wanne irin kuskure kk qoqarin tafkawa ne haka?"
"Baki da wayo, ki tsaya ki ji me zai biyo baya,"
Tari ta ci gaba da yi a hankali alamar data sha ruwa tarin ya lafa.
"A gaskiya ba sai kun bar mana wannan uwar dukiyar ba, saboda mu ba wasu masu qarfi bane, mun godewa Allah da abinda ya azurtamu da shi, in ta koma hannun ku zaku iya mata komai da kuke so,"
"A gaskiya Yaron mu yayi dacen samun mace ta gari, kud'in abin alfahari ne gaskiya duba da irin society da kuke ciki, to amma ku tsaya ba za a yi haka ba, zamu koma da su kamar yanda kk buqata sai dai zamu ajiye mata a wajen mu, dik sanda aka kai ta gidan ta sai ta d'inga amfani da su, dama kayan ta ne ai,"
"To wannan kuma ba zan hana ku yi ma diyar ku abinda kuke so ba, amma anan kam mahaifin ta ma na san ba zai bari ayi ta kashe dukiya haka ba,"
Da haka akai sallama akan matan su fita zasu koma, cike da godiya da jajanta bata basu komai ba dan basu san da zuwan su ba.
Baban Jameela bakin shi har kunne dan kuwa ya ji daɗin yanda suka zo neman aure a lokaci ɗaya aka sa rana da komai, ina ma zai iya da yace su dawo gobe a d'aura aure, amma dole ya sama wa diyar shi qima a idanun su kar su ga kamar neman kai yake yi da ita, ko da dai sun ce basu son a kaita da komai na kayan d'aki dole ko gara mai rai da lafiya yayi wa 'yar shi ya fidda ta kunya, dan haka zai yi amfani da kud'in kayan d'akin da za a yi mata ya narka mata su a gara.
Umar yaso ya zanta da Jameelaah amma hakan ba zai yu wu ba tinda ba shi ɗaya ya zo ba.
Kuka Jameela ta fashe da shi a cikin hijab ganin ana ta ficewa da kayan lefen ta, bata ko duba su ta gani ba.
Aiko suna tafiya ta fara masifa tana kuka ta na fad'in,
"Gaskiya Ramai kin cuceni, wataran sai na dinga tinanin anya kina son ci gaba na ma kuwa? an kawo kaya masu uban yawa da tsada haka dik da sun ce ba su yi wani shiri babba ba amma kin sa an maida su, haba Ramai haba Ramai,"
"Dalla kiyiwa mutane shiru ki ji dalilina,nayi hakan ne ba dan komai ba sai dan gudun b'arayin cikin gida da na waje, yanzu baki san a cikin garin nan satar kayan lefe ake ba ko? Ko a yan ganin kaya ko barayin dare, ba ki da wayo sam, kuma da na yi hakan baki ji yanda mutuncin mu da qimar mu ta qaru a idon su ba, suna mana ganin wasu salihai, marasa son abin duniya"
Muryar Baba ce ta katse masu hirar da suke yi, cikin baqin ciki ya ce,
"Allah ya shirya ku Ramai ke da 'yar ki wato ba dan Allah ki ka yi abinda ki ka yi ba, gaskiya kuna bani mamaki matuqa, mutanen nan domin Allah suke son ku fa, amma ku zuciyar ku ba Allah, sai ku shirya watannin da suka rage nayi na aurar da ita ta bar min gida ko na huta nima,"
"Baba kaima madadin kasa sati biyu ko uku amma sai ka kai abun har tsahon wata biyu,"
Duka ya kai mata ta goce Mamalo ce ta yi sallama a d'akin dan karb'ar littafin ta, sannan kuma taji gulma, miqa mata littafin Jameelah ta yi ta komawar ta ciki ta yi banza da Mamalon.
Ran Mamalo kuwa idan ya yi dubu to ya ɓaci, a qalla ai ta taimaka mata ta rufa nata asiri amma Jameelah bata gani ba, amma ba komai gobe ma rana ce.
********************
Umar ya maida hankali sosai wajen karatun shi, domin yanzu haka a shekarar shi ta uku yake, yana da sauran shekaru a gaba dan zama kwararren likitan mata.
Umaimah na ta jin daɗi Jameelah zata zama matar Yayan ta, dan kuwa tana qaunar ta tsakani da Allah sai dai tsoron halayen ta da ba kowa ya sani ba ke dakushe farin cikin ta, sai kawai ta maida hankali wajen yi wa qawar ta ta addu'ar Allah ya shirya ta.
Jameelah ta ci gaba da zuwa makarantar islamiyyah inda Ramai ta dage da shiga kasuwanni wajen nemawa Jameelah maganin matsi dana qara ni'ima tare da na mallaka.
Ba abinda magungunan nan ke qarawa Jameelah in ba sha'awa ba,gashi Ramai tayi tsayin daka dan hana ta zuwa wajen Babawo, Bukar kuwa sai amshe ma Babawo kuɗi yake da sunan zai san ya zai ya fito da Jameelah ko a boye ne.
Ramai ashe zata iya hana Jameelaah fita tun da ba ta hana ta ba har ta zama abinda ta zama a yanzu, sai yanzu ne take iya hana ta dan kar a tambad'ar da maganin mallaka da na qarin ni'ima a waje, ya ilahi wannan Rayuwa ce muke ciki?
A haka aka ci gaba da shirye-shiryen biki domin lokaci ya na ta qaratowa,duk wani gyaran jiki ciki da waje Ramai ta dage ta na ta yi wa Jameelah saboda ta kai ta gidan miji da kwaskwarimar da suke yi na b'oye yanayin da 'yar su take ciki.....
*Godiya mai tarin Yawa zuwa ga makaranta MAZAUNA GIDA ina jin daɗin sharhin ku matuqa...sharhi shi ne takin marubuci mai zaburar da shi ya qara qaimi akan rubutun sa .keep on commenting guys za ku ji daɗin labarin anan gaba fiye da yanda kuke ji a yanzu...wanda aka bari a baya basu karanta previous pages ba su yi hakuri a kammala a haɗa document.*
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 12:
Ansha bikin Umar da Jameelaah cikin wadata da walwala dan kuwa biki ne daya samu halartar mutane sosai, 'yan cikin unguwar su Jameelah an zazzo kamar an yi ruwan jama'a saboda yawa, anko kuwa sai da Jameelaah ta fidda kala biyar, saboda a cewar ta kowa ya riqe gudummawar shi a kece raini kawai wajen fidda ta kunyar saka ankon bikin ta, wasu sun samu sunyi dika dan kar su ji kunya, wasu kuwa sun samu yin wasu basu samu yin dika ba, wasu kuwa ko ɗaya ma ba su samu damar yi ba saboda ta abinda za a ci ake ba ta anko kala biyar ba,ai kuwa wanda basu yi ba sun sha gori da habaici wajen Mamalo babbar qawar amarya, wadda itama amarya ce ta agaza mata da wasu ankon dan kar ta ji kunya a ce babbar qawar ta ma bata yi anko dika ba.
Sadakin Jameelaah ya sa qawayen ta sake girmama ta a cikin layin dan kuwa dubu hamsin cif haka aka bata, a tarihin layin su kuwa mace bata wuce dubu goma ko a shirin,tayi wuta shine ake bata ashirin din.
Anci ansha da kud'ad'en da Ramai ke ta tari dama saboda bikin d'iyar ta tilo, gara kuwa Baba ya aje ba laifi a qalla a layin su ba a taba yin ya su ba,buhun shinkafa biyu na gwamnati, taliya kwali biyu silver, sugar buhu ɗaya, maggi kwali ɗaya, gishiri qaramin buhu,manja da man gyada manyan jarkoki, kowanne ɗaya-d'aya, sannan ya ɗora dubu goma wai na cefane, mutanen unguwar wasu cewa suka yi ma surukan ne suka bayar dan su fidda su Jameela kunya, da magana ta dawo kunnen Jameelaa, kuwa ta yada nata maganar dan a sake watsa ta kowa ya san iyayen ta ne suka yi wahala da gumin su.
Babawo daya ji maganar bikin a qurarren lokaci ɗan qaramin hauka ya yi masu, Jameela kuwa ba kunya ta tsefe shi tasss ta wanke shi da zagin rashin mutunci, dan kuwa ta sanar dashi dik kud'in da ya bayar ya fanshe abin shi dan haka ba mai binta bashi a dik fad'in unguwar nan.
Kowacce amarya in za a kaita d'akin mijin ta tana kokawa amma banda Jameela, ganin haka ne ya sa Ramai ta nemi kub'ewa da 'yar ta ta, suna shiga d'aki kowa ya fita ya basu waje ana ta tausayin rabuwar su dan an san akwai shaquwa a tsakanin su irin tasu da ta banbanta da ta mutanen kwarai, abun lura dai kawai shine shaquwar 'ya da uwa shaquwa ce kawai,cikin faɗa Ramai ta ce wa Jameelah
"Wai ke wace iriyar sokuwar yarinya ce ne Jameelah? ko kin manta shirin da muka haɗa ne? Naga idon ki gyamas ba hawayen komai, dan Allah kar ki rusa mana shiri Jameelah ki fara kuka tun yanzu ko na ci uban ki, ki yi ta turjewa ki na ihu,amma dan iskanci kin tsaya kina abu kamar wata bazawara Allah-Allah ki ke ki je gidan miji, to ko zawarawan yanzu suna kuka in za a kai su gidan miji balle ke budurwa"
"Ah ah fa Ramai yaushe kuka zai samu mahalli a idanu da zuciya ta a wannan dare mai tarin farin ciki a waje na? Allah ya d'auken wahala meye kuma na yin kukan? Kin san kuwa yanda nake jin tsananin farin cikin rabuwa da gidannan ? Dan haka banga baqin cikin da zai sa na zubda hawaye ba, dan Allah kar ki sake danganta ni da bazawara kuma bana so, dan ba wanda ya sanni a matsayin 'ya mace ni,"
"Dallah rufe min baki shashasha kawai, an faɗa maki lallai sai an kwanta da mace ne budurci ke ɓaci? ke dai jeki ko na qarya ne kiyi,"
Suna zuwa zasu fita daga d'akin, Ramai taga Jameelah bata da niyyar yin kuka,ai kuwa sai ta maida ta baya ta wanke ta da wani had'ad'd'en mari mai mugun zafi, nan take kuwa Jameelah ta saki ihun kuka, Ramai tace,
"Yauwaaa irin wannan kukan nake so naji, maza riqen riga a b'anb'are ki da kyar a jiki na,"
Jameelaah kuka take saboda zafin mari ga kuma takaici a ranar da zata bar gidan su an falla mata gigitaccen mari wanda tunda take tunb'elan ta a gidan ba wanda ya taɓa kafa mata shi a kunci,wannan wace iriyar muguwar al'ada ce ta kuka haka.
Dan haka bata da zaɓin da ya wuce na tayi abinda Ramai tace mata, qanqame Ramai tayi kuwa da mugun qarfi dan har sai da Ramai ta saki 'yar qara dan kuwa ba qaramin ruqo ta yi mata ba, sai zunduma kuka take yi, 'yan daukan amarya da suka zo kuwa suna ta tausaya mata, harda Umaimah aka zo ɗaukan amarya dan kuwa ta ce ba za a barta a baya ba sai ta zo,ita tai ta lallashin qawar ta ta, tausayin ta ne mai yawa a ruhin ta, ganin za a raba Jameelah da gidan su sai ta fara hango ta itama an fidda ta a gidan su watara za a kaita inda bata sani ba, nan da nan ta fara kukan tausayawa qawar ta ta, Ramai kuwa sai da ta yi dana sanin yima Jameela hud'ubar ta riqe ta a b'anb'are ta da kyar a jikin ta, dan kuwa hannun ta sai da ya sauya kala ya koma ja, to abinka da farar mace, da kyar din kuwa aka b'anb'are Jameelar a jikin ta.
Ko da aka sanya ta a mota mai sanyin AC ga qamshi sai Jameelah ta saki wata ajiyar zuciya mai qrifin gaske saboda daɗin da taji ya ratsa ta, yau dai gata a babbar mota mai AC za a kai ta gidan miji.
Kuka ta sake fashewa da shi dan tina plan ɗin su da Ramai,anyi anyi tayi shiru amma inaaa ta qi sam.
A haka suka isa gidan nasu Umaimah inda amarya zata tare da surukan ta, Jameelaa kan ta a qasa suka shiga da dangin iyayen ta dika bangaren Baba da Ramai,Mum sai kwarara mata addu'a take yi ita da angon cikin tsananin so da qauna, sannan qannen Ramai biyu da suka rako ta suka d'aga ta dan kai ta d'akin Umar dake gidan, Daddyn su yace sai ya kammala makaranta kafin su tare a sabon gidan shi da suke gina masu shi da Mum.
Ta haka ne har zata fara zuwa makaranta ita da Umaimah ta fara karatun ta babu takura,shi ma kuma ya samu damar yin karatun shi a nutse.
Umar da abokan shi na makaranta suna waje suna jiran 'yan kai amarya su tafi su raka ango wajen amarya kamar yanda ake yi a al'ada, can qasan ran shi kuwa baya son kowa ya shiga masa d'akin mata, dan yana da kishi ainun kuma a yanayin kamun kai irin na Jameelaah ya san ba zata so wani ya shigar masu d'aki ba.
Iyayen Jameelaah da suka kawo ta sun yi mata nasiha sosai dan sun san halin ta sarai, sun bata shawara akan ta aje dik wani makaman rashin tarbiyyar ta dan kuwa da alama gidan masu tarbiyya ne wannan, jin su kawai take yi ko d'aga kan ma basu samu arzqi ba balle ta amsa masu.
Haka suka gama suka tafi, 'yan unguwar su da suka zo ganin kwakwaf suka yi ta shiga suna ganin d'aki suna yabawa, dik da ba wani ɓangare guda aka ware mata ba ba kuma parlour, d'akin su babba a haɗe yake da parlourn gidan,cikin d'akin ta ya sha kayan gado da kujeru masu kyau, doguwar kujera ɗaya aka saka sai qarama ɗaya, da tafkeken gado wanda ya sha babban zanin gado mai tsadar gaske, ga labulaye masu tsada suma an baza sai suka qayata d'akin abun sai wanda ya gani kawai, akwatunan lefen ta ga su nan a aje a d'akin, kowa sai kalla yake yi daga nesa, Jameelaa Allah-Allah take yi kowa ya watse dan ta kalli d'akin nata da kyau.
Ba su suka gama kalle kallen su ba sai wajen 10 na dare, ta cika ta yi famm kuwa a wannan lokacin, Umar ma dake waje yana jiran kowa ya tafi dik ya qagu kowa ya watse ɗin.
Lokacin da kowa ya tafi, Umaimah ce a wajen ta, da wayo da dabara ta kora Umaimah, dan kuwa cewa tayi kan ta na tsananin ciwo so take ta huta, magani Umaimah ta ajiye mata da ruwa ta fita, tana tausaya ma qawar ta, a zaton ta kewar barin gida ne ke damun ta.
Koda Umar ya shiga da abokan shi a parlour ya barsu, dan bai yarda da shigar masu d'aki ba,wasun su sun ji haushi kuwa, amma da d'aya daga cikin su ya yi musu bayanin illar shiga d'akin ma'aurata da sunan rakiyar ango sai suka fahimce shi, suka masu fatan alkhairi tare da tsokana irin ta abokai suka miqe dan tafiya, ledar da suka siyo masu kazar siyan baki suka miqa masa suka tafi, dakin Mum yaje dan yi mata sallama ya ji a kulle alamun tana d'akin Dad ɗin su, dan haka sai ya leqa d'akin Umaimah ya yi mata sai da safe tare da aje mata ledar ice cream ya fita.
Ko da ya shiga luf take a gado, tana shaqar qamshin turaren da aka saka ma gadon, ga AC na ratsa ta, wani irin daɗi take ji har cikin qoqon ranta yau gata a dakin aure itama.
Umar ya shiga ya tsaya yana ta kallon ta, godewa Allah kawai yake yi a zuciyar shi, domin kuwa yau burin shi na biyu ya cika a rayuwar shi sauran ɗaya.
Zama yayi a gefen gadon tare da yi mata sallama, tana jin muryar shi ta zabura ta koma gefe a tsorace tana zaro ido waje ita a dole a tsorace take da shi.
Murmushi yayi sannan ya sake godewa Allah, dan kuwa ya san shi zai koyar da matar shi komai, ba abinda ta sani.
"Relax dear, ba abinda zan yi maki, taso kici abinci dan nasan yunwa kike ji, Umaimah ta sanar dani irin kukan da kika sha ta waya yau, taso kin ji inshaa Allahu ba zaki yi kewar gida ba zan dinga kai ki akai-akai ,sannan dikan mu zamu haɗu mu kawar maki da tinanin gida, taso nan kin ji ,"
Tashi tayi cikin sand'a kamar wadda za a kama, Umar kam dariya kawai yake yi mata qasa-qasa.
Zama tayi nesa da shi, a haka suka ci kazar nan, sai hawayen murna take yi, Umar kuwa ya yi zato na tinanin gida ne.
Sai da suka gama suka yi alwala suka yi sallah, tare da gabatar da nafila, sannan ya yi mata addu'ar da angwaye ke yi wa amare, suka yi shirin bacci.
Umar ganin yanda take a tsorace dashi ne kuma shima bai shirya yin komai da ita ba a yanzu, zai riqe alqawarin da ya yi ma Mum na sai sanda ya kammala karatun shi zai bari wani abu ya shiga tsakanin su, sai ja pillow daga gefen inda take a zaune ya yada a qasan carpet ya ɗauki wani bargo a saman gadon.
A qasa yayi shimfid'a ya kwanta, yana danne abinda yake taso masa na son kusantar amaryar tashi, ganin haka yasa ta ji daɗi dan plan din su zai tafi dai-dai yanda suka tsara.
Cannn cikin dare, suna bacci Jameelaa ta fara kuka tana ihu tare da buge-buge da cizge-cizge..........
*Makaranta zaku ga na yanke wasu abubuwan na tafi aure direct, nayi hakan ne saboda bana son tsawaita labarin, ina son na kammala da wuri saboda wasu uziri nawa da suka taso ba zato ba tsammani, ina fatan hakan bai rage maku daɗin novel din ba*
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 13:
"Dan Allah kuyi hakuri, kar ku taba ni, wayyooo Allah na, kar ku taɓa ni, bana so......bana so.....kuji tsoron Allah kar ku taɓa ni.......wayyooo Baba ka zo ka cece ni,innalillahi wa inna ilaihirraji'un, lahaulawala quwwata illa billah, wayyoo Allah na...."
Sai kokowa Umar da Jameelah suke tafkawa a d'akin a qoqarin shi na ganin ta samu natsuwa, amma hakan bai samu ba, sai da Mum ta shigo d'akin a guje dan babu inda ihun Jameelah bai shiga ba a gidan, Mum sanye take da doguwar riga ta bacci mai santsi kalar blue, rungume Jameelaah tayi tana ta karanto ayoyin qur'ani tana tofa mata, Jameelaah kuwa dik ta haɗa zufa saboda dambe da suka sha da Umar, shi kan shi gwama nunfashi yake yi dan kuwa ya gaji ainun.
Kallon yanda ta ke sauke ajiyar zuciya ya yi cikin tausayawa ya ke ayyana
'Haka yarinyar nan take da qarfi? Me ke damun ta to?ko dai ta na da aljanu ne bamu sani ba?'
Amsar da Umar ke ta son samu kenan, wani mugun kallo Mum ta zuba masa Jameelaa na kwance tayi luf jikin Mum, tana shaqar qamshin turaren ta mai daɗi, bacci ya ɗauke ta, bacci ne mai nauyi na huce gajiyar biki, gyara mata kwanciya tayi ta rufe ta, sannan ta tofa mata addu'a, da hannu ta yafice shi,suka fice a tare.
"Mum na ga kina ta harara ta lafiya kuwa? Ban taɓa ganin kina min irin wannan kallon ba"
"Dole na yi maka wannan kallon mana Umar, ina alqawarin da ka ɗaukar min? Ashe ba zaka iya hakuri ba har ka kammala karatun ka? Shikenan ba zan tauye ka ba, dan kuwa matar ka ce halal ɗin ka ce ita,amma haushi na ɗaya da ka yi min alqawarin barin ta har ta sake yin hankali, kai ma ka gama karatu a lokacin cikin kun saba da juna kuma ta qara wayo da hankali amma ka kasa cika min alqawarin da ka dauka,"
Nan da nan ya gano me take nufi, wata iriyar kunya ce mai nauyin gaske ta kama shi, cikin tattaro dikkan gaskiyar shi ya fara magana, da bayyana mata komai da ya faru tsakanin shi da Jameelah.
"Mum yanda kika ji ihun ta haka nima naji shi, na kwanta a qasa ita tana gado kenan, bayan mun gabatar da komai daya dace dan kwantawa, har ma na fara bacci kawai naji kukan ta kaɗan kaɗan cikin baccina, daga baya da na farka kuma naga tafara bige-,bige tana qanqame jikin ta, sannan kuma tana surutai kamar wadda ake so a yi wa wani mugun abun, nayi qoqarin na tsaida ta, amma na kasa, shine fa kk shigo,"
Ta gamsu da bayanin shi, dan haka tace,
"Ikon Allah, kome ke damun ta? Amma kamar jinnu, kamar kuma mummunan mafarki, gaskiya yafi kama da mummunan mafarki,"
"Nima haka nake zargi, Allah ya kyauta,"
"Ameen ya Allah, haka ne kuma muje mu kwanta ka kula da ita sosai, inda buqatar taimakona ka tada ni, in na ji ku ma zan zo,"
"OK Mum, sai da safe,"
"Allah ya kai mu"
Jameelah bata tashi ba sai da gari ya waye tangararau, shima bai tashe ta ba dan bai san a ya zata tashi ba, abinda tai jiyan ya matuqar tsorata shi.
Taji daɗin yanda ya barta ta sha bacci a gadon nasu mai laushi da daɗi.
Tsabar makirci irin na Jameelaah sai ta miqe tana salati da nuna tashin hankali na ta makara yin asuba akan lokacin ta ga shi gari ya gama waye wa batai sallah ba, harda kwalla.
"Sorry love yi komai a hankali kin ji? jeki kiyo alwala sai kiyi sallah abin ki, kizo mu ci abinci har an kawo mana,"
D'aga kai tayi tana jin daɗin yanda yake lallaba ta.
Alwala tayo tayi sallah, tare da yin azkar abinda bata taba yi ba dik tsawon rayuwar ta,ta na gamawa sai ta fara rera karatun qur'ani da ka, Umar dan daɗi har wani lumshe ido yake yi, sai da ta kai qarshe sannan ta yi addu'a ta kwantar da kan ta jikin gado, hawaye na zuba daga gefen idon ta, Umar ne ya buɗe ido ya gan ta a haka, da sauri ya tashi ya zauna a gaban ta tare da lankwashe qafafun shi, yana mai tambayar ta dalilin kukan nata.
"Yah Umar ka yi hakuri, dan Allah ka yafe min ni na yarda kuma zan hakura sannan zan jure ko da zaka rabu dani a wannan ranar ne, amma ba zan taba iya haɗa shimfida da kai ba,"
"Innalillahi Jameelaah kina da hankali kuwa? Me ya shiga kan ki ki ke kiran kalmar rabuwa a tsakanin mu? ni ne fa Umar naki, me ya same ki? Akan me kike kira mana rabuwa, jiya jiya Allah ya hada mu a bainar jama'a Allah ya mallaka min ke sannan ki so rabuwar mu a yau da na tashi cikin farin cikin kin zama mallaki na,"
Kuka ne ya k'wace mata mai tsanani har tana shessheka, Umar hankalin shi ya tashi ainun, dan haka ya matsa ya jata jikin shi sosai ya na lallashi,aikuwa sai ta shige jikin shi tayi luf tana ci gaba da kukan,cikin zuciyar ta tana ayyana daɗi da laushin jikin shi.
"Dan Allah ki sanar dani me ke damun ki kar zuciya ta ta buga,"
"Yah Umar inna ce maka ni ɗin ba budurwa bace zaka iya ci gaba da zama dani? Na san ba zaka iya ba, kuma babban kuskuren da muka yi kenan nida Mamana, wanda har Babana bai sani ba har yau, dan Allah ka rufa min asiri kan kowa ya ji ka sallame ni na tafi gidan mu, na yi dana sanin rufewa wanda zuciyata ke matuqar so wannan babban sirrin saboda tsoron kar ka rabu da ni tun kafin ka aure ni, zan iya mutuwa akan son ka amma ba zan iya jure ha'intar ka ba,"
Kuka take sosai kamar an aiko mata Ramai ta fece qiyama.
Ji yayi kamar an doka masa guduma a tsakiyar kan sa, amma ganin yanayin da take ciki sai ya sanya shi nutsuwa dan jin me ya faru har ta rasa budurcin ta.
"Zan iya hakuri da dik wani abu a duniya, amma ba zan iya hakuri na rasa soyayyar ki ba, ba zan iya ci gaba da rayuwa in bake a cikin tawa rayuwar ba sanar da ni me ya faru ki ke waɗannan kalaman masu tada hankalin mai sauraro,"
'Wayyooo dadi,lallai maganin mallakar nan na aiki, tin yanzu ya fara ji na kamar wani sashe na jikin shi,'
Cikin tsananin kuka da kauda kai wai ita kunyar bashi labarin da zata faɗa yanzu take yi ta soma magana.
"Yah Umar...........
*A dandana wannan, da babu gwanda ba daɗi, na san wasu zasuce yayi kaɗan, ayi hakuri da ban yi niyyar typing ba ma yau dan babu appetite ɗin taifin ɗin sammmmm*
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 14:
"Yah Umar tin....tin....tin inaaa yyyarinya ne.....aka yi min fyad'eeee"
Kuka take mai tsananin ratsa zuciyar wanda bai san wace ce Jameelaa ba, Umar sakin ta yayi ya kafe ta da ido, a hankali idanun shi suke rinewa daga haske zuwa jawur, yawun bakin shi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 30