Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta ta ci gaba ɗin, to sai ta huta. Ta kuma jira ta ga idan babu wani mataki da iyalan Shettiman za su ɗauka. Sanye cikin doguwar rigar atamfa da mayafinta da ta yi amfani da da shi wajen yafa shi a kanta da babu ɗankwali take takawa zuwa lambun gidan da ta tabbatar Baba yana can. Aikuwa a can ɗin ta same shi zaune. Sai ta ƙarasa cikin ladabi ta zauna tana faɗin "Baba barka da wannan lokacin." Sai da ya kalle ta sannan ya ce "Barka dai Ammeeyna." Sai ta yi murmushi hannayenta biyun riƙe da mayafinta tana wasa da shi. "Me ya faru?" Baba ya faɗa bayan ya gyara zamansa. Da ma ta san ko ba ta faɗa ba Baban zai fahimci akwai abin da take so, shi ya sa kai tsaye ta taho wajensa, sanin da ta yi yana da mugun kula a kan 'ya'yansa, ta yadda yake saurin ganowa idan suna da wata matsalar. "Baba da ma ka ga ƙawar nan tawa Aysha ce, ba ta zuwa makaranta. Shi ne na ce don Allah ko za a kai ni in je in duba ta ka ji Baba?" Ta ƙare maganar kamar za ta saka kuka, tana kuma marairaice fuska, duk don Baban ya tausaya mata. Shiru Baba ya yi bayan gama jin abin da Ammeeyn ta faɗa, zuwa can ya ce "Ikon Allah! To Allah Ya sa dai lafiya." "Ameen Baba, ka ga ai gwara in je in duba ta ko?" Ta sake tambaya cike da zaƙuwa da son jin amsar da za ta fito daga bakin Baban. Sai ya yi murmushi, don duk ya gane wayonta, sai ya jinjina kai sannan ya ce "Ah ya kamata kam." "Yawwah Babanmu." Ta faɗa tana murmushi. Daidai lokacin da Muhammad ya ƙaraso wajen, ya yi kyau cikin shigar ƙananan kaya, idan ka gan shi sai ka ɗauka ba shi da wata damuwa, ko kuma ya manta ne da duk wani abu da ya faru. Sai dai a zahirin gaskiya, kwana biyun dukka ba shi da sukuni, shi kaɗai ya san binciken da yake yi, ba kuma ya so ko kaɗan Baban da ya yi shiru ya ji. Shi a wannan karon Baba ya sake ba shi mamaki, yadda ko kaɗan bai nuna al'amarin ya dame shi ba. Abokansa da yawa sun kira shi, amma ya nuna musu ba ya buƙatar taimakon su. Gidajen radio da television duk sun yi ƙoƙarin yin hira da su amma ya ce ba zai yi ba. "Barka da wannan lokacin Baba." "Barka dai Muhammad. Fita za ka yi ne?" Baba ya yi maganar lokaci guda. Sai ya jinjina kansa sannan ya ce "Eh zan yi wa Saleem rakiya ne." Ya faɗa a taƙaice. Mayar da dubansa Baba ya yi kan Ammeey, yana shirin yin magana ta ce "Barka da wannan lokacin Yah Muhammad." Kamar ba zai amsa ba, don ya ɗauka ko ba ta san da wanzuwar sa a wajen ba, sai kuma ya tuna Baba na wajen, don haka a ɗan daƙile kamar wanda aka yi wa dole ya ce "Barka." "Ammeey tashi ki je maza yayanki ya ajiye ki a gidan ki duba jikinta." Baba ya faɗa. Da mamaki Muhammad ya kalli Baba jin abin da ya faɗa, daidai lokacin da ita ma Ammeeyn ta ji jikinta ya yi sanyi. Fisabilillahi wane irin Yah Muhammad kuma? Ita wallahi ba ta so. To ba ma gwara abokin nasa ya kai ta ba a kan shi? "Baba." Ya ambata har lokacin yana kallon sa. Jinjina kai Baba ya yi kana ya ce "Eh." Har ya soma shirin cewa wani abu, sai kuma ya maaze kawai, bayan ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ai ba don za mu fita ba da na sauke maka ita a ko'ina ne ma." Sarai Baba ya gane wannan maganar tasa, don haka sai da ya yi murmushi sannan ya ce "Babu komai. Ko na minti biyar ne kai ta ta ga jikin ƙawar tata, ka dawo mini da ita, sai ka wuce inda za ka je." Bai saba dogon musu da Baban ba, don haka ya sauke ajiyar zuciya kawai ya juya ya bar wajen. Ko bai yi magana ba, daga Baban har ita Ammeeyn sun fahimci me yake nufi, don haka jiki a sanyaye Ammeeyn ta miƙe ba tare da ta ce komai ba. "A'ah Ammeey??" Baba ya ambaci sunanta cikin sigar tambaya. Sai a lokacin sannan ta ce "Baba da ma kai ko Yah Saleem ɗin ma ka ce ya kai ni wallahi." Shiru Baba ya yi yana kallon Ammeeyn. Ya rasa mene ne dalilin da ya saka jininsu bai wani zo ɗaya ba. Ga dai shi suna rayuwa cikin gida ɗaya, amma duk ba sa yin junansu. To amma ya suke so ya yi da ƙudurinsa na shekaru da shekaru? A wasu lokuta da dama yana sane yake yin wasu abubuwan da za su janyo kusanci tsakanin Muhammad ɗin da Ammeey, sai dai duk da haka, kamar har yanzu gaisuwa ce kaɗai ke shiga tsakaninsu. To ko ma dai mene ne, Allah Na gani, kuma shi Zai tabbatar musu da alkairinSa. "Ina za ki je?" Muhammad ya faɗa yana kallon ta lokacin da take ƙoƙarin shiga sashensu. Sai da ta kalli sashen sannan ta dawo da dubanta kan Muhammad ɗin ta ce a sanyaye "Ɗankwalina zan je in ɗakko." "Kina ƙara taku ɗaya gaba, sai dai ki nemi mai kai ki." Hakan da ya faɗa shi ne dalilin da ya sanya ba ta sake taku ɗaya zuwa gaban ba kuwa. Tuni idanunta sun yi rau-rau, babu yadda ta iya, don ta san tun da ya faɗa ɗin zai aikata ne, hakan ya sanya ta dawowa da baya kawai tana gyara zaman mayafinta. Saleem da ke zaune a wajen mai zaman banza yana kallon duk abin da yake faruwa ya ce "Malam ka daina tsorata mini mata. Don Allah ji yadda ka firgita mini ita." Ya yi maganar har lokacin yana kallon Ammeeyn. Shi dai Muhammad tsaki kawai ya ja, don shi yanzu Saleem ɗin ma haushi yake ba shi, idan yana magana a kan Ammeeyn. Shi gani yake kamar shirme ne, ya zauna yana son wannan yarinyar; da ko gama sanin kanta ma ba ta yi ba. Kai tsaye gidan baya ta buɗe ta shiga ta yi ƙwamm. A ƙofar gidan ya tsayar da motarsa. Ammeey ta sauka daga motar, daidai lokacin da Saleem ke faɗin "Bari na ɗan taka mata." Wata uwar harara Muhammad ya jefa masa sannan ya ce "Malam ka dinga jan girmanka mana, salon ta raina ka?" "Raini kuma?" Saleem ya tambaya cike da mamaki. Wai shi guy ɗin nan me yake ɗaukar kansa ne? Kamar yaya raini? Ina ruwan soyayya kuma da wani raini? Ba don ya bi maganar Muhammad ɗin ba ya zauna kawai cikin motar yana watsa masa kallon banza. Shi kuwa nunawa ma ya yi kamar bai san yana yi ba. Sai ya kalli Ammeey ta tagar da ke kusa da shi ya ce "Ammeey." Sai ta juyo da sauri tana kallon sa. Agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya nuna ya ce "Kin ga ƙarfe nawa ko? Minti biyar ki yi maza ki fito, idan ba haka ba ki nemi mai da ke gida. Kin ji ko?" Sai ta jinjina kai jiki a sanyaye, sannan ta taka zuwa gidan. Amfani da wannan lokacin Muhammad ya yi wajen ɗaukar wayarsa ya shiga dannawa kawai. Don shi kansa ya san ya faɗi zai tafi ya bar ta ɗin ne kawai ba don zai iya ba. Don duk wani aiki da Baban ya saka shi, bai kuma san ta yadda za a yi ya kasa cika shi ba. Tun da har ya umarce shi da ya kawo ta ya kuma mayar masa da ita gida, to tabbas zai yi hakan. Lokacin da Janan ta ga wadda ta zo gidan nasu, ji ta yi kamar ta yi me don tsananin farinciki. Sai a lokacin sannan Ummee ta nemi waje ta zauna ganin Janan ɗin ta san wace ce Ammeeyn. Don tana ganin ta lokacin da ta shigo gidan ta shaida fuskarta, idan kuma ba ta manta ba, Farouk ya ce mata 'ya ce a gidan Shettima. To kenan me ya kawo ta gidan? Me ta zo yi gidan nasu? Ko kuwa duk dai a kan waccan maganar ce? Tambaya da ta yi ko Aysha na nan, shi ne abin da ya ɗan kwantar mata da hankali. Yanzu kuma da ta ga da gasken Janan ɗin ta san ta, sai ta sauke ajiyar zuciya bayan ta zauna. "Na yi kewar ki sosai Aysha." Ammeey ta faɗa. Lumshe idanunta Janan ta yi sannan ta ce "Ni ma haka Amina. Ina makaranta?" "Makaranta tana nan tana jiran dawowar ki. Wai ba kin warke ba?" Ta tambaya tana sake nazarin yanayin AyshaJanan ɗin. A hankali Janan ta kalli Ummee wadda ita ma ita take kalla, sai kuma ta mayar da dubanta kan Ammeey, kafin ta kai ga cewa komai Ummee ta ce "Za ta dawo in sha Allah. Amma sai ta sake warwarewa." Hakan da Ummeen da faɗa, ba ƙaramin ƙwatar Janan ɗin ya yi ba daga tunanin da ta tafi. Don da ma har ga Allah ba ta san me za ta ce ba. "Tam, Allah Ya kai mu, sai kin dawo." Ta ƙare maganar tana kallon ƙaton agogon da ke manne a bangon ɗakin. Sai ta miƙe kamar wadda aka tsikara ta ce "Aysha bari na tafi. Yayana ne ya kawo ni, kuma sauri yake yi." "Ke don Allah wai har za ki tafi?" Janan ta faɗa kamar za ta yi kuka, don da gasken gaske ta yi kewar ƙawar tata. "Eh fa." Ita ma Ammeeyn ta amsa a sanyaye. "Ummee na tafi." "To ki gaishe da gida." Ummee ta yi maganar har lokacin jikinta a sanyaye. Don da ma gabaɗaya ta sauya tun da abin nan ya faru, ta kasa sukuni. Duk kuma wanda ya gan ta zai fahimci tana cikin damuwa, duk kuwa da takamaimai har yanzu babu wani abu da ya biyo baya. To amma ta san halin masu kuɗi, za su iya biyowa ne ta inda ba ta yi tsammani ba. Ga shi kuma har yanzu ta kasa samun Maimuna, duk irin binciken da ita kanta take yi, da kuma wasu ma da suke taya ta. Da daddare Ummee na zaune tana aiki cikin laptop ɗin da ke gabanta. Ita kaɗai ce cikin ɗakin, yau ɗin ko kaɗan Janan ba ta damu ta zauna ta taya ta ta hanyar kallon abubuwan da take yi ba. Za ta iya cewa gabaɗaya ɗiyar tata ta sauya, tun bayan rabuwar ta da yaron da sakacin Ummeen ya yi tasiri wajen yin soyayya da shi da kuma haɗuwa da shi. Don ita kam har yanzu ba ta daina ba wa kanta laifi ba, aikin da take yi ya so ya shafi tarbiyyar Janan ɗin. Don da tana zama kullum a gida tabbas za ta san abubuwa da dama da ke cikin rayuwar ɗiyar tata. Tunanin nata ya katse lokacin da wayarta ta soma ruri. Ɗan lumshe idanunta ta yi, tana jin yadda wayar ke ƙoƙarin katse mata muhimmin aikin da take gabatarwa. A karo na biyu wani kiran ya sake shigowa bayan na farko ya katse, ganin idan ba ta ɗaga ɗin ba, aikin nata ba zai daina katsewa ba, ya sanya ta janyo wayar ta ɗaga ba tare da ta kalli mai kiran ba. "Barka da wannan lokacin Umma." Aka faɗa daga can ɓangaren "Barka dai." Ummee ta amsa, daidai lokacin da take zame wayar daga kunnenta don kallon number jin ba ta san muryar ba. "Sunana Adam, ni ne wanda ya zo a kan maganar Aysha." "Adam." Ummee ta maimaita sunan a kan laɓɓanta don da gaske ba ta shaida shi ba. "Eh Umma, wanda na zo wajen Baba, da ba ya nan, sai na shigo muka yi magana da ke a kan Aysha." "Ohh!" Ummee ta faɗa saboda gane waye da ta yi. Sai da ta ɗan gyara zama sannan ta ce "Mun wuni lafiya?" Sai a lokacin sannan ya ji hankalinsa ya kwanta ya ce "Eh Alhamdulillah." "Madallah." Ummee ta faɗa kamar za ta ajiye wayar don ci gaba da aikinta. "Da ma Umma na ce idan babu damuwa don Allah mu gaisa da ita ko na minti ɗaya ne mana." Kamar za ta musa, sai dai ba ta ma buƙatar ɓata lokacinta, ta gefe guda kuma hankalin yaron ya burge ta, hakan ne ya sanya ta faɗin "Babu damuwa." Godiya ya shiga yi kamar wanda aka yi wa albishir ɗin wani babban abu ba. Ita ba ma ta ji ba saboda sauke wayar da ta yi tana kiran Janan. Babu daɗewa Janan ɗin ta shigo cikin ɗakin. Kai tsaye miƙa mata wayar ta yi tana faɗin "Ga shi nan ku gaisa." Cike da mamaki Janan ta ce "Ummee wace ne?" "Wani ne, zan faɗa miki ko wane ne shi, ke dai ku gaisa." Jikinta a matuƙar sanyaye ta karɓi wayar ba tare da ta sake cewa komai ba. Ita kuma Ummee sai ta ci gaba da aikinta cikin laptop, ya yin da Janan ta kara wayar a kunnenta. "Hello." Ta faɗa duk a takure don ba ta san da wa za su gaisa ba. Ajiyar zuciya Adam ya sauke, dukan dodon kunnensa da muryarta ta yi, a nutse ya ce "Amincin Allah Ya tabbata a gare ki." "Ina wuni?" Shi ne abin da ta faɗa don ta ƙagu ta ji wane ne, da kuma dalilin kiran don akwai abin da take yi. "Kwantar da hankalinki Aysha. Ni ne wanda na kai ku asibiti kwanaki ke da ƙawarki." Ya yi saurin faɗa mata hakan, don yana tsoron kar ta katse masa kira. Sai a lokacin ta ji hankalinta ya kwanta, ta ce a sanyaye "Mun gode sosai, Allah Ya saka da alkairi." Murmushi Adam ya yi, kafin ya ce "Haba! Mene ne kuma na godiyar? Na kira ne da ma na ji ya jikinki?" "Na warke." Ta faɗa kai tsaye. Jin hirar tasu na neman ƙarewa, shi kuma har ga Allah ba ya so ta katse ya sanya shi faɗin "Kin samu damar yin magana da shi kuwa? Ina nufin kin ji ta bakinsa?" An zo wajen da take jira, hakan ne ya sanya ta satar kallon Ummee, ganin gabaɗaya hankalinta na kan aikin da take yi ya sanya ta zamewa ta fice daga ɗakin. "A'ah" Ta faɗa a taƙaice. Lumshe idanunsa Adam ya yi kafin ya ce "Ki kwantar da hankalinki, in sha Allah hakan ne mafi alkairi. Kin san akwai lokutan da muke kasancewa da wasu abubuwan cikin rayuwarmu, ba tare da sanin su ɗin ba alkairi ba ne a gare mu. To amma da tasirin addu'a, sai ki ga Allah Ya fitar mana su daga cikin rayuwarmu ya kawo mana madadin su. Hakan da ya faru da ke ba sabon abu ba ne, don ya faru da ƙanwata. Yanzu zancen da nake yi miki ta yi aure da wanda Allah Ya turo mata daga baya, ta fitar da wancan cikin tarihin rayuwarta gabaɗaya." Shiru Janan ta yi tana sauraron maganganun Adam ɗin. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ci gaba da faɗa mata maganganu cikin hikimar zance da Allah Ya ba shi. Kawai sai ta ji ta saki jiki da shi tana sauraron sa, har kuma ba ta so ma maganar da yake yi ɗin ta zo ƙarshe. "Na san na ishe ki da surutu ko?" Ya faɗa cike da fargabar amsar da za ta fito daga bakin Janan ɗin. Sai ta girgiza kai kamar tana gabansa, lokaci guda tana ɗan tura bakinta ta ce "A'ah, ina jin ka." Ta yi maganar tana sauya hannun da ke riƙe da wayar da ɗayan hannun nata. Mhiz Innocent 08124818273 *♡☆BIYU BABU☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) YOTA Writers Ass.. Book 1 Pg 19 A ɓangaren Adam, lumshe idanunsa ya yi, har cikin zuciyarsa yana jin daɗin abin da Janan ɗin ta furta. Sai dai kafin ya kai ga cewa komai, ya ji ana ƙoƙarin fuzge wayar, cikin ɗaga murya Nafisa ke faɗin "Munafuki! Da wacce munafukar kake waya?" Ta yi maganar tana ci gaba da ƙoƙarin ƙwace wayar da ya yi wa wani mugun riƙo, tun da ya ji tana shirin ƙwacewa. Sauri ya yi ya katse kiran, ya kuma kulle ta gabaɗaya, daidai lokacin da Nafisa ta yi nasarar karɓar wayar. Saboda tsananin masifar da take ji da ita, jikinta har wani rawa yake yi, idanunta gabaɗaya a kan wayar. Sai dai ga mamakinta, sai ta ga wayar ta ƙi buɗuwa, duk kuwa da ba yau ne karon farko da ta soma ɗaukar salular Adam ɗin ba. A karo na barkatai ta sake gwada wani password ɗin, amma har lokacin bai yi ba. Wurgi ta yi da wayar cikin ɗaga murya take faɗin "Canja password ɗin ka yi saboda akwai munafurcin da kake ƙullawa? Wallahi sai ka faɗa mini da wacce tsinanniyar kake waya." Kallon ta kawai yake yi har zuwa lokacin bai ce komai ba. Yakan ji shakkar ta lokaci zuwa lokaci, sai dai a wannan karon duk da yana jin ɗarr, amma rashin tsoron nata ya fi yawa. Don haka a nutse ya sauko da ƙafarsa daga kan gadon, ya tsaya a gabanta. Hannayensa ya rungume a ƙirjinsa, sannan ya ce "Wadda zan aura ce." Wani irin duka ƙirjin Nafisa ya yi, har ba ta san lokacin da ta yi azamar runtse idanunta ba. Sai zuwa can sannan ta buɗe, daidai lokacin da Adam ke ƙoƙarin raɓewa ta gefenta don ficewa daga ɗakin. Ba ta san lokacin da ta daka tsalle ta dawo gabansa ba. "Wallahi ba ka isa ba, ka yi kaɗan ka yi mini kishiya wallahi. Wallahi sai na kashe ta, sai na lalata mata rayuwa." Ta ƙarashe maganar tana ƙoƙarin cin kwalarsa. Sai dai ga ɗimbin mamakinta, sai ji ta yi ya ce "Kar ki soma. Kar ki fara wannan kuskuren, idan ba haka ba, za ki yi nadamar da za ta zamana kina yin ta har ƙarshen rayuwarki. Aure ne kuma kamar yadda na faɗa miki zan yi shi ko da amincewarki ko babu. Idan za ki kwantar da kanki ki kwantar, idan ba za ki kwantar ba, ki ci gaba da haukan, amma tabbas aure ne sai na yi shi." Kawai kallon sa ta tsaya tana yi, kamar wadda ta ga baƙon halitta. Da gaske Adam ɗin ne ke faɗa mata irin waɗannan maganganun? Anya kuwa Adam ɗin ya gane wace ce a gabansa? Nafisa ce fa. Nafisan da yake jin ko da shakkar ɗaga mata murya ne ballantana kuma a kai ga yana sanar da ita zai yi aure ko da amincewarta ko babu. 'Shin me yake shirin faruwa ne? Ko kuma ma dai yake faruwa?' Ta tambayi kanta tana ci gaba da bin Adam ɗin da idanu kawai, lokacin da ya fice daga ɗakin. Kawai sai ta yi zaman ɗabaro a wajen tana fashewa da wani irin kuka da ke fitowa tun daga can kasan zuciyarta. Tana bala'in son Adam, ta yadda ba za ta taɓa iya sharing nasa da wata ɗiya mace ba. Ba za ta taɓa iya kwatanta irin son da take yi masa ba, shi ya sa ko kaɗan ba ta samun sukuni duk lokacin da zai fita daga gidan. Kai a gabaɗaya rayuwarta ita ba ta sakewa da duk wani takunsa, shi ya sa kullum take a cikin zarginsa. Wanda ba ta san hakan ba ƙaramin kashe son ta da Adam ɗin yake yi, abin da take yi yake ba. Don ita a wajenta, wannan ce kaɗai hanyar da za ta saka Adam ɗin ya yi shakkar cin amanarta, ta hanyar son wata matar. To wallahi ko ma wace ce sai ta lalata rayuwarta, sai ta ruguza mata farincikinta. Sai ta zamo sanadiyyar da za ta saka ta tsani kowanne namiji a rayuwarta. Ɗaukar plate ɗin da ta gama zuba abinci cikinsa ta yi, kai tsaye ta wuce parlourn, inda Ummee da Farouk ke zaune. Kai tsaye ta ƙarasa ta ajiye a gaban Farouk ta ce "Yah Farouk ga shi." Sai da ya ɗan ɗaga idanunsa a nutse ya kalle ta sannan ya ce "Sannu." Daga haka ta koma kan kujera ta zauna. Ita a ɓangarenta sai ta ce abin da ya faru daɗi ya yi mata, saboda yadda Ummeen tata ke zama a gida kullum. Idan ta tashi daga bacci za ta gan ta, kai ko me ta gama cikin gidan za ta ga Ummeen tata a zaune kusa da ita. Ita kuwa me ya fiye mata wannan? A gefe guda kuma tun ɗazu ta kasa manta wayar da ta yi da wannan mutumin. Haƙika maganganun da ya yi mata sun yi mugun tasiri a ƙwaƙwalwa har ma da gangar jikinta. Ba ta ga dalilin da zai saka Khaleed ya ci gaba da hana ta sukuni ba. Me ya sa ba za ta goge shi a gabaɗaya rayuwarta ba? Shi yanzu haka fa ƙila ma ya manta da ita ya ci gaba da rayuwarsa kamar bai taɓa sanin ta ba. Me ya sa ita ma ba za ta goge shi daga tarihin rayuwarta ba? Gabaɗaya ta ci gaba da rayuwarta kamar ba ta taɓa haɗuwa da wani mai sunansa ba? Ita sam ba ta so ma wayar da suke ta katse ba, don ba ƙaramin kwantar mata da hankali ya yi ba. Irin kwantar da hankalin da babu wanda ya yi mata shi. Tun da kowa laifin abin da ta aikata yake gani. Sai ga shi shi wannan bawan Allahn sai kwantar mata da murya yake yi, yana ba ta shawara, yana kuma ƙara wa da daɗaɗan kalaman da suka sake kwantar mata da hankali. Daidai lokacin da Abee ya shigo ɗakin da sallama ɗauke a bakinsa. Duka suka amsa kusan a tare. Bayan ya nemi waje ya zauna yaran suka sake gaishe da shi. A hankali Janan ta miƙe don shigewa ɗakinta, don tun da abin nan ya faru wannan good time ɗin da suke da Abeen suka daina yin shi. Ita yanzu gabaɗaya ma daga ta ga Abeen sai ta ji kuka ya taho mata. "Ayshatou." Ya faɗa yana kallon ta. Sai da ta juyo sannan ta ce "Na'am Abee." "Ina za ki je?" Ya tambaya har lokacin yana kallon ta. Sai kawai ta yi murmushi tana ɗan sosa gefen wuyanta ba tare da ta furta komai ba. Sarai ya fahimci ita kanta ba ta san inda za ta je ba, don haka ya ce "Dawo ki zauna mu yi magana." Sai ta lumshe idanunta sannan ta koma ta zauna a hankali. Bayan kamar shuɗewar mintina biyu Abee ya ce "Ayshatou, kullum Ummeenki na sanar da ni irin roƙon da kike yi a kan makaranta bayan ba na nan. To ina so ki buɗe kunnenki da kyau ki ji ni." Sai ta jinjina kai tana jin wata ƙwalla na taho mata, kafin ta ce "To Abee." "Za ki ci gaba da zuwa makaranta in sha Allah. Sai dai a wannan karon dole ki zaɓi ɗaya, auren ko kuma karatun. Idan kin zaɓi karatun ki ci gaba da zuwa makaranta, zuwa lokacin da kika shiga aji ɗaya na jami'a, zan bar ki ki fara kula samari. Idan kuma tun yanzu kin zaɓi aure, sai ki turo mini wanda kika zaɓa ɗin ya zo mu yi magana." Kafe ta da idanunsa Farouk ya yi bayan gama saurarar abin da Abeen ya faɗa, burinsa ɗaya, ya ji amsar da za ta fito daga bakin ƙanwar tasa. Zuwa can ta buɗe baki da ƙyar ta ce "Abee ai na faɗa wa Ummee. Karatu nake so." Lumshe idanunsa Farouk ya yi lokaci guda yana sauke ajiyar zuciya tare da fesar da wata iska daga cikin bakinsa. "To ma sha Allah. Sai ki fara shiri." Cikin tsananin farinciki ta zube a ƙasa, wani irin kukan farinciki na ƙwace mata ta shiga faɗin "Na gode sosai Abeena, Allah Ya saka da alkairi, Ya ƙara maka girma. Na gode Abeena." Murmushi dukkansu 'yan ɗakin suka yi. Ko babu komai su ma za su samu sauƙi, za kuma su ci gaba da ganin dariya da walwalar AyshaJanan ɗin, wadda ta ɓace a cikin kwanakin nan. Babu daɗewa wayar Ummee ta shiga ruri. Sai da ta ji zuciyarta ta buga ganin mai kiran. Sai dai ganin hankalin kowa ya dawo kanta ya sanya ta miƙewa tana amsar wayar. Ta fi mintina biyar tana yin wayar, lokacin da ta dawo cikin parlourn Farouk da Janan duk sun koma ɗakinsu, sai Abee kawai da ke zaune yana danna wayarsa. Tun kafin ta

Chapter 14 of 24