san wannan bala'in da take ciki dik Mamalo ce ta jefa ta a cikin shi, da ta sani da bata amsar mata bashin ba, gashi komai nata ya tsaya cak bata samun ko sisi tunda ta karb'i bashin har lokacin mutuwar Mamalon ita da Umar a rana sai ya bata 5k, wataran ma aje kuɗi yake masu yawa yace in tana so ta d'iba ta yi hidimar gaban ta,amma yanzu ko ɗari biyar bata haɗa su tinda abunnan ya faru baya barin sisi ma a gidan dika,hanyoyin samun ta sun qare tasss, rarar 30k data samu a sunan Humairah da ta san haka zai faru data adana bata kashe a banza ba, a qallah ai da ta d'aga dubu saba'in yanzu gashi ɗan abinda ya rage a ciki take ta kuɗin mota shiga can fita can duk dan ta rufawa kan ta asiri.
Har Umar ya shiga parlourn bata sani ba tana nan zaune tana tinanin da ba mafita, sallama yayi ta yi kafin daga baya ta tsorata ta miqe tsaye tana amsawa.
"Ya akayi ne? My love kwana biyu na kula kamar baki cikin nutsuwar ki me ye matsalar ki ne? Faɗa min na yi maki maganin ta,dan kin san ni a duniya bana son na gan ki cikin damuwa ko ya ya ne ba tare da na kawo maki qarshen ta ba"
Hawaye ne ke qoqarin zuba mata ta danne, ba zata yi subul da baka ba, dole ta rufe magana har sai taje ta saida sarqa, in kuɗi bai cika ba ta roqa ya cika mata.
"Ba komai kawai na gaji da zaman gidan ne, anjima ina son zuwa gida na gaida Mamana, wataqila naji daɗi,"
"Indai wannan ne kar ki damu, bari na ci abinci muje na ajiye ku,"
Bai jira me zata ce ba ya fita parlour ya zauna kan dinning din su madaidaici mai kyau na glass ya fara zubawa kan shi abinci, sauri tayi ta shirya, ba komai indai zata samu ya aminta ta fitan ai tayi satar hanya suje su siyar su koma gidan nasu sai yaje can ya ɗauke ta.
Tana gama shiryawa ta d'ebi kayan Humairah ta kaiwa kulu dan ta sauya mata, shiryawa sukai sika karkashe kayan wuta da fitilu na gidan (a dinga kulawa nan gaba kadan sanyi za a shiga, a saba da kashe kayan wuta kan a bar gida, Allah ya kare)
Keys din shi ya koma d'aki ya ɗauko suka fita suka shiga mota sai gidan Hajiya Ramai, sarqar da d'ankunne na maqale a jakar ta, har da abun qafar dika ta d'akko.
A qofar gida ya ajiye su ya ce in ya dawo ɗaukan su ya gaida Maman ta kafin nan ma Baba ya dawo.
A qofar gidan suka maqale sai da suka daidaici ya tafi suka fita a qafa suka tsaida mai adaidata sahu suka haye sai kasuwa, wajen saida gwalagwalai nan kulu ta kai su,suna isa bayan sun tattauna akan saida gwal ɗin nata ta miqa dan a auna, zafi ya dami Humairah sai zanyara kuka take yi amma ko a jikin Jameelaa ita dai ta d'aga ajin ta wajen qawayen ta kar su yi mata terere.
Dubawa akai dika sarqa da dan kunne zobe da abin qafar ya kai dubu dari hudu da sittin , wata iriyar shewa ta saki a kasuwar, nan da nan tace ta siyar babu ko ciniki a tsakanin su, ai kuwa da jin haka sai suka lalo kuɗin ta casss suka bata,dubu ɗari da saba'in ta dauka ta miqa sauran tace a bata wata sarqa da dan kunne ko da ba abun qafa da zobe.
Nan kuwa suka bata wasu masu shegen kyau har ma da zobe amma bai kai wancan girma ba a haka Jameelah tai ta murna tana godewa Kulu, nan ta ɗauki Humairah a gaban masu saida gwalagwalan ta zaro nono ta fara bata tana ta hira da shewa da murnar samun warakar matsalar ta, Kulu sai kakkare ta take yi dan sai taji wani irin kunyar ganin Jameelaa na shayarwa a gaban kowa, aiko mazan wajen sun ga N*** a arha ba su biya ba, sai kallon ta suke yi suna ta biye mata ana ta hira.
Sai da Humairah ta qoshi suka koma gidan Ramai dubu biyu ta zara ta bawa Kulu kyauta dan murna.
A nan ne take zayyanewa Ramai dik abinda ya faru suka jajantawa juna, amma Ramai tace Allah ya kashe ta Lantai bata isa taci wannan jakunkuna da takalma da sauran kayan ita ɗaya ba, ko su raba ko ta tona mata asiri, sai da Ramai ta gwammace bata faɗi haka ba, nan Jameelaa ta dinga masifa da bala'i tana wa Raimai warning akan kar taje garin fad'ar ta aro wa mamalo kuɗi a gano ita ma aron kuɗi tayi taci suna ajin ta ya zube.
Da kyar Ramai ta hakura itama, tai ta wa Jameelaa faɗa akan wautar da ta yi,
"Yanzu akan kare ajin ki shine kika bar ma matar nan kayan kuɗi masu yawa haka,"
"Na bar mata ɗin Ramai,barta taci da ace ma Bukar har yanzu yana taɓa sace-sace da shi zan aika ya saton amma tinda baya yi yanzu dole na hakura da dai ajina ya zube, kin ko san sai kowa na lungun nan ya sani? Wataqila magana ta bazu har gidan surukaina, inaaa ba zan iya ɗaukan wannan abun kunyar ba batta kawai taci Allah ya isa"
"To ni yanzu me zan samu?"
"Kamar ya fa? Ke wai Ramai me yasa dik qoqarin da nake baki godewa Allah akai ne? Kina fa jin bala'in dana shiga fa wanda yanzu haka du kuɗin nan wasu qattin zan bawa banci nanin ba ga nanin nan na ci na,"
"Ko dubu ɗaya ba zan samu ba kenan Jameelah a wajen ki?"
Cikin fushi ta buɗe jakar ta ta zaro dubu ɗaya ta miqa mata ranta a mugun bace,ba kunya kuwa Ramai ta amsa ta soke a bra,Kulu kuwa na zaune ta na ganin ikon Allah gaba ɗaya uwar da d'iyar ba tarbiyya.
Qarshe da suka tashi hirar wajen malamai sai suka bawa Kulu Humairah wai suje parlour su sha iska.
Ita da ba qaramar yarinya ba, sarai ta gane za ai wata maganar rashin gaskiyar ne.
Sai da suka kammala tsara yanda za a kai umar gidan wani sabon boka, dan sun gaji da bin malamai ba nasara gwanda yanzu suje wajen tsafi sosai, suna son albashin shi yana damqawa a hannun Jameelaa, yanda ba zasu dinga matsalar kuɗi ba.
"Amma fa kema sai kin saki kuɗi aiki zai kankama shegen maqon kuɗi gare ki,"
"In da ina samu ɗin ai ba sai an kaishi wajen kowa ba, babu ne shi yasa, ɗan wanda yake bari a gida bai wuce dubu goma ko ashirin shikenan fa, tinda ma na shiga matsalar nan ko sisi bai bari yanzu, ke kuma komai sai kice sai an kawo kuɗi, wasu iyayen da kan su suke nemawa yaran su taimako ba sai sun biya ba,"
"Laaaa kin raina wanda nake yi miki kenan Jameelaah, Allah sarki ashe dik wahalar da nake in shiga tafasa da mazamfari saboda ke baki gani, daɗi na dake rashin godiyar Allah,"
"Yanzu dai ki yi hakuri, in Allah ya yarda zan sake hannu dan kuwa ina cikin matsalar kuɗi gaskiya"
"Shi kenan zako ki ga aiki dan kuwa ana yabon bokan nan sosai,"
Baba ne ya dawo, ya siyo kayan marmari Ramai ta Karb'a ta yanka ta raba sannan ta kai masa abinci da ruwa, sai da ya gama cin abinci sannan jameelaa ta shiga suka gaisa, yaji daɗin ganin ta sosai itan ma haka, fatan alkhairi yayi mata sannan ya mata nasiha sosai akan komai za ta yi ta dinga jin tsoron Allah, kuma ta bi mijin ta ta yi masa biyayya ta kyautata wa iyayen sa da 'yan uwan sa,ta zauna da maqotan ta lafiya kuma ta maida hankali a karatun ta, ta dinga aikata abubuwan alkhairi saboda yaran yanzu a wajen basu tarbiyya ko ka faɗa masu suna so su ga kana aikatawa kaima kafin su bi,inda Jameelaa wata mai hankalin ce da ta dauka ta zauna lafiya a gidan auren ta ds rayuwar ta ma baki ɗaya, amma yanda ya gama yi mata nasihar haka ta bar masa nasihar shi a wajen.
Umar na tashi wajen aiki gidan su Jameelaa ya je, suka gaisa da iyayen ta sannan suka tafi gida.
Washegari da sassafe tai ma qawayen ta waya akan suje su amshi kuɗin su, sun so ta aika ta acc kawai amma tace kash ne itakuma bata son zuwa banki, nan dai suka ce in an tashi daga makaranta zasu je su Karb'a.
Kafin su je Jameelaa ta sha wanka ta zuba babbar atampa mai tsadar gaske, ta saka sabon zinaren ta, ta sa Kulu ta qalqale gidan fiye da da, har d'akin Umar yau ya samu arziqin gyara sosai sannan an buga girki mai daɗi da ya ji nama da kayan lambu.
Humairah ma an sa mata riga mai kyau da tsada abun dai sai wanda ya gani, ga lemo da zob'o na musamman da ta aka haɗa, tana zaune tana sana'arta ta wato kallo suka shiga mutum uku ne suka samu zuwa, wasun su sunce a Karb'a kawai ba sai sun zo ba.
Cikin fara'a ta miqe tana masu sannu da zuwa abinci aka gabatar masu, ai kuwa sun ɗan ci dan daga makaranta suke suna jin yunwa, sannan ta je ta d'akko masu kud'in ta miqa masu cike da izza da taqama tace ko za su qirga ne?
"Habaa ai ba komai mun yarda dake, ke din babbar yarinya ce ba kya harkar qaranta,"
Wayyooo daɗi kashe Jameelaa
'Ajiiiiii kenan Alaji'
Ta ayyana a ran ta, zahiri kuwa murmushi tayi tace,
"Habaaa ai kune manyan yara, a shekarun ku kuna yin dabarar tara irin wadannan kud'in ai gaskiya ba na biyun ku sannan iyayen ku na ji daku ba qarya"
Haka sukai ta yabon juna da faranta ran junan su sannan suka tafi masu ɗaukan su na jira a mota.
Umar daya dawo ya ga kwalliyar da Jameelaa ta sha yayi ta yabawa, amma yana mamakin sabuwar sarqar da ya gani a wuyan ta.
Qarshe ya gaji ya tambaye ta ya ce,
"My love a gaskiya kin yi kyau, na kasa ɗauke ido na daga kallon ki,bayan tsantsar kyau da Allah ya zuba maki ga wata kwalliya da ki ka zuba,kin qawata kwalliyar da sarqar zinare mai ɗaukan ido,ina ki ka samu wannan sabuwar sarqar dan ban san ki da ita ba"
Nan take idon Jameelah ya raina fata..........
*Yau na ji daɗin comments ɗin ku gaskiya, Ameen to all ur prayers*
[08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 31:
Shiru ya yi yana jiran amsar ta tare da kafe ta da idanun shi, cikin wata jarumta ta tattaro dik hankalin ta waje ɗaya sannan ta yi masa fari da ido, wanda ta san yana jan hankalin shi ta ce,
"I am sorry Abban Humairah naso na yi maka suprise ne dama, shi yasa ɗazu nace maka ka kaini gidan mu, dama na je na sauya sabon design ne na sarqar da d'ankunnen yanzu irin wanan ake yayi, kuma kasan mu mata yana da kyau mu dinga sauya abubuwan mu, lokaci zuwa lokaci dan birge ababan qaunar mu"
Ta qarasa maganar cikin yi masa wani irin wasan da ya mugun tafiya da shi, lumshe ido yayi tare da sauke numfashi, ya jata jikin shi abun nema ya samu, sai da su kayi romancing junan su sosai sannan ta daga shi,cikin wata iriyar murya Umar yace,
"Ina zaki je kuma Ki qarasa binda kika fara mana ko ladan naki ya cika?"
Ya qarasa maganar shi yana wani lumshe idanu.
"Ina zuwa bari na kaiwa Kulu Humairah na dawo"
Tana kai Humairah wajen Kulu ta koma sai da wasa yayi wasa sanan Jameelaa tayi shiruuu, Umar ya matsu ya kammala abinda ya fara amma 'yannan tai mursisi taqi bashi dama.
"Come on my love, ya kika tsaya,"
"Ni ba komai kawai tinani nake yi ne ina son na ɗora ma Mamana jari amma bani da kuɗi, bata son zama ba sana'a"
"Indai dan wannn ne zan baki 50k ki kai mata zai isa?"
"Anya kuwa kasan fa sai ta sake kayan aiki, ta yi awon dik wani abu da zata yi amfani da shi, sannan...."
"Please love ki bar maganar can a gefe ki qarasamin abinda kika fara, i promise to take care of all her needs, i will give her money to start her business again, please love,"
Jameelaa na jin maganar kuɗi zasu shigo kawai ta ci gaba da gigita Umar hankalin ta kwance bata tsoron Allah bata tsoron cewa mace haramun ne ta amshi kuɗi ko wani abu a dai-dai lokacin da mijin ta ke tsaka da biyan buqtar shi a wajen ta, wallahi dik macen da ke hana mijin ta kan ta sai ta yi ciniki dashi ko sai ta nemi wata biyan buqatar ta ta son zuciya, ko sai ya mata alqawarin wani abu wanda ta san zai cutar da shi to ta sani ko a ina take ko a wanne lokaci za ta koma wajen Allah zata gamu da Allah ta yanda batai tsammani ba, domin kuwa shi zunubi ko wanne iri ne ana son bawa ya bar shi kafin lokaci ya qure masa, mata masu hali irin na Jam Jam a nutsu a ji tsoron Allah, maza masu kuɗi kuna sakewa matan ku su ci arziqin ku, matan ku sune abokan rayuwar ku, masu tara haram ma dan matan su suji daɗi da yaran su suke yi balle kai me tara halal? K akashe kud'in ka ta halal ka more rayuwar duniya da lahira, dan in ka kashe ma mace kud'in ka wallahi at the end kai zaka mora dan kai za ai wa qunshi, kitso, siyan kayan kwalliya, siyan turare, yi ma yaran ka siyayya, rage maka cefane mata muna da tausayi, rashin ganewar ku ne maza yasa kuke mana dik abinda kuke so mara kyau wai dan tsare gida , ka sake zuciyar ka ma mace kaga yanda zata maida kai ɗan lele, sai dai in kaga mace na mugun abu to yar uwar Jameelaa ce,kuma Ramai ita ce maman ta,sannan mata masu karb'ar kuɗi a wajen mazan su dan mazan sun sauke buqatar su ta sha'awa a wajen su su sani da su da karuwai na kan titi 'yan gudu ibinin (Good evening) basu da banbanci.
Washe gari Jameelaa ta yi ma Ramai waya akan ta aika Bukar ai kuwa kamar wanda take jira, ta katse wayar ta yi wa Baban Jameelaa qarya da cewa,
"Malam Jameelaa ke kira na naji Humairah na ta tsala kuka, wai sun rasa me ke damun ta magani anyi har na asibiti, shine nace bari naje na gwada na gida,"
Ko d'ago kai Malam Jameel bai yi ba ya ci gaba da yankan farcen hannun sa ya ce,
"Yaushe kika zama mai bada maganin gargajiya banda labari Ramai? Da alama kin manta da wayar ki ana iya jiyo qarar mai magana dake tsabar qure mata sauti da ku kai , to ba inda zaki je ki aika Bukar kamar yanda tace ko kuma ki fita ba da izini na ba kamar yanda kika saba,dana gama yanke farce na zan fita anjima zan aiko a kawo cefane, na ga kamar kayan miya sun qare"
Cikin jin haushin shi ta amsa da,
"A had'o da nama dai ah toh,"
"Inshaa Allahu za a had'o da shi kuma a daina yi wa jika ta qaryar ciwo irin wannan bana so,"
"Anyi din"
Ta furta a hankali,
"Na'am magana ki ke?"
"Ince me?😏"
Murmushi yayi ya ajiye rezar a saman window ya fita, ya kula har yanzu matar tashi na da halin yara, ji yanda take wani kumbura dan ya yi mata faɗa kuma ya hana ta fita.
Bata da zaɓin daya wuce na ta aika Bukar ɗin, dan haka ta faɗa d'akin ta dan ta dan jira ya kammala shirin makaranta ta sanar da shi,in an tashi daga makaranta ya je ya ji meye kiran Jameelaan,
Tana nan zaune bacci ya kwashe ta sai zabga munshari take yi Bukar kuwa da yaga tana bacci ya wuce makaranta abun shi, kamar wadda aka maka wa duka haka ta miqe ta hau kiran Bukar, jin shiru ya sa ta sanya mayafi ta rufe gidan ta sa kai zata je gidan Jameelaah da kan ta.
Surutu take ta yi ita ɗaya a hanya, akan bari tai sauri ta koma kan wancan jarababben ya koma yaga bata gida,fakam fakam fakam take tafiya cikin sauri,har ta yi nisa sosai tana tafiya amma babu abin hawa, kamar daga sama taji an kwashe ta an watsar a qasa a gefen hanya, wasu matasa ne a kan babur sun yo goyon biyu su na ta yi mata magana dan ba horn a babur ɗin nasu ga qarar babur ga ihun da suke mata amma tana can tana tinanin gidan Jameelaa me za a samu ya sa bata ji su ba har sai da suka iso suka rasa yanda za su yi su kauce mata, qarshe dai suka kwasa ta a saman hanya.
A kan qafar ta ta hagu Ramai ta cake ai kuwa nan take ta samu tsagewar qashi,tini ta zube a wajen sumammiya, mutane an taru a kan ta wanda suka buge ta kuwa sun gudu abin su.
An duba ta tsaf ba a samu waya ko wani abu da zai nuna daga ina take ba, sabuwar unguwa suke balle a ce wani ya san ta, qafa tayi tsami ta fara kumbura mutane sai video ake yi mata, wasu sun fara rubutun qarya akan videon ta da pictures da suka ɗauka suna turawa social net kamar su facebook, instagram, whatsapp da sauran su, kowa da kalar labarin da yake qirqira akan ta, amma ba masu daɗi bane kaff labaran, an rasa mai taimakawa koda farfadowa ne a samu ma tayi.
Wani bawan Allah ne ya kutsa ya hau tura mutane baya yana masifa,
"Meke damun ku ne mutanen wannan zamani ? Kun manta da taimako Allah Allah kuke ayi wani abun ku fara qirqirar qarya kuna yaɗawa, yanzu da kuka d'au hotuna da video shine abinda tafi buqata? Ba mai qoqarin kaita asibiti, dubi qafar ta yanda ta kumbura, yanzu da kun tura social net wasu masu qaramin tunanin zasu yi ta sharing, wanda in da wani abun alkhairi aka rubuta da zai amfani al'ummar annabi ba za a yi sharing ba, sai labaran batsa, da videos na batsa, da labarai masu saka shubuha da masu fidda mutum a musulunci ma dika kuji tsoron Allah fa tamm"
"Kaii kama min ita mu kaita asibiti daga can sai mu bada cigiyar 'yan uwan ta,"
"Haka kuwa aka yi nan aka sanya ta a motar bawan Allahn nan ya tuqa suka tafi basu tsaya a ko ina ba sai a asibiti, accident and emergency aka shige da ita nan take likita da nurses suka fara bata taimakon gaggawa da sun ce sai an kawo police, mutumin yace indai basu kula da ita ba ta mutu shi kuma zai maka su kotu.
Yana ganin sun amshe ta ya koma gefe ya jira a waje yana hoping ta tashi ta fada masa ita wace ce? a ina take?........
*Hummmm wanda bai ji bari ba zai ji hoho ai, Allah gwai inji Kabawa😂*[08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 32:
Koda Baban Jameelaa ya aika da kayan miya gida ɗan aike yafi awa ɗaya bata nan ga kuma gida a kulle, ya gaji da jira ya koma ma Baban Jameelaa ya sanar da shi ba kowa a gidan a rufe ma gida yake,kad'a kai ya yi ya amsa suka ci gaba da aikin su a ran shi yana ayyana,
'Allah ka shirya min iyali na Ramai ba ta jin magana ta dik maganar da na ke mata baya shiga kunnen ta sai da ta tafi hankalin ta ya kwanta'
Sai da lokacin tashi daga wajen sana'ar shi yayi ya wuce gida, Bukar na qofar gida zaune yunwa ta gama yi masa illa sai matse hawaye yake kamar ba namiji ba, Baban Jameelaa ne ya dafa shi nan take ya fara shan majina yana d'aga kafad'a tare da share hawaye,
"Kayi hakuri Bukar daina kukan haka ya isa, bata dawo ba ko?"
"Eh Baba bata dawo ba ni yunwa nake ji, ko karyawar kirki ban ba na fita kuma ban je makaranta da kuɗi ba gashi na dawo tin rana ba kowa, banda kud'in abun hawa balle naje wajen ka ko wajen Jameelaa"
"Yi hakuri Allah ya qara maka hakuri akan wanda ka ke dashi Allah ya qara shiryar min da kai, Allah ya yi maka albarka, zo ga dari biyu kaje ka sai wani abun, ga mai soya awara can a bakin titi je kaci, bari na kira wajen Jameelaa nace ta dawo haka tinda ita batai tinanin dawowa ba har yanzu ɗazu na kira wayar ta naji a kashe"
Wayar shi ya ɗauka ya fara kiran Jameelaa, Bukar kuwa ya wuce titi dan siyan awara ya ci.
Sai da ta kusan tsinkewa sannan Jameelaa ta dauka,
"Hello Baba, barka da yamma,"
"Barka dai Jameelahn Baba babar ku na nan? Ina ta kiran ta baya shiga, tace kina kiran ta ɗazu ko? To kice ta dawo ta bamu ɗan makulli in yaso ta dawo ku kwana anan"
"Baba ai nima bata zo ba kuma tin safen nake kiran ta naji Bukar shiru dama nace ta turo shi,"
"Ah ah, to ina taje kuma?"
"Ba ta gida ne?"
"Bata gida tin hantsi na aika a kai mata kayan miya bata nan, ina kuma kyautata zaton halin ta data saba ne dana sa qafa na fita itama ta fice, to ina zata je in bata zo nan ba?"
"Ikon Allah, bari nayi ma Abban Humairah waya ya faɗa ma 'yan sanda a fara binciken inda taje, na shiga uku,"
Kuka ta fashe da shi dan kuwa hankalin ta bai kawo komai ba sai ko ta b'ata ne? Ko wajen sabon bokan da tace zata ta tafi ta b'ata a hanya?
"Daina kuka ina zuwa naje tsohon gidan mu ko taje masu ziyara,"
Kashe wayar yayi ya jira saida Bukar ya dawo sannan ya ce ya jira a qofar gidan in yaga ya dad'e bai dawo ba ya je gidan Jameelaa ya kwana, nera dari ya bashi na abun hawa sannan ya tafi.
Shi din ma adaidaita sahu ya hau sai unguwar su ta da.
Ba binciken da bai ba gida-gida amma kowa sai ya ce ai ta dad'e rabon ta da unguwar ma.
Malam Jameel ya fa fara shiga tashin hankali, bai san yana ji da Ramai ba sai yanzu, ada kullum halayyar ta na sa yaji ta fita akan shi, amma rashin ta ya d'aga masa hankali, ko ba komai matar shi ce kuma abar son shi, halayen ta ne abin qi a gare shi.
Gidan Jameelaa ya wuce shima dan ya san Bukar baya gida yanzu, koda yaje ya tadda Bukar na cin abinci, shima zuba masa Jameelaa tayi amma haka ya kasa ci, ruwa kawai ya sha ya yi jigum.
Umar ne yayi sallama ya dawo daga kai ma 'yan sanda qorafin rashin ganin ta da ba ai ba, Malam Jameel ya shiga matsananciyar damuwa a wannan dare, da kyar sukai ta tausar shi har ya samu ya sha tea kawai, Umar da cewa yayi ya kwana anan gidan amma yace inaa zuwa zasu yi su yanke kwad'on su shiga, in yaso an sai wani.
A mota Umar ya maida su shi da Jameelaa wadda sai kuka take tayi, dan bata san wane hali Ramai ke ciki ba.
Umar ma dik ya damu ganin habibiyar shi na kuka.
Sai da aka buge kwad'on suka shiga sannan suka juya, Malam Jameel bai iya kwantawa ba bayan Bukar yayi bacci ya buɗe qofa ya fita, shiga nan fada can haka yayi ta yawo yana tambayar mutane ko sun ga mace mai kama kaza da kaza.
kowa yace masa bai gani ba, zama yayi qofar wani gida yana zubar da hawaye, dare yayi sosai, dan kuwa 12am tayi a lokacin, qoqarin tafiya gida ya ke, wani mutum a babur ya zo shigewa, sauran kadan ya buge shi, kauce masa yayi yana masifa.
"Ku dattijan nan sai ku dinga tafiya akan hanya, dazu mai babur ya bankad'e wata dattijuwa yau,sai wahalar neman dangin ta nake ban samu ba, asibitin da na taimaka na kai ta an hana ni tafiya yanzu ma gudowa na yi, kana son na buge ka na koma cikin wahalar dana baro daga taimako,"
Cikin sauri Malam Jameel ya bi bayan mutumin yana kwala
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 30