ta yi Jameelah bata daina kuka da roqon Baba akan ya barta ta koma gidan su Umaimah ba, a ranar da safe Jameela ta tashi idanun ta sun yi mata qanana saboda kuka da ta kwanayi, haka ta shirya zuwa makaranta dan samun sauqin rad'ad'in da take ji a zuciyarta, a hanya ko ci kan ki bata ce wa Mamalo ba da ke ta yi mata surutu, ko kanzil Jameelah bata ce mata ba,Mamalo da ta kula oganniyar bata da niyyar yin magana sai taja bakin ta ta tsuke bata sake cewa komai ba har suka isa makaranta.
Koda Malam Haroon ya shigo ajin su ya kira Jameelar shiru ta yi kamar bata ji shi ba, wadda ke zaune kusa da ita ce ta maimaita mata mai yace nan ta fara masifa ta na fad'in ai ta ji shi dan ita ɗin ba kurma bace bata ga damar amsawa bane sai yaya? Umaimah ce ta kama hannun ta ta na lallashin ta akan ta yi hakuri ta daina fushin da basu san dalilin yin shi ba,
Nan take Haroon ya ji dik ta fita a ranshi, a da yana yi mata kallon mai hankali ashe ba wani hankali a tare da ita, fita yayi yana tina yanda malamai ke masa bayanin halin ta tare da ganin wautar shi na bata monitan ajin, ko shi yasa yaran suka yi ta nuna basu son ta ranar saboda bata da kirki?
A cikin satin sai da Haroon ya gane wace ce Jameela, a satin ya kwace muqamin monitan da ya bata ya miqa shi ga Umaimah.
Jameela ko a jikin ta kuwa dan dama ta gaji da playing good girl da take faman yi ba riba,a haka Haroon ya fara sabawa da Umaimah har shaquwa mai qarfi ta shiga tsakanin su.
In an tashi break ya kan yi wa Umaimah karatu na musamman, nan da nan Umaimah ta wuce sauran 'yan ajin su a karatu.
***********************
Cikin wata iriyar murya da ke nuna tsananin matsuwa da buqatuwa take magana,
"Haba Haroon, in baka biya min buqata ta ba wajen wa ka ke so naje? Ko so ka ke na fara kawo maza gidan yayan naka?"
"Amma dai Aunty baki da tsoron Allah kwata-kwata a rayuwar ki, mata da dama mazan su na tafiye-tafiye na tsahon shekaru ma ba iya sati biyu ba ko wata ɗaya, kuma suyi hakuri su riqe amanar auren su, amma ke ba zaki iya yin hakan ba? ke kenan chatting ɗin banza da wasu mazan da auren ki, sannan babban abin takaicin wai qanin mijin ki uwa ɗaya uba ɗaya kike neman ya biya maki buk'atar sha'awar ki wannan wace iriyar musiba ce haka fisabilillahi?"
"Kai ka san wannan Haroon ni ban san haka ba, laifin waye dan na nemi qanin mijin nawa? Kana da masaniyar cewa yayan ka ba irin yanda ban dashi ba akan ya dinga tafiya dani wajen kasuwancin shi amma yaqi, ba zan taba iya hakuri har na tsahon sati biyu ba babu shi a kusa da ni, ya na da kud'in da zai yi duk wata zirga-zirga da ni amma ya ki yin hakan,ai ni din ba dutse bace ina da bukatar miji na a kusa kuma na sanar da shi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba amma ya k'i ji"
"Aunty fita ! Fita min a d'aki bacci zanyi bana son abinda ki ke yi min,"
"Sai dai ka rife ina ciki, ba inda zani"
Takawa tayi kusa da shi tare da cire doguwar rigar da ta dora akan wasu tallatattun kayan bacci da ta saka, wani irin qamshi ne mai sanyi ya ziyarci hancin Haroon, kafe ta yayi da ido idanun shi sun sauya kala zuwa jawur saboda ɓacin rai dan kuwa kwata-kwata bata bashi sha'awa ba duba da yanda ya tsani zina da dikkan dangogin ta kuma cewar ya na yawan yi wa kan shi addu'ar Allah ya tsare shi daga zina da dikkan abinda ya shafi zina har qarshen rayuwar sa, shi yasa Allah yake kare shi da jin sha'awar Aunty Hauwa'un a duk sanda ta zo masa da buqatar ta,kafin yayi wani yunquri ta fada jikin shi qirjin ta ya na gogar nashi,a kid'ime Haroon ya furta kalmar,
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musib....."
Da sauri ta rufe bakin ta da nashi, ta fara sumbatar shi,wata iriyar bangaza ya yi mata ta bugu da jikin ginin d'akin nashi, nan da nan goshin ta kuwa ya kumbura ya tashi ɗaukan rigar ta yayi ya wurga mata, tare da d'aga murya cikin tsananin bacin rai ya ce mata,
"Allah ya saka mini abinda ki ka yi min ba zan taɓa yafe maki ba azzaluma mai cin amanar auren ta, Allah ya shirye ki ya yaye maki wannan jaraba da musiba da take tare da ke, wannan wanne irin zamani ne lalatacce haka ni namiji ban neme ki ba ke mace ki ke nema na? Ki bar min daki ko na illa taki yanzun nan mara hankali da tunani kawai,"
"Ni ka wulaqanta haka ko Haroon? Ni ka tozarta Haroon? Tabbas sai na wulaqanta ka kamar yanda ka wulaqanta ni, zaman gidannan sai ya gagare ka Haroon, mu zuba mu gani ni da kai wa ye mai nasara,"
"Nasara tana a wajen Allah kuma a wajen shi nake neman tsari da ke da dikkan sharrin da ke tattare da ke, komai zaki min zan barshi akan qaddara ta ce a hakan kuma ba zan yi fushi ba, zan godewa Allah a dik yanda yaso ya ganni, kuma ta Allah ba taki ba,"
"Mu zuba mu gani, mara rabo kawai,"
"Gaki nan babbar mara rabo, kina da aure ki ke neman qanin mijin ki,"
Ɗaukan rigar ta tayi ta saka tare da ficewa a d'akin nashi ta daki qofar a yayin futar ta.
Rintse ido yayi yana sauke numfashi mai zafin gaske, ya zai yi da wannan jarababbiyar mata, gata bata fushi da duk abinda zai yi mata gobe ma sake dawowa zata yi, dik yanda ya so ya mata rashin mutunci sai dai in yayan shi bai yi tafiya ba amma sai ta sake fito masa da wani sabon salon, har abin key ɗin d'akin shi sai da ta sa aka cire gaba ɗaya saboda rufewa da yake yi ta ciki.
Hango sanda ta ke masa kiss yayi a idanun sa cikin sauri ya sa hannun sa na dama yana ta goge bakin shi tare da zubar da hawaye gami da yi mata Allah ya isa.
"Ya Allah ka kare ni daga sharrin wannan baiwa taka, kar tayi galaba akaina, Allah ka kare ni daga aikata zina har qarshen rayuwa ta"
Kad'e wajen kwanciyar shi yayi sau uku tare da bismillah ya yi addu'ar bacci ya rufe ido ko bacci zai ɗauke shi ya manta da abinda ya faru,amma sai bacci ya qi zuwa masa sam a wannan daren, shin me zai yi ya taimaki rayuwar shi ne?
'Ina ganin maida hankali zan yi akan kasuwanci na, na daina dawowa gidannan ko a shago sai ina kwana musamman sanda Yah Ishaq yayi tafiya, in ba haka ba zuciya bata da qashi ban san sanda matar nan zata iya ribata ta ba, ya Allah ka agaza ma rayuwar maraya'
Da wannan tinanin bacci ya ɗauke shi cike da mafarkai kala-kala wanda suka sanya shi tashi cikin mamaki.
"Me zai sa nayi mafarkin ta kuma? Bayan ba wata alaqa ta soyayya a tsakanin mu?.......
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 10:
Tunda ya farka yake ta qoqarin kawar da tinanin mafarkin da yayi akan ta amma ya kasa mantawa, har ya gama shiryawa dan zuwa makaranta bai bar tunanin ta ba, daga qarshe sai ya sakar wa zuciyar shi ragamar ci gaba da tunanin ta dan yin hakan shine kawai mafita a gare shi a wannan lokacin.
Yau Aunty Hauwaa har qarfe takwas na safiya ta yi ta na d'aki bata fito ba,saboda kai ya kumbura mata ya yi him ta gaban goshin ta, ga wani azabbben ciwon kai da take ji ta rasa inda za ta saka kan ta ta ji daɗi a ran ta,cikin ran ta take ayyana,
'Ni yaron nan ya tozarta haka,ai kuwa daga daren jiya yayi na qarshe, ko ya biya min buqata ta ko kuma na rusa masu kyakkyawar alaqar dake tsakanin shi da dan uwan shi dani yake zancen in ya san wata bai san wata ba'
Bangaren Haroon kuwa yana zuwa makaranta da ita ya fara tozali, murmushi tayi masa sannan ta sauke kan ta qasa tana kallon qur'anin ta, kafe ta yayi da ido yana tuno mafarkin da yayi da ita, da sauri ya fara korar shaid'an sannan ya buɗe murya ya fara karatun qur'ani, nan da nan kowa ya nutsu suka bashi hankalin su, Jameela ce take tab'o Umaimah wadda hankalin ta gaba ɗaya na kan karatun da ake yi masu.
"Ke Umaimah, dallah tambayar ki zan yi,"
"Dan Allah ki bari a gama mana qari in ya fita sai muyi maganar,"
"Yana da matuqar amfani a wajena"
"Menene haka da ba zai iya jiran malam ya fita ba?"
"Da wannan surutun da kike yi da amsa ki ka bani tini da an wuce wajen,"
Malam Haroon ne ya ce,
"Jameela fito nan,"
"Me nayi?"
Wasu daga daliban ne da sauri suka riqe baki dan jin tambayar da ta yi ma Malam Haroon, malamin da kowa ke girmamawa saboda ba shi da takura kwata-kwata, cike da Mamaki ya kalle ta ya ce,
"Tambaya ta ma me ki ke yi meyasa? OK fito nan in yaso sai na maki bayani,"
Cikin gantsaro girji ta fita gaba ɗaya na shanun ta sai kad'awa suke yi dan ta nuna masa ita fa ta girma tafi qarfin a na wani kiran ta gaban aji ana dizga ta, ɗauke kai yayi daga kallon ta, shaid'an na sake maida idon shi wajen kallon qirjin nata, da sauri ya ɗauke kan shi tare da a'uziyya a cikin ran shi,cikin ranshi yake ayyana,
'Tin jiya na fara jin wannan baqon lamarin akan mata, meke damuna ne haka?'
Ganin ta zo kan shi ta tsaya qerere ne ya sanya shi saurin dakatar da ita ya ce,
"Tsaya can malama, ko kin ji na ce ki zo daf dani kamar zaki fado min akai ne? Ke wai me ya sa baki da tarbiyya ko kaɗan ne? Amma babu komai Zanyi maganin ki yau, faɗa min a wacce sura muke sannan aya ta nawa muka tsaya?"
Tinani ta hau yi ta rasa ina suke kwata-kwata, sai wani qiqqifta ido take ta na d'aga kai sama ita a dole tuna inda suke take son yi,ta kalli wajen su Mamalo da Umaimah dan a taimaka mata da amsa sai motsa baki suke yi ana faɗa mata amma ta kasa ganewa saboda tun asali bata maida hankali ta gane a ina ake ba balle ana faɗa ta gane ta iya furtawa,ganin ta kasa faɗa ne ya sanya ta murgud'a masa baki sannan ta ce,
"To ai ba ni kadai bace nake surutun ai harda Umaimah, ai da ita muke magana sanda ka ganni,"
Umaimah ce ta d'aga kai da sauri tana zaro ido waje jin Jameelah na so ta ja mata duka,dan ita ba a taɓa ma fidda ta gaban allo ba da sunan laifi, tasan ta yi surutu amma bata fatan a hukunta ta akan hakan dan ba da niyya ta yi ba,malam Haroon da ya kalli sashen Umaimah ya ganta a tsorace sannan ya gane Jameelah so take kawai a yi mutuwar kasko dan haka sai ya ce mata,
"Ban gan ta ba ke na gani, ki karanta min surar da muke yanzu ko na saɓa maki,"
In-ina ta fara yi kawai daga qarshe ta hau yi masa wata surar daban, sai da ya bari ta kai qarshe sannan yace a mata kabbara, ya yafe mata tinda a qalla ta iya karatu in yaso sai ya maimaita dan ta gane wajen da suke, sannan ya yi mata warning akan surutun daya ga tana yi, Ko irin godiyar nan bata yi masa ba haka tai komawar ta wajen zaman ta,Kad'a kai yayi tare da furta.
"Allah ya shirya ki Jameela"
Da break kuwa Umaimah yau sai ta haɗe fuska sosai, dan kuwa bata ji daɗin yanda Jameela ta tona mata asiri ba, da an dake ta fa?
"Haba qawalliya rabin duwais, me ne ne wai? Ke baki san wasa ba, na san ba zai taɓa fidda ki ba kawai na fada ne amma kiyi hakuri"
"Kin san dai bana son abinda zai zubda mutunci na ko ya yake,ke kika fara magana bani ba, amma kike son dole sai kin manna min laifin, yanzu to me kike son tambaya ta ɗazu a ajin da ki ke neman ja mana duka a banza?"
"Yauwaaaa, yanzu kuwa zan zayyano maki tambaya ta,"
Zama tayi daf da Umaimah sannan ta ce,
"Dan Allah wace shawara kika ji Mum ta yanke akan komawa ta gidan ku?dan kuwa ina da tsananin sha'awar karatun boko yanzu musamman ma ina so na ji ni ina turanci, kyau na ba zai taɓa haskawa ba in ban waye ba, ba mai kud'in da zai auren a haka na san ga talauci ga jahilci ,habaaa abun sai yayi yawa kuma,"
Baki sake Umaimah ke sauraren ta sai da ta kai aya sannan Umaimah ta ce mata,
"Yan zu ke Jameela har hango ki ki ke yi da aure a wannan shekarun namu? Har hango wanda zaki aura ma kike a idanun ki? Ikon Allah ni kuwa kin ganni ban taɓa hango ni da saurayi ba ma balle aure, ni ban san me ta yanke ba akan maganar gaskiya, sai in na je na tambayar maki ita,"
"Yauwa Ta'umancyna na gode sosai, ke in banda abinki ma yanzu fa muna kusan shekara ta 16 ne fa, sannan ace ba zamuyi tinanin aure ba? ki kalli zubina ki kalli naki mana, kina nan qirji a manne a bra kanar allo ki duba cika ta kin san........"
"In ki naiwa Allah mu bar wannan maganar, shekarun mu basu kai ba,"
Dariya mai qarfi Jameela ke yi wa Umaimah, Mamalo ce ta iso gaban su da awara a leda tana dame ta, zama tayi tare da yi masu bismillah, dan ta san ba me ci a cikin su,musamman Jameela data raina ta.
Cikin dariya Jameela ke yi wa Mamalo bayani, aiko dariya su kai ta yi mata suna nuna mata ita din bata waye ba kuma muguwar baqauyi ya ce sannan yarinya ce qarama, wasu manyan kalamai sukai ta fitowa da su daga bakin su suna faɗi, Umaimah tsoro da mamakin me suke faɗa dik ya kama ta, dan ta kula ba abin alkhairi suke faɗi ba, duba da yanayin da suke yi in zasu faɗa ɗin su maqale murya su kare baki da hijab.
Tashi tayi ta bar masu wajen tana mamakin su, anya ba zasu tabka kuskure ba kuwa ta hanyar gayyatar Jameelah zuwa gidan su? Kaiii da sakel.
***********************
Kusan wata biyu kenan da zuwan Mum dan roqon Baba akan yabar Jameela ta koma wajen su da zama, har yanzu ba su gajiya ba wajen roqon Baban, Jameelah na yi Mum nayi har ma da Dad ɗin su Umaimahn,kowa ya yi amma Baba ya qi amincewa.
Ramai ma tayi masifar har ta gaji tayi lallashin nan ma ya kafe, Jameelah ma ta yi fushi har ta gaji ta sauko, har da yajin cin abinci ta yi a gidan, Baba ko a jikin shi bai ma san ta na yi ba, hakan da take yi ma shi ke qara nesanta zuciyar shi da amince mata ta koma gidan su Umaimahn da zama tunda ba dangin iya balle na baba,kuma shi ba bokon ne baya so ba, ah ah komawar ta can ta ci jar miya anjima tace ba sune iyayen ta ba shine matsalar shi.
"Gaskiya ina ganin Daddyn su Umar ya kamata kawai a gudanar da gabatarwar aure a tsakanin Jameela da Umar, tinda ya nuna min yana tsananin son ta shima, amma bai furta mata kalmar so ba har yanzu saboda ganin makaranta yake yi ita kuma kamar ta yi qanqanta da soyayya, kaga shikenan ya hutar da mu tunanin kar mu tursasa shi yin abinda bai da niyya akai"
"Kwarai da gaske, ina jin ba sai an wani jira Umar ya kammala karatu ba, a auro masa ita kawai mun sa masu ido mu kula da su, in yaso sai ta fara makaranta kawai anan ai shi ma ba zai bar karatun shi da yake matuqar so ba akan mace,"
Dariya Mum tayi ta shafa qirjin shi,tare da kafe shi da kallon qauna ta ce,
"Daddyn Umar kenan, shin soyayyar ka raina ko macen?"
Shima cikin nishad'i ya kalle ta tare da murmusawa ya ce,
"Ni na isa na raina ɗaya a cikin su, bayan ina amfana da kowaccen su,"
Dariya suka yi cikin jin daɗin yanda dik da girman su suna nuna ma juna soyayya mai kyau da tsafta.
*****************
Mata ne dattijai masu shiga ta alfarma suka nufi gidan su Jameelaah dan kai dukiyar auren ta,sai kuma maza guda uku wanda sune a matsayin wakilan mahaifin Umar, tafe suke motocin su jere da na juna sun yi layi suna ta hirar su ta zumunci, Umar dake tuqa mazan bakin shi yaqi rufuwa saboda ya san auren gata za a yi masa.
Yamma ce liss matan layin su Jameelaa an firfito ana ta zance da samari, kun dai san ya zancen na su yake gudana.
Jameelaa na manne mattt da Babawo ko masaka tsinke babu a tsakanin su hannun shi na cikin rigar ta,yana yin abinda ya saba a cikin rigar ta ta idan ya shiga, motar su Umar ce ta yanko ta shiga layin ta haske gaban gidan, nan da nan samari da 'yan mata suka h[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMMAERH
PAGE 11:
Mamalo ce ta rugo da gudu ta tsaya a gaban su Jameelah, a qoqarin ta na kare Jameelar dan kuwa ta gane motar Umar a cikin jerin gwanon motoci guda uku da suka shiga layin nasu. Cikin hasala Jameelah ta ce wa Mamalo
"Mamalo wai me yasa baki da hankali ne,ke sai muna cikin hirar soyayya mai daɗi ki wani zo....."
"Kin kirani mara hankali idan Yah Umar ya gan ki a haka, ga shi nan harda mutanen gidan su suka zo,"
Da gudu Jameelah ta durqusa can qasan bencin wajen da suke zaune tana gyara zaman bra din ta da kyau a jikin ta,wata iriyar zufa ce ke karyo mata,cikin rawar murya ta ce,
"Mamalo banda kamar ki dik duniyar nan, dan Allah je ki boyo littafi a rigar ki ki zo min dashi nan, ko qur'ani ko hadithi, ko ishmawee, ke ko sirah ce ko iziyya ki dakkon yi gudu,"
Aiko da sauri Mamalo ta nufi gidan su, inda ta tadda mazan zaune a tabarma, matan kuma Ramai ta yi masu shimfid'a da tabarma babba a tsakar gida sun zauna ɗan d'akin nasu ba dai tarkace da duhu ba,Umar kuwa yana cikin Mota yana ta washe baki yana kallon qofar gidan, ya bar motar a bude fitila na haska shi a hankali take d'aga kai tana kallon shi, Babawo sai tambayar ta yake yi waye wancan ɗin da ta rud'e dan ta ji an ce ya zo amma Jameelah taqi amsa shi, saboda kar ya ji ta na son shi ya tada mata da hayaniya, gajiya ta yi da tambayoyin Babawon a qufule ta ce masa,
"'Yan uwan Ramai ne na Abuja suka zo, sun zo zasu dauken a maidani can dan na yi karatun boko, amma ba zan iya tafiya na barka ba, yanzu ka taimaka ka tafi gobe da rana kazo mu tattauna akan wannan matsalar, kaga babban ɗan Yayan Ramai can kar ya gan mu ya fad'awa Baban shi, dukan tsiya za a yi min, ba zan samu damar basu hakuri ba ma kar su tafi da ni, dan Allah kaje sai gobe kazo,"
Kad'a kai kawai yake kamar wani qadangare alamun yana fahimta, daga qarshe ya roqe ta akan ta musu qoqari kar a raba su, bai san yana mugun son ta ba sai yanzu da yaji zancen rabuwa.
Har zai tafi ta riqo wandon shi ta ce masa,
"Ina kudina na yau? Ko kana nufin kaci bulus ne?"
"Ke dai mayyar kudi ce, gashi nan, ana cikin wannan halin tashin hankalin amma ki na zancen kuɗi"
Miqa mata dubu ɗaya yayi ya wuce, tana nan zaune sai zagin Mamalo take yi da bata kai mata komai ba, ta kai minti huɗu duqe, sannan Mamalo ta kawo mata iziyya ta miqa mata tace,
"Wannan na samu ana can ana bada dukiyar auren ki, akwatunan nan da kika ga an shige da su cikin gida to dika naki ne,wato kayan lefen ki idan kin gane hausata, yanzu haka na baro su naji ana saka ranar auren ki, ban gama ji ba dai na fito, dama aure za a maki ko labari babu? Gaskiya baki da mutunci,"
Wani irin daɗi ne ya kama Jameelah har sai da ta saki kukan murna mai karfi sai da tayi mai isar ta sannan ta leqa dan ganin ina Yah Umar ke kallo, ganin yana kallon qofar gidan su ne yasa ta miqe ta gyara hijabin ta,ta ja skirt din ta qasa da kyau, sannan ta fita riqe da littafin ta a hannu kamar wata mutuniyar kirki, cikin wani irin yanayi na wadda ta samu nasara akan cikar burin ta ta ce wa Mamalo,
"Mamalo amsoshin tambayoyin ki sai gobe zan baki su,"
Kanta a qasa ta zo wucewa cikin gidan da sauri Yah Umar ya buɗe mota ya hau kwalla mata kira, cikin sunne kai ta kalli wajen da yake tsaye, cike da nutsuwa ta taka zuwa inda yake, Mamalo na tsaye tana ganin ikon Allah.
Gaisawa suka yi, ya ke tambayar ta daga ina take,
"Yah Umar na ɗan je gidan wata qawata ne can layin qasa da mu kaɗan dan ta sake koya min qarin da aka yi mana, saboda bana son a wuce ni ban iya ba kuma na yi shiru,ga shi ko sallahr isha'i ban samu nayi ba ina ta sauri na dawo gida,"
"Allah sarki Jameelaah tawa, Allah dai ya nuna min ranar da zaki zama mallaki na, lallai zan kwashi ilimin addini a wajen ki ba kaɗan ba, nima taho min da ruwan alwala nayi anan,"
Amsawa tayi ta shige ciki, a qofa ta durqusa har qasa ta gaida baqin da ke zaune a tabarma da Baban ta da 'yan uwan Baban ta da ke kusa da aka kira su dan karb'ar dukiyar auren ta,ganin littafin dake hannun ta ne ya sanya su suka dinga jin daɗin zata kasance surukar su a nan gaba, da gani daga makarantar dare take, ga Mata nan MAZAUNA GIDA ba abinda suke sai iskance-iskance a lungun, amma ita ta maida hankali wajen neman ilimi.
Haka matan ma ta bisu da gaisuwa kafin ta ajiye littafin ta koma dakin su Lantai ta zauna,sukan su matan gidan mamakin sauyawar Jameela suke yi,ta na abu kamar wata wahainiya, yau lafiya qalaou zaka gan ta, gobe kamar 'yar tasha.
Ruwa ta d'iba a buta ta fita waje ta kai ma Umar ta koma cikin gida, alwala tayi ta koma d'aki ta tada sallah a lungun d'akin su, matan da aka ma shimfida a tsakar gida suna kallon yanda take sallah a nutse suna ta sha'awar ta, sun tabbata Jameelah ta fita daban a cikin yaran unguwar tunda sun ga yanda yaran unguwar suke basu da tarbiyya amma ita ta fita daban.
Matan gidan suna ta kallon kaya suna yabawa, wasu kuma na ta kyab'e baki da yada magana, wanda matan basu fahimta ba sam, dan a iya ganin su Jameelah mutuniyar kirki ce,dan haka karin maganar da wasu daga matan suke bai shafe ta ba.
An saka ranar aure wata biyu masu zuwa wanda Jameela ji ta yi dama sati biyu aka saka ba wata biyu ba, me zata yi a wata biyu a wannan gidan nasu? Ai wata biyu yayi yawa.
Lefen Ramai ta roqa su koma da shi dan kuwa su ba su yin bidi'a, Jameelah na d'aki tari ya sarqe ta jin wani karambani a wajen Ramai.
Ramai ruwa ta ɗauka a cup dan ta kai mata kuma su tattauna game da abinda ta ce kar Jameelar ta saki baki ta yi mata wauta a gaban baqi,tana bata ruwan Jameelah ta damqi hannun ta, ta ci gaba da tari, can kuma sai ta yi qasa da murya sosai sannan tace,
"Ramai in kk bari aka koma da kayan nan ko na je gidan sisi ba zaki ga na kawo maki ba,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 30