Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba. Tana zuwa ta wani d'aure fuska ta zauna a kujerar da in ta zauna akai take jin kan ta kamar a office take, nan take ta kalli Babawo ta sakar masa murmushi, shima murmushi ya sakar mata da kyakkyawan haqoran shi da suka rine da hayaqin sigari,gira ya daga mata ta sake sakin wani sabon murmushin. Nan da nan ta fara zuba masa abincin sa, wanda baya bata kud'in a wajen sai da dare in ya zo zance a nan ya cake mata kudin ta,banza tayi ma masu kiran sunan ta ta je har gaban shi ta aje masa, sannan ta juya tana kad'a mazaunan ta Babawo ji yayi kamar ya ture mutanen dake wajen ya riqe ta tsam a jikin shi,wani ihu ya kurma sannan ya ce, "Allah ya kaimu dare,bu.....ub....nan kayyasa" Abincin ya ja gaban shi ya dau spoon yana ci yana santi tare da kallon ta, haka tai ta zuba abinci tare da masu taimaka mata tana masifa kamar wadda take basu kyauta,wasu kuma da ta san suna bar mata canji in sun sai abinci sai ta washe masu baki har da fari, su na sane suke bada dubu ɗaya  su ce a yi masu had'in ɗari biyu ko uku su bar mata canji, wasu ma dubu biyu zasu dunqule su bayar ta zuba masu na dari uku suce ta riqe sauran tsabar rashin sanin ciwon kai dan kuwa da damar su ma masu aure ne sun baro gida ba na cefane amma suna kashe wa wadda bata da lokacin su kuɗi. (Sun baro halal din su sun taho su na yaba haramun,matan su da yara a gida kuwa ko za su wanke kan su a inji ba sa burge su, wannan ta wajen da ba halalin su bace shaid'an ya qawata masu ita su na ganin ta ma fi matan su na aure kyau,sannan ita ta fi cancanta su yi wa kyautar kud'in da zai iya ci da iyalan su.) Baban ta ne ya zo zai shige gida yana takaicin yanda d'iyar cikin shi ke wannan sana'a da ya hana ya hana amma anqi ji, ya tabbata tinda ya ganta da wuri haka, ko dai bata je makaranta ba ko kuma ta gudo, dole dai akwai dalilin dawowar ta ta da wuri. Rasa hanyar wucewa ya yi dan kuwa cikin gidan ma kan shi maza da mata ne a cakud'e ana ta hada-hada, ji yayi ba zai iya zaman awa ɗaya bama a gidan, dan haka sai ya fidda dubu ɗaya ya bawa Ramai yace ta qulle masa abincin sa a leda zai koma can wajen aikin shi yaci, aiko ba godi bare na gode ta amshe,haka rayuwar ta take sam bata san meye godiya ba ita, dan haka baya ganewa idan ya kyautata mata shin ta ji daɗin abu ko akasin hakan Zuba masa tayi a ledar ko arziqin kwano bai samu ba a matsayin sa na mai gidan ta miqa masa, ya ko sa kai ya bar gidan yana zuwa soron ya jiyo muryar Jameelah ta na ihun sai an cake mata kudin ta casss ba za ta yarda ba,sai wani fari take yi tana zaro idanu waje. Ganin yanda ta cukuikuye ɗan barno yasa Baban ta daka mata tsawa, sannan yace masa ya tafi ba tare da ya biya kuɗin ba, Cike da rashin kunya haɗe da tsoro-tsoro tace wa Ɗan borno, "Zaka dawo zaka ga ni indai a waje na ne ba zaka sake cin abinci ba, kuma dik inda na ga kuɗi a wajen ka sai na k'wace," "Allah ya shirya min ke jameela," Shi ne kawai abinda Malam Jameel ya iya furtawa cikin takaici ya wuce wajen sana'ar shi, ita kuwa haka ta ci gaba da banbamin faɗa tana bada abincin ta. Sai wajen huɗu na yamma suka tashi daga wajen saida abincin, da wuri abincin ta ya ke qarewa amma bata shiga gida da wuri anan zata zauna har huɗun ko biyar na yamma,zama take su yi ta wasa da mazan wajen da ita da Mamalo da sauran yaran matan gidan da sunan amso kwanuka da kud'in abincin su. Wata ma direct a mazaunan ta namiji zai d'aka mata duka sannan a bata kud'in tana dariya tana fad'in "kaaabaaariiii" wanda bai kai zuci ba. Bayan sun gama sai su ka shiga wajen iyayen nasu suka miqa kudin da su ka yo a ranar,gidan ya yi dan dama duk an tattafi sai masu naci da masu siyan kwantan abinci wajen wanda suka yi kwantai, Mamalo da Jameela ne zaune suna  tatauna yanda za su yi wankan yau. "Kin san me? Yau mu qure wa wanka laya, yaran layin can wai har damu suke takara, atampar da kika saka rannan ta wajen Babawo shi wai Saudatun qasan layi ta sa itama shekaran jiya,ya kamata mu shiga kasuwa fa saboda gaskiya kayan mu sunyi qasa. "Dan Allah fa? Rabu da 'yan wahala kin ji Mamalo duk abin su ba za su taɓa kamo ni gayu ba sai na wuce su biyo baya na ni ce zan dinga raba wa 'yan hassada aiki ba biyan albashi, amma rabu da ita yau zata sha mamaki ,dan kuwa kayan da zan saka kowa bai sanni da su ba ma, zata san dani take gasa a layin nan, sai na gasa ta sosai kamar aya," "Shi yasa kike burgeni tawan, ni kam ko aramin wanda ki ka saka waccan juma'ar kiyi dan Allah, sai na shirya a d'akin ku, kin san Lantai matsala ne da ita ba zata barni ba(kun ji 'yar zamani mai zamammiyar qeya ko?) "Kar ki damu Mamalo kema leshi zan ara maki ki saka yau,ni wannan da zan saka yau kuɗi na tara na siya na kai ɗinki jiya na amso, yau kuma zan buga abuna na ji shegiyar da zata faɗan maganar banza," Su na gama tattaunawa suka sallami juna kowa ta wuce d'akin su, ta na shiga ta cire kayan jikin ta dan ta na so ta huta kafin magariba a yi shirin fita zance kuma,ta na nan kwance ba tare da ta tuna bata yi azahar ko la'asar ba ta hau rera dik wata waqa da ta zo mata a kan ta, (kanta baya ja wajen hadda amma yana ja wajen waqa Jameelah ta daban ce) A haka bacci mai daɗin gaske ya sace ta, kamar wadda aka kwad'awa mari haka ta miqe a firgice a zato na ma tunawa ta yi da bata yi sallah ba sai na ga ta miqe tsaye ta hau sauya doguwar rigar da ta saka kafin ta kwanta zuwa wani lace ruwan zuma farar saqa mai guntun hannu da fad'in qirji, rigar guntuwa ce dan kuwa  da zata ɗan d'aga hannun ta sama ba abinda zai hana a ga cibiyar ta,skirt ɗin rigar ta saka matsattse sosai,sai ta qasa ya bude sosai,ta kafe kan nan da d'auri mai kyau,ga kwalliyar ta nan bata goge ba, Jameelah saboda son gayu na musamman ta sai kayan kwalliya masu tsada irin wanda ake amfani da su a saloon,ta yi hakan ne dan ta nuna wa sa'annin ta ba ɗaya suke ba, da ta yi kwalliya za ka gane da kayan kwalliya masu tsada ta ke amfani, lokuta da dama idan za a yi aure ma har baiwa qawaye aro take yi dan ta nuna masu sune a qasan ta ita ta wuce ajin su. Mayafi siriri ta yafa a kafad'a ɗaya ta saka takalmin ta kalar mayafin, tana wani shan qamshi tare da tauna mutumin nata wato cingam, kudi ta Karb'a wajen Ramai tace zata siyo abinda zata ci yunwa take ji, cike da washe baki Ramai ta ce, "Ga shi, mai nemowa ai in baya ci yana qoshi wataran sai an nemo shi, sai kin dawo," Jameelah na fita tsakar gida ta ɗauki buta ta kurkure bakin ta sannan ta hau kwala wa Mamalo kira, "MAMALOOO ! idan baki fito ba zan wucewa ta fa," Karkad'a jiki take yi ita a dole ta makara kamar wata wadda zata je wata ma'aikatar. Can sai ga Mamalo ta fito sanye da wata shadda da ta ɗan sha wanki, amma ta amshe ta ba laifi tayi kyau sosai itama dai-dai kyaun ta, "Kin ari kaya a waje na me yasa baki saka su ba? ko 'yan baqin cikin iyayen naki sun hana ki sakawa ne? Dama ni dan ki kankaro wa kan ki mutunci ne yasa nake ara maki, ki qure wanka kema a gan mu ba raini amma tunda sun hana sai mu jera kowa ya kalle ki kamar wata mai aiki na,muje ya na iya," Mamalo ta muzanta sosai dan bata ji daɗin abinda Jameelah ta yi mata a tsakar gida ba kowa na ji da gani, amma haka suka ɗauki hanyar zuwa shagunan da ake saida kayan kwalama irin su shawarma da gasasshen kifi da meat pie da sauran su. Su na isa Jameelah ta shiga wani sanannen shago a wajen haka ta hau nuna abinci kala-kala sai ta yi wani fariiii farrrr da idanu tare da lanqwasa harshe tana kad'a qirjin da ba ta gama rufewa dika ba tare da  yatsina ta tambayi farashi,a haka suka gama siyayyar su a wajen suka faɗa wani shago da ake saida qananan kaya nan ma ta sai abinda za ta siya suka ɗauki hanyar komawa gida mai nisa, dan bata so su isa gida da wuri,ta hanyar makarantar su suka bi har an tashi yara kowa ya wuce gidan su sai qalilan da ɗaukan su ake yi su na zaune a waje ɗaya su na jiran iyayen su dan kuwa magariba ta gabato, su na isa layin su ta qarasa cire siririn mayafin da ke kafadar ta ta hau jujjuya shi a hannun ta ta na wani juyi da jikin ta ta na lilo da ledar hannun ta,a dai-dai inda suke zama su yi zance ta ga Babawo babu b'ata lokaci kuwa ta tsaya a wajen suka zauna, Baban ta kuwa na tsaye a qofar gida dan bai jima da dawowa ba ya ga qofar gidan da duhu wanda ya san ya saka k'wan fitila shekaran jiya da safe amma gashi yau ma har an samu wanda ya fashe shi, sai duba wajen k'wan lantarkin gidan yake yi yana mamakin kusan koda yaushe in ya saka k'wai a wajen sai an samu mai fashe shi, amma har yau ba a kama me aikatawa ba ya na gama dubawa ya shige gida ba tare da ya san ya baro 'yar shi a bayan shi ba. Zaune suke su na ta hirar soyayya abun su Mamalo ma na tsaye tana masu hira itama, anan suka cinye abinda suka siyo ta duba sabuwar shimi da panties ɗin da ta siyo a gaban Babawo ko kunya bata ji shi kuwa sai yabawa yake yi tare da fatan watarana ya siyo mata wanda suka fisu kyau ta saka a gaban shi ya gani,suna gama ganin kayan Babawo ya fiddo naman daya siyo mata suka hau ci. Kafin a kira sallar isha'i naga 'yan mata na ta fitowa cikin wanka da kwalliya kamar ana wani kwarya-kwaryan biki a layin cike da mamaki na buɗe baki ina bin su da kallo.......... [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻. MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 4: kamar kullum yauwa da safe haka Jameelah ta tashi ta kammala dik wani shiri data saba yi ta shirya dan zuwa makaranta, tare da qudirin yau zata sai dik abinda take so a lokacin break,idan ya so daga baya sai ta sanar ma da Umaimah tana son ta bita gidan su ranar juma'a, so take dai sai ta ga gidan su Umaimah hankalin ta zai iya kwanciya, babbar motar da ake kawo ta ake ɗaukan ta na matuqar girgiza ma Jameela zuciya, ga irin cimar da take kawo masu makaranta kullum kala-kala na sake tabbatar mata da su Umaimah masu kuɗi ne,dan kuwa haka take zuwa musu da kaji a cikin abincin su suci har su qoshi, sannan wataran ruwan roba take zuwa da su gora biyu zuwa uku, ga kudi da bai gaza dari biyu ba ita ko hamsin in ba ta zara a na abinci ba ba mai bata. Karatu ake ta zabgawa a ajin nasu ko da ta isa,kowa ya maida hankalin akan abinda ake koyarwa banda Umaimah wadda ta tattara hankalin ta gaba ɗaya akan qirjin Jameela, wanda a ran ta take matuqar mamakin cikar su, a iya tinanin ta shekarun su daya amma ita da tafi Jameelah girman jiki bata da cikar girji irin na Jameelan, ikon Allah kawai take ta kalla. Kamar daga sama ta ji muryar Jameelan, cikin kare baki dan kar a gan su ta ce; "Yaushe wai zaki kai ni gidan ku ne? Ko dai baki son naje cin arziqi nima? Lallai Umaimah ban taba sanin ke marowaciya bace sai yau, ashe dik abinda ki ke ban a iya nan ne ba zaki iya gayyata ta gidan ku ba? Himmm duniya kenan, yau da ace nima 'yar wani ce da tini kin gayyace ni, shike nan, na gane irin zaman da zan nayi dake daga yau," Cike da mamakin yanke hukuncin da Jameela tayi a kan ta take kallon ta, "Kinyi kid'an ki kin yi rawar ki,kin taɓa ji nace bana son na kai ki gidan mu, Kawai daga fara magana sai ki qarasa ta da kan ki? Ni ba wai bana son kai ki gidan mu bane,halayen da kike yi ne bana so,haka kawai na je na kai ki gidan mu ki jamin faɗa, gaskiya shine dai matsala ta dake" "Indai wannan ne matsalar ki an kauda ita,yanzu yaushe zaki kai ni?" "Ko rannn.... wayyoo Allah malam," Saukar bulala ce da ihun Jameelah ya karad'e wajen, nan da nan kuwa Umaimah ta nutsu ta shiga hankalin ta saboda tasan dukan akan ta zai qare daga qarshe, dan kuwa Jameelah ta riga da ta jawo mata duka, shirun da ta ji ne ya tabbatar mata ita ba za a dake ta ba. Qunquni Jameela take tayi ta na fad'in, "Yarinya ba dan ina son naje gidan ku ba ko dan na bada labari kuma na ci daɗi nima da sai na fanshe dukan nan a jikin ki yau," Bayan an tashi break, Mamalo ta ce ma Jameela, "Qawa zo muje ki ji, ki yi sauri akwai labari, na jira ki mu taho aka ce ai kin yi gaba," "Ban na sha mutuniya ta, nima ki ji nawa," Nan kowaccen su ta faɗa  ma 'yar uwarta yanda suka yi da saurayin ta, cike da zumud'in jin qarshen yanda Babawo ke ma Jameela wasanni Mamalo ke kallon ta, sai da ta gama ji ta d'akko dubun ta ta nuna wa Jameelah, aiko Jameela na gani ta ce, "Yauwaaa ya kamata ki fara tarin kudin ankon Furairah, kinga kar azo baki dashi, dan ke ba kullum kike samu ba," "Waya fada maki? Ai yanzu Sadeeq yace ina fada masa komai nake so, kuma zai dinga ban dubu daya kullum, amma kin san meke damuna? Ni nafi son muna irin soyayyar ku, amma shi kwata-kwata ya qi ya na abu kamar wani baqauye" "Wai me kuke ta tattaunawa ne haka? Kunyi shiru, ko kuna bitar karatun dazu ne," Wata harara Mamalo ta watsa wa Umaimah da ta matsa kusa da su, Mamalo na jin kishin yanda yanzu Jameela ke qawance da Umaimah sosai,cikin washe baki Jameelah ta ce wa Umaimah, "Babu komai zauna muyi hirar dake," Bayan sun gama hirar su suka hau cin abincin su Umaimah, daga nan suka je wajen yin break suka dinga siye-siyen kayan kwalama da abinci, a wannan ranar sai da suka ci suka yi nak sannan suka koma aji. Lokacin da aka tashi kowa sai ya tafi gida,cike da zumud'in zuwa gidan su Umaimah Jameelah ta koma gida, dan haka tin a ranar ta ware kayan da zata saka dik randa zata je gidan su Umaimahn, kaya ne masu kyau da tsada ta ɗauka ta ajiye a saman jakar kayan ta,dama ita ta na tanadin irin kayan fita unguwa na ba raini ɗin nan da kud'in talla ko na samari take siyan irin kayayyakin, tare da taimakon Ramai za a mata dinkin na garari dan kuwa watarana ma Ramai ce da kan ta zata kai mata tace wa tela ayi mata dinkin 'yammata da ake yayi dan kuwa 'yar ta ta 'yar zamani ce, haka za a yi mata dinki ko a auna ta dik Ramai na gani, matsattsen dinki daya bayyana kowacce surar ta amma sai Ramai tana jin daɗi har cikin ran ta ta na jin cewar diyar ta kyakkyawa ce da ba kamar ta a layin har ma da layin dake kusa dasu. Cikin ja da baya ta ke kallon kayan da ta fitar dan zuwa gidan su Umaimah Jameelah ta ce, "Toooo yanzuuuu ina zan samu hijab babba, mai dan kyau da zai shiga da kayan nan, ina da takalmi da jakar da zan saka 'yar qaramar can dana siyo a gwanjo, kaiii Allah yayiwa gwanjo albarka, gaba daya sai ka siya kai luf a bayan shi, a zaci dama abu na ka ne tin fil azal,Allah dai ya biya masu gwanjoooo, Ramaiiii!" Ta k'wala wa mahaifiyar ta kira da ke tsakar gida, babu b'ata lokaci kuwa ta amsa kamar ita ce 'yar ba uwa ba. "Na'ammm 'ya guda ɗaya tamkar zinare ya aka yi?" Cikin shagwaba da bubbuga qafa da wani yauqi da tasan yana qara mata kyau ta burge dik mai kallon ta take maganar, hakan kuwa na tasiri a zuciyar Ramai sai tana ganin ohhhh ni nake da wannan kyakkyawar d'iya, domin Ramai in ba fari ba gaskiya sai a hankali ce, amma kyau da hasken fata na wajen Baban Jameelah, dik da dai yanayin aikinsa ya sa ya yi duhu. "Ramaiiii ! kinga wannan qawar tawa Umaimah ce ta gayyacen gidan su ranar juma'a kuma banda hijabin sakawa, dan gidan su gidan Ustazai ne bana son zuwa da mayafi hijabi nake so na saka dan Allah ki ban kuɗi na d'inka hijabiiii, tayi tayi naje gidan su saboda rashin hijabi yasa ban je ba har yau," "Me yayi zafi ina da kuɗi kuma kece me nemowar muje ciki na baki" Da murna a ran ta tabi Ramai suka koma dakin, amma a fuska sai ta nuna kalar shagwab'a da tausayi kar ace dama son amshar  kuɗi kawai take yi tunda Ramai ta san halin ta sarai, ba zato babu tsammani suka ji muryar Bukar na fad'in, "Ni ma Yasin sai an ban wani abu, kullum sai a dinga bata dik abinda take so ni ba me bani, inna sata ace min b'arawo, ai in ba a son yaro ya ɗau abin da ba na shi ba a dinga bashi abu in yace yana so," "Sannu ubana, nace sannu ubana, ga ta nan, dube ta daga sama har qasa wa ka taɓa gani me kyau a dik layin nan sama da ita? Amma ba talla take yi ba dan a rufa wa kai asiri? Nan take sai da abinci ta sama mana wannan kud'ad'en da ka sa wa ido, kai ruwan piyawata nace zan dinga baka kaima kana zama qofar gida,da aka yi sau ɗaya ka tattara kud'in kai gaba kasha maro abin ka,to tsoron ka nake yi da zan sake baka kid'i na? Ka fita daga ido na in rufe Bukar, ka iya faɗan min abinda ya zama wajibi iyaye su wa yaran su amma baka iya aikata wanda yara zasu ma iyaye dan suna sama masu kudi ba ko,bar nan kan na ma rotse dan uban ka," "Habaa Ramai ko hamsin ki bashi mana ya sai wani abun ko ɗari ce ma haka," Dan bata fuska ta yi kafin daga baya ta d'au wata tsohuwar ɗari ta wurga masa, da murna ya dauke yana mata kirari, sai ga baki an washe, ana cewa "Ja'iri ! sauran a sai sigari kuma, da kudina dai aka sai sigari ban yafe ba," Ficewa yayi yana mata dariya, har sholi an sha da kudin ta dan sigari, yafiyar ta ba abinda zata yi masa a ganin shi. (Ina fatan ko da ban sharhi ba kun fahimci saqon wannan kalaman nata, ta kira shi ja'iri, da damar mutane suna ce ma yara ja'irai wanda ya na nufin 'yan wuta kenan, da wasa ba a sani ba ana kiran yara 'yan wuta, sannan tace ma yaro mara jin magana bata yafe ba, ko sanin amfanin ta bai ba balle yafiyar ta a gare shi, bare har ya kiyaye me tace kar ya halaka,kenan in ya aikata abinda tace masa din Allah zai iya sawa ya qara lalacewa, tinda tace bata yafe ba? Mu kiyaye mu kula da bakunan mu akan yaran mu) Hijabi mai kyau Jameela ta siyo kalar ja mai shiga sosai, dan kalar atampar ta kenan, so take ta burge sosai, amma dole sai ta nuna ma iyayen Umaimah su talakawa ne dan a tausaya mata, sosai. ****************************** Rana bata qarya sai dai Uwar d'iya taji kunya, yau juma'a kuma yaune ranar da Jameela zata je gidan su Umaimah, da kayan ta ta tafi a jaka, fuskar ta yau ba kwalliya, asalin kyaun ta ya bayyana, sai qamshi take zubawa, haka ta saka uniform ta tafi makaranta sai taunar cingam take yi. Ta tinama Umaimah zancen binta gidan su da za ta yi yafi sau bakwai, Umaimah dariya tai ta yi mata, daga baya tace, "Ina sane da wannan ranar Jameela dan kuwa na sanar ma da Mum din mu, ta san da zuwan ki, yau kina da sa'a dan kuwa Dad na nan shi ma, Yah Umar ne ban da tabbas din zaman shi a gida, amma ina fatan ya ga babbar qawa ta shima a yau," Tsaki mamalo ta yi dan jin ance ma Jameela itace babbar qawar, cikin jin haushi Jameelah ta kalli Mamalo ta ce, "Dalla meye na yi wa mutane tsaki? In ba za ki ji hirar mu ba ki bar nan ba wanda ya ajiye ki," Washe baki Mamalo tayi ta dafa kafad'ar Jameela, Jameela ta zame hannun Mamalo da ke kafad'ar ta, umaimah kuwa ta gama gano mamalo, dan haka kawai sai ta buɗe Hadith ɗin ta tana bita ta yi masu shiru, Mamalo sai hirar gida take yi masu tana ta zuba qarya, anyi kaza da kaza a d'akin su, Jameela kuwa bata son ai ta bada labarin gida a makaranta yara su gane talaucin su, ana mata kallon babbar yarinya,cikin hasala ta sake cewa Mamalo, "Dalla ki yi mana shiru, kamar a gidan ku ne kawai ake cin biredi da bota," Dariya aka dinga yi wa Mamalo ta yi abin tausayi, ta d'au jakar ta ta koma nesa da su ta fara karatu, Jameela sai kuma ta ji babu daɗi, amma haka ta basar ta ci gaba da manne ma Umaimah. Drivern su Umaimah ne yazo daukan su ta buɗe mota ta shiga, Jameela data sauya kaya a aji bayan kowa ya fita ta buɗe ɗayan side d'in ta shige, Mamalo na tsaye zuciyar ta baqqirin ji tayi dama ace itama iyayen ta na da kuɗi dan kawai ta burge Jameela, tana son ta da abota sosai, haka ma jameelan amma tafi son umaimah domin kud'in su. Suna tafe tana ta ganin unguwannin masu kudi tana ta santin gidajen a ran ta, amma a fuska ba zaka taba gane irin son abin duniyar da qaramar yarinya irin ta take ɗauke da shi ba. Wani qaton gida taga an nufa, iska ta shaqa mai daɗi ba mai warin kwata da sigari da hammata ba na unguwar su, wata kwallar kwad'ayi ce ta taru a idon ta a zuci take roqar Allah daya fito da su daga wancan lungun nasu ya kawo su sarari irin wannan. "Jameela menene Ko baki son zuwa ne? Ko wani abu ke damun ki," Cikin sauri ta buɗe baki tace, "Ni ce bana son zuwa nan din? Hauka nake da zan ce bana son zuwa irin wannan wajen? Shiga gaba muje ki gani," Da sauri ta bi Umaimah, tana sake qarewa kyakkyawan gidan Kallo. Bayan sun shiga cikin gidan ne Jameelah ta samu qasa gefe da inda Iyayen umaimah suke ta zauna kan ta a qasa take gaida su, sun yi matuqar yabawa da tarbiyyar ta, sun ji daɗi da 'yar su ke da qawa irin Jameelah mai kamun kai da matsuwa, sunyi sunyi ta zauna a kujera amma taqi. Kayan motsa baki aka kawo mata kala-kala dakin Umaimah saboda ta qi shan ko ruwa a gaban iyayen Umaimahn, tana shiga taga gado babba da kayan alatu irin wanda take mafarkin mallaka a d'akin ta a matsayin ta na budurwa me tashe, ji tayi kamar kar ta koma gidan su,

Chapter 2 of 30