ma yau ɗin bai wani nuna hankalinsa a tashe yake ba, kar a ce don ɗiyarsa ce. Iya yadda Baba ya shiga damuwa kaɗai an biya shi. Yana kuma ji a jikinsa tabbas zai yi nasara. Nasarar da za ta kai shi ga farinciki na har abada. Don haka tun da ya ga Ammeeyn hamdala kawai ya yi.
"Ammeeyna me ya faru? Me ya kawo ki asibiti?" Baba ya faɗa cikin kwantar da murya.
"Yallaɓai ka ga kuwa wanda ya kawo su asibitin bai daɗe da barin asibitin nan ba ma." Wanda yake tsayen dai ya sake yin magana yana kallon Baba. Da mamaki Baba ya mayar da dubansa kan mutumin ya ce
"Ya faɗa maka dalilin kawo su nan ɗin? Ina ɗaya ita yarinyar?" Ya yi tambayar da Farouk ke shirin yin ta.
"Tana ciki, an yi mata allura ta samu bacci."
Wani irin bugawa zuciyar Farouk ta yi jin abin da mutumin ya faɗa. Ta samu bacci? Me ya samu ƙanwar tasa? To ko mota ce ta kaɗe ta? Duka kansa yake yi wa tambayar, cike da fatan ya samu amsoshinsu cikin ƙanƙanin lokaci.
"Me ya same ta? Don Allah ku yi mini bayani kafin zuciyata ta tarwatse. Me ya samu ɗiyata?" Ummee ta yi tambayar duka lokaci ɗaya.
"Ki kwantar da hankalinki Hajiya, babu abin da ya faru. A iya binciken da muka yi kuma babu wani abu da ya faru. Shi kansa wanda ya kawo su asibitin ba bige su ko wani abun ya yi ba. Kawai ya ga suna buƙatar taimako ne shi ya sa ya taimaka musu. Za ku iya jin duk wani ƙarin bayani daga bakin ita Aminar." Ya ƙare maganar yana nuna Ammeey. Sai a lokacin sannan Farouk ya ɗan ji sauƙi, amma duk da haka yana so ya je ya ga ƙanwarsa, ta gefe guda kuma yana so ya ji takaimaimai me ya faru? Mene ne musabbabin zuwansu asibitin?
"Baba ƙawata kar ta mutu, wallahi ina son ta sosai. Ta ce mini tana ji kamar zuciyarta za ta buga. Baba don Allah kar ku ce za ku tafi da ni in bar ta a cikin asibitin nan."
I zuwa lokacin hankalin Abee, Ummee da Farouk ya gama ƙololuwar tashi.
"Ba zan iya jira ba. Ina buƙatar ganin 'yata, ina da buƙatar ganin ta." Ummee ta faɗa cikin tsananin tashin hankalin da kalaman Ammeey suka jefa ta ciki. Da sauri Abee ya riƙo hannunta, kafin ya kai ga cewa komai, mutumin da ya fi kama da ɗansanda ya ce
"Babu lallai likitoci su bar ki shiga. Don yarinyar ba ta daɗe da samun bacci ba. Ina ga kamar sai ya fi kyau ku ji duk wani abu daga bakin Amina." Ya ƙare a wannan karon ma yana kallon Ammeeyn.
"Ammeey ki yi wa mutane bayanin abin da ya faru mana." Ummanta ta faɗa, don ita kanta duk da ta ga 'yar tata amma tana buƙatar jin duk wani da ya faru wanda ya haɗa da dalilin rashin ganin su. Sai da Ammeey ta lumshe idanunta sannan ta soma magana.
"Don Allah Umma ku yi haƙuri, na san na yi laifi. Amma ina so na ga ƙawata na farinciki shi ya sa har na aikata abin da na yi." Daga haka ta shiga bayar da labarin abubuwan da suka faru.
Lokacin da Janan ta ji cewar ba Abee ne ko Yah Farouk zai zo ya ɗauke ta ba, sai haka nan kawai zuciyarta ta shiga bijiro mata da tunane-tunane barkatai. Tun tana yakice hakan, har ta ji ba za ta iya ba. Sosai take kewar Khaleed, take buƙatar ganin sa, take kuma buƙatar ji daga gare shi. Shin ya manta da ita ne da zai bar ta har tsawon sati biyu ba tare da ya neme ta ba? Shin ya daina son ta ne? Gabaɗaya waɗannan tambayoyin su suka saka ta ga a yau ɗaya za ta taka umarnin da Yah Farouk ya yi mata. Za kuma ta sake ɓata masa rai wanda ta tabbatar idan har ya gano hakan ransa zai yi mummunan ɓaci. Don haka lokacin break suna zaune ita da Ammeey ta kalle ta ta ce
"Amina za ki taimaka mini?" Da mamaki Ammeey ta kalle ta sannan ta yi dariya
"Kin ji mu da ke kuma, taimako kuma? Me?" Hannun Ammeeyn Janan ta kamo sannan ta ce
"Ni dai ki yi mini alƙawarin za ki taimaka mini." Shiru Ammeey ta yi tana nazarin ƙawar tata da ta ga yanayinta gabaɗaya ya sauya, ta koma kamar wata babba. Sai ta jinjina kai sannan ta ce
"Na yi."
Tiryan-tiryan Janan ta shiga ba wa Ammeey labarin soyayyarta da Khaleed, har zuwa wannan lokacin da take jin zuciyarta na mata wani irin suya na rashin ji daga Khaleed ɗin. Kallon ta kawai Ammeey ke yi cike da mamaki. Idan wani ne ya ba ta labarin nan a kan ƙawarta, babu ɓata lokaci za ta ƙaryata shi, don ta san ƙawarta ba haka take ba. To amma kuma ita da kanta take faɗa mata, ta tabbatar kuma zahiri ne wannan ba mafarki ba.
"Kar ki ga laifina Amina, wallahi ni ma ban san yadda aka yi hakan ta kasance ba." Janan ta yi saurin faɗar hakan ganin irin kallon da Ammeeyn ke yi mata. Ajiyar zuciya Ammeey ta sauke bayan dogon lokacin da ta ɗauka ba tare da ta ce komai ba.
"To yanzu me kike so a yi?"
"Yawwah." Janan ta faɗa tana gyara zama, sannan ta ɗora da faɗin
"Ina so ki raka ni wajen da muka saba haɗuwa da shi don Allah. Ƙila yana can yana jira na, yana can yana tsammanin zuwana, tun da Yah Farouk ya datse duk wata hanya da zan iya samun damar magana da shi. Ki taimaka kar ki ce mini a'ah." Cike da mamaki Ammeey ta zaro idanunta don gani take wannan ɗin ba abu ne me yiwuwa ba. Ta yaya ma hakan zai faru? Ta bi ta, ta ce ta je ina?
"Aysha so kike yayyena su ɓalla ni?" Ta faɗa idanunta a waje tana kallon Janan ɗin. Kanta Janan ta kifa a kan cinyarta tana ji kamar ta fashe da kuka. Shin me ya sa Yah Farouk ya raba ta da Fa'iza? Fa'iza ita ce ƙawar da za ta iya taimaka mata a ko ma wanne irin yanayi ne. Yanzu me kenan aka yi? Tun da ga ƙawar da take taƙama da ita ta watsa mata ƙasa a ido. Ba ta son zuwa ita ɗaya, don ba ta taɓa zuwa ɗin ba. Tun da kullum ita da Fa'iza suke zuwa. Sai kawai ta miƙe ba tare da ta ce komai ba tana ƙoƙarin wucewa, Ammeey ta yi azamar riƙo hannunta ta ce
"Ina za ki je?"
"Wajen Fa'iza, don na san ita ɗaya ce za ta iya taimaka mini." Ta faɗa tana runtse kyawawan idanunta da suka yi jajir. Da sauri Ammeey ta ce
"Ba Yah Farouk ya raba ki da ita ba?"
"To ya zan yi Amina? Na rasa yadda zan yi. Zuciyata ta kasa sukuni, ina son ganin sa, ina son ji daga gare shi. Ya kike so in yi? In bar abin a zuciyata har daga ƙarshe ta yi bindiga ko kuwa ya zan yi?" Ta ƙare maganar tana fashewa da kuka. Tashi ita ma Ammeeyn ta yi tana rungume Janan ɗin cike da tausayinta. Tana matuƙar son ƙawar tata, sai dai ba ta tunanin za ta iya biye mata har su je wani wajen. To amma kuma sai ta ji cikin ƙanƙanin lokaci zuciyarta tana tunzura ta, tana kuma nusar da ita kamar idan ta yi wa Janan ɗin haka ba ta kyauta ba. Shiru ta yi har zuwa lokacin da Janan ɗin ta gama kukan ta yi shiru. Sai da ta ɗan ja wasu mintina sannan ta ce
"Shi kenan Aysha mu je zan raka ki idan dai har hakan zai faranta miki. Amma yaushe?" Cikin tsananin farinciki Janan ta sake rungume ƙawar tata, sannan ta ce bayan ta sake ta
"Na gode sosai Amina. Na gode kin ji?" Ta ƙare maganar kyakykyawar fuskarta na ƙawatuwa da murmushin da ya matuƙar yi wa fuskarta kyau. Ita ma murmushin Ammeey ta yi sannan ta sake maimaita tambayar da ta yi mata.
"Yaushe to?"
"Kin ga ba yau za a je gaisuwa ba? Idan an dawo daga gaisuwar sai mu je."
"Ta yaya? Bayan an ce za a kai kowa gidansu ne?" Ammeey ta katse ta da faɗin hakan.
"Kin manta ba cikin gida za su kai mu ba? Idan suka ajiye mu sai mu sake haɗuwa a wani wajen mu je, tun da dai a gida ba za su san ƙarfe nawa muka dawo daga gaisuwar ba." Narkar da fuska Ammeey ta yi sannan ta ce
"Har ga Allah ina jin tsoro."
"Wallahi ni ma haka." Ita ma Janan ta faɗa fuskarta kamar za ta yi kuka. Da gaske tana jin tsoro, kai idan ta ce ma ta fi Ammeey tsoro ba ta yi ƙarya ba. Ita kaɗai ta san irin yadda zuciyarta ke bugawa, tun kafin ma ta aikata abin da take shirin aikatawa. To amma ya za ta yi? Zafin da zuciyarta za ta ci gaba da yi sai ya fi na yanzu, idan dai har ba ta san halin da Khaleed ke ciki ba. Ta rasa wannan wanne irin abu ne, da ta san haka ake fama, da ba za ta sake ta ba wa zuciyarta damar fara son wani halitta ba.
"Shi kenan, Allah Ya tsare." Ammeey ta faɗa jiki a matuƙar sanyaye.
Kamar yadda suka tsara hakan ce kuwa ta faru. Kowaccensu a ƙofar gidansu aka sauke ta. Sai suka hau mota suka haɗu a inda suka tsara za su haɗu.
A hankali take ƙarasawa inda suka saba tsayawa, kamar wata zararriya sai ta soma murmushi, tana ci gaba da kallon wajen. Ita dai Ammeey kallon ta kawai take yi cike da mamaki. Ga mamakinta kuma, kawai sai ta ga Janan ɗin ta soma kuka kanta kife a jikin bango ba tare da ta ce komai ba. Ita dai kam lamarin ƙawar tata ya fara ba ta tsoro.
"Aysha." Ta ambata lokacin da ta ƙarasa inda take a tsaye. Sai a lokacin sannan ta ɗago ta zuba mata jajayen idanunta da suka janye saboda kukan da suke ta sha.
"Amina ba ya nan, ba ya nan ɗin ma. Shin ina yake?"
"AyshaJanan." Kamar daga sama ta ji an ambaci sunanta. Da sauri ta ɗaga kai ta kalli mai kiran nata. Yana tsaye daga ɗan nesa kaɗan da su cikin ƙananan kaya. Zuba masa idanu ta yi don so take ta fahimci ko ta san shi. Amma sam ba ma ta taɓa ganin fuskar ba ballantana ta yi tunanin inda ta san shi. To amma ya aka yi ya kira sunanta? Wane ne shi? A ina ya san ta?
"Ke ce?" Shi ne tambayar da ya yi mata yana kallon ta. Tambayar da ta shigar da ita ruɗani, ba ma ita kaɗai ba har da Ammeey da ita ma shi take kalla. Kamar wata doluwa, sai ta shiga jinjina kai kawai ba tare da ta ce komai ba.
Ajiyar zuciya mutumin ya sauke yana ajje zazzafan numfashin da mutum ke iya saukewa idan ya gaji. Ko kuma bayan samun wani abu da ya daɗe yana biɗa. Ƙarasawa ya yi inda suke tsaye. Ya sake kallon Janan sannan ya ce
"Na daɗe ina jiran zuwan ki wannan waje. Na fi kwana nawa kullum sai na zo ko Allah Zai kawo ki amma shiru. Yau dai ga shi Allah Ya yarda kin zo." Cikin rashin fahimta duka su biyun suke kallon shi. Don ko kaɗan ba su fuskanci inda zancen nasa yake son zuwa ba. 'Me yake ƙoƙarin cewa ne?' Janan ta tambayi kanta. Kamar ya san me suke tunani duka su biyun kuwa ya gyara tsayuwarsa.
"Na san ba ki san wane ne ni ba. Na kuma san kina ta mamakin mene ne haɗinki da ni da har na kira cikakken sunanki. To ba tare da na ɓata muku lokaci ba. Ni ɗan aike ne daga wajen Khaleed."
Cike da wani irin farinciki Janan take ci gaba da kallon sa. A hankali tana jin wani irin sanyi na ratsa dukkan wasu gaɓoɓin jikinta. Ita da ma ta sani, ta san masoyin nata na nan yana tunaninta, yana kuma tunanin a wanne hali take ciki kamar yadda ita ma take tunani.
"Kin ji ko Amina? Na faɗa miki. Ni na san tabbas akwai wani abu, shi ya sa zuciyata ta kasa samun sukuni har sai da na zo nan ɗin. Don Allah ka sanar da ni ina Khaleed ɗina yake." Ta ƙare maganar tana kallon mutumin.
"Ai Khaleed ba zai iya ganin ki ba a irin wannan lokacin. Saƙo ya ba ni in kawo miki. Za ki ji komai cikin takardar. Ni da ma wannan shi ne ya kawo ni, ga shi." Ya ƙare maganar yana miƙa mata wata farar takarda. Cike da zumuɗi ta sanya hannunta ta karɓa, daidai lokacin da mutumin ya juya don barin wajen. Babu ɓata lokaci ta soma ƙoƙarin buɗe takardar. Da sauri Ammeey ta riƙo hannunta ta ce
"A'ah Aysha kar mu daɗe. Gwara mu tafi gida idan ya so sai ki karanta a can."
"Ba zan iya ba Amina." Janan ta yi maganar kamar za ta fashe da kuka. Kana ganin ta ka san gabaɗaya a dame take, abin da kuma ya sake sakawa take son buɗe takardar shi ne yadda ta ji bugun zuciyarta ya ƙaru. Ammeey ba ta musa mata ba, ta saki hannun nata, daidai lokacin da ta ida warware takardar. Wani kati ne ya faɗo daga cikin takardar, sai ta tsuguna ta ɗauka ba tare da ta damu da abin da ke cikin katin ba ta zuba idanunta a kan takardar. A nutse ta shiga bin rubutun ɗaya bayan ɗaya tana karantawa.
"Amincin Allah Ya tabbata a gare ki AyshaJanan. Na san za ki yi mamakin rubuto miki wannan zungureriyar wasiƙar da na yi. To ba komai ba ne face ina so in sanar da ke wani abu da tun da daɗewa na kasa sanar da ke, da kuma abin da ya faru yanzu haka babu zato babu tsammani. Na kasance ina son ki sosai, to amma an ce duk abin da Allah Bai yi ba ba zai faru ba. Iyayena sun zaɓa mini wadda suke so na aura har ma an tsayar da ranar aure. Na rasa yadda zan yi na musu bayani a kanki su fahimce ni, shi ya sa ba don ina so ba kawai na amince musu. Amma ki sani, ina son ki, kuma ba don wannan abu ya faru ba, da tabbas ke zan aura. To amma babu yadda na iya, na ɗauka zan iya tausar iyayena su bar maganar aurenmu da cousin ɗita, amma abin ba zai yiwu ba. Saboda ko kaɗan ma ba ni da ƙwarin gwuiwar fuskantar su, tun da tun kafin mu haɗu nake tare da waccan yarinyar. Ni kuma ba zan iya yi musu jayayya ba, shi ya sa na yarda na amince. Ɗaurin aurena ranar Juma'a mai zuwa. Ki yi haƙuri, ki yi haƙuri, Allah Ya ba ki wani mai son naki. Ga katin ɗaurin auren nan." Tabbas Janan ta san ba ta da cikakkiyar lafiyar ido, amma idan dai har ta saka glass tana gani sosai. Sai dai yau ta tabbatar da akwai glass ɗin a idanunta, to amma wani irin dishi-dishi take gani. Rubutun har wani tasowa suke yi, amma ba za ta iya daina karantawa ba, ko ta halin yaya ne za ta samu ta karanta ta kuma tabbatar da ta fahimci abin da take karantawa ɗin. Da ta zo nan, a hankali takardar ta shiga zamewa a hannunta ta faɗi ƙasa. A nutse ta shiga ɗaga idanunta don kallon mutumin da ya ba ta wannan takardar da ke yi wa numfashinta barazanar barin gangar jikinta. Sai dai sama ko ƙasa ba ya nan, babu shi babu alamunsa. Ba ta damu da hakan ba, sai ta sake yin ƙarfin halin ɗora idanunta da hawaye ke neman sake hana ta ganin rubutun da ke jiki a kan katin da ɗazun ya faɗi, ɓalo-ɓalo sunan Khaleed ɗin ke a jikin katin, haɗe da sunan wata macen, wata macen da ba ita ba. Ba ta san lokacin da katin shi ma ya faɗi ya yi nasa wajen ba, saboda tsananin yadda jikinta ke rawa. Tuni idanunta sun sake rufewa ruff. Duk da a buɗe suke, amma idan ta ce tana ganin wani abu ko daidai da ƙwayar zarra ne ta yi ƙarya. Jin ta ta yi tana yawo a cikin iska, zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu da ya mugun wuce na ƙa'ida. Khaleed? Khaleed ɗin? Shi ne abin da kawai take iya tunawa cikin ƙwaƙwalwarta. Ta ma kasa tunanin komai, ta kasa cewa komai, ta kasa aikata komai. Gabaɗaya ta ma rasa a wanne yanayi take, shin a tsaye take ko ko a zaune? Don ita dai kawai ta ji kamar tana yawo a cikin iska ne. Shin ƙwaƙwalwarta ta zauce ne wanda har ya kai ga ta kasa tunanin komai ko mene ne? Wani irin bugawa da zuciyarta ta sake yi, shi ne abin da ya sanya ta saurin sakin wata ƙara ba tare da ta shirya ba. Cikin tsananin tashin hankali Ammeey ta kira sunan Janan da ƙarfi. Sai a lokacin sannan ƙwaƙwalwarta ta dawo daga hutun rabin lokacin da ta tafi. Da gaske Khaleed ne ya rubuto wannan wasiƙar? Da gaske Khaleed ne yake sanar da ita waɗannan kalaman da ke neman tarwatsa ba ma iya zuciyarta ba, har da ranta gabaɗaya?
"Aysha." Ammeey ta faɗa tana kallon Janan ɗin da ta riƙo ta, ganin da ta yi kamar ba ta a cikin hayyacinta, duk da har lokacin idanunta a buɗe suke. Sai dai kafin ta sake cewa komai, Janan ta yi wani irin baya kamar wadda aka ja ta faɗi a wajen sumammiya.
Mhiz Innocent
08124818273
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 13
A gigice Ammeey ta kira sunan Janan da ƙarfi tana zubewa a kan ƙafafunta. Sai dai ko alamar Janan ɗin za ta amsa ba ta gani ba ballantana a kai ga amsawar. Kuka ta fashe da shi tana faɗin
"Na shiga 3 Aysha, don Allah ki tashi kar ki mutu." Ta faɗa tana jijjiga ta. Sai dai ina, kwata-kwata Janan ba ta wajen idan ban da gangar jikinta.
Suna nan a wajen ba tare da Ammeey ta san abin yi ba. Kamar daga sama ta ji ana faɗin
"Me ya faru?" Sai ta ɗaga jajayen idanunta ta sauje a kan mai maganar, ba tare da ta damu da ta san ko waye ba ta shiga faɗin
"Aysha ce za ta mutu, don Allah ka taimaka mini." A nutse ya sauke idanunsa a kan Janan ɗin da ke kwance babu alamar akwai rai a jikinta, cikin ƙanƙanin lokaci ya ji zuciyarsa ta buga. Sai ya juya ya kalli gefe, ya sake juyawa ya kalli ɗayan gefen amma babu kowa. Ita kuma Ammeey babu abin da take sai ci gaba da roƙon sa a kan ya taimaka mata. Babu yadda ya iya haka ya koma motarsa ya buɗe sannan ya dawo, ya saɓi Janan ya sanya ta a mota, Ammeey ta hau motar suka nufi asibiti. Ammeey ce ta roƙe shi a kan kada ya ce zai mayar da ita gida, ko kuma ya ce zai kira iyayenta, saboda suna zuwa za su tafi da ita gida. Ita kuma ba za ta iya barin ƙawarta a nan ta tafi, ba ta san a wanne irin yanayi take ciki ba, gwara ta ci gaba da zama har zuwa lokacin da za ta farfaɗo. Matashin mai suna Adam, bai bar asibitin ba sai can dare bayan da mahaifiyarsa ta kira shi a waya a kan tana son ganin sa. Babu yadda ya iya haka ya tafi ya bar Janan ɗin.
Takardar na hannun Yah Farouk lokacin da Ammeey ta gama sanar da su abin da ya faru. Tass ya karance takardar yana jin yadda zuciyarsa ke wani irin tafasa kamar za ta ƙone. Duk da tun farko bai so alaƙar Khaleed ɗin da Janan ba, amma wannan cin amanar ya taɓa shi. Ya sha jin abubuwan da suke faruwa a yanzu, na yadda samari ke yaudarar 'yan mata daga ƙarshe su ce an haɗa su da cousin ɗinsu. Bai taɓa tunanin hakan zai zo har kan shalelen ƙanwar tasa ba. Ashe shi ya sa tun da ya ga Khaleed ya ji hankalinsa sam bai kwanta da shi ba? Yana sane ya ce masa ya turo da iyayensa don ko kaɗan bai ji ya yarda da shi ba. So yake ya tabbatar da zargin da zuciyarsa ke ɗarsa masa a kan Khaleed ɗin shi ya sa ya ce iyayensa su zo. Sai ga shi ya nuna masa ainahin kalarsa. Ashe ba son AyshaJanan ɗin yake ba, kawai yana yaudarar ta ne? Runtse idanunsa ya yi yana sake jin zafin wannan abu, duk da ta wani ɓangaren sai yake jin wani irin wasai, kamar an ɗauke masa wani dutse da ya danne masa zuciya, wanda ya san hakan na da alaƙa da rashin faɗawa cikin ha'ula'i da ƙanwar tasa ba ta yi ba.
Sosai iyalan gidan Shettima suka jajantawa su Ummee, kafin suka fara ƙoƙarin tafiya. Ammeey ji take kamar ta fasa ihu, ba ta so ta bar ƙawarta ba tare da ta san halin da take ciki ba. Bayan zuwansu asibiti ta farfaɗo ba a bar ta ta gan ta ba, har kuma zuwa wannan lokacin da ta sake samun bacci. Har ga Allah ba ta son komawa gida. To amma ya ta iya? Haka tana ji tana gani ba don ta so ba ta bi su Baba.
Shiru Ummee ta yi tana bin bayan iyalan gidan Shettiman da kallo kamar mai son ganin wani abu. Sai dai a zahiri ba su take kalla ba, zuciyarta ta yi zurfi ne wajen tunanin da ya hana ƙwaƙwalwa da gangar jikinta sukuni. Me yake faruwa ne? Janan ɗin ce ke soyayya? Soyayyar da har ta kai ta ga kwanciya a kan gadon asibiti? Ta yaya aka yi hakan ta faru? Duk tana ina waɗannan abubuwan suka faru? Ashe sakacin nata har ya kai haka? Ashe rashin kulawar tata har ya kai ɗiyarta na soyayya ba tare da ta sani ba? Har ya kai Janan ɗin na zuwa ta haɗu da wani ba tare da ta sani ba? Anya kuwa ta yi wa kanta adalci?
"Ya Hayyu Ya Ƙayyum." Ta faɗa a kan laɓɓanta tana girgiza kanta. Shi dai da ma Abee tun da aka gama bayar da labarin bai ce ko uffan ba, kai bai ma san me zai ce ba. Bai taɓa tunani ba, bai taɓa hasaso cewar irin haka za ta faru ba. Duk irin kulawar da yake ba wa Janan ɗin? Duk irin takatsantsan ɗin da ba ma shi kaɗai ba har da Ummeenta da Yah Farouk suke a kanta amma da abin da ta saka musu kenan? Ashe shi duk kula da itan da yake yi a banza? Duk yadda ya ɗauki Janan ɗin ashe ta wuce haka. Lallai da ma an ce wani lokacin soyayya na taka muhimmiyar rawa wajen lalata tarbiyyar yara. Yanzu me hakan ke nuna masa? Da abin da Janan ɗin za ta saka musu kenan?
Babu wanda ke cewa da ɗan'uwansa ko uffan ne, haka suke zaune kamar kurame. Da ma Farouk ya san idan dai har su Abeen suka san da abin da yake faruwa, to tabbas sai haka ta faru. Abin da ya dinga jiye wa Janan kenan. Bai kuma taɓa tunanin tun yanzu za su kai ga sani ba. Shin ya makomar ƙanwar tasa a yanzu? Yaya batun makarantarta zai kasance? Mene ne zai faru bayan iyayen nata duk sun ƙwallafa mata rai a kan sai ta yi karatu mai zurfi kafin aure? Ita da kanta ta riga ta amince. Ta kuma amshi cewar duk ranar da ta zo musu da zancen wani, to fa ƙarshen karatunta ya zo. To yanzu wanne mataki iyayen nasu za su ɗauka? Bai sani ba, babu kuma wanda zai ba shi wannan amsar, har sai idan su da bakinsu suka buɗe baki suka faɗa masa.
A cikin asibitin Ummee ta kwana, ya yin da Abee da Farouk suka kwana a gida. Sai dai daga sallahr
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 24