Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tare da ya jira amsarta ba ya koma cikin parlourn. Kai tsaye ɗaukar abin da ya shigo da shi ya yi ya fice daga sashen gabaɗaya. Sai da ya fita sannan ta sauke wata ƙatuwar ajiyar zuciya tana komawa ta yi zaman daɓaro jikin ƙofar ɗakin. Ta kai wajen minti ɗaya, kafin numfashinta ya koma daidai. Sai dai cikin ƙanƙanin lokaci sai ta ji tana tuhumar kanta a kan abin da take aikatawa. Anya kuwa? Anya kuwa tana yi wa kanta adalci? Anya kuwa wannan ita ce hanyar da ya kamata ta bi wajen saka wa iyayen nata da ma ɗan'uwanta irin ɗimbin kulawar da suka ba wa rayuwarta? Me ya sa ne zuciyarta take da rauni? Eh, ta fahimci hakan ne, ta yadda cikin ƙanƙanin lokaci mutum ke nasarar sace mata zuciya. Ta ga hakan a kan Khaleed, sai ga shi Adam ya zo ya shafe shi daga rayuwarta. Adam ɗin da ba za ta iya cewa ga yadda fuskarsa take ba. Adam ɗin da kalamansa na ɗaya daga cikin abin da ya soma tafiya da ita. Shin me ya kamata ta yi? Ta ci gaba da biye wa Adam, ko kuma ta yi ƙoƙarin manta shi? Wanda hakan zai saka iyayenta kar su yi fushi da ita? Ita ma kanta ta huta da wannan ɓoye-ɓoyen? Sai ta runtse idanunta da wani irin ƙarfi tana jin yadda wani sabon bugun zuciya ya soma ziyartar ta. 'Shin wai ita ɗin wacce irin 'ya ce?' Ta tambayi kanta lokaci guda hawaye na ƙwace mata. Haɗin kai ta ba shi, ta shiga rera kukan kamar wadda aka yi wa mutuwa. Sai dai cike da takatsantsan take yi don kar sautin ya fito ballantana har ta janyo hankalin mutanen gidan. Shi ke driving ɗin cikin haɗaɗɗiyar motarsa. A ƙofar ƙaton gidan nasu ya tsaya yana yin horn. Babu jimawa aka fara buɗe masa ƙofar. Daidai lokacin da idanunsa suka sauka a kan wata adaidaita da ta tsaya a ƙofar gidan nasu. Cikin sakannin da ba su wuce goma ba, waɗanda ke cikinta suka sauko. Tsohuwa ce wadda aƙalla ta ba wa 70 baya, sanye cikin atamfa riga da zani, da zanin atamfar da ta yafa shi, kanta ɗaure da irin ɗankwalin nan na da. Siririya ce, tana ɗaya daga cikin irin tsoffin nan masu kyawun jiki. Wata matashiya ce tsaye a gefenta, ita ma sanye cikin riga da zanin, sai dai saɓanin tsohuwar, ita tana sanye ne cikin mayafin nan na da, wanda aka fi sani da fashmina. "Hamida sauko da kayan." Tsohuwar ta faɗa tana kallon budurwar. Kallon tsohuwar wadda aka kira da Hamidan ta yi kafin ta ce "Kin ji mu da Innar nan, tun daga gida fa ni na ɗakko, yanzu ma kuma ki ce ni zan ɗauka." "To ko ba za ki ɗauka ba ne?" Ta faɗa tana jefa mata harara. Tunkuɗo bakinta gaba ta yi kamar zai faɗo ƙasa tana magana ƙasa-ƙasa. Ba don ta so ba, haka ta saka hannu ta sauko da kayan da ke ajiye bayan adaidaitar. Sai da ta fito da duka, sannan suka soma takawa. Daidai lokacin da mai adaidaitar ya sakko daga motar yana faɗin "Hajiya ba fa ki ba ni kuɗina ba." Wani banzan kallo Innar ta juya ta watsa masa sannan ta ce "Ina ganin kamar ba ka ga gidan da na zo ba, ka ga ya yi kama da gidan rashin arziƙi? Jira ni yanzu zan saka ɗana ya aiko a biya ka kuɗinka har ma da ƙari saboda farincikin ka ajiye masa ni lafiya. Kai ne talaka." Ta ƙare maganar tana yin gaba. Bin ta daga ita har kayan jikinta ya yi da kallo yana jan tsaki ƙasa-ƙasa. Wato wasu tsoffin su suke jawowa yara su yi musu rashin kunya. Ban da haka, daga yin maganar kuɗinsa mene ne abin faɗa masa magana kuma? "Inna!!!!" Ya ambata a kan laɓɓansa yana jin yadda zuciyarsa ta ɗan doka lokaci guda, sai ya runtse idanunsa yana jin yadda lokaci ɗaya, wani irin tarin rashin sukuni da rashin jin daɗi ya ziyarce shi. "Yau kuma da wanne ta zo?" Ya tambayi kansa, duk da ya san babu wanda zai ba shi amsa. Mhiz Innocent 08124818273 *♡☆BIYU BABU☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) YOTA Writers Ass.. Book 1 Pg 21 "A'ah, ai kamar yaron nan ne cikin motar nan ko?" Inna ta faɗa tana leƙe cikin motar MuhammadAalin. Sai a lokacin ya sauke numfashi, har yana ƙoƙarin tura kan motar tasa zuwa cikin gidan, sai ƙwaƙwalwarsa ta tunasar da shi wace ce Inna, mene ne za ta iya yi, da kuma wanda ba za ta iya ba. Wannan dalilin ne ya sanya shi dakatawa. Ba don ya so ba, sai don yana gudun halayenta, hakan ya sa ya buɗe ƙofar motar sannan ya fito. "Oh, ni na san shi ne a ciki, amma don rashin ta ido yana ƙoƙarin wucewa kamar bai gan ni ba." Ta faɗa tana watsa masa wani kallo. Ko nuna alamar ya gani bai yi ba, sai tura murfin motar da ya yi yana ƙoƙari wajen ganin bai nuna ɓacin ransa a fili ba. Don idan dai har ya ce ya ji daɗin ganin matar, to tabbas ya yi ƙarya ne. "Je ka biya mai adaidaitar can kuɗin motar da ya kawo mu." Ta faɗa tana nuna matashin da ke kallo inda suke. Bai ce komai ba, bai kuma nuna alamar ya ji abin da ta faɗa ɗin ba kawai ya yi gaba, wanda hakan ya nuna mata ya ji ɗin, ya ƙarasa ba tare da ya tambayi matashin kuɗinsa ba, ya miƙa masa kuɗin da ya ɗakko daga cikin motarsa. Daga haka ya juyo, daidai lokacin da Inna ke faɗin "Eh lallai ya ƙaro wulaƙanci." Sai a lokacin sannan ya danne zuciyarsa, ya taushi kansa, don gudun ɓacin ran mahaifinsa ya ce "Barka da zuwa." Wani kallo ta yi masa sannan ta watsar, ta ja hannun Hamida suka shige cikin gidan ba tare da ta ce komai ba. Shi a wajensa ma hakan daɗi ya yi masa, don yana da tabbacin babu lallai magana mai daɗi ta fito daga bakinta. Kai tsaye cikin motarsa ya koma ya tayar ya shige cikin gidan. Kallon Inna Hamida ta yi lokacin da suka shiga cikin gidan ta ce "Wai wannan ma kin san shi?" Numfashi Innar ta sauke kafin ta ce "Shashasha shi ne Muhammad ɗin ai." Wani irin zaro idanunta Hamida ta yi har tana dakatawa daga inda take ta ce "Wai shi ne wanda kika zaɓa mini ɗin?" Ta yi maganar hannunta ɗore a kan ƙirjinta. Girgiza kai Inna ta yi lokaci guda tana yin wani miskilin murmushi ta ce "Kwantar da hankalinki, hakan ba wani abu ba ne. Shi dai wannan ɗin, shi ne mijinki na gobe." Zubewa Hamida ta yi a wajen ta yi zaman daɓaro ta shiga faɗin "Na shiga 3 Inna zan mutu saboda farinciki. Wannan zuƙeƙen mutumin? Kuma ma ba sai ki faɗa mini ba, in watsa masa kallon soyayya ba? Inna da gaske wannan ni zai aura? Inna ko a lahira aka ba ni wannan kawai a matsayin tukwuicin zaman da na yi a duniya ai an sallame ni." Dariya sosai Inna ta yi, ita da ma ta san dole ne ta tashi kan jikar tata. Don Hamidar ta kasance wadda ake ji da ita a ƙauyensu, shi ya sa take murza rashin mutuncin da ta ga dama, musamman da ya kasance tana da masoya bila adadin a ƙauyen nasu, waɗanda kowa so yake ta zaɓe shi a matsayin wanda take so. "Ai ba a banza ba nake bin bayanki idan kika tashi korar saurayi ba. Ni na san zaɓin da na yi miki ai, lokaci kawai nake jira, kuma ga shi ya zo. Maza tashi mu tafi." Babu musu Hamida ta miƙe tana jin wani irin farinciki kamar ta taka rawa. Wai wannan haɗaɗɗen mutumin ne zai zama mijinta? Ita kuwa ina za ta saka kanta don daɗi? Wani irin fari ta yi, tana hasaso yadda cikin ƙanƙanin lokaci za ta tafi da zuciyarsa ta hanyar farin da ta saba yi wa samarinta. Tun daga nesa Daddy ke hangen Innar, jikarta biye da ita da kaya niƙi-niƙi a hannun wani mai kula da bishiyun gidan. "Jaraba! Me ya kawo wannan matar gidan nan kuma?" Ya tambayi kansa cike da mamaki idanunsa a kan Innar. Kafin ya kai ga lalubo wa kansa amsar tambayar Innar ta ƙaraso. Cikin girmamawa ya ce "Barka da zuwa Inna." "Yawwa barka dai Aminu." "Mu je ciki ko?" Daddy ya tambaya yana mata nuni da sashensa. Sai da ta ɗan yi jimm kamar mai tunani sannan ta jinjina kai bayan amincewa da abin da ƙwaƙwalwarta ta saƙa mata, sai ta bi bayansa zuwa sashen nasa. Kallon parlourn take yi tun daga sama har ƙasa, yadda aka sauya tsarin ya matuƙar yi mata kyau da daɗi, don ta tabbatar sashen Baba sai ya fi wannan tsaruwa. "Barka da zuwa Inna." Umman Ammeey ta faɗa bayan ta miƙe daga zaunen da take. Sai da ta nemi waje ta zauna tana sauke numfashin gajiya sannan ta ce "Yawwa." Ita ma Hamida neman waje ta yi ta zauna bayan ta gama ƙare wa wannan haɗaɗɗen gida kallo, wanda ya fi mata kama da aljannar duniya. Ah da gaske 'yan birni suna hutawa, ita kam tana son harkar watayawa, shi ya sa babu abin da ba za ta iya yi a kan samun hakan ba. "Mu je ku samu ku watsa ruwa ko?" Umma ta faɗa tana murmushi. "Ni ba wankan da zan yi gaskiya, yunwa kawai nake ji." Hamida ta faɗa, kamar wadda ke magana da sa'ar ta. Kallon ta Umma ta yi cikin basarwa, ba tare da ta nuna ta ji wani abu a kan maganar da ta yi mata ba. "Gaskiya dai, fara kawo mana abinci tukunna." In ji Inna. Babu musu Umma ta amsa da "To." tana ƙarasawa zuwa kitchen ɗinta. Bin ta da kallo Daddy ya yi, kafin ya dawo da dubansa kan Innar. Wani irin takaicin zuwan nata yake yi matuƙa, ji yake kamar ya rusa ihu. Bai san me ya kawo ta ba, amma a jikinsa yake ji ko ma dai mene ne zai yi wuya idan alkairi ne saboda sanin hali. Ga shi kuma har da ɗakko jikarta ta taho su ɗebo uban kayan nan su yi musu dirar mikiya cikin gida, ka rantse suna da gado. Shi dai don takaici bai iya cewa komai ba ya fice daga ɗakin. Ko bayan da Umma ta kawo musu abinci bajewa suka yi cikin ɗakin, suka kwashi abinci son ransu. "Inna mu ɗauki ragowar saboda tsaro ko?" Hamida ta faɗa ƙasa-ƙasa, ganin tulin abincin da suka rage duk kuwa da yadda suka cika uwar tumbinsu. Tsaki Inna ta ja sannan ta ce "Ji mini jarababbiya. Kin ga idan za ki kama kanki cikin gidan nan ki kama kar ki ja mini asara? Wa ya faɗa miki sai mun yi guzurin abin da za mu ci? To idan abinci sau goma za ki ci babu wanda zai ɗaga ido ya kalle ki." "Don Allah Inna?" Hamida ta faɗa tana zaro ido. "Naki wasa ne, zuba ido ki gani." A sashen Daddyn suka wuni, har zuwa lokacin da Baba ya dawo, shi ma kai tsaye sashen ya nufa don an sanar da shi zuwan Innar. Ya ji daɗin zuwan nata, don da ma ta kwana biyu ba ta zo ba. Ganin ta kuma yana sanya shi tunawa da cewa har lokacin suna da wadda suke kalla a matsayin uwa. Don Inna ta kasance ƙanwa ga mahaifinsu, wadda ita ɗaya ta rage musu yanzu haka. Gaisawa suka yi cikin girmamawa yana tambayar yadda suka baro ƙauye. "Ƙauye suna lafiya." Innar ta faɗa. Bai wani daɗe ba, ya miƙe yana faɗin "Inna bari na je ciki, zan dawo in sha Allah." "To! Ba damuwa, sai mun shigo." Bai kawo komai ba a ransa ba ya ce "To shi kenan." Daga haka ya fice daga ɗakin. Bayan isha'i, Inna ta kalli Hamida da ta lalace a kallon T.V, jin ta take kamar a aljannar duniya, ta ce "Ɗaukar mana kayanmu mu yi gaba." Da mamaki Hamida ta ce "Gaba kuma Inna? Ina za mu je?" "Dalla idan za ki ɗauka ki ɗauka, inda za mu kwana mana." Ji ta yi kamar ta ɗora hannu a ka ta rusa ihu, ita ai duk tunaninta ta ɗauka su ma a nan ɗin za su kwana. Ba don ta so ba ta miƙe ta ɗauki kayan nasu, cikin tura baki take faɗin "Haka nan kawai, sai da aka fara ɗanɗana mini zuma, kuma a ce in bar kallon? Ni wallahi sai na dawo." Jin abin da Hamidar ke faɗa ne ya sanya Inna faɗin "Ke dai shashasha ce, to inda za mu je ya fi nan ɗin ma." "Don Allah?" Ta tambaya da sauri. "Naki wasa ne." Ta yi maganar tana kallon Ammeey da ta fitodaga ɗakinta. Ita gabaɗaya ta kasa sakin jiki tun da ta dawo ta ga baƙin a sashensu. "Kin ga kira mini Ummanki, ki ce mata za mu wuce." Da "To." ta amsa tana shigewa ɗakin Umman. Babu daɗewa sai ga ta ta fito, ta ce cike da mamaki "Inna ina za ku je ne ni kam?" Murmushi Inna ta yi sannan ta ce "Sashen Yayan nasu za mu, ai a can ya kamata mu sauka da ma." Cike da mamakin dai Umma ta ce "Inna nan ɗin bai yi miki ba ne?" Ta tambaya jiki a matuƙar sanyaye. Sai ta girgiza kai kana ta ce "Babu wani abu, amma dai kam a can za mu zauna. Ke Hamida mu je." Ta yi maganar tana fara tafiya. Har Umma na ƙoƙarin bin su, Ammeey ta yi saurin riƙo hannunta tana faɗin "Umma don Allah ki bar su." Ta yi maganar ƙasa-ƙasa. Harara Umman ta watsa mata, don da ma tun ɗazu ta fahimci yadda take ta raɓe-raɓe tun bayan zuwan baƙin. "Yallaɓai da ka sani ka ɗauki mataki. Idan ka ji yadda mutane ke yawan yi mini magana a kan abin da ya faru sai ka yi mamaki. Zan zo a ce ka magantu ko yaya ne." Hajiya Turai ta faɗa. Murmushin yaƙe Baba ya yi, wanda ake kira ya fi kuka ciwo. "Ki kwantar da hankalinki, komai zai daidaita in sha Allah. Ke kin san wane ne mijinki, kin san abin da zai iya da kuma wanda ba zai iya ba. Kin kuma san wane ne Muhammad. Ina ganin wannan kaɗai ya isa ya saka ki kwantar da hankalinki." Ajiyar zuciya kawai ta sauke ba don ta so ba ta ce "Shi kenan Yallaɓai, Allah Ya bayyana gaskiya." "Shi ne abin da nake so na ji kin faɗa. Ina ta kuma addu'a, duk wanda ya yi hakan, ba zai samu nutsuwa ba har sai ya ƙaryata kansa.." Maganar tasa ta katse, lokacin da Inna da Hamida suka yi sallama cikin sashen. Da sauri Baba ya miƙe yana faɗin "A'ah Inna da kanki kuma? Ai da ba ki wahalar da kanki ba, yanzun nake ƙoƙarin shigowa sashen." "Babu komai, ai ga mu ma mun kawo kanmu, abin da ya rage kawai a gyara mana wajen kwanciya." Kallon juna Baba da Hajiya Turai suka yi, sai kuma Baba ya yi murmushi bayan ya kalli Innar ya ce "To shi kenan, Turai, maza gyara musu ɗakin da za su kwanta." Babu musu ta amsa da "To." Sai dai kafin ta je ɗakin, sai da ta tsaya suka ƙara gaisawa da Innar, tana lura da Hamida da ta saki baki tana kallon ɗakin hanci da baki duka a sake. "Kin yi girkin ne?" Adam ya faɗa yana kallon Nafisa. Ko kallon inda yake ba ta yi ba, ta sake haɗe girarta waje ɗaya tana gyara zamanta. A karo na biyu ya sake maimaita mata tambayar, sai a lokacin sannan ta ce "Ka je wadda kake waya da ita ta girka maka. Ai ba 'yar iska ka ajiye a cikin gidan nan ba. Za ka je ka gama abin da kake yi a waje sannan ka dawo mini gida ni aikina kawai in girka ne da kuma biyan buƙatarka. To wallahi ba zan girka ba, kai daga yau ma ka nemi mai yi maka girki idan dai har ka zaɓi ka ci gaba da kula wata mace bayan ni. Ka ɗauka hoto ce ni kawai a gidan nan." Cike da mamaki Adam ke kallon ta, wai shin me yake damun Nafisa? Shin a ganinta wannan abin da take yi shi ne zai saka ya fasa auren Janan? A ganinta wannan ce hanyar da za ta saka ya fasa abin da ya yi niyya? "Haka kika ce?" Ya faɗa cike da takaici. Don ta tabbatar masa da abin da ta faɗa ya sanya ta jinjina kanta sannan ta ce "Eh haka na faɗa." Ɗaga kafaɗarsa ya yi kafin ya ce "Ohk." Daga haka ya yi waje yana jin yadda hakan ya yi masa ɗaci. Daidai lokacin da yayar Nafisar ta shigo ɗakin. Da ma ƙiris take jira, hakan ne ya sanya ta fashewa da kuka tana miƙewa ta rungume Yayar tata. "Ni dai daga ganin yanayin Adam na san ba lafiya ba. Faɗa mini me yake faruwa? Mene ne ya saka ki kuka?" "Yaya wallahi Adam ya daina so na, Adam ya daina bin umarnina a cikin gidan nan. Wai Yaya Adam ke waya da wata a cikin gidan nan bayan ina ciki? Har yake kallo na yana faɗa mini cikin ƙwarin gwuiwa zai ƙara aure? Shin me na ragi Adam da shi da zai saka mini da haka? Me ya sa Adam zai saka mini da abin da na fi tsana a duk duniya." Ta ƙare maganar tana ɗagowa daga jikin Yayar, sai kuma ta ɗora da "Yaya kin fi kowa sanin yadda nake ƙaunar Adam, wallahi ba zan yarda ya raba soyayyar da yake mini da wata ba. Yaya ba zan iya ba, wallahi zan iya kashe yarinya. Yaya zuciyata kamar za ta fashe don baƙinciki, ta yaya zan jure ganin wata halitta na rayuwa cikin gidan nan a matsayin matar Adam? Ba zan taɓa iyawa ba. Wallahi na gwammace a ɗauki gawar Adam da tawa da ta yarinyar a lokaci guda, da dai in bari wata ta raɓe shi." Ta ƙare maganar tana fashewa da sabon kuka. Ajiyar zuciya Yayar ta sauke ta ce "Kwantar da hankalinki Nafisa. Mene ne na kukan? Ba dai Adam ba ne? Mene ne na ɗaga hankalin? Ya zauna a ƙarƙashinki ma ballantana wannan ƙaramin aikin? Za a raba shi da yarinyar ta yadda ba zai sake waiwayar ta ba." "A'ah Yaya ba na buƙatar haka. Ina so ta yi nadamar ƙoƙarin shiga gonata da ta yi, ina so a lalata mata rayuwa ta yadda shi da kansa zai ce ya fasa auren ta don Allah Yaya." "Shi kenan?" Yayar ta faɗa tana yin wani sassanyan murmushi cike da fatan hakan ya sanya hankalin ƙanwar tata ya kwanta. "Eh Yaya, ni idan aka yi mini haka an biya ni." "Shi kenan, yadda kike so haka za a yi. Babu wata wadda ta isa ta raɓi Adam ba tare da ta ja wa kanta masifa ba. Adam naki ne ke ɗaya, don ke kaɗai aka halicce shi. Da ke kaɗai zai rayu duk tsayin rayuwarsa, ko yana so ko ba ya so. Yadda kika dama dole haka za a sha." Rungume Yayar Nafisa ta yi tana jin wani irin farinciki na ziyartar ta. "Ban ƙi ba ko nawa ne zan kashe Yaya, wallahi ko da duk dukiyata za ta ƙare wajen tarwatsa rayuwar yarinyar da yake so zan ƙarar. Ko da hakan na nufin sai na ƙarar da har dukiyar Adam ne, ba ni da damuwa. Ni dai kawai in rayu da shi ko ma cikin wanne yanayi ne, in ma arziƙi ko talaucin da za mu dinga kwana babu abin da muke da shi wanda za mu ci. Idan dai har zan ga Adam a kusa da ni, ba ni da wata matsala da wannan." Murmushi Yayar ta yi sannan ta ce "Kar ki damu hakan ma ba za ta faru ba. Ke dai ki tanadi maƙudan kuɗi na aikin. Ni na san me zan saka a yi mini, cikin ƙanƙanin lokaci Adam zai fasa auren yarinyar." Ta ƙare maganar cikin murmushin dai. Ita ta san irin mahaukacin son da Nafisa ke yi wa Adam, irin son nan da ba ta ganin kowa sai shi, ba ta ji ba ta ganin kowa sai shi. Tun kafin aurensu haka take ta fama, izuwa yanzu kuma sai abin da ya ƙaru a soyayyar Adam ɗin. Da mamaki Baba ke kallon Innar da ke zaune a kan kujerar parlourn. Ya ƙaraso a nutse yana faɗin "Inna wai ba ki yi bacci ba?" Sai ta girgiza kai sannan ta ce "Ina fa bacci. Amma dai ba wannan ba, ya aka yi kai har yanzu ba ka yi bacci ba?" "Zan duba Muhammad ne ko ya shigo gidan nan. Tun ɗazu nake jiran kiran sa ban ji shi ba. To sai da na duba wayar na ga ashe babu network ne. Wataƙila ya shigo gidan, ya kira ni kuma bai same ni ba. Shi ya sa zan je na duba shi." Dagalo Inna ta yi tana kallon Baban cike da mamakin wannan shegantaka da yake faɗa. Yo shegantaka mana! "Yanzu wannan goɗai-goɗai da shi ɗin za ka ce kana jiran shigowar shi gida? Shi a hankalinsa bai san ya dawo gida lokacin da ya dace ba, kafin kuma kowa ya yi bacci ba?" Girgiza kai Baba ya yi da sauri sannan ya ce "Akasi aka samu Inna. Amma idan dai ba wani uzurin ba, ba ya wuce ƙarfe goma a waje. Ki yi haƙuri." Baba ya faɗa don so yake gabaɗaya ma a bar maganar sanin halin Innar da ya yi musamman a kan Muhammad ɗin. Sai dai ga mamakinsa sai ji ya yi ta ce "To ashe ma ni na zo a daidai. Wallahi kamar na sani hankalina ya kasa kwanciya a kan yaron nan. To ka san mene ne mafita?" Ta tambaya tana kallon sa. Ba tare da ya fahimci abin da take faɗa ba ya girgiza kansa. Ba ta jira ya ce komai ba ta ce "Abu ɗaya za a yi masa wanda zai saka hankalinsa ya dawo jikinsa. Wanda zai saka ko ya ƙi ko ya so ya dinga dawowa gida, wato aure." Jinjina kansa Baba ya shiga yi cike da yin na'am da maganar Innar. Sai dai kafin ya ida tunanin nasa, ya jiyo muryar Inna na faɗin "Ai ka ga Hamida da na zo da ita ko?" Ba tare da Baba ya kawo komai a ransa ba ya ce "Eh Inna." "Yawwa.. To abu ɗaya ne ya kawo ni gidan nan a wannan karon. Na zo da ita ne don a sasanta, a ɗaura mata aure da Muhammad." Cikin rashin fahimta Baba ke kallon Innar, har bai san lokacin da ya furta "Inna wanne Muhammad?" Ita ma kallon tuhumar ta jefa masa, cikin jin haushin tambayar rainin hankalin da ya yi mata. "To Muhammad ɗin kuma nawa ne? Muhammad dai naka nake magana a kai." Wani dogon numfashi Baba ya ja, kafin ya sauke shi. Wannan shi ake kira da ƙa-ƙa-ƙara-ƙa-ƙa. Sake gyara zama ya yi a inda ya zauna sannan ya buɗe baki da niyyar yin magana, Inna ta katse shi da faɗin "Kada ka manta, ni ɗin nan yanzu ni ce mahaifiyar da ba ku da kamar ta. Idan kuwa haka ne, bin umarnina kamar abu ne da ya kamata. Kada ka ce komai a kan wannan maganar, ka je ka yi tunani sai ka zo mu yi magana. Amma dai abu ɗaya nake so ka dinga tunawa, wannan ɗin kamar umarni ne nake ba ka, ba wai shawara ba." Mhiz Innocent 08124818273 *♡☆BIYU BABU☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) YOTA Writers Ass.. Book 1 Pg 22 Shiru ne ya wanzu cikin ɗakin na tsawon mintina. Duk abin da Baba ya yi niyyar faɗa, sai ya ji a take a wajen ƙwarin gwuiwar nasa na zagwanyewa yana yin nasa wajen. Ya sauke numfashi a karo na barkatai sannan ya ce "Shi kenan Inna, sai kin ji ni." "To yawwa dai." Ta faɗa tana miƙewa, daidai lokacin da Baba yake ƙoƙarin ficewa daga ɗakin. A hankali yake tafiya, zuciyarsa cike fall da saƙe-saƙe. Shi kam ta ina zai fara gabatar da wannan abu da Inna take so? Kenan hakan na nufin ya fifita farincikinta a kan na shalelen nasa? A haka ya ƙarasa sashen mazan gidan. Daga waje ya tsaya ya

Chapter 16 of 24