Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
faɗa ɗin ya ɗan yi masa ɗaci. Amma tun da shi kansa ya san idan ya ce ba ya son kuɗi ƙarya yake yi, kawai dai yana kama kansa ne a waje da dama, sai kawai ya basar. A cikin kwanaki biyu, aka nemo wa Yayar hoton Janan, ta hanyar wata da ta haɗa hannu da ita, bayan Nafisa ta samo musu number ɗin Ummee da ke cikin wayar Adam. Wannan ya saka aikin nasu ya zo da sauƙi. Saboda haka kai tsaye bayan an kawo mata hoton, ta damƙa wa Al-ameen shi babu ɓata lokaci. Shiru ya yi yana kallon hoton yarinyar da alama an ɗauke shi ne ba tare da ta sani ba, ba ya iya ganin fuskarta sosai, amma kuma ko ta gefe ya kalle ta zai iya shaida ta. Shiru ya yi na tsawon sakanni yana saƙe-saƙe cikin zuciyarsa kafin ya yi murmushi. Wato yanzu arziƙinsa ya dogara ne da wannan halittar? Ya tambayi kansa. Cikin ƙanƙani lokaci ya lalubowa kansa amsar tambayar, wato "Eh." Tun da dai duk wani abu da yake ƙoƙarin samu yana tare da yarinyar, tun da sai ya yi abin da suke buƙata a kan yarinyar sannan za a ba shi kuɗin. Kuɗin da aka ce za a iya ba shi cheque ya rubuta iya abin da yake buƙata. Lallai shi kam yana cikin alkairi. Shi da ma gabaɗaya ma ya gaji da zama ƙarƙashin Baba, yana so ya kafa kansa ne, ya zamana wasu ne a ƙarƙashinsa. Shi yadda ba ya sakin jiki a kan dukiyar Baba, hakan ba wani damun sa ya yi ba, to amma yanzu tun da ga shi yana ƙoƙarin samun dama, gwara ya dama da ita. Duk kuwa sosai Baban ke iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya yi musu duk wani abu da suke buƙata. Duk abin da ɗa zai buƙata a wajen mahaifinsa, in dai Al-ameen ɗin ya sanar wa da Baba to zai yi masa, komai yawan kuɗin kuwa, idan dai har na amfani ne. Hakazalika kuɗin kashewa ma ba a bar shi a baya ba, lokaci zuwa lokaci yana ba wa kowannensu kuɗin kashewa, duk kuwa da kuɗin da ake tura wa kowannensu bayan an yi lissafi a kasuwa, da kuma lokaci zuwa lokaci. To duk dai wani gata na rayuwa Baban ya yi musu. To amma fa shi ma zai so ya kafa kansa, ya zama wani kamar yadda Baban ya zama. Don haka ya zama tilas ya yi aiki tuƙuru, don ba a samu a zaune. Kai tsaye ɗakinsu ya shige, daidai lokacin da MuhammadAali ke shirin fitowa daga ɗakin. Gabaɗaya ya sauya, duk da dama can ba ma'abocin dariya ba ne, amma fuskarsa ta sake cunkushewa, duk ya sake zama mara walwala. Shi gabaɗaya haushin kansa yake ji ne, wanda saboda haka ne duk irin tambayar da Saleem da ya kira shi a waya, saboda ya bar garin ne na kwana biyu zai je ya dawo, amma ce masa ya yi babu komai. Don bai san da wanne baki zai buɗe ya sanar da shi cewar yarinyar da ta mare shi zuciyarsa ta kasa mantawa da ita ba. Ta yaya ma hakan za ta kasance? Me yake ƙoƙarin fahimta? Har kuma lokacin kamar wani sammu, ya kasa mantawa da hoton fuskarta da ta zama aba mafi muhimmanci da ya kasa mantawa. Duk irin yadda yake yakice tunanin amma hakan ya citira, don haka ya yi watsi da lamarin kawai, duk lokacin da ƙwaƙwalwar tasa ta gaji za ta haƙura ta daina. A tsakiyar ɗakin suka yi magana kafin MuhammadAali ya fice, ya yin da Al-ameen ya ƙarasa ya buɗe drawer ɗin gefen gadonsu ya saka hoton a ciki. Sai ya koma ya kwanta a kan gadon yana fito da wayarsa ya fara dannawa. "Shigo mana Aminu." Inna ta faɗa tana gyara zamanta. Babu musu ya ƙarasa cikin ɗakin ɗauke da sabuwar sallama a bakinsa. Neman waje ya yi ya zauna yana gaishe da Innar, ta amsa tana tambayar sa iyali. "Alhamdulillah Inna, ina Hamidar?" Sai da ta kalli toilet sannan ta ce "Tana wanka ne." Sai ya jinjina kai kawai, ba tare da ya ba wa amsar tata muhimmanci ba ya gyara zamansa kafin ya ce "Wato Inna wata magana ce mai muhimmanci ta kawo ni." "To! Ikon Allah! Ina jin ka." Numfashi Daddy ya sauke kafin ya ce "Wato Inna, wannan mummunan al'amarin da na ji shi ne ya saka hankalina ya kasa kwanciya." Da sauri Inna ta ce "Wanne al'amari ne wannan kenan?" "Auren Hamida da Muhammad mana? Wanne kalar saɓo ne ake ƙoƙarin aikatawa? Shin kin san kuwa Muhammad har shaye-shaye yana yi? Ta yaya ma za a ɗauki yarinya kamar Hamida a aura masa?" Taɓe baki Inna ta yi, jin inda maganganun nasa suka dosa. "Kai rabu da wannan don Allah." "Shaye-shaye fa Inna." "Allah Ya sa shi ya ƙirƙiri kayan mayen ma. Hamida za ta auri Muhammad, ko ana so ko ba a so." Wani yarr Daddy ya ji, jin abin da ta faɗa ɗin, me take nufi kenan? Wane ne ba ya son auren? "Inna ki dai duba lamarin." Ya faɗa yana jin wani irin ɓacin rai na taso masa. "To." Ta amsa da hakan tana ɗauke kanta. Babu ɓata lokaci Daddy ya miƙe sum-sum-sum ya fice daga ɗakin a fusace. Wallahi in dai yana raye Hamida ba za ta taɓa auren Muhammad ba, dole ma ya san abin da zai yi wanda zai saka a fasa auren nan. Kai ko da hakan na nufin zamowa ƙarshen alaƙarsu da Innar, shi wannan ba damuwarsa ba ce. Amma dai tun da haka ta taka, to ya zama dole ta bar musu gida ko ya samu salama. Don kuwa tun da abin nan ya faru, bai sake samu ya runtsa da kyau ba. Gabaɗaya tunaninsa ya koma yadda za a yi kada hakan ta faru. Ta yaya ma ya gama wahalar, ya gama share fagen amma a ɗauki Muhammad ɗin a aura wa wata baƙauyiya Hamida? Ai hakan ma ba zai yiwu ba. Tun kafin ya ƙarasa yake hangen Baba da ke cikin manyan kaya na shadda. Ya matuƙar yin kyau, ya sake fitowa a kyakykyawan Bahaushe sakk. "Barka da dawowa Yaya." "Barka dai Aminu, ya aikin?" Ya tambaya cike da kulawa. Sai da Daddy ya yi murmushi kafin ya amsa da "Aiki Alhamdulillah, muna ta kwantatawa dai don kar a samu matsala." "In sha Allah ma ba za a samu matsala ba." Baba ya ƙare maganar fuskarsa ɗauke da murmushi. Don shi ma yanzun kuma sai ya ji hankalinsa ya kwanta, tun bayan da ya ɗora ƙannen nasa a gurbin waɗancan mutanen nasa da ya sallama bayan an kama su da laifin cin amana. Don haka yanzu Daddy, da kuma Abban Al-ameen su ne a kan wannan gurbin. Ya kuma san ba shi da matsala ko kaɗan da hakan, ya sake barin komai a hannun ƙannen nasa, musamman da ya kasance ba wani sosai yake fita ba. Abu ɗaya ne ma yake sakawa yake ɗan fita, wani dalilinsa da shi kaɗai ya bar wa kansa sani, wanda kuma hatta MuhammadAali ba ya so ya sani sai lokacin da komai ya kammala. Tare suka ci gaba da takawa zuwa sashen Baban, wanda Daddy ya yi amfani da wannan damar wajen soma faɗin. "Yaya maganar auren Muhammad da Hamida, anya kuwa ba ka ganin akwai wani abu a ƙasa?" Dakatawa Baba ya yi, ya kalli Daddyn sannan ya ce cikin rashin fahimta. "Ban gane ba Aminu,, kamar me kenan?" Sauke numfashi Daddy ya yi, da ma so yake su yi magana sosai ta fahimta, don haka shi ma ya dakata sannan ya ce "Duk irin tsanar da ta nuna wa Muhammad a baya sai yanzu kwatsam ta zo ta kawo jikarta a matsayin tana so mu haɗa zuri'a da ita? Gaskiya Yaya idan dai har na isa da Muhammad, to ban amince da wannan haɗin ba. Don haka kawai hankalina ya ƙi kwanciya. Mu cire batun zumunci a gefe, ni da kai duk mun san halin Inna, to ba zai yiwu ta yi amfani da kallon da muke mata na uwa ta tilasta a yi wannan haɗin ba. Gaskiya hankalina bai kwanta da hakan ba. Kuma ta gefe guda ma inda Muhammad ya tashi da inda Hamida ta tashi ai akwai tazara mai nisa, idan muka haɗa shi da ita kamar ba mu duba masa ba." Shiru Baba ya yi yana nazarin maganganun Daddyn na farko. Wajen second 40 sannan ya sauke ajiyar zuciya. Shi kam sam bai ma san me zai ce ba. Shi dai bai san da wanne ido zai kalli Inna ya ce mata bai amince ba, kuma a yadda ta sake masa maganar, cewa ta yi cikin wata ɗaya take so a yi komai a gama. To ta yaya zai ce mata bai amince ba? Duk kuwa da ta gefe guda shi kansa ba ya son tilastawa ɗansa, don kuwa ya tabbatar idan dai har ya buɗe baki ya cewa Muhammad ya auri Hamida, to tabbas zai aure ta. To amma ba ya so ya kasance uba mara adalci ga ɗansa, shi ma mutum ne, kuma yana da zaɓinsa, ya kuma sanar da shi ba zai iya auren Hamidar ba sai dai idan har umarni ne yake ba shi. To me ya kamata ya yi? Shi duk wani abu da Daddyn yake faɗa a kan Innar bai dame shi ba. Ko ma dai mene ne a ranta wannan ita ya shafa, bai dame shi ba. Abu ɗaya ya sani, duk wani mai nufinsa da sharri Allah Ya fi shi, ballantana ma shi ya kasance mutum mai matuƙar yarda, wanda ba ya taɓa zargin na kusa da shi, idan dai har ba hujja ya gani ɓalo-ɓalo ba. "Shi kenan Aminu, za mu yi maganar, yanzu haka ina so na je na huta ne." Baba ya yi maganar jiki a matuƙar sanyaye. "Shin akwai wani abu ne Yaya?" Daddyn ya faɗa da sauri. Sai ya girgiza kai sannan ya ce "Babu komai." Daga haka suka rabu bayan sun yi sallama. A ɓangaren Inna kuwa tsaki ta ja bayan fitar Daddy. "Shashasha, karr nake kallon ka." Ta yi maganar tana juyawa ta kalli Hamida da ta fito daga toilet. Ba ta ce da Inna komai ba ta shiga shiryawa, cikin wasu riga da wando da ta ɗakko a ɗakin Ammeey ba tare da ta sani ba. Kallon ta kawai Inna take yi har ta gama shirin ta zari mayafi ta yafa sannan ta kalli Inna tana murmushi ta ce "To Inna zan fita jawo hankali." Ta yi maganar tana wani kwarkwasa. "Oh ni na shiga 3 ni 'yar nan." Inna ta faɗa bayan ta dafe kanta. "Da wannan shegen gudajin ƙirjin naki za ki jawo hankalin ko kuwa da waɗannan shafaffun mazaunan?" Ta jefa mata tambayar rai a ɓace. Gyara tsayuwarta Hamida ta yi tana jin wani irin ɓacin rai na taso mata. Ta yaya ma za a yi Innar ta kira ta da ƙwaila? Bayan duk irin yadda take jan hankalin maza da surar da take da ita. Ai wallahi ma ta fi ƙarfin a kira ta da hakan, don kuwa in dai diri ne ita ta san tana da shi. Ba tare da ta ankara ba, Inna ta miƙe ta kulle ƙofar ɗakin. Sai da ta dawo sannan ta lura. Ihu ta saka tana faɗin "Inna don Allah kar ki mini haka. Inna don Allah ki buɗe mini ƙofa kin ji?" "Idan kin yi hankali sai ki sanar da ni." Inna ta faɗa tana ƙarasawa kan gado ta baje. Ci gaba da magiya ta yi har da haɗawa da kuka, amma Innar ta ƙi saurarar ta. Don haka da kanta ta gaji ta haƙura. Sai cikin dare, bayan Innar ta yi nisa a bacci sannan ta miƙe, ta ƙarasa inda ta kwanta ɗin ta faki idanunta ta ɗauki mukullin, kai tsaye ƙarasawa ta yi ta buɗe ƙofar sannan ta fice daga ɗakin tana sauke ajiyar zuciya. Ta ga alama Innar tana ƙoƙarin zama shamaki ga cikar burinta. Ta san Innar na son kasancewar al'amarin nan, to amma idan ta sanar da ita abin da take ƙoƙarin aikatawa, ta san ba za ta goyi bayanta ba. Shi ya sa ta kama kanta ta yi shiru, sai dai kawai ta ji labari idan komai ya kankama. Cike da takatsantsan ta ƙarasa ta tura ƙofar ɗakin, cikin sa'a kuwa a buɗe take. Ta saki ajiyar zuciya tana jin wani irin daɗi na ziyartar ta. Kai tsaye bedroom ɗin ta nufa, ta tura ƙofar ɗakin a hankali tana leƙen sa. Ba ta iya hango fuskarsa, saboda yana kwance ne a kan gado yana danna waya. Sai ta yi amfani da hannunta, don ta riga fahimci inda sockets ɗin ɗakunan gidan na kunna ƙwai suke. Don haka ta kashe ƙwan, cikin ƙanƙanin lokaci duhu ya mamaye ɗakin. Tsalle ta yi cike da kula, tana jin wani irin daɗi na kama ta. Ko babu komai yau burinta zai cika, don ko me zai faru ba za ta bar ɗakin ba har sai wani abu ya shiga tsakanin su. Kai tsaye ɗakin ta faɗa, ta lafe a daidai inda socket ɗin yake, bayan ta yi amfani da hannunta wajen jan ƙofar ɗakin cike da fatan ta rufu ba tare da an ji motsi ba. Daga inda yake zaune ya ja tsaki yana kunna fitilar wayarsa ya ajiye ta a kan gadon, ya zama ta haske sama, haske kaɗan ya ɗan bayyana a cikin ɗakin, sai dai ba komai ake iya gani ba. Don haka shi kai tsaye hasken ya je don ya kunna, ba tare da ya lura da mutum a wajen ba ya kai hannunsa da niyyar kunnawa. Sai hannun nasa ya sauka a kan dokin wuyanta, da sauri ta riƙo hannun da kyau, kafin ya yi wani yunƙuri ta faɗa jikinsa cikin wani irin yanayi na jan hankali tana faɗin "Wayyo Allah.." Mhiz Innocent 08124818273 *♡☆BIYU BABU☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) YOTA Writers Ass.. Book 1 Pg 28 Cike da mamaki Al-ameen ya buɗe idanunsa cikin ɗan hasken da yake iya gani, lokaci guda yana sauraron muryar Hamidan da ta sake sauke numfashi cikin salo na jan hankali. Da sauri ya yi baya, yana kuma yin amfani da hannunsa wajen ƙoƙarin janye ta daga jikinsa, sai ta samu damar sake ruƙunƙume shi. Zuwa lokacin ransa ya sake ɓaci, don haka ya saka hannayensa duka biyun ya janye ta daga jikinsa, bai yi wata-wata ba, ya jefar da ita gefe, kafin da sauri ya ƙarasa ya kunna ƙwan ɗakin. Nan da nan haske ya mamaye ɗakin. Da sauri ya sauke idanunsa a kan Hamida da ta faɗi ƙasa, wadda ita ma shi take kalla. Sai dai cikin rashin sa'a, idanunta suka sauka a kan fuskar Al-ameen da ke kallon ta cikin tsananin mamaki. Runtse idanunta ta yi, cikin tsananin ɓakinciki. Shin me ya shiga kanta ne haka? Me ya sa ba ta fara tantance wane ne cikin ɗakin ba ta fara abin da ya kai ta? Me ya sa ta yi gaggawa? Yanzu me za ta cewa wannan mutumin? "Ke!" Al-ameen ya faɗa cike da mamakin dai ɗauke a kan fuskarsa. Ƙarasawa inda take zaune ya yi ya sake kafe ta da idanunsa ya ce "Me ya kawo ki cikin ɗakin nan?" Ya faɗa a tsawace yana kallon ta. Ba ta san lokacin da kuka ya ƙwace mata ba, ta shiga rera shi, kafin da ƙyar ta iya buɗe bakinta ta ce "Don Allah ka yi haƙuri, na fita ne sai na yi ɓatan sashe, na zo komawa inda muke sai na faɗo nan. Na ɗauka Inna ce shi ne nake so na tsoratar da ita." Ta ƙare tana ci gaba da kukan, cike da fatan ya yarda da abin da ta faɗa. Shiru kawai ya yi yana kallon ta ba tare da ya ce komai ba. Har zuwa lokacin da ta miƙe har lokacin tana kuka ta ce "Don Allah ka yi haƙuri." Daga haka ba tare da ta jira ya ce komai ba, ta ja ƙafafunta ta fice daga ɗakin da sauri cike da danasani. Shin yau ina wayo da dabararta suka tafi? Me ya sa kai tsaye ta afka ɗakin bayan ta san ba shi kaɗai ke zama a ciki ba? Ko bayan fitar ta, komawa Al-ameen ya yi ya zauna a kan gado yana tuna abin da ya faru cikin ɗakin. Anya kuwa wannan yarinyar? Wannan yarinyar ita ce ake so a aura wa Muhammad? Me yake ƙoƙarin fahimta da shigowarta ɗakinsu? Me ya kawo ta? Me take ƙoƙarin nuna masa? Duk shi kaɗai yake yi wa kansa tambayar, duk kuwa da ya san babu mai ba shi amsa. Kamar wanda ke magana da wani, haka ya shiga girgiza kai. Ko kaɗan wannan yarinyar ba ta dace da shi ba, domin kuwa duk wayonta, duk irin tsara shin da ta yi, kawai jin ta yake yi, domin kuwa ya riga fahimce ta, ya kuma gane ƙarya kawai ta shirga masa. A ɓangaren Hamida kuwa, kai tsaye kan gado ta faɗa tana ci gaba da kukanta. Gabaɗaya yau ɗin a bai-bai ta zo mata, duk kuwa da irin shirin da ta yi mata, sai ga shi a banza. Yanzu wanne kallo Al-ameen ɗin zai yi mata? Da wanne ido za ta ci gaba da kallon sa bayan ta riga ta ɓata shirin nata gabaɗaya? Yau ɗaya ta ji haushin kanta ya kama ta. Ji take kamar ta fasa ihu ko ta ji daɗi, sai dai kuma ta san tana yin hakan Inna za ta iya tashi. Idan kuma ta tashi ta ce mata mene ne? Don haka haka nan ta ci gaba da zama tana ta saƙe-saƙe cike da neman hanyar da za ta zame mata mafita. Ko da safe bayan Inna ta tashi tana lura da Hamidar da har zuwa lokacin ba ta tashi ba. Ta ƙarasa ta ɗan taɓa ta kafin ta ce "Ke!" "Uhmm." Ta amsa jikinta a matuƙar sanyaye. Don gabaɗaya ta rasa inda za ta tsoma kanta ta ji daɗi, saboda yadda shirin nata ke neman tashi a banza. "Ina miki magana kina wani amsawa a ciki-ciki, mene ne?" Sai da ta zumɓuro bakinta gaba sannan ta ce "Ni fa na ce miki babu komai, ki ƙyale ni don Allah." Ta yi maganar tana juya mata baya. "Iyeee!!" Inna ta faɗa tana riƙe haɓa. Daga haka ba ta sake bi ta kanta ba, ta yi gaba kawai. "Mun yi iya bakin ƙoƙarinmu don ji daga bakin Shettima, amma hakan ya gagara, mun yi magana da shi kansa amma ya ƙi ba mu haɗin kai, ballantana ya yi magana mu samu damar kawo muku, wanda hakan ya sanya mutane da dama yarda da cewa duk abin da ke yawo a cikin garin nan gaskiya ne. Za ku fahimci hakan ne, biyo bayan saƙonnin da za mu karanto muku, waɗanda ke ɗauke da raayinku ku masu sauraro." A karo na biyu Baba ya sake saurarar abin da abokinsa ya turo masa, kasancewar shi ɗin ba ma'abocin jin radio ba ne, ya sanya bai san abin da ke ci gaba da faruwa ba. Shiru ya yi na tsawon sakanni yana ci gaba da nazarin maganganun. Shin me ya kamata ya yi? Anya kuwa lokaci bai yi ba da zai magantu ko hakan zai zama silar goguwar wannan ƙagen da aka yi masa shi da ɗansa? Ya fara gajiya da abin da ke faruwa. Domin kuwa idan dai har ya fahimta da kyau har mutanen unguwa wasu sun fara canja masa fuska. Sau da dama kuma yakan fahimci wasu suna so su tambaye shi ne don su ji tabbacin abin da suka ji, sai dai suna jin shakka da kuma kwarjininsa da ke tasiri wajen sanyawa su kasa tambayar tasa. Idanunsa na kan wayarsa, sai dai gabaɗaya hankalinsa ba ya wajen. Da ma ya san dole ne duniya ta zarge shi da aurarrakin da ya yi a rayuwarsa, wanda ba da niyyarsa ne hakan ke faruwa ba, tun da komai yana faruwa ne da dalili, dalilin ma mai ƙarfi. To ta yaya da hankalinsa zai dinga sakin mata haka nan kawai babu dalili? Sau da dama sai ya danne, ya ga kamar zai zauna da mace ne duk kuwa da munin halinta, sai abin ya zo ya citira. To ashe bai tsira ba, duk da haka sai da Maimuna ta ɓata masa suna. A yau ba don Alhaji Abbas Shettima ne hakan ta faru a kansa ba, da 'yan unguwar gabaɗaya sai sun juya masa baya. To Alhaji Shettiman kamar wani bango ne da suka dogara da shi, wanda suke matuƙar ganin girmansa, suke kuma girmama shi, saboda shi ɗin mutum ne har da rabin mutum. Bayan faruwar abin nan kuma, dukkansu sun rasa yadda za su yi. Sun ji kamar su je su same shi da maganar, sai dai suna ganin kamar cin mutunci ne a gare shi idan dai har suka amince. To amma ba su da hujjar da za ta saka su ƙaryata hakan, ba kuma su da wadda za ta saka su gasgata hakan. Don haka kawai sai suka ja bakinsu suka yi shiru, tun da shi kansa wanda ake magana a kan nasa bai fito ya yi magana ba, don haka ba su da damar yanke hukunci sai dai su zuba wa sarautar Allah ido. "Barka dai Adam ya mutanen gidan?" Abee da da kansa ya kira Adam ya tambaya cike da kulawa. Daga can ɓangaren Adam ya amsa da "Alhamdulillah." Sannan shiru ya biyo baya, kafin zuwa can Abee ya ce "Wato na kira ne don na sanar da kai ina so ka zo don ina buƙatar ganin ka, magana ce mai muhimmanci a kan ka da Aysha." Shiru Janan da ke ƙoƙarin shiga ɗakin Abee ɗin ta yi tana saurarar abin da yake faɗa. Sai dai ba ta iya jiyo abin da Adam ɗin yake faɗa. "To madallah, zan jira ka in sha Allah kafin na fita. Don ina so ne a yi komai babu ɓata lokaci." Shi ne abin da Abee ya faɗa, wanda ya sanya ta daskarewa a wajen. Shin me Abee ke cewa ne? Me yake ƙoƙarin aikatawa? Shin wai ba za a iya saurarar ta ba ne ko da kaɗan ne ba? Shin ba za a iya ba ta damar ƙarshe wadda za ta gyara kuskurenta ba? Da gudu ta fice daga ɗakin, kai tsaye ɗakin Farouk ta nufa cikin kuka, irin gigitaccen kukan nan. Yana zaune a kan kujera, a zaune, babu abin da yake yi sai wannan tunanin da ya zame masa jiki a yanzun. A kan cinyarsa ta ɗora kanta tana fashewa da wani sabon kukan. Da sauri Farouk ya ɗaga kansa ya kalle ta, don sam bai san da shigowarta ba, saboda yadda hankalinsa gabaɗaya ba ya wajen. Lumshe idanunsa ya yi kafin ya buɗe ya sauke su a kan kanta da ke ɗore a kan cinyarsa. Idan da so samu ne, cewa zai yi ta tashi zaune su yi magana, to amma a yanayin da take ciki, ko ya faɗi hakan ma babu lallai ta zauna ɗin. Don kuka ne take yin sa tun daga can ƙarƙashin zuciyarta, wanda idan har ba ta da daina ba, zai ci gaba da illata zuciyarsa ne. Sai da ya ja dogon numfashi yana jin yadda zuciyarsa ke ci gaba da harbawa sannan ya ce "Me ya faru Aysha?" Kamar jira take yi dama. Sai ta sake fashewa da kukan kafin ta ɗaga kanta ta kalle shi ta soma faɗin "Yah Farouk don Allah ka yi wa Abee magana ya janye abin da yake ƙoƙarin aikatawa. Duk da ina son Adam, ai ni ba aure nake so ba. Ni wallahi ba na son aure Yah Farouk." Murmushi kaɗan Yah Farouk ya yi sannan ya ce "Kina son aure mana Janan." Da sauri ta sake kallon sa, jin yadda ya yi maganar kamar wani maraya. Bai jira ta ce komai ba ya ɗora da faɗin "Me ya sa wanda ba ya son aure zai fara soyayya? Hakan na nufin kina so, ki amince da umarnin Abee kawai. Aure za su yi miki a nan nan kusa." Ya faɗa cikin rarrashi, don sosai yake so ya ga ƙanwar tasa cikin walwala, ko shi ma ya samu damuwar da ke danƙare cikin zuciyarsa ta ragu. "Yah Farouk da kana bin bayana idan na kawo maka ƙara. Ko na yi maka laifi ne ban

Chapter 21 of 24