masu kyau da kuma takalma biyu na roba.
Taji daɗin yin sayayyar sosai, haka ta dawo gida suka baje kayan suna gani kowa ya dauki nashi, suka gyara dakin a tare suka sanya sabon zanin gadon, nan da nan d'akin ya d'au kyalli, Bukar kuwa ya sha faɗa akan shaye-shaye da sace-sace da yake yi, sannan sun masa barazana akan in ya sake zuwa majalisar 'yan shaye-shayen zasu kai shi ga hukumar masu kama masu shan kwaya da miyagun kayan maye, ya kuwa yi matuqar tsorata dan haka ya yi masu alqawarin rage shaye-shaye har Allah ya sa ya daina dika.
(Ba a gyara dan Allah ba ana son a gyara dan a cuci wasu )
Ranar da Baban su Jameela ya dawo yaga an gyara komai ya yi fes har da sabbin kwanuka da zanin gado, sake fitowa yayi ya koma waje dan a zaton shi d'akin wata ya fada, cikin d'aga murya ya ke kiran,
"Ramai ! Ramaiii !!"
"Baba bata kusa ta shiga bayi dannta yi wanka, sannu da zuwa Baba ga abinci nan ka zauna, "
Cikin ladabi Jameela ke yi masa magana, wanda hakan ya d'aurewa Baban nasu kai ainun.
Zama tayi da mafici a hannu yana cin abincin tana yi masa firfita,a kunnen shi ne yaji wasu abubuwa na yi mai yawo tsabar daɗin abincin, sake kallon abincin ya yi da kyau nan take ya gane wannan abincin ba irin nasu bane, yau in bai manta ba ma dari biyar ya bayar kan ya fita, d'aga kai yayi ya kalli Jameela, yace,
"Daga ina aka samu kudin dafa wannan da sauye sauyen da na gani?"...........................
*Toooo readers Allah ya sa mutuniyar ku kar ta gilla qarya dan bata mata kaɗan a baki*
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*Sanarwa !*
*Dan Allah masu nema daga farko ku yi haƙuri ku na duba groups ɗin da muke ciki tare,saboda sake turawa a private gaskiya na ci min tuwo a ƙwarya, wannan dalilin ne ya sa nakan ce ko bai baka sha'awa ba da fari ana tarawa maybe daga baya ya baka sha'awa, a yi min haƙuri adinga tambaya a group dan Allah maybe mutum ya dace da mai shi a tura nasa ko a dinga komawa sama a duba za a samu da yardar Allah....na gode.*
PAGE 8:
"Shin kina da saurayi? Ko nace kin taba yin saurayi?"
Wata iriyar faduwa gaban Jameelah yayi, amma sai ta maida hakan wani irin salo na yaran da ba su san komai ba ɗin nan.
"Yah Umar saurayi kuma? Ni Jameelah da yin saurayi a shekarun nan nawa? Tabdi jam, ai ni da ka ganni ban taɓa yin saurayi ba ban qi ba idan ka ce ki na da masu son ki? Sai in ce maka akwai masu so na da aure da yawa, amma ni ko zance ma ban taɓa fita ba dan kuwa ba a bari na a gida, yaran lungun mu na zuwa dai amma ni kam Baba baya bari ni kaina ma bana so balle nayi,"
Kamar ta ɗauki ruwa mai tsafta ta wanke masa zuciyar shi haka Umar ya ji, sai ya gyad'a kai kawai ba tare da yace mata komai ba, cikin matsuwar taji meye ra'yin shi akan ta har ya mata wannan tambaya ta kalle shi cikin wasa tace,
"Yah Umar kai fa? Ko mun kusa shan biki ne?"
Sosa kai yayi tare da yin murmushi sannan ya nuna ta da yatsa yana kad'awa ya ce,
"Jameelaah, Jameelaah, kin cika tambaya ba a wajen karatu ba, ba wajen surutu ba,"
Dariya tayi zuciyar ta na zillo dan kuwa ta gama gane menene a ran shi game da ita,gyarawa ya umarce ta da tayi dan su wuce ya ajiye ta a gida.
Ba haka ta so ba ta so ya bayyana mata matsayin da ya bata a zuciyar shi,ta na so ta ji ya furta mata kalma mai tsada wato kalmar so,dan kuwa ta san tabbas akwai wani abu a game da ita a ran shi.
Ramai na zaune tana kwashe tuwo a zauren girki,Baban su Jameelah kuma na d'aki yana shafa mai dan bai jima da ya fito daga wanka ba, Bukar kuwa na qofar gida yana ta uban musu da matasan gidan akan ball lokacin sallah ya qarato ko a jikin su, iyayen su na ta hada-hadar haɗa abincin dare, kowa dai yana ta harkokin gaban shi.
Jameelah ta shiga gidan ba sallama ta faɗa d'akin su a gaggauce ta gaida Baban su da ke shiryawa, nan da nan wasu a gidan suka hau gulmar ta, wasu kuwa suna taya iyayen ta murnar gyaruwar ta cikin ɗan qanqanin lokaci,kaya ta sauya dan ta riga tayi wanka a gidan su Umaimah sai ta fito tsakar gida suka hau hira da Ramai,anan ne Ramai ke tambayar ta a kwasa tuwo da ita,Jameelah sai ta yatsina fuska ta ce,
"Habaa Ramai ni nan da ki ka ganni a qoshe nake, haka kawai sai yanzu na wani ci tuwo da dare? Gaskiya ni Ramai bana son irin cimar da ake yi a gidannan, gaba ɗaya gidannan ma ya fita akai na, yanzu na dawo daga gida me rab'a AC iya AC alaji,kamata ya yi yanzu ace koda haya muke yi na samu na koma gidan mu mu kaɗai ba wai na dawo nan gidan ba kamar wata kasuwa,"
Baban ta dake d'aki yana saka riga ne ya saki baki dan jin kalaman ta a ran shi yake fad'in,
'Biri yayi kama da mutum, wato saboda tana zuwa gidan masu hali shine take raina gidan nan, lallai zan d'au mataki babba akan hakan, tinda take su basu taɓa zuwa ba gidan nan ba sai itace ke liqe da su, saboda ɗan banzan kwad'ayi' cikin ɓacin rai ya hau k'wala mata kira kuwa,
"Jameelah ! Jameelaah ! Zo nan,"
Miqewa ta yi tana wata iriyar tafiya ita a dole ranta b'ace yake ta isa wajen shi ta tsaya qiqam,cikin mamakin yarinyar ya ce mata,
"Me naji kina fada? Wato ke gaki kina da gida biyu maganin gobara ko? kije can ki wuni ki zo nan ki kwana sannan mu iyayen ki da muka haife ki ki zage mu, daɗin abun naga anan aka haife ki tin farkon auren mu nan na zauna, ko kina da inda yafi nan ne?"
"Bab...."
"Yi min shiru 'yar wofi kawai, to bari kiji wani albishir da zan yi maki yanzu, Jameela kar na sake ganin ki kin je masu gida in ba su zo nan ba ki tsahirta da zuwa gidan mutane ya isa haka, ke baki san meye kamun kai ba kina mace? Haba Jameelaah a zato na fa kin sauya halin ki ne tsakanin ki da Allah ashe abun ba haka bane,dan Allah ki dinga tsayawa a inda Allah ya aje ki,"
"Baba kana jin fa yanda yanzu na iya karatu sosai a wajen Umaimah nake koya, inna daina zuwa ya zanyi to?"
"In kika roqe ta ta dinga koya maki a makaranta zata dinga yi maki, ko ki roqi malaman ku su koyar da ke ba dole sai ita ba, ko ki jira na dawo saina dora maki,"
Dariya ta kwashe da shi ta na kallon shi a karkace wai shi zai koya mata karatu, da karatun makarantar allon zata yi karatun da zai birge Umar da iyalan shi?
"Habaa Baba, Allah ya kiyaye na zauna a koya min karatun zaure kaga ana ta kiran sallah bari na zuba maka ruwan alwala a tafi a sauke faralin sallah,"
Ficewa ta yi tana ta surutai akan ba zata daina zuwa gidan su Umaimah ba har sai ta samu nasarar samun Umar a hannun ta, sai da yayi alwala sannan ya tafi masjid take sanar da Ramai yanda suka yi, dariya sukai tayi suna gulmar shi.
Da dare ya yi Babawo ya aiko mata da gasasshiyar kaza da kuma Viju guda biyar sai dan lemo da ayaba, ya sha wanka da gayu yana jiran ta a waje, dan yayi tinanin wannan 'yar son abin duniyar da Babar ta in bai sake kuɗi ba ba zai dinga samun hutawa da ita ba.
Aiko ba laifi ranar Babawo ya samu abinda yake nema a wajen Jameelah a ranar,dan kuwa sai da ta ci kazar nan ta gyatse Ramai na ta zagin ta akan ta yi sauri taje kar ya gaji da jira,tana gamawa ta wanke baki da brush ta fesa turaruka sannan ta fice, zaune yake kan bencin su da suka saba zama.
Wani shan qamshi ta isa ta na yi tare da ɗauke kai, nan take tana zama Babawo ya zura hannayen shi bibbiyu a cikin rigar ta tare da sakin ajiyar zuciya mai qarfi sosai itan ma ajiyar zuciya ta sauke,Babawo ya yi kewar ta sosai haka zalika itama.
Sun dad'e suna abun su da suka saba yi idan sun haɗu, kafin daga qarshe su samu nutsuwar rabuwa da junan su, bayan ta sallami Babawo ta kama hanya za ta shiga gida a bakin qofa ta haɗu da Mamalo sanye da kaya masu nuna surar jikin ta, dariya ta fashe da ita dan kuwa Mamalo na nan kan bakar ta ta na so Sadeeq ya samu yana yi mata irin soyayyar zamanin nan, shi ko kan shi a qasa ya kasa kallon ta a haka yake bata labarin gari da abinda garin ke ciki, daga qarshe ya hau roqon ta dan ta sa baki iyayen ta su bashi izini ya turo maganar auren su.
Cike da tsokana Jameela tace,
"Washhhh Allah ! bawa ya ji daɗin shi bari ya je ya miqe ya yi bacci da saleb'a, Babawo ya hadu a rayuwa ...... Ahhh Mamalo kece a nan ?sannun ku ya na gan ku a tsaye haka, Ko ku naku salon a tsaye ne?"
Cike da takaici Mamalo ta buɗe baki zata fara zubawa Jameelah surutu sai Jameelah ta shige ciki tana ta dariya, ta na shiga ciki ta dawo baya ta tsaya tare da leqa kan ta waje,nan taga matan layin nasu na zuba soyayya yanda suka ga dama kowa da irin zaman da suke yi da masoyin ta, da kuma irin soyayyar da ake zubawa a wajen,murmushi ta yi ta ce,
" MAZAUNA GIDA kenan, na bariki na can ana buga harkar arziqi"
Dik wani iskanci da Jameela take aikatawa bata san tayi wankan tsarki ba,iyaka ta wanke gaban ta tayi zaman ta a haka, a cewar ta ba wanda ya taba saduwa da ita, dan haka ba wankan da ya kamata,koda kuwa ta fidda abinda ke wajabta wanka wato (maniyyi) kunji aikin jahilci, sannan ba zata je yin wanka ba a gane abinda ta aikata. Matasa masu soyayyar zamani in baku yin wankan tsarki kuna cikin azaba da gararin rayuwa, ga sabon Allah an aikata sannan ga zama babu tsarki, tayaya zaku yi ibada to ba tsarki?
*******************
"Mum tinda yau alkhamis ko zamu je gidan su Jameela? Bamu taba zuwa ba ina matuqar son naje,"
"kar ki damu zamu je ne kamar kin shiga zuciya ta, inshaa Allahu zamu je amma sai anjima in yayan ki ya dawo sai ya kaimu,"
"Ok Mum Allah ya kaimu,"
"Ameen"
"Mum me zamu kai masu?"
"D'aga ni to na je na ɗan dudduba me zan kai ma ita mahaifiyar ta ta,"
'Yan kayan sawa sabbi, guda biyu, da kayan ciye ciye da shaye shaye(bana maye ba😂) ta haɗa masu, sannan ta d'au turare wanda za ta ba wa mahaifin Jameelah guda biyu.
Da yamma liss Umar ya dawo daga makaranta bayan ya ci abinci ya yi wanka yana hutawa Umaimah ta shiga d'akin shi ta zauna a gefen shi ta ce,
"Yah na zo maka da saqo daga wajen Mum,sai dai naga kamar ka gaji bari na barka ka huta zuwa anjima sai na sanar da kai,dan na kula karatun ku na son hutu, in ka huta zan dawo na baka labari,"
"Ai kuwa dai na gaji kamar an min duka haka nake ji na, amma ina zaku da yamman nan haka na ga kun ci kwalliya?"
"Gidan su Jameela zam....."
Kan ta qarasa ya miqe zaune daga kwancen da yake ya ɗauki Key ɗin motar shi, da kallo Umaimah ta bishi ta na tuhimar sa da idanun ta shin ina gajiyar da ta gani a tattare da shi ɗazu? Lallai ma yayan nan, me yake nufi akan Jameelah ne?
"Muje," Umar yace ya na sosa kan shi da hannun sa na hagu ya na murmushi.
Bata yi masa maganar komai ba ta wuce d'akin ta bayan ta sanar da Mum Yah Umar ɗin zai kai su,hijab ɗin ta ta saka taje ta taya Mum d'iban kayan dake cikin ledar da zasu tafi da shi.
Sun isa layin nasu da yamma liss, 'yan mata an sha kwalliya an fara fitowa qofar gida, yau Jameela bata jin zuwa ko ina dan haka kwance take a d'akin su tana ta zabga tsaki lokaci zuwa lokaci, kyaun ta ace ita yar wani hamshaqin ce, yanda gari yayi kyau ɗin nan ta tafi shopping da Dad ɗin ta ko Mum ko kuma ita ɗaya a mota, amma dan rashin sa'a a rayuwar ta gata kwance gidan yawa ana ta hayaniya.
Juyi tayi tare da sakin sabon tsakin dayafi na da ,da sauri ta miqe zaune dan jin shigowar Ramai tare da ɗaukan mayafin ta da ke rataye a jikin qusar d'akin mayafin yayi maqal maqal da datti.
"Ke tashi ga wata hajiya nan da diyar ta sun zo ina kyautata zaton sune su Umaimah,"
Wata iriyar sufa tayi ta d'akko qur'anin ta ta buɗe ta ajiye a gaban ta ta na motsa baki, sannan ta yane kan ta da hijab kamar yanda ta saba idan ta na karatu a gidan su Umaimah.
Ramai ce tayi ma su Mum iso su kuwa suka shiga cikin d'akin da ke da duhu sai Mum ta yi amfani da wayar hannun ta ta kunna haske dan su dinga ganin ina suke jefa qafar su, ba laifi d'akin a share yake sosai, amma ba wani wajen zama sai ledar d'akin da ta ji jiki d'akin cike yake da tarkacen kayan su ko ta ina a qulle a zani.
Cike da jin kunya Jameelah ta tsaya kallon qur'anin tana murmushi alamar na gan ku amma sai na kai aya zan yi magana.
Shafa kan ta Mum tayi tare da sanya mata albarka, tana jin daɗin kamun kan Jameela, waje suka samu a gefen tabarmar da Jameelah ke shimfid'a ta kwata idan dare ya yi suka zauna, ta na gama muimui da bakin nata ta washe baki ta na fad'in,
"Mum sannun ku da zuwa, Umaimah shine baki faɗan zaku zo ba yau?"
"Ta ina zan sanar dake baki da waya, an baki kuma kin qi Karb'a, yanzu dai gamu mun yi maki zuwan bazata, na karya surutun ki na bana zuwa gidan ku gashi mun zo har da Mum da yah Umar ya na can waje duk na kawo maki su"
"Aka dai kawo ki, ka ji bakin ta a wajen"
Dariya suka yi baki ɗayan su Ramai ta kawo masu kunun aya da zobo, dibulan da kilishi, ashe dik dad'ewar da ta yi aikan data karkasa yara a sayo mata kenan,
Mum taji daɗin karamcin Ramai kwarai ainun.
"Mama ! bari na kai wa Yah Umar shima tare suke yana waje,"
Ramai ke ta zazzare ido jin an kira ta da Mama, taji matuqar daɗi kuwa a ran ta.
Ɗaukan gora ɗaya na zob'o ɗaya na kunun aya tayi ta saka cup ta sa hijab ta tafi kai masa a waje.
Yana zaune cikin motar ya qurawa hanya ido yana jin kamar ya fada gidan ya gan ta ko zai samu sauqin abinda yake ji game da ita a qoqon zuciyar shi ta fito.........
*Wai ni Umarrrr what do u mean? Iyyee? Nace what is ur nufi ne akan Jameelaa?*
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 9:
Bai san sanda wani qayatattacen murmushi ya kub'uce masa ba a kyakkyawar fuskar shi,sai ya sa hannayen shi biyu ya gyara zaman rigar shi a jikin shi, sannan ya bude qofa ya fita waje tare da kafe ta da idanun shi da yake wani lumshewa, yauce rana ta farko da Jameelah ta ji kunya wai dan namiji yana kallon ta.
Buɗe mata mota yayi ta zauna tare da zuba masa kunun ayar ta miqa masa, shanye wa yayi bayan yayi bismillah ya na ci gaba da kallon ta ya miqa mata cup din ta sake cika masa ya shanye, cike da murmushi da jin kunya ta ce,
"Yah Umar ya qare fa"
"Auu ai ban kula ba ma ni"
Dariya suka yi tare, sannan ya kafe ta da ido ya ce,
"Kin san wani abu kuwa Jameelahhh?"
"Sai ka fada Yah Umar"
"Kina da kyau mai ban mamaki Jameelah, the more mutum yana kallon ki, the more yana ganin kyaun ki na qara fitowa,"
Cike da jin nauyin shi ta ce,
"Yah Umar kenan, ai dik wani mai kyau a zamanin nan namu ya bi bayan ka, in ana neman mutum kyakkyawa aka same ka an gama nema an hutadda kowa,"
Umar ya ji daɗin kalaman ta,dan kuwa yau ce rana ta farko da wata mace ta taɓa zama ta yi masa irin wannan kalaman duk da cewa ya na samun mata masu nuna suna son shi sosai, babu wadda ta taɓa yi masa irin kalaman Jameelah, kashe murya ya sake yi sannan ya ce,
"Da gaske kike yi ko wasa?"
"Da gaske nake Yah Umar ba na biyun ka wajen kyau,"
"Kice in muka yi aure yaran mu za su fi kowanne yara kyau tinda mu ɗin kyawawa ne,"
Sakin baki tayi ta na kallon shi qirjin ta na d'agawa da sauri da sauri dan tsabar farin cikin jin kalaman shi, wata kwallar farin ciki ce ta taru mata ta sauke ƙwayar idanun ta qasa ta na wasa da robar kunun ayar da ya qare, matsawa ya ɗan yi kusa da kunnen ta cikin murya mai ɗaukan hankali ya ce,
"Ko ba zaki iya auren namiji kyakkyawa wa ba Jameelaaahhh?"
Da sauri ta fita daga motar tana dariya ta tsaya a jikin motar ta na sauke numfashi, ita a dole wai taji kunya, murmushi Umar yayi ya shafo kwantaccen sajen shi wanda ke haɗe da dogon gemu mai cika da tsaho irin na matasan da ke ji da k'walisa,a hankali take tafiya zuwa cikin gida ta na ji a jikin ta Umar na bin ta da kallo dan kuwa idanun mutane bai taɓa sanya ta jin kamar za ta faɗi ba ta riga ta saba da idanun maza na bin surar jikin ta da kallo, ta tabbata Umar ne kawai ke da wannan damar da ya sanya jikin ta sauyawa,ta na shiga ta tarar da Ramai a tsakar gida da alama leqawa za ta yi kiran ta suka haɗu a hanya,cikin yin qasa da murya Ramai ta ce,
"Daga kai ruwa kin je kin yi zaman ki,ai da kiran ki zan je na yi,"
"Ai gani na dawo, bari su tafi na baki labari,"
Mamalo da Umaimah na ta hira ta qarasa dakin, zama tayi suka sake gaisawa da Mum sannan Mum ta miqa mata abubuwan data kawo masu,daga bisani ta ce zasu tafi,Ramai ce ta shiga ta na neman waje a bakin gado ta zauna ta ce,
"Ku ɗan jira kaɗan yanzu zaki ga baban nasu ya dawo, sai ki yi masa maganar da muka yi dake ɗazu da kan ki, dan zaifi ɗaukan abun da mahimmanci,"
"To shikenan bari mu yi alwala muyi sallah kafin yazo,"
Ko rufe baki mum bata gama yi ba Baba yayi sallama ya shiga gidan, a bakin qofa ya tsaya suka gaisa sannan Ramai ta masa bayanin ko su ɗin su waye, cike da fara'a Baba ya ce,
"Allah sarki, barkan ku da zuwa muna fa godiya sosai yanda ake kula mana da Jameelah Allah ya qara zumunci,"
Anan su Jameelah da Mamalo da Umaimah suka koma d'akin su Mamalo dan su ba wa iyayen nasu waje su tattauna akan abinda ya kawo su Mum,sannan Mum ta ci gaba da magana ta ce,
"Babu komai Malam, dama yanzu nake faɗawa Maman Jameelahn ni da mahaifin su Umaimah muna neman izinin ka akan ka bamu Jameelah ta koma wajen mu dan mu haɗa ta da Umaimah su dinga zuwa makarantar boko, dan kuwa na taɓa tambayar ta ko tana zuwa makarantar boko amma sai ta sanar dani cewar baka da ra'ayin ilimin boko,ilimin zamani na da matuqar amfani ga rayuwar 'ya mace Malam, domin kuwa yana taimakawa al'ummar Annabi Muhammad sosai ta fannoni da dama, misali kuwa shine aikin asibiti,mace na iya zama lauya ta tsaya wajen kare wa mata 'yan uwan ta hakkin su akan fyad'e ko wata cutarwa da ake masu a rayuwar zaman aure ko zamantakewar yau da gobe, in mace na da ilimin boko ko yawan gulmace-gulmace da dambace-dambace da kuma rashin abinyi yana raguwa a unguwanni da cikin al'umma baki ɗaya,dan kuwa za ka samu irin matan da suka yi ilimin boko da na addini da aji,sannan yawan gasa da sa miji yayi abinda bai da ikon yi yana raguwa,dan Allah ka min wannan alfarmar ka bamu ita mu taimaka ma rayuwar ta itama ta taimaki al'ummar annabi kamar yanda nake yi, dan ni din ma'aikaciyar jinya ce,"
Tinda ta fara magana Baba ke nazarin maganganun ta,tabbas tana da hujjoji masu qarfi, amma ba zai iya bada Jameela mai son abin duniya ta tafi gidan masu hali ba, shi in so samu ne da da tsayayye ma aurar da ita zai yi ya huta, amma kuma kunyar matar yake ji baya so ya yi mata musu,amma duk da haka Baba ya rufe ido ya ce,
"To baiwar Allah na ji bayanan ki kuma na gode da soyayyar da kuke yiwa jini na, Allah ya kare maku zuri'a daga tab'ewa, amma gaskiya Jameelah dai bana da ra'ayin sanya ta a boko, ni da ina da tsayayyen miji ma aure zan yi mata, dan haka ki yi hakuri a bawa Alhajin shima haƙuri, a hakan ma zumuncin da ake mana ina jin daɗin shi sosai,"
Dik yanda aka kad'a aka raya Baba yaqi aminta ya bada Jameelah daga qarshe haka Mum ta hakura da suka tashi tafiya sai aka kira Umaimah da ga d'akin su Mamalo suka wuce, suna tafiya Jameelah ta shiga d'akin nasu da murna dan jin hukuncin da Baban nata ya yanke akan komawar ta gidan su Umaimah,nan Ramai ta zauna ta rattab'a mata bayani sala-sala, jin yace bazata koma gidan su Umaimah ba sai kawai ta saka uban kuka, kuka ta yi tayi mai sauti tana sambatun Baba baya son ta huta a rayuwa yafi son ta yi ta zama cikin talauci da quncin rayuwa.
Yah Umar ya matsu ya ji me iyayen Jameelah suka yanke akan wannan lamari da Mum ɗin shi ke bashi labari amma Mum ta qi qarasa maganar ta saboda fad'awa duniyar tunani da ta yi,ta yi nisa cikin nazarin kalaman Baban Jameelah suka isa gida, tabbas mutum ne shi talaka amma ya na riqe da k'imar sa da martabar sa baya son mutuncin shi ya tab'u, lallai gidan su Jameela akwai tarbiyya da sanin ya kamata.
Bayan sun je gida sunyi sallah sunci abinci ne Dad na zaune yana shan tea Mum ta faɗa masa yanda suka yi da mahaifin Jameelah, Yah Umar na d'akin shi yana karatu Umaimah ma na nata d'akin itama. Dad ne ya ajiye mug ɗin da yake hannun sa ya ce,
"Lallai na dad'e ban ga talaka mai kamun kai kamar wannan ba, amma kina ganin in har Umar zai amince ya aure ta ba zamu haɗa su aure ba? Ta haka ne zamu sanya ta makarantar boko dan ta sake samun ilimi sosai da zai amfane ta, a yanayin tarbiyyar dana kula tana da shi musulunci zai alfahari da samun yarinya kamar ta dan kuwa zata yi amfani da ilimin ta wajen taimakon mata har ma da mazan ma,"
"Wannan gaskiya ne Daddyn Umaimah,na ji daɗin maganar ka sosai dan kuwa ni kaina nayi wannan tinanin, tinda yana son ta yi aure ai sai ta zama surukar mu, amma kuma kana ganin Umar zai yarda? karatun shi fa?"
"Babu komai zamu iya mu kai komai na aure, ya zamana dai an san yaron mu ne zai aure ta, in yaso sai mu sanya ta makarantar bokon a can gidan su ta fara zuwa,tare da amincewar mahaifin ta amma, daga sanda Umar ya kammala karatun shi sai a daura masu aure ta tare ko ya kika gani?"
"Gaskiya Honey shawarar ka tayi kyau sosai, Allah ya zab'a mana abinda yafi alkhairi,"
"Ameen"
Da wannan shawarar suka tashi zuwa makwancin su.
**********************
Har ranar asabar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 30