saboda lokuta da dama takan shigo ɗakin ta ga ɗiyarta kafin ta koma ɗakinta. Wani lokacin ta same ta ido biyu, wani lokacin kuma ta same ta ta yi bacci. Sai ta yi saurin lumshe idanunta don kar Ummeen ta san ba ta yi bacci ba. Sai dai ga matuƙar mamakinta, har bayan wajen mintina biyu ba ta ji motsin Ummeen ba ballantana maganarta. Hakan ne dalilin da ya sanya ta buɗe idanunta ta zube su cikin ɗakin. Duhun dare, da kuma tasirin marasa lafiyar idanunta ya sanya ba ta iya ganin abin da ke cikin ɗakin. Kawai sai ta ji zuciyarta ta buga, cike da tsoro ta furta
"Waye?" Ta yi maganar tana gyara zamanta, ba kuma tare da ta damu ta saka glass ɗinta ba ta soma yunƙurin miƙewa don ta kunna ƙwan ɗakin. Sai dai cikin ƙanƙanin lokaci, kamar kuma wancan lokacin ta ji an mayar da ita kan gadon. Ba ta san lokacin da ta saki wata ƙara ba cikin tsananin tashin hankali. Ba tare da ta ankara, ta ji an toshe bakinta da hannu, lokaci guda kuma mutumin na ɗora kansa kan wuyanta, ya shiga shanshanar wuyanta a haukace kamar wanda ke neman zaucewa. Cikin tsananin tashin hankalin da tun da uwarta ta haife ta ba ta taɓa jin sa ba ta shiga zamewa ƙasa, jikinta na wani irin mahaukacin karkarwa. Sai dai ko gezau, ba a sake ta ba, sai ma ci gaba da yin amfani da hannunsa da ya yi wajen sake zame hannun rigar jikinta yadda zai ji daɗin soma rikita mata lissafi, ya kuma kashe mata jiki, kafin ya aikata abin da ya kawo shi cikin ɗakin. Wata gigitacciyar ƙara ta saki, wadda ta sanya mutumin saurin sakin ta, don ya san dole ta jawo hankalin mutanen gidan. Hakan ya sanya shi ficewa daga ɗakin da wani irin gudu. A gigice ta bi bayanshi, don ba ta san mene ne za ta zauna ta ci gaba da yi cikin ɗakin ba. Da wani irin gudun da ba ta san tana da shi ba ta ƙarasa ɗakinsu Ummee, a gigice take bugawa kamar za ta fasa ƙofar, kuka kawai take yi kamar ranta zai fita.
Cike da mamaki Abee da idanunsa biyu, ya ƙarasa ya buɗe ƙofar yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa. Ganin Janan tsaye a bakin ƙofar tana kuka da dukkan wani ƙarfinta ya sake sanyawa ya ji tsoro ya shige shi. 'Shin me ya faru?' Ya tambayi kansa. Daidai lokacin da Ummee ta ƙaraso hankali a tashe, babu ɓata lokaci Janan ta faɗa jikinta tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Cikin tashin hankali Ummee da Abee suka haɗa baki wajen faɗin
"Me ya faru?" Allah kaɗai Ya san irin tashin hankalin da Ummee ta tsinci kanta a ciki, ban da bugu babu abin da zuciyarta ke yi. Ta kasa cewa komai, ta kasa yunƙurin yin komai, kawai kukan take ci gaba da yi cikin rashin sanin abin yi. I zuwa lokacin hankalin Ummee ya sake tashi.
"Ki yi shiru Janan ki sanar da ni abin da ya faru." Ta yi ƙarfin halin faɗar hakan muryarta na rawa.
"Aysha! Ki yi shiru kin ji? Sanar da mu me yake faruwa?" Shi ma Abee ya faɗa yana jin tashin hankalin, kawai mazewa yake yi. Hannunta ta ɗaga ta shiga nuna hanyar ɗakinta, sai dai ta kasa furta komai.
"Me ya faru?" Ummee ta yi azamar tambayar hakan tana kallon hanyar ɗakin Janan ɗin.
"Ummee wani ne ya shigo cikin ɗakin, Ummee wallahi wani ne ya shigo ɗakin, ranar nan ma ya shigo har na faɗa wa Yah Farouk, da gaske nake Ummee ba mafarki ne na yi ba. Wani ne ya shigo wallahi." Ta yi maganar, wadda jikinta da muryarta ke nuna a rikice take, saboda yadda ilahirin jikinta ke rawa kamar mazari. Daidai wannan lokacin Farouk ya shigo cikin ɗakin, saboda hayaniyar da ta jawo hankalinsa lokacin yana zaune cikin ɗakinsa ɗauke da waya a hannunsa. Bai riga da ya yi bacci ba, don wannan ɗin ɗabi'arsa ce, rashin bacci da wuri. Da fari kamar ya so ya jiyo ƙara, sai kuma bai gasgata hakan ba, don haka ya ci gaba da abin da ya zaunar da shi da daren, har daga baya ya tabbatar da tabbas akwai wani abu da ke faruwa a sashen nan. Hakan ne ya sanya shi tasowa ya ƙarasa sashen, wanda maganar da Janan ɗin ta yi a kunnensa ta sauka. A'ah, gabaɗaya sai kansa ya kulle. To ko dai da gaske Janan ɗin take yi? To amma ta yaya? Ta ina wani zai iya shigowa gidan nasu har cikin ɗakinta ba tare da sun sani ba?
"Wani? Aysha me kike ƙoƙarin cewa ne?" Baba ya faɗa yana ci gaba da kallon ta, don so yake ya nazarce ta.
"Eh Abee, wallahi da gaske nake." Ita dai Ummee ta kasa cewa komai, don abin ya mugun ɗaure mata kai. Tun kafin su kai ga cewa komai Farouk ya wuce ɗakin nata. Sosai ya bincika ko'ina, har cikin toilet amma bai ga kowa ba.
"Duba har waje." Abee ya faɗa lokacin da Farouk ɗin ya fito daga ɗakin. Babu musu ya shiga duba cikin parlourn kansa, ko'ina sai da ya duba, sannan ya fice zuwa harabar gidan. Iya dubawa ya yi ta, sai dai ko alamar mutum bai gani ba, ballantana kuma ta kai ga wata alama da za ta nuna cewa an shigo gidan ko an fita. Bai yarda ba, sai da ya sake dubawa har cikin motocin gidan sannan ya dawo. Zuwa lokacin daga Ummee har Abee kowannensu yana zaune jiki a matuƙar sanyaye.
"Me ya faru?" Ummee ta faɗa tana kallon Farouk ɗin.
"Ummee babu wata alama da ke nuna an shigo gidan nan, ballantana har ta kai ga na ga wani mutumin. Kwanaki can Janan ta taɓa faɗa mini irin hakan, lokacin duk ba kwa nan, kawai na ji ban gasgata al'amarin ba ne shi ya sa ban sanar da ku ba. Sai dai yau na so in gasgata ɗin, to amma ban san wacce hujja zan riƙa ba. Tun da babu wata alama ko guda ɗaya."
"Farouk, ya zama dole a bincika ko ma ta yaya ne. Hankalina ba zai kwanta ba, har sai an tabbatar da babu wani abu da ke faruwa." Abee ya faɗa.
"Ni ma nawa hankalin ya kasa kwanciya." Ummee ta ba shi amsa jiki a matuƙar sanyaye. Sauke ajiyar zuciya Farouk ya yi, shi kansa zai so hakan ta faru, to amma kai tsaye me za su fara yi? Shi dai haka kawai ya ji yana kokwanto, ba ya tunanin hakan me yiwuwa ne, har kuma yanzun ya fi tunanin wani mummunan mafarki ne 'yar'uwar tasa ke yi, sai ta farka a tsorace. Ban da haka, ai ko da wata alama guda ɗaya ce za a gani, wadda za su riƙa a matsayin eh lallai tabbas haka ɗin ne. Ba ya son wannan tsoron nata ko kaɗan. Gabaɗaya kiɗimewa take yi idan ta tsorata, ko a gaske ne ko da kuwa a mafarki. Shi ya sa yake ganin yanzun ma haka ɗin ne. To ko ma dai mene ne, zai sake bincikawa don tabbatar da al'amarin, duk da kawai dai yana ganin hakan ma ba mai yiwuwa ba ne.
Sun shafe fiye da rabin awa zaune cikin ɗakin, har zuwa lokacin Janan na jikin Ummee, tun tana kukan har ta haƙura ta yi shiru, sai dai da ma bacci tuni ya ƙauracewa idanunta. Ba ta jin ko alamar bacci ne bare shi kansa ya zo.
"Aysha tashi ki je ki kwanta, dare yana sake yi." Abee ya faɗa bayan shuɗewar wasu mintina ba tare da kowa ya ce wani abu ba. Idanunta a lumshe har lokacin ta ce
"Abee ba zan iya ba wallahi, ba zan iya ba." Gajeren numfashi Abee ya sauke sannan ya ce
"Ummee ɗauke ta ku je ta samu ta kwanta. Rashin baccin ma ba shi da amfani. Ko ma mene ne zan bincika, duk da da wuya gaskiya idan ba... Kodayake dai, ba za mu ƙi tata ba, za mu bincika ɗin kawai. Allah Ya ƙara tsarewa."
"Ameen." Ummee da Farouk suka haɗa baki wajen faɗin hakan. Daga haka Ummee ta miƙe, daidai lokacin da Janan ke faɗin
"Ummee ni ba na son ɗakin wallahi, Ummee ba na son ɗakin."
"Ba zan bar ki ke ɗaya ba Aysha, mu je na taya ki kwana." Ummee ta faɗa cikin rarrashi. Sai a lokacin sannan ta ji sanyi, ta shiga bin Ummeen kamar raƙumi da akala har suka isa ɗakin nata. Duk da babu glass a idanunta, amma da Ummee ta kunna ƙwan ɗakin a haka ta dinga amfani da idanun ko za ta gano wani abun.
"Ya isa haka Janan, bacci nake so ki yi ba tunane-tunane ba." Ummee ta fadi hakan, ita a karan kanta tana ji lallai tabbas ɗiyar tata tsorata ce dai irin wadda ta saba yi idan ta yi mafarkin wani abu mai tsoro. Idan ba haka ba, me ya sa ba su ga wata alama da ke nuna an shigo gida ko ɗakin ba? Amma ba ta nuna mata ba, ta taimaka mata wajen kwanciya, ta ɗora kanta a kan cinyar Ummeen tana saurin lumshe idanunta, cike da fatan bacci ya yi awon gaba da ita cikin ƙanƙanin lokaci.
Parking ɗin motar kansa ba a daidai ta yi shi ba. Tana tsayawa ta fito daga cikin motar ko jakarta da ke ajiye a wajen mai zaman banza ba ta ɗauka ba, kai tsaye ta wuce cikin gidan. Babu kowa cikin parlourn kasancewar yau tun safe Janan ta tafi islamiyya, kasancewar Asabar ce. Zama ta yi a kan kujera hannunta ɗore a kanta. Bayan wajen minti ɗaya ta fesar da wata zazzafar iska daga bakinta. Daidai lokacin da wayarta ta soma ruri, kamar da ma jira take yi, ta miƙe sannan ta saka hannunta ta amsa wayar babu ɓata lokaci tana kara ta a kunnenta. Wajen mintina biyu ana yi mata magana sannan ta katse, daidai wannan lokacin Farouk ya shigo cikin ɗakin. A nutse yake nazartar Ummeen, ko ba ta faɗa ba, tabbas ya san akwai abin da ke faruwa. Da sauri ya ƙarasa, jin ko damar amsa sallamar da ya yi ba ta yi ba.
"Ummee lafiya?" Ya faɗa kai tsaye yana jin yadda hankalinsa ya soma tashi saboda yanayin yadda ya ga Ummeen a ciki. Idanunta na kan wayarta lokacin da ta ce
"Farouk akwai matsala." Haka nan kawai ya ji zuciyarsa ta buga, cikin ƙanƙanin lokaci ƙwaƙwalwarsa ta tafi tunano masa wacce iriyar matsala kenan take nufi? Me yake faruwa? Me ya faru wanda har ya ɗaga hankalin jajirtacciyar Ummeen tasu? 'Ko dai a kan Janan ne?' Ya tambayi kansa, sanin yadda al'amarin Janan ɗin ke saurin tayar mata da hankali. Ban da gumi babu abin da Ummee take yi. Daidai lokacin da wayarta ta sake yin ruri, ji ta yi kamar kar ta ɗaga, sai dai ba ta san kuma me za a ce mata cikin wayar ba, duk da haka nan kawai take jin tsoro bayan hakan ba ɗabi'arta ba ce. Hakan ne ya sa ta ɗaga wayar.
"Hajiya da gaske dai aiki ya ɓaci. Yanzu na ci karo da posting a kan Alhaji Abbas Shettima. Da gaske sun nemo ta, ita kuma ta ambaci sunansa." Aka faɗa mata daga can ɓangaren. Kawai sai ta sake komawa kan kujerar cikin rashin sanin abin yi. Wayar ma da take yi ba ta sani ba ko ta katse ko ba ta katse ba, ta ajiye ta ne ko faɗuwa ta yi, ita dai ta san a yanzu da take zaune babu waya a hannunta. Gabaɗaya man kanta ya tsotse, ta ma rasa wanne irin tunani za ta yi ballantana ya kai ta ga nema wa kanta mafita.
Mhiz Innocent
08124818273
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 16
"Ummee wai me yake faruwa ne?" Farouk ya faɗa bayan ya ƙarasa kusa da Ummeen sosai, yana ci gaba da nazarin ta. Yadda take a ruɗe shi ne abin da ke sake tsorata shi.
"Nemi waje ka zauna Farouk, bari na bincika wani abu." Ta faɗa tana neman waje ta zauna har lokacin hannunta ɗauke da wayarta. Kamar ba zai zauna ba, sai kuma dai ya bi umarnin Ummeen ya nemi waje ya zauna, cike da zaƙuwa da son jin abin da ya faru haka. Daidai lokacin da aka soma knocking ɗin ƙofar gidan, sai da Farouk ya kalli Ummee da ita ma shi ta kalla sannan ta ce
"Je ka duba." Babu musu ya miƙe, ba tare da ya ce komai ba ya fice daga ɗakin. Yana tsaye sanye cikin manyan kayan da suka karɓi jikinsa, idan ka gan shi sai ka ɗauka hankalinsa a matuƙar kwance yake, sai dai ko yanzu kafin ya fito sai da Nafisa ta ɗaga masa hankali, haka kawai ya fito daga gidan don ya samu zuciyarsa ta huce. Wannan dalilin ne ya sanya shi sake zuwa gidan, don tabbas so yake ko za a ji tausayinsa a aura masa Janan, don ya gaji da auren Nafisa, rashin kwanciyar hankalin da yake fama da shi kullum ya fara isar shi. Kallon juna shi da Farouk suka yi sannan ya yi masa sallama bayan ya miƙa masa hannu. A nutse Farouk ya miƙa masa nasa hannun har lokacin yana kallon sa. Ganin irin kallon da Farouk ɗin ke yi masa ya sanya shi ƙaƙalo murmushi cike da fata kala-kala ya ce
"Na zo wajen Baba ne don Allah." Sai a lokacin sannan Farouk ya sauke numfashi ya ce
"Ayyah Abee ba ya nan gaskiya."
"Babu damuwa, don Allah ko za ka haɗa ni da Umma?" Cike da mamaki Yah Farouk ke ci gaba da kallon sa. Ummee kuma? Lafiya? Me ya faru? Duka ya tambayi kansa, cike da fatan Adam ɗin ya ji abin da yake saƙawa cikin zuciyarsa, ya sauƙaƙa masa wajen ba shi amsa.
"Don Allah, ba wani abu ba ne. A taimaka mini." Adam ya sake faɗa, don wallahi shi kaɗai ya san yadda soyayyar Janan ɗin ke nuƙurƙusar zuciyarsa. Jin abin da ya faɗa, shi ne ya sanya ya ɗan ji sauƙi, sai ya sake sauke numfashi a karo na barkatai sannan ya ce
"Shigo." Ya yi maganar yana yin gaba.
"Na gode ƙwarai." Adam ya faɗa yana ji kamar ya taka rawa. Sai ya bi bayan Yah Farouk ɗin har suka ƙarasa ɗakin Ummeen. Shiga ya yi ciki, bayan wajen mintina uku ya fito ya yi wa Adam ɗin izinin shiga. Tun da ya shigo Ummee ke kallon fuskarsa, don so take yi ta fahimci ko ta san shi. Sai dai sam ba ta taɓa ganin fuskar ba.
"Barka da wannan lokacin Umma." Adam ya faɗa cike da girmamawa kansa a ƙasa ba tare da ya bari sun haɗa ido da Ummeen ba.
"Barka dai." Ta faɗa, tana iya bakin ƙoƙarinta wajen danne tashin hankalin da take ciki. Shiru ne ya wanzu cikin ɗakin, ita Ummee tana jira ta ji abin da Adam ɗin zai ce, ya yin da shi kuma yake ta kokawa da kalaman bakinsa, cikin rashin sanin ta inda zai fara. Daga ƙarshe dai da ya ga ba shi da mafita dole ya buɗe bakinsa ya ce
"Umma da ma wata alfarma na zo nema a wajenki don Allah."
"Alfarma?" Ummee ta faɗa tana kallon sa. Shi dai Farouk ya yi shiru kawai sauraron abin da yake cewa yake yi.
"Eh Umma. Wato na zo wajen Baba na sanar da shi ina da niyyar neman auren Aysha, ya sanar da ni idan dai har zan iya jiran ta to yana maraba da ni. Na nemi alfarmar ko da sau ɗaya ne a wata a dinga bari na na zo na gan ta. To shi ne dalilin da ya sa kai tsaye na sake zuwa wajensa, don neman alfarmar ko da a waya ne a dinga bari na muna gaisawa saboda ta san da ni. Sai dai cikin rashin sa'a ban same shi a gidan ba, sai na ga zuwa wajenki ma yana da matuƙar amfani. Don Allah a taimaka mini Umma, wallahi da gaske nake ina son Aysha, kuma a shirye nake na yi duk abin da kuke so, matuƙar dai za ku aura mini ita."
Ajiyar zuciya Ummee ta sauke bayan gama jin dogon jawabin Adam. Ta yi shiru har na tsawon mintina biyu ba tare da ta ce komai ba. Kafin zuwa can ta ce
"To sannu muna godiya, don duk wanda zai ce yana son naka to tabbas masoyinka ne. To amma wani hanzari ba gudu ba, kamar yadda mahaifinta ya faɗa maka, ni ma dai shi ɗin zan maimaita. Wato a taƙaice dai ba yanzu zai aurar da Aysha ba."
"Na fahimta duka Umma. Abu ɗaya nake nema a yanzu, ko da ta waya ne mu dinga gaisawa don Allah." Ya faɗa jiki a matuƙar, cike da fatan kar wannan damar ma ta suɓuce masa. Numfashi Ummee ta sauke, ta ƙagu ya tafi ne ma ita kam, don akwai abubuwa a gabanta, don Farouk ya roƙe ta sosai ne a kan ta bari ta gan shi ko na mintina ne, ya sa ta haƙura ta bar shi. Ba don haka ba, ita kaɗai ta san mene ne a gabanta, da kuma irin yanayin da zuciyarta ke ciki.
"Shi kenan.. Wannan numberta ce, ka kira ni, sai ku dinga gaisawa ta nan." Ta yi maganar tana miƙa masa katin da ke ɗauke da number wayarta. Wani irin gauron numfashi ya sauke cikin tsananin farinciki, yo shi ko a haka aka bar shi ai an biya shi. Me kuma yake buƙata bayan wannan babbar alfarmar da aka yi masa?
"Na gode sosai Umma, Allah Ya saka da alkairi, Allah Ya biya ki da aljanna, Ya ƙara girma." Gabaɗaya ya ma rasa da wanne baki zai yi wa Ummeen godiya, da gaske ta gama biyan sa, irin biyan da bai san shi da me zai iya saka mata ba.
Hannu ya miƙa wa Farouk lokacin da ya zo tafiya, a nutse ya miƙa masa nasa daidai lokacin da Adam ɗin ke faɗin
"Na gode Yayanmu." Ya faɗa yana sakar masa murmushi. Lumshe idanunsa Farouk ya yi ba tare da ya iya furta komai ba, har zuwa lokacin da Adam ɗin ya fice daga ɗakin.
"Ummee ina zuwa." Ya yi ƙoƙarin fizgo waɗannan kalaman ya faɗa, bai kuma jira amsar Ummeen ba ya fice daga ɗakin. Ba ta lura da yanayinsa ba, don kuwa da ma kawai so take Adam ya fita ta ci gaba da abin da take yi.
Kai tsaye ɗakinsa ya wuce, yana tafiya da sauri kamar zai tashi sama. Kai tsaye kan kujerar ɗakinsa ya zube yana ɗora kansa a kan bangon kujerar, idanunsa a lumshe. Ya kai wajen mintina biyu a hakan sannan ya buɗe idanunsa, ya kafe wayarsa da idanu na tsawon minti ɗaya, daidai lokacin da Janan da tun da ta shigo cikin gidan ta hangi ɗan'uwan nata ta biyo shi. Kawai tsayawa ta yi tana kallon sa har zuwa lokacin da yake kallon wayarsa. Sai a lokacin sannan ta ƙarasa inda yake ta saka hannu tana ƙoƙarin karɓar wayar, lokaci guda tana faɗin
"Yah Farouk." Sam bai lura da shigowarta ba, bai kuma ji alamar tsayuwar mutum a wajen ba, sai da ta yi magana. Sai ya yi azamar kashe wayar yana gyara zamansa. Gabaɗaya ta yi kalar tausayi, don har yanzu abin da ya faru da daddare bai sake ta ba, ga shi kuma ta dawo ta ga ɗan'uwanta cikin damuwa.
"Yah Farouk ɗina mene ne?" Ta faɗa kamar za ta fashe da kuka tana kallon sa. Komawa Farouk ya yi ya sake kwantar da kansa a kan kujerar lokaci guda yana lumshe idanunsa, a daidai lokacin da zuciyarsa ke wani irin bugawa kamar za ta fito daga ƙirjinsa.
"Janan." Ya ambaci sunanta, wanda Janan ɗin ta yi saurin sake kallon sa don tabbatar da da gasken shi ne ya kira sunanta ko ba shi ba ne, saboda yadda ta ji muryar kamar ba tasa ba.
"Na'am Ya Farouk, ba ka da lafiya ne?" Ta sake tambaya duk a dame. Sai ya jinjina mata kai har zuwa lokacin idanunsa a lumshe. Sai ta gyara zamanta sannan ta ce
"Me yake damun ka?" Ta sake tambaya cike da ƙaguwa da son jin abin da ke damun sa. Sai ya sauke numfashi sannan ya buɗe idanunsa lokacin da suka sauya kala, ya zube su a kan fuskarta sannan ya ce
"Ina son ta Janan, ina matuƙar ƙaunar ta. Ina jin zuciyata kamar za ta fashe saboda tsananin ƙaunar ta." Cike da mamaki Janan ke kallon Yah Farouk ɗin, jin abin take kamar a mafarki. Shin da gaske Yah Farouk ɗin ke sanar da ita yana son wata? Yaushe hakan ta faru? Sai dai cikin ƙanƙanin lokaci ta ji murmushi ya suɓuce mata. Sai ta tashi ta koma kusa da shi, kan kujerar da yake kai ta ce
"Faɗa mini Yah Farouk, ya take? Yaushe za ka kai ni wajenta na gaishe ta." Zazzafar iska Farouk ya fesar daga bakinsa kana ya sauke wani bijimin numfashi ya ce
"Ba ta san ma ina yi ba." Cike da mamaki Janan ta ce
"Kai! Yah Farouk ba ta sani ba kuma?" Sai ya jinjina mata kai kawai har lokacin idanunsa a kan fuskarta.
"To me ya sa?" Ta sake tambaya.
"Ba zan iya sanar da ita ba. Ina jin kamar ko da son ta zai yi mini lahani ba zan iya sanar da ita ba. Na gwammace na bar shi cikin zuciyata, ko da hakan na nufin buguwar zuciyata ne idan ta kasa jurewa rashin ta."
"Yah Farouk???" Janan ta ambaci sunansa cikin sigar tambaya. Da gaske yana nufin abin da ya faɗa? Kenan wannan wanne irin so ne? Idan haka ne mene ne amfaninsa? Mene ne kuma dalilin da ya sa ya ce ba zai sanar da ita ba? To ko dai ba da gaske yake son nata ba? Duk ita kaɗai take yi wa kanta tambayar, har lokacin tana kallon Yah Farouk.
"Eh Janan haka na ce." Ya sake ba ta amsa don ya tabbatar mata da abin da ya faɗa. Kawai sai ta yi shiru don ta ma rasa me za ta ce kuma. Gaskiya ta fi tunanin ba son yarinyar yake yi ba, idan ba haka ba ya zai zauna yana azabtar da zuciyarsa. Ita ta ɗanɗana soyayya, shi ya sa take matuƙar mamakin Yah Farouk ɗin.
"Je ki huta." Ya yi maganar a nutse.
"To amma Yah Farouk da ka faɗa mini ni sai na je na sanar da ita idan akwai abin da kake tsoro." Ɗaga idanunsa ya yi da suka ɗan sauya kala ya zube su a kan fuskar Janan ɗin, murmushin nan da ake kira ya fi kuka ciwo shi ne ya suɓuce masa sannan ya ce
"Je ki ciki, ina buƙatar hutawa Aysha." Kamar za ta ce wani abu, sai kuma ta fasa. Ta miƙe ba don ta so ba, ba kuma don ta haƙura ba, sai don ta cika umarnin da ya ba ta. Tafiya take yi amma gabaɗaya ƙwaƙwalwarta ta tafi tunane-tunane. Kamar yadda Yah Farouk ɗin ya saba yin amfani da duk wata dama da Allah Ya ba shi wajen cire ta a damuwa, ita ma za ta taimaka masa. A duk inda yarinyar take za ta binciko ta, za kuma ta tabbatar da ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin Yah Farouk ɗin ya samu abin da yake so. Ba za ta iya jure ganin ɗan'uwanta cikin damuwa ba. Damuwar da shi da bakinsa ya ambaci za ta iya zama sanadiyyar bugawar zuciyarsa. Shin me ya yi zafi? Ba za ta taɓa zama haka nan ba tare da ta taimaki ɗan'uwanta ba.
MuhammadAali ke driving, ya yin da Baba ke gefensa. Suna tafe jefi-jefi suna hira cike da shaƙuwa da ƙaunar junansu. Kana ganin su ka san akwai mugun sabo a tsakaninsu. Muhammad na jin wayarsa na ƙara amma bai kula ta ba, sai ya yi amfani da hannunsa wajen kashe sautin kiran, har zuwa lokacin da suka ƙarasa gida. Yana ƙoƙarin yin parking ɗin motarsa, wayar Baba ta yi ruri, cike da mamakin ganin wanda ke kiran nasa ya ɗaga yana kara wa a kunnensa, lokaci guda yana sauka daga motar.
"Yallaɓai wai me yake faruwa ne haka? Mene ne
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 24