kan fuskarsa. Yana sanye cikin ƙananan kaya masu bala'in kyau. Sumar kansa a buɗe take, irin mai cikar nan ce. Hannayensa duka biyu saƙale a ƙirjinsa, idanunsa gabaɗaya a kan Hajiya Turai. Lokacin da idanunta suka sauka a kan nasa idanun sai ta ida rikicewa, ba ta san lokacin da ta dire a kan ƙafafunta ba ta fashe da kuka. Iska ya ɗan fesar daga bakinsa a nutse kafin ba tare da ya bi ta kanta ba ya ƙarasa, ya ɗan ranƙwafa yana miƙa hannunsa ya ɗauki wayar. Ba tare da ya ce ko uffan ba ya yi gaba don wuce wa ɗakin Baba. Cikin wani irin kuka ta yi azamar zagayawa gabansa ta soma faɗin
"Don girman Allah ka yi haƙuri, ka yi haƙuri ka rufa mini asiri. Kar ka zamo silar fita ta daga gidan nan. Kar ka zamo silar zamowa ta bazawara. Ka rufa mini asiri Muhammad don Allah." Ta faɗa hawaye na sakkowa a kan kuncinta. Shiru ya yi yana nazarin abubuwan da take faɗa, har kuma lokacin bai ce da ita ƙala ba. Don haka sai ta samu damar ci gaba da magana.
"Wallahi ba wani abun nake yi ba. Kwana biyu kowa ya damu a gidan nan saboda yadda yake fita da sassafe, ba kuma ya dawowa sai cikin dare. Shi ne nake so in ga wane ne ke sanya mini miji yana fita ba tare da ya gama uzururrukan da yake son yi a cikin gida ba. Duk gida an damu, shi ne na yi ƙundunbalar bincikawa don a samu mafita. Kuma ban ma kai ga duba komai ba, saboda ban saba ba. Za ma ka iya duba wayar. Ni dai burina ɗaya don Allah kar ka zamo silar zamowa ta bazawara."
Gajeren numfashi Muhammad ya sauke kafin ya buɗe bakinsa a karon farko ya ce
"Allah Ya kyauta." Daga haka ya haye saman. Sai a lokacin ta samu damar sauke ajiyar zuciya, don a ɗan zamanta cikin gidan ta fahimci wasu daga cikin halayensa. Duk da da farko ta yi tunanin ko sumumu-kasau ne, sai kuma ta fahimci yanayin yadda ta gan shi a fuska haka yake. Duk da haka, sai ta din ga takatsantsan da shi, saboda tun kafin ta shigo gidan aka gargaɗe ta a kan ta guje wa cutar da Muhammad ɗin idan dai har tana son zaman lafiya a gidan.
Sai da ya yi knocking a ƙofar ɗakin. Baba da bai riga ya shiga bedroom ɗinsa ba ya ce
"Shigo."
Da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga ɗakin hannunsa ɗauke da wayar Baban.
"Welcome my son." Baba ya faɗa bayan ya ƙaraso ya rungume ɗan nasa, idanunsa a lumshe cike da farincikin ganin sanyin idaniyar nasa.
"Baba." Ya faɗa bayan shi ma ya rungume shi. Ƙarasawa suka yi suka zauna a kan kujera, Baba na tambayar sa ya hanya.
"Here is your phone, you left it downstairs."
"Oh!" Baba ya faɗa cike da mamaki yana kallon wayar. Kafin ya ɗan ɗaga kafaɗarsa ya saka hannu ya karɓa.
"Mu je ka samu ka ci wani abu." Baba ya faɗa yana miƙewa. Ɗan yamutsa fuskarsa ya yi kafin ya ce
"No Baba, ba na jin yunwa."
"Mu je Turai ta dafa maka ko ma mene ne kake so." In ji Baba, ba tare da ya nuna ya ji abin da Muhammad ɗin ya faɗa ba.
"Baba please, kar a wahalar da ita." Cike da mamaki Baba ya kalle shi.
"A wahalar da ita?" Ya dakata a nan yana ci gaba da nazarin Muhammad ɗin, sai kuma ya ɗora da
"Ko dai akwai wani abu ne?" Girgiza kansa ya yi lokaci guda yana kai hannunsa kan tulin sumar kansa ya shafa ya ce
"Ko ɗaya Father." Ya kira shi da sunan da lokuta da dama yake kiran sa da shi. Sai a lokacin sannan Baba ya sauke ajiyar zuciya yana jinjina kai.
Kamar wanda aka jefo haka ya faɗo cikin ɗakin yana faɗin
"Ina Ammeey?"
Umman Ammeeyn da ke zaune kan kujera tana karatu ta kalli Daddy cike da mamaki. Fatanta ɗaya, Allah Ya sa ba laifi Ammeeyn ta yi ba, don ta san halin ɗiyar tafa in dai wajen fitina ne sai dai a shafa mata lafiya.
"Daddyn Ammeey lafiya?" Ta yi maganar bayan ta ajiye Al-Ƙur'anin hannunta lokaci guda tana miƙewa.
"Lafiya ƙalau, maza kira mini ita ta zo ta kai wa Muhammad abinci, yanzun nan ya shigo gidan." Wani sabon mamakin ne ya sake kashe ta a tsaye, don haka ta ce
"Abinci kuma Daddy.. Me ya.."
"Eh, abinci na ce.. Ko laifi ne hakan? Ko kuwa don ɗiyata ta kai wa ɗan yayana abinci laifi ne? Me kike nufi ne?" Ya yi maganar yana bin ta da kallon tuhuma.
"A'ah babu laifi ko kaɗan, amma bari na je na haɗa abincin idan ya so da kaina sai na kai masa." Wani kallo Daddy ya watsa mata kafin ya ja tsaki.
"Da ma ai ke za ki haɗa abincin, amma bari ki ji in faɗa miki Ammeey ita ce za ta kai masa abincin nan. Kar ki sake ki tambaye ni dalili, wannan shi ne abin da na ce."
Numfashi mai tsayi Umman ta ja kafin ta sauke, har ta soma takawa don zuwa kitchen sai ta kasa jurewa, don haka ta juya jiki a sukwane ta ce
"Ka yi haƙuri Daddyn Ammeey, amma don Allah idan ma akwai wani ƙuduri a ranka ka bar shi har Allah Ya yi ikonSa. Idan so kake Muhammad ya so Ammeey ba sai ka din ga cusa masa ita ba, har garin neman gira a rasa ido. Ka san kuma an ce matar cushe ba ta daraja. Don Allah ka taya ɗiyarka jan mutuncinta a matsayinta na 'ya mace."
Kamar wani ƙaramin yaro haka yake kallon Umman tun da ta soma magana, cike da mamaki. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ji ɓacin ran da ya soma ji na sake mamaye shi. Me matar nan ke nufi? Ya take neman saka masa ido ne a kan al'amuran rayuwarsa da ɗan'uwansa? Me ya sa take ƙoƙari wajen ganin ta zama shamaki a kan cikar burinsa? Ta san adadin shekarun da ya ɗauka yana jiran zuwan wannan lokaci? To ba ita ba, kaff cikin gidan nan bai ga wanda ya isa ya hana shi abin da ya yi niyya ba, ko da hakan na nufin sanadiyyar rugujewar farincikin ko ma wane ne, ciki kuma har da ɗiyar tasa.
Mhiz Innocent
08124818273
*♡☆BIYU BABU☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
YOTA Writers Ass..
Book 1
Pg 04
Ganin irin kallon da yake bin ta da shi ne ya sanya ta juyawa jikinta a matuƙar sanyaye ta wuce kitchen ɗin. Ta shafe wajen mintina goma, zuwa can ta fito hannunta ɗauke da flask guda biyu. Ta ƙaraso ta ajiye a hankali ba tare da ta ce komai ba ta soma ƙoƙarin juyawa.
"To za ki kira mini Ammeeyn ne ko kuwa?" Ji ta yi kamar ta share shi, sai kuma ta ga rashin dacewar hakan, don haka a sanyaye ta ce
"To." Daga haka ta wuce ɗakin Ammeeyn. Lokacin da ta shiga Ammeeyn bacci ya fara ɗaukar ta. Dole ta saka hannu ta shiga tashin ta.
"Umma don Allah bacci nake ji." Ta faɗa tana juya wa Umman baya.
"Maza ki tashi Daddynki na jiran ki." Ba ta san lokacin da ta buɗe idanunta ba.
"Daddy kuma?" Ta tambaya a mamakance tana kallon Umman.
"Yanzu da kika ji na kira Daddy ai ga shi kin tashi. To je ki gyara fuskarki ki wuce yana jiran ki a parlour." Ba don ta so ba, haka ta miƙe ta faɗa toilet, bayan wajen mintina biyu ta fito tana ɗan cuno baki kamar za ta fashe da kuka. Kasancewar abaya ce a jikinta ya sanya ta yafa mayafinta sannan suka fita tare da Umman.
"Ga abinci nan ki ɗauka ki kai wa yayanki Muhammad yana sashen Babanku."
"Daddy Yah Muhammad kuma?" Ta faɗa bayan ta buɗe manyan idanunta. Sai ya jinjina kai sannan ya ce
"Kwarai, ba na son jin wani abu daga bakinki. Ki ɗauka ki je ki kai masa." Ta san halin Daddyn sarai, ba ƙaramin aikinsa ba ne yanzu ya kai mata duka ba, don haka ta saka hannu ta ɗauki abincin tana ji kamar ta fasa ihu ta fice daga ɗakin. Tuni ƙwallar da ta taru a idanunta ta soma sauka a kan kuncinta. Sai tana tafiya tana tsayawa ta goge sai ta ci gaba da tafiya.
Da sallama ta shiga ɗakin cike da fatan babu kowa a ciki, ta wani ɓangaren ma ji take kamar ta je ta zubar da abincin a shara ta je ta cewa Daddyn ya cinye. Amma sanin halinsa zai iya bibiyar ba'asi ya sa ta yi watsi da abin da zuciyar tata take saƙa mata.
"Ahh Ammeey." Baba ya faɗa lokacin da idanunsa suka sauka a kan ɗiyar ƙanin nasa. Ganin Baba ya sanya ta sakin murmushi kana ta ƙarasa tana faɗin
"Na'am Baba, barka da wannan lokacin." Sai da ta ajiye abincin hannunta sannan ta ɗora da
"Da ma Daddy ne ya ce wai.. a kawo wa.. wai Yah Muhammad abinci." Ta ƙare maganar tana ɗan satar kallon inda yake tsaye yana latsa wayar hannunsa. Ko kaɗan ba za ka yi tunanin ya san da wanzuwar wata halittar a cikin ɗakin bayan Baba ba.
"Ma sha Allah. Yanzu kin san abin da za a yi?" In ji Baba. Sai ta girgiza kai a sakarce ba tare da ta ce komai ba.
"Taimaka ki yi serving nasa, bari na je na dawo." Cike da mamaki Muhammad ya ɗaga idanunsa ya kalli Baba jin abin da ya ce. Kafin a hankali ya mayar da idanunsa kan Ammeey, wannan abar ce za ta zuba masa abinci kuma ya ci? Wa ma ya sani ko ita ta dafa? To me ma ta iya da har za ta dafa? Idan ma ta zuba ɗin ta ya ya zai ci? Dududu yaushe ta daina fitsarin kwance? Ba da shi ba.
"Faaza." Ya faɗa yana kallon Baban da ke ƙoƙarin barin ɗakin.
"MuhammadAali." Baba ya faɗa bayan ya kafe ɗan nasa da ido.
"Baabaaa.." Ya ja ƙarshen sunan Baban idanunsa a runtse sosai. Bai jira Baban ya ce komai ba, don bai kira shi ne don ya amsa ba ya ɗora da faɗin
"Sunana Muhammad ne kawai ba Aali ba."
"Bari na je." Baba ya faɗa yana ficewa daga ɗakin fuskarsa ɗauke da murmushi. Yana son kasancewar wannan alaƙar, da gaske yana son Ammeey ƙwarai, kasancewar sunan mahaifiyarsa ta ci. Babban abin da Daddy ya yi masa wanda har abada ba zai taɓa mantawa ba, wato sanya wa ɗiyarsa sunan mahaifiyarsa, bayan ga sunan tasu mahaifiyar amma bai saka ba sai ta shi. Wannan na ɗaya daga cikin alfarmomin da aka taɓa yi masa a duniya wanda in dai yana da rai har abada ba zai taɓa mantawa ba.
Taɓe baki Ammeey ta yi, sai dai cikin basarwa don kar ya gan ta. Ita ba ta taɓa ganin mutumin da ba ya son nickname nasa ba sai shi. Ita kuwa yadda take ƙaunar Ammeey ai Allah kaɗai Ya sani. Sai shi don iyayi wai dole sai an kira shi da real name nasa. 'To ko ma dai mene ne, ya ci kansa' Ta faɗa a kan laɓɓanta tare da ƙarewa da sake taɓe baki.
Bai sake bi ta kan Baban ba, sai ya sauke idanunsa a ƙasa, daidai lokacin da Ammeeyn ke ƙoƙarin zuba masa abincin. Cikin ƙanƙanin lokaci ƙwaƙwalwarsa ta tafi tunanin me ya sa Baban ya kira shi da wannan sunan da ba kasafai ya fiya faɗansa ba? Kai a kaff gidan ma babu mai kiran sa da sunan sai mutanen waje. Su ma ɗin tun da suka fahimci ba ya son MuhammadAali, sai suke ragewa kai tsaye su kira shi da Muhammad ɗinsa, ko kuma su haɗa da sunan Baban nasa su kira shi Muhammad Abbas Shettima. Ko da yake ya san hakan na da nasaba da zuwan Ammeey, ya san tabbas ya yi hakan ne don ya ɓata masa rai ya bar shi salin alin ya fita. Amma kenan ya zaɓi farincikin Ammeeyn a kan shi shalelensa? Tunanin nasa ya katse lokacin da ya ga Ammeeyn na ci gaba da aikin da Baban ya saka ta
"Maza kwashe kayanki ki fita da su." Ya yi maganar a dake bayan ya ɗan ja da baya kaɗan. Kamar ba za ta iya cewa komai ba, sai kuma ta cije ta shanye tsoron da take ji ta buɗe baki da ƙyar cike da ƙarfin hali ta ce
"To ai Baba ne ya ce in zuba maka."
"Ni kuma na ce ba na so, kwashe kayanki ki je." Kamar wadda ke shirin fashewa da kuka ta ce
"Don Allah ka bari kar Baba ya ga ban yi abin da ya saka ni ba, idan ya so.." Cike da mamaki yake kallon yarinyar jin tana ta magana raɗau haka. Ya ɗauka za ta ƙarasa abin da ta fara faɗa, ga mamakinsa sai ya ji ta yi shiru. Abin da bai sani ba a karan kanta mamakin yadda ta tsaya tana ta yi masa bayani haka ta yi.
"If you speak again, you will regret it.. Kwashe kayanki ki fice." Kamar yadda ya buƙata ɗin kuwa shiru ta yi, ta shiga tattara abin da ta shigo da shi, bakin nan kamar zai faɗo saboda zumɓura shi da ta yi, sai dai duk da haka takatsantsan take yi don kar ya gan ta. Sai da ta gama haɗa komai sannan ta miƙe har ta juya ta fara tafiya ya ce
"Ammeey." Ba tare da ta ce komai ba ta juyo ba tare da ta kalle shi ba.
"Saura ki faɗa wa wani ban ci ba. Na ƙoshi ne, ki ba wa wani a waje. Kin ji ko?" Shiru ta yi tana gyara zaman flask ɗin hannunta. Cike da mamakin shirun da ta yi a karo na biyu ya sake cewa
"Kin ji ko?" Nan ma dai ta yi shiru tana gyara tsayuwarta.
"Ammeey.." Ya kira sunanta a tsawace. Tuni hawaye suka fara sintiri a kan kuncin Ameeyn, ta buɗe bakinta cikin kuka ta ce
"Cewa fa ka yi kar na sake magana." Iska ya fesar daga bakinsa yana jan gajeren tsaki. Wato duk inda yaro yake sai ya nuna yarintar tasa.
"Je ki." Ya faɗa kai tsaye. Da wani irin sauri ta fice daga ɗakin tana ɗauke hawayen da gefen kafaɗarta.
A ɗaya ɓangaren kuwa gabaɗaya yau ɗin ko da na minti ɗaya ne zuciyarta ta kasa sukuni da tunanin Khaleed. Duk wani motsi nata sai ya faɗo mata, ko da tana karyawa sai dai kawai ta dakata da cin abincin ta yi shiru tana tuna kalamansa, da kuma fuskarsa da ko da sau ɗaya ta kasa barin ƙwaƙwalwarta. A kwanaki biyun nan babu ranar da bai zo cikin mafarkinta ba. Ji take kamar ta jawo ranar Monday da Fa'iza ta ce mata ya ce zai zo su haɗu. Ko kusa ko alama ba ta yi musu ba, don kuwa ita kanta zuciyarta ta kwaɗaitu da son sake ganin fuskarsa, kunnuwanta kuma sun yi kewar muryarsa da a wajenta yanzu babu muryar da take son ji kamar ta.
Farouk ne ya kai ta makarantar kasancewar Abee ba ya garin gabaɗaya. Lokacin da aka kusa tashi tuni ta gama shirin ta na ficewa daga makarantar don haɗuwa da Khaleed. Duk da yadda zuciyarta ke bugawa, tana kuma jin wani irin tsoro da ya hana ta sukuni, amma ta ɓangare guda, ba ta tunanin za ta iya bijirewa haɗuwa da Khaleed ɗin, saboda yadda zuciyarta ke azalzalar ta da son ganin sa kamar mai jin ƙishirwa. Ji take kamar ana jan ta, ji take zuciyarta na mata wani irin zafi, har sai da ta kai ta fara tuhumar kanta. Shin me yake damun ta? Fa'iza ce ta yi ƙoƙarin kwantar mata da hankali tana ba ta baki a kan cewar babu abin da ba a iya yi a kan soyayya. Ko kuma da ta zauna ta fayyace mata abubuwan da take ji a kan Khaleed ɗin, buɗar bakinta sai cewa ta yi
"Wannan ita ake kira soyayya. Wallahi ƙawata ke ma kin shigo layin. Sai yanzu za ki san ke mace ce, sai yanzu za ki san me ake kira da rayuwa. Yanzu za ki more ƙuruciyarki." Ita dai Janan jin ta kawai take yi, amma wannan tsoron har lokacin bai fice mata ba. Anya kuwa idan ta yi haka ta yi wa Ummee, Abee har ma da Yah Farouk adalci? Duk irin tsayawar da suke yi a kanta wajen ganin ta zama wata, wadda ba ma su kaɗai ba har duniya za ta yi alfahari da ita? Sai dai cikin ƙanƙanin lokaci wani ɓangare na zuciyarta ya tunasar da ita tasirin abubuwan da take ji game da Khaleed ɗin da ta yi masa gani ɗaya. Shin a karon farko idan ba ta bi abin da zuciyarta ke so ba ta yi mata adalci? Don dai haɗuwa da shi ba wani abu ba? Tunanin nata ya katse lokacin da Fa'iza ta ce
"Ki yi da jiki Janan." Sai ta sauke ajiyar zuciya tana bin bayan Fa'izan. Wani abu da ya kusa kashe ta a mamaki shi ne yadda Fa'izan ta yi amfani da wayonta da dabara ta ɗauke hankalin maigadin makarantar tasu, har ita kuma Janan ɗin ta fice daga makarantar. Lokacin da ta tsinci kanta a ƙofar makarantar ba ta san lokacin da hawaye suka sauka a kan kuncinta ba. Sai dai daga zarar ta tuna laifin da take ƙoƙarin aikatawa, sai kuma ta ji wani ɓangare daga zuciyarta ya tunasar da ita Khaleed na can yana jiran ta.
A inda suka yi za su haɗu ta same shi. Yana zaune kan wata kujera hannunsa a kan ɗaya hannun yana ɗan bubbugawa lokaci zuwa lokaci, idanunsa na a lumshe. Kamar an ce masa ga ta nan ya buɗe idanunsa. Bai san lokacin da wata ajiyar zuciya ta ƙwace masa ba.
"My love." Ya faɗa yana jin wani irin sanyi na ratsa shi.
"Mu yi sauri zan koma makaranta kar a tashi." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce
"Ina wuni?"
Ɗan cuno bakinta gaba kaɗan ta yi lokaci guda murmushi na suɓucewa a kan kyakkyawar fuskarta ta ce
"To ina wuni?" Murmushi ya yi kafin ya ce
"Wa ya faɗa miki ko ba ki gaishe ni ba zan damu? Ai wannan ɗin aikina ne ranki ya daɗe." Sauke ajiyar zuciya ta yi tana yin ƙasa da kanta, don da gasken gaske kunya take ji, ba kuma ta san yadda za a yi ta iya kallon shi ba.
Sosai ya ci gaba da zayyana mata irin ɗimbin ƙaunar da yake yi mata, yana sake roƙon ta a kan kar ta guje shi don bai san halin da zai tsinci kansa a ciki ba. Daidai lokacin ya kara wayarsa da aka kira a kunne bayan ya ɗauki uzuri daga wajen abar ƙaunar tasa. Jinjina masa kai kawai ta yi tana ci gaba da wasa da hannunta. A hankali ta yi ƙoƙarin ɗaga idanunta ta saci kallon sa, ko da hakan zai sa ta samu wani sabon hoton da zuciyarta za ta din ga tunasar da ita shi a duk lokacin da ya faɗo mata. Daidai lokacin da ya ɗaga idanunsa ya kalle ta, idanunsu suka faɗa cikin na juna. Da sauri ta yi ƙasa da nata tana gyara zamanta. Ya yi murmushi yana jin lallai tabbas zai yi nasara a kan Janan ɗin.
Sun shafe fiye da rabin awa, har sai da ya rage saura mintina 15 a tashi sannan ta miƙe ta ce
"Zan koma makaranta."
"Yanzu tafiya za ki yi ki bar ni?" Ya yi maganar kamar wani ƙaramin yaro. Ita wlh duk sai ya ba ta kunya, ba dai ta ce komai ba. Sai ya miƙe tsaye yana faɗin
"Mu je in taka miki." Da sauri ta shiga girgiza kai kafin ta ce
"A'ah ni dai don Allah ka zauna. Bari na tafi."
"Ki ce kina so na don Allah." Ya faɗa a marairaice idanunsa duka zube a kanta. Sai ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe kyawawan idanunta. Zuciyarta kamar me har lokacin ba ta daina bugu ba.
"Please." Ya sake faɗa a marairaicen dai. Duk wata gaɓa ta jikinta a karan kanta take ji ta amince da soyayyar Khaleed, tsokar kuwa da ke sarrafa tunaninta tuni ta ci gaba da harbawa kamar za ta baro ƙirjinta. Ba ta san lokacin da ta furta
"Ina son ka." ba. Daga haka a guje ta fice daga wajen cike da wata irin matsananciyar kunya da kuma tsananin mamakin kanta da take ji. Khaleed ji ya yi kamar an ɗauke shi an tsoma shi a aljanna saboda wani irin farinciki da ya ji.
"Yessss!!" Shi ne abin da ya faɗa yana yin amfani da hannunsa wajen nuni da abin da ya faɗa ɗin, fuskarsa annuri kamar zai yi magana.
Cikin sa'a kuma tana komawa ana tashi. A ƙofar makarantar ta jira zuwan Yah Farouk saboda gudun samun matsala. Ai kuwa ko mintina biyu ba a yi ba sai ga shi ya zo.
"A'ah Shalele yau kuma a nan?" Ya yi maganar yana kallon ta lokacin da take ƙoƙarin zama a mazaunin mai zaman banza.
"Eh fa, na ƙagu in koma gida."
"Gaskiya ne. To ya makarantar?" Ba tare da ta tsammata ba sai ta ji faɗuwar gaba ta ziyarce ta, ta yi ƙoƙarin basarwa lokacin da take faɗin
"Lafiya ƙalau."
Daidai lokacin wayarsa ta soma ringing. Ya kalli fuskar wayar sannan ya ajiye ta ya tayar da motarsa. Ba su yi nisa ba wani kiran ya sake shigowa. Janan ta kalli yayan nata ganin bai nuna ko alamar ya gani ba, ta ce
"Yah Farouk.. ana kiran ka fa." Ta yi maganar tana ɗan leƙa cikin wayar.
"Na gani, yaushe Abee ma ya ce zai dawo?" Ya yi maganar lokaci guda.
"Kai Yah Farouk ko dai budurwarka ce ke kira." Ta yi maganar tana nuna shi fuskarta ɗauke da murmushi, irin na gano ka ɗin nan. Cike da mamaki Farouk ya juya yana kallon Janan ɗin jin abin da ta faɗa. 'Budurwa' ya maimaita a kan laɓɓansa. Ganin kallon ta da ya yi ya mayar da kansa kan titi ya sanya ta saurin basarwa ta ce
"To yi haƙuri." Ta ƙare tana kamewa a kan kujera. Sake kallon ta ya yi, ba tare da ya ce komai ba ya ɗan lumshe idanunsa kana ya sake mayar da hankalinsa kan titi. A nutse ya ɗan girgiza kai lokaci guda fuskarsa ɗauke da murmushi, har kuma lokacin bai ce komai ba.
Har wajen ƙarfe 7 na daren ranar Ummee ba ta dawo ba, kasancewar tana da program ɗin da za ta gabatar a babbar gidan radion da take aiki. Abee kuma ba ya garin saboda wani aiki da ya sa ya bar garin a jiya. Ya yin da Yah Farouk aka yi masa kiran gaggawa a wajen aikinsu. Sai ya zamana ita ɗaya ce a gidan. Duk da kasancewar ta matsoraciya, wanda hakan ya sa Ummee ba kasafai ta fiya son barin ta ita ɗaya a gida ba, sai dai idan Abee ko kuma Farouk yana nan. Amma a hankali a hankali dole ta fara sabawa, tun da ɗabi'ar aikin Ummeen tata haka yake. Kwata-kwata yau ɗin ma gabaɗaya sai ba ta ji wani tsoro ba, saboda yadda hirar da suka yi da Khaleed ke ta dawo mata. Wani irin farinciki take ji, murmushi ya ƙi barin kyakykyawar fuskarta. Kai daga ƙarshe ma dai sai ta tafi ɗakinta kai tsaye ta haye kan gado. Ba ta damu da zuwa ta kulle ƙofar gidan ba, tun da ta san dab Ummee take da dawowa. Ta cire glass ɗinta ta ajiye shi sannan ta kwanta ta lumshe idanunta. Ta san a irin wannan yanayin, tunanin Khaleed ɗin zai fi yi mata daɗi. Don haka ta ɗora kanta a kan hannayenta biyu tana sake hasaso fuskar Khaleed ɗin lokacin da yake danna waya. Ta shafe wajen rabin awa, ba tare da ta tsammata ba bacci ya yi awon gaba da ita.
Can cikin bacci, kamar daga sama ta soma jin motsi, kamar idan ba ta yi ƙarya ba, hannu take ji a kan cinyarta. Cikin tsananin tsoro ta buɗe idanunta da saboda daɗewar da suka yi a rufe ya sa ganin nata ya sake yin rauni. Da ma ya lafiyar kura bare ta yi zawo? Cikin azama ta miƙa hannunta gefen gado tana laluben glass ɗinta don ta samu ta ga me ke faruwa a cikin ɗakin. Don
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 24