Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
halitta shashashar banza da wofi." Ta yi maganar tana kai mata duka. Sai a lokacin sannan ta miƙe, tana ci gaba da zunkuɗa bakin gaba kamar za ta fashe da kuka. A karo na biyu ta sake kaucewa dukan Innar ta yi gaba lokaci ɗaya tana furta "Saboda Allah sai a hana ka gudanar da rayuwarka cikin sakewa. To idan ban kula su na yi hira da su cikin gidan ba da wa zan yi? Wa yake kula mu ma ballantana mu yi hira? Kuma ma kika san irin kuɗin da zan samu daga wajensu idan na ci gaba da biye musu? Ɗayan fa sabon zuwa ne ma, amma cewa ya yi in dai zan dinga zuwa wajensu zai dinga ba ni kuɗi. Kuma sai ki hana ni? Chaɓ-ɗi-jam. Wa ya ƙi kuɗi?" "Oh ni na shiga uku da Hamida. Yo ni na ɗakko ki da zummar kin yi hankali ashe har yanzu mahaukaciya na ɗauko? Yo mahaukaciya mana. Nan ɗin fa gidansu wanda za ki aura ne, ji 'yar iskar rigar da kika saka kamar ta amaryar da za ta nufi turaka. Duk waɗannan gantalallun abin da kike fafa da su ana gani saboda rashin lissafi shi ne kika fito tsakar gida kina tallan su. Ke mahaukaciyar ina ce? Idan yaron nan ya gan ki kina ganin zai yadda ya aure ki ne? Ai kuma da shi kenan kin ja mana asara. Maza wuce ki je ki canja 'yar iskar shigar nan tun kafin raina ya ɓaci na keta ta tun a wajen nan. Ke ba ki ga da yadda na shawo kan Abbas ya amince zai aura miki Muhammad ba, ke har sai da na haɗa da 'yar barazana, kike ƙoƙarin sakawa ta tashi a banza? To nan ba ƙauye ba ne don iyayenki idan za ki nutsu ki nutsu. Mutanen birni kuma ba na ƙauye ba ne. Idan can kina kuɓuce mini ki je a lalube ki don ki samu kuɗi, nan wallahi gabaɗaya za su lalube ki su bar ki fanko. Idan za ki nutsu ki nutsu, idan kika auri Muhammad ko ma me kike so za ki samu." Ita dai ba ta tankawa Innar ba, don maganganunta sun shiga ne ta kunnenta na dama sun fice ta hagu. Ta yaya ma za ta ga bati ta ƙyale? A ƙauye ma take zuba abin da ta ga dama, ballantana a birni? Ai wallahi sai dai idan Innar ba za ta yi bacci ba. Amma tana yi za ta fice ta je ta nema wa kanta kuɗi. Ita ma Innar ai tana son kuɗin, ko ba ita ta fara nuna mata muhimmancinsa ba tun tana ƙanƙanuwarta ba? "Inna, me yake faruwa ne a nan?" Daddy ya faɗa bayan ya ƙaraso wajen cike da mamaki, yana fatan amsar da Innar za ta ba shi ta ƙaryata abin da ƙwaƙwalwarsa ke saƙa masa. "Babu gaisuwa ne Aminu. To ina wuni?" "Inna barka da wannan lokacin. Aure za ki yi wa Hamida ne?" Ya yi maganar lokaci guda cike da zumuɗin jin amsar da za ta fito daga bakin Innar. Sai da ta yi murmushi sannan ta ce "E." Ta faɗa a taƙaice kamar ta san so yake ya ji fiye da hakan. "Da wa kenan? Ko daga can ƙauyen naku yake?" Sai da ta kalle shi sannan ta ɗan taɓe baki ta ce "A'ah..a'ah, ai ka san komai na Allah ne. Aure dai ya wuce tsakanin Muhammad da Hamida." Kallon ta kawai Daddy yake yi yana ji a ransa lallai tabbas kunnensa ya samu matsala. Idan kuwa har bai samu matsala ba, to tabbas wata gagarumar matsala ta faru a cikin masarrafar tunanin Innar. Aure? Aure tsakanin Muhammad da Hamida kuma? To a garin gaɓa-gaɓa ake ko kuma mahaukata ne su da za su aura wa Muhammad Hamida? Ai wannan ma kwata-kwata ba abu ne mai yiwuwa ba. Sai yanzu ya gasgata maganganun da kunnuwansa suka jiye masa. Kenan da gaske har ma ta yi magana da Baba kuma ya amince? Kenan ta yaya aka yi haka ta kasance? Don kawai ɗan nasa ya kasance mai biyayya a gare shi sai kuma ya zama mai tauye masa haƙƙi? Ta yaya ma za a haɗa shi da Hamida? A wannan karon tabbas zai tashi tsaye, ya nuna shi ma yana da ido a kan Muhammad ɗin, kuma aure tsakaninsa da Hamida ba zai taɓa yiwuwa ba. Ya san halin Inna, ya san ba za ta taɓa roƙar hakan babu wata manufa a ranta ba. Ya riga ya san wace ce ita, ya kuma tsinci kalaman da ta sanar wa Hamida. Idan dai kuwa har yana numfashi, aure tsakanin Muhammad da Hamida ba mai yiwuwa ba ne. Har gaban abada Ammeey ce kaɗai za ta zama mallakin Muhammad ɗin, kuma wadda zai kasance da ita har abada. Kawai sai ya bi Innar da kallo lokacin da ta ɓace wa ganinsa. Ya ja wani dogon numfashi yana jin yadda ɓacin rai ke sake turnuƙe shi. Shi da ma shi ya sa tun da ya ga Innar jikinsa sai da ya ba shi wani abu ne ya kawo ta. Ya gama fahimtar halayenta, komai tana yin sa ne da dalili. A karo na barkatai ta sake kallon Ummeen da ke ci gaba da haɗa kaya cikin akwati. Har ta gama ba ta sake cewa uffan ba, don da farko ta tambayi Ummeen ta ce ta yi shiru kawai. "Idan da akwai wani abu da za ki ɗauka ki ɗakko mu wuce." "Ummee wai ina za mu je?" Ta tambaya jiki a matuƙar sanyaye kamar mai shirin fashewa da kuka. "Janan sabon gidanmu za mu je mu yi kamar sati biyu, sannan sai mu dawo." Da mamaki Janan ɗin ke kallon Ummeen. "Ummee gidanmu kuma?" "Shalele tashi ki shirya, kada mu ɓata lokaci." Babu musu ta miƙe sai dai har lokacin jikinta a sanyaye yake. Bayan wajen mintina biyar ta fito ta ce "Ummee na gama." Daidai lokacin da Farouk ya shigo ɗakin sanye cikin ƙananan kayan da suka matuƙar amsar jikinsa, ya yi kyau kamar me. Hannunsa ɗauke da mukullin motarsa ya ƙaraso cikin ɗakin. A kan Janan idanunsa suka fara sauka, wadda ke sanye cikin doguwar riga da mayafinta da ta yi rolling da shi. Ta yi masifar kyau, irin kyan nan da ke tafiya da mai kallon ta, musamman idan zuciyarsa na cike da begen ta. Da sauri ya janye idanunsa daga kanta yana jin zuciyarsa na ɗan bugawa. Sai ya lumshe idanunsa lokaci guda yana ƙoƙarin saita kansa. Da ƙyar ya iya fuzgo "Ummee ba za ki haƙura ba?" Ya faɗa a nutse yana kallon Ummeen. "A'ah Farouk, gwara na bar gidan nan hankalina sai ya fi kwanciya. Babu lallai ko na ce musu ba na nan su ƙi zuwa. Idan suka zo suka samu ba ma nan za su haƙura su koma. Ba zan iya zama ba Farouk, wuce mu je." Ta yi maganar tana tura masa akwatin kayansu da ta gama haɗawa. Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ja akwatin ya yi waje. Ummee da Janan suka rufa masa baya. A ƙaton gidan nasu mai kyau da ya fi wanda suke zaune ciki ya yi parking na motarsa. Tuni da ma Ummee ta saka an gyare mata shi tsaff. Don haka ko da suka shiga, kai tsaye Ummeen kitchen ta nufa don ɗora musu abin da za su ci. Da ma tun ɗazu Janan ɗin ke jira Ummee ta matsa daga wajen ta samu ta ɗauki wayarta. Don haka tana shige wa kitchen ɗin ta yi azamar ɗaukar wayarta ta tura wa Adam ƙaramin saƙo kamar haka. "Ina fata kana cikin ƙoshin lafiya. Ka yi haƙuri ba za ka sake ji na a waya ba. Saboda da ma wata dabara na yi ya saka muke jin muryar junanmu. To yanzu kuma ba ma ma gida, amma idan dai har na samu dama za ka ji ni. Ina son ka." Ta yi azamar turawa hannunta har karkarwa yake yi. "Janan je ki yi girkin, bari na duba wani.." Maganar tata ta katse saboda yadda Janan ta zabura ta ajiye wayar tana miƙewa. Wanda kallo ɗaya Ummeen ta yi mata ta fahimci ba ta da gaskiya. "Aysha." Ummee ta faɗa tana ƙarasowa inda Janan ɗin take. "Me ya faru?" Ta sake faɗa tana kallon ta. Girgiza kai ta shiga yi, lokaci guda ƙwalla na taruwa cikin idanunta. "Sanar da ni abin da ke faruwa Janan, mene ne kike ɓoye mini." Har zuwa lokacin Janan ta kasa furta komai. Ban da bugu babu abin da zuciyarta ke yi, ga shi kuma ƙwalla ta cika idanunta wadda har ta zamo sanadin da ya saka take ganin dishi-dishi. Daidai lokacin da wayar Ummeen ta yi ƙara alamar shigowar saƙo. Kusan a tare suka kai idanunsu kan wayar. Wani irin bugawa zuciyar Janan ta sake yi a karo na barkatai, lokaci guda hawayen suka fara sintiri a kan fuskarta. Hannu Ummee ta kai ta ɗauki wayar, kai tsaye ta shiga kan saƙon da ya shigo, wanda take kalla cike da mamaki ganin number ɗin Adam. "Na ji babu daɗi sosai, amma babu komai. Allah Ya kawo mana ranar da za mu yi waya ba a ɓoye ba, ba kuma tare da tunanin wani ya gan mu ba. Ni ma ina son ki, son da na san tabbas wanda nake yi miki ya fi wanda kike yi mini." Kusan sau uku Ummee na karanta saƙon cike da tsananin mamaki. A hankali ta ɗaga idanunta ta kalli Janan ɗin da zuwa lokacin hawaye tuni ya gama wanke mata fuska. "Janan." Ta kira sunanta kamar wadda ke a tsorace. Ba ta iya ko da ɗaga idanunta ta kalli Ummeen ba ne, ballantana kuma ta amsa. "Yaushe hakan ta faru?" Ummee ta faɗa cike da mamaki. Don ita dai da gasken gaske ba ta san lokacin da hakan ta faru ba. Tun da ita dai a iya saninta sau ɗaya Janan ɗin ta taɓa yin waya da Adam ɗin. Kamar mai jiran ƙiris kawai sai ta fashe da sabon kuka mai sauti tana zubewa a wajen. "Kai! Ya Hayyu Ya Ƙayyum. Shin me yake shirin faruwa da ɗiyata ne ni kam? Duk ta yaya hakan ta faru? Ya aka yi har kuka saba haka har ta kai ga ya yi nasarar sace miki zuciya?" Ummee ta faɗa jikinta a matuƙar sanyaye, haka zalika muryarta a mugun sanyaye tana ji kamar ta fashe da kukan ita ma. "Ummee ki yi haƙuri don Allah. Ba da saninki ba muke waya da Adam, kuma Ummee har sockets ɗin gida ma ni na lalata don ki kawo wayarki ɗakina in samu damar yin waya da shi. Amma Ummee don Allah ki yi haƙuri ba zan ƙara ba. Zan kasance mai yin duk abin da kika umarce ni na yi. Ummeena ki yi haƙuri don Allah." Zuwa lokacin Ummee ta ma rasa me za ta ce gabaɗaya. Kawai sai ta nemi waje ta zauna a cikin ɗakin, hannunta ɗore a kan goshinta hawaye cike cikin idanunta. Shin me ya kamata ta yi? Me ya kamata ta ce? Tana ji Janan ɗin na ci gaba da kuka kamar ranta zai fita, tana kuma ci gaba da ba ta haƙuri, da sanar da ita a wannan karon da gaske take ba za ta sake saɓa musu ba. "Wannan ba maganar haƙuri ba ne Aysha. Ya zama dole ni da mahaifinki mu yi duba zuwa ga rayuwarki, mu kuma tsaya mu yi nazari mu san abin da ya dace da rayuwarki." Daga haka Ummee ta shige ɗakinta. Sabon kuka ne ya ƙwace wa Janan, ta shiga rera shi kamar wadda aka yi wa mutuwa. Ita kaɗai ta san yadda zuciyarta ke yi mata wani irin zafi, haka zalika idanunta ma gabaɗaya sun yi wani irin ja, ga kuma wani azababben ciwo da suka fara yi mata. Sai dai gabaɗaya hakan bai dame ta ba, babbar damuwarta ita ce yadda Ummeen ta tafi ta bar ta a wajen ba tare da ambaci ta yafe mata ba. Babban abin da ke nuƙurƙusar zuciyarta shi ne damuwar da ta hanga tattare da Ummeen. Shin ita kam ina za ta tsoma rayuwarta, bayan ta kasance wadda ke zama sanadiyyar baƙincikin mahaifi da mahaifiyarta. Shin ita kuwa mene ne sunanta? Me ya kamata a kira ta? Wanne irin tofin ala tsine ya kamata duniya ta yi mata? Ta shafe fiye da awa ɗaya cikin ɗakin ta kasa matsawa ko da nan da can ne. Zuwa can sai ga Ummee ta fito sanye cikin shirin fita. "Tashi ki shirya ki raka ni. In sha Allah daga rana irin ta yau, duk inda zan je tare da ke zan je. Ba zan sake bari ki yi nisa da ni ba, ballantana har wani abu ya ɗarsu a cikin zuciyarki." Ba ta musa ba, ta miƙe jiki a matuƙar sanyaye. Kawai sai ta bi bayan Ummeen, don a shiryen da suka zo gidan take har yanzu. A motar Ummeen da ta riga ta saka aka kawo mata ita tun kafin su zo suka fice daga gidan bayan ta kira Farouk da ya fita saboda kiran gaggawa da aka yi masa a wajen aiki. Tun da suka soma tafiya babu wanda yake cewa ko uffan ne. Ita Janan har zuwa lokacin hawaye sun kasa daina sauka a kan kuncinta saboda yadda ta fahimci Ummeen na fushi da ita, tun da har ta ɗauki wannan lokacin ba tare da ta yi mata magana ba. Kasuwa suka je, Ummee ta fita ta siyo abubuwan da ta san za su buƙata sannan ta dawo cikin motar. Lokacin da take ƙoƙarin shiga motar shi ma ya buɗe ƙofar baya ya shiga, tana zama ya zauna, tana jan ƙofar motar ta rufe shi ma ya ja ya rufe. Kusan a tare Ummee da Janan suka juya suka kalli cikin motar cike da mamaki. Yana zaune a kame idanunsa a kan motocin da ke yawo a kan titi. Ya yin da yake zaune kai ba za ka ce akwai wani abu da ke damun shi ba, idan kuma ba ka sani ba, sai ka yi tunanin ko motarsa ce wannan ɗin ake tuƙa shi. Cikin tsananin mamaki Ummee ta ce "Wane ne kai? Lafiya ka shigo mini cikin mota?" Shiru ya yi kamar bai ji abin da ta faɗa ba, sai ka ce wadda kuma ta yi magana da dutse. Sai suka kalli juna ita da Janan, daidai lokacin da ta sake furta "Lafiya ka shigo mini cikin mota?" Sai a lokacin sannan ya ɗaga fuskarsa da ko kaɗan babu alamar annuri a kanta, ya zube idanunsa a kan Ummeen da har lokacin ke ci gaba da bin sa da kallon mamaki. Mhiz Innocent 08124818273 *♡☆BIYU BABU☆♡* Zahra Yusuf (Mhiz Innocent) YOTA Writers Ass.. Book 1 Pg 24 Kamar wanda ba shi da niyyar cewa ko uffan haka ya yi shiru. Har zuwa lokacin da Ummee ta fara ƙoƙarin buɗe murfin motar. "Kashedi ne ya kawo ni, haɗi kuma da neman matar da kuka haɗa baki da ita don ku ɓata wa mahaifina suna." Cike da mamaki Janan ke ci gaba da kallon MuhammadAali, ya yin da ta ɓangaren Ummee zuciyarta ce ta wani irin bugawa. Cikin ƙanƙanin lokaci ta runtse idanunta tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da harbawa. Ita da ma ta san wani abu makamancin haka ka iya faruwa. Wannan dalilin ne ya saka tun da abin nan ya faru hankalinta ya kasa kwanciya, gabaɗaya tunaninta ta ina za su biyo mata? A nutse ta buɗe idanunta ta zube su a kan MuhammadAalin lokacin da yake faɗin "Ina kika ɓoye matar?" Ya tambaya kai tsaye yana kallon ta. Kamar ba ta fahimci tambayar ba, haka yanayinta ya nuna. Kafin ta kai ga cewa komai ya ce "Kar ki nuna kamar ba ki sani ba, ina kika ɓoye ta? Idan kin sanar da ni, cikin sauƙi za a gurfanar da ita don ta ƙaryata abin da ta yaɗa wa duniya da taimakonki." Girgiza kai Ummee ta yi cikin jin ɗacin maganganun da yake faɗa mata. Da ƙyar ta iya buɗe baki ta ce "Ko kaɗan ba da taimakona hakan ya faru ba. Ban san za ta je ta ƙarasa bayar da labarin duk da mun katse shirin ba. Kuma ban san a kan Shettima ne take bayar da labarin ba, har sai da muka yi nisa, ta yadda cire shi ka iya taɓa inganci da kuma tasirin gidan radionmu." "Ohk, tasirin gidan radionku ya fiye muku a kan ɓata wa wanda babu ruwansa suna?" MuhammadAali ya tambaya cike da takaici. Kafin ta gai ga nemo amsar da za ta ba shi, ya ɗora da faɗin "Ki sanar da ni inda take kawai. Bayan nan kuma zan gargaɗe ki.." Ya yi maganar yana ɗaga hannunsa na dama. Ya shiga nuna ta da hannunsa na kusa da babban yatsa, kana ya ci gaba da cewa "Ko ba yanzu ba, ki guji ɗora abin da ba ki da tabbas a kansa. Kodayake wannan ke ta shafa ma. Abu ɗaya na sani, kada wani tsautsayi ya saka ki sake yin shiri, ko kuma wani abu da ya shafi hakan a kan mahaifina. Yin hakan babban kuskure ne. Idan har kika maimaita hakan, ya nuna ba kuskure kika yi ba, shi kuma wanda ya maimaita abin da ya taɓa aikatawa, ya zama ganganci kenan, don haka za ki ga sakamakon da hakan zai janyo. Mahaifina ba jigari-jigarin mutanen da za ki taɓa ki zauna lafiya ba ne." Ya ƙare maganar tare da kafe yatsan nasa waje guda. Cikin rashin tsammani, kawai sai jin saukar wani lafiyayyen mari ya yi a kuncinsa. Cikin tsananin mamaki shi da Ummee suka ɗaga idanunsu gabaɗaya, suka sauke a kan inda suke da tabbacin daga nan marin ya fito. Kafe Janan da fuskarta ke a ɗinke tsaff ya yi cike da tsananin mamaki, ya yin da Ummee kallon ta kawai take yi cikin tashin hankali da mamaki. Anya kuwa Janan ɗin ce? Ko dai akwai wani bayansu cikin motar? Ta tambayi kanta a lokaci guda. Sai dai tunanin nata ya katse ne, lokacin da ta tsinto muryar Janan na faɗin "Haka zalika ba ka isa ka taɓa mahaifiyata ka zauna lafiya ba. Ai wanda ya raini ɗan kirki shi za a ji shakkar faɗar magana a kansa. Kuma ko ma me ya faru ɗan nasa shi ya janyo masa zagi. Idan yana so kar a sake faɗin munanan kalamai a kan mahaifinsa sai ya canja halayensa, ya zama na gari. Daga nan sai ya gani idan wani zance mara daɗi zai sake tashi a kan mahaifinsa. Saboda haka kamar yadda ka kasa jurewa a zubar wa da mahaifinka mutunci, ka yi kaɗan ka ci mutuncin tawa mahaifiyar a gaban idanuna na ƙyale." Ta ƙare maganar cikin wani irin zafi, zuciyarta ban da bugawa babu abin da take yi. Ita kanta ba ta san tana da irin wannan ƙwarin gwuiwar ba, ba ta san lokacin da ta iya zubo waɗannan kalaman ba. Duk kuma da irin yadda ƙwayar idanunsa ke ci gaba da yawo a kan fuskarta, hakan bai sanya ta janye nata idanun ba. Sai ma kafe shi da nata da ta yi cikin tsananin ɓacin rai. Hannu MuhammadAali ya saka ya buɗe ƙofar motar ya fice. Sai a lokacin sannan Janan ta fashe da kuka tana ɗora kanta a kan guiwarta. Ita kam Ummee bin Muhammad ta yi da kallo kamar wata saƙaguwa. Gabaɗaya ji take kamar ta tafi hutun taƙaitaccen lokaci ne. Ta shafe wajen mintina biyu har lokacin tana sauraron yadda Janan ɗin ke yin kuka, sannan ta sauke ajiyar zuciya. "Janan me kika aikata haka? Me ya sa haka Janan?" Sai a lokacin sannan ta iya ɗaga idanunta da suka yi wani irin jajir ta kafe Ummeen da kallo. "Ummee kina tsammanin na zuba ido ya ci gaba da ci miki mutunci a gabana? Da yatsansa fa yake nuna ki Ummee. Ai hakan na nufin ba shi da tarbiyya ne, kuma wa ma ya sani ko abin da aka faɗa ɗin gaskiya ne. Idan ma baban nasa ƙarya aka yi masa mutumin kirki ne, ai shi ga shi halayensa sun nuna mana wane ne shi." "Amma da ba ki mare shi ba Janan, me ya kai ki don Allah? Ko mene ne ya faru ai laifina. Ni na fara ɗora shiri a kan mahaifinsa, bayan na san irin ƙarfin faɗa a jin da yake da shi a wannan ƙasar. Wannan bai kai laifin da za a tuhume ni ba?" "Ummee duk da haka bai ci a ce an yi miki magana ta haka ba. Ke ma fa uwa ce, kamar yadda yake taƙama da mahaifinsa." Janan ta faɗa a gajiye, cike da fatan Ummeen ta bar maganar gabaɗaya. Aikuwa kamar Ummeen ta sani, sai ta yi shiru kawai tana gyara zamanta kan kujerar da take kai. Ita Janan yarinya ce, babu lallai ta gane abin da take tunani. Idan har ya zo ya yi barazana saboda taɓa darajar mahaifinsa da aka yi, me zai iya aikatawa kenan ga wadda ta taɓa ji kimarsa? Girgiza kai Ummee ta yi cikin rashin sanin abin yi, zuciyarta gabaɗaya a cunkushe. Ta ma rasa me ya kamata ta yi tunani. Ta gefe ɗaya dai, hankalinta ya fi tafiya inda za ta samu Maimuna. Kenan ina ta je ta ɓoye? Idan har da gaske ta ɓoye ɗin, hakan na nufin zai iya yiwuwa ƙarya ne labarin nata. Ko kuma ta ɓoye ne saboda kar mutanen Shettiman su yi mata wani abu ko da kuwa gaskiya ta faɗa a kansa, don suna tsoron kar a ɓata masa suna. 'Allah masani' Ta faɗi hakan a kan laɓɓanta cikin rashin sanin abin yi. Ta ɓangaren MuhammadAali kuwa, tun da ya fito daga motar Zaki ke biye da shi, har zuwa lokacin da yake dab da inda motarsa ke ajiye. "MuhammadAali." Ya kira sunansa da sauri ganin yana ƙoƙarin shiga motar ba tare da ya kula shi ba. Kamar bai san da wanzuwar wata halitta a wajen ba, haka ya faɗa cikin motarsa kai tsaye ya tashe ta. "Muhammad." Shi ne abin da Zaki ke ta faɗa amma ko alamar kula shi bai nuna zai yi ba. Da wani mahaukacin gudu ya figi motar ya bar wajen kamar wanda ke ƙoƙarin tashi sama. Da sauri wanda suke tare da Zakin ya ƙaraso cike da mamaki ya ce "Tafiya ya yi ya bar ka?" "Ga shi kana gani." "Kamar fa marinsa yarinyar nan ta yi." Ya faɗa har lokacin fuskarsa ɗauke da mamaki. Sai da Zaki ya ɗan yi jimm, sannan ya ce "Ni ma na lura da hakan. Amma me ya sa babu wani abu da ya faru? Anya kuwa wannan MuhammadAalin da muka sani ne?" Ya ƙare maganar yana kallon inda motar Muhammad ɗin ta bi. "Ina tantama, lallai tabbas akwai babbar matsala. Ba su ƙara mintina biyar ba kai tsaye suka wuce inda suke da tabbacin za su samu Yallaɓan nasu. Yana zaune shi da Oga, wanda shi ma ya kasance ƙarƙashin Alhaji Maude (Yallaɓa). Tun ɗazu suke jira su ji an zo musu da kyakykyawan labari, musamman ma dai Yallaɓai da ya kasa zaune ya kasa tsaye kamar koyaushe idan ya saka a yi masa aiki. Da mamaki yake kallon su, ganin alamar kamar jikinsu a sanyaye yake. Tun kafin su ƙaraso ya ce "Ina Muhammad? Me yake faruwa?" Ya tambaya cike da zumuɗin jin amsar da za ta fito daga bakinsu. Sai da Zaki ya ɗan sauke ajiyar zuciya sannan ya ce "Wallahi Muhammad ya canja Yallaɓai. Muhammad ɗin da muka gani yau ba shi ne wanda muka sani tuntuni ba. Na ma rasa ta yadda zan yi maka bayanin abin da ya faru. Yallaɓai yarinya ƙarama ce fa ta mare shi, amma bai ɗauki wani mataki ba, bai kuma nuna alamar zai ɗauka ba. Kai daga ƙarshe ma dai abin da ya kai shi ɗin bai kai ga samun sa ba. Me hakan ke nuna mana?" Runtse idanunsa Alhaji Maude ya yi, yana jin wani irin ɓacin rai, lokaci guda zuciyarsa na wani irin bugawa. Shin me ya sa Muhammad ɗin ke ƙoƙarin ɓata rai har haka? Me ya sa yake wahalar da shi kawai don yana son ya ci gaba da aiki da shi? Wanda suke tare da Zaki ya ce "Ni ma na fahimci canjin nasa Yallaɓai tun lokacin da.." "Ya ishe ni haka." Alhaji Maude ya faɗa cikin ɗaga murya. Tsitt

Chapter 18 of 24