Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
masa kira, "Malam dan Allah tsaya ya kamannin matar yake, ni ma nan da ka ganni neman mata ta nake yi a ina abun ya faru?" Ɗan tsayawa mutumin yayi ya juyo, sannan yayi baya kaɗan inda malam jameel yake tsaye, bayanin yanayin matar da inda abun ya faru ya yi wa Malam Jameel. Sujjada malam Jameel ya koma gefe yayi yana ta godewa Allah,cikin farin ciki ya cewa mutumin, "Bawan Allah na gode Allah ya biya maka dikkan buqatun ka na alkhairi, yanzu faɗan inda uwar 'ya'yana take mata ta ce, tin rana ta bar gida yau kusan gaba ɗaya neman ta muke" Faɗa masa inda ya kai ta yayi sannan ya ce dan Allah yaje gare ta, shi kam ya gama taimakon nasu yau ko wajen nemawa iyalin shi abinci bai je ba, Da sauri Malam Jameel ya dakko wayar shi ya kira no Umar, ya sanar da shi har sun fara bacci a parlour, Jameelaa kwance a jikin shi da Humairah a qirjin ta ta ci kuka har tayi bacci. Ya so sanar ma da Mum din shi amma ta kafe akan bata son kowa ya san ba a ga mahaifiyar ta ba, har sai nan da kawana uku, ko bayan an ganta bata son kowa ya sani, Umar kuwa ko da wasa bai ji yana son sanar ma da kowa ba tunda gimbiyar ta hana. Ai yana faɗa mata an ga maman ta ta miqe a firgice sauran kadan ta kada Humairah ya riqo ta, da sauri ta saka mayafi suka bar gidan basu zame ko ina ba sai asibiti. Ramai ta farfaɗo ciki fal yunwa tin shayin bunu na safe da tasha bata ci komai ba, ta sawa ranta shegen kwad'ai za ta gidan Jameelaa taci me daɗi. Da gudu Jameelaa ta faɗa a jikin ta ta fashe da kuka. "Ramai na me ya same ki haka? Dan Allah kar ki qara yin nisa ki bar ni inna rasa ki mutuwa zanyi," "Gani ai daina kukan kun zo min da abinci? Yunwa nake ji Jameelah tun safe ban ci komai ba" "Ah ah bamu kawo komai ba, tinda bamu tabbatar ke ce ko bake bace, munzo dai muga wace ce,dik da Baba yace yana kyautata zaton ke ɗin ce ma," Kuka Ramai ta fashe da shi, "Ni kuka ya kama Jameelaah kin ganni nan wata iriyar mahaukaciyar yunwa nake ji qirjina har zafi yake min, ban jima sosai da farkawa ba, ban ma san waya kawo ni nan ba, dan Allah ku taimakan da abinci kar ku rasa ni," Umar da Malam Jameel har rige-rige suke dan fita suje shagon dake cikin asibiti su sama mata abin da zata ci. Koda suka kawo mata fresh milk da biscuit ci ta hau yi kamar wadda ta shekara bata ci ba. Tausayin ta Jameelaa tai ta ji Malam Jameel kuwa ba mai gane halin da yake ciki, dan kuwa kallon Ramai kawai yake. Ramai kuwa sai tinanin qaryar da zata shimfid'a masa take tayi amma ta rasa yau dai qaryar ta ta qare. A nan Malam Jameel ya kwana Jameelaa kuwa suka koma gida da mijin ta hankali ya kwanta, dan tsagewar qashi tayi tinda an mata gyara sai a jira ya warke kuma. Ramai ta kasa haɗa ido da Baban Jameela, shi kuma ya qi yi mata magana akan abinda ta yi yana zaune saman kujera a haka yayi bacci. Washe gari Kulu ce ta kawo abinci ita da Umar, Jameelaa ta tashi da ciwon kai saboda rashin ishasshen bacci da bata samu ba, da kuma kukan da tayi. Ramai an kwashi garar da ake so, nama ta dinga tsama tana ci na kaza da dankalin turawa da akai mata farfesun su, Malam Jameel dik kunya ta kama shi, Umar kuwa tinani yake ko dan ta kwan da yunwa ne yasa take cin abincin haka kamar mayunwaciya. Kulu kuwa tsaf ta fara gano halayen su, dan haka ta san tsantsar kwad'ayi ne kawai ba wani abu ba. Satin Ramai biyu a asibitin aka sallame su,randa suka koma kuwa ta sakan kance Baban jameelaa ya manta da abinda tayi, ta sha gayu ta zauna zaman jiran Baban Jameela. Bashi ya dawo ba sai goman dare, lokacin dik kwalliyar ta goge yana cin abinci ya watsa ruwa ya kwanta a qasa, cikin mamaki da gatsali ta ce masa, "Sabon salo, wanne irin abu ne haka zaka kwanta a qasa, na dad'e bana gida yau na dawo shine zaka wani kwanta a qasa?" Ko lashi kan ki bai ce mata ba balle yace ta ci kan ta, tayi maganar tayi surutun ya mata shiru, daga qarshe ma sai minsharin shi ta jiyo yana tashi. Haka Malam Jameel ya qaurace ma Ramai a d'akin su na tsahon sati ɗaya akan sati biyun baya da ta yi tana jinya kamar yanda islam yace in zaka qaurace ma mace ka qaurace mata a daki, ga ka ga ta amma ka hanata kan ka. Ramai fa ta jiga ta matuqa gaya ko hirar da suka saba yi basu yi, bayan sallama da amsa gaisuwar ta baya ce mata ta fasa balle yace sauke. Bukar daga boko yake wucewa islamiyya, dan haka bai wani kula da sauyawar mahaifin nashi ba, musamman da ya zamana shi sukan zauna suyi hira abun su da shi. Yau dai Ramai tayi alqawarin sauke ma kanta wannan hukunci da ake mata, dan haka Bukar na tafiya makarantar boko ta zube gaban shi ta fashe da kuka, tana neman gafara, bai kula ta ba dan kuwa so yake ya ga ko da gaske ta yi na dama, kukan ta na taba shi, amma haka ya kyale ta ya fita wajen aikin shi. Ramai fa har ramewa tayi saboda tsakanin ta da Allah bata son fushin mijin ta, abinda bai taɓa yi mata ba kenan a duk tsawon zaman su, wannan hukuncin na shi ya yi mata tsauri,tun da jajayen sawaye ma ba a hukunta ta haka ba sai yanzu? Da yamma ta dafa masa abincin da ya fi so ta gyara gidan tsaf kamar ba gidan da ta fara b'atawa da qazanta ba, ta saka kayan ta na qarshen adaka, sannan ta kunna turaren wuta a gidan, tana zaune tana jiran dawowar ɗan dattijon mijin ta ko kwantawa yace tayi yau za ta yi ta ba shi hakuri, ba zata iya jure fushin shi na kusan wata biyu ba dan ta horu ainun. Abinda bata sani ba shine shi kan shi Baban jameela ya gaji da wannan hukuncin da yake yi mata, dama nema yake ta bashi hakuri ya huce taurin kai irin nata ya sa ta dad'e bata bada hakurin ba, wajen masu gasassun kaji yaje ya sai masu 'yar guda daya ya wuce gida da ita. Ko da ya shiga sauyin da ya gani a gidan ya sa ya sake samun nutsuwa, daya yi wanka ya koma parlour sai yaga an jera masa abinci a sabbin mazubin da ta zo da su tin sunan Humairah, daya buɗe yaga abincin da yake so ne, ji yayi ya yafewa Ramai dik abin da ta yi masa, ci ya yi ya qoshi ya kora da ruwa mai sanyi. Ramai ce ta shiga da sallama ta durqusa ta fara neman gafara harda kukan ta, dan abun ya gama isar ta ta matsu su daidaita. "Ramatu ni na yafe maki tin tini, ina hukunta ki akan halayen da kike aikata min ne shekara da shekaru, ban niyyar amsa maki ba, nayi niyyar rama shekarun da kikai kina min abinda kika ga dama nima kafin na amsa ki," Zaro ido ta yi ta fara lissafin shekarun auren su, dan in bata manta ba tinda Jameela ta fara girma suka fara samun matsala da shi, in ya hana abu ta kafe shi za ai tsoro taji ya kama ta, "Habaa Baban su ba za ai haka ba, dan girman Allah ka yafe min, in dai ni ce ba zan sake aikata abinda dik ka hana ba," "To shikenan ya wuce ina maki nasiha da kiji tsoron Allah ni ba wai ina hana ki abu bane dan son rai na, ko dan na b'ata maki rai ba, ina hana ki ne dan Allah ya hana ne, Ramatu waye ya halicce ki?" "Allah," "Me yasa in ya hana abu kike yi? Ko kin manta shi ya halicce ki, kuma zai iya ɗaukan ran ki a dik sanda ya so kin manta da hakan ne? Kin manta cewar dik abinda ki kai akwai littafi ana rubuta maki mai kyau ko mara kyau? Dan Allah yanzu ki zauna na baki minti ashirin ki tina a rayuwar ki kaff me kika aikata da in kin je lahira zai tseratar da ke daga fad'awa wuta, sannan me da me kika aikata na haramun da zai kai ki wuta, in kika bawa kan ki amsa, ki zo ki samen a d'aki bayan kin tuba ga Allah, kuma kiyi qoqarin sauya rayuwar ki daga mummuna zuwa kyakkyawa in ba haka ba qarshen zaman mu ya kusa dan ba zan ci gaba da zama da wadda bata ɗauki sabon Allah a abakin komai ba musamman abinda ya haɗa da shirka," K'walalo ido ta sake yi waje ido ya yi mata jawur ga hawaye faca faca, me yake nufi da shirka? "K'warai shirka nace,ko ji kike ban san kina zuwa wajen malamai yan duba ba? Masu sabon Allah na sani Ramatu, komai da kike aikatawa akan idona yake, idona ya rufe da son ki ne a baya amma yanzu in baki gyara rayuwar ki ba kin qoqarta gyara ta Jameelaa ko zan rasa raina gwanda na rasa dana ci gaba da zama dake, kar ki manta ki zauna sai nan da minti ashirin ki biyo ni ki yi tinani," Ko da ya fita ya shiga d'aki, addu'a ya dinga yi Allah ya sa qarshen rashin tarbiyya ne ya zo a gidan shi, Allah ya amsa kukan shi akan shiryuwar matar shi. Ramai kuwa tinda ta fara tinani daga quruciyar ta zuwa yanzu ta d'au sama da awa biyu a wajen bata sani ba ma, kuka ta dinga yi ta na istighfari, da sauri ta d'aura alwala ta shiga d'aki ko ta kan malam bata bi ba ta sa hijabi ta dinga rabka sallolin da bata san iyakar adadin su ba, tin tana yi a tsaye sai da ta ci gaba dayi a zaune, da taji bacci na neman cin qarfin ta ta yi addu'a da neman yafiyar Allah tare da nemawa kan ta shiriya da iyalin ta dika,sannan ta cire kayan adon da ta sha ta kwanta dan kuwa Malam ya dad'e da yin bacci. *********************** Aunty hauwaa da Sapnah ke waya tana bata labarin makaranta sannan ta sanar da ita sauran wata ɗaya ta yi jarabawar qarshe ta dawo gida kwata-kwata "In kin dawo dan Allah ki zauna a nan gidan, kinga wannan cikin nawa shima har ya yi nauyi, na kusan haihuwa, nan da wata biyu inshaa Allahu zan sauka kin san Safiyya mayyar gida ce ba zata zo min ba, ko yanzu inna ce ta dan zo ta taya ni wasu abubuwan ba zuwa take yi ba, ga Umaimah na laulayin qaramin ciki itama kinga ba mun sa matar mutane aiki ba ko?" "Kar kiji komai ai ni ina son zuwa gidan ku,ina wannan matar wan Umaimahn qazamar nan?" "Ohhh ni Hauwaa har yanzu baki manta ta ba watanni nawa yanzu da zuwa gidan nata? Inajin 'yar su ma za ta yi wata biyu yanzu fa," "Allah sarki Aunty ban san me yasa ba haka kawai sai ina yawan tina Yayan Umaimah, ina matuqar son sake sanya shi a ido na,ban san me yasa ba dik da na kula baya kallon kowacce mace da gashi in ba qazamar matar shi ba," "Sapnah kina da hankali kuwa? Kin kuwa san me kike faɗa? Mijin fa wata kike maganar kina son gani?" "Aunty hawauaa ba laifina bane, ni kaina ina mamakin faruwar hakan," "Kinga mu bar maganar nan sai anjima, ki maida hankali akan karatun ki kar ki saka shiririta kin ji ko? Kuma kiji tsoron Allah ki kare mutuncin ki, kar ki biyewa samarin makaranta kin ji," "Eh naji na gode Aunty Hauwaa sai anjima a shafan babyna, ina gaida Umaimahn da Yayana," "Zasu ji" Hauwa shiru tayi tana tinanin Sapnah, Ohhh Allah ya sa ba qalatar son maza qanwar ta take da shi ba kamar yanda tayi a baya.......... *Hummmm Allah shi kaɗai ya san karatun bebe* [08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 31: Shiru ya yi yana jiran amsar ta tare da kafe ta da idanun shi, cikin wata jarumta ta tattaro dik hankalin ta waje ɗaya sannan ta yi masa fari da ido, wanda ta san yana jan hankalin shi ta ce, "I am sorry Abban Humairah naso na yi maka suprise ne dama, shi yasa ɗazu nace maka ka kaini gidan mu, dama na je na sauya sabon design ne na sarqar da d'ankunnen yanzu irin wanan ake yayi, kuma kasan mu mata yana da kyau mu dinga sauya abubuwan mu, lokaci zuwa lokaci dan birge ababan qaunar mu" Ta qarasa maganar cikin yi masa wani irin wasan da ya mugun tafiya da shi, lumshe ido yayi tare da sauke numfashi, ya jata jikin shi abun nema ya samu, sai da su kayi romancing junan su sosai sannan ta daga shi,cikin wata iriyar murya Umar yace, "Ina zaki je kuma Ki qarasa binda kika fara mana ko ladan naki ya cika?" Ya qarasa maganar shi yana wani lumshe idanu. "Ina zuwa bari na kaiwa Kulu Humairah na dawo" Tana kai Humairah wajen Kulu ta koma sai da wasa yayi wasa sanan Jameelaa tayi shiruuu, Umar ya matsu ya kammala abinda ya fara amma 'yannan tai mursisi taqi bashi dama. "Come on my love, ya kika tsaya," "Ni ba komai kawai tinani nake yi ne ina son na ɗora ma Mamana jari amma bani da kuɗi, bata son zama ba sana'a" "Indai dan wannn ne zan baki 50k ki kai mata zai isa?" "Anya kuwa kasan fa sai ta sake kayan aiki, ta yi awon dik wani abu da zata yi amfani da shi, sannan...." "Please love ki bar maganar can a gefe ki qarasamin abinda kika fara, i promise to take care of all her needs, i will give her money to start her business again, please love," Jameelaa na jin maganar kuɗi zasu shigo kawai ta ci gaba da gigita Umar hankalin ta kwance bata tsoron Allah bata tsoron cewa mace haramun ne ta amshi kuɗi ko wani abu a dai-dai lokacin da mijin ta ke tsaka da biyan buqtar shi a wajen ta, wallahi dik macen da ke hana mijin ta kan ta sai ta yi ciniki dashi ko sai ta nemi wata biyan buqatar ta ta son zuciya, ko sai ya mata alqawarin wani abu wanda ta san zai cutar da shi to ta sani ko a ina take ko a wanne lokaci za ta koma wajen Allah zata gamu da Allah ta yanda batai tsammani ba, domin kuwa shi zunubi ko wanne iri ne ana son bawa ya bar shi kafin lokaci ya qure masa, mata masu hali irin na Jam Jam a nutsu a ji tsoron Allah, maza masu kuɗi kuna sakewa matan ku su ci arziqin ku, matan ku sune abokan rayuwar ku, masu tara haram ma dan matan su suji daɗi da yaran su suke yi balle kai me tara halal? K akashe kud'in ka ta halal ka more rayuwar duniya da lahira, dan in ka kashe ma mace kud'in ka wallahi at the end kai zaka mora dan kai za ai wa qunshi, kitso, siyan kayan kwalliya, siyan turare, yi ma yaran ka siyayya, rage maka cefane mata muna da tausayi, rashin ganewar ku ne maza yasa kuke mana dik abinda kuke so mara kyau wai dan tsare gida , ka sake zuciyar ka ma mace kaga yanda zata maida kai ɗan lele, sai dai in kaga mace na mugun abu to yar uwar Jameelaa ce,kuma Ramai ita ce maman ta,sannan mata masu karb'ar kuɗi a wajen mazan su dan mazan sun sauke buqatar su ta sha'awa a wajen su su sani da su da karuwai na kan titi 'yan gudu ibinin (Good evening) basu da banbanci. Washe gari Jameelaa ta yi ma Ramai waya akan ta aika Bukar ai kuwa kamar wanda take jira, ta katse wayar ta yi wa Baban Jameelaa qarya da cewa, "Malam Jameelaa ke kira na naji Humairah na ta tsala kuka, wai sun rasa me ke damun ta magani anyi har na asibiti, shine nace bari naje na gwada na gida," Ko d'ago kai Malam Jameel bai yi ba ya ci gaba da yankan farcen hannun sa ya ce, "Yaushe kika zama mai bada maganin gargajiya banda labari Ramai? Da alama kin manta da wayar ki ana iya jiyo qarar mai magana dake tsabar qure mata sauti da ku kai , to ba inda zaki je ki aika Bukar kamar yanda tace ko kuma ki fita ba da izini na ba kamar yanda kika saba,dana gama yanke farce na zan fita anjima zan aiko a kawo cefane, na ga kamar kayan miya sun qare" Cikin jin haushin shi ta amsa da, "A had'o da nama dai ah toh," "Inshaa Allahu za a had'o da shi kuma a daina yi wa jika ta qaryar ciwo irin wannan bana so," "Anyi din" Ta furta a hankali, "Na'am magana ki ke?" "Ince me?😏" Murmushi yayi ya ajiye rezar a saman window ya fita, ya kula har yanzu matar tashi na da halin yara, ji yanda take wani kumbura dan ya yi mata faɗa kuma ya hana ta fita. Bata da zaɓin daya wuce na ta aika Bukar ɗin, dan haka ta faɗa d'akin ta dan ta dan jira ya kammala shirin makaranta ta sanar da shi,in an tashi daga makaranta ya je ya ji meye kiran Jameelaan, Tana nan zaune bacci ya kwashe ta sai zabga munshari take yi Bukar kuwa da yaga tana bacci ya wuce makaranta abun shi, kamar wadda aka maka wa duka haka ta miqe ta hau kiran Bukar, jin shiru ya sa ta sanya mayafi ta rufe gidan ta sa kai zata je gidan Jameelaah da kan ta. Surutu take ta yi ita ɗaya a hanya, akan bari tai sauri ta koma kan wancan jarababben ya koma yaga bata gida,fakam fakam fakam take tafiya cikin sauri,har ta yi nisa sosai tana tafiya amma babu abin hawa, kamar daga sama taji an kwashe ta an watsar a qasa a gefen hanya, wasu matasa ne a kan babur sun yo goyon biyu su na ta yi mata magana dan ba horn a babur ɗin nasu ga qarar babur ga ihun da suke mata amma tana can tana tinanin gidan Jameelaa me za a samu ya sa bata ji su ba har sai da suka iso suka rasa yanda za su yi su kauce mata, qarshe dai suka kwasa ta a saman hanya. A kan qafar ta ta hagu Ramai ta cake ai kuwa nan take ta samu tsagewar qashi,tini ta zube a wajen sumammiya, mutane an taru a kan ta wanda suka buge ta kuwa sun gudu abin su. An duba ta tsaf ba a samu waya ko wani abu da zai nuna daga ina take ba, sabuwar unguwa suke balle a ce wani ya san ta, qafa tayi tsami ta fara kumbura mutane sai video ake yi mata, wasu sun fara rubutun qarya akan videon ta da pictures da suka ɗauka suna turawa social net kamar su facebook, instagram, whatsapp da sauran su, kowa da kalar labarin da yake qirqira akan ta, amma ba masu daɗi bane kaff labaran, an rasa mai taimakawa koda farfadowa ne a samu ma tayi. Wani bawan Allah ne ya kutsa ya hau tura mutane baya yana masifa, "Meke damun ku ne mutanen wannan zamani ? Kun manta da taimako Allah Allah kuke ayi wani abun ku fara qirqirar qarya kuna yaɗawa, yanzu da kuka d'au hotuna da video shine abinda tafi buqata? Ba mai qoqarin kaita asibiti, dubi qafar ta yanda ta kumbura, yanzu da kun tura social net wasu masu qaramin tunanin zasu yi ta sharing, wanda in da wani abun alkhairi aka rubuta da zai amfani al'ummar annabi ba za a yi sharing ba, sai labaran batsa, da videos na batsa, da labarai masu saka shubuha da masu fidda mutum a musulunci ma dika kuji tsoron Allah fa tamm" "Kaii kama min ita mu kaita asibiti daga can sai mu bada cigiyar 'yan uwan ta," "Haka kuwa aka yi nan aka sanya ta a motar bawan Allahn nan ya tuqa suka tafi basu tsaya a ko ina ba sai a asibiti, accident and emergency aka shige da ita nan take likita da nurses suka fara bata taimakon gaggawa da sun ce sai an kawo police, mutumin yace indai basu kula da ita ba ta mutu shi kuma zai maka su kotu. Yana ganin sun amshe ta ya koma gefe ya jira a waje yana hoping ta tashi ta fada masa ita wace ce? a ina take?........ *Hummmm wanda bai ji bari ba zai ji hoho ai, Allah gwai inji Kabawa😂* [08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 33 Mum ce zaune a parlour ita da Umaimah wadda ta kai wa iyayen nata ziyara,suke tattauna wa game da halin Jameelaa. "Umaimah ni fa halayen qawar ki gaba ɗaya sun sauya, rabon ta da ta zo  gidanan har na manta,an ce masu Daddyn ku ba lafiya, Umar yazo yafi sau huɗu amma ita bata zo ba, nima nayi ciwo ko aiki bana zuwa amma yarinyar nan bata zo dubani ba, da na ji sauqi naje dan na ga lafiya suke ko fitowa daga d'aki batai ba, sai da na gaji da zama na tafi, sannan ta min waya wai tana toilet ne, can u imagen, tana toilet for over an hour kenan? Habaa ai dai mai motsuwar kai ma ba zai ɗauka ba balle ni, abinda ya fi ban mamaki jiya na je gidan Kulu ta kawon lemon abarba da suke yi su aje a fridge wai yarinyar nan take tambayar kulu dika ta juyo min? Kulu tace ah ah ba dika bane, sai kulu tace ai yana nan cike da jarka babba. Yau ko dika aka juyo min kuma bata sha ba ai a gani na bai kamata ta yi magana akai ba, kuma tana gama maganar ta shige d'aki ta kwanta tana wasa da yarinya, sai da na gaji da zama bata fito ba na yima kulu sallama na wuce, dan bana son na kai lokacin dawowar Umar ya ji me tamin na haddasa masu rikici," "Hummm Mum ko Malam ma haka yace Jameelah fuska biyu gare ta mune bamu gane ta ba har yanzu, tana da munanan halaye wanda sai mai wayo ne zai gane tana dasu,  nima wataran na kan fuskanci wasu abubuwan a tattare da itan na rashin kyautawa, ga qazantar tsiya, ki duba ki ga lokacin da tana ita ɗaya yanda gidan yake, yanzu da kulu tazo ne aka samu sauqi,amma d'akin baccin su ko dawasa yanda kike da tsafta ba zaki iya shiga ki jima ba," "To ubangiji ya ganar da mu abinda bamu da ilimi akai,ya kawo mana mafita mafi alkhairi," "Mum bari na zo na koma,Malam yace daga kasuwa zai wuce gida, basu da makaranta,gashi har yamma tayi ban kula bama" "Ya kamata ki koma kam,Allah ya maku albarka, ya sauke ki lafiya," "Mummmm, ni dai ban da komai, dan Allah ki daina min irin wannan maganar," "Kinji da gulmar ki,muje na raka ki," "Mum sammin dambun nama da dadaddawa, in kina da kuka a ɗebar min, ina son na yi tuwo yau," "Muje kitchen din, sai na d'eba maki" Komai data lissafa sai da Mum ta d'ibar mata, harda wanda ma bata ce ba driver ya maida ta gidan ta. Haroon ne ke kitchen yana tuqa masu tuwon semo ta yi sallama ta shiga, dariya ta fashe dashi ganin yadda dik ya zubar da garin a qasa, gashi ya shafa wani a gemun shi, sannu da aiki ta yi masa ya maqale kafad'a ya buɗe mata hannayen shi, zuwa tayi ta kwanta a jikin shi, ya maida hannayen shi ya rufe, sannan ya yi mata kiss a wuyan ta lumshe ido tayi, tace "Bari na je na rage kayan jiki na sai na zo mu qarasa girkin tare, da baka wahal da kan ka ba ma babe tinda ga abinci nan na aje maka," "Duba ki ga na tashi da shi tsaf, yau ai a gajiye na dawo kuma da yunwa, kuma na ga ya kamata na taya ki ne, tinda kina yin tuwon nan kullum,

Chapter 20 of 30