Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba ina ji kuma ina gani inshaa Allahu," "To kulu zan yi bincike akai, yanzu ki koma gida kar ta neme ki na gode," "Ta san na zo nan dan da izinin ta na zo nan, yana daga cikin laifukan ta shine satar fita, daya fice ta sa qafa ta fice itama," "To yayi haka kulu, zan bincika na gode," Dubu ɗaya ta bata tace ta hau abin hawa ta koma gida, godiya tayi ta koma. La'asar ake kira lokacin da ta isa gida ta tarar da Jameelaa bata gidan, ta kuma tabbata bata fita ba sai da ta tabbatar Umar ya ci abinci ya koma, kad'a kai tayi ta faɗa kitchen dan ɗora abincin dare, ta sake gyara inda aka b'ata. Jameelaa ce ke ta bulayin neman layin da aka kaita jiya, in an shiga layi ta ce ba nan ba, har suka shiga wani layin da ke kusa dana bokan nata, yana zaune cikin abokai ana zuqe-zuqen kayan maye, shi sigari yake ta busawa, yana hango ta cikin adaidaita sahu ya sunkuyar da kai, sai da suka wuce ya bi ta siririyar hanyar ya d'iba da gudu zuwa gida, shagon shi ya maida kamar na boka, yana tsaka da saka rigar bokan cin shi ya ji ana buga qofar, surkulle ya fara yi, yana faɗin a jira shi, yana gamawa da 'yar matumbura. Sai da ya shirya tsaf ya zauna sannan yace a shiga, shiga ta yi tana ta washe baki ta zauna tace, "Ta kan tsamiya ta taimaki boka, boka na zo godiya ne, aiki yayi kyau, shine nace dole na zo na kawo gaisuwa ta musamman" "Tiiirrrrr, sirrrrr, firrrr, bucaaaaa, kin kyautaaa, kin kyautaaa, hakan yayi daidaiiii, Ta kan tsamiya na jin ki, kuma itama ta ji daɗi," "Boka sai dai akwai wani hanzari da nake tafe dashi a yanzu, jiya da kyar yarinya ta ta farka daga baccin nan na karya sihiri, dan saida muka je asibiti aka ce mana maganin bacci ta sha," Dan zazzare ido yayi sannan yace, "Kar ki damuuu, ai su likitoci basu so a ce basu iya aikin su baaaa shine kawai, amma maganin karya sihiri na baku dika, kuma ya karye, sai dai akwai matsala aikin Uwar mijin ki bai yi ba, sai an......." Wayar ta ce ta katse masu hanzari, janyo jakar ta tayi ta duba, no Mum ta gani nan ta nuna masa, ya yi mata izinin d'agawa sai kace wayar shi haka ta bi umarnin shi ta d'aga,bayan gaishe-gaishe ne Mum tace, "Jameelaa lafiya kuke kuwa? Rabon ki da zuwa gidannan har na manta, ko a waya baki kira a gaisa in ba ni na kira ki ba, ko akwai wata matsalar ne ki sanar da ni?" Sai da ta gama rashin kunya da baki da ido sannan tace, "Ni ba komai kawai 'yan zuwan ne basu zo ba, amma dik sanda na so zuwa zan zo" Tirqashi ! Mum ce ta miqe tsaye sakamakon saurarar kalaman Jameelaa da tayi, lallai maganar Kulu akwai qamshin gaskiya aciki, "Jameelaa lafiyar ki kuwa kike yi min magana a haka?" "Qalaou nake ni yanzu bana nan na dan fita unguwa in anjima munyi magana," Kit ta kashe wayar, "Kinji me nake fada makiiii,aikin ta bai yi baaa, sai an sake aiki akan ta, ki tube a yi maki aiki,ki tubeeee, tubeeee, tubeeee" Ai jiki na rawa Jameelaa ta tube, kallon da ya ke binta da shi ne ya fara tsorata ta, gashi yau bashi da maganin da zai sanya mata, dan haka ya hau borin qarya yana faduwa yana miqewa, shi a dole aljanu ne suka zo, "Lale maraba da zuwan ku na Nijer, maraba maraba, yauma ta dawo a yi mata aiki, a raba ta da Uwar mijiiiii, ta dawo a yi mata mai sauqiiiii" Nan ya fara da fesa mata ruwa kamar jiya, daga nan ya fara shafe mata ruwan daya fesa mata, tin tana daurewa har ya fara bata wani yanayi a jikin ta, (kun san dai mutuniyar ku, ba sai anyi ta dogon bayani ba😂) nan da nan cikin sauqi ya same ta, ita da ake ma aiki sai ta dawo tana aiki, nan suka samu suka gama lalacewar su, ta gyara jikin ta tsaf ta tashi, "Dama irin wannan ne aikin? Aini jiya baka sanar dani ba, ga mallakar miji na samu, yau kuwa ina fatan na samu ta uwar miji, aikin ka akwai biyan buqata ta kowanne fanni," Kudi ta laluba ta damqa masa, ta goye Humairah ta fita, a gaskiya ba qaramin nutsuwa ya samu da ita ba, da da yanda zaiyi kullum tana zuwa ai shi bai da case. "Ki daina bani kudiiii bana soooo, bana soooo, aje su cannnn Ta kan tsamiya zata daukaaaa, ki dawo gobeee sai kinyi wata kina zuwa kafin aikin ki yayi kyau, shi irin sihirin nan na dindindin yana buqatar ayi wata ana yin shi, in ya kama jiki har abada ne, sai kin mutu aljanin dake baki kariya zai rabu dakeeee," "Lallai da na zama mai sa'a na mallaki umar da iyayen shi har mutuwa ta,da kuwa na mallaka maka dukiya kaima mai tarin yawa,na yi maka alqawari dik abinda na samu zan raba uku na baka kashi ɗaya," "Bana son kudiiii, bana soooo, bana soooo, sai dai ki kawo na yankan Takan tsamiya," "Shi ɗin dai za a Kawo babban boka mai babban aiki, bari na koma ni kar a neme ni a ga shiru na gode bokan duniya, Ta kan tsamiya ta taimaki babban boka" Nan ta fice tana murna, aikin akwai daɗi kuma akwai biyan buqata. (Wannan shi ake cewa tsafi gaskiyar me shi) Yau ma sai magrib ta koma gida Umar bai koma gida ba,  kulu na kula da dik abinda take yi, wanka ta fesa mai kyau kamar ba abinda ya faru, ta sha kwalliya sosai koda Umar ya dawo ya ganta wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar shi, Humairah ma an mata gayu sai qamshi take zabgawa. Ɗauke take da Humairah ta je yi masa Oyoyo, dikkan su ya haɗa ya d'aga su sai dariya suke yi gaba ɗayan su, kafin daga baya ya ajiye su ya amshi Humairah yana yi mata wasa, ita kuma Jameelah sai ta amshi jakar shi suka shige ciki. 'Kaiiii da na san da wannan boka tin asali da na je, da Umar ya dad'e ashe mallake a hannuna, rashin sani ya fi dare hudu, ba zan kuwa wasa da dama ta ba, sai na ci gaba da zuwa na wata ɗayan nan cirr, na samu a mallakan shi na har abada' Abinci ta zuba masa ya fara ci ya yi masa daɗi sosai abincin amma ba halin yayi santi tinda ba ita ta dafa ba, in yayi santi sai tace yana yabon girkin wata bayan ita ba tai masa ba da kan ta. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya daga baya ma idan zata fita yawon ta sai ta aje ma Kulu Humairah ta fice, dan kar a asirin ta ya tonu sai take raba qafa, taje gidan su sannan ta wuce, ko in ta dawo daga wajen bokan ta je gidan nasu. ************************ Umar na duba marasa lafiya ya bar wayar shi a Office, koda ya koma ya tarar da missed calls da yawa,No Umaimah ce sai ta Mum, yana cikin dubawa Umaimah ta sake kira. "Assalamu alaikum, sweet sis," "Uncle Umar wa'alaikumussalam,albishirin ka" "Sapnah me kike nufi da uncle? Kar ki faɗan umaimah na ta haihu sai yanzu ake sanar da ni?" "Kwarai da gaske Umaimah ta haihu lafiya  mun samu mace tin da ta fara naquda nake ta kiran ka ba ka daga ba ai, Mum ma nan sai kiran ka take yi shiru baka ɗauka ba, so kaga kenan ba laifin mu bane" "Haka ne baku da laifi me muka?" "Mace muka samu," "Masha Allah,Allah ya raya mana, gani nan zuwa na gama abunda nake yi dama kuna ina?" "Muna gida a gida ta haihu," "Ok sai nazo to," Tattara wayoyin shi yayi ya rufe office sai gidan su Umaimah. Murna ta hana shi rufe baki yana matuqar qaunar qanwar shi sosai, gashi ta haifa masu yarinya,Humairah ta samu abokiyar wasa. Jameelaa ya kira ya sanar da ita yace ta kira ta yi wa Umaimah barka. Cikin murna kuwa ta kira qawar ta ta, daga wayar Sapnah tayi dan Umaimah na bacci. "Qawata qanwa ta kuma maman Baby barka... barka.. barka, kin sauka qalaou?" "Lafiya qlou ta sauka, kina magana da Sapnah ne," "Mtsssss me ye naki na amsa wayar mutane ke kuma karere, ke kenan ba zaki zauna gidan yayar ki da kika zo ba sai kin je gidan Umaimah, salon ki kwacewa mutane maza ko? An tsufa gidan tsoho ana neman wajen sakad'a d'uwais ba a samu ba shine ake bin mazan mutane, to kurwar mazan mu kur ba ki isa samun mazauni a zuciyar mijina ba, ni nafi qarfin ki bari kiji na faɗa maki tun yanzu dan ki san na san menene qudirin ki akan Umar d'ina, aikin banzaaa kawai ko da boka kike yawo akan ki baki isa mallake min miji ba,duk ki gama asire-asiren naki munafuka kawai, in ba rashin imani ba har yarinya qarama kike yiwa asiri? To ta Allah ba taki ba,kuma kin kai qarshen iskanci da asiri tinda kin taɓa ni " "Keee malama dakata min! Sapnah ce fa kike magana da ita ba wata ba ni me na yi maki?" "Zaki ga me kika min in na zo gidan, zaki ga hauka ganin idon ki," Sapnah riqe wayar tayi a hannu hawaye na zuba mata cikin tsananin takaici, tinda take ba wanda ya taɓa yi mata rashin mutunci irin haka, harda zargin tana asiri? Akan me zatai asiri bayan tana da Allah. "Me ya faru kike kuka? Ke da wa?" Aunty Hauwaa da Mum ke mata wannan tambayar, bata iya amsa su ba ta aje wayar Umaimah ta fita daga gidan gaba ɗaya, wayar Aunty Hauwa ta ɗauka, ta ga sunan Jameelaa shine last call da aka dauka. "Ikon Allah ! Mummy kiran Jameelaa ta d'aga fa take kuka, ko me ya faru kuma sai Allah," umar yaga shigar ta gidan Ishaaq tana kuka amma bai san dalili ba, ko me ya same ta kuma oho? Sai ya ji ranshi na masa zafi dan ganin kukan ta, amma son ganin umaimah da babyn da aka haifa masu yafi yawa a ran ranshi dan haka sai ya fita ya nufi gidan Umaimah. Mum na ɗauke da jaririyar ya shiga nan suka fara yi wa juna barka, "Ina Umaimahr?" "Tana d'aki bacci take an yi mata wanka, taci abinci sai kuma ta b'ingire da bacci" "Allah sarki ina maqale matan mijin ta yake naga ban gan shi ba?" "Yana kasuwa, ana ta kiran su shi da yayan nashi ba su d'aga ba, sunje store fidda kaya" "Allah sarki na riga shi ganin baby, sai yazo na san ya dame mu akan ba a sanar da shi ba.....Mum me ya faru naga Sapnah ta fita tana kuka?" "Ka gan mu muma tambayar da muke wa kan mu kenan, ana zaune lafiya lafiya, ta na sanar ma da mutane haihuwar sannan tana amsa wayar Umaimah sai matar ka ta kira sukai magana shine ta aje ta fita tana kuka" "Subhanallahi ! to me ya faru? Me tace mata? Bari dai naje na ji daga bakin Sapnah me aka yi mata" Basu babyn yayi ya fita zuwa gidan Ishaaq, ya na zuwa sai ya hau buga gate, ya dad'e yana bugawa kafin Sapnah ta leqa idon ta yayi mugun ja hancin ta ma haka, tana ganin shi ta sake fashewa da kuka, da sauri ya qarasa gaban gate ɗin, ya durqusa kamar yanda tayi, "Sapnah dan Allah ki sanar dani me ya sa ki kuka? Kin dai san dik wanda aka haɗa da Allah an gama komai ko? Ki fad'an meke zuciyar ki tsakanin ki da Allah," Zayyana masa komai daya faru ita da Jameelaah tayi, sannan ta qara da cewa, "Yah Umar tabbas na san zuciyata ta kamu da son ka, kuma ban san sanda hakan ta faru ba, na tabbata saboda kyawawan halayen ka ne ya sanya, amma na hakura na danne a raina ban taɓa yunqurin kai kaina wajen ka ba, dik da a baya na so yin hakan, sai na ga bai kamata ina mace nai ta cusa kaina wajen ka ba na hakura, dan ko no da kace na baka ina sane na hana ka,kawai shine matar ka zata zargeni da yi maka asiri, shirka fa kenan? Akan namiji sai na sab'awa Allah na?" Kuka ta sake fashewa da shi Umar kuwa ji yayi wata iriyar soyayyar Sapnah mai tsafta na fizge shi, kallon ta kawai yake yi bai ma san me zai ce mata ba a wannan yanayin da ya shiga wanda shi kan shi bai san da wanne suna zai kira shi ba, abinda kawai ya sani shine ba zai taɓa bari Sapnah ta kub'uce mashi ba. "Kutum......bur......ubancan kayyasa, yau za a mutu a unguwar nan me nake gani haka?" Ashar din da suka ji ne ya sanya su juyawa gaba ɗayan su a tare sannan suka miqe daga durquson da suka yi, tin kan adaidaita sahun ya tsaya ta dira, kan Humaira kuwa ya buge da qarfen adaidaita sahun, kuka ta fasa mai qarfi da gigicewa, amma Jameelaa ko a jikin ta, Umar ne ya tafi da sauri zai amshi Humairah, Jameelaa ta hankada shi baya, "Kar ka kuskura ka taba mu maci amana, ashe kana nan ma sanda nake mata magana tana nuna min bata san meke faruwa ba, kuna nan kuna cin amana ta, yau sai an mutu, dan uwar ki fito nan munafuka kike b'uya a bayan mijina," Nan da nan kuwa 'yan gulma suka taru ana kallon su, faɗa ba sabon abu bane a wajen Jameelaah dan kuwa sanda tana lungun su har da maza yi take yi, 'yan kallo kuwa ta gan su kala-kala  waɗannan tsirarun ba za su hana ta ci wa Umar da Sapnah mutunci ba,shi kuwa Umar kunya dik ta gama baibaye shi,Sapnah kuma kuka ba baki, ita a duniya tafi son ai ta hira ana darawa ta tsani faɗa da tashin hankali. Umaimah data tashi a bacci ce tace, "Mum hayaniya nake ji a waje, kamar ana faɗa," "Faɗa kuma? Wanne irin faɗa anan unguwar taku?" "Nima dai abun ya ban mamaki, dan bamu saba jin hayaniya haka ba," Nan dai Aunty Hauwa ta aje Muhammad ta sa mayafi ta fita, tana ganin abinda ke faruwa ta koma ta kira Mum, kunyar duniya ta gama kama Mum, jin irin ruwan ashar da rashin mutuncin da Jameelaa ke saukewa Umar da Sapnah, har da kiran su Mazinata. Saphan nata aikin kuka, dan ita kam cin fuska an gama yi mata shi. "Jameelaa muje ciki ayi maganar a ciki saboda kinga mutane na ta kallon ki mutuncin mu kike zubarwa anan fa," Tankad'a Mum tai sai da ta fadi qasa warwas irin fad'uwar nan ta bazata, sannan ta nuna ta da yatsa tace, "Ku har wani mutnci gare ku, d'anki na waje yana zina da wata kuna ciki a zaune yana nan yana cin amana ta, amma kike maganar mutunci, wanne mutunci ya rage maku kuma?" Sapnah ce ta yi saurin d'aga Mum daga qasa, Umar kuwa fuskar shi tayi jawur saboda tsananin ɓacin rai da shiga tashin hankali da baqin ciki akan abinda yake gani a gaban shi,Jameelahn shi mai natsuwa da kamala da hankali ce yau ta tura mahaifiyar shi abar son shi da qaunar shi qasa????........... *Hummmmmm lallai ne Jameelaa, Umar yau ka nuna min ka haihu cikin Mum😡* *Makaranta ina son jin qarin bayani a game da zuwan Jameelaa gidan boka, da nasarar da take samu, akwai wadda ta fahimci abinda na fahimta kuwa? Sai naji amso shin ku zan gane ko akwai mai irin tinani na ko wadda ta fini ganewa* *Haermeen Haermmearh love u XoXo❤* [09/09, 10:32 am] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 38: Juyawa tayi zata ci gaba da yi ma Umar masifa taji wani gigitaccen mari ya ziyarce ta wanda ya sa ta tafi da baya zata faɗi qasa, da sauri ya tare goyon nata ya kwance 'yar shi cike da fushi mai tsanani ya qarasa turata qasa, zai bi ta ya take Mum ta kira sunan shi da qarfi, juyawa yayi idon shi ya kad'a yayi jawur, Mum bata taɓa ganin ɗan nata a wannan yanayin ba duk da yanda kowa ya san masu sunan Umar da zafi da faɗa nata Umar ɗin nada sauqin hali da sanyin hali, ashe dai ba a taɓa samun wanda ya yi pressing ɗin shi irin haka bane, ita kan ta sai da ta ji shakkar shi ta kama ta , sai ta kasa furta masa komai,Haroon da Ishaaq kusan a tare suka iso gidan, gani suka yi qofar gidan nasu an cika ana ta kallo,haka suka kutsa suma nan suka yi arba da abinda ke faruwa, Haroon ne ya je gaban Umar ya dafa kafad'ar shi yace, "Broth ko me ke faruwa kayi hakuri mu shiga ciki, sai a gama maganar a cikin gida, kaga mutane suna ta kallo" "Da wa za a shiga gidan? Ni Umar ni nake auren Jameelaah Jameel ko? to yau na sawwaqe mata aurena akan ta da igiya ɗaya, ko gidana ban amince ta shiga ba, in kuma zata shiga gidan ku ni zan tafi na bar maku gidan," "Ta shiga ta yi mana mi? Muje ciki " In ji cewar Haroon da tun asali ya washi Jameelaah, tun da ya ga haka ta faru kuwa ya san asirin ta ne ya tonu. Nan suka shige suka rufe gate suka bar Jameelaa tsaye baki sake, ta kasa tantace ita Jameelan aka saka ko wa? Ganin kowa ya watse an barta a wajen, kuma an  shige da Humairah ta kwalla wata qara cike da hargowa ta bi su, ta dinga buga gate tana kuka tana baiwa Umar hakuri, akan ya maida ta d'akin ta ta tuba ba zata sake ba, sai kiran sunan Mum take tana kuka,ba wanda ya kula ta, suka shige ciki,da ta dame su Umar ya zabura zai je ya mata rashin mutunci Mum ta hana shi Umaimah ta tsorata da ganin Umar a wannan yanayin kai har Mum din ma, dan tinda ta haife shi bata taɓa ganin shi cikin irin wannan yanayin ba , Umar mutum ne mai hakuri da son 'yan uwan shi, tare da tausayawa na qasa da shi. Amma yau gaba ɗaya ya sauya,ko kalar fukar shi ta koma jawur kamar qosai. "Umar kaayi saurin yanke hukunci da baka sake ta ba, gata da yarinya tana shayarwa, kishi ne kawi ke damun ta ba wani abu ba," "Mum dan Allah ki bar wannan maganar, kishi hauka ne? Akan ta aka fara zancen kishiya? Ko ta taɓa jin nace zan yi aure, meye bana yi mata dan kawai ta ji daɗi,dik abinda take min kauda kai nake yi dan a zauna lafiya, bata isa ta taɓa mahaifiya ta a wannan yanayin na kyale ta ba, ban haifu ba ma kenan" "Yah wai sakin ta kayi? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" "Ni dama na dad'e da sanin halayen ta, kune baku gane wace ce Jameelaa ba, har bincike sai da na yi akan ta, ba mutanen kirki bane ita da mahaifiyar ta, mahaifin  ta ne mutumin kirki,Allah ya kyauta ya sa hakan shine mafi alkhairi, in da rabon zama a gaba Allah ya shirya ta," "Babu ma rabon zama, ba wadda ta isa ta taban mahaifiya ko mahaifa na kyale ta," "To Allah ya kyauta mana" "Ameen" Kowa ya amsa, sai sannan Haroon ya fara neman jaririyar shi, Ishaaq ya dauke ta ya yi mata addu'a, Haroon ma haka, nan aka fara hira kamar ba abinda ya faru, Umar kuwa ya kulle idon shi yayi shiru, yana jin rad'ad'i a ran shi, wanda ya san na farko dai akwai wulaqanta masa mahaifiya da Jameelaa tayi, na biyu kuma akwai rabuwar shi da macen da yake tsananin so, sannan na uku sanin mummunan halin Jameelaa da yayi, tabbas yayi nadamar fadawa soyayyar ta, Sapnah ke riqe da Humairah, wadda ta lafe a jikin ta kamar mai jin bacci, lokaci zuwa lokaci tana satar kallon Umar, tausayin shi ne fall zuciyar ta, can kamar wanda aka mintsina, ya ɗauki waya ya kira Kulu, tana ringin ta ɗauka tayi sallama, ya amsa sannan yace, "Kulu ki rufen gidana ki kai min keys gidan Mum ki zauna acan ko waye ya je shiga in bani na dawo ba kar ki bari koda kuwa Jameelaah ce, ki rufe har d'akuna da ko ina," Ko amsar ta bai jira ba ya kashe wayar, ya sake kulle idon shi, kowa shiru yayi, Aunty Hauwaa ce ta fara fita, sannan Sapnah ta miqe dan bin bayan ta, ajiye Humairah tayi wajen Mum ai kuwa ta sa kuka, ta riqe mata riga, har qirjin ta na bayyana ta sama, da kyar ta samu ta amshe , Umar ne yace ta miqa masa ita, zuwa tayi ta miqa masa yarinyar, ta tsaya tana kallon shi, sannan ta juya ta kalli sapnah, daga qarshe taje wajen Umar, kowa sai dariyar qiwar ta yake yi, banda Umar da Sapnah, wanda su kadai suka san mene ne a zuqatan su, Umar sai kallon ta yake da yanayi na tsantsar so da qauna, yau ya tabbata ita kaɗai ce zata iya son shi ta haɗa da dangin shi, murmushi ya yi mata a hankali ya furta, "Thank u" "For what?" "For everything" "Ur welcome, and thank u too" "For what?" "For staring" Murmushi sukayi, ya qarasa karbar Humairah sannan ta yi ma Mum sallama, da mai jego ta tafi. A nan Umar da Mum sukai magrib, dan kuwa sai da Mum tai wa Umaimah wanka sannan Haroon ya kira Aunty Hauwaa akan su zauna zai maida Mum ya d'akko Kulu ta ci gaba da kula da Umaimah da babyn su. Haka kuwa aka yi ,Umar ma a gidan su ya kwana ranar, dan kuwa Humairah ba a saba zuwa da ita gidan ba bata saba da Mum ba, kuka ta dinga yi da za a bar ta, dan haka Mum tace ya kwana kawai. ********************** Jameelaa da ɗan sauran dubu ukun dake jakar ta ta yi gidan bokan ta, dan kuwa bata ga ta zuwa gida ba, in bata je an juyo mata da kan Umar ba ya maida ta a daren. Koda taje a kulle taga shagon dan haka ta zauna anan, tana jiran shi dik inda yaje ya dawo ya yi mata aikin ta ta koma d'akin ta,sai bayan isha'i ya koma gidan, yana ta zuqar sigarin shi, shida mai adaidaita sahun daya kawo ta ran farko. Tana ganin su ta miqe ta na hamdala, "Boka ka taimake ni... dan Allah ka taimaken ka sa mijina ya maida ni gidana, ya sakeni ya raba igiyar dake riqe da auren mu,na shiga uku inna rabu da Umar, shine rayuwa ta, dan Ta kan tsamiya ka taimakamin," Kallon juna suka yi da abokin shi, dik da ba wani haske sosai, amma har sun karanci junan su, "Bude qofar muje ciki," Bude qofa mai adaidaita yayi  suka shiga gaba ɗayan su, nan boka ya zaro kayan aiki, kamar sokuwa kanta ya toshe ta kasa gane komai ba gaskiya bane. "Gaskiya kinyi azarb'ab'i, ke da aka ce maki sai anyi wata ana aiki, shine kika kasa hakuri watan yayi? Yanzu haka daga zuwa binne mahaifar karya muke, dan ya zama sai yanda kikai da shi daga qarshen watan nan, gashi nan kin rusa mana komai, dole a sake aiki daga farko, amma yau tinda auren ya qare ki kwana a kwana ana yi maki aiki, shima wannan da kike gani yana taimaka min wataran musamman binne abubuwa a bayan gari, kamar yanda muka je binne wannan mahaifar karyan da shi, maza ki tashi ki tube a fara yi maki aiki, kai jeka daga waje, in za a miqo abu zan kira ka," Mai adaidaita waje ya fita yana ta murna, yau zasu yi till down suna raqashewa, ruwa aka fara fesa mata, zuciyar ta ba daɗi samm, ko sha'awa bata da shi, haka ya fara sarrafa ta, yana cikin sarrafa jikin ta, tinani ya fado mata, me yasa yau bai tuma ba na zuwan aljanun Nijer? Sannan yau kwata-kwata bai zancen Ta kan tsamiya ba, ba wani surkulle yau, ga shi an sake ta, anya kuwa bokan gaske ne wannan? Sai zuciyar ta ta fara qaryata shi sai wata ta gaskgata shi, tace da baya ci ai da kwanaki baki samu nasarori wajen Umar ba harda kud'in da kika tara a dakin ki da baki yi nasarar samun su ba, tinawa da kudin data tara a dakin ta ne yasa ta bangaje shi ta miqe tsaye, Tsawa ya

Chapter 23 of 30