Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yasa ake qara maki jini, an deb'i na mahaifin ki aka sanya maki," Wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskar Jameelaah, har ta kasa rufe wa saida ta saki ihun murna, sannan ta hau cewa, "Wayyoo Allah na daɗi ana baqin ciki in an yi.j bari ni dai murna nake, dana haifi shege ni jameelaah dana barwa kaina mummunan tabo a rayuwata, daga nan duniya har lahira, wayyooo Allah na gode maka, Ramai zubarwa kika sa ayi?" "Yo wa ya san ya akai ya zube, ba dai mu an zo an kiramu ba muna gida aka ce ga ki a kwance,shine muka tare me tasi aka kawo mu asibiti, likita yace aiki me yawa kikai ko dai wata wahalar kika sha shine ya janyo zubewar cikin,dan kuwa tin a can inda kika faɗi muka same ki cikin jini face-face, dama so nake ki farka naji ina kika je? JAMEELAAH baki san kiyi nadama ba ko? Shine kika je kika zubda cikin? Jameelaah ba dan mahaifin ki ya taushen bama ba zaki ga haqorina ba yanzu" "Ramai ban zubda ciki ba, ban taba sawa a raina zan zubda ba, tabbas wahalar dana sha ne na zuwa na sami waɗanda sukamin cikin shine ya sa ya zube, amma Ramai koda cikin shegene ban sa ma raina zubda shi ba, sai dai na san dik sanda na haifi abinda nake ɗauke dashi qarshen farin ciki ya zo min kenan har abada" "Allah na ganin ki, in ma zubarwa kikai, dan dai ke yanzu ba abar yarda bace," Likita ne ya shiga ya duba ta, sannan ya mata murna da farfaɗo eada tayi, dan Ramai ta sha kuka har ya tausaya mata. Sai da suka yi sati da wasu kwanaki aka sallame su, sannan likita yace ta guji yin aikin wahala nan da wasu watanni, mahaifar ta ta samu rauni sosai. Ramai ta yi iya qoqarin ta na ganin Jameelaah ta gyara lamuran ta ba laifi, rashin Umar kaɗai ya shiga jikin ta ya sa tayi laushi ta koma ga Allah. ************************* Bayan dogon bincike da tabbacin nagartar zuri'ar su Hauwaa, Iyayen Umar sun kai qoqon barar nema wa Umar ɗin auren Sapnah, ba wata ja in ja kuwa iyayen ta suka amince, nan da nan kuwa aka fara shirye-shiryen biki ba kama hannun Yaro, Umar ya yi iya qoqarin shi na ganin Sapnah amma rowar kan ta take yi masa, wataran haka ba zai zo neman ta tana lab'e tana ganin shi amma tace bata nan, Aunty Hauwa da Umaimah sun yi dik iya yin su taqi yarda ya gan ta, kullum sai dai suyi waya da Chatting, Da sadaki da lefe dik gaba ɗaya aka kai tare, Umar Allah Allah yake ranar d'aura auren su tazo. Yau Sapnah na zaune a parlour ita ɗaya, Aunty Hauwaa sun haɗa baki da Umar da Umaimah akan sai ya ga farin cikin shi yau, tana zaune da Muhammad tana sanya masa kaya ta yi mishi wanka, sai qiriniya yake yi, sanye take da doguwar riga mai kyau kalar maroon, da aikin baqi a jikin ta, ta dora gular rigar akan ta, tana miqewa hular ta sauka ta bayyana gashin ta da ya ke ta shan gyara saboda gabatowar auren ta, bata wasa wajen gyara kan ta, dik wanda ya santa watanni biyu baya ba zai gane ta ba yanzu sai ya kalla da kyau. "Muhammad ka nutsu ko na sa maka wando a matsayin riga," Dariya yaron yayi tayi kamar ya na gane me take faɗa. Qamshin turaren shi ta ji , mai sanyi da kwantar da hankali, limshe ido tayi, ta yi murmushi ta tabbata kizo qamshin shi yake yi mata, amma ta san ba Umar bane. Hular ta ta maida saman kan ta, sanan takwashe sauran kayan Muhammad dake qasa, ta juya cike da murmushi zata koma d'aki ta aje kayan. "Ko baki faɗa ba nasan tinani na kike yi," Ihu ta bude baki zata yi ta toshe da hannayen ta biyu da sauri, kayan Muhammad da man da komai suka watse a qasa, Murmushi kawai Umar ke bin ta da shi, hannayen shi zube a aljihun shi,  takawa ya farayi gaban ta tana qanqame idanun ta, sai da ya gama qare mata kallo, sannan ya duqa ya fara kwashe kayan da ta zubar. Bude ido tayi a hankali ta gan shi yana kwasar kaya, da sauri ta duqa itama ta na kwashewa, kallon juna suka tsaya yi, da sauri ta amshe na hannayen shi zata gudu ya tare qofar d'akin, "Ai baki isa ba yarinya, ki dawo kawai mu sha hira, na riga na gama ganin abinda ake min rowar ta shi, a gaskiya ba dan kar na yabi kaina ba da nace kin yi kyau sosai, soyayya ta ta karɓe ki," Hararar wasa ta yi masa, sannan ta dawo gefen shi ta tsaya tace, "Soyayya ta dai ta karɓe ka, kaga yanda kai kyau kuwa? Har wata qiba kayi," "Lallai yarinya kince wani abu, wato ma tsokana ta kike ko? Zaki gane ne dan Allah ki maimaita hakan randa aka kaimin ke in kin cika matsokaniya," "Kai ma ka maimaita kaga in ban maimaita ba, kasan in aka ce min A sai na ce Z" Kad'a kai kawai Umar yayi, yasan bata san dawan garin bane shi yasa, Zama yayi a kujerar dake kusa da shi, ya kama goshi da hannu daya, "Washhhh kaina ciwo yake yi yarinyar nan zaki gane Umar kika ba wa baqar izaya haka, sanda zan damqe ki ina tausaya maki," Bata ce komai ba sabida ta gano me yake nufi sarai, Ruwa ta d'akko masa da juice, sannan da maganin ciwon kai, aje masa ta yi ba tare da ta ce komai ba ta koma kitchen, abincin da ta dafa ta d'eba masa, sannan ta yanka fruits ta kai masa. Zama yayi ba kunya ba musu ya cika tumbin shi, tana ta kallon shi, tana lumshe ido, hango ta kawai take a jikin shi bayan aure suna cin abinci tare, firgigit tayi kamar wadda aka mintsina, ta kalle shi taga ko ya gano irin tinanin da take "Lafiya kike kuwa?" "Qalaou nake,to ya aikin yau? Ina fatan komai normal?" "Ehhhh to gaskiya akan sauran ranaku yau na samu sauqin komai, sai dai na sha wahala kafin mu haɗa plan din ganin gimbiya," "Habaa habaa ai  dama na faɗa da wadannan masu kan mutanen aka haɗa baki ka samu damar sani a kwana haka, ba komai zan rama ne," "Well, hakan na da kyau ai kin san in aka maka abin alkhairi ana son ka maida da alkhairi kaima," "Ya yi maka kyau, ai kai yau kamar sallah haka ke jin kana san," "Kema kuma haka ba, na san kin ga ɗan saurayi kyakkyawa hankalin ki ya kwanta," "Kaine ka ganni yau ni kusan dik zuwan da kake yi ina ganin ka ai" Zama ya gyara ya kalle ta, ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya fasa, ya jinjina kai alamar zamu haɗu ne, dariya ta dinga masa, "Ka ishen da surutu ban tambayi d'iya ta ba, hope tana lafiya ko?" "Kwarai kuwa tana lafiya, sai dai ta na kewar ki fiye da yanda nayi kewar ki," "Ka dai dage sai anyi zancen ka, ni maganar d'iyata nake ba taka ba,ka shafamin kan ta in ka koma, Allah ya yi mata albarka," Sallamar Ishaaq da Hauwaa ce ta katse su, dan har yamma tayi lokacin dawowar su Ishaaq din basu ma kula ba suna ta hira, "Ohhhh Sapnah an boye miji anan ana ta shan hira, aka koramin mata waje," "Yah ni fa bani bace, in fact haɗa ma baki suka yi sai ganin shi kawai nayi anan," "Sapnah ba kyau qarya fa, ke kika min waya kika ce nazo kin kora Aunty hauwaa gidan Umaimah," Kallon shi tai da wani kallon inna kama ka zaka wahala a hannu na, dariya sukai ta yi mata,ta shige d'akin ta, ta kwanta tana murmushn jin daɗin ganin ruhin ta. Bata san sanda ya tafi ba sunyi-sunyi ta fita suyi sallama taqi, Ishaaq yace baya son gulma tana zaune tana kalallame shi da hira sai da ta gan shi shine zata qi fita,tana jin su tayi luf abinta tana dariya qasa-qasa. *********************** "Assalamu alaikum, aban awara ta nera hamsin" "Zauna ka bi layi bari na gama sallamar waɗannan sun riga ka," Jameelaah ce ke ta soya awara a cikin gida sanye da mayafi da riga da zani, dik ta rage haske dan kuwa tin da taji sauqi sosai ya bata sake saka qafarta a waje ba, kullum tana gida, ganin shiru da tinani zai iya sanya mata ciwo ne kawai sai ta maida hankali wajen saida awara a cikin gida, mutane kuwa nan da nan aka fara siya, kun dai san Jameelaa da nasibin talla, wayar ta ce ta fara ringing, ta d'aga ta zaro ta daga jikin ta, no qawar ta ta makaranta ta gani, wadda suka bata bashin kuɗi taci suna. Share majina tayi da gefen mayafin ta ta d'aga kiran tace, "Hello Khadeejah, ya kk?" "Lafiya qlou, kina lafiya kuwa? Kwata-kwata ko a social net an daina ganin ki, tinda kika haihu kika daina zuwa school, qawayen mu ana ta tambayar ki, yaushe zaki dawo na yi masu albishir?" "Dan Allah qarasa zuban awarar," "Ta nawa ma kace? Yi hakuri ina waya," "Ta ɗari zaki samin," "Wake saida awara? A ina kike ne haka?" Shiruuu tayi zuciyar ta na raya mata ta yanka qarya kawai, saboda kare AJIN ta.................. *What do u think guys? A kare aji ko aji down?* [09/09, 10:39 am] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA   💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 43: Shiruuu ta yi har Khadeejaah tayi zaton ko layin ya tsinke ne, sai taji suna magana. "Shegiyar qarya, ai na je gidan mijin na ga ba ta nan, dana bincika sai naji ance ya mata dukan tsiya ya kore ta, ya mata saki uku, yanzu haka tana gidan su, ko gidan ma mijin ne ya sai masu, sana'ar da Baban ta yake da abin hawan shi dik shi ya basu, amma ta dinga qera mana qarya tana kiran uban ta qusa ne a gwamnati, qusa a gwamnati ko qusa a gyaran machines" Dariya sosai suke yi, Allah kaɗai ya san iya mutum nawa ne suka ji wannan labarin dan kuwa taji dariyar mutane da yawa ba zata iya tantance mutum nawa bane a wajen, ga kida qasa-qasa yana tashi tana jiyowa Allah kaɗai ya san ko ma a gidan biki ko Bd party suke tinda su bini-bini an yi party dan kawai a kashe kuɗi. Hawaye ne ya dinga sauka ta na zuba awara tana miqawa, kuma taqi kashe wayar, dan ta san ko kud'in sun qare suna da na sake sa wasu. Khadeejaah ce ta ɗauki wayar ta dan suyi hotuna,kawai sai taga bata kashe ba ashe, ji tayi gaban ta ya faɗi, (kunsan gulma in kayi ta ko kana sane kayi in aka kama ka ba daɗi) Da sauri ta kashe ta na nuna ma sauran, sune suka dinga nuna mata sai me dan Jameelahn ta ji ai da sun san ma gidan uban nata har can sai sunje sunga kwal uwar daka, (gulma ba a wajen talaka ta tsaya ba fa ooo, masu kud'in ma manyan magulmata ne wasun su, sai dai su gulmar su akan abin duniya ta fi tasiri). Bayan ta kammala saida awarar ranar ne ta ware riba ta ajiye, sauran jarin ta bayar a siyo kayan yinna gobe, dik ta zama wata so silent magana ma wahala take yi mata sai abinda ya zama dole take tankawa ko ta faɗa, haddar qur'anin ta data bari ta zube a banza ta kama tana tisawa, ta nan ta samu zuciyar ta ta fara yin sauqi, amma still soyayyar Umar na nan daram a ranta ta san da shi zata koma ga mahaliccin ta. ********************** Sai da ya gama kwashe komai mai amfani na d'akin nasu wanda zai buqata, sannan ya kai mota ya zube su, dakin ta ya nufa dan dubawa ko akwai wani abu mai amfani da zai cire mata, sauran dik bayarwa zai tinda da kud'in shi ya siya ba da na wani ba, Kamar ance ya bud'a kayan ta, yana bud'awa yaga wata baqar leda Viva zarowa yayi, yaga damin kuɗi a ciki, a qallah sun haura dubu ɗari uku bai tsaya qirgawa ba, yana ganin yanayin su ya san na shi ne wanda yake bata, bai taɓa bata lokaci ba ya saka a aljihun shi, ya ci gaba da duba kayan, sarqoqin ta kayan kwalliyar ta da dikkan kayan sawar ta, ya kwasa ya kai wata motar, yaran da suke taya shi aiki suna ta sanyawa a motar, yana kammalawa, ya bama drivern kwatancen gidan su Jameelaah, ya bashi da ledar aljihun shi ta kuɗin yace su kai mata su dawo a ɗebe kayan gadon a kaiwa Kulu can asalin gidan ta. Kulu harda kukan murna tayi, dinning din shi anan aka bar shi, da manyan fridge guda biyu, sabon fenti za ai ma gidan, a gyara shi, iyayen Sapnah sunce su zasuyi kayan d'akin diyar su basu buqatar komai nashi. Koda saqo ya iske Jameelaah kuka ta sanya sosai tana sake danasanin abinda ta aikata, kuɗi take so da mallaka meye bata samu ba a wajen Umar? Meye Umar bai mallaka mata ba? Ya bata kan shi, ya bata jikin shi zuciyar shi da rushin shi, ya mallaka mata dukiyar shi, ya bata dikkan soyayya da kulawa, wanda da wahala a samu miji mai halin Umar a wannan zamani amma ta yi fatali da komai saboda son zuciya ta na hango fiye da abinda take samu. "Baiwar Allah ki nuna mana inda zamu aje kayan mana ko mu bar maki anan zaki shiga da su ne?" Cikin sanyin jiki ta nuna masu hanya, suka dinga shiga da kayan sawar ta, manyan laces ɗin ta da atampopi dik ba wanda ya taba mata, jakunkuna kamar lefe, ta kalman ta da komai da komai Umar bai taɓa mata su ba, harda sarqa da d'ankunnen ta na zinare sai da ya had'o mata da su da kayan Humairah, ɗaukan kayan humairah tai ta qanqame tana ta rusa kuka. "Dan Allah Yah Umar ka dawon da d'iya ta ka maida kayan ka bana son su, kaico na ni Jameelaah na yi mummunar shukar guba, ga ta tana illata kowacce gaba ta jiki na, ina zan saka raina yau, wayyooo Umarr, dan Allah ka maida ni d'aki na" "Dan Allah kiyi hakuri ki rufen baki, kar ki sa maqota su kasan kunne habaa, kan ki aka fara saki? Ki godewa Allah ma ya maido maki da wannan, wani ne ko tsinke ba zaki gani ba, kuma wannan abin da yayi ya yi dai-dai, na tabbata ba zai qi barin Humairah in tai wayo tana zuwa mana hutu ba, tinda har ya iya aiko kaya, yanzu dole yaji tsoron hana ki d'iyar shi kar a koya mata mummunan hali, Jameelaah ni mahaifiyar ki ce, iyaye kan nemi gafara wajen yaran su musamman in sun san sun cutar da su, a yau ina neman gafarar ki akan cutarwar da na yi miki ta bangaren tarbiyya, ki yafe min, kuma ki ban had'in kai na koyar dake abinda ya dace mai kyau, ki yafe min, ki yafe min Jameelaah," Jameelaah rungume Ramai tayi sukai ta kokawa, har Bukar ya koma da saqon kayan yin awara ajewa yayi ya isa ya zauna yana tambayar waɗannan kayan fa masu tarin yawa daga ina? Nan Ramai ta masa bayani shima ta nemi yafiyar shi, suka yafe wa juna. "Mama (sunan da suka koma kiran Ramai dashi kenan)  ni ina da shawara fa, tinda kin iya girki, mai zai hana ki samu ki dinga yin dambun naman kaza ana siyarwa? A irin robobin nan, a kafa waje anan qofar gidan, tinda kan hanya ne, za a yi kasuwa, sosai" "Kuma kacewani abu fa Bukariri, bari mahifin ku ya shigo ayi maganar in shawara ta tsaya ni da kai na zan dinga yi," Kallon Jameelaah tayi ta ji me zata ce akan hakan amma taji shiru, Jameelaah na can duniyar tinani, ta langwab'e kai gefe hawaye na zubar mata, fatan ta kawai Umar ya maida ta gidan shi. ********************** An d'aura Auren Sapnah da Umar akan sadaki nera dubu ɗari, ba wata hidimar biki da akai in ba wuni da iyayen su suka yi ba, Umaimah da Aunty Hauwaa da Mum sun tsara zasu ɗauki nauyin yi ma ango da amarya walimah bayan an kai amarya gidan ta kamar yanda islam ya tsara, sun gama qayyade iya adadin mutanen da zasu gayyata, sun gayyaci kala-kalan mutane  guda hamsin, a babban wani hall za a haɗu  duk a yi walimar. Sun riga sun yi order na abincin da za a ci a sha, sannan da takeaway da mutane zasu tafi da shi. Ishaaq da Haroon tare da Daddy sun sake ma matan su kuɗi dan cika burin su, dan haka ba zama sun zama busy, hakan ya sa Sapnah damuwa ainun, tana cikin matsanancin buqayar lallashi a wajen Aunty Hauwaa da Umaimah, dan kuwa Umaimah qawar ta ce sosai, sun shaqu matuqa. Daga ita sai Safiyya a d'akin, tana ta kukan rabuwa da iyaye da 'yan uwan ta, Maman ta ta shiga ta same ta kwance saman cinyar Safiyya suna ta kuka. "Ikon Allah ! kuna nan kuna ta kuka ga qawayen ku can a d'akin ku kun baro su kun dawo d'akin Abban ku, wa ya fada maku aure mutuwa ne? Ai ranar farin ciki ce yau, addu'ar neman alkhairin dake cikin shi da neman kariya daga sharrin dake ciki zaki tayi a zuciyar ki amma ba kuka ba, dan ban ga me kukan zai qara maki ko ya rage maki ba, ke kuma da kika zauna kike taya ta kin kai ma mutanen da nace ki kai masu abinci abincin?" "Eh na kai Ummaah, Ummah kukan kewa muke yi ai, yanzu in ta tafi ba zan dinga ganin ta ba akai-akai," "Ban son shashanci, da ɗin akai-akai kike ganin ta? Ina makaranta take yi da a can wani waje, daga baya ta koma wajen Jidda, to yanzun ma in ta koma gidan ta ba wani abu bane sabo in kin so ganin ta zaki je can," "Taso kin ji ta gidan Ummaah, daina kuka, ke dai ki riqe biyayyar aure, bana jin ki ta kowanne fanni,saboda na san baki da dama wajen iya girki, kwalliya, iya tsara kalamai masu daɗi, shagwava kuwa har ta saidawa kina bayarwa, ga shi wajen qamshi a gaskiya ke din abar yabawa ce mutum baya gajiya da shaqar qamshin jikin ki, kina da tattali baki da almubazzaranci, dai-dai misali kina da tsoron Allah da ibada, Sapnah ko ta wanne bangare za a lissafa Kyakkyawan hali kin mallaka, to me ne ne abin kuka? Kuka ya kama wadda bata da dik waɗannan abubuwan da na lissafa amma ba ke ba, share hawayen ki, zuwa qarfe biyar za a zo a kai ki d'akin ki kinji? Dan Allah kar ki bani kunya, kar ki kunyata zuri'ar mu, Allah ya yi maki albarka, ya baku zuri'a d'ayyiba saliha mumina, Allah ka saɓa halayen su, in yayi fushi ke ki sauka,in kinyi fushi shi ya sauka, Allah ya kare ku daga sharrin zamani da rud'in duniya, Allah ya kare ku daga sharrin shaid'an kin ji? Taso maza kije wajen qawayen ki, dan ke suka zo ba dan kowa ba, ba daɗi ki bar su su kaɗai ki dawo nan ki tare" Share hawayen ta tayi suka jera da Umman nasu tana riqe a jikin Umman suka fita, wasu yan uwan su suna ta tsokanar ta akan shagwab'ar ta tayi yawa ko Safiyyah dake qarama bata shagwab'a sai ita, sake lafewa tayi jikin Ummaan nasu, tare da boye kan ta. Daf za su shiga d'akin su suka ji qawayen su na ta hira, wata Ameerah na magana, "Dik irin kurin Sapnah ace bikin ta ko dinner babu, ba wanai casu ba party,  a gaskiya wannan yawa ne, ba aji" Safiyyah ce ta bude qofar cikin fushi zata yi magana Sapnah ta hana ta, nan da nan kuwa ta kafe ta da ido, ranta ya ɓaci, ta danne ɓacin ranta, "Kar ki ce komai Safiyyah, dik kuri na ban taɓa yi wa kowa qarya ba, na godewa Allah ina da surutu na sani amma ban taɓa cewa kowa komai akan aure bama balle nai qaryar za a cashe a bikina, gobe ki zo hall.......... ki ga me za ai inshaa Allahu, ina gayyatar kowa a cikin ku dan ganin me zai wakana goben," Nan da nan kuwa qawayen su sukai ma Ameerah caaa, har wadan da da ace bata zo ba suna da niyyar topa albarkacin bakin su, amma ganin an kama Ameerah ya sa sukai lif suka wayance. Zama Sapnah tayi ta takure, tana jin su bata tanka ba, Safiyyah dataji daɗin amsar da Sapnah ta bayar ta ware sai hira da qawayen su take yi. Umar ke ta kiran ta amma taqi d'agawa, dan sai take jin wani haushin shi dan zai raba ta da iyayen ta da kowa nata, sai take ganin hakan a matsayin son kai. Message ya tura mata ta whatsapp, da kwalliyar da yayi, lokacin daurin aure, murmushi ne ya k'wace mata, dan kuwa ya tafi da numfashin ta, Itama tura masa nata tayi, ya maido mata da qatuwar heart, ~kiyi magana mana babes, ki faɗan yanda kike ji a yanzu, na matsu lokacin kawo ki gare ni yayi, na matsu na nuna maki tsantsar qaunar dake danqare a ruhi na, ina son ki Mrs Umar~ Zaro ido tayi waje fall hawaye, lallai ma Umar dinnan mugu ne, wato ya matsu akai ta ya gwada mata muguntar daya tanadar mata dai, banza tayi da message ɗin ta ci gaba da share hawayen ta, qirjin ta na bugawa da qarfi a dik second ɗin dake qarato da kaita d'akin mijin ta. Kiran sallar la'asar ne ya tada su, wasu kuma suka zauna saboda basu yin sallah, wasu basu tashi ba saboda kar su goge kwalliya, wasu kuma da alwalar su, Aunty hauwaa ce tayi sallama ta shiga d'akin, Sapnah na ganin ta ta kwab'e baki irin na shagwab'ar nan ta miqa mata hannayen ta, kamar wadda za a ɗauka, aunty hauwaa da sauri ta isa gare ta ta fara lallashin ta. "Taso muje kiyi sallah," D'akin Abban su suka shiga, ruwane zundum mai qamshi sosai da lalle aka cika kwamin wanka da shi, (lallen jiqawa ake a tace sai a zuba a ruwan wanka ko bayan anyi wanka sai a wanke jiki da zallan ruwan lallen saboda fata tai santsi da haske). Kayan ta aunty Hauwaa ta fara taya ta cirewa bayan ta mata bayani tayi wanka kafin tayi alwala, tayi sallah su shirya ta ita da Umaimah. Bata musa ba dan ko ta musa ba kyale ta zasu yi ba, taji daɗin ruwan d'umin kuwa sosai, ya dauke mata gajiyar da tayi sai da ta jiqu da ruwan lallen nan qamshin turarukan suka ratsa ta, sannan Aunty Hauwa ta d'akko irin garwashin nan na leda ta turara ta da kayan qamshi,ta bata farin musk mai kyau ta shafa a HQ, ta shafa mata alimun a hammata kadan, bakin ta kuwa sai da tayi brush,wanke da mouth wash ta qara da fesa mouth freshner, sannan ta bata kaninfarin guda ɗaya ta tauna, tai ta yamutsa fuska kuwa wai da yaji, Aunty hauwaa bata kula ta ba ta ci gaba da gyara qanwar ta ta ko ta wanne kusurwa bata bar wani datti ko kafar wari a jikin ta ba, gashin ta kan shi sai da ya sha turaren wuta dana gashi, sannan ta gyara mata shi ta d'aure mata. Wasu fitinannun kaya Aunty Hauwaa ta deb'o ta bawa Sapnah ta saka riga ne da wando, rigar qarama sosai ta manne da cikin ta, hannun bra gare ta, sai wando iya cinya, kalar baby pink, sai ta bata wani skirt dogo mai faɗi sosai har qasa yake ja, da wata riga mai shara-shara itama mai dogon hannu da mannewa a jiki tace tayi sallah sannan suyi kwalliya. Bayan sunyi sallah dika Umaimah ta gama shayar da Ummee, ta je ta tsara mata kwalliya mai kyau,irin simple din nan,nan da nan kuwa ta qara yin kyau, ga turaruka masu kyau da tsada da suka feshe ta da su(inma baki da mai tsada amarya ko ɗan d'ure mai daɗin qamshi da sanyin qamshi asanya abinki, iya kud'in ka iya shagalin ka kar dai a yi tsami) Laffaya kalar baby pink mai ratsin baqi da golden a jiki kamar kayan dake jikin ta suka naɗa mata, takalmanta da qaramar jakar hannun ta golden ta

Chapter 26 of 30