Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ke yawo a social media?" Shi ne abin da aka faɗa daga can ɓangaren. Cike da mamaki Baba ya ce "Social media kuma? Me ya faru?" Ya yi tambayar da yake jiran amsarta. Sai dai cikin ƙanƙanin lokaci ya ji amsar tambayar da yake nema ya tafi nasa wajen, saboda ido biyu da ya yi da 'yan'uwansa duk su biyun, matansu, har ma da matarsa Hajiya Turai a tsaye kamar da ma jiran sa suke yi. Kawai sai ya ji faɗuwar gaba ta ziyarce shi. Wadda ta sanya shi saurin dafe ƙirjinsa yana jingina da motarsa. "Baba." MuhammadAali ya kira sunansa da ƙarfi yana riƙo shi. "Kwantar da hankalinka, babu abin da ya faru." Ya faɗa har lokacin idanunsa a ɗan lumshe. "Baba ba ka da lafiya ne da ma ban sani ba?" Muhammad ya faɗa zuciyarsa na ɗan harbawa. Sai ya girgiza kansa sannan ya ce "Taka mu je. Ina ji dai a jikina babu lafiya, amma ba lafiya ta jiki ba." Ya yi maganar idanunsa a kan mutanen gidan da duk shi suke kalla. Sai a lokacin sannan hankalin Muhammad ya je wajen. Su kuma fa? Me suke yi a nan? Wani abu ya faru ne da ba su sani ba? Ya dinga jefe wa kansa tambayar, lokacin da suke takawa zuwa inda suke. "Sannu da zuwa Yaya." Abban Al-ameen ya faɗa, ganin yadda tashin hankali ya gama bayyana a kan fuskar Baba, shi kuma ba ya son wani abu ya ɗaga masa hankali, saboda lafiyarsa. "Me yake faruwa ne uhmm?" Baba ya yi tambayar lokacin da yake jin wayarsa na ci gaba da ruri, amma bai bi ta kanta ba, ko ma dai mene ne ya ji shi a bakin mutanen gidan nasu. Shiru ne ya wanzu na tsawon lokaci, har zuwa lokacin da Baba ya ce "Ku sanar da ni mana. Ina Ammeeyna? Ina kuma Al-ameen?" Ya yi tambayar a dame. "Babu abin da ya faru da Ammeeynka ko Al-ameen Yaya." Daddyn Ammeeyn ya faɗa. Sai ya sauke ajiyar zuciya kana ya ce "Idan haka ne mene ne ya faru?" Sai da Daddy ya sauke ajiyar zuciya, shi kansa yana tunanin ta ina zai fara sannan ya ce "Wani mummunan abu ke ta yawo a kafafen sada zumunta Yaya. Maimuna (tsohuwar matar Baba ta biyu da suka rabu da ita), ita ce aka ce ta bayyana dalilin fitar ta daga gidanka. Hakan ya faru ne biyo bayan wani shiri da ake gabatarwa a gidan radio a kan mutanen da suka sha gwagwarmayar rayuwa. Ta bayyana sunanka a matsayin wanda bai san darajar 'ya mace ba. Wanda yake aurar mace don biyan buƙatar sa. Sannan ta ce ka sake ta ne, sanadiyyar ɗanka da ya neme ta a gado, ita kuma ta ƙi ba shi haɗin kai. Bayan hakan ya faru, ta nemi da a ƙwatar mata haƙƙinta ko ta kai ƙara, ka nuna idan dai har tana son ci gaba da zama a gidanka to sai dai idan za ta rufa wa ɗanka asiri. Ita kuma ta ƙi amincewa shi ne dalilin rabuwar ku. Ta kuma yi niyyar kai ka ƙara, haƙarta ba ta cimma ruwa ba, saboda amfani da ka yi da kuɗi wajen watsa mata ƙasa a ido. Aka yi fatali da kokenta saboda kana da kuɗi. Wai cikin ikon Allah sai ga shi Allah Ya kawo mata mafita, wadda za ta bayyana kokenta, mutane su taya ta kuka da alawadai da halayenka, ta wannan sabon shirin da aka fara gabatarwa a radio." Daga nan Daddy ya yi shiru, saboda lura da yanayin Baba da ya yi. Tuni ya runtse idanunsa yana jin waɗannan munanan kalaman da ake jifan sa da su shi da shalelensa. "Yaya zauna don Allah." Abba ya faɗa yana ƙoƙarin taimaka wa Baban. Bai musa ba, don shi kansa a jikinsa yake ji kamar yana ƙoƙarin faɗuwa ne. Don haka ya zauna da taimakon Abba. Kallon sa kawai Muhammad yake yi yana jin yadda zuciyarsa ke wani irin bugawa. Kawai sai ya zube a kan ƙafafunsa, hannayensa ɗore a kan guiwar Baba ya ce "Baba Allah ba Zai taɓa bari na ba idan dai har na kasance na aikata abin da ake ƙoƙarin laƙaba mini. Baba Allah Ya wadaran halayena idan dai har na aikata wannan mummunan abu, Baba Allah kar Ya ba ni abin da nake nema idan dai har na aikata haka. Baba." Shi ne abin da MuhammadAali ke faɗa cikin tsananin tashin hankalin da zai iya cewa tun da ya zo duniya bai taɓa jin irin sa ba. Duk kuwa da akwai abubuwa masu yawa da suka faru cikin rayuwarsa, amma yadda yake jin wannan ɗin kamar ya fi kowanne. Yanayin da yake ganin Baba ciki kaɗai ya ishe shi tashin hankali. Gabaɗaya ya ma rasa yadda zai yi, ya ma rasa waɗanne kalamai zai yi amfani da su wajen fahimtar da Baban bai aikata laifin da ake ƙoƙarin ɗora masa ba. "Ka ga Muhammad, ka bar shi ya ji da abin da ke damun sa, idan ma dai ka aikata ɗin ai yunƙuri ne ka yi, ba ka kai ga aikatawa ba. Kawai abin da za a yi sai ka san yadda za ka kare kanka a wajen jama'a." Daddy ya faɗa a fusace yana kallon Muhammad ɗin. A wani irin fusace Muhammad ɗin ya miƙe, jin waɗannan munanan kalaman da Daddyn ke jifan sa da su. Har bai san lokacin da ya ɗaga hannunsa ba kamar zai  kai masa duka ba. "Muhammad!" Baba ya faɗa cikin ɗaga murya. Abin da ya janyo Muhammad ɗin ya dakata kenan yana kallon Daddyn yana fidda wani irin huci kamar mayunwacin zaki. Daddy ƙanin mahaifinsa ne, amma ko kaɗan, ba ya ƙaunar sa, kamar yadda sau da dama yakan fahimci shi ma ba wani ƙaunar sa yake yi ba. Sai dai wani lokacin idan ya yi wani abu yakan ba shi mamaki. "Ai da ka bar shi ya dake ni, ka ga sai ya nuna maka irin tarbiyyar da yake da ita." Runtse idanunsa Baba ya sake yi yana jin zafin kalaman Daddyn matuƙa. "Baba." Muhammad ya faɗa yana girgiza kansa bayan ya sake zubewa a kan ƙafarsa. Ya rasa yadda zai yi, ya kuma rasa me zai aikata ya ji daɗi. "Yanzu Aminu da kanka kake zargin ɗana da aikata wannan mummunan abun? Ko da na san Muhammad ba ya ji, amma ina da tabbacin ba zai aikata hakan ba. Na san halin ɗana, na san abin da zai iya da wanda ba zai iya ba. Ina da tabbacin ƙage ne aka yi masa. Muhammad ba zai taɓa aikata haka ba, ba zai yi ba. Ban san ƙin nasa da kake yi har ya kai haka ba, to ka sani, yadda ka yarda Muhammad ka iya yin abin da aka faɗa, ya fi yi mini zafi a kan maganganun da aka faɗa a kaina da shi kansa. Ka ba ni mamaki ƙwarai Aminu. Na ɗauka duk wani abu da ya shafe ni mai muhimmanci ne a wajenka? Abin yarda kuma a wajenka?" Ya ƙare maganar a sanyaye yana kallon Daddy. Wani irin sanyi jikin Daddy ya yi, sanyin kuma ba na komai ba sai don yadda ya ji bakinsa na ƙoƙarin jawo masa asara. Me ya sa ne bakinsa kullum ba shi da linzami? Wai ashe Baba har ya san ba ya wani son Muhammad ɗin? Shi kuwa wannan wanne irin rashin rabo ne ke jan sa? To idan ya ci gaba da haka, ta yaya Baban zai amince Muhammad ɗin ya auri Ammeey? Mhiz Innocent 08124818273 *♡☆BIYU BABU☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) YOTA Writers Ass.. Book 1 Pg 17 Sai da ya gyara tsayuwarsa sannan ya ce "Ka yi haƙuri Yaya, raina ne a ɓace har ya kai ga na yi wannan furucin, amma ka yi haƙuri, ba ina nufin abin da na faɗa ba. Kuma ni ma babu yadda za a yi na tuhumi ɗanka da wannan mummunan abu, don na san tarbiyyar da ka yi masa. Ka yi haƙuri." Girgiza kai kawai Baba ya yi ba tare da ya ce komai ba. Haka ma duk wanda ke wajen bai sake cewa komai ba, har zuwa lokacin da MuhammadAali ya ja ƙafarsa da wani irin sauri ya shige sashensu. Bin sa da kallo Baban ya yi, yana jin wani irin tausayin ɗan nasa na kama shi. Shi ba shi kansa yake tausayi ba, duk kuwa da irin munanan kalaman da aka faɗa a kansa, ya fi jin ɗan nasa, musamman da ya kasance mai sanya abubuwa a ransa. "Yallaɓai mu je ka samu ka huta ko?" Hajiya Turai ta faɗa bayan ta ƙarasa inda Baban yake. Shiru ya yi na tsawon sakanni kafin zuwa can ya ce "Ina son kasancewa da ɗana a halin yanzu. Can zan nufa." Ya yi maganar yana miƙewa. Da sauri Daddy ya ce "Za dai ka iya ko?" Ya yi maganar bayan ya yi saurin ƙarasawa inda Baban yake. Jinjina kansa Baba ya yi kana ya ce "Eh, kowa ya koma ciki don Allah. Ganin ku a hakan ka sake ɗaga mini hankali." Babu wanda ya musa, duk sai suka juya zuwa sashensu. Kai tsaye Baba sashensu Muhammad ɗin ya wuce. A parlour ya hango shi zaune, hannunsa duka biyun lume cikin sumar kansa da lokaci guda ta hargitse. A nutse Baba ya ƙarasa kusa da shi ya nemi waje ya zauna. Tsayin lokaci bai ce komai ba, sai zuwa can sannan ya ce "Muhammad." Da sauri ya buɗe idanunsa don ko kaɗan bai ji shigowar Baban ba. Sai ya runtse idanunsa da suka matuƙar sauya kala ya ce "Faaza." "Damuwar ta mene ne?" Baba ya yi maganar a nutse, cike da son ba wa ɗan nasa ƙarfin guiwa. Hakan kuwa ya yi tasiri a wajen Muhammad ɗin, sai ya gyara zama ya ce "Baba hankalina ba zai taɓa kwanciya ba bayan muna zaune ana can ana mana wani irin kallo. Baba me ya sa matar da ka rabu da ita za ta yi mana haka? Me ka taɓa yi mata na rashin kirki da har za ta zaɓi zubar maka da mutunci a idon duniya? Baba ka yarda abubuwan da ta faɗa duk ƙarya ne? Ba zan taɓa iya aikata haka a kan kowacce mace ba, ballantana kuma wadda ka ajiye a matsayin matarka. Baba ba ka ji irin munanan kalaman da ta yi amfani da su a kanka ba? Zuciyata ba ta da wannan ƙwarin, ba zan iya jurewa ba." "Ya isa haka Muhammad. Ba na buƙatar sake jin kalaman nan daga bakinka. Kana tunanin zan amince ne da abin da na san ba za ka aikata ba? Ko kaɗan hakan bai yi tasiri a wajena ba, ballantana har ta kai ga na yi zargin wani abu. Sharri ne kawai irin na Maimuna. Allah ne kuma kaɗai Ya san dalilinta na yin hakan." Shiru Muhammad ya yi yana nazarin kalaman Baban, tabbas Allah kaɗai Ya san dalilinta na yin hakan, sai dai idan har ya yi bincike zai gano dalili. Zai kuma gano ko ma mene ne yake faruwa cikin ruwan sanyi. Don haka ya ɗauki wannan alƙawarin, sai ya binciko tun tali-talin yadda ma aka yi hakan ya fita a duniya, da ita kanta Maimunan. Sai kuma ta karɓi kashinta a hannu, ta girbi abin da ta shuka, ta kuma yi nadamar abin da ta aikata. Ya san halin Baba sarai, zai iya cewa ya haƙura ba sai an hukunta ta ba, shi ya sa ma ko kaɗan bai yi masa maganar zai saka a yi masa bincike ba. A ɗaya ɓangaren kuwa, ya shafe fiye da awa ɗaya cikin ɗakin bayan fitar Janan, zuciyarsa fall cike da saƙe-saƙe iri-iri. Kamar wanda aka tsikara ya miƙe, sai da ya faɗa toilet ya wanke fuskarsa sannan ya fice zuwa ɗakin Ummee. Har lokacin tana zaune inda ya bar ta, kamar dai ɗazun, yanzu ma waya ce a hannunta tana dannawa. A nutse ya ƙarasa ya nemi waje ya zauna. A hankali Ummee ta kalle shi cikin son ta nazarce shi ta ce "Farouk." Sai da ya ɗan ja numfashi gajere sannan ya ce "Na'am Ummee." "Me yake damun ka? Ba ka da lafiya ne?" Ta yi tambayar har lokacin tana kallon sa. Sai ya yi azamar wanzar da murmushi a kan fuskarsa sannan ya ce "A'ah Ummee, me kika gani?" Ya yi tambayar, sai dai tun kafin Ummeen ta kai ga cewa komai ya ɗora da faɗin "Ummee ya ake ciki? Ba ki sanar da ni abin da ya faru ba." Wannan tambayar da ya yi mata yanzu, ita ta yi nasarar danne wadda ya fara yi mata a farko. Don da ma ita ce ta shigar da ita yanayin da take ciki a yanzu. Sai ta ja numfashi kafin ta yi shiru na tsawon sakanni, sai dai har lokacin Farouk bai sake cewa komai ba, don ya san tana shirin cewa wani abu ne. "Farouk akwai matsala kamar yadda na faɗa. Shin ba ka hau social media ka ga abin da ke faruwa ba?" Da mamaki yake ci gaba da kallon ta, sai kuma can ya ce "Na hau Ummee, amma a kan me kike magana?" "Alhaji Abbas Shettima da ɗansa." Ta ba shi amsa kai tsaye. Shiru ya yi kamar ba shi da abin cewa, sai can ya ce "Na gani Ummee.. Amma abin da na kasa ganewa, mene ne haɗinki da abin da ke ta yawo? Mene ne ya saka kuma kika damu?" Lumshe idanunta Ummee ta yi tana jin har ba ta so ta yi magana a kan abin da ya farun. Sai dai babu yadda ta iya, don haka ta ce "Komai ya faru ne ta sanadiyyata." A'ah, mamaki fa ya kusa kashe Farouk a zaune, ta yadda har ta kai ga ya kasa furta ko uffan ne. Ita ma Ummeen ba jira take ya ce wani abu ba, hakan ne ya sanya ta ci gaba da faɗin "Idan ba ka manta ba akwai sabon shirin da na sanar da ku zan fara gabatarwa. Shiri ne wanda ake yin hira da mutanen da suka sha gwagwarmayar rayuwa. Wata mata mai suna Maimuna ta zo da niyyar sanar da labarin rayuwarta. Ban amince ta fara bayarwa ba har sai da na yi bincike sosai, kamar yadda muka saba kafin soma ɗora kowanne shiri. Tiryan-tiryan ta soma bayar da labarin, wanda cikin ƙanƙanin lokaci hankalin jama'a ya komo kan labarin da ma shirin gabaɗaya. Kasancewarsa sabon shiri, wannan labarin ya jawo mana mutane da dama fiye da tunanin mai tunani. Tun da aka zo wani bigire, ta soma ƙoƙarin kama suna, wanda a ƙa'idar shirin ba a ambatar sunan ko ma wane ne da ya fito cikin labarin. Sai dai ba ta daddara ba, akwai lokacin da na ce mata za a daina ɗora shirin in dai har tana ba mu matsala. Don sau da dama sai dai mu datse wajen mu ɗora. A karo na ƙarshe har ta soma ambatar sunan Alhaji Shettiman, wannan dalilin ne ya saka aka katse shirin ma gabaɗaya. Sai dai ba mu sani ba, ashe mu ba mafita muka nema ba. Ɗimbin mutanen da ke saurarar shirin tuni suka soma ƙalubalantar mu. Daga ƙarshe dai muka sanar da su an cire labarin matar, ba za a ci gaba ba saboda wani dalili. Shirin ma kansa an dakata da yin sa na ɗan wani lokaci saboda wasu gyare-gyare da muka yi. Ba mu taɓa sanin ashe mu ba mafita muka nema ba, sai da muka samu labarin cewar masu sauraron mu sun nemo matar nan, sun kuma yi mata tambayoyi a kan labarin, inda ta ƙarashe musu shi har zuwa ƙarshe. Ta kuma ambaci sunan Alhaji Abbas Shettima a matsayin wanda ta aura ɗin, da kuma ɗansa Muhammad Abbas Shettima wanda ta ce ya neme ta da fasiƙanci. Abin da ake ta kira na ana sanar mini kenan, abin da ya dugunzuma mini hankali, saboda duk abin da ya faru ya faru ne sanadiyyata Farouk. Na yi iya bincikena don na ga ta inda wannan labarin ya soma fita na kasa ganewa. Kuma ba ka ga yadda mutane ke ta tagging ɗina a comment section ba. Na rasa yadda zan yi, na rasa sukuni. Gabaɗaya a tsorace nake, me ya sa matar nan za ta yi mana haka? Mene ne fa'idarta na yin hakan? Ta yaya zan zame kaina daga cikin wannan al'amarin Farouk?" Wai!! Wannan shi ake kira tashin hankali ba a saka masa rana. Farouk ya raya hakan cikin zuciyarsa. Sosai maganganun Ummeen ke ci gaba da yi masa yawo a cikin kwanya. Idan dai har ya fahimta da kyau, dole ne Ummeen ta shiga cikin tsaka mai wuya, tun da kamar yadda ta faɗa, komai ya faru ne sanadiyyar ta. To amma abin da bai gane ba, me ya sa tuntuni matar ba ta kai ƙara ba? Me ya sa ba ta yi amfani da wannan damar ba tun lokacin da abin ya faru ta sanar wa da al'umma ba sai yanzu da Ummee ta fara shirin nan? "Ummee anya kuwa babu wani abu a ƙarƙashin wannan labarin? Sai na ji kawai hankalina bai kwanta da labarin ba. Alhaji Abbas Shettima fa, mutum mai matuƙar kamala da sanin yakamata. Idan za ki iya tunawa, mun haɗu da shi a asibiti lokacin da ba mu ga Janan ba. Ba na tunanin zai iya aikata haka ba, domin ko kusa ko alama yanayinsa bai nuna hakan ba." Ajiyar zuciya Ummee ta sauke sannan ta ce "Ban taɓa tunanin a kan wannan babban mutumin za ta bayar da labarinta ba. A iya binciken da na yi, na ɗauka kawai mutum ne dai kamar kowa, kuma mara imani. Sai da tafiya ta yi tafiya sannan takamaimai ma muka gano a kan wanda take bayar da labarin. A lokacin mun yi niyyar daina saka labarin nata gabaɗaya, sai dai manyanmu sun yi tunanin irin asarar da za su yi, saboda yadda labarin nata ya samu karɓuwa, wannan ne dalilin da ya saka aka ci gaba da sakawa sai dai cike da takatsantsan, to amma ka ga abin da ya faru. Gabaɗaya binciken da nake yi ma yana ƙoƙarin ya tashi a banza, saboda har yanzun ban wani samu cikakken abin riƙa ba. Babu kuma abin da ya fi damu na, irin tagging ɗina da ake ci gaba da yi." Dogon numfashi Farouk ya sauke bayan gama jin abin da Ummeen ta faɗa. Ya ma rasa me zai ce, ya kuma rasa ta ina zai fara. A karo na barkatai wayarsa ta sake yin ruri. Ya ɗauke kansa idanunsa a lumshe, duk da yadda yake ji a ransa kamar ya ɗaga wayar, sai dai ya fi yarda da wani ɓangare na zuciyarsa da ke hana shi ɗaukar wayar. Amma a wannan karon, cikin ƙanƙanin lokaci ya ji hankalinsa ya tafi kan ɗaukar wayar. Don haka ya ɗauki wayar a hannunsa ya kalli mai kiran nasa, bai tsaya sake yin wani dogon tunani ba ya ɗaga yana kara wa a kunnensa. "Ranka ya daɗe tun ɗazu nake kiran ka babu amsa. Ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya." Sai da Baba ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Alhamdulillah." "Yallaɓai ba ka ga abin da yake ta yawo a kafar sada zumunta ba? Lallai yana da kyau a yi hira da kai ka ƙaryata kalaman wannan makirar matar. Idan kuma hakan ba zai yiwu ba, ka ba mu dama mu saka a kama ta, a kuma maka ta a kotu yadda za ta girbi abin da ta shuka. Wanne irin hauka ne wannan?" Murmushi Baba ya yi kafin ya sauke gajeren numfashi ya ce "Au har sai na yi bayani sannan za a fahimci wane ne ni? Babu wanda zan je in yi hira da shi, muna nan da kai in sha Allah, Allah Zai yi ikonSa. Ba zan ɗaga hankalina ba, duk da kusan hakan ba mai yiyuwa ba ne, amma zan yi iya ƙoƙarina. Ba na buƙatar a miƙa ta ko'ina, ko kuma a ce sai na fito na yi wa duniya bayanin abin da ya faru." Shiru kawai MuhammadAali da ya shigo ɗakin ya yi lokacin da ya gama jin maganganun Baban. Shi da ma ya san wane ne mahaifinsa. Ya san abin da zai yi da kuma wanda ba zai yi ba, ya san da ma abin da zai faru kenan, ko kuma me zai faru babu lallai Baban ya yi magana. To shi kam ba zai zauna ba, sai inda ƙarfinsa ya ƙare. Ba zai bari a ci gaba da yi wa mahaifinsa kallon mutumin banza ba, ba kuma zai bar ta ta ci bulus ba, dole ne ta girbi abin da ta shuka. Tunanin nasa ya katse lokacin da wayarsa ta soma ruri. Hakan ne ya sanya shi juyawa tun kafin ma Baban ya gan shi ballantana ya yi masa wata magana a kan abin da ya faru. Cikin tsananin mamaki yake kallon number da ke yawo a kan wayar. Zai iya cewa ya kai watanni da goge number, amma saboda yawan kiran number da yake yi, da kuma ake yi masa a wancan lokacin ya sanya ya haddace number tass a kansa. Ko kuma daga bacci ya tashi tabbas zai shaida number ɗin. Sai dai kuma gabaɗaya kansa ya kulle, shin mene ne dalilin kiran? Ya aka yi mamallakin number ɗin ke kiran sa a irin wannan lokacin? Me za a ce masa? Mene ne kuma sauran alaƙar sa da mamallakin number ɗin? A yi haƙuri da wannan, ba na cikin yanayi mai daɗi da zan iya typing da yawa. In sha Allah gobe za mu haɗe. Mhiz Innocent 08124818273 *♡☆BIYU BABU☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) YOTA Writers Ass.. Book 1 Pg 18 Sai da ya fita daga ɗakin sannan ya soma ƙoƙarin ɗaga wayar. Don da farko bai yi niyyar ɗagawa ba ma, amma zai so ya ji ko mene ne dalilin kiran nasa. "Muhammad." Shi ne abin da aka faɗa daga can ɓangaren bayan ya ɗaga wayar. Numfashi ya ɗan fesar kaɗan daga bakinsa, ba tare da ya amsa kiran sunansa da aka yi ba ya ce "Ina jin ka." "Sai ka ce waɗanda ke shirin yin dambe?" Daga can ɓangaren aka sake faɗa. Runtse idanunsa Muhammad ya yi, saboda yadda lokaci guda ya ji ransa ya soma ɓaci, don haka ya ɗan dakata daga tafiyar da yake yi kana ya ce "Ka faɗi dalilin kiran nan, ina da abubuwan yi da yawa." Murmushi mutumin ya yi kafin ya sauke numfashi ya ce "Ko dai ba ka gane mai magana ba?" A fusace Muhammad ya ce "Waye kai ban da wanda ya yi ƙoƙarin shiga tsakani na da mahaifina? Akwai wani abu da zan sanar da kai wanda zai sa ka gane ina sane da wanda nake yin waya?" A wannan karon ma murmushi ya yi, don sosai ya fahimci Muhammad ɗin na cikin fushi ne har lokacin. "Wato na lura har yanzu Muhammad fushi kake yi da mu. To mene ne abin fushi da mu? Ba mu ya kamata mu yi fushi da kai ba, mu ɗin da ka rabu da mu rana tsaka duk da tsayin shekarun da muka ɗauka muna aiki tare? Saƙo ba aike ba, ni da kaina na kira ka. Na ga duk abubuwan da suka faru a kan kai da mahaifinka, me zai hana ka dawo ka sake haɗewa da mu don mu yi maganin abun?" Ɗan jujjuyar da kansa Muhammad ya shiga yi a fusace. Da gaske wannan maganar ke fitowa daga bakin Ogan, ko ko dai ya manta wane ne Muhammad. "Kar.. ka sake kira na." Ya yi maganar cike da kashedi ga wanda yake yi wa magana. Daga haka ya katse wayar kai tsaye ya jefa ta cikin aljihunsa ya ci gaba da tafiya ransa a matuƙar ɓace. A ɓangaren Ummee kuwa, kwana biyu da faruwar wannan abu ba ta je wajen aiki ba. Duk kuwa da irin kiran da ake ta yi mata a kan rashin zuwan nata. Sai dai tana ganin kamar za ta haƙura ne da shirin ko gidan radion, kai ko aikin ma gabaɗaya, a kan dai ta zamo sanadiyyar ɓata wa wani bawan suna, ko kuma ita kanta sunanta ya ɓaci. Farouk ma dai ya goyi bayanta, don shi kansa bayanin da ta yi masa ya gamsar da shi. To jiran dawowar Abee da ba ya garin suke yi, don su sanar da shi, ko dai ta ajiye aikin, ko kuma ta canja wajen aiki. Amma idan ma dai za

Chapter 13 of 24