Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ina yin😢* [09/09, 10:39 am] Aunty Hameeda: 💅🏼  *MAZAUNA GIDA*  💅🏼 *WRITTEN BY HAERMEEBRAERH* Page 50: Ajiye jaridar hannun shi ya yi ya miqe tsaye Sapnah da ke riqe da lemon da ta bare masa ta bi qafafun da yake kallo da idanun ta,Jameelaah ce ta shiga sanye da atampa riga da zani sai mayafin daya yi kala da kayan jikin nata, haka ma takalmi da purse ɗin ta iri ɗaya ne, kamala da kwarjini tare da nutsuwa sun bayyana a fuskar ta, lallai dik kyaun mutum in baida kamala bai gama cika mutum ba, yanzu ne Jameelaah take cikkkiyar kyakkyawar. Sapnah ce ta tashi ta je gare ta fuskar ta ɗauke da murmushi mai qayatarwa, ta kama hannun ta tana mata sannu da zuwa, ciki ta shigar da ita, sai da ta zauna suka gaisa sannan Jameelah tace mata, "Ni da maigidana muka zo yana waje," "Ahhh shi ne baki yi magana ba, bawan Allah ya na can waje a tsaye ai da kun shigo tare duk gida ne ai" Zuwa ta yi tayi ma Umar bayani haka nan sai yaji dik wani haushin ta da yake ji ya kau a ran shi, gaba ɗaya yanda yaso ya yi mata rashi mutunci ya farfaɗa mata maganganu marasa daɗi a dik sanda ta zo wajen shi sai ya ji ko kallon banza ba zai iya yi mata ba. Shigar da Tsalha ya yi cikin gidan, Tsalha zama ya yi kusa da matar shi sai ta miqa masa lemon da aka tsiyaya mata,cike da tsokana Sapnah tace, "Ohhhh Maman Humairah wato soyayya daɗi ko, ai gashi zan zuba masa nashi shima," "Ammin Humairah baki da dama, wato har yanzu baki bar surutu ba ya huta shima ko?" Dariya suka yi dikan su harda Umar, Umar kuwa sai kallon Jameelaah yake yi Tsalha ma na kula da kallon da yake ma matar shi,nan da nan kishin 'yan mazan jiya ya motsa,sai ya yi gyaran murya ya fara magana dan suyi suyi abinda ya kawo su su bar gidan, "To da farko dai dalilin zuwan mu shi ne, mun zo ne dan mu bada hakuri akan abubuwan da suka faru a baya,ba sai an maimaita su ba a yanzu,na san duk irin abubuwan da Amaryata Jameelah ta aikata maka marasa daɗi a baya,gamu mun zo tana mai neman gafara akan su, ina fatan zaka dubi girman Allah ka yafe mata su,mun sani dika Allah baya barin haqqin wani akan wani, koda Allah ya yafe mata kaima tana da buqatar ka tausaya mata ka yafe mata," Umar dake kallon yanda take tsiyayar da hawaye ne ya ji jikin shi ya yi sanyi, sai ya ji me yasa ya ɗauki wannan tsahon lokacin bai yafe mata ba ? saboda ko ba komai Jameelaah ta so shi kuma shima ya so ta, ya daukake ta a rayuwar shi, ya girmamata a lokacin da dik bata cancanci hakan ba, me zai hana ya yafe mata a yanzu da ta zama mutuniyar kirki, har ta buɗe baki za ta yi magana Umar ya riga ta da faɗin, "Na yafe mata Allah ya yafe mana baki ɗayan mu,dama ita rayuwa ana son mutum in ya yi laifi ya nemi yafiya, shi kuma wanda akai wa laifin ya yafe, shine cikar mutuntaka, dan haka na yafe mata dik abin da ta yi min wanda na sani da wanda ban sani ba, nayi hakan ne kuma domin Allah, ina fatan nima Allah ya yafe min," Jameelaah ce ke ta shasshekar kukan farin ciki, abubuwan da ta aikata masu muni a baya na ta dawo mata a kwanya da zuciyar ta, kallon gidan ta sake yi taga yanda aka sauya komai, arziqi ya haura na da, Sapnah ce ta miqe ta tafi d'akin Humairah,tana tafiya Jameelaah ta buɗe baki tace, "Na gode Abban Humairah, Allah ya qara girma da daukaka, kaima Allah ya sanya ka farin ciki fiye da yanda ka sanya ni a da da kuma yau, na gode na gode," "Ba komai ya wuce,ina fatan nima ki yafe min in akwai abinda na taɓa yi maki da ya b'ata ran ki," "Ba ka min komai ba Yah Umar innace ga abinda ka yi min yau mara daɗi na maka qazafi, baka rage ni da komai ba, ka bani dikkan kulawa da girmamawa tare da cikakkiyar soyayya, ni ce nai fatali da komai, in ma yi kamin wani abun ko menene shi na yafe maka, Allah ya yafe mana baki ɗaya," "Ameen ya Allah, sai kuma maganar Humairah ga ta can dik sanda suka samu hutu inshaa Allahu zata dinga zuwa, ko kuma da weekends, zata zo har ku saba da juna inshaa Allahu," "Muna godiya malam Umar nima kaga ka koya min wasu darussan na zaman duniya, Allah ya albarkaci rayuwar iyalin ka, muna godiya sosai," "Babu komai, nima na gode" Nan Sapnah ta shigo da Humairah da ta dame ta da tambayar ina zasu je? Sapnah taqi sanar da ita ta dai ce ta saka kaya sosai ta sanya mayafi ko hijabi, dan haka sanye take cikin riga da skirt na leshi, ta ɗora hijabi a saman su sai zaro ido take yi taga suprise ɗin da aka ce zata gani, su na zuwa parlour taga Jameelaah, cike da murna ta isa gaban ta ta rungume ta, Uwa Uwa ce😍 itan ma rungume ta tayi, tana shafa bayan ta, baki yaqi rufuwa, daga baya Humairah cike da jin kunya ta zauna a qasa, ta gaida su suka amsa, Jameelaah na shafa kan ta tace, "Lallai Humairah kema girman jiki gare ki kamar ni," Dariya sukai banda Humairah da ba ta so ana ce mata yar lukuta,tinda a iya shekarun ta jikin ta babba ne,dan har bra take sawa a yanzu. Turo baki tayi tana kallon Umar, alama ce ta ta kai qarar Jameelah wajen shi, "Yi hakuri Daddy's girl wasa na ke yi maki, to jikin ki kamar na Abban ki," Murna ta fara yi, dan kuwa har yanzu Umar kowa ya san shi da suka sake haɗuwa yanzu ba zai ce ya sauya ba, sai dai ma a ce ya qara kyau da haiba. Murna sosai Humairah tayi bayan sun taba hira Tsalha ya ceto su fa zasu tafi, "Habaa ku dan qara zama mana, ga abinci can ya kusan yi," Inji Sapnah da ta yi maganar har cikin ran ta, dan kuwa ba qaramin daɗin samun wannan daidaito a tsakanin Umar da Jameelah ta yi ba ko dan Hunairahn ta ta samu farin ciki mai d'orewa. "Ahhh ba komai kar ku damu, 'yan uwana nacan na jiran mu muci abinci, dan kuwa na ce masu ba jimawa zamuyi ba." Tsalha yaji daɗin maganar ta sosai, saboda ko ba komai zuwan ta gidan shi ya sauya daga gidan qazamai ya koma na masu tsafta, tarbiyya ta wadatu, shi kan shi dik wata furfura da wani rama dik sun zama labari, yi 'yar qiba mai ban sha'awa yayi haske, ba wanda ya damu da furfurar shi, saboda kyaun da ya yi. Umar kuwa d'aki ya shiga ya sanya kaya sosai, ya deb'i wasu shaddoji guda biyu masu tsadar gaske, da turaruka biyu, sai hula ɗaya takalmi ɗaya ya saka tashi hular ya ɗauki makullin mota sannan ya fita yace suje ya sauke su a gida daga nan yaga wajen da suke da zama ma. Ai kuwa basu yi masa musa ba dan yanda Umar yayi magana ba damar musu n ma gashi yayi gaba ya bar su baya alamar su yake jira, sai da suka fita Sapnah ta fito itama ɗauke da ledar ta a hannu, kayan kwalliya ne da turaruka sai wani sabulun wanka da body scrub da skin oil sai hair oil da hair mask duk na kamfanin HAMIBRAH BEAUTY PALACE kaya ne dake gyara fata kuma basa saka bleaching sai dai suyi maganin quraje da qesbi, sannan gashi ya yi kyau ya yi tsawo ya yi daɗin maintaining. Jameelaah tayi ta godiya kamar ba zata daina ba Sapnah har taji kunya ma ta kama ta, sanda zasu tafi Umar yace Humairah ta shiga daga nan sai su dawo tare. Cike da murna kuwa tashige kusa da Jameelaah suka wuce. Har gidan ya kaisu kuwa ya jira dan saida Jameelaah da Humairah suka shiga ciki sannan Umar ya baiwa Tsalha kayan daya d'akko masa, Umar na ganin alamun Tsalha zai qi Karb'a ne ya yi saurin riga shi yin magana ya ce, "Don Allah kar ka qi Karb'a, ga shi nan a yi ma matan gidan kwalliya, yanzu ni da ku ai mun zama daya inshaa Allhu," "Kaiii amma na gode, ba dan ka roqe ni ba da sai nace ka bar su, daga zuwa neman gafara sai a had'o mu da irin wannan kab'akin arziqin haka?" "Alamu ne na an yafe maku kenan ai," Dariya suka yi, Tsalha ya shiga gidan shi a dakin Jameelaah ya aje kayan sannan ya ma matan shi izinin su sa Hijabi su gaisa da Umar, a soron gidan suka tsaya suka gaggaisa,bayan sun koma cikin gida ne sukai ta yaba Kyau da kwarjini tare da kud'in Umar, dan kuwa ko a jikin shi ya nuna shi din ya shaqi nera. Nan da nan suka sake girmama Jameelaah a zuqatan su, ace tai zaman aure da irin wannan zankad'ed'en miji ta dawo ta auri tsoho sa'an baban ta? Sai da suka rungume junan su sannan Humairah ta sake shigewa jikin Jameelaah,Jameelah ce ta bude motar ta sanya ta ciki, tare da sumbatar kuncin ta, sai d'aga masu hannu suke yi bayan sun wuce Jameelaah ta share qaramar k'wallar dake idanun ta, suka koma ciki da mijin ta abin son ta wato Malam Tsalha. Tin daga wannan lokacin Umar yake kai Humairah wajen su Ramai, tayi masu weekend, wani satin kuma wajen su Mum, wani sati kuma gidan Jameelaah, ba qaramin jin daɗin ziyarar da take yi ba take, wataran kuma Sapnah zata kai ta gidan iyayen ta da gidan su Umaimah da Aunty Hauwaa, ganin su take yi suma a matsayin kakannin ta, Humairah da Ummee 'yar gidan Umaimah sun zama best friends kuma best sisters, komai tare suke yi saboda makarantar su ma ɗaya ce,Muhammad ma makarantar su ɗaya ya yi girman jiki shima kamar Humairah, dan tsaurin ido cewa yake shi yayan su ne, saboda dik inda mace take namiji ne gaba da ita, shi ke kula da ita. Bayan shekara biyar Bukar da yayi aure ne suka je gidan Ramai dan kai gaisuwa, matar Bukar fiddausi anan maqotan su ya gan ta ya ji yana son ta har aka yi musu aure tare, ta yo girki mai daɗi guda biyu, ɗaya na gidan su Bukar ɗin ne ɗaya na gidan iyayen ta,dik zubi ɗaya ta yi musu ba bu bambamci, hatta da mazubin dik a abu iri ɗaya ta saka, saboda ba ta son kowa ya zargi ta fifita wani sama da wani. Ramai na alfahari da samun suruka kamar fiddausi, dan bata ɗauke ta a uwar miji ba a uwa ta ɗauke ta, dan haka itama a d'iya ta ɗauke ta,  in taje ta tadda wanki, ko wani aikin Ramai bata yi ba to zata zage suna hira tana yi mata aikin, dik wani abu in bata iya ba bata jin nauyin tambayar Ramai, saboda yanzu ita ce uwa a wajen ta, gane hakan da Ramai tayi ba qaramin jin daɗi take yi ba, ko ba komai itama ta sake samun wata d'iyar. Matar Bukar na ɗauke da ciki wata biyu, Bukar da ya kaita zai gudu, wai kunya yake ji ace matar shi na da ciki, Ramai tace ohhh ji soko ita mace bataji kunya ba sai shi namiji, haihuwa inda rai da rabo ai an fara yi kenan, in Fiddausi ta koma gida kuwa tai ta tsokanar shi, in ya neme ta tace itama kunya take ji, sai yayi ta bata hakuri sannan take yarda. A tsakanin waɗannan shekarun Jameelaah da Sapnah Allah ya azurta su da samun haihuwa, dika maza, Tsalha ya saka sunan Malam Jameel, inda suke kiran shi da Abbah, Umar kuwa ya sanya sunan Baban su Sapnah, dan kuwa zaɓi ya bata ita kuma ta sanya sunan mahaifin ta, Abdulqadeer, suna ce nasa Abdul. Tin daga nan haihuwa ta buɗe masu, in sun ziyarci juna suna hira suyi ta faɗin, ikon Allah sai da d'iyar su ta girma ta isa kaiwa d'akin miji sannan haihuwa ta buɗe masu. Jameelaah tace indai aka aurar da Humairah zata rufe haihuwa, akwai kunya aje sunan nata haihuwar sannan a tafi na d'iyar ta, Sapnah sai tace ai ba komai haka Allah ya qaddara, kar ta bi na mutane, in haihuwa ne bata yi ba zasu ce bata haihu ba, yanzu da ta haihu, kuma zasu sa mata ido, ba a iyawa ɗan Adam, dan haka ta rungumi dik abinda Allah ya bata kawai. ********************** Dr. Aeeshaah Humairah Umar likitan yara ce yanzu a asibitin Ameenu Kano, dake cikin garin Kano burin ta ya gama cika a yanzu ita da Ummee, twins ma wasu mutanen ke kiran su, dik da cewar Ummee tafi Humairah tsaho, ita kuma Humairah tafi Ummee cika, shape din ta irin na Jameelaah ne sak, ta dai qi amincewa ne dan ana ce mata 'yar lukuta, dik da ba wata qiba sai cikar qirji da mazaunai. Ummee ta samu miji daga dangin su Umaimah, wan da ake kira da Abbas, (Ba Abbas din Fauziyya ba fa na littafin MUGUN MIJI NA MASOYIYAR MARUBUCIYAR KU HAERMEEBRAEH) ma aikacin gidan talabijin na NTA ne dake a Lagos, Humairah kuwa ta samu nata ne a nan asibitin su, shi kuma likitan Mata ne kamar mahaifin ta mai suna Imraan, Dr. Imraan iyayen shi ba wasu masu hali bane, kusan shi ke kula ma da su, amma Alhamdu lilLAAH akwai rufin asiri, ya mallaki gidan kan shi da abin hawa. An saka ranar auren su a tare, dan haka Iyayen amare an fara gyaran amare sosai ba kama hannun yaro, lokuta da dama sunfi haɗuwa a gidan su Jameeelaah dan kuwa Jameelaah har yau bata sake da su Mum ba tana jin nauyin abinda ta yi mata a baya, dik kuwa da qoqarin da Mum take akan ta saki jikin ta, amma inaa ta kasa hakan, dan haka wataran gidan su Jameelaahn Ummee da Humairah suke zuwa, ta yi masu gyaran jiki, ko ta koya masu wasu abubuwan da ya dace ace sun iya. An daura auren Ummee da Humairah, akan sadaki daidai aljihun mazajen su, aure ne daya halarci zuri'a kala-kala, ta kowanne ɓangare dangi sun halarta, dangin Ramai dana Malam Jameel, dangin mum dana Dad, ga bangaren su Sapnah, ga wajen angwaye,suma dangin uwa da uba duk sun halarta. Biki dai sai wanda ya gani, rabon da na ga amare sun sha kwalliya mai kyau irin wannan har na manta, doguwar riga ce fara tass mai kyallin stones masu haske, an kama daga qirjin su aka sake ta daga qasa, dogon hannu gare ta sai mayafin ta mai cikar ado, aka yafa masu saman daurin da aka kafa masu da gwaggwaro irin na wannan zamani, da ake yayi, fuskar su ta sha kwalliya, sun sha kwalliya mai qayatarwa ga abinci nan cima kala-kala ko a KFC albarka😂. Ana nan ana ta shan dinner kowa ka gani cikin farin ciki yake, yau ga Ramai ga kaji da snaks, amma ba handama ba had'ama, taci iya cin ta ta kauda kai tai hamdala, tare da sanya albarka a auren jikokon nata. An kai amare gidajen su lafiya,  inda Humairah take zaune anan garin Kano a unguwar Gedi-Gedi, Ita kuma Ummee sun lula ta jirgi sun tafi Lago shine your eyes, suna zaune a unguwar Yaba. Bayan watanni shida Matar Bukar ta haihu, Jameelaah ana ta hidimar suna, Sapnah da su Umaimah da Aunty Hauwaa ana ta aikin d'ura sobo a gorina, Mum da Ramai suna ciki suna ta hira suna ganin yanda 'yan uwa da abokan arziqi ke ta taimaka masu wajen yin abinci da kuma ganin komai ya tafi dai-dai, Humairah ce kwance tana danna waya suna hira da mijin ta, sai shagwab'a take yi masa akan sai ya kawo mata agwaluma, tana jiran shi ya bata hakuri ta bari har ta koma gida taqi, gashi tin safe bata karya ba har 1pm tayi, ganin bai da zaɓin daya wuce na ya je ya nemi dik inda agwaluma take ya kai mata ne yasan shi ya miqe daga office ya ɗauki makullin mota ya fita gefe daya kuma yana nan yana ci gaba da magana da ita ta waya. "To gani nan na tafi, wannan babyn in ta/ya zo duniya sai na mammake shi/ta, wahala iya wuya na sha ta, zanci soyayyan quli quli sabuwar suya, zan ci awara mai yaji, zan sha kankana, ga abinci masu gina jiki sosai ba za a daure a ci ba sai k'walama," "Ni kake yi ma faɗa ko? Bari ka ga na sa kuka a waya in an tambayen na ce cewa kai zaka zo ka d'auken ba za ai suna da ni ba, sai dai su zo sunan naka babyn," Qamewa a inda yake ya hau bata hakuri, dan Humairah na da iya shege in tace zatai abu, to kuwa zata yi ɗin, sai da taji ya yi nadamar faɗan daya mata sannan ta fara dariya tace, "In banda abinka banda hankali ne da zan hau maganar ciki da su," "Yo na sani," "Kace mi??" "Ah ah cewa nayi bari na kashe naje na siyo maki, bye love u," K'wafa tayi tana murmushi, ta san sarai yayi magana da ita, tashi tayi dan zuwa ta taya su aiki, Sapnah ta kira ta ɗauke da kwanon tuwon shinkafa miyar taushe, ya ji naman rago, sai zobon da suka gama qullawa ta bata. Tana ganin kwano ta fara tura baki,ahaka tana qi tana qi Sapnah ta sa ta ci mai yawa, kowa a wajen ta burge su sosai,dan kuwa wanda basu san alaqar su ba ganin ta suke mara kunya tana sangarta d'iyar ta a gaban kowa. (Mutum kenan kayan Allah, ka nuna ma ɗan ka gata ace ka sangarta shi, yayi laifi ka hukuntashi ace ka tsane shi, ka barshi ya lalace ace baku da tarbiyya😂 ya ilahi which one man go do na? Bama ɗan ka tarbiyya iyakar iyawar ka, ka toshe kunnen ka daga surutun mai surutu, as long as kasan akan dai-dai kake, to kowa yaci kan shi ) Rayuwar su haka take ci gaba da tafiya cikin nishad'i da walwala cike kuma da arziqi da wadata,sai dai abinda ba a rasa ba na yau da gobe dan kuwa rayuwar dama yau fari ne gobe tsimma, yau zuma ce gobe kuma mad'aci, yau arziqi gobe talauci,haka rayuwar kowa take tafiya. *Alhamdulillahi dika-dika anan na kawo qarshen novel dinnan mai suna MAZAUNA GIDA, ina fatan Alkhairin dake ciki Allah ya sa mutane su amfana da shi, akasin haka kuma Allah ya shafe shi cikin rubutu na da zuqatan bayin shi. Allah ya sa ka ma dik wanda suka karanta da alkhairi sukai comments masu daɗin karantawa, Allah ka saka ma mutan group dina na HAERMEEBRAERH NOVEL GROUP da alkhairi ka haɗa da GROUP ƊIN GIDAN ƊAN LITI ya Allah ka haɗa da dikkan hausa novel groups ɗin dake karanta wannan labari. Allah ka sanya mu a aljannah ta sanadiyyar karanta abun alkhairi ko wanne iri ne.* *Ya Allah ka sa rubutun nan nawa da nake yi su zame min alkhairi a ranar gobe qiyama,Allah ya sa na kafa hujja da su a gaban ka ya Allah kar su zame min hujja akai na.* *Wadda dik na batawa sanadin wannan novel a yafeni, masu ciki Allah ya sauke ku lafiya,masu yara Allah ya raya ya yi musu albarka, masu neman haihuwa Allah ya bada masu albarka.* *Fidda Allah ya qara maki hakurin rashin da kika yi ya kawo masu albarka, Yaya Barira Allah ya jiqan ki ya yi maki rahama, Allah yaraya abinda kik bari da imani* *HAERMEEBRAEH ❤️CE* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 30 of 30