idan dai har idanunta sun nuna mata daidai, hasken ɗakin da ta bar shi a kunne kansa yanzun a kashe yake. Cikin rashin sa'a, garin ɗakko glass ɗin, hannunta ya tura shi ya faɗi ƙasa. Sai ta yi saurin miƙewa domin ta ɗauka ta saka, zuciyarta na wani irin bugawa, don ba ta iya ganin komai sai dishi-dishin da take sake rufe idanunta ta buɗe ko da hakan zai sa ta gani sosai. Ba tare da ta ankara ba, ta ji an mayar da ita kan gadon, lokaci guda kuma ana ƙoƙarin raba ta da rigar jikinta. Ai ba ta san lokacin da ta fasa ihu ba, ƙarfin da ba ta san tana da shi ba ta saka tana ƙoƙarin ture mutumin da ta tabbatar namiji ne, lokaci guda kuma tana sake buɗe idanunta da ƙarfin gaske, tamkar hakan da ta yi shi ne zai saka ta ga abin da ke ƙoƙarin faruwa a cikin ɗakin nata.
Mhiz Innocent
08124818273
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 05
Ihun da ya ji ta saka ne ya ba shi damar daina ƙoƙarin raba ta da rigar jikinta da yake yi. Sai ya yi saurin yin amfani da hannunsa wajen toshe bakinta. Iya bakin ƙoƙarinta ta yi wajen janye hannunsa amma ta kasa, saboda ba ƙaramin riƙo ya yi mata ba. Cikin rashin sanin abin yi ta sake runtse idanunta a karo na barkatai lokaci guda tana yin amfani da bakin nata wajen gartsa wa hannunsa wani mummunan cizon da sai da ta tabbatar ta tattaro duk wani ƙarfi da ya rage mata waje guda sannan ta yi masa. Ba tare da ya shirya ba ya saki hannun nata da wani irin sauri, lokaci guda yana yin gefe, kusan rabin nauyinsa da ya ɗora mata duk ya sauke shi a gefen gadon. Sai ya shiga yarfe hannunsa cikin tsananin jin zafin cizon da ya tabbatar ta kusa cire masa fata saboda azabar zafin da yake ji. Gefen da ya koma shi ne abin da ya ba ta damar saurin tashi, har lokacin ta kasa daina kuka. Ta yi saurin kai hannunta ƙasan gadon tana laluben glass ɗinta cike da fatan Allah Ya sa ta gan shi. Cikin ikon Allah kuwa, sai hannunta ya faɗa a kan shi, ta yi azamar ɗauka ta sanya a idanunta, daidai lokacin da mutumin ya yi wuff ya fice daga ɗakin da gudun gaske. Ɗan sake runtse idanunta ta yi kafin ta buɗe shi cikin glass, da wani irin gudun da ba ta san tana da shi ba ta ƙarasa ta kulle ɗakin, ta bar mukullin a jiki. Bayanta na jingine a jikin ƙofar ta fashe da sabon kuka tana zubewa a ƙasa. Wani irin kuka take yi mai tsuma zuciyar mai sauraro, kukan da ke fitowa tun daga can ƙasan zuciyarta. Har kuma lokacin ilahirin jikinta bai bar karkarwa ba. Ta shafe fiye da mintuna goma tana ci gaba da raira shi, har zuwa lokacin ba ta ji ya ishe ta ba, don haka ta kifa kanta a kan guiwarta tana ci gaba da yi.
"Janan." Kamar daga sama ta soma jiyo muryar Yah Farouk daga parlour. Daga farko zuciyarta ce ta buga, don ba ta sani ba ko mutumin ne ya dawo. Sai dai sake kiran sunanta da ya yi shi ne abin da ya tabbatar mata da Yah Farouk ne. Amma duk da haka ba ta yi yunƙurin tashi ballantana ta buɗe ƙofar ba.
Da ƙarfi yake buga ƙofar ɗakin nata, don haka kawai rashin ganin ta a parlourn ya ɗan ɗaga masa hankali, tun da ya san ita ɗaya suka bari a gidan. Kuma yawanci ta fi zama ta jira su a parlourn ne. Miƙewa tsaye ta yi tana kallon ƙofar da Farouk ke ci gaba da bugu cike da fargabar jin shirun da ya yi, don tun da ta ji muryarsa kukan ya ɗauke gabaɗaya.
"Janan.. Ba kya ji na ne? Janan." Shi ne abin da yake ta faɗa zuciyarsa fall tsoro. Kamar wata shashasha haka ta ɗaga ƙafarta kamar mai tsoron taka ƙasar. A nutse ta saka hannu ta buɗe ƙofar. A kanta idanunsa suka fara sauka, don haka bai san lokacin da wata ƙatuwar ajiyar zuciya ta suɓuce masa ba. Kawai sai ta fashe da sabon kuka. Cike da tsoro ya ƙarasa shigowa cikin ɗakin yana faɗin
"Subhanallahi! Janan me ya faru?" Jikinsa ta faɗa tana ci gaba da kukan. A yanzu kam bai hana ta ba, sai ya bar ta ta ci gaba da kukan don ya san tabbas akwai wani abun. Sai dai yana fatan ko ma mene ne ya kasance ba babba ba ne. Sai da ta gaji don kanta sannan ta yi shiru. A nutse ya kama hannunta ya ƙarasa da ita kan gado ta zauna. Cikin kulawa ya ce
"Kwantar da hankalinki, faɗa mini me ya faru?" Kamar wadda ke tunanin har llokacin akwai wani a cikin ɗakin, ta shiga jefa ƙwayar idanunta cikin ɗakin kafin ta dawo da shi kan Farouk ta ce
"Yah Farouk wallahi wani ne ya shigo mini cikin ɗaki yanzu." Zuba mata idanu kawai Farouk ya yi cike da mamakin furucinta. Wani kuma? Ta ya ya? Wane ne shi?
"Wani kuma?" Tambayar ta suɓuce a kan laɓɓansa ba tare da ya shirya ba. Sai ta shiga jijjiga kai sabbin hawaye na ambaliya a kan fuskarta ta ce
"Eh Yah Farouk, wallahi wani ne ya shigo nan. Da gaske nake yi Yah Farouk." Cikin rashin sanin abin yi da kuma tsananin mamakin maganganun da ke fitowa daga bakin Janan ɗin yake kallon ta. Abu ne sabo wanda bai taɓa tsammatar sa ba. To amma hakan ma kamar ba abin kamawa ba ne, saboda babu ta yadda za a yi wani ya iya shigowa gidan. 'Ko kuwa dai mafarki ta yi?' Ya tuhumi kansa. Kamar ta san abin da yake tunani sai ji ya yi ta katse shi da faɗin
"Yah Farouk ba mafarki na yi ba. Da gaske abin nan ya faru. Yah Farouk ba zan sake zama a gida idan duk ba kwa nan ba. Ba zan sake ba Yaya." Ta ƙare tana kifa kanta a kan cinyarsa. Ajiyar zuciya ya sauke, ya san halin ƙanwar tasa na tsoro, wataƙila mafarki ta yi ta tsorata ainun shi ya sa ta ɗauka da gaske ne. Idan ba haka ba ina mutumin yake? Ya aka yi bai ga wata alama ko ɗaya da ke nuna wani ya shigo cikin gidan ba?
"Shi kenan Janan, tashi mu yi magana." Babu musu ta tashi zaune tana kallon sa, abin da ya ɗaure masa kai, har lokacin jikinta karkarwa yake yi.
"Ki yi shiru, ki samu ki kwanta ki yi bacci. Kar ki faɗa wa Ummee ko Abee, idan ba haka ba kin san hankalinsu zai yi matuƙar tashi. Ki bar abin a tsakaninmu, in sha Allah ko ma wane ne ya shigo, zan nemo shi. Zan kuma yi maganin abun."
Ita dai ba ta iya cewa komai ba, sai jinjina kai kawai da ta yi. Ba ta yarda ya bar ɗakin ba har sai da ta yi sallar isha'i sannan ta kwanta ta runtse idanunta tana janyo duk addu'ar da ta zo bakinta. Bai bar ɗakin ba sai da ya tabbatar da bacci ya ɗauke ta. Ya miƙe ya kashe mata ƙwan ɗakin sannan ya fice. Kai tsaye a parlour ya ya da zango, yana tunanin maganganun ƙanwar tasa. Ko ma dai mene ne ya fi tunanin mafarki ta yi, don sau da dama ta saba yin mafarki idan ta tashi kuma ta yi ta kukan abin da ya faru. Ya tabbatar yau ɗin ma haka ne ya faru. Amma ko ma dai mene ne zai yi ƙoƙari wajen ganin ba a sake barin ta ita ɗaya a cikin gida a irin wannan lokacin ba.
A karo na barkatai ya sake gwada kiran layin Muhammad ɗin, kamar ɗazun, yanzu ma faɗa masa ake ba za ta shiga ba. Zazzafar iska ya fesar daga cikin bakinsa yana jin wani tashin hankali na soma ziyartar sa. Ko kaɗan ba ya ƙaunar kiran layin ɗan nasa ya ji shi a kashe ko kuma ya ƙi shiga. Ƙarfe 12 ne na daren ranar, har kuma lokacin bai shigo gida ba. Da ya san irin faɗuwar gaban da yake ji a halin yanzu da ya kira shi ya sanar da shi ba zai dawo da wuri ba. A irin wannan lokacin da ɗan nasa ba ya gida, cikin dare, ba kuma tare da ya sanar da shi dalilin rashin dawowar tasa gida ba, ya fi komai ɗaga masa hankali. Yana tsoron kar wani abu ya same shi, kar wasu su ja shi su sake gurɓata masa tarbiyya. Kar ya koma gidan jiyan da ya yi masa alƙawarin in Allah Ya yarda ba zai sake komawa ba. Yana tsoron tasirin abokai, duk da ya san ɗan nasa abokinshi guda ɗaya ne ƙwallin ƙwal, wanda duk gidan sun san shi. Sai kuma ɗan'uwansa Al-ameen. Duk wani wanda yake kulawa to sai dai idan aiki ne ya haɗa shi da shi.
"A'ah Yaya.." Kamar daga sama ya jiyo muryar Daddyn Ammeey. Sai ya gyara zamansa yana faɗin
"A'ah Aminu."
"Na'am Yaya. Ai tun ɗazu nake hango ka a wajen nan. Lafiya dai ko?" Murmushi Baba ya ɗan yi bayan ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ce
"Babu wani abun damuwa, ka je ka kwanta. Ina jiran Muhammad ne." Girgiza kai Daddy ya yi, da ma ya san zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi.
"Ai ka ji. Yaya kamar ma ba ka da lafiya fa." Ya yi maganar yana kallon sa. Girgiza kai Baba ya yi ya ce
"Babu abin da ke damu na. Daga zarar na ga ɗana kuma zan sake samun lafiya." Ajiyar zuciya Daddy ya sauke, shi dai wannan ƙauna wannan ƙauna har mamaki take ba shi. Kamar son da Baba ke yi wa Muhammad ɗin ya yi yawa.
"Yaya kar fa ka ja wa kanka ciwon zuciya a kan wannan yaron. Ka daina damun kanka, ƙila yana can wani ɗan siyasar ya saka su aiki kamar yadda suka saba. Ba ka sani ba ma ƙila kana nan kana damun kanka, ya yin da yake can riƙe da adda yana tsoratar da al'ummar mu...."
"Aminu." Baba ya faɗa cikin ɗaga murya, wanda hakan ya tilasta wa Daddy katse maganar da ya soma. Wai shin me yake damun shi ne shi kam? Me ya sa sam ba ya yi wa bakinsa linzami? Anya idan har bai din ga yi wa kansa faɗa ba akwai lokacin da Baba zai yarda ya amince da auren Ammeey da Muhammad ɗin? Duk shirin da yake shiryawa yana neman tashi a banza? Shi fa nan jira yake a sake kwana biyu ya bijiro da maganar aurensu, a matsayin ya ga Muhammad ɗin ya daina harkar shashanci, saboda haka a amince a aura masa Ammeey. Don ya san idan dai har hakan ta kasance, to tabbas nan gaba shi zai yi murna har da taka rawa. Sai dai kuma ga shi yana neman ruguza komai da wannan bakin nasa da ba ya gani ya yi shiru.
"Kar ka sake faɗar mummunar magana a kan Muhammad. Muhammad ɗana ne, duk kuma yadda Allah Ya so ya jarrabe ni a kansa, zan saka hannu bibbiyu ne in karɓa. Wannan abu kuma da kake faɗa, tuni ya watsar da shi. In dai ka san ka zo wajen nan ne don ka faɗi aibun ɗana, don Allah ka tashi da ma ban nemi wani ya taya ni jiran dawowar shi ba. Idan dai har ba cewa za ka yi Allah Ya shirye shi ba don Allah ka tashi ka je."
"Ka yi haƙuri Yaya, ka yi haƙuri don Allah. Wallahi ina jin babu daɗi ne idan na gan ka cikin damuwar da Muhammad ne ya saka ka. Ka yi haƙuri."
"Muhammad bai saka ni cikin damuwa ba. Ina kuma addu'ar ya kasance har ƙarshen rayuwata kar hakan ta faru."
"In sha Allah hakan ba zai faru ba." Daddy ya faɗa don so yake ya wanke kansa gabaɗaya. Shiru ne ya wanzu na tsawon mintuna goma babu wanda ya sake cewa ko uffan. Daddy cike bakinsa yake da maganganu a kan harkar kasuwancinsu. Sai dai kuma ya ga alama ran Baban ya ɓaci. Don haka sum-sum-sum ya miƙe yana faɗin
"Allah Ya ba mu alkairi."
"Ameen." Baba ya faɗa, ya yin da Daddy ya wuce sashensa.
Bayan wajen mintina goma, motarsa ta danno kai cikin gidan. Bai lura da Baba da ke zaune ba, amma cikin zuciyarsa fata yake Allah Ya sa bacci ya ɗauke Baban, duk da ya san abu ne mai wuya. Har ya gama parking na motarsa bai kula da shi ba, har ya soma jin farinciki ya mamaye zuciyarsa. Sai dai yana saka hannunsa zai buɗe ƙofar idanunsa suka sauka a kan Baba da ke zaune yana ɗan karkaɗa ƙafarsa idanunsa a kan MuhammadAali ɗin. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ji jikinsa ya yi matuƙar sanyi. Ya runtse idanunsa yana jin matsanancin haushin kansa na kama shi. Shin sai yaushe ne zai daina ɓata wa Baba rai? Shin sai yaushe ne zai daina barin Baba cikin damuwa da fargaba? Kamar wanda jikinsa babu laka haka ya yi ƙoƙarin sakkowa daga cikin motar. Sanye cikin riga da wando 'yan ubansu, waɗanda suka matuƙar amsar jikinsa. Sai da ya yi iya ƙoƙarinsa wajen sake saita kansa don kar Baban ya gane ko ya sha wani abu, kafin a hankali ya soma takawa zuwa inda Baban yake lokaci guda yana kai hannunsa yana ɗan shafa kwantacciyar sumar kansa. Kafin ya kai ga ƙarasawa Baba ya tashi don koma wa sashensa, tun da da ma abin da yake jira kenan. Dawowarsa yake jira, ga shi kuma ya dawo.
"Baba." Ya faɗa a raunace cike da fatan ba fushi Baban ya yi da shi ba.
"Ka je ka kwanta." Shi ne abin da Baba ya iya faɗa yana ƙoƙarin soma tafiya. Sai ya yi azamar sake takawa gaba ya zube a kan ƙafafunsa yana ɗan runtse idanunsa da suka ɗan janye ya ce
"Baba don Allah ka yi haƙuri kar ka yi fushi da ni." Juyowa Baba ya yi saboda yadda ya ji muryar ɗan nasa.
"Ni na ce maka na yi fushi da kai? Kai kanka ka san ba na iya fushi da kai. Abin da kake yi ne dai ba na so. Yanzu wanne ɗa ne zai kai har ƙarfe 1 a waje, bayan ya san mahaifinsa na cikin tunanin halin da yake ciki tun da wayarsa ba ta shiga?" Runtse lumsassun idanunsa ya sake yi a karo na barkatai ya ce
"Ka yi haƙuri Baba, ka yi haƙuri." Shi ne abin da ya faɗa, wanda hakan ya saka Baba kafe shi da idanunsa yana nazarinsa.
"Ka bi wasu 'yan siyasar ne ko kuwa me ya sa ka yi dare a waje?" Ya riga ya saba, ko me ya yi ba ya taɓa iya ɓoye wa Baban, don haka ya ɗan fesar da iska daga bakinsa ya buɗe bakinsa da ƙyar ya ce
"Na daɗe da yi maka alƙawarin har abada ba zan sake yi wa wani ɗan siyasa aiki ba. Faaza ɓacin rai nake ji ɗazun shi ne na..."
Hannu Baba ya ɗaga masa tun kafin ya kai ƙarshen maganar tasa, don ya san abin da yake ƙoƙarin faɗa, hakan ya tilasta wa MuhammadAali yin shiru.
"Ka yi haƙuri don Allah Baba." Baba bai ce da shi komai ba ya wuce sashensa. Bin sa ya yi da kallo a ransa yana ji lallai yau ɗin da gaske Baba ya yi fushi. Sai dai abu ɗaya ya sani, ba da shi ya yi fushin ba. Don wannan ya san ba abu ne mai yiwuwa ba. Ya kuma san ko gobe ya koma don ya sake ba shi haƙuri zai amsa masa. To amma ya rasa gane kansa, ya rasa gane abin da ke damun shi. Duk ƙaunar da yake yi wa Baba, da kuma ƙaunar duk wani abu da yake so, da kuma ƙin duk wani abu da ba ya so ya kasa daina shan kan maye. Akwai abubuwa da dama cikin rayuwarsa, wanda in dai har ya tuna su sai ya bugu yake jin ya koma daidai. Akwai wasu lokutan da kalaman mutane ne kawai za su janyo ya sha wani abun. Ba don komai ba kuma, sai don wasu al'amura da yake tuna wa cikin ƙwaƙwalwarsa. Wani lokacin kuma yana sha ne kawai don sha'awa. Sai dai ta ɓangare guda duk lokacin da ya tuna Baba ba ya so sai ya ji wata nadama ta lulluɓe shi. Ya ji duk ya tsani kansa. Shin shi ɗin wanne irin ɗa ne da ba zai zame wa uba kamar Baba ɗa nagari ba? A kaf rayuwarsa a wannan wajen ne kawai ya taɓa saɓa wa Baba. A da ya kasance karen farautar 'yan siyasa, waɗanda ke amfani da su wajen cimma buƙatarsu. Tun da Baba ya nuna masa ba ya so, ba ya kuma buƙatar ya sake yi ya watsar da harkar gabaɗaya. Jiki a matuƙar sanyaye ya miƙe don wucewa ɗakinsu har lokacin idanunsa a ɗan janye saboda abin da ya sha.
Haka nan kawai ya ji hankalinsa ya kasa kwanciya tun lokacin da aka sanar da shi ana neman sa a makarantarsu Janan ɗin. Driving yake yi, amma ji yake kamar ya tashi sama don ya isa makarantar. A office ɗin shugaban makarantar aka karɓe shi. Cikin mutunci suka gaisa, shi dai amsawa kawai yake yi amma burinsa ya ji dalilin kiran.
"Wato wani al'amari ne ya faru, sai muka ga dacewar kiran wani daga gida kafin mu yanke hukunci." Jinjina kai kawai Farouk ya yi alamar yana ji, don ya ma kasa furta komai. Yana tsoro Allah Ya sa ba wani abu ne ya faru ba.
"An samu Aysha, da laifin fita daga makaranta a lokacin karatu, ba kuma ta dawo ba gabaɗaya har aka tashii." Kamar wani soko haka yake kallon matar, me take faɗa ne? Me take ƙoƙarin faɗa masa? 'Aysha ta fita daga makaranta?' Ya raya hakan cikin zuciyarsa. Anya kuwa wannan zancen kamawa ne? Janan ɗin? Ko kuwa dai matar nan ta yi kuskure ne?
Mhiz Innocent
08124818273
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 06
Driving kawai yake yi amma gabaɗaya hankalinsa yana wajen Janan. Shin da gaske fita ta yi daga makaranta bayan lokacin karatu ne? Me ya fitar da ita? Ina ta je? Tambayoyin da ke ta yi masa lugude kenan a ƙwaƙwalwa, sai dai babu mai ba shi amsa. Don haka duk wani burinsa sai ya tafi wajen son ganin Janan ɗin ya tuhume ta. Ya san yanzu haka idan ya koma gida tana islamiyya, kasancewar bayan azahar ne. Makarantar kuma da ma ba su kira shi ba sai bayan an tashi. Ba don haka ba ko islamiyyar ba zai bari ta je ba, har sai ta sanar da shi inda ta je.
MuhammadAali ke driving ya yin da Baba ke zaune a gefensa. Lokaci zuwa lokaci Muhammad ɗin kan ɗan kallon mahaifin nasa, sai kuma ya ci gaba da driving ɗin.
"Baba." Ya faɗa ba tare da ya kalle shi ba yana kallon titi.
"Muhammad." In ji Baba yana ci gaba da danna wayarsa. Jim kaɗan Muhammad ya yi kafin ya ɗan lumshe kyawawan idanunsa da yanzun suka yi wasai, kyawunsu ya sake fitowa sannan ya ce
"Wai fushi kake yi da ni?" Numfashi Baba ya sauke kana ya ce
"To ci gaba da tambaya ta, ko da rabon tambayar za ta saka na yi fushi da kai. Idan kuma ba ka son hakan, ci gaba da driving ɗin da kake yi, ta gefe ɗaya kuma ka canja halayenka." Sarai ya fahimci maganganun Baban, don haka ya yi ɗan murmushin gefen baki kafin ya ce
"Na gode Faaza." Shi ma murmushin Baba ya yi yana girgiza kai. Shi kansa har yanzu yana mamakin irin ɗimbin ƙaunar da yake yi wa ɗan nasa, wadda take sa wa ya kasa fushi da shi. Sai dai idan dai har ya yi abin da ba daidai ba, duk yadda ya yi ƙoƙarin ɗauke kai ya nuna wa Muhammad ɗin bai yi fushi ba, hakan ba ya gamsar da shi, har sai ya tabbatar da ya wanke kansa a wajen mahaifin nasa.
A daidai lokacin da Muhammad ɗin ke shirin sauka daga kan titin da yake kai ya hau wani, daidai lokacin da wata ƙatuwar mota da ke a bayansa ta dakata. Mutane uku ne a cikin motar, sai dai kusan dukkansu ba a iya ganin fuskarsu. Domin kuwa biyunsu fuskarsu ɗauke take da face mask. Ya yin da ɗayan kansa ke a kife a gefen kujerar da yake kai.
"Oga yana shirin ɓace mana fa." Ɗaya daga cikin wanda ke sake da face mask ya faɗa yana kallon wanda fuskarsa ke a duƙe. Sai a lokacin sannan a hankali ya shiga ɗaga fuskarsa, kai tsaye a kan titin ya dire idanunsa. Kamar ba magana zai yi ba, sai kuma ya buɗe bakinsa ya ce
"Bar shi." Shi ne abin da kawai ya furta yana murmushi, kafin bai jira amsar kowa ba ya yi danne-danne a wayarsa, bayan wasu sakanni ya kara a kunnensa, wajen minti 1 yana saurarar abin da ake faɗa masa, kafin ya ce
"Yallaɓai muna kan bibiyar sa. Ba zai taɓa suɓuce mana ba." Shi ne abin da ya faɗa don so yake ya ba wa wanda suke magana a cikin waya tabbaci. Bayan wajen minti 1 ya sauke wayar. Sai ya sauke wani numfashi mai matuƙar huci saboda tsananin ɓacin ran da yake ji. 'Me ya sa?' Ya tambayi kansa, jajayen idanunsa na sake rinewa, lokaci guda bugun zuciyarsa na ƙaruwa.
A ɓangaren Baba kuwa, a ƙaton katafaren shagonsu da ke reshen da suka nufa suka sauka. Tun da suka fito mutane suka fara kwasar gaisuwa a wajen uban gidan fita kunyar nasu, wato Alhaji Abbas Shettima, mai son cigaban na kusa da shi. Shalelen ɗansa na gefensa, duk inda ya gifta yana biye da shi. Har zuwa lokacin da suka ƙarasa office ɗinsa da sai ka ɗauka cikin wani ƙaton company yake, saboda tsananin yadda ya tsaru. Kuma ya kasance cikin kowanne babban shagonsa yana da irinsa, bambancin ɗaya ne, wannan na musamman ne, duk wasu abubuwa masu amfani a cikinsa yake yi. Yanzun ma wasu muhimman abubuwa ne suka kawo shi, don ba kasafai ya fiya zuwa ba, saboda akwai amintattun da suke yin duk wasu abubuwa da idan yana wajen zai iya yin su. Bai kuma saka su a kai ba sai da ya tabbatar da ingancinsu. Waje ya nema ya zauna kafin Muhammad ya zauna shi ma.
"In dai har za ka ci gaba da biyo ni kasuwa, ina dab da hana ka saka irin waɗannan kayan." Baba ya faɗa yana nuna kayan jikin Muhammad." Hannu ya ɗan kai ya shafi sumar kansa kana ya ce
"Faaza yanzu mene ne aibun kayan nan?"
"Kai da nake so ka gaje ni? Dole ka koma saka manyan kaya." Baba ya faɗa yana janyo wasu takardu waɗanda Muhammad ɗin ne ya miƙo masa su. Sai ya yi murmushi kawai, irin murmushin nan nasa da ya saba na gefen baki. Tabbas zai so a ce ya gaji Baban a rayuwarsa, to amma ta ya ya ne zai iya rayuwa kullum da manyan kaya? Yana sakawa amma ba kasafai ba, su ma da tursasawar Baba, da kuma fahimta da ya yi Baban na matuƙar jin daɗi idan ya ga ya saka manyan kaya, shi ne dalilin da ya sa yake sakawa. Sun shafe fiye da awa biyar a office ɗin, har zuwa lokacin Baba aiki yake yi. Muhammad ɗin na taya shi da abubuwan da ba a rasa ba.
A nutse Muhammad ke nazarin Baban, lokacin da hannunsa ke ɗauke da pen yana ɗan karkaɗawa a kan haɓarsa. Kafin ya kai ga cewa komai Daddy ya shigo cikin office ɗin. Kai tsaye ya shigo don yana da hurumin yin hakan. Kujera ya ja ya zauna yana nazarin yayan nasa.
"Yaya kafiya kuwa?" Ya tambaya cike da mamaki. Iska Baba ya fesar daga bakinsa kafin ya gyara zamansa lokaci guda yana ajiye takardun hannunsa.
"Akwai matsala ne?" Daddy ya sake tambaya a karo na biyu. Jinjina kai Baba ya yi kafin ya ce
"Ina tunanin hakan." Kallon sa kawai Muhammad yake yi yana nazarin Baban cike da mamaki, don idan dai har bai manta ba, wannan ne karo
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 24