da ta qunshi komai da komai a cikin ta, abinda ka zata da wanda ba ka zata ba shi zaka gani a ciki,abinda kake son gani da wanda baka son gani duk zaka tarar a cikin ta.
*Cassssssss ni dai a radu ina lab'e ko kowa ya kai amarya ya tafi ni gidan nika kwanci yau sai an ci kaza da ni😂*
[09/09, 10:39 am] Aunty Hameeda: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 44:
'Yan kai amarya dai jama'a a gidan suka sami ango shi ya yi masu iso zuwa cikin gidan, sai dariya kuwa ake yi masa ana qusqus,shi kuwa ko a jikin shi, ganin haka mutane suka yi ta fita suna komawa mota tinda sun ga gida kuma sun sanya albarka zaman me za su yi? Sai fatan alkhairi da suke yi wa Sapnah da Umar ɗin , Safiyyah sai kuka take da zata tafi, Sapnah ma tsabar kukan da ta sha kan ta sai sarawa yake yi bayan tafiyar kowa Umar ya shiga ya same ta tana ta tsiyayar da hawaye, jingina yayi da gefen gadon da take zaune, ya kafe ta da ido, cikin yanayi na tsokana ya furta,
"Ohhhh Allah na, daɗi na da aure yana sa dik wani mara kunya mai surutu yayi ladab,who could have thought wai Sapnah zatai laushi ta yi irin wannan kukan kamar wadda akai wa auren dole? Ah ah ah..... na manta fa, maybe auren dole aka yi mata bata so na wayyooo...abin tausayi ni Umar ..... gaskiya Umar in ka barta ta kwana a gidan ka baka kyauta ba, ya kamata ka maida baiwar Allahn nan wajen Umman ta,...ko dai wajen Aunty Hauwaa zan maida ki?"
Tinda ya fara maganar tayi d'if dan ta samu damar jin me yake faɗa da kyau, jin tambayar da yayi mata ne ya sa ta kallon shi, suna haɗa ido kuwa ta zabga masa harara, idon nan kamar zai faɗi qasa, bakin kuwa kamar zai tsinke saboda murgud'a shi da take yi.
"Dawa kike?"
"Da kai nake"
Ta faɗa muryar ta sam bata wani fita sosai, amma yaji me tace sarai,
"Kayyaa... na zaci tsiwar taki ta hayaqa ashe iya gida ta tsaya ba a zo da ita gidan miji ba, da ki faɗa mana kice dani kike da qarfi ki ga ya zan maida ke yan zunnan"
Shiru tayi dan bata son dik wani abu da zai sa Umar ya kusance ta a yau, a matuqar tsorace take da shi.
Sai takalar ta yake yi ita ko ta yi masa banza, daga baya ya fara da cire mata mayafi, nan fa ta qanqame qammm, Umar yayi yayi ya cire ya kasa tabdi jam, ashe bayan surutu Sapnah gwanace wajen qarfi, saki yayi kar yaji kunya, yarinya sai shegen qarfi kamar wadda ake taya wa?
"Ina zuwa be a gud girl please yanzu zanje na dawo, na san me yasa kike b'ata rai, ba kiji qamshin mutuniyar taki ba ne ko ? wato kaza, bari na je na siyo na kawo kazar amarci, harda kud'in siyan baki zan had'o miki,"
B'are baki tayi ta fashe da kuka wai Umar me ya maida ita ne, sai wani tsokanar ta yake yi, tama gama gane ina ya dosa da kalaman shi, son auren take yake nufi ko kuma qin auren take yi kenan oho, sai yayi tufka ya warware.
Rungume ta yayi tsam a jikin shi yana shafa bayan ta, tin tana kukan har ta fara sauke ajiyar zuciya, qamshin junan su kawai suke shaqa, Umar ji yake gaba ɗaya sai a hankali, in bai samu yanda yake so ba akwai matsala, dole ya samu had'in kan Sapnah yau, tin da yayi auren farko ya fara kusantar Jameelaah bai taba nesa da matar shi ba sai da Jameelaan ta fara iya shegen ta, da sauri ya sake qanqame Sapnah, zuciyar shi na bugawa da qarfin gaske.
'Jameelaah, Ya Allah ka sa wannan ba halin su ɗaya ba, Ya Allah ka sa halin ta yanda yake a fili na b'oye yafi shi kyau,'
In Sapnah ta kasance irin Jameelaah zuciyar shi bugawa zata yi, a da ya zaci ba zai sake son wata sama da Jameelaah ba amma a yanzu ji yake ba kamar Sapnah a zuciyar shi dik duniya, d'aga ta yayi daga riqon da ya yi mata yace,
"Tashi kiyi alwala muyi sallah dan gode ma ubangijin da ya mallaka mana juna mu, mu roqe shi daya yi mana albarka, ya sa mutuwa ce zata rabamu"
Babu musu ta miqe cikin dishewar murya ta ce masa,
"Ina da alwala"
"Anyaaa kuwa Sapnah? Fadi gaskiya anya bata karye ba?"
Dukan wasa ta kai masa a qirjin shi, ya riqe hannun ta a wajen yana shafawa da hannun ta,
"Ouchhh,hannun ki na da zafi fa, kar ki karyan haqarqari fa, bari naje nai alwala ki jira ni"
Zama tayi tana murmushi haka Umar yake dama, yes ta san yana da magana kamar yanda take da magana, dik da Umaimah tace da ita yake sakewa yayi surutu mai tsaho haka, amma bata taɓa zaton ya zama mai shegen tsokana irin wannan ba.
Shimfid'a masu abin sallah tayi ta gyara laffayar ta ta rufe jikin ta sosai, ya jima sosai dan sai da yayi brush ya sake gyaggyarawa ya fita, sallah sukai raka'a biyu sannan ya yi masu addu'a, ya dafa kan ta ya karanto addu'ar da tazo a sunnah ango na yi wa amaryar shi, sannan ya ce,
"Taho muyi hira mu rage lokaci, dan yau daren namu zai yi tsaho"
Sanya ta yayi a tsakanin qafafun shi, ya fara da yi mata tambayoyin da suka shafi addini, tana amsa masa dai-dai gwargwado, a zaton shi a iya boko ta k'ware kawai, ashe ta bangaren islam ma ba laifi,sauraron ta yake tayi, tana zuba masa bayani akan tambayar da ya yi mata na yanda ake wankan tsarki, ta haɗe dikkan kala-kalan wanka da ake a islam tana yi masa bayani da banbancin su, Umar yayi kasaqeee da kunne yana sauraron ta.
"Da kyau, ba zan boye maki ba wasu abubuwan ma yanzu na san su, Allah ya yi miki albarka, zadakillahul ilm wa taufiq wa fatahallahu alaiki"
"Ameen ya zaujissalih"
"Iyyeee lallai ne yarinyar nan da gaske kina so na, soyayya ta ta rufe maki ido gaskiya ke da kike cika baki in kin zo ko kallo na baza ki yi ba jibe ki yanzu kwance a jikina, kin wani qanqame ni"
Da sauri ta d'aga shi ta koma can saman gado tana dariya, tare da rufe fuskar ta,
Tashi yayi ya je Allah ya bashi sa'a ya k'wance laffayarta ta sama, adon da tayi ne ya bayyana, tare da wani irin qamshi mai sanyi ya bugi hancin shi qoqarin Karb'a take yi, ya kai hannun shi wuyan ta wani iri ta ji a jikin ta, sai da ta rintse ido hannu ya sa ya cire band din da aka d'aure mata gashi da shi, nan da nan gashin ta mai madaidaicin tsaho ya bazu a kafad'ar ta, d'aga kai tayi ta kalle shi, bata taba ganin shi a wannan yanayin ba, zama yayi daf da ita, yana qare mata kallo, cikin bushewar lips dan tsoro ta zaro harshe ta tsotsi lips din ta, Umar ji yayi kamar da gayya tayi hakan, bai bata lokaci ba wajen kai nashi bakin zuwa nata.....
Yana cikin jagwalgwala mata kwalliyar ta da Umaimah ta bata lokaci wajen tsarawa, aka kira sallar magrib, hamdala tayi a cikin ran ta, dan kuwa ta gama zata ta shiga hannu kenan.
Bata tashi sanin me Umar ya mata ba sai da ya daga ta zai je masjid taga daga ita sai dan qaramin wandon rigar dake jikin ta, gashin ta dik ya yamutse saboda saka hannun shi daya dinga yi, jikin ta tini ya ɗauki rawa ta ja mayafin ta ta ruje jikin da shi, Umar dariya yayi ta qasan maqoshin shi, dan magana ba zata samu ba a wannan yanayin da yake ciki.
Sai da ta tabbata ya tafi sannan ta sake watsa ruwa ta sanya turarukan wanka da ta gani a toilet ɗin, tasan aikin aunty Hauwa da Umaimah ne, murmushi tayi ta masu addu'a a ran ta, ta kammala ta daura alwala, sannan ta fita, doguwar riga ta zira kawai ta tada sallah,
Umar a mota ya fita yaje ya yi masu siyayyar abubuwan da zasu buqata, sai ya koma masjid, bayan anyi sallar isha'i ya ɗauki hanyar gida.
Itama sai da tayi sallah sannan ta nemi wani riga da wando na bacci masu santsi da kuma kyau ta saka, gani tayi kayan gaba daya qanana ne sosai na bacci a haka wannan ne mai mutunci a kaf lefen nata, shima sunan riga da wando ne amma komai a bayyane yake.
Hijab ta ɗora a kai ta haye gado ta rintse ido cikin ta sai kukan yunwa yake, dan ita kan ta bazata iya tina rabon ta da abinci ba, amma ta qudirta ba zata tashi ba sai safiya.
Ko da ya shiga yaga an karkashe fitilu ya san ta kwanta kenan, amma ai da kyar in tayi bacci.
Shigar da komai yayi ya zuba a inda ya dace, sannan ya zubo masu turkey daya siyo a plate, ya d'oro a babban trey, ga fresh milk a sama da cups biyu sai wuqa da cokali mai yatsu.
"Assalaaamuuu alaikummmm, Mrs Umar tashi muci abinci yunwa zata ma Umar din ki lahani, na jima rabona da abinci,"
"Balle kuma ni da....."
Da sauri ta damqe bakin ta, tariga da ta tona kan ta surutun tsiya baida amfani, ohhh Allah yau ta shiga ukun ta wajen Umar da tsokana ta san.
Kwalla ce ta taru a idon ta ,tana kwance taji ya yaye bargon da ta rufa da shi, sannan yana qoqarin cire mata hijab din jikin ta ya na tambayar ta da,
"Balle ke kuma mi? Taso amaryar qauye, waya ce maki ana wannan yayin kwana da hijabin?"
"Ni ba ruwana ban san me ake yayi ba ka barni nayi bacci na gaji,"
"Sannu kin ji, zan maki tausa bayan kin ci abinci sai ki i baccin ki, taso na san kina jin yunwa"
Mammatsa qafarta da hannayen ta yake,ita kuma tana kaucewa,
"Ni bana wani jin yunwa, dan Allah ka barni"
Cikin ta ne ya qarya ta ta, Umar kuwa ya sake kai kunnen shi cikin nata yana dariya, ɗaukan ta yayi ya dire a qasan carpet, sai mutsu-mutsu take, ita dik a tsorace take dashi, bata son abinda Umar keyi mata sai wani kusanta kanshi da ita yake, alhalin da ba haka yake ba,
('Yannan yanzu kin zama mallakin shi, he has the right to touch every little part of u, ba yanda zaki yi😂 and a gaskiya soyayyar Umar da sapnah ni kaina tana burgeni har gobe, na amince da cewar miji da matan da basu san juna ba kafin auren su auren yafi qarko, Umar da Sapnah kafin aure ba suyi soyayyar zamani ba, amma wallahi wallahi wallahi a wannan zamanin yana wahala a ce budurwa da saurayi suyi wata ɗaya suna soyayya bai lalube ta ba, an dad'e ayi shekara biyu wasu sun gama sanin dik wani part na junan su ta hanyar wayar nan da kuma ido da ido, wasun su kuwa wallahi har saduwa sunayi ba aure, ciki anyi an zubar an kuma an rufe an zubar daga qarshe a yi aure kuma a haka, wace irin rayuwa ce wannan ake gudanarwa kenan? Zai wahala yara su yi shekara da shekaru a tare a wannan zamanin ace ko hannu basu taɓa riqewa ba, masu mutuncin cikin sune suka tsaya a rungume-rungume da kisses, d'aid'aiku ne suke aure salim alim ba lalata, Sapnah da umar na daga cikin qalilan na gari da suka rage da basu yin soyayyar shan minti,'yan uwana mata da maza mu dage sosai dan Allah mu bawa shaid'an kunya mu tsaftace rayuwar auren mu kafin mu shige ta.)
Suna ci Umar na tsokanar ta, amma taqi kula shi, dan da ta fara ci taji daɗin na ratsa ta sai yunwar ta motsa bata tsaya fulako ba sai da ta qoshi ta sha madara ta je ta wanke baki da hannu sannan ta koma ta kwanta,
"Imm imm imm imm Mrs Umar, this is really bad, ya zaki ci abinci ki kwanta? Ai sai ki yi qaton tumbi, yanzu ki tashi ki zauna, bari na wanko hannu na nazo mu ɗan motsa jiki kin ji,"
Kashe mata ido ɗaya yayi ita ko ta zare ido tare da shaqar iska, ta toshe bakin ta, dan kuwa ta gane me yake nufi,abun na Umar kuma ya koma sai lahaula,ta bashi award ɗin sarkin surutu ta bar masa sarautar.
Umar bai fito ba sai da ya gama shirin bacci, ya kwashe komai ya kai kitchen, ya koma bayan ya kashe komai da ya dace a kashe, ya ma qofar gidan su ayatul kursiyyu sannan ya shiga,addu'ar bacci ya samu tana yi, ya kashe fitila ya kwanta, shima ya fara yin addu'ar tsabar neman magana irin na Umar ya yi addu'ar shi amma yake neman magana,
"Ki shafa min addu'a nima please Mrs Umar,"
"Dan Allah Yah umar kayi bacci ni ma bacci nake ji, kaga in ka damen zan gudu can d'akin na kwanta"
"Shikenan tinda ke ba zaki shafamin ba, ni ban da rowa bari ki gani"
Ina ganin Umar ya shige bargo ya ja Sapnah jikin shi, nace tooo an gama leqen asiri Haermeen Haermmaerh, an shiga hurumin manya su Sapnahn Umar😂
Washe gari da sassafe Umar ya yi wa Safnah wanka idon ta yayi luhu luhu saboda kuka,muryar ta ta idasa dudashewa, zazzabi take yi sosai, tabbas Umar ya same ta a budurwa,ashe yana da rabon ya d'and'ani zaqin mace budurewa kuma mai dimbin ni'ima a rayuwar shi? jinin da ake ta cewa wai ana kai mace budurwa ake gani a washegarin aure kamar an yanka rago duk bai gan shi ba, a matsayin sa na likitan mata kuwa ya san possibilities ɗin dake sanyawa a rasa wannan jinin, amma ya tabbatar da cewa matar shi Sapnah budurwa ce.
Bayan ta gama shiryawa cikin wani farin lace mai matuqar kyau da tsada, an masa adon pink da flowers masu kyau, riga da zani ne buba aka mata, tayi irin shigar yan garin su Oduduwa ta dakko abun hannun ta na zinare ta saka, ta d'akko sarqar ta da d'ankunne irin na Indiya, zata saka ta ji an zagaye mata wuya da sarqa mai ɗan nauyi.
Haɗa ido suka yi ta mirrow da Umar ta sauke nata kwayar idon da sauri, dan kuwa wata iriyar kunya Umar ke bata, ba abinda take tinawa sai kukan da ya dinga yi sosai bayan ya gama mata sala sala, ita kuka shi kuka, a zaton ta ko bai gamsu da ita bane, amma sai taga yana bata kulawar da tinda take ba wanda ya taba bata, sai ko da tana yarinya.
"Daga idon ki ki kalle ni so much with pride my love i am all urs, and u ar all mine, and i promise to keep us together for rest of our lives, Sapnah Allah ne kaɗai zai sanya ki a irin irin farin. cikin da kk sakani jiya har fiye da haka ma, kuma ina fatan in ya tashi saki a farin cikin ya ninninka maki,ta yanda ba baqin cikin da zai rab'i wanin ki ma ba ke ba, Allah ya saukar da albarkar shi akan ki, wannan kyauta ce ta iya abinda zan iya mallaka maki a yanzu, kafin Allah ta sake hore min, bayan zuciyata da jikina da ruhina dana baki na mallaka maki wannan sarqar, Mum d'ina ce ta bani tace na baki, sarqa ce mai mahimmanci a wajen ta, ta gaje ta wajen mahaifiyar ta,ina fatan zaki so ta kema ki adana ta, har Allah ya kawo mana ɗan da zai girma shima yayi aure ki bashi ya bawa matar shi,"
Wani irin shauqin son shi ke fizgar ta wanda ada bata ma san tana yi masa kalar wannan son ba, da sauri ta juya ta qanqame shi har d'aurin da ta kafa yana fad'uwa, sun jima a haka kafin ya d'ago ta yace,
"To ya isa kar ki goga min wannan hodar da kuke shafawa a farin kaya, ina ustaz na fita ace na rungume mace,"
Goga fuskar ta ta sake yi a jikin shi, sanna ta d'aga tana hararar shi, har ya isa yayi wata magana akan rungumar mace bayan abinda yayi mata jiya?
Ɗan kunnen ya sanya mata da zoben, sannan ya ɗauki dankwalin ta da ya faɗi yana dariya, ta amshe tana nuna shi da yatsa, dan ta san halin tsokanar shi,
"Not a word from u,i said not a word!"
Qunshe dariyar shi yayi, tare da d'aga hannayen shi sama ya fita, itama dariyar tayi, ta zauna tana kallon kan ta, Umar har ya maida ta basarakiya, dibi yanda take kyalli, d'aurin ta sake yi, ta kalli dakin taga yanda ya gyara masu shi ko ina fess, kamar ba d'akin su ba da ya hautsina jiya tashi tayi da kyar dan dik jikin ta ciwo yake yi mata, taje kitchen dan wanke kayan da suka ci abinci taga ba komai an wanke an gyara, lallai ta dad'e a wajen wanka tinda har yayi aiki haka bata fito ba.
'Yan walima fa sun fara hallara, masu kuɗi da suka ga harda talakawa a wajen wasu ransu ya baci, gani sukai an qasqantar da su, wajen cin abinci an jera mai kuɗi ɗaya talaka ɗaya duk anjera su akan carpet dogaye, wannan na kallon wannan, wancan na gogar jikin wannajn, ga abinci nan mai rai da lafiya an rarraba kowa an zuba masa zama kawai za a yi a fara zubawa uwar hanji wato tumbi...............
*Ayi hakuri da wannan, zuwa gobe ko anjima inshaa Allah zan ci gaba, mai son zuwa walima ta shirya a yi walimar bikin su Sapnah da ita💃*
[09/09, 10:39 am] Aunty Hameeda: 💅🏼 *MAZAUNA GIDA* 💅🏼
*WRITTEN BY HAERMEEBRAERH*
Page 47:
Tagumi ta zuba tana bin shi da kallo shi da tsiren nashi yana ta maganar shi shi ɗaya bata iya ce masa komai ba,rayuwa kenan gajiya tayi da zaman ya cinye nashi ya na buɗe mata nata zai bata a baki, ita kuma tana qoqarin cire nad'in mayafin jikin ta,dan bata ga amfanin lullub'ar nan ba, wace kunya ce zata ji wajen tsoho sa'an Baban ta?
"Amarya Jameelaah, ina zuwa haka?"
"Zan zaga ne nayo alwala banyi sallar isha'i ba,"
"Subhanallahi, maza maza kije ki yi sallah,ba a wasa da ibada ko me mutum zai yi kar yayi wasa da ibada,"
Daga masa kai tayi ta fita sai taga babu buta a waje sai ta dawo dan ta ɗauki butar,taga yana lashe hannu alama ta nunaya ci mata tsiren ta kenan murmushi tayi da taga ya diririce,
"Dama na mayar na rufe ne tunda naga baki ci ba kar ya gama shan iska,"
"Kar ka damu Baba ka ci kawai ni a qoshe nake, in ma inajin yunwa zan ci kayan garan can,"
"A ina ne da kayan garan? "
Cikin nuna tsananin kwad'ayi yake maganar, nuna masa ta yi a bokitan da suke, sannan ta debi ruwa ta sa kai zata fita, kiran ta yayi murya can qasa yace,
"Kin ga ki a dana mana wannan, kar ki bari kowa yasan akwai su,a hankali zamu dinga ci har ya qare,"
D'aga kai kawa tayi ta fice ta san komai game da salon rowar shi, akwai yarinyar shi dake aure a Kazaure suna ce mata Hajjo, sukan haɗu da da Jameelaah jefi jefi, har wajen Ramai mamar ta Uwar gidan take aiken ta a da dan a sammata garin tuwo ko wani abun dai, saboda ba kullum kasuwar ke buɗe masu ba sannan ga shi shi kuma akwai matsi.
Jameelaah ta yi alwala tayi sallar ta ta samu ta sauya kayan jikinta ta kwanta,
"Amarya ba kin yi gayyataba a taya ki hirar dare?"
Washe bakin shi yayi da ya ke fidda warin albasar tsiren da ya gama cinyewa, ga kalar goro data qara ma bakin kyankyami, yana kusantar inda take taji wani mugun warin hammata ya dake ta,ba shiri ta miqe,taso kwarai ta basar ya gama dik abinda zai yi da ita amma inaa juriyar nan ba zata samu ba,cikin raunin murya tace,
"Dan Allah na tambaye ka Baba,"
"Allah ya sa na sani Amarya, ki daina kirana da baba ina laifin ango? Ko ki kirani da suna na Tsalha kamar yanda sauran suke yi, ko ki kirani da Baban Hajjo,"
"To kayi hakuri Baban Hajjo, dama ina son na tambaye kane dan Allah kaji wani wari na fita daga jiki na?"
"A'uzubillahi me ya haɗa ki da wari kuma? Irin wannan qamshi dake tashi a jikin ki, kamar wadda ta fito daga kamfanin turare"
"Na gode da wannan yabon da ka yi min, amma baka tambaye ni ni ya naji game da kai ba, ko baka son na ji qamshin da kaji a jikina ne ?"
Shiru yayi na wani lokaci, can yace,
"A gaskiya ba zan b'oye maki ba, rabona da wanka tin shekaran jiya dan haka na san bama na qamshin da kike so,"
"In kana so ni da kaina zan iya taya ka kayi wanka yanzu na baka sabon brush da abun wanke baki saboda yau daren amarcin mune, kaga dole mu gurji amarci da kyau ko ya ka gani?"
Cinyar shi ta shafa ta tsakiya, wani ihun murna ya saki, ya sauka a gadon yana faɗin,
"Allah na gode maka ashe da rabon nima zan yi qara'in quruciya ta, muje ki wanke ni tatas,kamar yanda malamai ke faɗa ayi wanka da mata akwai soyayya a ciki, nan ba wadda ta taɓa min haka,tunda jajayen sawayen mu gashi har an jeme"
Sauka tayi ta fita ta kai ruwan wanka, sai da ta tsaya ta sha kukan ta ta goge hawayen ta sannan ta sanar dashi ta kai ruwa ya fito, wanka mai kyau Jameelaah ta yi masa, sai ga Tsalha ya fito fess dashi, haqoran nan kuwa tana goge su tana kauda kai,dan kuwa kamar zatayi amai haka take ji.
Shi kan shi sai yaji wani irin iska da nutsuwa na ratsa shi,da datti dik ya maqale masa akafar gashin jikin shi.
Alwala ya d'aura domin yana son su gabatar da nafila kafin komai ya kankama tsakanin su.
Ranar Tsalha ya ba ma Jameelaah kunya, har yasa ta dinga tinanin ya zata kalli matan shi da yaran shi da safe?
Tasha sambatu da sanya albarka, ko ta toshe masa baki sai yayi ta surutai a cikin hannun ta, da kyar tasamu ya kammala ya miqe, Jameelaah ta sha mamki, kamar ba dattijo ba, lallai duk yadda zatai zatayi ta gyara shi, su more auren su, tinda Allah ya qaddara mata zama da shi.
Yana gama hutawa ya tashi yace ta tashi taje suyi wanka, kar su kwanada janaba, baya da kyau hakan,ita dai yana bata mamaki dan kuwa akwai ibada.
Sai da sukayi wanka suka koma d'akin kwantawa suka yi, yana son ya rungume ta yana jin nauyi, ta kula da hakan sai ta kad'a ido sama,a ranta tace,
'Wai kunya yake ji saida ya gama lallashe ni kota ina sannan zai dinga wani sunnekai, indai ina son na samu na mallaki soyayyar shi dole sai na sake masa jiki, nayi amfani da wannan damar na daidaita lamarin shi ko zamu mori rayuwar auren mu'
Janyo hannyen shi tayi ta ɗora a saman qirjin ta bayan ta juya masa baya, ma'ana yayi kamar shi ya rungume ta ta baya.
Wata ajiyar zuciya ya sauke tare da sake sanya mata albarka, amsawa tayi tayi shiru,hawaye na tsiyaya a idon ta, haka bacci ya dauke su.
Da sassafe taji ana ta hayaniya, ga zage-zage ana ta yi sai d'ura ashar ake a tsakanin yaran, manyan kuma na ta bada umarni da hayaniya.
Tashi suka yi da sauri dan yin sallah
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 30