zuci, ta samu abin hawa sai gida.
Da kuka ta faɗa jikin Sadeeq, shi kuwa a gigice ya kama ta yana son jin me ya same ta sai da tai kukan baqin cikin daya tokare mata zuciya sannan ta labarta masa dik abinda ya faru, sannan ta qara masa da cewa,
"A yanda muka taso da Jameelaa, ni nayi sadaukarwa kala-kala akan ta amma ita a kullum bata da burin da ya wuce ta ga tana muzanta, ni mai iya yin dik wani aiki ne dan ta haihu ba tare da gajiyawa ba, amma duba ka ga yanda take ta wulaqanta ni gaban qawayen ta sabbi masu kudi, ni na tashi a banza kenan, naso umaimah ma taje dana danji sanyi-sanyi araina, amma bata je ba ni Fateemaa nayi alqawarin ko da bashi da saida kayan dana mallaka ne sai na bawa Jameelaa mamakin abin da ta aikata min, sai na nuna mata ba ita kadai bace zata fantama da kuɗi ba a duniya..........[08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 28:
Haroon ne zaune cikin motar da Ishaaq ya sai masa sabuwa dal yana jiran su Umaimah dan kai su gidan Jameelaah haka nan shi dai bai son Jameelaah har yanzu, dan ganin ta ya ke yi irin mutanen nan masu halayya biyu, amma da alama su ba su gane ta ba, ita ɗin ma ba son shi take yi ba dan ta ga alama ya gama gane ta tsaf, shi yasa bai son Umaimah na rab'ar ta sosai.
Sai da suka gama b'ata lokaci sannan suka fito yana ganin shigar Sapna ya b'ata rai, sai da ya bari ta zo daf zata shiga ya d'aga kai yace,
"Ince dai ba ni zaki bi a haka ba ko?"
"To da wa zan bi? A mota fa muke,"
"Habaa hajiya, gaskiya ko ki sauya mayafi ko ki sauya kayan jikin ki dika, dibi wata muguwar tsagu da akai ma skirt din ki, dibi saman rigar ki ke a ganin ki wannan shiga ta dace da mace mumina?"
"Ya ustaz Attaqwa hahuna anyi nuni da saitin zuciya so a zuci abun yake ba wai a shiga ba, ba kayan da zan sauya nidai sai dai kace kawai ba zaka d'auken a motar ka ba na hakura,ko na hau adaidaita sahu,"
"Kin manta da ayar da tace a faɗa ma matan annabi da muminai su sanya jalbab? Ba dole sai hijabi ba koda mayafi ne ki saka amma wanda zai rufe ko ina na jiki to Shima jalbab ne, kuma sutura da zata rufe jiki dikkanin shi itama jalbab ce,ke yanzu amma gaba daya kinyi shiga ta tabarruji sannan ga uban turare kin fesa wanda tin kan ki iso na ke jin qamshin jikin ki sannan kice attaqwa hahuna? Kina tinanin in har akwai taqawa cikakka a zuciyar bawa a jikin shi ba za a same ta ba? Tinda a iya sani na zuciya ke juya jiki, ban hana ki dan tozarci ba, na hana ki ne kawai saboda ke kina daga cikin ahalina yanzu, mun zama ɗaya Aunty Hauwaa Yayata na ɗauke ta ta jini ba iya matar wana ba,dole inna ga wani nata ya yi ba dai-dai ba na nusar dashi, last warning ki koma ki sauya kayan jikin ki ko minti nawa zaki ɗauka ina jiran ki,"
Maganganun shi sun shige ta sosai, amma kunya take ji ta koma ya gan ta musamman tsagar bayan ta, sai yanzu ta ji kunyar fita a haka,
"Dan Allah ki je ki sauya muna jiran ki, na san ba zai tafi ba sai dake, mutuncin ki yake kare maki jikin mace na da daraja da qimar da ba kowanne jaki da doki ya kamata ya gani ba sai muharramin ta, jikin mace yana da matuqar qima da daukakar da yafi dukiya da dik wani abu mai mahimmanci, tinda ko gobara akai aka ce komai ya qone zakiji an fara tambayar anyi asarar rai? Ki je ki sauya, baya son jikin ki ya zama makamashin wuta ne, kije...."
"Ya isa haka Umaimah say no more please, na fahimce shi tin farko ban san ya zan na wuce ta gaban shi da tsagar skirt dina bane kunya nake ji,"
"Muje na raka ki, muje wajena na baki hijabi,"
Jan ta Umaimah ta yi, sukai ciki ta aje mayafin ta, ta bata hijab madaidaici kalar kayan ta, ita kan ta sai tafi jin daɗin da sakewa a cikin hijabin unlike da ta sa mayafi sai tai ta ja dan rufe wani wajen da bata son ya fita.
Koda suka dawo Haroon fuskar shi ɗauke da murmushi suka shige suka ja sai gidan mai jego Jameelaah.
Ramai na ta haɗa kaya tana sharar kwalla dan kuwa an kawo mai aiki mai suna kulu, da kulun gatsal Jameelaa ke kiran ta, dik da cewa matar ta girmi Ramai, Umar kuma yana ce mata Iya, d'akin da Ramai ta zauna nan aka kai mata dan qullin kayan ta, Kulu ta iya aiki sosai, ga iya girki musamman na gargajiya, Umar yaji daɗin samun ta a matsayin wadda zata na taimaka masu.
Jameelaa ta buɗe abubuwan data samu tana gani sai murna take da jin daɗi, dan kuwa ta tara sutura ba kadan ba, daga ita har jaririn ta, ga kudi da ta samu ta biya bashi har da ragowar 30k a sama ta samu, dubu biyar ta bawa Ramai a ciki, Ramai kuwa ranta ya baci k'warai ina laifin ta bata dubu goma? dik aikin data tiqa a suna da kafin sunan ya tashi a banza kenan? Umar ya bata kudi wanda Jameelaa bata san nawa bane sai son sanin nawa ne aka bata take yi amma Ramai ta damqe abun ta ta kuma kwashi kayan gara, sai da ta haɗa buhu da kayan sawa dana abinci da tarkacen abubuwa dai harda flask.
Umar yaso maida ta ta kafe zata tafi ya wuce office kawai, dan haka ya fita bayan ya bata saqon gaida Baba da yi masa godiyar basu ita da ya yi.
Motar su Haroon ce ta tsaya, suka fita dikan su shi kuma Haroon sai ya wuce kasuwa, tare da alqawarin komawa qarfe uku dan maida su gida, tinda azumi ake su yi masu abin shan ruwa.
Da sallama suka shiga Kulu ce taje ta buɗe qofar, bayan gaishe-gaishe ta wuce d'akin ta, Jameelaa na zaune bayan fitar Ramai, tana kallo tana bawa baby nono taga su Umaimah sai ta hau murna tana fad'in,
"Ahhh lale maraba da Umaimah, sannun ku Aunty hauwaa, barka da zuwa, qawata ammmm???"
"Sapnah,"
Sapnah ta tuna mata da kan ta, sai Jameelah ta qara qashe baki ta ce,
"Yauwa mai sunan mutanen can, sannun ku da zuwa bismillah ku zauna"
'Allah ya sa kun zo da kayan barka, ko dake na fi son kuɗi akan kaya na gaji da amsar kaya haka kud'in ne dai ko dubj ɗari zaku bani ba za su yi min yawa ba'
Wata leda ta gani a hannun Aunty hauwaa baki ta qara washe masu sosai tana masu maraba,
"Gashi azumi ake yi da an kawo abin motsa baki,"
"Wannan sai ku masu jego miqo ta nan wajen Goggon ta"
Miqawa Umaimahn babyn tayi suka dinga ɗaukan ta, wannan ya ɗauka wannan ya aje,hira sukai tayi ta na ba Umaimah labarin yanda sunan ya gudana bayan tafiyar ta.
"Kaiii amma nayi missing na kuwa so mu haɗu da Fateemaa, mun jima bamu haɗu ba sosai da sosai, anya tin kafin auren ta ma mun haɗu kuwa?"
"Gaskiya bana jin kun hadu, ai ta kusan haihuwa itama a wannan watan inshaa Allahu, kin ga sai kije suna,"
"Haka ne Allah ya kai mu,"
"Ameen"
Hira suke tayi kamar ba za a daina ba lokacin sallah yayi, Aunty Hauwaa ce ta miqawa Jameelaa ledar hannun ta, aiko kamar jira take yi haka ta cafke tana ta zabga godiya, dik sun zaci a sakin fuskar ta ne da mutunci da take dashi ya ta yi hakan, Aunty hauwaa ce ta tambayi bandaki Jameelah ta nuna mata hanyar waje, dan ba toilete a kowanne daki sai nasu, wajen ta fita Sapnah tace,
"Ohhh aunty Hauwa dama ki bari na shiga a matse na ke da fitsari,"
"Da kina zaune da fitsarin kuma baki yi magana ba? To da ban ce zani ba a zaune zakiyi shi? nima a matsen na ke sai ki jira ni,"
Matse qafa Sapnah ta yi tace taje ta na jiran ta ta dawo, ganin haka yasa Jameelaa tace ma Sapnah ta shiga na dakin su.
Da sauri ta cire hijabin ta ta shige band'akin dake cikin d'akin su ita da Umar dan nan ne kaɗai ke da band'aki dika gidan, sai ko na waje, daga shigar ta d'akin ta ci karo da komai a baje, gadon ba gyara, komai 1-1, ganin haka sai kawai taji ba zata iya shiga bayin ba, dan bata san me zata tarar ba fita tayi, ta wayance tace,
"Bari na jira Aunty Hauwa na shiga naga alamar kamar d'akin me gidan ne, d'akin miji ai ba a barin kowa ya shiga zan iya matse shi har ta gama"
"Ohhh su Sapnah manya,"
Haka dai sukai ta mata tsiya tana yaqe dik sai ta raina Jameelaan, dan dai ko mace bata zama mai tsananin tsafta ba ana so a same ta dai ba qazama ba, amma da alama parlourn ma dan mai aiki ta gyara ne da ba zai ganu ba, ai gwanda ta shiga na tsakar gidan ta san mai aikin ta gyara shi.
Suna nan Aunty Hauwaa ta dawo, ita ma ta shiga sai da tai fitsarin ta sannan ta yi alwala ta koma suka yi sallah, Umaimah ma tayi sallah suka ci gaba da hira, sun dad'e ba su haɗu sun yi hira haka ba.
"Yanzu ya zaki da maganar makaranta?"
"Wai yace haka zan koma kulu tana riqen ita, ni dai gaskiya ba zan iya karatu da yarinya ba a bari na yaye ta kawai sai na koma,"
"Ai yara ba su hana karatu, ki yi hakuri ki ci gaba,"
"Shikenan zan duba na gani"
Suna zaune Umar ya dawo, Sapna na shafa powder, Umaimah na tsokanar ta akan a mota suka zo a mota zasu koma ba mai gani a hanya balle ta damu da powder.
"Ke kika sani sai dai na shafa ɗin, kika ishen mijin ki zan aura,'
"Aiko da na yi farin ciki da hakan,"
"Sannu da dawowa Yah umar"
"Yauwa yau kune a gidan namu, ance kin zo suna kin tafi da wuri"
"Eh Yah kasan shi baya son yawan fita,"
"Yayi dai-dai ai nima bana son yawan fitan nan"
"Sarkin surutu yau me ya sami bakin ki?"
"Ina yini?"
"Hummm lafiya,"
"Dama ka san ta ne?"
"Mun haɗu randa aka kai ki surutu gare ta kamar redio,"
Dariya suka yi tayi har Sapnan Jameelaa kuwa ranta ya baci ganin yanda Umar din ya sake da Sapnah ana wani hira jefi-jefi ta dinga sanya baki gaba ɗaya sai ta ji jikin ta ya mutu.
Qarfe uku dai-dai Haroon ya iso dan ɗaukar su Umar ne ya shigar da shi gidan da kan shi nan ya ga baby again bayan sun gaisa da Jameelaah kafin su tafi saida ya aje kuɗi yace na baby ne, Jameelaa sai washe baki take yi Haroon kuwa sai b'ata rai yake saboda ya gama gano ta yar son abin duniya ce.
Bayan sun tafi Umar ya dami Jameelaa da maganar su Umaimah da Sapah, da yanda suka fara haɗuwa,cikin hasala da b'acin rai ta ce,
"Kai ni dan Allah ya ishe ni haka bana son surutun tsiya, sai wani zancen Sapnah kake ma mutane, ko dai son ta kake yi ne?"
"So kuma Jameelah Wanne irin so ? dan Allah ki daina wanan maganar tinda baki son maganar su na daina, kawai ina qara yi maki bayani ne akan yanda muka haɗu da ita, dan na kula kin b'ata rai da kika ji na san ta tin da,"
"To dai magana ta qare haka dan Allah ni, bana son na sake jin zancen wata wai ita Sapa take kowa oho,"
Umar ne yayi dariya sosai sannan ya kwantar da kan shi a bayan ta, tare sa saqalo qugun ta a hannayen shi ya ce,
"Ohhhh mata ta na kishi na ashe har haka? To kar ki damu Umar naki ne ke kaɗai,ba zan taɓa haɗa ki kishi da wata ba,"
Qara kwantar da jikin ta tayi a jikin shi,tana dariya itama,
"To to ya isa haka dagani gwanda ke, nikam inni sa'imun"
Bin shi tayi zata yi masa cakulkuli sai ga Kulu zata tambayi me za a dafa, basarwa suka yi Umar ya shige daki ita kuma ta kame kamar ba ita ba.
********************
"Aunty Hauwaa ni kam mutumin nan ya bani tausayi "
"Wa kenan?"
"Mijin Jameelaa mana matar wan umaimah"
"Ke fa kina da matsala sapnah yanzu mene na tausayin nashi? Mutumin da Allah ya azurta da komai na rayuwa dai-dai misali, wata nakasa kika ga yana da ita?"
"Kwarai kuwa dan kuwa bai yi sa'ar mata ba, ki duba d'akin ta kiga baqar qazantar dake ciki, wai a ce nan ne dakin miji? Ga wani uban wari daga ji daga toilet yake fita, shi yasa na qi shiga, namiji bai sa'ar mace me tsafta ba ai abun tausayi ne,kuma fa ki ga da alama bata aikin komai, karatun ma ta samu dama miji na son taci gaba amma wai ita bata so, wannan wace irin mace ce, ga son abun duniya, kiga da Haroon ya bata kudi ya ce na baby ne kamar za ta kifa,"
"Hhhhhhh baki da dama wajen bata lokaci ki karance halayen mutum, to yana baki tausayi ta ya za ki taimaka masa? Dan na san halin ki sarai yanzu sai kice zaki taimaka, wannan dai ba almajiri bane balle ki bashi sadaka,"
"Shi kam ba abinda zan yi masa dan taimaka masa amma dai kam akwai gyara,"
Umaimah ce ta aje naman da taje cirowa a freezer ya qanqare da kyar ta ciro ta ji suna hirar yayan ta sai tace,
"To ko dai za ki je a ta biyu ne? Kin ga sai ki taimaka masa kawai,"
"Keeee Umaimah rabani da shiga gidan qazama, ni mijina ni zan fara bare shi a leda kamar yanda zai bareni a leda shi kuma yayan ki second hand ne fa,"
"Baki abin magana aikin kuke ko surutu?"
"Yah Ishaaq sannu da dawowa gaskiya zan fara azumin magana, kowa ya d'aukeni a mai surutu, inna daina magana zanga wanda zaku na kira da me surutun,"
"Ai shi surutu ko ka daina yana nan maqale da kai, tinda shi kamar ciwon qanjamau ne da ka fara baka iya bari,"
"Zan baku mamaki kuwa" in ji Sapnah.
Ranar haka Umar da Sapnah suka kwana tinanin junan su, ba wai tinani irin na soyayya ba, tinanin umar akan sapanah shine yawan surutun ta, ita kuma tana tausaya masa akan qazantar da yake zaune ciki gashi Kyakkyawa kuma ɗan gayu...........
*In ba iyayi ba da kuma wata qullaliya a qasa meye na tinanin juna, Umar ina tausaya maka in Jameelaa tai leqe ta gano da tinanin wata kai bacci😂*
[08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 27:
Tin daga wannan ranar Mamalo bata sake komawa gidan Jameelah ba,haka itama Jameelaah bata neme ta ba, duk wata sutura da sarqa da d'ankunne haɗe da takalmi da jaka da ta so sawa sanyawa take yi ta k'wame k'wam abinta, Jameelah tayi yanda take so har ma fiye da hakan dan kuwa Umar ya tsaya mata, komai an kawo na abincin suna Ramai ta rud'e ta kid'ime k'warai dan ganin kala-kalar cimataku na abinci, Bukar daga makaranta kullum nan yake zuwa yaci abinci har zuwa dare sannan ya tafi gida, da a son shi ne ma idan yazo a dinga bashi renon d'iyar tashi saboda qaunar dayake yi mata, Baban Jameelaa ya zo sau ɗaya ya ga jikar shi, daga nan ne suka je gidan su Umar domin yin godiya akan alkhairin da ake ta yi masu kala-kala da shi da iyalin shi, Daddy ya karɓe shi hannu goma ma ba biyu ba saboda mutuntawa, dan kuwa sai da Baban Jameelaa ya gano inda Umar ya gaji arziqi da mutunci, fatan shi Allah ya gwada masa nashi iyalin sun zama mutanen kirki kamar haka, yanzu dai ya samu Bukar ya kintsu, yana yiwa Ramai da Jameelaah fatan shiriya suma,a tare suka yi sallar Azahar da Daddy sannan suka dunguma dikan su har Daddyn dan ganin jikar su, Daddy ya yi mata addu'a sosai sannan suka yi sallama da Baba ya koma wajen aikin shi, Daddy kuma ya wuce Abuja domin gabatar da aikin shi shima.
Umar akan dole yake zuwa asibiti saboda kula da marasa lafiyar da suka zama dole akan shi, gashi kuma gidan kullum a cike yake da mutane duk yanda ya so zama dole ya basu waje, 'yan uwan Mum da Dad ne yawanci sannan ga 'yan uwan Ramai da Baban Jameelaah gefe ɗaya ga mutan unguwar su da Jameelah ta dinga shigewa daf lokacin da taga ta kusan haihuwa dan su bata gudummawa kuma babu laifi sun bata kuɗi sosai da kayayyakin jinjira.
Ramai har wani ja take a kwanakin nan tsabar yanda ta yi haske ta yi qiba, sai wani bud'a hanci take ita a dole uwar me jego,Jameelaa ta ware mata kaya na musamman tana sauyawa itama dan bata son a raina mahaifiyar ta, ga sarqa da dan kunne masu kyau da takalma duk ta bata ,gaba ɗaya wanda ya san Ramai me shinkafa da wake a da ba lallai ya gane ta ba yanzu, sai a zaci tana da Hassana ko Hussaina ne.
Matan gidan su na da da matan layin da suke dan zumunci a da sai gulmammaki ake yi akan su ita da 'yarta, wasu kuwa murna suke taya su na samun ci gaban rayuwa da suka samu.
(Allah ka sanya mu a cikin masu taya 'yan uwan mu musulmi murna akan ci gaban su ka kare mu daga cikin bayin ka masu yawan qyashi da hassada)
Jameelaah ce zaune ta na doka murmushi saboda kallon kayan da ta baza zata sanya ranar sunan da ya samu halartar manyan mata na dangin su Umar da kuma qawayen ta na social media da yaran masu hannu da shuni na makarantar su ta boko, a wannan rana Jameelah ta yi kuma ta na kan yin yanda ta so dama abinda bata taɓa zaton zata yi shi ba, dan kuwa ko a cikin unguwannin masu kuɗi aka yi sunan da aka yi a nata an kai aya,wani hamshaqin gidan ɗaukan hotuna aka gayyata dan daukan hoton sunan Humairah, duk wanda ya halarci taron nan ya ci ya sha ya yi guzurin abinci.
A ranar Mamalo ji ta dinga yi kamar kar ta je, amma haka ta hakura ta shirya da yamma liss, ta sanya dinkin ta mai kyau abunta wanda Sadeeq ya d'inka mata shi da hannun shi, atampa ce mai kyau ta amshi jikinta ta kafe d'auri mai kyau, koda ta zo mutane dik sun ragu d'aki ɗaya Jameelaah ta ware ta zuba kayan gifts da ta samu, kuɗi kuwa ta same su da yawa wajen qawaye da kuma 'yan uwan mijin ta, sanda Mamalo ta isa gidan Jameelaa na d'aki tana shayar da Humairah dik ta gaji, amma jira take yi yarinyar tayi bacci ta sanya ta a gadon ta, ta sake wasu kayan ta fita ta qara yin barazana, Mamalo na ta gaisawa da mutanen da ta sani ana ta yi mata fatan itama Allah ya sauke ta lfy, tana masawa da Ameen.
Jameelaah ce ta fito ɗauke da Humairah, (sunan da suke kiran A'i'shaa kenan) ta sauya kaya da wata shadda milk da aka zubawa uban aiki ruwan zuma mara duhu, sai ta kafe d'auri mai ban sha'awa ga qamshin turare na tashi, sarqa harda ta qafa sai da ta sanya irin ta mutanen india, qaryar mutum yace bata ratsa shi ba saboda haɗuwar da ta yi.
Mamalo baki sake take kallon ta, dan kuwa bata zaci Jameelaah ta shiryawa sunan har haka ba,nan take zuciyar ta ta raunana ta fara waswasin anya kuwa zata iya kamo Jameelah? Wani yawu ta had'iya mai dumi ta fara gaida Jameelan tare da yi mata barka,sai ta d'akko ledar kayan jaririyar da ta zo da shi ta ajiye mata a gaban ta,a cikin ledar kuwa riguna ne guda biyu, da atampa ɗaya sai takalmin yarinya biyu da sabulu sinqi ɗaya.
Jameelaah bud'a ledar tayi ta kalla sai tayi murmushi ta ajiye a gefen ta tare da yin godiya.
"Ramai ki ce da Khadeejah a kawo ma qawata abinci,a sanya mata komai da komai dan Allah,"
"To shikenan bari na duba ta ina jin tana can tana gyara kitchen,"
Ramai ce ta samu Khadeejaa ɗaya daga cikin dangin Umar ne, da sukai ta taimakawa a sunan dan aikin ya yi ma Ramai yawa, Umar har ya yi magana da Mum a sama masu mai aiki babba wadda zatana kula masa da gidan da iyalin shi, sun tsayar bayan suna za a kawo mai aikin, Ramai tayi iya yin ta dan ta hana a kawo kowa amma sunqi hanuwa sunce in bayan suna ta koma wa zai na kula da su? tace ah ah ai ita zata zauna har bayan sunan Mum tace ai ba za a bar Baba shi ɗaya ba, ta dad'e anan ya kamata ta koma gida,ba dan ta so ba ta hakura dole zata koma gidan nasu.
Babban trey ne aka doro abinci kala-kala akan shi da abubuwan sha sai wata qatuwar leda da aka ciko da abinci again aka dire gaban Hajiya Mamalo, ganin kayan kwalamar da ke gaban ta ne ya sanya yawun ta ya kai maqura wajen tsinkewa, bata b'ata lokaci ba kuwa ta sa a gaba tai ta ci, Jameelaah na murmushin mugun ta, sai da ta kammala ci ta yi nak sukai ta hira, dan kuwa ta sake mata sosai saboda daga ita sai mamalon ne ba wasu important mutane da take jin kunya , sun sha hira ba kamar wancan zuwan ba, har mamalo taji bata kyauta ba data dinga jin kamar Jameelaa ta wulaqanta ta rannan sannan ta janye qudirin ta na son fin Jameelah a abubuwan more rayuwa na yau da gobe dama ba halin ta bane haushin da aka bata ne yasa ta ɗaukan wannan alwashin,sannan ta kulama ba zata iya yin competition da Jameelah ba.
Magrib na gabatowa Mamalo ta ma Jameelaa sallama, Jameelaa ta tashi dan raka ta, a hanyar su ta fita daga gidan ne Mamalo ke tambayar Jameelah Umaimah dan tinda tazo basu haɗu ba.
"Tazo da ita akai suna akai komai da safe ta koma dan kuwa kin san Malam kamar wani mayen ta haka yake baya barin ta ta sake ko kaɗan,tun wajejen 11am ya kawo ta ya dawo around 3:30pm ya ɗauke ta"
"Ikon Allah Jameelaa ina matuqar tayaki farin cikin yanda rayuwar ki ta kyautatu, dibi har turanci kike yi abun ki, Allah nima ya kaini wannan matsayin kema ya qara maku ɗaukaka,"
Murmushin qasaita Jameelaa tayi, sannan tace,
"Mamalo baki da wayo na baki shawarar yanda zakiyi ki tara kuɗi kema kiyi suna irin nawa amma kin qi, yanzu duba ki ga sunan nan dana yi, da kud'in bashin dana faɗa maki da shi na kashe wata yawar ko Umar be sani ba,gashi yanzu na maida kud'in har da riba, na fita kunya ko ban fita ba? dik da dai gaskiya Umar ma da mahaifan shi sun taka rawar gani sosai, amma ba dan kud'in dana ranta ba da tini na san ba zan fita kunyar qawaye na gaba ɗayan su ba,"
Murya qasa qasa sosai suke yin maganar saboda Jameelah bata so aji tana zuga Mamalo, Mamalo ce ta yi ajiyar zuciya sannan tace,
"Jameelaa yanzu inna ce zan yi aro wajen wa zani? Wa zai ara min kuɗi masu yawan da zan shiga na fita kamar yanda ki kai,kar ki manta mijina qaramar sana'a da aiki yake da"
"Kar ki damu indan wannan ne a inda na aro kema a nan zan aro maki, a ajin mu yaran masu hannu da shuni ke yin adashi, dik wata kowa na saka 20k su goma ne, ta haka suke siyan dik abinda suke so, ni kuma da sukaji waye mijina da surikina shine dana nemi aban d'iba na biyu aka bani, na samu Allah ya taimaken na sai kaya na d'inka tun a lokacin, na sai wasu daga abubuwan da aka raba a sunan nan, Umar ma ya sai min kaya masu kyau da tsada dan haka bai ma san nayi ba a zaton shi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 30